Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Ya Haidar ke ƙyara ta, kuma ƙyaran shi ke ƙara mini ƙaunarshi, har gobe ƙyarata yake ya tsane ni, kuma zuciyata har gobe kina ƙara ingiza ni cikin kogin soyayyarshi, meyasa? Me na miki zuciyata? Me na yiwa ya Haidar? Meyasa baya tausayina baya ƙaunata?.......", surutai take ta yi da sumbatu cikin matsanancin kuka mai matuƙar ciwo da ban tausayi. *** Bayan shigewan Husna sashin Haidar, Hajiya kallon zan saɓa miki ta aika wa Nihal da ke tura baki, ta ce, "Nihal ki fita a idona na rife." "Allah ya baki haƙuri Hajiya, amma kin san Ya Haidar daga ni har ita ba ƙyalemu zai yi ba." "Shi ne ai na ce ya kashe ku ma." "Allah ya baki haƙuri." "Amin", Hajiya ta amsa tana hararan Nihal ɗin. Nimra cikin yanayinta na sanyi ta ce, "Wallahi Husna tausayi take bani Hajiya." "Abar tausayi ce amma ga mai imani da ya kuma san darajan ɗan Adam, amma wannan Yaya naku sai dai Allah ya guttural mishi imani da zuciya irin ta mutane ko da kuwa kaɗan ne." "Yanzu Ya Haidar ɗin ne bai da Imani Hajiya?" Nihal ta tambaya cikin rashin jin daɗin yanda Hajiya ke goya bayan Husna bata duba Haidar da abinda yake so. "Nihal what's wrong with you? Ko dariyan da nake muku ne ya sa kikeson raina ni?." "Ni ba haka nake nufi ba Hajiya ki yi haƙuri", faɗin Nihal tana picking ƙiran da ya shigo wayarta, ta miƙe ta haura stairs ta wuce ɗakinta. Hajiya da kallon zan kamaki ta bi Nihal, sannan tayi ƙwafa tare da cewa, "Idan kin gama wayan ki zo ki faɗa wa Haidar ɗin na ce bai da imani, tunda shi ya haifeni ya ɗau mataki." "Allah huci zuciyarki Hajiya, Aunty Nihal neman magana take ji da shi kawai." "Tunda ni abokiyar wasanta ce dole ta nemi magana ta, daga ita har Haidar ɗin zuciyarsu iri guda, yara ko tausayin ƴar uwarsu marainiya basa yi, Allah dai ya shirya mini ku duka." "Amin Hajiyarmu, amma nikam ina tausayin Husna, Hajiya kinga mutanen da ke sonta kuwa? Manyan mutane fa da samari manya yaran manya, kawai dai zuciya da abinda take so ne, shiyasa ta dage sai Ya Haidar, duk da shi ma babba ne ɗan babban mutum, amma Allah a masu neman Husna akwai waɗanda suka fi Ya Haidar kuɗi ma, kyau ne kawai zai gwada wa wasun su, kuma Husna na san ba dan kuɗi ko kyau take son Ya Haidar ba, kawai soyayya ce saboda Allah." "Kuma in sha Allah sai ta aure shi ba, muddin dai ni ce uwarsa bai sauya uwa ba, to sai ya auri Husna da yardan Allah, bazan bar rayuwar marainiyar da aka bar mini ya tagayyara ba, gwanda shi da uwarshi da uban shi", faɗin Hajiya tana ƙwafa, ji take kaman ta ciro zuciyar Haidar ta kankare wata aba wai Sadiya, ta bar Husna kawai, su yi rayuwarsu su biyu kawai, tana matuƙar so da tausayin Husna, amma Haidar ya ƙi bata haɗin kai. Nimra a sanyaye ta ce, "Allah dai ya tabbatar da alkairi Hajiya." "Amin Nimra, in sha Allah kuma Husna alkairi ce ga rayuwar Haidar." "Ai wallahi Hajiya ba dan ba dan ba, ai da ma haɗe su yayi duka ya aura rana ɗaya, da Husna da Aunty Sady." "Alhajinku ne ai ba zai amince ba, nima da hakan ya fi mini, amma ba komai a je a haka, daga bayan ya aurota duk ɗaya ne in sha Allah, idan ya aureta shikkenan ya gama mini