Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tsakaninta da Haidar, yarda abu ne mai matuƙar, wuya, muhimmaci da buƙata a ko wacce iriyar zamantakewa, ba ta fatan a rayuwarta ta ƙeta yardar da ko ƙawa ce ta mata balle Haidar nata, Al-Sad nata, natsuwar ruhinta kuma farincikinta, ta kasance kullum ita ke tunatar da shi kada ya barta kada ya yaudareta, shi kuma ya yi alƙawarin ba zai yi ko ɗaya ba, yanzu ita idan ta bar shi me tayi kenan? "Ya Malikul Mulki ga baiwarka Halimatu", ta faɗa a fili daidai ta kai hannunta kan ƙaramin ƙofar gidan ta tura ta shiga da bismilla da sallam, domin duk wannan zancen zucin a tsaye a bakin ƙofa ta yi su, kuma yau ji take gidan ya zame mata tamkar sabo. Mai gadi da sauran ma'aikatan gidan ne suka mata sannu da shigowa, suna haɗa wa da sunan amarya, don Sadiya ba ta da damuwa akwai ƴar raha da su ranar da ta ga dama. Sama-sama Sadiya ta amsa musu sannanta shige palourn gidan da sallama, ba kowa a palourn, hakan ya sanya ya sauƙe gauron numfashi tare da samun waje ta zauna tana karantar wasiƙar jaki, gabas da yamma ya rasa ina za ta hi hanya ta ɓulle mata. ⭐️ ABUBAKAR SADEEQ POV      *** Khalid na gama daidaita sawayen motar, Sadeeq ya fara fitowa cikin kamewa da aji, ƙafafuwanshi ya fara fiddawa waje, tare da lumshe idanuwanshi yana shaƙar daddaɗar iskan gidansu, yayin da a zuciyarshi yake addu'ar Allah ya shiga tsakaninshi da ciwon da zai kuma saka wa ya jima haka a asibiti. Khalid da Umar kusan a tare suka fito, Khalid ya fara fidda tarkacensu da ke bayan boot, mai gadi da Hammadu direba suka ƙaraso da sauri tare da yi wa sh Khalid sannu da dawowa dan basu kula da Sadeeq ba ma, dan har yanzu ƙafafuwanshi ne a waje bai gama fitowa ba. Khalid gaba yayi, yayinda Umar ya zagaya gefen da Sadeeq yake ya ce, "Hey mai ciwon soyayya fito mu shige ciki, ka san yanzu barinka kai kaɗai risky ne, kana iya sake sumewa ka ja wa mutane asara, ka san ba iya amarya tsautsayi ke bibiya ba har da ango, wani abu ya same ka kuwa ka ga ba kanta batun soshalewa." Sadeeq da bismilla ya ƙarisa ficewa a motar, ba tare da ya kalli Umar ba ya ce, "Na san kai ɗan guguwa ne, but bansan ka wuce haka ba, anyway keep on talking like a parrot, if you mistakenly mess up around Mama or Umma, you'll explain very well." Hammadu direba da mai gadi, suna kallon Sadeeq suka washe baki, maganarsu ta hana Umar bai wa Sadeeq amsa, cike da matuƙar farincikinki da murna suka dinga jera mishi sannu, tare da fatan Allah ya sauwaƙa ya ƙara ƙarfin jiki, Sadeeq ya amsa sannann suka wuce ciki da Umar. *** Sadiya tana zaune a palourn shiru-shiru ta yi nisa a duniyar tunani, har Khalid ya shigo bata sani ba, ko hayaniyar mai gadi da musa direba basu fargar da ita ba, sai da Khalid ya aje abin hannunshi ya ƙarisa gabanta, ya yi clapping hannayenshi a gaban fiskarta, hakan ya sanya ta dawo dawo hayyacinta, duk da dai ta ɗan tsorata, ta ɗauka ma ko Mama ce, sai da ta yi tozali da fiskar Khalid yana sakar mata murmushi, sannan ta ɗan tura baki tare da cewa. "Yaya Khalid you scared me." "Haba jaruma Sady baby, ƙanwar Yaya Sadeeq, amaryar Haidar, autar Umma da