Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya ta kai ga yin saurinta to fa tafiyarta yanda yake haka yake za a gansa, ko gudu ma ita bata gudu da speed sosai, komai idan tana yi kallon rigimammiya ake mata. Haidar kamun ya buɗe idanuwansa sai hango ta yayi, tana ƙoƙarin shigewa gidan, ƴar dariyar da baya yinta kasafai yayi, kuma ta masa kyau sosai, domin wataƙila baya dariyar ne saboda ya san tana masa kyau na ƙure misali, a hanzarce ya miƙe tare da nufan motarsa ya shige, key ya mata sai da ya zo ficewa a gate ɗin sannan ya miƙa wa mai gadin kuɗi masu yawa yana faɗin su raba da ƴan uwansa, mai gadi godiya yayi sosai sannan ya kulle gate ɗin bayan Haidar ya ida ficewa, yana ɗaya daga cikin dalilin da ya sa daga Haidar ya iso suke gaggawan masa hidima, ta hanyar kawo masa kujera da abin sha, domin shi ɗin mai kirki ne da yawan kyauta, yawan alkairin shi ya sanya su da kansu suke wa Sadiya addu'an auran shi, domin shi ɗin mutumin arziƙi ne. Sadiya tana shiga palourn ta tsaya ta sha ruwa a fridge, tana ɗagowa ta jiyo muryan Umma daga sama tana faɗin, "Kema kenan da yanzu ficewanki a gida har kina neman ruwa, ina ga wanda ya zo da jimawa kuma yanzu sai ya ɗau hanya kamun ya isa gida, Auta Allah ya shiryaki da shirme da shiririta, ke ba za ki tuna kai wa mutum ruwa ba idan ba tuna miki aka yi ba, kar ma a kai ga ɗan abin motsa baki, kar fa kije gidansa kina masa haka, domin maza da maganan abin saka wa a baka to kuna iya samun damuwa da shi, Allah dai ya kiyaye ya shiryaki." Sadiya marairaice fiska tayi tare da amsawa da Amin, sannan ta wuce sama, sai da tayi alwala tayi sallah sannan ta sauƙo tana faɗin, "Umma bara naje na dubo Mama." "To ki gaishe ta", Umma ta faɗa tana cigaba da abinda take yi. Sadiya a nitse ta juya ta fice, mai gadi da ya hangota da sauri ya tashi ya buɗe mata ƙofa, yana faɗin a dawo lafiya, tana ƴar guntun murmushi ta amsa tare da ficewa, a ƙafa a nitse ta taka har gidansu, zuciyarta gefe guda cike da kewan Yaya Sadeeq, domin da yana nan da yanzu tare za su taho, ko kuwa da tana dawowa wajan Haidar za ta wuce wajanshi, Yaya Sadeeq ya kasance duniyarta kuma babban wa tamkar uba a wajanta, baki ba zai iya fassara irin matsayinsa da alkairinsa a gare tab ba, domin wani bin takan ji kaman ta fi jin shi a rai fiye da Ya Umar ma da suke uwa ɗaya uba ɗaya. Tana tunanin Yaya Sadeeq bata ankare ba sai jin muryan Mama tayi tana faɗin, "Ke Sadiya lafiyarki kuwa? Kya shigo haka gatsal-gatsal ba sallama." Sadiya marairaice fiska tayi a sanyaye ta ce, "Mama ni banma san na iso har palourn ba, gaba ɗaya hankalina yayi nisa", ta faɗa tare da juyawa ta fice a palourn ta yi sallama, "Assalamu alaikum ", sannan ta shigo. "Wa'alaikissalam", Mama ta amsa tare da ɗaurawa da faɗin, "Hankalinki yayi nisa ya tafi ina Sadiya? Me kike tunani har haka kaman wata mai ƴaƴa goma?" Sadiya ƙarasowa tayi ta zauna gefen Mama tare da ɗaura kanta a kafaɗar Mama tana faɗin, "Mama Yaya Sadeeqna nake tunani, Mama kun ƙi zuwa da ni na gano shi, abun yana damuna sosai Mama, kunsan bazan iya kasancewa cikin salama ba muddin ba Yaya Sadeeq a kusa ko ko bai da lafiya", cikin damuwa ta ƙarishe maganan. Mama ɗaga kan Sadiya tayi a kafaɗanta tana faɗin, "Ni kar ki karyan kafaɗa da ƙaton kanki, yarinya sai son jiki", sannan ta ɗaura da cewa, "Da kike cewa an ƙi zuwa da ke ai kinfi kowa sanin abinda ke tsakaninki da asibiti, mu za mu je da ke ne ki kama rashin lafiyan kema, ayi haihuwar guzuma ɗa kwance uwa kwance, ana ta mai babban suna sannan kema a kama taki tsabgar, a'a kiyi zamanki a gida in sha Allah nan da ƴan kwanaki zai dawo shi ma." Sadiya hawaye ta fara tana faɗin, "Mama amma dai kun san ban yiwa Yaya Sadeeqna adalci ba idan ban je dubo sa ba ko, Mama duk tsanar da na yiwa asibiti, muddin aka ce Yaya Sadeeqn yana can ko Umma, ko Yaya Umar, ko Abba ko Haidar ko kuma ke to Allah zan je, ko da kuwa idan naje zan mutu ne, Yaya Sadeeqna yana asibiti ina gida ina zan samu salama." Mama cewa tayi, "Aikwa dai ba za kije ba balle ma ki mutu dan kin je, kiyi zamanki kawai, ke da za kiyi aurenki ai daman kamata yayi ki sanya wa zuciyarki salama a kan mai babban suna, tunda dai ba binki gidan mijin zai yi ba idan ya aurar da ke shikkenan." Tura