ta yi wani yunƙuri har Najla ta miƙe ta fice da gudu ta dawo palourn, kai tsaye wajan Mama ta nufa, tana ɓata fiska ta ce, "Granny you beat small Mum ko? Granny ba a dukan babba fa."
"Ai ko Khausar bata wuce duka ba balle Sadiya."
Najla da ta ɓata fiska har da guntun hawaye, juyowa ga Sadeeq tayi tare da cewa, "Big uncle kazo mu rarrashi small Mum, she's crying."
Mama girgiza kai ta yi, domin ta san za'a rina wai an saci zanin mahaukaciya, "yanzu kukan me Sadiya ke yi? Me aka mata? Yarinyar nan dai bata iya samun waje ba, idan ta ga ana lallaɓata baza tijararta take har da salo, to Allah zai dawo da Umar lafiya shi ne daidai ita", Mama ta ƙarishe zancen zucin tana ƙwafa.
Sadeeq da tunda Najla ta ce Sadiya na kuka, wani iri ya ji a ranshi sosai, ji yayi zuciyarshi na mishi zafi da ciwo, sai dai fata yake da addu'an kada ya zama shi ne sanadin kukanta, domin wannan kawai ma ba zai yafe wa kanshi ba, a sanyaye ya ce, "Mama me aka yi mata?"
Ƙwafa Mama ta yi tare da cewa, "Wa ya san me aka mata babana, ita dai ta san me aka mata ko me ta ƙirƙira, sam-sam Sadiya tana da abun haushi da abun cika ciki, amma duk samun waje ne shiyasa, bari Umar ya dawo."
Marairaice fiska Sadeeq yayi tare da sassauta murya ya ce, "A yi mana afuwa Mama kar a haɗa ta da Umar, a dai tambayeta da farko me ke damunta, wataƙila akwai abinda ke damunta shiyasa take kuka, kuma dan Allah Mama in dai saboda magana nane, dan Allah a bari na yafe, a barta a mata abinda ranta ke so, abinda za ta yi farin ciki da shi", ya ƙarishe faɗa cikin jin kunyar Mama.
Numfashi Mama ta sauƙe sannan ta ce, "Babu ta yadda za a yi maganarka ta sa Sadiya kuka, kawai taɓarattace ta motsa, da ma idan ba kai ba waye ma zai iya da halin Sadiya? hali dubu babu na zaɓe duk abun taƙaici gare su, daga taɓara sai rigima, sai shagwaɓa sai shirme da sauransu."
Ƴar murmushi Sadeeq yayi tare da cewa, "A dai yi mana afuwa Mama."
"To, ta ci albarkacin babana, an yafe ba dan halinta ba."
Sadeeq murmusawa ya sake yi, duk da zuciyar shi a cike yake da son gani ko jin me ke damunta, amma rashin sanin a wani hali take ba ƙaramar cunkushe ran shi yake yi ba, a haka suna hira da Mama da raha har aka yi sallama aka shigo, manyan mata ne da yara, kana ganinsu ka san shatar mota suka ɗauko suka taho.
Mama da Sadeeq amsa sallamar suka yi, Mama na murmushi ta ce, "Lale marhabun da mutanen Minna, isowar yamma kenan."
Duk waje suka samu suka zauna, tare da amsa wa Mama sannun da ta musu, Sadeeq cikin mutuntawa ya gaishe da manyan matan, yaran kuma suka gaishe shi, ya amsa, sannan ya miƙe tare da yiwa Mama sallama, ya fice tana jaddada Allah ya ƙara mishi lafiya.
Mama da kan ta, ta ɗauko musu ruwa sannan ta zauna suna gaisawa.
Wacce ke matuƙar kama da Mama a cikinsu ne ta ce, "Ina amaryar ban ga gilmawarta ba? Ko tana gidan Abban nata ne?"
Mama girgiza kai ta yi, tare da cewa, "Sadiya tana ɗakinta, kawai bata jiyo hayaniyarku ba ne."