komai banda damuwa da shi kuma, albarkata haka za tayi ta bibiyarshi har ya iske aljanna. Hajiya cigaba suka yi da hira ita da Nimra da ta kasance autarta, suna zaune kwatsam suka ga fitowan Husna, Hajiya da mamaki take kallonta, "Ke Husna zo nan, lafiya kuwa? "Husna", Nimra ta ƙira sunanta, amma duk bata amsa su ba ta wuce. Daga Hajiya har Nimra da idanuwa suka bi Husna, sannan Nimra ta juyo a sanyaye ta ce, "Yanzu haka wataƙila wani abun ya mata, Allah ya Haidar tausayinshi sai a hankali kawai." "Hmmn!, da ni yake zancen, ƙyale ta shi Nimra, yanzu tashi ki je ki lallaɓata, na san indai nice to ko na je ba za ta ce mini komai ba, gwanda ke za ta fidda abinda ke zuciyarta ta ji sanyi, ku je sai da safe ko." "Hajiya dan Allah a duba lamarin", faɗin Nimra tana miƙewa tsaye. "In sha Allah zan yi abinda ya kamata Nimra, je ki sameta ko, mu kwana lafiya." "To Hajiya sai da safe", Nimra ta faɗa tana haye stairs, kai tsaye ɗakinsu ta wuce amma bugun duniya tayi Husna ta ƙi buɗe mata, kuma tana jiyo sautin kukanta da sambatunta, sai da Nimra ta ce, "Wallahi Husna ni kaɗai ce ba Hajiya, amma idan baki buɗe ba zan sauƙa ƙasa na ƙirawota ta zo ta sanya ki buɗe wa." Ko da Husna da ke kuka ta jiyo haka, jiki a mace ta taso ta buɗe wa Nimra ƙofan sannan ta koma kan gadota ta kwanta ta cigaba da rera kukanta mai cin zuciya. Nimra ƙarasowa tayi ta zauna gefen Husna tare da fara bata baki, "Husna kina wahalar da zuciyarki, idanuwanki, hawayenki da bakinki, kai har ma da gangar jikinki, idan fa kika taushi kanki kika yi haƙuri wallahi za ki auri Ya Haidar da yardan Allah, ko kina so Hajiya ta fita tsabgarki ne?" Husna cikin kuka ta girgiza kai tare da cewa, "Nimra ba za ki gane ba, ba za ki taɓa ganewa ba, wallahi ko maƙiyi na bana yi wa fatan azabar da nake ji a zuciyata a kan soyayyar Ya Haidar, Nimra tabbas ko aurena Ya Haidar yayi hakan ma ya wadaceni na gode wa Allah,  Hajiya Alhaji da shi kan shi Ya Haidar ɗin, amma Nimra cin fiska babu daɗi, a gabana Ya Haidar ke waya da Aunty Sady, Nimra ashe ba zan ci albarkacin ƙaunar da nake mishi ya mini kara ba? Nimra ya rayuwata za ta ƙare? Ya zuciyata za ta ƙarasa daddagewa a gaba? Ban ce tabbas Ya Haidar idan ya aure ni ya so ni ko ya haɗa jiki da ni ba dan nasan wanna ba mai yiwuwa bane, amma dai ai ya taimaka ya mini kallon rahama, ko sau ɗaya ya kalleni da idon rahama ko ba don son da nake mishi ba, ko dan saboda Allah da kasancewata ƴar uwarshi ƙanwarshi, yanzu Nimra ashe Ya Haidar bai isa idan ya ga ina wahala ina azabtuwa a kan wani haka ya taimaka ya ɗau mataki ya nema mini salama ba? Ashe idan ana sayo soyayya Ya Haidar ba zai sadaukar da wani ɓangare na dukiyarshi ya saya mini soyayyar wanda nake azabtuwa a kanshi ba? Nimra ba sayowa ba, ba a kan kowa ba, a kanshi duk nake shan wannan baƙar azaba amma ya ƙi ya rahamceni, Nimra zuciyata na gaf da bugawa na mutu, ina masifar ƙaunar Ya Haidar." "Ba sai kin faɗa ba Husna, duk wannan na sani kuma kowa ya sani, amma komai haƙuri ake yi, kuma a sannu ake bin shi, Ya Haidar muddin ya aure ki to tabbas zai so ki, mai wuyan ne ya aureki komai zai zo da sauƙi bayan