wa dawa ba, babana yayi laifi amma a yafe shi ya tuba mun tuba duka, a taimaka a yi wa mutanen nan bayani ta fahimta, kuma indai ta ni ce wallahi na bai wa mai babban suna Sadiya duniya da lahira, halak malak Allah ya tabbatar musu da alkairi da zuri'a masu albarka."
Umma murmushi ta yi, domin ta san tunda Mama ta zo magana ya ƙare, ko Abba bai saurareta ba to zai saurari Mama.
Abba numfasawa yayi tare da gyara zama ya ce, "To.....
***
Za ku iya samun littafin a waɗannan manhajoji.
●BAKANDAMIYA HIKAYA.
●WATTPAD
@UwarBatoorl96
●AREWABOOKS.
@Uwarbatoorl96
●WHATSAPP
09161720046
a kan Naira #500.
Idan littafi ya zama completel 1k yake in sha Allah.
# Hareeyh
# 09161720046
# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚[07/12/2025, 13:34] Uwar Batoorl✍️❤️🥰: https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980
💔NAUYIN BAKI....👄💔
Na
Uwar Batoorl.
𝗕𝗜𝗦𝗠𝗜𝗟𝗟𝗔𝗛𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗠𝗔𝗡𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗘𝗘𝗠
اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤🤍
WANNAN PAGE NAKI NE
Maman Muhammad, Hajiyata mai capacity.
🅿️ 31 _ 32
⭐️
Umar yana sababben aikinshi da system (dama shi ko a company field nashi kenan, dan shi computer science ya karanta, he's both computer engineer and software engineer).
Bai tashi a wajan ba sai da aka fara ƙiraye-ƙirayen sallahn magrib, hakan ya sanya ya ajiye system ɗin ya rufe, kana ya miƙe ya shige toilet nashi ya ɗauro alwala, a madaidaicin closet nashi ya ciro jallabiya ya sanya, ya feshe jikinshi da daddaɗar turarenshi.
Umar haɗaɗɗe ne matuƙa, komai nashi cikin tsafta da aji yake yi, duk da kasancewar gidansu madaidaici kuma na rufin asiri, amma ɗakinshi na da ɗan girma, inda yake da gadonshi isashshe mai taushi, wanda ke kasancewa a malmale cikin tausasshen bedsheet ko da yaushe, saboda Umar akwai tsafta, dan har Mama watarana ta kan ce mishi, "Umar da matarka ce za ta ke maka wanki to da ta shiga uku, wannan ƙalƙale-ƙalƙalen naka da yawa yake".
Shi dai Umar sai dai ya murmusa, domin ya san gaskiya Mama take faɗi, tunda ga shi ko yanzu ma ya cire jallabiyan da ya shigo da shi, wani ya saka.
Akwai Sofa a ɗakin nashi, one-one seater guda biyu da centre table a tsakaninsu, daga gefe akwai madaidaicin fridge, sai mirror, sai closet nashi madaidaici, da kuma studying table da kujerarshi, inda yake adana systems da files da sauran abubuwan da suka shafi aikinshi ko na karatu.
Ɗakin nashi ba hayani sosai, kuma a ƙayace yake matuƙa, centre carpet mai laushi da ke lailaye a tsakiyar ɗakin, sai ya haska ɗakin sosai, ƙamshi da haɗuwar ɗakin Umar, idan suka haɗu da kana tsaye a kan wannan carpet ɗin, sai ka kusa mance inda kake.
Yana kammala feshe turarenshi ya ɗau wayarshi ya fice a ɗakin, ba kowa a palourn nasu hakan ya sanya ya fice kai tsaye, a ƙafa ya ƙarisa masallacin, yana isa Abba na isowa, musabaha suka yi da Abba sannan ya mishi barka da fitowa, suka shige masallaci suka bi sahu, a ka kabbara cikin jam'i aka yi sallah, bayan an idar sun shafa addu'a sai Abba ya miƙe yana faɗin, "Bari mu shiga ciki kamun isha'i ya yi", alamar dai akwai uzurin da zai hana Abba jiran isha'i.
Umar ma miƙewa ya yi tare da cewa, "Dama akwai maganar da za mu yi Abba mai muhimmanci."