Ɗaya matar ta ce, "Kulu ƙyaleta ta huta, kin san Sadiya sarai da son jiki, yanzu ga gajiyar hanya sai ta nemi ƙara mana wata gajiyar."
Mama dariya tayi kawai, daga haka suka ci gaba da gaisawa da hirar ya bayan kwana biyu.
**
Sadeeq riƙe da wayar shi a hannun shi ya fito a palourn, yana ƙoƙarin amsa ƙira sai ga Umar ya shigo, hakan ya sa ya fasa amsa ƙiran, ya sanya wayar a silent ya maida aljihu daidai Umar ya iso inda yake.
"Assalamu alaikum bro", Umar ya faɗa yana miƙa wa Sadeeq hannu.
A dake Sadeeq ya amsa tare da miƙa mishi hannu suka yi musabaha, sannan ya janye hannun shi tare da sanya su a aljihu.
"Ka zo zance kenan?", faɗin Umar yana dariya.
Sadeeq taɓe baki yayi tare da cewa, "Da yake yau na fara zuwa gidan ai."
Ƴar murmushi ta nemar magana Umar ya yi tare da cewa, "Ba yau ka fara zuwa ba, kuma ko a baya da walakin goro a miya kake zuwa, amma dai zuwar yau ta daban ce, ina fata kun gama sasanta kan ku?"
"A a jira muke ka sasanta mu."
"Yo ai ba komai a ciki, kai ka sani, na sasanta ku shi ya fi komai sauƙi a wajena, sannan na ɗaura muku aure, na kai maka ita har ɗakinka."
"Za ka aikata", Sadeeq ya faɗa a taƙaice.
Dariya Umar yayi tare da cewa, "Abba ya ƙira ni ɗazu ina office, wai idan an yi sallahn isha'i mu haɗu da ni da kai da shi a sashinka, ina ji dai za mu ƙarisa tattauna yadda shirye-shiryen za su tafi ne."
"So zan jira ka a waje, idan ka kammala sai ka fito."
"Yanzu-yanzu ma kuwa ba ɓata lokaci", Umar ya faɗa tare da ƙarisawa ƙofar shiga palourn, da sallama ya shiga, ya kuwa gaisa da su aunty Kulu cikin fara'a da girmamawa, sannan ya wuce ɗakin shi, a gurguje ya watsa ruwa ya sanya ƙananan kaya kamar dai irn shigar da Sadeeq ya yi, sannan ya fito sai baza ƙamshi yake yi.
A ƙofar gida ya samu Sadeeq, ya hakimce a saman booth na motar shi, ƙarisawa yayi ya tsaya tare da jingina a jikin motar, ya ce, "Bro, ina fata ba za ka jima ba za ka dawo aiki?"
Sadeeq da ke danna wayarshi ya ce, "Tunda an sallamoni a asibiti me ya rage? Zaman me zan yi kuma a gida?"
"Zaman angwanci mana, wannan sati na bikinka ne, after bikinka kuma amarci za ku ci tukunna, dan haka kar dai ka jima."
"Hmmn!", Sadeeq ya faɗi yana girgiza kai, alamar Umar ya yi nisa sai addu'ar Allah ya taro shi.
Suna tsaye a wajan, suna hira jefi-jefi har aka ƙira magrib, hakan ya sa suka nufi masallaci, a can suka yi alwala sannan suka shiga suka bi jam'i aka yi sallah, bayan an idar, suka fito suka koma wajan motar Umar, tattaunawa suka shiga yi a kan abinda ya shafi company, sannan ne Sadeeq ya buɗe baki da kyau yake magana.
Sai da aka ƙira isha'i suka yi salla, sannan suka shige gidan Abba, kai tsaye sashin Sadeeq suka wuce dan ba kowa a palourn, ko da suka shiga sashin, sun samu abinci an kawo an jere, suka zauna suka ci, Umar ya tattare kulolin ya mayar kitchen na Umma, ya fito a kitchen ɗin kenan sai ga Abba na sauƙowa daga bene, hakan ya sa Umar ya dakata har Abba ya sauƙo, cikin girmamawa ya ce, "Barka da dare Abba."