Abba", Khalid ya faɗa yana ƴar dariya. Sadiya ta buɗe baki da jiyar amsa ma Khalid kenan, sai ga sallaman Umar da Sadeeq, wanda ko mutuwa ta yi ta dawo za ta gane muryoyin nasu, jin muryarsu dukansu biyu lokaci guda wani irin bugawa ƙirjinta ya yi, she have to be happy saboda jin muryar Yaya Sadeeq yana nufin an yi discharge nashi kenan, that's mean he's feeling better, amma a yanzu ba ta da sauran kuzarin ɗin da za ta nuna farin cikinta, she can't. Sadeeq na stepping ƙafarshi cikin palourn, idanuwansu suka gauraye cikin na juna, domin idanuwanta na a kan ƙofar ta kasa janyewa. Wani irin kallon kallo suke yiwa juna, kallo mai ma'anoni da yawa, kallon da kowa da abinda yake kitstsimawa a zuciyarshi. *** Za ku iya samun littafin a waɗannan manhajoji. ●BAKANDAMIYA HIKAYA. ●WATTPAD @Uwarbatoorl97 ●AREWABOOKS. @Uwarbatoorl96 ●WHATSAPP 09161720046 a kan Naira #500. Idan littafi ya zama completel 1k yake in sha Allah. # Hareeyh # 09161720046 # 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩 # 𝙇𝙞𝙠𝙚 & # 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚 [09/12/2025, 19:47] Uwar Batoorl✍️❤️🥰: https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980 💔NAUYIN BAKI....👄💔        Na Uwar Batoorl. 𝗕𝗜𝗦𝗠𝗜𝗟𝗟𝗔𝗛𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗠𝗔𝗡𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗘𝗘𝗠     اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤🤍 🅿️ 37 _ 38 ⭐️ Wani irin kallon kallo Sadiya da Sadeeq ke yiwa juna, kallo mai cike da ɓoyayyiyar ƙauna daga Sadiya ga kuma rauni da jin rashin kyautawa, yayinda Sadeeq ke mata kallon bayyananniyar ƙauna da soyayya tsantsa, tausayi, farinciki, buri da muradin mallakarta, da kuma matsananciyar kewarta. "Ke kin zuba wa mutane idanuwa kamar mayya, are you out of your sense ko kuwa sallamar ce kika mance yadda ake amsawa? Rubbish girl kawai", Umar ya faɗa rai a ɓace, saboda ganin yacce ta wani tsare Sadeeq da idanuwa cikin rashin kunya, wannan tun bata ga makwancin Sadeeq ba kenan, idan ta gani kuwa ai a gaban mutane sai ta nemi rungumeshi, dan shi Umar bai hangi komai a tattare da ita ba sai kewar Sadeeq da ƙaunarsa, kuma ko ma dai menene Sadeeq ne ya ja wa kanshi, ya rasa wa zai nemi mutuwa a kanta sai Sadiya wacce ya kusa haifa, hakan ya sanya Umar yin ƙwafa. Sadiya da sauri ta janye idanuwanta daga cikin na Sadeeq, ta yi ƙasa da kanta idanuwanta na ciko da ƙwalla wanda a yanzu ta rasa ɗaya na menene, na farin cikin dawowan Sadeeq da kewarsa ne, ko kuwa na abinda ke gabanta da bata ma san ta yaya za ta fara tunkara ba, hakan ya sanya zazzafar hawaye ya silalo kuncinta. Khalid da ya kula da hawayen Sadiya, a tausashe ya ce, "Sorry Sady, ai ga Yaya Sadeeq ɗin ya dawo kewa ta ƙare kuka ya fece, Yaya Umar please ka yi haƙuri", Khalid ya ƙarishe faɗa yana marairaice wa Umar, alamar kada ya kuma yi wa Sadiya faɗa ya yi haƙuri. Ƙwafa Umar ya sake yi, yayinda Sadeeq da har sannan idanuwanshi ke a kanta, a hankali ya lumshe haɗaɗɗun kyawawan mayatattun idanuwanshi, sannan ya buɗe su kuma dai a kanta, hawayen da ya zubo a idanuwanta suna faɗa mishi cewa saboda shi ne, hakan ya sanya