auren, kuma kin ga ba abinda zai hana shi aurenki sai ikon Allah.......", Nimra tausan Husna ta dinga yi cikin kalamai masu sanyi da sanyaya zuciya. "Nimra ina son Ya Haidar kaman zan mutu, kaman na ba shi kyautan rai na." "Ba ma za a kai ga haka ba Husna in sha Allah, soyayya ma ƙaddara ce, to ki ɗauki son Ya Haidar a ƙaddararki kuma Allah ya baki ikon ci, ya mallaka miki shi, kuma bayan kin mallakeshi kiyi amfani da soyayyar wajan haƙuri da shi, yi mishi biyayya da kaucewa ɓacin ran shi, kin ga kuwa kin ci ribar ƙaddararki in kika yi haka, kuma daman abinda ake so da bawa kenan ya cinye jarabawarshi ya jure wa ƙaddararshi, Husna kina da komanki dai-dai gwargwado, kyau, ilimi, nitsuwa, hankali da tarbiya da asali, duk abinda addini ya horar a auri mace saboda shi Allah ya buwayaki da shi, to ki gode wa Allah, domin duk namijin da ya zauna da ke ko da baya sonki to sai ya fara son ki in sha Allah." "Allah ya sa, Allah ya amince, Allah ya yarda, Allah ya tabbar, Nimra idan hakan ya faru komin tsawon rayuwa, ko da na manta ki tuna mini, wallahi zan baki gagarumar kyauta, duk abinda kike so nayi alƙawarin baki muddin Allah ya nufi hakan ya faru." Murmushi mai kyau Nimra ta saki cikin yanayinta na sanyi da sanyin hali, tare da cewa, "Ai kuwa ki shirya cika alƙawari in sha Allah, domin yanzu kaman kin yi bakance ne, wanda kamun ka furta shi mustahabbi ne, amma muddin ka furta kuma Allah ya baka abinda ka yi bakancen a kanshi to ya zama wajibi, Allah ya baki ikon cikawa ya kuma ja kwana mu riske lokacin, Allah tabbatar mana da duk abinda yake alkairi dan isar Annabi SAW." "Sallallahu Alaihi Wasallam, Amin Nimrata." Daga haka Husna ta ɗan ji sanyi a ranta, suka ɗan taɓa hira Nimra na ƙara tausarta, har lokaci ya ɗan tafi suka tashi, Husna ce ta fara shiga toilet ta watsa ruwa ta yi shirin kwanciya, sai da ta fito sannan Nimra ta shiga, bayan duk sun gama, sai da safe suka yi wa juna, sannan kowa ya bi lafiyar gadonshi ya kwanta. Hajiya sai da ta kashe abubuwan wuta da ya kamata, sannan ta wuce nata ɗakin, dan Alhaji bayanan, da yamma ya tafi Abuja.   Ta kammala shirin kwanciyarta ne tana saƙe-saƙen matakin da za ta ɗauka a kan Haidar tun da ya ce shi bai san kara ba, sai da ta gama saƙa komai sannan ta kwanta zuciyarta fes tana addu'an Allah ya dafa mata ya bata iko. ⭐️ RAYFIELD      SADIYA POV         *** Tun da Sadiya suka yi magana da Umma, shikkenan ta ƙoƙarta wajan sanya wa zuciyarta salama, musamman da ya kasance kullum sai ta yi waya da Ya Sadeeq nata, sannan a gefe guda suna kan soye wa da Al-Sad nata, shiyasa ta murje ta yi wani sihirtaccen kyau, ga sihirtaccen ƙamshi da ke tashi a jikinta kamar an yi ɓarin turare, kowa ya kalleta ya san yanzu damuwarta da sauƙi, hakan kuwa ba ƙarmin salama ya sanya a zuciyar Abba, Umma da kuma Mama ba, har su Khalid sun ji daɗin ganin Sadiya ta sauya ta haƙura da damuwan da take sanya kanta. A ɓangaren Umar kuwa kai da fata ya dage wajan laluɓo abinda Sadeeq ke ɓoyewa, office na Sadeeq da ke a companynsu ya yiwa binciken ƙwal uwar daka, haka ɗakin Sadeeq, motocin da yake hawa, wayarshi ma sai da ya bincike tsaf sannan