"Yauwa Umaru barkanmu, ina shi Abubakar ɗin?"
"Yana sashin shi."
"To muje, dan wajanku za ni dama", faɗin Abba yana mara bayan Umar da yayi gaba.
Da sallama suka shigo sashin, Sadeeq da ke danna wayar shi, amsawa yayi tare da ɗan muskutawa ya gyara zama saboda ganin Abba, a ladafce ya ce, "Barka da shigowa Abba."
"Yauwa Abubakar, barkanmu dai, ya ƙarfin jikin?"
"Alhamdulillah Abba."
"Ma sha Allah, Allah ya ƙaro sauƙi da ƙarfin jiki."
"Amin Ya Rabbi", Sadeeq da Umar suka haɗa baki wajan amsawa.
Abba gyara zama yayi tare da yin gyaran murya ya ce, "Da farko da kai zan fara Abubakar, ina son naji dalilin da ya sa ka fidda wannar magana da naji a bakin Mamanku da kuma Umar, meyasa ka fidda maganar?"
"Kayi haƙuri Abba", Sadeeq ya faɗa a taƙaice a gajarce yana mai lumshe idanuwanshi.
Abba girgiza kai yayi tare da cewa, "Ba na buƙatar ban haƙurin ka Abubakar, domin ko ma menene kanka ka yi wa, ba wa ni ba kuma ba wa kowa ba, kanka ka cutar, shiyasa ban tambaye ka me yasa ka ɓoye ba, ban kuma tambaye ka me yasa ka yi ruwa da tsaki a lamarin Aliyu ba, bayan ka san kai ma kana son ta, damuwana ɗaya kuma shi na tambaye ka, me yasa ka yi maganar a yanzu?, so kake ka mayar da ni ƙaramin mutum? Ko so kake mutane su zage ni da wanda bai riƙe amana ba ya so kan shi? Tukunna ma ina hankalin ka da tunanin ka da ilimin ka? Ina ka kai su?"
Sadeeq ƙasa yayi da kai, zuciyarshi na zafi, domin ko Abba bai ƙarishe maganar shi ba, to zuwa yanzu ya fahimci makomar shi, hakan ya sa duk bai amsa wa Abba ba, "Kayi haƙuri Abba", haka ya kuma faɗa a taƙaice.
Ƙwafa Abba yayi tare da mayar da kallon shi ga Umar, sannan ya ce, "Kai ka bani amasar da ya kasa bani, me yasa sai yanzu ya ta da maganar?"
Ƙasa da kai Umar ya yi, tare da cewa, "Ka yi haƙuri..."
Dakatar da shi Abba ya yi, ta hanyar ɗaga mishi hannu, ran shi a ɓace ya ce, "Ba na son haƙurin da kuke bani, idan haƙurin mai muhimmanci ne kuma na gaske, me yasa ku baku yi haƙurin ba kun bar wannar magana? Me yasa za ku ta da wannar magana bayan kun san kwanaki kaɗan suka rage a ɗaura aurenta da Aliyu?"
"Abba ka yi haƙuri, amma laifi na ne ba na Sadeeq ba, ɓoyewan da yake ta yi shi ya sa har ya kwanta ciwo, wallahi ko da na fara zargin lamarin, da na same shi da maganar faɗa muka yi da shi sosai, ya nuna mini ba komai a zuciyar shi, idan kuma ina musawa to na nemo hujja, ni kuma hakan ya sa na duƙufa na dinga yi mishi bincike, gida da office da motar shi duk ba inda ban bincika ba, har sai ranar da Khausar ta zo, ta tayani muka bincika muka samo hujja, ko sannan ma ya so musa mini sai da na nuna mishi na san komai sannan yayi shiru, ko da ya faɗa mini dalilin shi na ɓoyewa, na ce zan muku magana, amma yace ba zai auri Sadiya ba muddin bata amince dan raɗin kanta ba."
