Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kan Umar, sanin halin Abba ya sanya ta cewa, "Tashi ka je Umar", ta ƙarishe faɗa ne tare da yi mishi alamar za su yi magana daga baya. Jiki a sanyaye Umar ya miƙe, domin bai tsammaci haka daga Abba ba, ko da ya fice a gidan bai koma gidan Mama ba ya wuce masallaci, layin Khausar ya ƙira tare da sanar da ita ta shirya, yana dawowa masallaci, za su wuce asibiti tare ** Umma idanuwanta a kan Umar har ya fice, sannan ta ja numfashi tare da yin shiru ta kuma yi ƙasa da kanta, har sun ci mintuna a haka, da ta gundura da zaman ne ƙarshe yunƙurawa ta yi da nufin barin palourn,  sai Abba ya dakatar da ita ta hanyar cewa, "Koma ki zauna Halimatu." Komawa Umma tayi ta zauna, tana kallon fiskar Abba da ke a haɗe alamar ɓacin rai, hallau dai shiru ta yi bata ce komai ba, hakan kuwa ba ƙaramin sake ɓata ran Abba yayi ba, a ɗan kausashe ya ce, "Abubakar bai da hankali, tukunna wannan ma wani irin magana ne? Na san Umar ba zai mini ƙarya ba tunda ba ya mini, amma kuma bana jin na yarda da wannan batu."   Sai da Abba ya numfasa, sannan ya ɗaura da cewa, "Halimatu kin yi shiru ba za ki ce wani abu bane? Kin barni ni kaɗai sai magana nake ta yi", a ɗan hasale Abba ya ƙarishe maganar, saboda shirun da Umma ta yi ya dame shi, ita kuma ta yi shirun ne saboda guje wa faɗar shi amma bata tsira ba. A sanyaye Umma ta ce, "To ni me zan ce Abban Sadeeq?" Sai sannan Abba ya ɗan sake fiska tare da gyara zama, ya ce, "Halimatu kina ganin da gaske ne kuwa? Abubakar zai aikata wannan rashin lissafi da rashin hankalin? Yana son auta meyasa duk bai faɗa ba?" "Abinda nima nake ta lissafawa kenan Abban Sadeeq, amma da wataƙila mun saurari bayanin Umar da mun ji dalili", Umma ta faɗa da kwantacciyar murya. Abba girgiza kai yayi tare da sake ɗaure fiska ya ce, "Ba ma zan bari yaran nan su ga wannan fiskar ba, balle su ce za su mini bayani, ba wani bayanin da zan ji ko na saurara, Abubakar bai isa ya maida ni ƙaramin yaro ba, a matakin da ake ciki ko Sadiya ba za ta sa na muzanta gaban mutane ba, mu gama magana da iyayen yaro da jama'a, sannan yanzu a shiga satin biki kuma a nemi sauya magana, to ba zan lamunta ba sam-sam, duk wanda zai mutu ya mutu, amma Haidar zan bai wa auren Sadiya." Umma da ɗan sauri ta ɗago ta kalli fiskar Abba da kyau, jin abinda ya ce daga ƙarshe.   Abba da gefen ido ya kalli Umma na kallonshi, hakan ya sa ya kuma haɗa fiska tare da juyawa gare ta suka haɗa ido, yana iya kallon tausayin Abubakar a idonta, wanda dama ya tsammaci haka sanin irin son da take mishi, amma kuma ba zai bai wa kowa wannan damar ba, ciki har da ita. A ɓangaren Umma kuma tana iya hango tabbacin abinda Abba ya faɗa a idanuwanshi, domin dama shi Abba mutum ne tsayayye mai magana ɗaya, idan ya ce abu to yana nufin haka ne ba sauyawa, kaifi ɗaya ne shi, hakan ya sanya ta sauƙe gauron numfashi tare da janye idanuwanta cikin nashi, ta kuma kau da kanta. Abba cewa yayi, "Na gama magana, tunda Sadeeq ya ce bai da hankali, to ya