ya ji zafi sosai a zuciyarshi, murya gently kamar bai son magana ya buɗe baki a taƙaice ya ce, "Umar please." Umar haɗe fiska ya yi ya buɗe baki da niyar sake yin magana, Umma da ta ƙaraso bayan Abba wanda yake tsaye da jimawa a wajan tun shigowarsu, yana kallon duk abinda suke yi da duk abinda ke faruwa da yanayin kowa a cikinsu, Umma katse maganar da Umar yayi niyar yi ta yi ta hanyar cewa, "Ahh!, ma sha Allah, an sallamo ku kenan da sassafen nan? Sadeeq kuna tsaye kuma? Ya jikin? Auta kin shigo ashe?", Umma ta faɗa tana washe baki dan ita bata san abinda ke tafiya a palourn ba. Umar da Khalid ne suka kai dubansu ga stairs ɗin, inda Abba da Umma ke tsaye, Umar dai kallon da Abba ke mishi ya sanya shi shan jinin jikinshi, shi kuma Sadeeq dama sake lumshe idanuwanshi yayi tare da kawar da su a kan Sadiya,  bai kalli wajan su Umma ba, domin haka kawai yake ji a jikinshi, Abba na jifarsu da wani kallo musamman da hawayen da Sadiya ke yi, ajiyar zuciya mai nauyi Sadeeq ya sauƙe a ɓoye tare da juyawa ya nufi kwanar sashinshi. Khalid na shirin yin magana, Abba ya dakatar da shi ta hanyar cewa, "Kada wanda ya ce mini wani abu, ku ɓace ku bani waje, Auta biyo ni ɗakin Ummanki", iya haka Abba ya faɗa ya juya. Sadiya tana jin alamar Abba ya juya, ta ɗago da sauri ta bi bayan Yaya Sadeeq da kallo, ji take kamar ta je gare shi yadda ta saba, amma ba za ta iya ba, a sanyaye kamun ya sha kwanar, ta buɗe bakinta ta ce, "Sannu da dawowa Yaayaana, Allah ya ƙara sauƙi", ta faɗa idanuwanta a kan bayanshi. Sadeeq ɗan dakatawa ya yi, ya kuma juyo kaɗan ya kalleta da wutsiyar haɗaɗɗun gajiyayyun idanuwanshi da suka rine, jinjina mata kai yayi tare da lumshe ido alamar ya amsa kuma ya gode daga haka ya sha kwana ya shige sashinshi, Umar ya mara mishi baya ran shi a ɓace, saboda a ganinshi wannan kamar munafurci Sadiya ke son musu a gaban Abba, tunda dama ƙoƙari suke su lallaɓa shi. Khalid ya dubi Umma ya marairaice fiska tare da cewa, "Wa ya taɓa mana Abba kuma Umma? Shi da zai yi farinciki first born na shi ya dawo lafiya jiki alhamdulillah, sai kuma ya hau mu da fushi." "Ga hanya nan Khalid ban hana ka wucewa ba, kuma ɗakina ba baƙonka ba, ka je ka tambayeshi da kanka", iya haka ta faɗa ta ƙarisa sauƙowa ƙasa. Khalid waro idanuwanshi yayi tare da cewa, "Wah? Caɓ! Ai wane ni Umma, Abba fa idan ranshi na a ɓace kamar zaki haka yake komawa, ganinshi nake kamar sojar da allurarshi ta motsa, dan mancewa yake da ni autan maza ne, dan haka bari na jida basket nan mu je mu karya da su Yaya Umar, dan Yaya Sadeeq matsa lamba ya yi bamu karya ba muka juyo, duk yunwa nake ji kamar zan rasu." "Allah ya shiryeka Khalid", Umma ta faɗa tare da shigewa kitchen. Da, "Amin", Khalid ya amsa, sannan ya ɗau basket ɗin ya nufi sashin Sadeeq. *** Sadiya sallama ta yi a ƙofar ɗakin Umma, sai da Abba ya amsa ya kuma ba ta izinin shiga daga ciki, sannan ta shigo da wata sallamar kanta a ƙasa.   Abba na zaune a bakin gadon Umma, fiskarshi a sake yanzu ba kamar ɗazu a palour ba.   