"To bismilla mu je Umaru."
Suna tafe Umar na ta ƙoƙarin yi wa Abba bayani cikin kwana-kwana, amma Abba bai fahimta ba, har suka ƙarasa ciki, Umar ya tsaya daga palourn ƙasa, Abba kuma ya haura sama, ba jimawa ya dawo, zama yayi a kujeran da ke kallon wanda Umar ke zaune, sannan ya ce, "Ina sauraranka Umaru."
Umar ya buɗe baki cikin ƙarfin guiwar sanar da Abba kai tsaye, sai ga Umma na sauƙowa daga stairs da hijabi jikinta, alamar ita ma idar da sallanta kenan, murmushi Umar yayi, tare da cewa, "Barka da fitowa Umma."
"Yauwa Umar, barkanmu, ya wunin yau ɗin? Fatan ka huta da kyau?", Umma ta ƙarishe maganar tana zama a kujeran da Abba ke zaune mai ɗaukar mutum uku."
"Alhamdulillah Umma, sai godiya."
"Ma sha Allah, haka ake so Umar, Allah ya muku albarka, sai haƙuri kuma da rayuwa, musamman mata, maƙota da kuma abokanan kasuwanci."
"In sha Allah Umma", ya amsa yana murmushi dan ɗazu Khausar ta faɗa mishi yadda suka yi da Umma.
Abba gyaran murya yayi tare da cewa, "Umar ina sauraranka."
Ƙasa Umar yayi da kan shi, a nitse ya ce, "Abba dan Allah a dube mu a kuma lamunce mana a yafe mana", yana gama faɗin haka ya yi shiru.
Amma jin su Abba basu ce komai ba sai ya numfasa tare da sake cewa, "Sadeeq yana son Sadiya, kuma soyayyarta shi ne sanadin ciwon da yake ciki, Abba kuma wallahi za mu iya rasa Sadeeq muddin bai samu Sadiya ba, tun sadda ya farka sanadin zuwan Sadiya asibiti, da wasu abubuwa da suka dinga faruwa suka ɗarsa mini zargin haka a zuciyata, har dai na ce maka in sha Allah zan bincika abinda yake ɓoyewa, to wallahi Abba sai yau na gano soyayyar Sadiya ce da yake ɓoyewa, ya zama maƙasudin komai."
Abba da Umma daman da farko sun yi shiru ne, sun zuba wa Umar ido saboda basu fahimci yafiyar da ya fara nema ba kamun bayani, amma yanzu da suka ji abinda ya ce, kamun Abba ya ce wani abu, Umma ta ce, "Shi Sadeeq ɗin ne yake son Auta? Da gaske ko da wasa Umar?"
Umar ƙasa yayi da kai tare da cewa, "Wallahi Umma da gaske ne, kuma dan Allah a taimaka mana."
Umma da Abba duk idanuwa suka zuba wa Umar, cikin rashin fahimtar me yake faɗa kuma me yake nufi da a taimaka musu, tabbas sun ji me ya ce, amma ba su fahimta ba har sannan, domin mamakin maganar suke.
Umma na ƙoƙarin sake yin magana sai Abba ya rigata ta hanyar cewa, "Umaru bana son shirme da shiririta, kana cewa auta shirmammiya, kai yanzu me kake yi? Abubakar ɗin ne ya ce maka Halimatu yake so? Yaushe kuka yi haka da shi? Kai duk ma ba wannan ba, a ina ka taɓa jin an nemi aure cikin neman aure ko a wasa?"
Umar Marairaicewa yayi, tare da sake yin ƙasa da kai, cikin muryar magiya da sigar tabbatarwa ya ce, "Wallahi Abba Sadeeq yana son Sadiya, kuma ai ba wani neman aure kan nema tunda....."
Abba cikin haɗe rai ya katse Umar, tare da cewa, "Ba na son shirme Umaru, ka tashi ka bani waje, ba mai maidamu ƙananun yara, auta da yardar Allah Aliyu za ta aura, daga kai har Abubakar ɗin ku bar wasar kwaikwayonku, domin ba zan ba shi auren Halimatu ba, ya mutu ɗin, Allah ya ji ƙan shi muma duk hanyar muka kama."
