Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yana sallamewa Umar ya turo ƙofar ɗakin ya shigo da sallamarshi ciki-ciki, kai tsaye wajan da su Khalid ke zaune ya kalla tare da cewa, "Ku je waje za muyi magana." Sa'ad da Khalid ganin yanayin fiskar Umar kaɗai ya isa sanya su shiga nitsuwarsu, dan haka a nitse suka raɓa tare da ficewa a ɗakin, basu tsaya a bakin ƙofa ba suka wuce harabar asibitin, suna batun Allah dai ya sa lafiya suka ga Yaya Umar haka. Sadeeq ya ji duk yadda Umar yayi da su Sa'ad, bai juyo ba bai ce musu komai ba, ya ci gaba da addu'arshi, sai da ya idar ya shafa sannan ya miƙe, ba tare da ya juya ga Umar ba ya nufi gado ya kwanta kai tsaye tare da lumshe idanuwanshi, yi yayi kaman bai ji abinda Umar ya ce ba, na su Sa'ad su fita za su yi magana. Umar yana tsaye har Sadeeq ya kwanta, hakan bai dame shi ba domin ko suma Sadeeq zai yi ya tashi to sai sun yi magana yau, hakan ya sanya ya ƙarisa takawa zuwa gaban gadon da Sadeeq ke kwance, tare da ajiye box ɗin a gefen Sadeeq, murya a dake ya ce, "Malam tashi ka mini bayani akan wannan box ɗin." Sadeeq bai ko motsa ba, saboda bai taɓa kawo wa a zuciyarshi box nashi bane. Umar da tun da ya shigo yake ƙoƙarin saita kan shi, da danne fusatar shi saboda matakin rashin lafiya da Sadeeq ke a ciki, da kuma kasancewarsu a asibiti, amma ganin Sadeeq na fama da rainin hankali sai ya rasa control, a fusace ya ce, "Shame on you Sadeeq, wallahi in dai kana da kunya to ka ji kunya, Sadeeq ka bani mamaki matuƙa wanda duk da na ga tabbaci da idona, amma ina kan mamaki ne, tare da sake ƙara dulmiya duniyar mamaki, Sadeeq wai soyayyar Sadiya ce ke neman kashe ka? Sadeeq anya ka yiwa Mama adalci? Sadeeq ka bai wa Mama matsayin da ta baka kuwa? Sadeeq mallakar Sadiya shi ne abu mafi sauƙi a gare ka a duniyar nan, amma meyasa ka tsaurara wa kanka da kanka ƙaddararka? Meyasa ka maida sassauƙar ƙaddara zuwa zazzafar ƙaddara, Sadeeq baka ɗauke ni a Amini ba tabbas, baka bani matsayin da na baka ba, Sadeeq ka ɓata mini rai wadda baka taɓa ba, ina jin haushinka ƙwarai matuƙa, Sadeeq me aka yi aka yo Sadiya? Abu mai sauƙi ne kawai ka ce Sadiya kake son aura, ni da kaina na biya maka sadaki, Mama kuma mai mallaka maka Sadiya ce duniya da lahira, Abba da al'umman Annabi su ɗaura aure, me abu mai wahala a nan da har za ka so ka hallaka saboda soyayyarta? Wallahi sai mun fi kowa murna ciki har da kai da Sadiyar, muddin ya zamana kai ne ka aureta, za mu kasance cikin farin ciki da nitsuwa, ta yacce ko da mutuwa ce ta riskemu lokaci guda ni da Mama, to ba za mu taɓa damuwa da Sadiya ba ko tunanin za ta yi maraici, domin kai Sadeeq ka ishe ta uwa, uba, yaya, ƙawa, ɗan uwa, adda, da komai ma ka ishi Sadiya, bata taɓa faɗa mini gaba da gaba ba, amma nakan ji idan tana maganar da wasu, Sadiya fa na ƙaunarka fiye da ni da muke ciki ɗaya, Sadiya na sha jin tana ambatar kai ne duniyarta, Sadeeq meyasa ka yi haka?" Wani irin juyawa kan Sadeeq ke yi, ciwon da yake ji a zuciya yana neman hawa, ga kan shi da ke mugun sara