"To bata amince ba, dan haka babu wannar magana, tun ran gini tun ran zane, ko ma menene to Abubakar shi ya saya da ƙudin shi", faɗin Abba yana aika wa Sadeeq mugun kallo, dan ko shi da kan shi yana jin haushin abinda Sadeeq ya yi, ai babu wanda ba zai so auren Sadeeq da Sadiya ba.
Umar ɗagowa yayi da sauri tare da kallon Abba, ya ce, "Abba wai ita Sadiyar ce ta ce haka da bakinta? Ita ta ce bata amince ba?"
"Sadiya bata faɗa da bakinta ba, amma yanayinta da halin da take ciki ya nuna haka, dan haka bana son takurawa ko tsawwalawa, sannan daga yanzu kuma a nan nake so wannar magana ta mutu kamar ba a taɓa yin ta ba, Aliyun da take so shi zan aura mata da yardar Allah."
Wani irin mashi ne, wani irin kifiya ne mai matuƙar kaifi da dafi ya daki ƙirjin Sadeeq, ya huda har ya isa ga zuciyar shi ya soke shi, a take idanuwan shi da suke a lumshe suka rine da raɗaɗi da zafin da ke a zuciyar shi, hakan ya sanya ya sake runtse idanuwan shi tare da taune leɓen shi, kan shi na wani irin sara mishi, abinda ya guda kenan tun farkon fari, da a kan ya amshi tabbacin Sadiya bata son shi daga bakinta, ya gwammace ya mutu yana ɓoye soyayyarta, wannan son da take mishi na Yaya da ƙanwa ma ya wadace shi, amma yanzu me Umar ya ja mishi? Zai iya jure ciwon nan kuwa?
Umar idanuwan shi a kan Sadeeq, yana kallon reaction na shi, hakan ba ƙaramin sake hasala shi ya yi ba, tare da sake ɓata mishi rai, Sadiya ba? Lallai zai saɓa wa Sadiya abinda bai taɓa yi mata ba.
Abba yana ta faɗan shi da surutu, Sadeeq da Umar duk ba ji suke yi ba, dan kowa ya yi nisa a abinda yake ji a zuciya, da kuma abinda yake lissafasawa, hakan ya sa, sai da Abba ya ƙira sunan Umar, sannan Umar ya ɗan yi fiska kamar da ma yana saurara, a hankali cikin girmamawa ya ce, "Mun ji Abba, in sha Allah kuma shikkenan ya wuce."
"Yauwa haka nake son ji, yadda ka dage ka binciko ka tono maganar, to ka dage ka binne maganar."
"In sha Allah Abba."
"Allah ya yi muku albarka, Allah ya shige gaba a lamuranku, Allah ya baku abinda yake rabon ku, ya tabbatar muku da dukkan alkairai na rayuwa da bayanta, kai kuma Abubakar, ka sanya salama da haƙuri a zuciyarka, tun farko dama a kan turbar haƙuri kake tafiya, dan haka sai ka sake ƙawata turbar da haƙuri fiye da a baya."
Murya ƙasa-ƙasa kuma can ciki, Sadeeq ya amsa, domin babu ma wanda ya ji abinda ya faɗa, kawai sun ga leɓenshi ya motsa ne.
Sai da Abba ya sake yi musu faɗa da nasiha, tare da sanya musu albarka, ya kuma yi wa Sadeeq addu'ar ingattacciyar lafiya, sannan ya miƙe ya fice.
Abba na ficewa Umar ya miƙe tsaye rai a ɓace shi ma ya nufi ficewa a sashin, Sadeeq da ke kule da Umar, murya ciki-ciki ya ce, "What did you think you're going to do? Did you want to make another mistake? Ko baka fahimce mu ni da Abba bane? I told you very clear, ba zan aure ta ba idan bata amince ba, Abba ya maimaita maka ba zai aura mini ita ba tunda bata amince ba, so after all this what are you going to do? Ka wani tashi a zafafe a fusace kamar mayunwacin zaki, abeg malam ka koma ka zauna, kai ka ja komai ai, you already know the truth, ignoring nashi kawai ka yi, but the word «some secrets are meant to be secrets forever» gaskiya ne, wani abu idan an ɓoye shi, a bar shi a ɓoyen shi ya fi alkairi."