Da wani irin sauri Umar ya ɗago kan shi jin furucin Abba, Umma ƙasa tayi da kanta ta ma rasa me za ta fara tunawa, Umar na ƙoƙarin magana, Abba ya dakatar da shi tare da ɗaga mishi hannu ya ce, "Tashi ka je na gama magana, ba zan bai wa Abubakar auren auta ba, Aliyu za ta aura."
Umar rau-rau-rau yayi da idanuwa alamar magiya, amma Abba haɗe fiskarshi yayi bai ko sake kallon inda Umar ke zaune ba, Umma kallon Abba ta yi, sannan ta kuma mayar da idanuwanta kan Umar, sanin halin Abba ya sanya ta cewa, "Tashi ka je Umar", ta ƙarishe faɗa ne tare da yi mishi alamar za su yi magana daga baya.
Jiki a sanyaye Umar ya miƙe, domin bai tsammaci haka daga Abba ba, ko da ya fice a gidan bai koma gidan Mama ba ya wuce masallaci, layin Khausar ya ƙira tare da sanar da ita ta shirya, yana dawowa masallaci, za su wuce asibiti tare
**
Umma idanuwanta a kan Umar har ya fice, sannan ta ja numfashi tare da yin shiru ta kuma yi ƙasa da kanta, har sun ci mintuna a haka, da ta gundura da zaman ne ƙarshe yunƙurawa ta yi da nufin barin palourn, sai Abba ya dakatar da ita ta hanyar cewa, "Koma ki zauna Halimatu."
Komawa Umma tayi ta zauna, tana kallon fiskar Abba da ke a haɗe alamar ɓacin rai, hallau dai shiru ta yi bata ce komai ba, hakan kuwa ba ƙaramin sake ɓata ran Abba yayi ba, a ɗan kausashe ya ce, "Abubakar bai da hankali, tukunna wannan ma wani irin magana ne? Na san Umar ba zai mini ƙarya ba tunda ba ya mini, amma kuma bana jin na yarda da wannan batu."
Sai da Abba ya numfasa, sannan ya ɗaura da cewa, "Halimatu kin yi shiru ba za ki ce wani abu bane? Kin barni ni kaɗai sai magana nake ta yi", a ɗan hasale Abba ya ƙarishe maganar, saboda shirun da Umma ta yi ya dame shi, ita kuma ta yi shirun ne saboda guje wa faɗar shi amma bata tsira ba.
A sanyaye Umma ta ce, "To ni me zan ce Abban Sadeeq?"
Sai sannan Abba ya ɗan sake fiska tare da gyara zama, ya ce, "Halimatu kina ganin da gaske ne kuwa? Abubakar zai aikata wannan rashin lissafi da rashin hankalin? Yana son auta meyasa duk bai faɗa ba?"
"Abinda nima nake ta lissafawa kenan Abban Sadeeq, amma da wataƙila mun saurari bayanin Umar da mun ji dalili", Umma ta faɗa da kwantacciyar murya.
Abba girgiza kai yayi tare da sake ɗaure fiska ya ce, "Ba ma zan bari yaran nan su ga wannan fiskar ba, balle su ce za su mini bayani, ba wani bayanin da zan ji ko na saurara, Abubakar bai isa ya maida ni ƙaramin yaro ba, a matakin da ake ciki ko Sadiya ba za ta sa na muzanta gaban mutane ba, mu gama magana da iyayen yaro da jama'a, sannan yanzu a shiga satin biki kuma a nemi sauya magana, to ba zan lamunta ba sam-sam, duk wanda zai mutu ya mutu, amma Haidar zan bai wa auren Sadiya."
Umma da ɗan sauri ta ɗago ta kalli fiskar Abba da kyau, jin abinda ya ce daga ƙarshe.
Abba da gefen ido ya kalli Umma na kallonshi, hakan ya sa ya kuma haɗa fiska tare da juyawa gare ta suka haɗa ido, yana iya kallon tausayin Abubakar a idonta, wanda dama ya tsammaci haka sanin irin son da take mishi, amma kuma ba zai bai wa kowa wannan damar ba, ciki har da ita.