je inda za a biye mishi a yi rashin hankalin, amma ba a wajena ba, kuma in sha Allah zai dawo gidan ya same ni, ko na je har asibitin na same shi, sai na saɓa wa Sadeeq, in ba mayar da mutane yara kaman shi ba, yana son autar me ya hana shi faɗa tun a baya? Kuma wa ya sa ya shige gaba aka tsayar da maganarta da Aliyu? In kuma ya ce yanzu ya fara sonta har ya kai shi ga kwanciya ciwo, to in zai taimaki kanshi ya tashi ya taimaki kanshi, domin mu ba jahilai bane mun san haramci nema cikin nema, dan naga alamar koma dai menene to Abubakar ya ba da ajiyar hankalinshi da iliminshi, ba sa a tare da shi....", faɗa sosai Abba ya dinga yi kamar zai ari baki, Umma dai tana zaune shiru ko tari bata kuma yi ba, balle ta tanka mishi ta ce wani abun, ta san halin Abba sarai yanzu sai faɗar tashi ta koma kanta, tunda dama yawanci iyaye maza haka suke, ko me yaro ya aikata to uwarshi ake gani da laifin. Abba yana yi har aka ƙira sallahn isha'i, sannan ya tashi ya fice ya tafi masallaci, bayan an idar da sallah ya dawo, surutun ya ci gaba da yi, har ya ci tuwo, sai da ya gama shirin kwanciya sannan ya bar mitar, tare da jaddadawa Umma kada ya ji kada ya gani, kar ma ya ji wannan maganar ta kuma tashi a gidan, zai ja wa Umar ma kunne, dan baƙi za su fara yi a satin na masu zuwa biki, ba zai yiwu a zo a ji wannan abin kunyar ba, dan abun kunya ne a ce ana tsaka da hidima maganar Sadeeq ta ɓullo, ba za a rasa a cikin dangin su Sadiya ma a samu masu ce musu suna da son zuciya ba, kuma duk haukar Sadeeq ne zai ja haka muddin aka biye mishi.   Dole Umma ta tsuke bakinta ta yi shiru, har dai bacci yayi gaba da Abba, sannan ta tashi ta shige toilet, ta ɗauro alwala ta zo ta gabatar da nafila tana mai roƙa wa yaran nasu alkairi, tare da addu'an sauƙi ga Sadeeq, raba dare Umma tayi tana addu'oi, domin ko da ta kwanta tsakar dare ta kuma tashuwa, nan kam har aka ƙira asuba tana kan sallaya har Abba ya farka. ****      SADIYA POV Khausar na kallon Sadiya ta ce, "Likitoci sun ce damuwa ce ta sanya Yaya Sadeeq ya faɗi lokaci ɗaya, wanda da ba a hanzarta ba da zai iya rasa rayuwarsa daga haka, saboda dama akwai abinda yake ba daidai ba a zuciyarshi, dogon suman da ya faɗa likitoci sun yi bayanin cewa ba lallai ya farka kusa kamar yadda ya faru ba, a cewarsu zai iya kai wata ɗaya, biyu, uku kai har ma shekara a wannan hali, amma cikin ikon Allah ya farka a sati guda a ranar da kika je, ko kin san dalilin hakan?" Girgiza kai kawai Sadiya ta yi, idanuwanta cike da ƙwalla, saboda ƙara dulmiya da tayi cikin kogin tausayin Yaya Sadeeq. Khausar na ƙoƙarin yin magana sai ƙira ya shigo wayarta, hakan ya sanya ta jawo wayar, ganin Umar ne ta ɗauka tare da yin sallama, ya amsa mata ya sanar mata ta shirya yana dawowa za su wuce asibiti tare, daga haka ya katse wayar, Khausar kuma ta miƙe ta fice, wajan Mama ta je ta sanar mata Umar zai koma asibiti, amma tare za su tafi a haɗa abinda za a kai wa Sadeeq, Mama amsawa tayi dan dama ita ta ce idan za su tafi asibitin su mata