Sadiya a ƙasa ta zauna kan carpet kusa da ƙafar Abba, kanta a ƙasa ta ce, "Barka da safiya Abba", murya a sanyaye cike da girmamawa ta yi mishi gaisuwar tana kuma daidaita kanta. Abba murmushi yayi na tausayinta, sannan ya ce, "Yauwa auta, barkanmu ko, fatan kun tashi lafiya? Ya yaran naku da yayarki?" "Duk muna lafiya alhamdulillah Abba." "To ma sha Allah auta, Allah ya muku albarka ya shige muku gaba a rayuwa ya tabbatar da alkairi a rayuwarku da ta zuri'arku, mu da ku duka kada Allah ya barmu da iyawarmu, Allah ya iya mana ya datar da mu." "Amin summ Amin Abba, Allah ya ƙara girma da lafiya, ya saka muku da aljanna maɗaukakiya." Da, "Amin Ya Rabbi", Abba ya amsa wa Sadiya ya kuma sanya mata albarka yana murmushi, sannan ya numfasa ya ce, "Auta ba sai na miki dogon bayani ba, na san Mamanku ta sanar da ke ko ma menene, da kuma dalilin da ya sa na yi ƙiranki, duk da na ga rabin amasata a yanayinki, amma kuma ina son jin tabbaci daga bakinki, auta kada ki wani kalleni kamar wai ni mahaifin Abubakar ne ki ji nauyin faɗa mini gaskiyar da ke zuciyarki, auta ni mahaifinki ne ba na Abubakar ba, ki saki ranki da zuciyarki ki sanar da ni iya gaskiyarki, bana son ki yi abinda zai dame ki ko za ki cutu, rayuwar aure rayuwa ce ta pleasing kanka ba wai ka daɗaɗa wa wani kai ka cutu ba, saboda kai za ka je ka zauna ba wani ne zai zauna maka ba, kuma idan muka aurar da ku fata muke mutuwa ce kawai za ta raba ku da gidajen mazajenku dun wahala duk daɗi." Sai da Abba ya numfasa, sannan ya ce, "Ki faɗa mini tsakanin Aliyu Haidar da Abubakar Sadeeq wanne zuciyarki ta fi kwantawa da shi? Wanne kika fi aminta da shi? Wa kike ganin kin amincewa ɗari bisa ɗari ya jagoranceki da igiyoyin aurenki?." Sadiya sake duƙar da kanta ƙasa ta yi sosai, hawayen da ta gama gogewa kamun ta shigo, sai ga su sun cigaba da zirya a kumatunta fiye da a palourn, a zuciyarta faɗi take, "Haidar, Haidar nake so Abba, da Haidar na aminta, Haidar shi ne farincikinki na Abba, amma ya za a yi na soma furta maka wannar magana, da nauyi sosai Abba, ina jin kunya da nauyin kasancewa butulu a gare ku da Yaya Sadeeq, kamar yadda ban shirya kasancewa mayaudariya macuciya ga Haidar ba, Abba ina tsaka mai wuya, amma Haidar shi ne zaɓi na a fili da baɗini na." Abba jin Sadiya ta yi shiru, sai ya sauƙe ajiyar zuciya, tare da sake sassauta murya ya ce, "Halimatu Sadiya, ni mahaifine a gare ki, wanda ke muradin jin zaɓin da ƴar sa ta yanke, dan ya cika mata cikin amincewar Allah da yardarshi, Halimatu ki faɗa mini kada ki ji komai, domin babu mai miki dole muddin ina numfashi, abinda kike so shi za a miki in sha Allah." Kuka kawai Sadiya ta fashe da shi amma ta kasa sanar da Abba cewa Haidar take so, kamar yadda take jin ba za ta taɓa iya furta ta yarda da Sadeeq ba, ko da kuwa kasheta za a yi. Kukan Sadiya a wajan Abba yana nufin abinda yake tsammani ya tabbata, kukanta na nufin Haidar ne zaɓinta kamar yadda ya yi tsammani tun farko, kukanta na nufin bata zaɓi Sadeeq ba amma tana jin nauyin amsa mishi, kuma sam-sam Abba bai ji zafinta ba, asalima haka ya mishi daɗi ya kuma burge shi, domin Sadeeq ya koyi hankali ya kuma tabbata da abinda ake cewa na kada mutum ya yi wasa da damar shi, duk ƙanƙantarta, domin