A ɓangaren Umma kuma tana iya hango tabbacin abinda Abba ya faɗa a idanuwanshi, domin dama shi Abba mutum ne tsayayye mai magana ɗaya, idan ya ce abu to yana nufin haka ne ba sauyawa, kaifi ɗaya ne shi, hakan ya sanya ta sauƙe gauron numfashi tare da janye idanuwanta cikin nashi, ta kuma kau da kanta.
Abba cewa yayi, "Na gama magana, tunda Sadeeq ya ce bai da hankali, to ya je inda za a biye mishi a yi rashin hankalin, amma ba a wajena ba, kuma in sha Allah zai dawo gidan ya same ni, ko na je har asibitin na same shi, sai na saɓa wa Sadeeq, in ba mayar da mutane yara kaman shi ba, yana son autar me ya hana shi faɗa tun a baya? Kuma wa ya sa ya shige gaba aka tsayar da maganarta da Aliyu? In kuma ya ce yanzu ya fara sonta har ya kai shi ga kwanciya ciwo, to in zai taimaki kanshi ya tashi ya taimaki kanshi, domin mu ba jahilai bane mun san haramci nema cikin nema, dan naga alamar koma dai menene to Abubakar ya ba da ajiyar hankalinshi da iliminshi, ba sa a tare da shi....", faɗa sosai Abba ya dinga yi kamar zai ari baki, Umma dai tana zaune shiru ko tari bata kuma yi ba, balle ta tanka mishi ta ce wani abun, ta san halin Abba sarai yanzu sai faɗar tashi ta koma kanta, tunda dama yawanci iyaye maza haka suke, ko me yaro ya aikata to uwarshi ake gani da laifin.
Abba yana yi har aka ƙira sallahn isha'i, sannan ya tashi ya fice ya tafi masallaci, bayan an idar da sallah ya dawo, surutun ya ci gaba da yi, har ya ci tuwo, sai da ya gama shirin kwanciya sannan ya bar mitar, tare da jaddadawa Umma kada ya ji kada ya gani, kar ma ya ji wannan maganar ta kuma tashi a gidan, zai ja wa Umar ma kunne, dan baƙi za su fara yi a satin na masu zuwa biki, ba zai yiwu a zo a ji wannan abin kunyar ba, dan abun kunya ne a ce ana tsaka da hidima maganar Sadeeq ta ɓullo, ba za a rasa a cikin dangin su Sadiya ma a samu masu ce musu suna da son zuciya ba, kuma duk haukar Sadeeq ne zai ja haka muddin aka biye mishi.
Dole Umma ta tsuke bakinta ta yi shiru, har dai bacci yayi gaba da Abba, sannan ta tashi ta shige toilet, ta ɗauro alwala ta zo ta gabatar da nafila tana mai roƙa wa yaran nasu alkairi, tare da addu'an sauƙi ga Sadeeq, raba dare Umma tayi tana addu'oi, domin ko da ta kwanta tsakar dare ta kuma tashuwa, nan kam har aka ƙira asuba tana kan sallaya har Abba ya farka.
****
SADIYA POV
Khausar na kallon Sadiya ta ce, "Likitoci sun ce damuwa ce ta sanya Yaya Sadeeq ya faɗi lokaci ɗaya, wanda da ba a hanzarta ba da zai iya rasa rayuwarsa daga haka, saboda dama akwai abinda yake ba daidai ba a zuciyarshi, dogon suman da ya faɗa likitoci sun yi bayanin cewa ba lallai ya farka kusa kamar yadda ya faru ba, a cewarsu zai iya kai wata ɗaya, biyu, uku kai har ma shekara a wannan hali, amma cikin ikon Allah ya farka a sati guda a ranar da kika je, ko kin san dalilin hakan?"
Girgiza kai kawai Sadiya ta yi, idanuwanta cike da ƙwalla, saboda ƙara dulmiya da tayi cikin kogin tausayin Yaya Sadeeq.