mishi, sannan wani irin nauyin Umar yake ji, domin kaf a maganarshi bai ga inda yayi kure ba, lallai ya cancanci fiye da fushi Umar yayi da shi, domin bai kyauta ba, amma ya zai yi? Ya ya iya da abinda Allah ya rubuto mishi, Sadiya ita ce ƙaddararshi, soyayyarta ce abincin ruhinshi kuma ita za ta zama silar raba ruhinshi da numfashi muddin ya rasa ta, ya tabbata kuma ya aminta da kalmar da ake cewa, "A bari ya huce shi ke kawo rabon wani", domin ga shi yana ji yana gani, nauyin bakin da ya yi da jinkiri ya sanya zai rasa rayuwarshi, domin ita ce rayuwarshi. Umar sake fusata yayi jin Sadeeq ya kuma yi mishi shiru, a hasale ya kuma cewa, "Na ce zan baka mamaki na yi alƙawari, to ga shi na cika alƙawarin, na kawo maka hujjar abinda na faɗa, wanda cikin zargi na faɗe shi, amma da yake zargin nawa gaskiya ne to Allah ya nuna mini, duk yadda ka ɓoye mini ka munafurce ni na tsawon shekaru, to Allah ya fallasa mini ya nuna mini, kuma na gode da ka nuna mini asalin yadda ka ɗauke ni, zan kiyaye kuma da yardar Allah, yadda baka so na shiga lamarinka to ba iya wannan ba, komai da ya shafe ka zan tsame kai na a ciki, yadda kake so haka za a yi, ka riƙe sirrinka na riƙe sirrina, ka yi rayuwarka na yi tawa, amma ka kwana da sanin a yau a kuma yanzu zan koma na shaida wa su Abba komai, kuma ka sani kawai zan sanar musu ne saboda na wanke kaina daga ganin da suke mini, na nasan me ke damunka amma na yi shiru, musamman Mama da take jin kamar ta rufe ni da duka akan haka kawai ta zuba mini ido ne, zan sanar da su ba dan zan sake kutsa kai cikin lamarinka ba, domin ba Aminta tsakaninmu kai ne kuma ka nuna hakan." Sadeeq lallaɓawa yayi tare da tashuwa zaune, shi ma ɗin jijiyoyin kan shi a tashe, idanuwanshi sun kaɗa na halin da yake ciki, ga ciwo ga bayyanar abinda bai shirya wa bayyanarshi ba har mutuwarshi, "Umar", ya ƙira sunanshi murya ba amo sosai. Umar haɗe fiska yayi tamau, tare da cewa, "Bazan saurareka ba Sadeeq, bazan taɓa saurararka ba, domin ba ka da uzuri a wajena, ba wani abu da za ka faɗa mini, Sadeeq ina kan mayen giyar mamakinka, Sadeeq kai fa da Mama a tare kuka raini Sadiya, Mama na yaye Sadiya ya zamana kulawar da take samu a wajanka ya ɗara wadda take samu a wajan Mama ko Umma, balle kuma ni da ban damu da shiga lamarinta ba, Sadeeq in dai tun a lokacin kake ƙaunar Sadiya menene har ya hana ka yin magana, wallahi wallahi wallahi ka ji na rantse maka har uku ba, to da wallahi za a aura maka Sadiya ka raini abarka, tunda dama kai ke rainonta, amma meyasa bayan ka gama shan wahalar rainonta da mata komai, ka raini soyayyarta a tare da ita, sannan dan ragwanci za ka sadaukar da soyayyarta ga wani can daban, wanda ko ciwon kanta bai sani ba balle na cikinta, wallahi Sadeeq kai ba jarumi bane, daga yau kar ka kuma ambata kan ka a layin jarumai, domin jarumi ba zai yi abinda ka yi ba, jarumi wanda ke da madafan iko da komai irinka, to da yanzu haka Sadiya ta jima da ƙenƙeshe ƙoyinshi ɗaya zuwa biyu, sannan fa mamakina ba zai taɓa ƙare wa ba na duk meyasa ka zaɓi yin