"What's said in the room, stay's in the room, right?" Umar ya faɗa yana kallon Sadeeq.
"You already know", calmly Sadeeq ya faɗa yana lumshe idanuwan shi, cikin jin zafi da raɗaɗin da yake har yanzu a zuciyar shi, ko maganar da ya yi kawai ya yi ne saboda Sadiya, he definitely knows muddin Umar ya tafi gida a yanzu, to duka ma zai iya yi wa Sadiya, and Mama won't stop him, tunda duk suna kan ra'ayi guda ne, he's the cause of everything dole ya taushi Umar, duk da nashi ran ma da ciwo.
Umar murmushin gefen baki ya yi tare da cewa, "Ba irin wannan ake nufi da sirrin da za a bar shi a sirri har abada ba", iya haka Umar ya faɗa ya hanzarta ya fice ba tare da ya bi ta kan ƙiran sunanshi da Sadeeq ke yi ba.
Sadeeq kuwa tun yana ƙiran sunan Umar a hankali, har ya ɗaga murya, amma ko waiwaye haka Umar ya fice, hakan ya sanya Sadeeq dafe kan shi, ba ya ganin laifin kowa sai na shi, ko me ya faru shi ne sila, shi ya ja komai kamar yadda Abba ya faɗa, ko ma menene to shi ne ba kowa ba, hakan kuwa bai sanya Sadeeq yin da-na-sani a kan soyayyar Sadiya ba, balle kuma ɓoyewan da yayi, da-na-sani ɗaya ya yi shi ne na gaza haƙuri har ya faɗi ciwon da ya yi silar fallasa komai, lallai ba iya magana ba ce zarar bunu idan ta fito bata komawa, hatta da wasu abubuwan da mutum ke yi, to kamar amai ne ta yadda idan ka yi ba za ka lashe ba, ka yi su kenan kuma ba ta yadda za ka mai da lokaci baya balle ka goge su, amma da ana yi to da ya mai da lokaci baya ya goge wannan ciwo da yayi, ya daure dan kar a zo wannan gaɓar ma.
**
Umar sai da ya shigar da motar shi harabar gidan, sannan ya ƙarasa ciki, lokacin ba kowa a palourn, Mama tana ɗakinta da su aunty Kulu, Sadiya kuma tana ɗakinta da sauran yaran, dan Khausar ta zo ta ɗauki Nayla da Najla sun tafi gidan Abba a can za su kwana.
Sadiya ta daure ta fito ta yi wa su aunty Kulu sannu da zuwa sun gaisa, amma ba raha kamar yadda aka saba, hakan kuwa ya sa su aunty Kulu suka tambayi Mama dalili, amma ta ce musu ba komai kawai rigimar Sadiya ce ta motsa, suka yadda a kan haka suka ƙyale ta.
Haidar ya ƙira Sadiya a daidai domin tana tare da su aunty Kulu, yana sanar mata za a kawo lefe gobe talata, ita kuma ta sanar wa su aunty Kulu, sannan ta miƙe ta koma ɗakinta, suka ci gaba da wayarsu, in da Haidar ke tambayar ko lafiya ya ji muryarta haka, amma ta ce mishi lafiya ba komai, juyin duniya ya yi ta faɗa mishi menene ya sanya ta kuka, dan ya ji alamar haka a muryarta, amma Sadiya ta ce nan duniya ba komai, hakan ya ɓata ran Haidar, ya kuwa kashe wayarshi, ta ƙira ta ƙira bai ɗauka ba, ta yi saƙo bai yi reply ba, hakan ya sake dagula mata lissafi ƙwarai, ta sake fashewa da wani kukan ciki-ciki, saboda kar yaran da suka zo da su aunty Kulu su ji kukanta, sai dai ta makaro dan masu wayon sun fahimci kuka take yi, amma ba wanda ya ce ƙala.