Khausar na ƙoƙarin yin magana sai ƙira ya shigo wayarta, hakan ya sanya ta jawo wayar, ganin Umar ne ta ɗauka tare da yin sallama, ya amsa mata ya sanar mata ta shirya yana dawowa za su wuce asibiti tare, daga haka ya katse wayar, Khausar kuma ta miƙe ta fice, wajan Mama ta je ta sanar mata Umar zai koma asibiti, amma tare za su tafi a haɗa abinda za a kai wa Sadeeq, Mama amsawa tayi dan dama ita ta ce idan za su tafi asibitin su mata magana, ta haɗa wa Sadeeq abin taɓawa da zai taimaka, wajan kauda mishi rashin daɗin baki irin na majinyata.
Khausar na ƙoƙarin juyawa sai Mama ta ce, "Fatan kun gama magana da ƙanwar taki? Dan ina son na je na samu Abbanku da kai na da wannan maganar, Umar ba lallai ya mishi bayani yadda ya kamata ba."
Murmushi Khausar tayi tare da cewa, "Muna maganar dai bamu ƙarasa ba, amma in sha Allah ba matsala daga small Mum, dan ko ni ma Abba na fi ji, shiyasa tun farko na ce da uncle U ya bari ki sanar wa Abba, ya ce a'a zai mishi bayani da kanshi."
"To madalla, dan nima bana tunanin matsala daga Sadiya, Allah dai ya shige mana gaba ya tabbatar da alkairi, ko Abbanku ma ina tunanin da yardar Allah da sauƙi komai zai zo duk da dai na san halinshi na kafiya."
"Amin Mama", Khausar ta faɗa sannan ta juya ta koma ɗaki wajan Sadiya saboda an shiga sallahn isha'i, samun Sadiya ta yi a zaune abinda ta barta tana hawaye, wadda Khausar ke da tabbacin hawayen a kan Sadeeq ne na tausayinshi ne, hakan ya sanya tayi gyaran murya tare da cewa, "small Mum zaman me kike ana sallah? Tashi mu yi", ta ƙarishe maganar tare da nunawa kamar bata ga hawayen da take yi ba.
Sadiya miƙewa tsaye tayi, tana share hawayen muryarta na rawa ta ce, "Aunty menene yake damun Yaya Sadeeqna? Kuma menene ba daidai ba a zuciyarshi?"
Khausar kabbara sallah tayi ba tare da ta kula Sadiya ba, hakan ya sanya Sadiya dole ta share hawayenta tare kabbara sallah ita ma, Khausar ce ta fara idarwa, domin Sadiya ko da ta kai goshinta a sujjadar ƙarshe, addu'ar samun lafiya ta dinga yi wa Sadeeq, tare da mishi addu'ar Allah ya yaye mishi damuwarshi, Allah ya sa ko ma menene kada ya ƙara faɗar da shi haka.
Sadiya da ta ɗago tayi tahiya ta sallame, addu'a ta kuma korowa, tana shafawa ta mai da dubanta ga Khausar tare da cewa, "Aunty dan Allah menene ke damun Yaya Sadeeq ɗin? Ki faɗa mini dan Allah."
"Yaya Sadeeq ya farka ne saboda wani abu da ya kusance shi wanda yake so ko yake ƙi, haka likitoci suka ce, kuma kece wannan abun small Mum, ke ce silar farkawar Yaya Sadeeq a kan lokaci cikin ikon Allah, soyayyar da Yaya Sadeeq yake miki ne sanadin hakan, damuwar da ke damun Yaya Sadeeq ma ke ce, soyayyarki ce ke damun shi, ita ce damuwarshi", Khausar ta faɗa tana kallon Sadiya da kyau.
Hawayene suka cigaba da gudu a kumatun Sadiya, hakan ya sanya ta buɗe baki, muryarta na rawa ta ce, "Aunty na san Yaya Sadeeq yana so na yana ƙaunata, shiyasa nima nake ƙaunarshi fiye da Yaya Umar, Yaya Sadeeq shi ne duniyata, uwata, ubana, Yayana da komai aunty, ina jin Yaya Sadeeq a zuciyata sosai, ko ni na fa ɗa halin da yake ciki to lallai zan farka saboda shi, kamar dai yadda ya farka saboda ni, kuma da rayuwa za ta bai wa mutum zaɓi, to zan so komawa ciki domin na fito a cikin Umma, Yaya Sadeeq ya zame bangona da komaina na jini na haƙiƙa."