magana, ta haɗa wa Sadeeq abin taɓawa da zai taimaka, wajan kauda mishi rashin daɗin baki irin na majinyata. Khausar na ƙoƙarin juyawa sai Mama ta ce, "Fatan kun gama magana da ƙanwar taki? Dan ina son na je na samu Abbanku da kai na da wannan maganar, Umar ba lallai ya mishi bayani yadda ya kamata ba." Murmushi Khausar tayi tare da cewa, "Muna maganar dai bamu ƙarasa ba, amma in sha Allah ba matsala daga small Mum, dan ko ni ma Abba na fi ji, shiyasa tun farko na ce da uncle U ya bari ki sanar wa Abba, ya ce a'a zai mishi bayani da kanshi." "To madalla, dan nima bana tunanin matsala daga Sadiya, Allah dai ya shige mana gaba ya tabbatar da alkairi, ko Abbanku ma ina tunanin da yardar Allah da sauƙi komai zai zo duk da dai na san halinshi na kafiya." "Amin Mama", Khausar ta faɗa sannan ta juya ta koma ɗaki wajan Sadiya saboda an shiga sallahn isha'i, samun Sadiya ta yi a zaune abinda ta barta tana hawaye, wadda Khausar ke da tabbacin hawayen a kan Sadeeq ne na tausayinshi ne, hakan ya sanya tayi gyaran murya tare da cewa, "small Mum zaman me kike ana sallah? Tashi mu yi", ta ƙarishe maganar tare da nunawa kamar bata ga hawayen da take yi ba. Sadiya miƙewa tsaye tayi, tana share hawayen muryarta na rawa ta ce, "Aunty menene yake damun Yaya Sadeeqna? Kuma menene ba daidai ba a zuciyarshi?" Khausar kabbara sallah tayi ba tare da ta kula Sadiya ba, hakan ya sanya Sadiya dole ta share hawayenta tare kabbara sallah ita ma, Khausar ce ta fara idarwa, domin Sadiya ko da ta kai goshinta a sujjadar ƙarshe, addu'ar samun lafiya ta dinga yi wa Sadeeq, tare da mishi addu'ar Allah ya yaye mishi damuwarshi, Allah ya sa ko ma menene kada ya ƙara faɗar da shi haka.   Sadiya da ta ɗago tayi tahiya ta sallame, addu'a ta kuma korowa, tana shafawa ta mai da dubanta ga Khausar tare da cewa, "Aunty dan Allah menene ke damun Yaya Sadeeq ɗin? Ki faɗa mini dan Allah." "Yaya Sadeeq ya farka ne saboda wani abu da ya kusance shi wanda yake so ko yake ƙi, haka likitoci suka ce, kuma kece wannan abun small Mum, ke ce silar farkawar Yaya Sadeeq a kan lokaci cikin ikon Allah, soyayyar da Yaya Sadeeq yake miki ne sanadin hakan, damuwar da ke damun Yaya Sadeeq ma ke ce, soyayyarki ce ke damun shi, ita ce damuwarshi", Khausar ta faɗa tana kallon Sadiya da kyau. Hawayene suka cigaba da gudu a kumatun Sadiya, hakan ya sanya ta buɗe baki, muryarta na rawa ta ce, "Aunty na san Yaya Sadeeq yana so na yana ƙaunata, shiyasa nima nake ƙaunarshi fiye da Yaya Umar, Yaya Sadeeq shi ne duniyata, uwata, ubana, Yayana da komai aunty, ina jin Yaya Sadeeq a zuciyata sosai, ko ni na fa ɗa halin da yake ciki to lallai zan farka saboda shi, kamar dai yadda ya farka saboda ni, kuma da rayuwa za ta bai wa mutum zaɓi, to zan so komawa ciki domin na fito a cikin Umma, Yaya Sadeeq ya zame bangona da komaina na jini na haƙiƙa." "Hmmn!, small Mum ba irin wannar soyayyar nake nufi ba." "Wani irin soyayya aunty?", Sadiya ta tambaya cikin rashin fahimta. Khausar na shirin bata amsa, sai Umar