wani lokacin sau ɗaya mutum ke samun wata damar a rayuwa, opportunity comes at once, hakan ya sanya ya murmusa dan ya ji daɗin da Sadiya ba za ta sanya ya ji kunyan manyan mutane ba, da kuma sauran al'umma, cikin kamalalliyar dattijuwar muryarshi irin ta mahaifi ga ɗiyarshi ya ce, "Allah ya miki albarka Halimatu, Allah ya tabbatar da alkairi a zaman aurenki da Aliyu, na fahimceki auta, kuma in sha Allah hakan za a miki, kuma haka zai zame miki alkairi mara iyaka a rayuwa, tashi ki je ko." Wani irin sanyi jikin Sadiya ya yi, zuciyarta ta karye sosai, nauyin Abba da Umma suka yi wani irin rufe ta, yanzu Abba ya fahimci bata yarda da maganar ɗan shi ba, hakan ya sanya ta tsagaita kukanta, ta ɗan ɗago gajiyan shanyayyun idanuwanta da suka kumbure zuwa yanzu saboda kuka, da zazzaƙar sansanyar muryarta ta ce, "Ka yi haƙuri Abba, ku yi haƙuri ku yafe ni, kuma Abba ba na nufin Haidar, Abba kawai na bar muku zaɓi, wuƙa da nama, duk abinda kuka yanke a gare ni alkairi ne in sha Allah, kuma zan yi biyayya da yardar Allah", iya haka Sadiya ta faɗa ta miƙe ta fice tana kuka mai cin zuciya da ƙaryar da ta yi, domin gaskiyar ita ce ko an aura mata Sadeeq to ba za ta iya yi mishi biyayya ba balle ta yiwa iyayensu, zunubi kawai za ta dinga kwasa na saɓa wa Allah da tauye haƙƙoƙin mijinta muddin ya kasance Sadeeq ne. Abba da kallo ya bi Sadiya har ta fice, sannan ya saki murmushin su na manya, a fili ya ce, "Na fahimci zaɓinki Halimatu, kuma Haidar ɗin za a aura miki da yardar Allah,  daga haka ya fice a ɗakin Umma ya wuce ɗakinshi. Sadiya kuwa tana gangarowa downstairs ta haɗu da Umma, duk da nauyi da kunyar Umma da take ji a yanzu, amma Umma na riƙo ta kawai ta faɗa jikin Umma ta fashe da matsanancin kuka, Umma lallashinta ta fara tare da bata baki tana faɗin,  "Ki yi haƙuri auta, komai yayi zafi maganinshi Allah, komai zai wuce in sha Allah nan da kwanaki, dama tsabgar aure ta gaji haka, an dinga samun wasu tsaiku da abubuwa kamun dai a kai ga ƙulla auren, saboda shaiɗan la'anannen Allah da baya son a haɗa sunna ta Allah da manzonsa, kuma in sha Allah da alkairi za a yi wannan aure, Allah ya miki zaɓi mafi alkairi da albarka ya haɗa kawunanku ya baku haƙurin zama da juna ya baku zuri'a masu albarka." Sadiya ta kasa cewa komai kuka kawai take yi, ƙiran da Abba ya yiwa Umma a waya shiyasa Umma ta miƙe tare da cewa, "Ki yi shiru ko auta, bari na je na dawo Abbanku na ƙirana", daga haka Umma ta wuce upstairs, Sadiya kuma bata tsaya jiran Umman ba, saboda yanzu kunyan mutanen gidan take ji, kawai miƙewa tayi ta fice tana share hawayenta, ko da ta isa gidan Mama, kai tsaye ɗakinta ta wuce ta shige can ƙurya ta nannaɗe a gado tana kuka. *** Sadeeq na shigowa palournshi ya saki ajiyar zuciya da shaƙar daddaɗar ƙamshin sashin, sannan ya zauna a sofa tare da kishingiɗa ya lumshe ido, tabbas ya ga wani abu a idon Sadiya, abinda baya son gani har abada, hakan na daga cikin dalilin da sanya ya ɓoye sirrinshi, amma Umar sai da ya bankaɗo, yana tsoron jin abinda ya hango a idanuwanta musannan daga bakinta, amma kuma lallai-lallai wannan karon dole ya yaƙi zuciyarshi fiye