Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
wayar ta na faɗin, "Ina daidai da zuciyarka da shegen kafiya da taurin kanka, idan an ɗaura auren ka sako mini ita a take, kuma duk kuɗaɗen da na kashe sai ka biya ninkinsu." Da yamma Nihal ta shirya dan zuwa Henna partyn Sadiya, sai Hajiya ta hanata tare da rufe ta da faɗa, a kan ba ta son Husna ba ta kishin Husna, idan ba haka ba mai zai hana ta tsaya a yi cocktail partyn da Husna za ta yi, dan dole Nihal ta haƙura da zuwa Henna partyn, ta tsaya wajan su Husna aka yi cocktail partyn. Washe-gari nan ma ta so zuwa Nupe day, amma ƴan uwan Hajiya da suka zo, suka cinyeta da magana, dole ta tsaya aka yi Berom day da ita, kasancewar su ƙabilar Berom ne a nan yankin Jos, kuma sun gabatar da shagalin ranar yaren nasu, cikin ado da al'adun yarensu, kama daga shigarsu, abinci har da waƙoƙin duk na yaren ne.   Haka ranar Waliman ma again Nihal bata samu zuwa ba, baƙin ciki kamar ta haɗiye zuciya, hakan ya sa ta samu Haidar da maganar hanata zuwa da Hajiya ta yi, amma Haidar da yake cike da taƙaicin maganar da Umar ya faɗa masa, zuciyarsa a cunkushe ga rashin waya da Sadiya, hakan ya sa ya ce da Nihal, ta yi zamanta kar ta damu.    A zahiri ne ya faɗa wa Nihal haka, amma a baɗini a zuciyarsa ya ji ba daɗi na haka da Hajiya ta yi, abun ya haɗe masa ga maganar Umar, ga fushi da yake yi da Sadiya, ga kuma abubuwan da Hajiya ke masa, sai dai tattara komai yayi ya aje a gefe ya bar shungullolin bikin kawai a gabansa, don ga gudu ba ja da baya a aurensa da Sadiya. Lamura na ta tafiya har dai ranar Asabar, wacce ta kasance ranar ɗaurin aure, aka ce rana ba ta ƙarya sai dai uwar ɗiya ta ji kunya.   Haidar tun wuri ya shirya, suka nufi masallacin da za a ɗaura auren shi da abokanansa, dan a babban masallacin Juma'a ta garin gaba ɗaya za a gabatar da ɗaurin auren, ko da suka isa ba jimawa Alhaji da ta shi tawagar suka iso, ga su Abba da tawagar sa mutanen Minna, baffanu da kawunai da yayyun su Sadiya.   Saɓanin ko da yaushe da idan Haidar ya haɗu da su Umar ya ke gaisawa da su cikin mutuntawa, fara'a da kuma girmamawa, to wannan karon wani irin kallo yake bin su da shi, musamman ma yadda yake kallon Sadeeq, sai dai saɓanin Umar shi Sadeeq normal fiskarsa yake kuma haka ya kalli Haidar, dan kallo ɗaya ya masa bai sake kallon inda yake ba, kuma fiskar Sadeeq a yalwace da murmushin da ya sake ƙawata shi, ya kuma sake fidda kamalarsa da kamewarsa. Umar wani irin kallo mai wuyar fassara yake aikawa Haidar, saboda ya na tuna maganar da suka yi ranar da ya sanar masa ya yi haƙuri, amma Haidar ya shafe wa idanuwansa toka ya faɗa masa maganganu, wanda ba a karan kansa ne ya dame shi ba, wanda ya faɗa a kan Sadeeq ne ya fi damunsa. Kallon-kallo ke gudana tsakanin Haidar da Umar, har dai aka fara shirye-shiryen gabatar da ɗaurin aure.   