yayi sallama daga bakin ƙofar ɗakin, hakan ya sanya Khausar ta fasa yin magana ta miƙe tsaye, Nayla da tayi bacci a wajan sallah ta kalla, sannan Najla da ke shirin tunkarar ƙofa, dan zuwa wajan uncle U tunda ta ji muryarshi, dakatar da ita Khausar tayi tare da cewa, "Oya go and sleep." Najla tura baki tayi ta wuce gefen Nayla ta kwanta, Khausar ta nufi ƙofa bayan ta amsa sallamar Umar tare da ce masa gata nan fitowa, ta kama handle za ta murɗa sai ta jiyo tambayar Sadiya. "Aunty wani irin soyayyar kike nufi?" Sadiya ta kuma tambaya murya a raunace. "Small Mum idan na dawo za muyi maganar", daga haka ta fice. Sadiya lumshe idanuwanta tayi tare da dafe kanta, domin bata gane nufin Khausar ba sam-sam, ƙiran da ya shigo wayarta shi ya katse mata tunanin da ta nitsa na son gano me Khausar ke nufi, daga ringing tone ɗin ta gane Haidar ne, hakan ya sanya ta ɗauki wayar tana mai jin kaso hamsin ya ragu a cikin abinda ke damunta, cikin soyayya suke wayarsu, duk da ya nazarci ba daidai take ba, hakan ya sanya ya ce, "Hey, what's wrong with you? Na ji wani iri a yanayinki." Murmushi ne ya suɓucewa Sadiya, saboda yaba ƙaunar Haidar da kulawarshi gare ta, tunda har ya gano duk da tana ƙoƙarin ɓoyewa, cikin son kauce mishi ta ce, "I've started missing sweet home." "Ohhh! Really? To shikkenan ai ba zan rarrashe ki tun yanzu na ƙarar da rarrashina ba, let's leave it to next coming Sunday, a lokaci kamar dai wannan, I'll make you forget everyone exists except me and you, kin ga ba za ki tuna missing ba." Cunna baki Sadiya tayi ba tare da ta ce komai ba. Haidar a ɓangarenshi ya ce, "Sweet Al-Sad, i love you soo much, i can't wait for this Saturday, kwana biyar kawai ya rage mana, a na shida za mu mallaki juna." "In sha Allah, I'll be officially Mrs Haidar", faɗin Sadiya, tana jin wani guguwar soyayya na bule ta. "Yeah! Matar Aliyu Haidar AKA Al-Sad." Guntun dariya Sadiya ta yi, daga haka suka ci gaba da wayarsu cikin soyayya da nishaɗi, hakan ya sa Sadiya ta aje batun maganar Khausar a gefe, sun ɗau lokaci sosai suna waya, dan Haidar bai kashe wayar ba har ta gyara komai, ta maida Nayla da Najla wajan kwanciyarsu, ta aje wayar a haka ta je ta watsa ruwa ta zo ta yi shirin bacci, sannan suka cigaba da wayar, yana jin ta tayi addu'an bacci ta shafa shi ma ya shafa, sai da ya tabbatar bacci yayi gaba da ita sannan ya datse ƙiran cike da ɗimbin ƙaunarta da shauƙinta. **** Khausar tana ficewa a ɗakin ta mara wa Umar baya, tana isowa wajan motar lokacin ya sanya basket da Mama ta bayar a back seat, sannan ya buɗe mazaunin direba ya shige, ita ma Khausar ta shiga gefe ta zauna, ya yiwa motar key suka fice a gidan, suna tafe a hanya ya labarta mata yadda suka yi da Abba, tare da cewa, "Akwai matsala fa sis, don Abba ya ƙi fahimta, kai bai ma bari na mishi bayani ba." "Hmmn!, nima dama abinda nake gudu kenan, kowa ya san halin Abba da kafiya, amma dai ɗazu mun yi magana da Mama ta ce gobe idan Allah ya kai mu da safe za ta shiga wajan su Abba su yi magana." "To