haka, dan shirme har ka shigewa wani gaba wajan ganin ya mallaki Sadiya, akan me? Saboda me? Kuma a dalilin me? Ko ka taɓa ganin inda gida bata cika ba aka kai dawa?........", masifa kawai da surutu Umar ke yi, ta inda yake shiga ba ta nan yake fita, wanda kuma duk ba dan komai yake yi ba sai dan saboda ƙaunar da yake yiwa Amininshi, domin ba ya tunanin a yanzu da ya san gaskiyar sanadin ciwon Sadeeq, to ba zai yi gangancin wajan ganin ya bar wani ya raba Amininshi da cikon numfashinshi ba, indai yana numfashi to sai Sadiya ta auri Abubakar Sadeeq. Cikin matuƙar gajiya Sadeeq ya dafe kunnuwanshi, da ƙarfi a harzuƙe ya ce, "Enough Umar, ya ishe ka, ya isa." "Bai isa ba Sadeeq, wallahi bai isa ba, domin kai baka isa ka sa nayi shiru ba, zan faɗa wa su Abba kamar yadda na ce, kuma zan aura maka Sadiya da kai na, amma kuma babu ni babu kai, domin bazan iya ci gaba da zama da kai kana munafurtata ba." "Kar ka fara Umar, kar ka soma wannan gangancin, ba zan auri Sadiya ba, kar ka wahalar da kanka, Haidar Sadiya za ta aura", Sadeeq ya ƙarishe faɗa yana lumshe ido zuciyarshi na wani irin harbawa. "Hmmn! Ko da na ce kana son Sadiya musa mini ka yi, you even challenge me for evidence, and i prove it, so a karo na biyu zan baka mamaki, ko ka ƙi ko ka so za ka auri Sadiya, Haidar yake da suna or whatsoever am not fucking care, dole zai haƙura ya bar maka Sadiya." "Umar don't ever try this, ka bar Sadiya ta auri wanda take so." "Abubakar Sadeeq kai Sadiya take so, kuma kai za ta aura, ko kuna so ko bakwa so." Yanayin yadda Umar yayi maganar, da abinda ya ce, yayi matuƙar motsa zuciyar Sadeeq, da har sai da ya sanya Sadeeq ɗagowa tare da zuba wa Umar ido, bai ci gaba da jiyo abinda Umar ɗin ke cewa ba, domin kalma guda ne ke ta amsakuwwa a kunnenshi, yana kuma kan nanata kanshi a ƙwaƙwalwarshi da zuciyarshi, "Sadiya kai take so", me Umar ke nufi? Me ke faruwa? Da gaske Sadiya shi take so?, cikin kamammiyar jarumar muryarshi ya ce.... *** Za ku iya samun littafin a waɗannan manhajoji. ●BAKANDAMIYA HIKAYA. ●WATTPAD @Uwarbatoorl96 ●AREWABOOKS. @Uwarbatoorl96 ●WHATSAPP 09161720046 a kan Naira #500. Idan littafi ya zama completel 1k yake in sha Allah. # Hareeyh # 09161720046 # 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩 # 𝙇𝙞𝙠𝙚 & # 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚 [07/12/2025, 13:34] Uwar Batoorl✍️❤️🥰: https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980 💔NAUYIN BAKI....👄💔        Na Uwar Batoorl. 𝗕𝗜𝗦𝗠𝗜𝗟𝗟𝗔𝗛𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗠𝗔𝗡𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗘𝗘𝗠     اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤🤍 🅿️ 29 _ 30 ⭐️ Sadeeq ya ce, "Umar what did you mean? And me kake cewa? Sadiya ni take so? When did she told you? Kuma a ina ta sanar da kai haka? Umar please keep this as secret kamar yadda nayi keeping nashi for all those year's, Sadiya Haidar take so kuma shi za ta aura." "Mtswww!, na bi soyayyar da ita Sadiyar da Haidar ɗin da mugun gudu, kai Sadiya za