Ko da Haidar ya ga mazaunin da Sadeeq ya zauna, ba ƙaramin ɓaci ransa ya yi ba, domin muddin Umar ya ce zai ta da maganar hana sa auren Sadiya a masallacin, to komai zai faru sai dai ya faru, kai komai ma na iya faruwa amma ba zai iya bar wa Sadeeq Sadiyarsa ba, ba ya jin ko zai mutu ne zai bar Sadeeq ya auri Sadiya, kishi ma ba zai barsa ba kar a kai ga son da yake mata. Wani irin kallo yake yi wa Sadeeq, kallo mai ma'anoni da yawa, domin ya rasa kunya zai ce wa Sadeeq ya ji, ko asara zai ce yayi na son yarinyar da ta ɗaukesa fiye da yayanta ciki ɗaya, haka kawai ya dinga nuna shi mutumin kirki ne shi mai son abinda Sadiya take so ne, amma ashe da lauje cikin naɗi, shiri yake ya kassarata ya rusa ta, don ba ko wai yana da tabbacin shi Sadiya take so, daga ƙiran da take masa da saƙo ya san shi take so, ko damuwar da ya ji ranar a muryarta, bai da haufi ba zai wuce a kan maganar Sadeeq ba ne, shiyasa ya haƙura amma sai ya nuna mata muhimmancin sanar da shi halin da ake ciki tukunna. Nisa da Haidar ya yi cikin tunani ya hana shi sanin me ke tafiya a wajen, sai ji yayi ana shafa fatiha, hakan bai kaɗa masa zuciya ba kamar jin da yayi Alhaji na cewa, "Yauwa sai a ɗaura na ita Husna da shi Aliyun, ga sadaki nan." "Whatt? Husna dai?...", maganar da Haidar ya yi a fili ba tare da ya sani ba ya katse saboda kallon da Alhaji ya masa, sannan ne ya san ba a zuciyarsa ya yi maganar ba kamar yadda ya yi tsammani. Wani irin tuƙuƙi Haidar ke ji a zuciyarsa, hakan ya sanya bai jira an gama ida ɗaurin auren ba ya miƙe ya bar wajan, Alhaji bai yi yunƙurin tsayar da shi ba sanin halinsa, sai da aka kammala komai sannan jama'a suka fara ficewa a masallacin. Haidar da idanuwansa ke kan ƙofar, ya na ido biyu da Sadeeq da ya fito ya na sakin murmushi, wani irin sake baƙancewa zuciyarsa ta yi, kai tsaye ya nufi Sadeeq ya na huci, ya na isa ya tsaya a gabansa, a fusace ya buɗe baki tare da cewa... **** MADALLA MA SHA ALLAH MUN KAMMALA BOOK 1 WANDA YA KASANCE FREE. SAI MUN HAƊU DA KU A BOOK 2 NA ƘARSHE IN SHA ALLAH, A NAN ZA MU WARWARE KOMAI. MASU DARAJA HABIBTIES WAI YAYA NE?🤣🤣 KUNA DA TAMBAYOYI DA YAWA KO? DA WA AKA ƊAURA AUREN? HAIDAR BAI MA SAN DA BATUN AUREN HUSNA BA, SHIN YANZU DA AKA ƊAURA ZAI AMSA KO ZAI SAKAR WA HAJIYA ƳAR TA? KUN SAN HAIDAR DA ZUCIYARSA TUNDA GA SHI YA NA LARA SADIYA MA DA YAKE SO😂 ABUBAKAR SADEEQ FA? TO WAI ITA SADIYA A WANI HALI MA TAKE CIKI TUKUNNA? ME KE TAFIYA ME KE FARUWA? TAMBAYOYIN DA YAWA HAR MA DA ƊAURE KAI, BALLE AMSOSHIN, KU DAI KU BIYA 500 NAKU KACAL KU MORE WANNAN TAFIYA, DOMIN HAR YANZU MA TUKUNNA BA MU JI ASALIN SU SADIYA BA BALLE AMINCIN TSAKANINSU DA SU SADEEQ. MU JE ZUWA MASU DARAJA HABIBTIES NA UWAR BATOORL. Sai da kuuuuuuuu🫶❤️ *** Za ku iya samun littafin a waɗannan manhajoji. ●BAKANDAMIYA HIKAYA. ●WATTPAD @Uwarbatoorl96 ●AREWABOOKS. @Uwarbatoorl96 ●WHATSAPP 09161720046 a kan Naira #500. Idan littafi ya zama completel 1k yake in sha Allah. # Hareeyh # 09161720046 # 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩 # 𝙇𝙞𝙠𝙚 & # 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 32 of 32