ya kai mishi wayar, amma bai samu burbushin komai ba, a haka har aka ci sati guda, inda Sadeeq ke da sati biyu a asibiti, bikin Sadiya saura sati guda, sannan a wannan satin jama'a za su fara zuwa bikin, musamman Khausar kam a ranan take hanya tare da yaranta, dan dama ta ce ranan Asabar za ta taho. Sadeeq dai a nashi ɓangaren sai dai godiya ga Allah, jiki dai alhamdulillah dan ana shirin sallamanshi ne ma, amma fa a zahiri ne da kuma ƙarfin magani ke nuna jikin nashi da sauƙi, domin a ciki a zuciyarshi ciwon yana nan, musamman da yanzu yake waya da Sadiya kullum bisa umurnin Umma, sai dai idan suka yi waya sau ɗaya a rana kashe wayarshi yake ko ya sanya call forwarded ko ya sanya a flight mode, dan in ba haka ba to Sadiya bata san zancen wai su yi waya sau ḍaya a rana ba, za ta ƙira ne ta kuma sake ƙira, ta tambayi jikinshi sanna ta sanar da shi shirye-shiryen da suke da ƙawayenta waɗanda suka kasance school mate's nata ne biyu, sai wata ƴar anguwarsu guda, sai uku daga Familyn Mama da kuma Babanta. Sadeeq yana son ya daure ya ke sauraran Sadiya ankan shirye-shiryen bikin, tun da daman ta saba shi ne abokin shawararta, amma kuma zuciyarshi a yanzu ba za ta jure wa hakan ba, shiyasa daga zarar ta kawo maganan sai ya datse ƙiran, sannan ya kashe wayarshi, saboda hakan ƙara barazana yake ga zuciyarshi, domin tuni ne gare shi na yana daf da rasa ta na har abada, wanda kuma yake dai-dai da daf da rasa rayuwarshi har abada, domin yana ji a jikinshi ranar da aka ɗaura auren Sadiya da wanin shi, to ranar zai kasance ranar mutuwarshi ne. A gefe guda kuma shirun da Umar ya mishi yana sake ɗaure mishi kai, domin ya san Umar sarai ya san waye shi, Umar murɗaɗɗen mutum ne, kuma mutum ne wanda idan ya sa abu a gaba sai ya ga bayanshi, duk da Aminta da shaƙuwa da ke a tsakaninsu, amma yana gudun zuciyar Umar watarana, duk da dai shi ma yana da nashi zuciyar amma da sauƙi ba kaman na Umar ba.   Tun ranar da Umar ya mishi magana da daddare bai sake mishi magana akan me ke damunshi ba, Umma da Mama da Abba su ke kan matsa mishi akan me ke damunshi, amma su ma ya ce musu ba komai kawai yanayin aiki ne, sai dai ba su yarda ba kuma basu fasa takura mishi a kan tambayar menene damuwarshi ba, amma duk ba ya ta su, ta Umar yake yi, baisan abinda Umar ke shiryawa ba da ya sanya yayi shiru.   Umar zai je ya wuni company, sannan da dare ya shirya ya taho asibiti su kwana, amma ba sa dogon hira da Sadeeq. ⭐️ YUKUBU GOWON AIRPORT JOS. A hankali Umar ke driving har ya ƙarasa inda ya kamata ya adana motar shi ya parker, buɗe murfin motar yayi ya fito, sanye yake da ƙananun kayan da suka yi matuƙar amsar shi, yayi kyau sosai. Sai da ya kulle motar sannan ya sanya hannayenshi a aljihun rigar jikinshi, mai kama da sweater saboda yanayin garin an tashi da ruwan sama yau to ana sanyi, a kamammiyar takunshi ya ƙarasa har in da yake da tabbacin zai samu su Khausar, yana isowa kuwa ya hangi Najla suka yi ido biyu, buɗe hannuwanshi yayi tare da durƙusawa akan guiwanshi guda, ƴar kyakkyawar yarinyar da ba za ta haura shekara biyar ba ta rugo da gudu ta ɗane jikinshi, sai da ya rungumeta