ta aura, batun tana sonka ko ba ta sonka kuma kai ka fi ni sani, tunda kai kana sonta." "Sadiya ba ta so na, Haidar take so", Sadeeq yayi saurin faɗa yana katse Umar. Umar taɓe baki yayi har sannan fiskarshi a haɗe, ya ce, "Sai ta mutu da son Haidar ɗin, amma kai za ta aura." "Don't try this Umar, kar ma ka sake faɗan irin haka, na fi son ta rayu fiye da na rayu, ka barta ta auri wanda take so ta rayu da shi." "Lemme tell you Sadeeq, yanzu ina barin nan sai wajan Mama first, in tabbatar mata har da shaidu, ina da tabbacin a take za ta mallaka maka Sadiya, kuma da mace na ɗaura aure to ina da tabbacin a wajan za ta aura maka Sadiya ba tare da na motsa ba, sai dai daga wajan Mama zan wuce wajan mai ɗaura wa Sadiya aure, wato Abba, na sanar mishi da komai da saƙon Mama shi kuma ya shige gaba a ɗaura auren da kai, su kuma waɗancan a ba su haƙuri." "Umarr!", da ƙarfi kuma a tsawace Sadeeq ya ƙira sunan Umar ɗin. Umar ma a tsawace ya ce, "You can't stop me Sadeeq, na faɗa maka ba ka isa ka sa nayi shiru ba, ba ka isa ka sa nayi abinda banyi niya ba, baka isa ka sa na ɓoye munafurtata da kayi ba, duk abinda za ka yi ga fili ga mai doki ka yi, amma sai an ɗaura muku aure da Sadiya in sha Allah muddin ina numfashi." "Wai Umar ina ruwanka da ni? Umar me damuwarka da ni? Ubanwa ya ce ka je ka mini bincike? Akan me ma za ka mini bincike? Waye ya buɗe maka box ɗin?" "Ina da ruwa da kai, damuwata da kai ka samu abinda kake so sai kuma munafurtata da kayi, sannan uban da ya ce ka ɓoye mini halin da kake ciki shi ya ce na maka bincike ɗan rainin hankali kawai, kuma na binciko ka jima baka yi abinda za ka yi ba, ai kai ka ƙalubalance ni a kan hujja, kuma ga shi na kawo maka, batun buɗe box bazan faɗa ba idan kana da ƙarfi ka sa na jiyo ƙamshin barzahu sai na faɗa maka." "Umar a karo na ƙarshe, am warning you, kada ka bari kowa ya ji wannan magana." "Assume it as topic of the day, daily news, or even international newspaper, duk wadda ranka ya so ka ba shi wannan matsayin, domin loudspeaker ne kawai bazan ɗauka ba, but babu wanda ba zai ji maganar nan ba, take Khausar as example domin ta sani kamun na taho ma." Sadeeq ya ce, "Umar don't try me." "Sai na kai ka bango Sadeeq yadda ka kai ni, Sadeeq ka gama raina mini wayo wallahi." "Okay, then go ahead, ka je ka sanar musu, kai ne ni? Ko kai ne baki na? Ba dai ga box ɗin da ka ƙwaƙulo dan shegen gulma ba, to ga box ɗin a wajena idan ka sanar musu sai ka nemo wata hujjar ka basu, domin baka isa ka matse mini baki ba balle har ka saka ni dole na amsa akan gaskiya kake faɗa, kuma duk abinda kayi creating tsakanina da Sadiya na ƙiyayya ta sanadin haka, ka kwana da sanin you'll pay for it." Wata iriyar dariyar rainin hankali ce Umar ya saki, yana nuna Sadeeq ya ce, "Duk sammakonka to ni a hanya na kwana, eh tabbas picture's, letter da sauran tarkacenka suna ciki har ma waya, duk da dai komai na duba wayar ce ɓacin rai ya hana ni tsayawa na duba shi dan nayi plugging nashi a chaji, amma fa ka sani wannan keyn yana hannuna, wanda