"Hmmn!, small Mum ba irin wannar soyayyar nake nufi ba."
"Wani irin soyayya aunty?", Sadiya ta tambaya cikin rashin fahimta.
Khausar na shirin bata amsa, sai Umar yayi sallama daga bakin ƙofar ɗakin, hakan ya sanya Khausar ta fasa yin magana ta miƙe tsaye, Nayla da tayi bacci a wajan sallah ta kalla, sannan Najla da ke shirin tunkarar ƙofa, dan zuwa wajan uncle U tunda ta ji muryarshi, dakatar da ita Khausar tayi tare da cewa, "Oya go and sleep."
Najla tura baki tayi ta wuce gefen Nayla ta kwanta, Khausar ta nufi ƙofa bayan ta amsa sallamar Umar tare da ce masa gata nan fitowa, ta kama handle za ta murɗa sai ta jiyo tambayar Sadiya.
"Aunty wani irin soyayyar kike nufi?" Sadiya ta kuma tambaya murya a raunace.
"Small Mum idan na dawo za muyi maganar", daga haka ta fice.
Sadiya lumshe idanuwanta tayi tare da dafe kanta, domin bata gane nufin Khausar ba sam-sam, ƙiran da ya shigo wayarta shi ya katse mata tunanin da ta nitsa na son gano me Khausar ke nufi, daga ringing tone ɗin ta gane Haidar ne, hakan ya sanya ta ɗauki wayar tana mai jin kaso hamsin ya ragu a cikin abinda ke damunta, cikin soyayya suke wayarsu, duk da ya nazarci ba daidai take ba, hakan ya sanya ya ce, "Hey, what's wrong with you? Na ji wani iri a yanayinki."
Murmushi ne ya suɓucewa Sadiya, saboda yaba ƙaunar Haidar da kulawarshi gare ta, tunda har ya gano duk da tana ƙoƙarin ɓoyewa, cikin son kauce mishi ta ce, "I've started missing sweet home."
"Ohhh! Really? To shikkenan ai ba zan rarrashe ki tun yanzu na ƙarar da rarrashina ba, let's leave it to next coming Sunday, a lokaci kamar dai wannan, I'll make you forget everyone exists except me and you, kin ga ba za ki tuna missing ba."
Cunna baki Sadiya tayi ba tare da ta ce komai ba.
Haidar a ɓangarenshi ya ce, "Sweet Al-Sad, i love you soo much, i can't wait for this Saturday, kwana biyar kawai ya rage mana, a na shida za mu mallaki juna."
"In sha Allah, I'll be officially Mrs Haidar", faɗin Sadiya, tana jin wani guguwar soyayya na bule ta.
"Yeah! Matar Aliyu Haidar AKA Al-Sad."
Guntun dariya Sadiya ta yi, daga haka suka ci gaba da wayarsu cikin soyayya da nishaɗi, hakan ya sa Sadiya ta aje batun maganar Khausar a gefe, sun ɗau lokaci sosai suna waya, dan Haidar bai kashe wayar ba har ta gyara komai, ta maida Nayla da Najla wajan kwanciyarsu, ta aje wayar a haka ta je ta watsa ruwa ta zo ta yi shirin bacci, sannan suka cigaba da wayar, yana jin ta tayi addu'an bacci ta shafa shi ma ya shafa, sai da ya tabbatar bacci yayi gaba da ita sannan ya datse ƙiran cike da ɗimbin ƙaunarta da shauƙinta.
****
Khausar tana ficewa a ɗakin ta mara wa Umar baya, tana isowa wajan motar lokacin ya sanya basket da Mama ta bayar a back seat, sannan ya buɗe mazaunin direba ya shige, ita ma Khausar ta shiga gefe ta zauna, ya yiwa motar key suka fice a gidan, suna tafe a hanya ya labarta mata yadda suka yi da Abba, tare da cewa, "Akwai matsala fa sis, don Abba ya ƙi fahimta, kai bai ma bari na mishi bayani ba."