sannan ya miƙe da ita a hannunshi, tana dariya ta ce, "Ayoyo uncle U." "Welcome to Jos my girl." Washe ƙananan kyawawan haƙoranta ta yi, har dimple nata da ke one side ya lotsa, yarinyar kyakkyawa ce sosai kuma fara tass sannan ƴar duma-duma ce, ga shi an sha mata dogon riga ta kanti mai kyau da kuɗi, kanta an mata kisto mai shape na heart ya sha beads, ga shi tana da gashi ma sha Allah. "Uncle U, wai Najla kawai ka kalla halan?", faɗin wata kyakkyawar mace mai kimanin shekaru talatin a duniya, kyakkyawa ce ita ma ajin ƙarshe, tana kama da Sadeeq sosai sai hasken fata da ta fi shi, domin ita kana kallonta kana kallon Najla da ke a hannun Umar to ka san ita ta haifi Najla saboda kaman su, kawai Najla ta ɗara ta haske ne ita ma. Umar juyawa yayi yana murmushi ya ƙarisa gabanta yana faɗin,  "Afuwan Sis Khausar,  kin san idan ina tare da wannan ɗiya tawa mantar da ni kowa take." "I can see", Khausar ta faɗi tana hararan Najla da ta lafe a jikin Umar kaman wata ƴar mage. Umar hannu ya miƙo ya amshi baby Nayla da ke hannun Khausar,  domin ita ma sai wage mishi baki take tana miƙa mishi hannu, ita ma kyakkyawa da ita kamar dai Najla, kitson su iri ɗaya, haka kayan jikinsu, ita Nayla bata gama cika shekara biyu ba. "Tunda duk sun maƙale maka bari na ja trolley na da kaina na kai mota", faɗin Khausar tana yin gaba. Umar da yaran duka biyu a hannunshi ya rufa mata baya suka ƙarisa wajan motar, Najla ya aje a seat da ke gefen na direba, sai ya shiga mazaunin direba ya aje Nayla a ƙafanshi, Khausar baya ta shige tana faɗin, "Wannan yara tun da na kawo su duniya suke saka wa ake nuna mini wariyar launin fata, ake nuna mini ƴan ubanci." Dariya Umar yayi tare da yiwa motar key suka fice a airport ɗin suka kama hanyar Rayfield. Khausar ta ce, "Ya shirye-shirye kuma?" "Alhamdulillah ana ta fama Sis, mu samu ita ma Sadiyar mu miƙa ta mu huta." "Uncle U a dai dinga rage wa small Mum ɗin su Najla fa." Caraf Najla ta ce, "Uncle U,  amma ai da ni small Mum za ta tafi ko?" Cikin gwalanti Nayla take faɗin ba da Najla za a tafi ba da ita za a tafi, da surutun nasu ya ishi Khausar, haɗe fiska tayi tare da cewa, "shut up my friends, ko yanzu in sa uncle U ya tsaya mu sauƙe ku a nan, musamman ke Najla." Cunna baki Najla tayi ta yi shiru, Nayla ma shirun ta yi, sai ta maida hankali kan stairy da Umar ke sarrafawa. Khausar ɗan shiru tayi jim, kamar ta haɗiye maganar da ke cikinta game da Sadeeq da Sadiya, sai can kuma ta fasa ta numfasa tare da cewa, "Uncle U... *** Za ku iya samun littafin a waɗannan manhajoji. ●BAKANDAMIYA HIKAYA. ●WATTPAD @Uwarbatoorl96 ●AREWABOOKS. @Uwarbatoorl96 ●WHATSAPP 09161720046 a kan Naira #500. Idan littafi ya zama completel 1k yake in sha Allah. # Hareeyh # 09161720046 # 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩 # 𝙇𝙞𝙠𝙚 & # 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚[07/12/2025, 13:34] Uwar Batoorl✍️❤️🥰: https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980. 💔NAUYIN BAKI....👄💔        Na Uwar Batoorl. 