da a baya, dole ya daure fiye da a baya, ko da kuwa dan iyayensu da kuma Umar ne, dole ya daure ya cika wa Sadiya muradin ganin ta samu farincikinta, muddin dai ta nuna Haidar ta zaɓa, zai yi jarumta matuƙa ba zai kuma yarda ya kwanta ciwo ba, balle har ya faɗi irin wannan faɗuwa mai matuƙar hatsarin. Da sallama Umar ya shigo ya samu waje ya zauna, tare da faɗin, "Wallahi dai kana ja wa mutane raini da yawa wajan shirmammiyar nan, ka ga kallon da take maka kamar mai ido a tsakar ka, ni fa gani nake kamar ma ba Mama bace ta haifi Sadiya sauyi aka mana, ji fa yadda ta zuba maka ido, na tabbata daga kuma ranar da ka tuɓe a gaban Sadiya shikkenan sai abinda Allah ya yi." Sadeeq bai yi ko niyar tanka Umar ba, amma maganarshi sai da ya ba shi murmushi, kuma ya yi iya leɓe wanda sai ka ƙura mishi ido za ka fahimci ya murmusa ne, kamar bai son magana ya ce, "Ina dai ni zan tuɓe ba kai ba? To dan Allah ka raba ni da irin maganar nan yanzu ba muhallinta tukunna." "Gwanda dai a yi muhallinta domin ba so nake ka ɗaga mata ƙafa ba, wataƙila haka ya sa ta daina wannan shirmen nata, in ba shirme ba me aka mata na kuka?" "You're too harsh on her, please Umar ya isa", Sadeeq ya faɗa yana gyara  kishingiɗar da ya yi. Umar zai yi magana sai Khalid ya shigo, hakan ya sanya Umar ya fasa maganar, Khalid ya shigo ya aje basket, serving nasu yayi duka ya miƙa wa kowa nashi, sannan ya zauna da nashi a hannunshi, a ƙasa ya zauna a kan pillown sofa, sannan ya rage murya ya ce, "Yaya Umar please ka daina yi wa Sadiya faɗa, Allah akwai alamar tana a cikin damuwa." "Ba zai sake ba, ci abincinka", Sadeeq ya tari numfashin Umar da ke niyar yin magana, ya bai wa Khalid amsar, saboda baya son hayaniya da yawan magana a dame shi. Suna gama karyawa Khalid ya tattare komai ya fice da shi, yana fita ya haɗu da Abba da ke shirin ficewa, sai sannan ya yiwa Abba sannu, Abba ya amsa tare da ce mishi ya yiwa Sadeeq sannu, yana sauri zai fita sai ya dawo, a dawo lafiya Khalid ya yiwa Abba ya wuce kitchen da basket na hannunshi, Abba ya fice ya shige mota direba ya ja suka tafi   Khalid ko da ya fito kitchen sai da ya je ya isar wa Sadeeq saƙon Abba, sannan ya fice ya koma ɗakinshi, wanka ya yi ya fito shi ma ya nufi company. Umar ma sallama ya yiwa Sadeeq tare da jaddada mishi ya kwanta ya huta, ango mai jiran gado sai da hutu kar a shiga hidindimu nan ma ba hutu, ya zo ya kasa taɓuka komai a daren farko, Sadeeq sai dai ya girgiza kai tare da yiwa Umar addu'an Allah ya taro shi, a haka suka rabu da ɗan raha, Umar ya fice Sadeeq ya miƙe cikin ingirman surarshi da tafiyarshi ta jarumai mai cike da izza da aji ya shige ɗakinshi, haɗaɗɗun kyawawan idanuwanshi a ƙanƙance ya ƙare wa ɗakin kallo a taƙaice, duk da dai ya ga alamar an gyara, amma kuma ɓaro-ɓaro ya gane an hargitsa ɗakin, wanda yake da tabbacin garin bincike ne irin na Umar, ɗan furzar da iska a bakinshi ya yi sannan ya ce, "In kai mai shiryuwa ne Allah ya shiryaka Umar", daga haka ya wuce toilet nashi, shower ya sakar wa kanshi, wanka ya yi wanda ya kwana biyu bai yi ba, sai da ya tabbata ya ji daidai a jikinshi, jimawar da yayi a asibiti ya wanke da kyau, sannan ya kashe showern ya ja towel milk color ya ɗaura a waist nashi ya fito.   