nake da tabbacin na secret lockern da na gani a home office naka ne ko studying room oho maka, na tabbata zan samu wata shaidar a can, dan haka ka sha zamanka ka rungume box naka da kyau, ban damu da sanin me ke a wayar ba, na drawern ne yanzu next target na, kuma muddin na tafi to ko ma menene a ciki sai na yi presenting nashi wa su Abba, ko da kuwa menene ka ɗauka kawai su Abba sun gama gani, and you should start practicing how to explain your self to Mama. Dammm! Haka ƙirjin Sadeeq ya ba da bugu, jin Umar na tare da keyn wancan lockern, dairyn da ke a ciki yana ɗauke da abubuwan da suka fi wanda Umar ya gani a cikin box, domin ya ji hamdala da Umar bai kunna wayar ba, domin password na buɗe wayar shi ne na buɗe box ɗin, tunda har ya iya buɗe box to zai iya buɗe wayar, shiyasa yake hamdala da bai buɗe ba, amma ba zai taba yarda ko Umar ɗin ya karanta diaryn ba, balle kuma su Abba, Umar ɗin ma wanda ya gani yanzu a box ɗin ya ishe shi tunda ya samu tabbacin abinda yake neman. "Ka shirya yiwa su Abba bayani", Umar ya faɗa tare da juyawa da niyan barin ɗakin. Da sauri Sadeeq ya girgiza kai, cikin dauriya da dakiya ya ce, "Ka tsaya mu yi magana." Umar tsayawa yayi ba tare da ya juyo ba ya ce, "Au!, wai yau za muyi magana kenan? Duk da nake ta bin ka muyi magana muyi magana ta fahimta me kake maida ni? Mahaukaci ko? To ni ma ba zan saurareka ba Sadeeq, ka yi maganarka da su Mama." "Please bro ka dakata mu yi magana dan Allah, tambayeni duk abinda kake so zan baka amsa, sannan zan amince da auren Sa'adiyah amma sai idan ta yarda tana so na, kuma ban hana ka sanar wa kowa ba, amma duk zan maka hakan ne idan ka bani keyn da ke wajanka", Sadeeq ya ƙarishe maganar very gentle yana lumshe idanuwanshi, zai amsa wa Umar komai, ko wataƙila idan ya fidda abinda ke zuciyarshi sanadin haka zai ji relief, sannan zai auri Sadiya muddin ba dole aka mata ba, domin dama fatanshi kenan da burinshi wato mallakarta, batun sanar da su Abba kuma ya san yadda zai yi da su, Mama ba za ta yi dogon fushi da shi ba za ta sauƙo, Abba da Umma idan ya musu bayani faɗa za su mishi kawai wataƙila shikkenan, Sa'adiyah! "Ya Rabbi ka sa tana so na ko da kuwa kwatan-kwacin yadda nake son ta ne, ta so ni ko ɗan kaɗan shikkenan ya wadatar da ni, domin tulin ƙaunar da nake mata ya ishe mu rayuwa cikin lafiya da aminci da soyayya", Sadeeq ya ƙarishe maganar zucin da bai san a fili yayi ba. "Hmm!", Umar ya ce saboda ya ji duk zancen Sadeeq na zuci, duk da kuwa ƙasa-ƙasa yayi maganar. Sadeeq wara idanuwanshi yayi tare da kallon Umar, ya ce, "Bani keyn, sannan ka tambayi komai." "Da haƙora na ciff a baki na, kai baka isa ka mini wayo ba, sai ka gama bayanin sannan zan baka keyn, sannan da ka lissafa kowa banda ni a ciki, wato dai da gaske matsayin da ka bani kenan? Munafurtata da ka yi ba komai bane ko?" Sadeeq mai da idanuwanshi yayi ya kulle, ba tare da ya bai wa Umar amsar tambayar da yayi a kan munafurtarshi da yake claiming yayi ba, kawai ya ce, "Let's get direct to the issue." "Tambayata na daga