ma sha Allah, da sauƙi, domin idan Abba ya tirje tsaf zan iya zuwa wani masallacin a ɗaura auren nan, sai dai kawai ku ji labari." Murmushi Khausar tayi tare da cewa, "Sai dai su Abba su ji labari dai, domin ni kam da ni za a kashe a binne." "Wannan haka yake, kece waliyiyar Sadiya, ni kuma waliyin bro." Khausar na dariya ta labarta mishi yadda suka yi da Sadiya tana faɗin, "Da alama ba za a samu damuwa da Sadiya ba, domin ban hangi hakan a idanuwanta ko yanayinta ba, balle ma zantukanta, small Mum ta damu da Yaya Sadeeq sosai kuma tana ƙaunarshi." "Ai duk rainin hankali ke damunsu sis, amma sarai suna son junansu, jira kawai dama suke a ari bakinsu a ci musu albasa", faɗin Umar yana sakin murmushin samun nitsuwa, domin an gama masu wahalar, Abba ma da yardar Allah Mama za ta fahimtar da shi, su Haidar kuma su ɗau na Annabawa, sai kawai ayi bikin tuwo na mai na.   A haka suna hira har suka isa asibitin, Khalid da Sa'ad suka yiwa Khausar da Umar sannu da zuwa, suka fice saboda basu damar magana, Khausar ce ta yiwa Sadeeq magana a tausashe cikin sigar girmamawa da lallashi, shawarwari da sauransu duka, shi dai Umar ƙala bai ce ba har ta kammala, sannan Sadeeq ya buɗe baki kamar bai son yin maganar ya ce, "Thank you sis." Khausar ta amsa tare da musu fatan alkairi, tare da sai da safe ta fice, tare da su Khalid ta dawo gida, suka ajiyeta a ƙofar gidan Mama, su kuma suka wuce gidan. Khausar tana shiga Mama ta mata sannu da dawowa, tare da tambayar ya mai jikin, Khausar ta amsa, tare da sanar da Mama yadda Umar yayi da Abba, Mama ta jinjina kai tana faɗin, "Na sani dama ai hakan na iya faruwa, Abbanku sai a hankali." Khausar ta ce, "Sai ku masa bayani dan nasan ku kam zai saurareku ke da Umma." "In sha Allah hakan za a yi, je ki kwanta abinko dare ya yi." "To Mama sai da safe." "Yauwa mu kwana lafiya a huta gajiya ko." "Allah ya sa Mama." Da, "Amin Ya Allahu", Mama ta amsa, sannan Khausar ta wuce ɗakin Sadiya, ta samu duk sun yi bacci, hakan ya sa ita ma tayi shirin bacci ta kwanta. ⭐️ PLATEU SPECIALIST HOSPITAL. ABUBAKAR SADEEQ POV      *** Bayan ficewar Khausar, Umar ya kammala abinda zai yi ya kishingiɗa, tare da ɗaura system nashi a saman ƙafafuwanshi, cikin ƙwarewa yske sarrafa system ɗin. "Agogo sarkin aiki." Umar ya tsinkayi muryar Sadeeq ya faɗa hakan a kame, ɗan guntun murmushi yayi domin tunda ya ga tun shigowarshi har yanzu Sadeeq bai mishi magana ba, ya ɗauka fushi yake akan abinda ya binciko har yanzu, shiyasa bai kula shi ba shi ma, amma jin abinda ya ce mishi, sai ya bashi amsa yana murmushi,  "Duk aikina ai ban kai ka ba, ko ƙafarka ban kama ba, matashin mai kuɗi duk da ƙananun shekarunka kuwa, aikin da kake yi tuƙuru shi ya kawo har ka wuce waɗanda suka girme maka a shekaru kan batun dukiya, ka ga kai kana gaba da agogo ma, ni fa mamaki nake yi ma yanzu ya za a yi da batun barasar ƙauna? Aiki kake ba wasa yau kana can gobe kana can, yanzu kuma ka ce aure, wa zai yi aikin? Wa kuma zai soshale ya tatile da barasar