Umar kai tsaye ɗakin Mama ya nufa da sallama, ya yiwa su aunty Kulu barka da dare, sannan ya ce da Mama ta ɗan zo, ba musu Mama ta taso ta fito, tana kallonshi ta ce, "Umar me ya faru? Lafiya na ga kaman ranka a ɓace?"
Ƙwafa Umar ya yi tare da cewa, "Mama kina jin abinda wannan yarinyar ta yi ba, wallahi Sadiya ba ta da hankali, har za ta nuna wa Abba bata son Sadeeq, bata yarda da maganar shi ba, yanzu ga shi Abba ya ce ba zai aura wa Sadeeq ita ba a bar maganar.....", ya ƙarishe tare da labarta mata yadda suka yi da Abba.
Ba iya Umar ne ran shi ya ɓaci ba, don na Mama ya fi na shi ɓacuwa, hakan ya sa ta ce, "Wato munafurcin dai da Sadiya ta je ta ƙulla ya hana ta fitowa yau, ta wuni a ɗaki kamar mace mai jego, ni Sadiya za ta watsa wa ƙasa a ido ta bai wa kunya? Ni dai?"
Umar ba tare da ya ce komai ba ya nufi ɗakin Sadiya, dan ya sake hasala ne, yana shiga ya yi da yaran magana su tashi su fice, sumui-sumui suka fice a ɗakin daidai Mama ta shigo.
"Sadiya", Mama ta ƙira sunan Sadiya rai a ɓace, tun kamun Umar ma yayi magana.
Sadiya da tun shigowar Umar hantar cikinta ta kaɗa, wani kukan ta fashe da shi mai ƙarfi lokacin da Mama ta ƙira sunanta, musamman da ta ji ran Mama alamar a ɓace.
"Za ki haɗiye kukan nan ne ki tashi ki bai wa mutane amsa, ko kuwa sai na zo wajan na yi ƙasa-ƙasa da ke, shirmammiya kawai wacce bata san ciwon kanta ba, wato ana miki gata kina botsarewa", Umar ya faɗa a ƙufule.
Ƙwafa Mama ta yi tare da cewa, "Ka dai haifi yaro ne amma sam baka haifi halinshi ba, idan ba haka ba yo Sadiya har in ba ki misali da kai na, amma ki ƙeƙeshe idonki ki je ki barbaɗa abin kunya, ke yanzu baki ji kunyar cewa Abbanku ba kya son ɗan shi ba?"
Sadiya da ta tashi ta zauna tana kuka, ƙasa da kanta ta yi bata ce komai ba.
"Keee! Ba da ke ake magana ba ne da ba za ki amsa ba?" Umar ya faɗa yana daka mata tsawa tare da aika mata wani mugun kallo, yau ba dan ta ci albarkacin maganar Abba da kuma Sadeeq ba, da sai ya sauya mata kamanni, har sai ta gane gata ake mata."
Jiki na rawa cikin muryar kuka, Sadiya ta ce. "Da..da..da ni ne...."
"Za ki haɗiye kukan nan ne ko sai na sa kin haɗiye da duka?"
Da sauri Sadiya ta girgiza kai, tare da toshe bakinta da tafin hannunta, tana ƙoƙarin haɗiye kukan.
Mama ta ce, "Ke baki ji kunyar cewa ba kya son mai babban suna ba? Da me kika fi mai babban sunan? Ko kuwa akwai abinda yake da naƙasu a kai? In dai na kintata daidai to sai dai shi ya gwada miki abubuwa da dama, ba dai ke ki gwada mishi ba ko wani ya gwada mishi."
Jinjina kai Sadiya ta yi, cikin muryar kuka ta ce, "Ha...ha..ha ka ne...., amma..wal..wallahi..Allah..ni ban ce wa Abba..Abba..ni ban ce wa Abba ba na son Yaya Sadeeq ba", ta ƙarishe faɗa tana sakin marayan kuka a cikin cikinta.
"Shi Abba naku ne ya miki ƙarya ko kuma Yayanki Umar?"
"A..a, Mama."