cikin issuen, so you most answer it first, munafurtata da ka yi baka ɗauke shi a bakin komai ba ko?" "Ban munafurce ka ba, na bari ne kawai akan sai lokacin da na nemi yardarta kamun na sanar da kowa ciki har da kai, but am sorry for that." "Hmmn! Riƙe sorrynka, domin idan aka kammala bikin ku za mu sake zama a kan haka, dole sai na shaƙe ka don ka tabbatar mini Amininka nake ko mara amfani a gare ka." "Ohk, then Allah ya nuna mana lokacin", Sadeeq ya faɗa a taƙaice kaman ba ya son yin magana. "Amin, amma meyasa lokacin da ya kamata ka nemi yardarta baka nemi yardarta ba?" "Na barta ta kammala secondary school ne." "Da ta kammalan meyasa baka sanar mata ba?" "Before ta kammala ta soma kawo mini batun Haidar." "Me yasa baka dakatar da ita ka faɗa mata soyayyarka gare ta ba." "Saboda na fahimci ta soma son Haidar, shi ne farincikinta kuma farincikinta nake so, dan farincikinta shi ne nawa." "Hmmn, Sadeeq kenan, amma dududu yaushe Sadiyar ta haɗu da Haidar?" "Na riga kowa sanin haɗuwarta da shi, ku ne sai daga baya kuka sani." "Amma dan Allah me yasa ka shige wa Haidar gaba? Wannan ai ragwanci ne." "Saboda farin cikinta." "Amma Sadeeq idan ka sanar mini ko Umma za mu ɗau mataki cikin salama, meyasa duk baka yi hakan ba?" Sadeeq ɗan hararan Umar yayi, domin ya tsani tambayoyi iri ɗaya mabambanta, amma ƙoƙarin miƙewan da ya ga Umar na shirin yi, ya sanya shi cewa, "Duk saboda farincikinta ne ban yi haka ba." "Meyasa kuma bayan kana sonta yanzu kake ce mini ba za ka aureta ba?" "Saboda ba nine farincikinta ba, Haidar ne farin cikinta." Umar a ƙufule ya ce, "Farincikinta, saboda farincikinta, dan farincikinta, bla bla bla, wai Sadiya ce kawai mutum? Are you not a human? Sadeeq da gaske ma kuwa kana son Sadiyar nan? Ai indai kana sonta da gaske to za ka so mata rayuwa da kai, domin kai ka san ka isa mijin taƙama da tinkaho ga ko wace mace mai sa'ar da ta samu damar mallakarka, so so ne Sadeeq amma son kai shi ne asalin so, ka so wa kanka ita ba wai ka so mata rayuwa da waninka ba." Murmushin gefen baki Sadeeq yayi, bai shirya wa murmushin ba amma dole sai da yayi, cikin haɗaɗɗiyar muryarsa ya buɗe baki kamar wanda bai son magana ya ce, "A wajena son Sa'adiyah ya fi son kai na, farin cikinta kuma da nake ambata to ya fi mini komai, kuma zan iya ba da komai dan ta samu farinciki, a cikin abinda zan iya bayarwa kuwa to har da sadaukar da rayuwata, tun ranar da Mama ta haifi Sa'adiyah ƙaunarta ya shigar mini ko ina, am 17years lokacin da Mama ta haifi Sadiya, na san so wanda da za a mini auren wuri to na kai aure tun a lokacin, amma tun daga lokacin na ƙuduri aniyar jirarta..." Maganar Sadeeq ne ya katse saboda Umar da ya ce, "And after all this ka jagoranci wani ya samu soyayyarta, so you'll keep on waiting for her kake nufi ko me da ka cigaba da yin shiru? Ko mutuwar da gaske kake shirin yi tunda za ka sadaukar mata da rayuwarka dan farincikinta? Sadeeq you're nonsense, very very nonsense, domin ban ga ta yadda za ka ɓille a wannan shirmen naka ba, ko za ka cigaba