ƙauna?" Umar ya ƙarishe faɗa yana dariya, idanuwanshi a kan system nashi. "Umar daga kai sai ɗan iska wallahi, in ba iskanci ba me na wannar magana? Kana abu kana tsare gida kamar boss a gaske, amma ka ƙware a maganar banza." Umar na ƴar dariya, ya ce, "Na ƙware a maganar banza kamar yadda ka aje kunya a gefe za ka auri wacce ka kusa haifa ba, Allah ya sa ma dai kar ka ɓalle wa Umma autarta, domin wanna shirmenta ba zai barta ta yi gwaɓi ba, kai kuma a direnka kake wane doki." "Ɗan rainin hankali." "Ƴan rainin hankali dai ni da kai duka, ai ko ƙafarka a nan ma ban kamo ba, kai fa a komai kana gaba da ni bro, wai ba ma za ka tambaya ya muka yi da su Abba ba?" "Dama na aike ka ne?" Sadeeq ya faɗa a taƙaice. "Ni na aiki kaina, kuma komai daidai, Mama ta baka Abba ya lamunce, sai ka shirya amgwancewa ka baza hajarka son ranka." "Ka yi abinda ke gabanka ka bar wa ƴan iska maganar banzarsu." "Ah! ina sam-sam ba zan bari ba, akan barasar ƙauna da ni da kai da kowa ma ƴan iskan ne, dan haka kabarni nayi lokaci ne, kuna fara aje mana yara ai dole na kame bakina na sanya masa code kamar yadda ka saka wa box ɗin ka", faɗin Umar yana dariyar neman magana. Ƙwafa kawai Sadeeq yayi tare da yin shiru, daga haka kuma Umar ke maganar Sadeeq na amsa mishi jefi-jefi, a haka suke hirar har Umar ya kammala ya kwanta, Sadeeq ma ba jimawa bacci yayi gaba da shi, wajajen ƙarfe biyu ya farka, nafila yayi tare da addu'oi, sannan ya koma ya kwanta, ko da asuba ta yi, Umar ne ya fara tashuwa dan har sun kusa makara, sai da ya ɗauro alwala sannan ya tashi Sadeeq, shi ma yayi alwalar, suka bi jam'i a nan ɗaki, bayan sun idar sun shafa addu'a, Sadeeq ya koma ya kwanta ba jimawa bacci yayi gaba da shi, Umar lokaci ya duba, ganin ƙarfe biyar da mintuna arba'in ne, sai ya koma ya kwanta zuwa ko bakwai ne kamun nan ya taɓa bacci. Ƙarfe bakwai da rabi Sadeeq ya farka, sai da ya wanko bakinshi ya fito sannan ya tashi Umar, wanda lokaci ɗaya da tashin da shigowan ƙira wayar Umar, hakan ya sa Umar ya tashi, ya ɗau ƙiran, a gajarce ya amsa wa wanda ya ƙira bayanin da yake mishi sannan ya kashe ƙiran ya wuce toilet. Zuwa takwas likita ya shigo, duba Sadeeq yayi, Sadeeq na ƙoƙarin yin magana a kan sallama, sai likitan ya ce Umar ya bi shi office, yana ficewa Umar ya rufa mishi baya, ko da suka je office ɗin, bayani likitan ya yiwa Umar tare da kafa mishi abubuwan da za a kiyaye game da Sadeeq, da kuma shi ma Sadeeq ɗin ya kiyaye, sai da suka gama tattaunawa sannan ya ba su sallaman. Umar na komawa ɗaki wajan Sadeeq ya samu Khalid ya zo da abun karyawa, amsa gaisuwar Khalid ɗin ya yi sanna ya ce, "An bamu sallama ma, mu tattara mu koma gida, idan kuma zai karya a nan tukunna sai ya karya mu wuce." "Mu je gidan, ma karya a can", faɗin Sadeeq yana tashuwa zaune daga kwancen da yake. Umar da Khalid ne suka haɗa ƴan tarkacen su da babu yawa, Khalid ya tattare ya kai mota, sannan suka fice a ɗakin suka wuce wajan mota, Khalid na mazaunin direba, Umar na seat da ke gefenshi, Sadeeq