𝗕𝗜𝗦𝗠𝗜𝗟𝗟𝗔𝗛𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗠𝗔𝗡𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗘𝗘𝗠     اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤🤍 🅿️ 23 _ 24 ⭐️ "Uncle U, ni fa kwata-kwata bana gane wa small Mum da Yaya Sadeeq, anya suna lafiya kuwa? Ko ciwon kewan rabuwa da juna suka fara, duk da ma dai na ga ai ba wani rabuwa, dan duk lokacin da kuka so za ku yi wa Haidar magana ku je ku dubo ta, kaman yanda kuke kai mana visiting muma, amma yadda nake jin yanayinsu a kwanakin nan tun da aka saka date na auren nan, Allah sam kamar ba su ba bana gane musu." Taƙaitaccen murmushi Umar yayi tare da cewa, "Ko ma menene dai su suka sani, nidai na ji daɗin zuwanki, domin akwai abinda nake bincikawa da nake buƙatar ki taya ni bincikowa a kwanakin nan kamun dai ranar auren." "Nidai sam bana jin daɗin yadda suke reacting, Allah dai ya sa ta shiga a sa a ya kuma ba su zaman lafiya." "Amin sister." "Uncle U menene kake bincikawa? Fatan dai ba wani matsalan bane?" "Ba dai zan ce matsala bane tunda tukunna ban tabbatar ba, amma sai mun isa gida za mu yi maganar da kyau." Daga haka Khausar tayi shiru tare da ciro haɗaɗɗiyar wayarta ƙirar Samsung, dai-dai ƙira na shigowa wayar nata, «Gentle Man», sunan da ya fito ɓaro-ɓaro, ba ɓata lokaci tayi picking, daga yanayin yadda take wayan kana ji ka san mijinta ne. Umar amsa surutun Najla da baby Nayla ya ci-gaba da yi, cikin nitsuwa yake tuƙin har suka isa gida, horn guda yayi mai gadi ya buɗe mishi makeken gate ɗin da sauri, slowly ya shige da motar cikin farfajiyar gidan, har ya dai-daita sawayen motarshi a ma'adanar motoci, Khausar ce ta soma fitowa tare da sauƙo da trolleynsu, wanda ma'aikatan gidan suka yi saurin isowa wajan motar, cikin girmamawa suka yi wa Khausar sannu da zuwa, tare da yiwa Umar da ya fito shi ma sannu da dawowa, sannan suka ja trolleyn suka yi cikin gidan da shi. Khausar cewa tayi, "Uncle U please ka sauƙe Najla ta tafi da ƙafarta, yarinyar nan kilo gare ta gwanda jaririyata Nayla." "To Allah na tuba mu da muke ɗaga kayan gym's ma, balle kuma yaran da basu shige duka mutum ya ɗage su da hannu guda ba", Umar ya ƙarishe faɗa tare da wucewa gaba yana rungume da yaran, Khausar ta rufa musu baya. Da sallama suka shigo palourn, wanda Sadiya ce kawai a zaune idanuwanta na a kan fankacecen TV da ke manne da bango, hannunta riƙe da wayarta da ke maƙale a kunnenta tana waya da ɗaya daga cikin ƙawayenta na makaranta, wacce ta kasance ita ce chief best nata, mai suna Zarah. Sallaman da Sadiya ta jiyo shi ya sanya ta amsawa, tana mai kau da idonta ga TV ta maida ga ƙofa dan tabbatar da muryan da ta jiyo, wani irin zabura tayi tare da katse ƙiran tayi jifa da wayarta a kan kujera, kai tsaye ta nufi Khausar da gudu, tana isa bata yi wata-wata ba ta faɗa jikinta, dan Khausar tun tuni ta huɗe mata hannu tana sakin murmushi, "small Mum kar ki karyawa officer ni fa." "Ayoyo one and only auntyna, wayyo nayi kewa, nayi matuƙar kewa nayi mugun missing naku, Auntyna sannunku da zuwa." Umar da tun-tuni ya ƙarasa cikin palourn, kuma ya ajiye Najla da take ƙoƙarin sauƙa dan ta je ga Sadiya, sai da ya zauna da Nayla a hannunshi sannan ya ce, "Wai kekam ba kya ji ne? Daga zuwan mutum ko huta