da jiranta har Haidar ɗin ya mutu sannan ka aureta? Ko kuwa ya sake ta ka aureta?" "Umar enough dan Allah, magana ya isa, ka yi fatan alkairi dan Allah, in sha Allah idan ta shiga gidanta sai mutuwa ne zai fiddata, ba na son yadda kake tsaurara wasu kalamanka, na faɗa maka ina son ta fiye da kai na." Umar ya ce, "Amin Ya Rabbi, kuma in sha Allah a gidanka za ta mutu", ya ƙarishe faɗa yana miƙewa tsaye. Da sauri Sadeeq ya kalleshi, tare da ɗago hannunshi ya miƙa mishi, alamar ya ba shi keyn. Murmushi Umar yayi tare da sanya hannayensa duka biyu a cikin aljihun jallabiyar da ke jikinshi, ya ɗage kafaɗa tare da cewa, "Ba wani key a wajena, duka tarkacenka suna cikin box naka, in ka so ka haɗiye su ma, na gano abinda zan gano, kuma ko ba hujja na san ya zan yi da su Abba, in Allah ya yarda sai ka auri Sadiya ko tana so ko bata so, ko kana so ko baka so, balle ma ɗan rainin hankali kana mutuwar so, kuma daga yau daga yanzu babban Yaya nake, Yaya sama Yaya ƙasa, Yaya Umar za ka ke ƙirana baki a cike, tunda ka aje kunya a gefe ka ce ƴar da ka kusa haifa kake so ƙanwar bayarka, kuma shirmammiya irin Sadiya, to sai ka ƙarata kai ka sani, Allah ya tabbar da alkairi amma daga yau Yaya za ka ce, kayi biyayya tunda ka zama babban gwaza, na ƙwace girman", daga haka Umar ya juya ya fice bai kuma sauraran me Sadeeq ke cewa ba, domin ya san tabbas sai ya zage shi, tunda ya shammace shi ya nuna mishi keyn na wajanshi, har ya sa ya saki baki yake ta zubo maganganu. "Ɗan iska, zan dawo gidan ne za ka yi bayani", Sadeeq ya faɗa yana jin nauyin da ke a zuciyarshi ya ragu, gefe guda kuma zullumi da tunanin Sadiya ne ya sake gilmawa a zuciyarshi, maganganun da take yawaita mishi na jaddada mishi, cewar Haidar ne farincikinta sai amsakuwwa suke mishi a kunnuwa, hakan ya sanya ya kunna karatun Ƙur'ani tare da ɗaukan box ɗin ya ajiye a gefen pillownshi, he wish maganar Umar ya tabbata kuma cikin son ran Sadiya da amincewarta, domin zai so gabatar mata da abubuwa da dama, sannan ya gwada mata soyayya fiye da wanda take mafarkin samu a wajan wani. Wannan tunanin ma katsewa yayi saboda tuno Haidar da yayi, "Ya Rabb", iya haka ya faɗa tare da watsar da ko wanne tunani ya shiga bin karatun. Umar yana ficewa ya yi da su Sa'ad magana ya kammala za su iya komawa ciki, Allah tsare hanya suka mishi, ya shige mota ya fige ta yayi gida, su kuma suka shige ciki suna Allah kyauta ya sauƙaƙa ko ma menene, ko da suka shiga ɗakin, a kwance suka samu Sadeeq yana bin karatu, sai suka samu waje suka zauna kowa ya cigaba da danna wayarshi. Ko da Umar ya dawo anguwarsu, gidan Mama ya wuce tare da ƙiran Khausar a waya, ba jimawa ta shigo gidan, a madaidaicin harabar ta same shi dan bai shiga ciki ba, da sallama da buɗe ɗaya side na gefen direba ta zauna tare da barin ƙofar a buɗe kamar yadda Umar ma ya bar nashi a buɗe, cikin nitsuwa ta ce, "Uncle U, ya ake ciki? Ya kuka yi da shi?" Tiryan-tiryan Umar ya labarta mata komai, tare da sanar mata abinda yake shiryawa, na sanar wa Mama zuwa

Chapter 17 of 32