kuma yana baya ya jingija da jikin kujera, suna ficewa a cikin asibitin, Sadeeq ya sa Khalid ya sauƙe mishi glass na ƙofar gefenshi, fresh air yake shaƙa yana jin nitsuwa na sauƙar mishi, da ƙwarin guiwar tinkarar abinda Umar ya ɓallo mishi, domin har ga Allah masifar binckken Umar ne ya ɓallo mishi wannan ruwa, kuma dole ya tare ruwan. Khalid ya ce, "Amma dai likitocin nan sun kyauta da sallamar safe." Umar ya ce, "Ya matsa musu ya takura musu ya suka iya, sallamarshi ya zame musu dole." Ƴar dariya Khalid yayi, shi dai Sadeeq bai tanka su ba, Khalid ya koma batun company, suka cigaba da tattaunawa da Umar, har suka isa gida. ⭐️ RAYFIELD      SADIYA POV         *** Da sassafe Mama ta sa Sadiya a gaba suka kama aikace-aikace, kamun bakwai sun gama komai, ta haɗa wanda za a kai asibiti, da kanta ta ɗauka ta fice a gidan bata bi ta kan Sadiya, da ke cewa ta bari za ta ɗauka mata ba.   Knocking na ƙaramin ƙofar gidan Mama ta yi, mai gadi ya buɗe mata suka gaisa cikin girmamawa, ya buƙaci ta ba shi basket ɗin ya shigar mata, amma ta ce ta yafe ta wuce ciki. Da sallama Mama ta shigo palourn, Umma ta amsa tana murmushi tare da cewa, "wai ke ce da sassafen nan Maman Sadeeq, da kin huta abinki ai Khalid ɗin zai bi ya amsa ka mun ya wuce." Zama Mama tayi tare da aje basket na hannunta tana cewa, "Umman yara ai fitowa da sassafe ya zama dole, mu da muke nema dole mu buga sammako, fatan dai Abbansu yana nan?" "Yana nan Maman Sadeeq", Umma ta faɗa tana ƴar dariya. "Yauwa maza a taimaka a mini magana da shi, na zaune bai ga gari ba, ai kuwa nima banga ta zama haka ba, babana na son autar Abba." "Sadeeq ne ko rigima, hmmn, wannan baba naki da nemar magana yake." "haka kuma za a yi haƙuri da shi a yi maganar ba, a taimake ni a mini magana da uban amarya." Umma na dariya ta miƙe ta haura sama, ba jimawa sai ga su sun sauƙo tare da Abba, ya ƙaraso ya zauna, cikin girma da mutunta juna Abba da Mama suka gaisa, sannan Abba ya ce, "Ya shirye-shirye kuma?" "Alhamdulillah Abban yara,shirye-shirye fa sai godiya, balle yanzu da abin ke shirin sauya sheƙa, ai yanzu za mu yi shirin gaske." Abba cikin rashin fahimtar maganar Mama da yake bai san ta san da maganar ba, ya ɗauka su kawai Umar ya sanarwa, shiyasa ma ya ce da Umma kar ya ji kada ya gani, yana murmusawa ya ce, "Allah ya shige mana gaba." "Amin Abban yara." Ɗan jima kaɗan palourn yayi shiru, sai can Mama ta ce, "Abban yara na zo ne a kan batun Babana da Sadiya." Abba da sauri ya juya suka haɗa ido da Umma, alamar yaushe ta sanar da maganar, Umma kuma tayi saurin girgiza kai, hakan ya sanya Abba ya nuna kamar bai gano nufin Mama ba, ya ce, "Me kuma ya faru Maman Sadeeq?" Murmusawa Mama ta yi, sannan ta ce, "Maganar dai da Umar ya same ka da ita, a kan mai babban suna yana son autarka, Umar ya faɗa mini yadda kuka yi, kuma haka ne Abban yara, gaskiya ne ba su kyauta ba, domin ba a nema cikin nema, amma kuma dan Allah a duba lamarin da idon fahimta, gida bai ƙoshi ba ai ba za a kai

Chapter 19 of 32