"Hmmn!, nima dama abinda nake gudu kenan, kowa ya san halin Abba da kafiya, amma dai ɗazu mun yi magana da Mama ta ce gobe idan Allah ya kai mu da safe za ta shiga wajan su Abba su yi magana."
"To ma sha Allah, da sauƙi, domin idan Abba ya tirje tsaf zan iya zuwa wani masallacin a ɗaura auren nan, sai dai kawai ku ji labari."
Murmushi Khausar tayi tare da cewa, "Sai dai su Abba su ji labari dai, domin ni kam da ni za a kashe a binne."
"Wannan haka yake, kece waliyiyar Sadiya, ni kuma waliyin bro."
Khausar na dariya ta labarta mishi yadda suka yi da Sadiya tana faɗin, "Da alama ba za a samu damuwa da Sadiya ba, domin ban hangi hakan a idanuwanta ko yanayinta ba, balle ma zantukanta, small Mum ta damu da Yaya Sadeeq sosai kuma tana ƙaunarshi."
"Ai duk rainin hankali ke damunsu sis, amma sarai suna son junansu, jira kawai dama suke a ari bakinsu a ci musu albasa", faɗin Umar yana sakin murmushin samun nitsuwa, domin an gama masu wahalar, Abba ma da yardar Allah Mama za ta fahimtar da shi, su Haidar kuma su ɗau na Annabawa, sai kawai ayi bikin tuwo na mai na.
A haka suna hira har suka isa asibitin, Khalid da Sa'ad suka yiwa Khausar da Umar sannu da zuwa, suka fice saboda basu damar magana, Khausar ce ta yiwa Sadeeq magana a tausashe cikin sigar girmamawa da lallashi, shawarwari da sauransu duka, shi dai Umar ƙala bai ce ba har ta kammala, sannan Sadeeq ya buɗe baki kamar bai son yin maganar ya ce, "Thank you sis."
Khausar ta amsa tare da musu fatan alkairi, tare da sai da safe ta fice, tare da su Khalid ta dawo gida, suka ajiyeta a ƙofar gidan Mama, su kuma suka wuce gidan.
Khausar tana shiga Mama ta mata sannu da dawowa, tare da tambayar ya mai jikin, Khausar ta amsa, tare da sanar da Mama yadda Umar yayi da Abba, Mama ta jinjina kai tana faɗin, "Na sani dama ai hakan na iya faruwa, Abbanku sai a hankali."
Khausar ta ce, "Sai ku masa bayani dan nasan ku kam zai saurareku ke da Umma."
"In sha Allah hakan za a yi, je ki kwanta abinko dare ya yi."
"To Mama sai da safe."
"Yauwa mu kwana lafiya a huta gajiya ko."
"Allah ya sa Mama."
Da, "Amin Ya Allahu", Mama ta amsa, sannan Khausar ta wuce ɗakin Sadiya, ta samu duk sun yi bacci, hakan ya sa ita ma tayi shirin bacci ta kwanta.
⭐️
PLATEU SPECIALIST HOSPITAL.
ABUBAKAR SADEEQ POV
***
Bayan ficewar Khausar, Umar ya kammala abinda zai yi ya kishingiɗa, tare da ɗaura system nashi a saman ƙafafuwanshi, cikin ƙwarewa yske sarrafa system ɗin.
"Agogo sarkin aiki."
Umar ya tsinkayi muryar Sadeeq ya faɗa hakan a kame, ɗan guntun murmushi yayi domin tunda ya ga tun shigowarshi har yanzu Sadeeq bai mishi magana ba, ya ɗauka fushi yake akan abinda ya binciko har yanzu, shiyasa bai kula shi ba shi ma, amma jin abinda ya ce mishi, sai ya bashi amsa yana murmushi, "Duk aikina ai ban kai ka ba, ko ƙafarka ban kama ba, matashin mai kuɗi duk da ƙananun shekarunka kuwa, aikin da kake yi tuƙuru shi ya kawo har ka wuce waɗanda suka girme maka a shekaru kan batun dukiya, ka ga kai kana gaba da agogo ma, ni fa mamaki nake yi ma yanzu ya za a yi da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 20 Chapter of 32