Sadeeq na da cikar zati da siffa fiye da hasashenku masu karatu, Sadeeq ya ƙeru ya haɗu ya gaji da haɗuwa, namiji ne har namiji, kuma namiji iya namiji da hasashenka za ta hasaso maka a matakin ƙarshe na mallakar komai, wata iriyar murɗaɗɗiyar jiki gare shi mai fisgar hankali da nitsuwa, godiya, tsarki, aminci da gaishe-gaishe su tabbata ga sarkin da ba ya gyangyaɗi balle bacci, sarkin da ke halittar bawanshi yadda ya so, kuma ya bai wa kowa kyau iya daidai shi da inda yake, Allah da girma yake da buwaya, kuma tsarkin mulkinshi da tsantsar tsara halittarshi sun isa, Allahu mai kun fa ya kunu, Allah muna godiya a gare ka. Sadeeq tsadadden turarenshi mai shegen ƙamshin ɗauke nitsuwa ya feshe ƙananun kayan da ya sanya na shan iska, gajeren wando wanda bai ƙarisa guiwarshi ba sai vest, sannan ya bi lafiyar gadonshi ya kwanta yana mai jin wani nitsuwa da lafiya da ƙarfin jiki na ratsa shi. ***   SADIYA POV Tana ƙudundune a ɗakin tana kuka ba ƙaƙƙautawa, domin ko ringing na wayarta da ta ji bai sanya ta dakata da kukan ta ɗau ƙiran ba. Mama da Khausar da kallo suka bi Sadiya, Khausar ta sauƙe numfashi cikin rashin daɗin rai, na tausayin Sadiya da kuma tausayin ɗan uwanta.   Ita ma Mama numfashin ta sauƙe tare da girgiza kai ta ce, "Allah ya kyauta ya dubi lamarinka Sadiya, mai babban suna zai sha taɓara kuwa, idan ba shi ba ma dama wa zai iya wa halinki, kuka kamar matar mamaci." Khausar bata ce komai ba, domin ita bata ji a jikinta kamar Sadiya ta yarda da batun Sadeeq ba, idan kuma ta faɗa wa Abba ta yarda to tabbas saboda girmamasu ne nauyinsu, ba wai dan tana son hakan ba, dan wannan kukan nata abinda yake nufi kenan. Sadiya kuwa kuka take da disashsshiyar murya take faɗin, "Haidar nake so, da shi na aminta da shi na yarda", irin sumbatun da take yi kenan har bacci ya yi gaba da ita na wahala da gajiyar kuka, ba abinda take yi a baccin sai jero ajiyar zuciya da shishshitar kuka, wanda ke nuni da kukan da ta sha mai yawa. Umar da sallama ya shigo palourn, inda ya samu Mama da Khausar a zaune, da gudu Nayla da Najla suka mishi oyoyo, ya ɗaga su sama tare da sumbatar goshinsu duka, sannan ya samu waje ya zauna tare da cewa,  "Barka da safiya Mama." "Barkanmu Umar, fatan an tashi lafiya? Ya mai babban suna da ƙarfin jiki?" "Alhamdulillahi Mama, yana gida ma dan an sallamo mu ɗazu." Waro idanuwa Mama ta yi cikin farinciki ta ce, "Kai ma sha Allahu, abu yayi daɗi sosai wallahi, dama ina abu zai yi kyau ango a asibiti, ai kuwa bari mu tashi yanzu mu dubo shi." "Na baro shi zai kwanta ya huta ne, ku dai bari zuwa anjima sai ku dubo shi." Mama ta ce, "ai kam ya kamata ya huta wa gajiyar asibiti, zaman asibiti ba daɗi sam-sam, sai idan ta kama ka to ba yadda ka iya, Allah dai yayi mana rowar ciwo, masu fama ma Allah ya yaye musu." "Amin Ya Rabbi", Khausar da Umar suka amsa, sannan Khausar ta ce, "Sannu da ƙoƙari uncle U, Allah dai ya ba da lada, Allah ya ƙara wa Yaya Sadeeq lafiya." "Amin Ya Rabbi sis." Khausar ta jinjina kai da

Chapter 23 of 32