gajiya bai yi ba, kin wani ɗale ta kin dabaibaye ta kamar kin zama ƙaramar yarinya, kika ka da ita za ki ji a jikinki." Khausar na dariya ta ce, "Uncle U ƙyale ta dan Allah, nima nayi kewarta mara adadi wallahi, shiyasa na so su Umma su bani ita mu je Abuja a mata gyaran jikin a wajena amma suka ƙi, we miss you more small Mum." Sadiya tura baki tayi jin surutun Umar, tana ƙoƙarin bai wa Khausar amsa, ta ji Najla ta rungume ƙafarta tana faɗin, "Ayoyo small Mum, i miss you da yawa." Sadiya mai da bakin tayi tare da washe shi, ta sake Khausar ta juyo ga Najla ta ɗaga ta sama tare da ɗan cillata tana taune leɓe, saboda Najla ƴar duma-duma ce akwai kilo, tana dariya ta ce, "Ta gidan Small Mum you're highly welcome." "Small Mum, mummy said aurenki muka zo, you're going with me gidanki ko?" Sadiya dariya tayi tare da cewa, "Capital yes darling, tare da ke za a kai mu, Uncle Haidar har da ɗakinki ya miki." "Awnn, I like Uncle H, shikkenan za a kai mu tare, am not going back to Abuja, Daddy zai yi missing na." Sadiya dai dariya ta kuma yi, tana rungume da Najla suka rufa wa Khausar baya, suka ƙarasa suka zauna a kujera, Nayla ma sauƙa tayi a jikin Umar, ta nufi Sadiya tana buɗe hannunta alaman oyoyo, ita ma a ɗauketa. "Ke dai Najla Allah ya shiryaki da ɗan banzan surutun ki", faɗin Khausar tana girgiza kai. Sadiya na ƴar dariya ta taso ta ɗaga Nayla sama, tare da yi mata peck a goshi tana faɗi, "My baby." "Small Mum", Nayla ta faɗa da tsamin maganarta rana washe bakinta. Umar ya ce, "Sister duk kin koyawa yaranmu ƙiran mutane Uncle da first alphabet na sunayenmu." "Haramun Uncle U, aikin Najla ce, nima ita ta koya mini, bakinta na bi har ya kama bakina, iyayi da manyancen Najla da kake gani da yawa suke, Uncle kawai na ce ta dinga ƙiran ku, amma dan tsabar rigima shi ne kowa ta ƙaƙaba mishi farkon sunanshi, ni ai sai dai kawai na sanya wa Najla albarka da addu'an shiriya." Najla tura baki tayi tana lafewa jikin Sadiya, yadda ka san sharri uwatta ke mata ba gaskiya ta faɗi ba. "Small Mum, where's granny's and uncle's namu?", faɗin Najla da ƙaramar muryarta siririya. Maganan Umma da ke sauƙo wa a step's shi ya dakatar da Sadiya da bai wa Najla amsa, "Ma sha Allah, lale marhabun da mutan Abuja, fatan dai ba ki taho mini da kinibabbun yarankin nan ba su zo su addabeni su nemi ƙwace mini miji." Sadiya da Khausar duk dariya suka yi, Umar ya murmusa, Sadiya ta ce, "Sai haƙuri Umma domin kwa dai ga su nan." "Here we're", faɗin Najla da ta miƙe tsaye a kan kujera tana nuna kanta da kuma Nayla da ke jikin Sadiya. Khausar ta ce, "Kwantar da hankali Umma, anjima kaɗan zan yi wa daddynsu waybill nasu." Umma na dariya ta samu waje ta zauna tare da faɗin, "ashe sun zama online products, a to na haƙura su zauna abinsu." Najla sauƙa tayi a kan kujeran ta ƙarisa wajan Umma, Nayla dai tana lafe jikin Sadiya.   Umma ɗaga Najla tayi ta zaunar da ita a gefenta gana cewa, "Kinibabba gidan ƙiriniya fatan kun iso lafiya? Ya kuka baro babanku?" "Lafiya granny, Daddy is fine, and he told me to pass his regards to you." "Mun amsa, turatu mamar turanci, ke kuma mai ƙuya

Chapter 13 of 32