Umar fiska a haɗe ya ce, "To, uban me kika ce wa Abba idan ba nuna mishi kika yi baki yarda da batun Sadeeq ba."
Sadiya ƙasa ta yi da kanta, murya na rawa ta ce, "Ni kawai ce mishi na yi, na bar mishi zaɓi, na san ba za ku zaɓar mini abinda zai cutar da ni ba", yanzu kam da kuka mai sauti ta ƙarishe maganar, dan Allah ya gani hakan ba ya nufin a zaɓar mata Sadeeq, ita Haidar take nufi, kuma ta san Abba ya kintata daidai, amma su Mama ba za su fahimce ta ba.
Wani kallo Umar ya wurga mata, tare da yin ƙwafa yana kaɗa kai, kana ya juya ga Mama, ya ce, "Tunda ita ishashshiya ce, sai ta kuma komawa ta sanar da Abba Sadeeq take nufi, idan ba haka ba haɗuwarmu na gaba ba zai mata daɗi ba, kuma idan ta kuskura ta ce matsa mata aka yi sai na saɓa mata kamanni, tunda duk dan ita da kuma gobenta ake duk haka."
"Dolenta ma ta koma ta amsa", Mama ta faɗa tana hararar Sadiyar ita ma.
Umar juyawa ya yi ya nufi ƙofa, sai da ya kama handle sannan ya juyo fiska a haɗe ya ce, "Idan kin tabbata wuyanki ya isa yanka to ki kuma faɗa wa Abba abinda kika faɗa, dan wani abu ya samu Sadeeq sanadinki sai kin sha mamaki na", ya ƙarishe maganar yana kallon yanayin da ɗazu Sadeeq ya shiga sanadin maganar Abba, ya san ko maganar da Sadeeq ya tsaya yi mishi kawai ta dauriya ce, ƙwafa yayi tare da ficewa ya banko ƙofar, kai tsaye ya wuce ɗakinta, ba abinda yake yi sai sakin tsaki a kai a kai da kuma yin ƙwafa.
Mama da mugun kallo ta bi Sadiya tare da yin ƙwafa ta ce, "Ki yi abinda kike so kike ganin ya fi miki, abinci kuma ƙin cin shi kan ki kika yi wa, dan ko gawarki ne sai na kai gidan mai babban suna, a matsayin matar shi kamun a wuce a binne ki", iya haka Mama ta faɗa ta juya ta fice ita ma, sannan yaran suka dawo ɗakin, lokacin Sadiya ta shige toilet.
Sadiya kuwa a cikin toilet kuka ta saki take yi bil haƙƙi da gaskiya, da ɓata wa Haidar rai da ta yi ya ƙi sauraranta za ta ji, ko da batun Yaya Sadeeq, da ta fahimci Yaya Umar ya shirya kassarata a kan Aminin shi, Mama kuma wataƙila ta yafe ta a kan mai sunan babanta, "Ya Allah ga ni gare ka, Allah ka sani ka fi kowa sani, Haidar nake so a matsayin miji, sannan duk wannan bai sa na tsani Yaya Sadeeq a matsayin shi na Yayana ba, sam ban ji haushin shi ba, domin ni ba butulu ba ce, na san alkairi, amma tabbas Haidar shi ne mijin da nake buri", ta ƙarishe faɗa tare da ɗaura alwala ta fito, ƙoƙarin saisaita kukanta ta yi, ta buge da nafila a nan bacci ya yi gaba da ita kan darduman tana kukan zuci ga yunwa tana ji.
⭐️
ALIYU HAIDAR POV
Fushi ya yi da Sadiya sosai, domin ƙwarai a kwana biyun nan ba ya gane mata, kuma abinda basu saba ba na ɓoye wa juna damuwarsu, ko yin ƙarya duk ya fahimci yanzu su take mishi, hakan ya sanya ko da ya kashe ƙiran, yana kallon ƙiranta har saƙo amma bai bi ta kan ko guda ɗaya ba, ya ƙarisa shirin kwanciyarshi ya kwanta, ba jimawa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 25 Chapter of 32