baki Sadiya tayi tare da ƙara sautin kukanta tana faɗin, "Ni dan Yaya Sadeeqna yana lafiya ina gidana ai banda danuwa Mama, dan nasan lokaci zuwa lokaci za su ke zuwa dubani har su Yaya Khalid, amma yanzu ni kasancewanshi cikin rashin lafiya ne ya dame ni." "To rasa kunya ɓeran danga, tashi ki bani waje, kina ƙaryar baki cikin salama mai babban suna ba lafiya, amma ai bai hana ki shumfiɗa mini rasar kunya ba, har wani kina gidanki, to masu gida, Allah ya nuna mana kwanakin da suka rage da rai da lafiya mu miƙa ki kowa ya huta da rashin ta idonki, yara ne duk kun zama ƴan zamani ba kunya balle." Sadiya tura baki tayi ta tashi ta wuce ɗakinta, sauya kaya tayi zuwa simple gown kasancewan lokacin zafi suke, saboda damina ya zo ƙarshe ruwa ya ja baya sai sa'i da lokaci. Tana gama sauyawa ta miƙe ta ɗauro alwalan isha'i, wayanta ta ɗauka da ke aje a kan gadonta, dan tun jiya da ta barshi a wajan bata waiwaye shi ba sai yanzun, a cike ta gani da chaji dan Mama ta sanya mata a chaji, ga misscalls da dama da message's, har da na ƙawayenta da basu jima da kammala paper ba, jamb nasu ma bai wuce wata ɗaya ba da suka rubuta, a cikin wannan watan ma suke tsammanin fitowan result na jamb ɗin kamun su jira na waec and neco. Kasancewan ta tura wa Haidar saƙon fatan ya isa lafiya ta wayan Umma, shiyasa bata bi ta kansa ba, ta aje wayan ta yi sallahn isha'i da aka kira yanzu, tana idarwa ta fice dan neman abinda za ta sanya a cikinta, fruit ta samu saura a fridge nasu, fitarwa tayi ta zauna ta yayyanka abunta sannan ta sanya madara, duk da sanyin da yake da shi sai da ta sanya ƙanƙara sannan ta zauna tana shan abinta, ko da Mama ta fito faɗa ta kama mata a kan ta hana ta shan sanyi, Sadiya dai narai-narai tayi da idanuwanta amma bata daina shan abinta ba, sai ma ɗibowa da take da yawa dan kar Mama ta ƙwace, Mama ganin haka sai da girgiza kai kawai ta wuce ta ɗibi nata abincin ta soma ci. Bayan Sadiya ta kammala ɗaki ta koma saboda ƙiran Haidar da ya shigo wayanta, wayansu suka fara kaman ko yaushe cikin soyayya da ƙauna da shauƙi da annashuwa, Haidar ke rigimar shi ne daga yayi magana sai ta tashi ta tafi ba amsa balle sallama, Sadiya sake kulle idonta tayi tana murmushi cike da jin kunya ta ce, "To ai kai ne ka sanya na tafi, amma ai am sorry." Haidar a ɓangarensa hamshaƙin murmushi ya saki tare da cewa, "Bakomai ai ki riƙe sorryn, a lokacin da babyna zai ke miki rigima a ciki to sai kiyi aiki da sorryn." Sake kulle fiska Sadiya tayi tana faɗin bata so, amma a zuciyarta har ta hango kanta da tulelen ciki yanda za tayi kyau, kaman yanda Aunty Khausar tayi kyau da cikin baby Nayla. Sadiya da Haidar soyayyarsa suka cigaba da sha, suna musayan kalaman ƙauna, kaman asabar tasu ta zagayo i yanzu da suke waya. ***MASU TALLA ƘOFA A BUƊE TAKE, KU HANZARTA DOMIN AYI INGANTACCIYAR TAFIYARNAN DA HAJARKU, KU KAWO TALLANKU CIKIN AMINCI A TALLATA MUKU SHI CIKIN ANNASHUWA DA SHAUƘI, KU TUNTUƁE NI A WANNAN LAMBA 09161720046.** ⭐️ PLATEU SPECIALIST HOSPITAL ABUBAKAR SADEEQ POV *** Umar shi ya wuni tare da Sadeeq a asibiti, kuma har zuwa wannan lokacin Sadeeq bai farfaɗo ba, sai da aka yi magrib sannan Sa'ad ya zo, Abba da Khalid kuma sai bayan isha'i suka zo, duk cikin jimami suke zaune tare da addu'an lafiya da tashuwa cikin gaggawa wa Sadeeq. Abba da Khalid gida suka koma wajajen ƙarfe sha ɗaya na dare, Sa'ad da Umar su suka kwana a asibiti, washe-gari da safe Umma ta taho da abin karyawa, sannan Sa'ad ya tafi dan ya shirya zuwa aiki, Umma cikin ƙauna da tausayawa take kallon Umar da ke shan tea a nitse, a sanyaye ta ce, "Kai ma ya kamata ka je gida ka huta Umar, ka samu ka sha iska har ka leƙo muku ma'aikatan naku." Umar janye kofin yayi a bakinsa, idanuwansa a ƙasa cikin girmamawa ya ce, "Umma kar ku damu, ina nan in sha Allah har Sadeeq ya farfaɗo, kuma jinyan namiji ai sai namiji." Girgiza kai Umma tayi ta ce, "Duk da haka ya kamata ka je ka huta, kuma ko ba za ka tafi dan ka huta ba, ya kamata ka tafi ko dan ka dubo masana'antarku, babu kai babu Sadeeq ai masu aikinma ba za su ji daɗi ba." "Khalid yana kula da komai Umma, kuma muna magana da sauran shuwagabannin masu aikin namu daga ko wanne ɓangare." Jinjina kai Umma tayi tare da barin maganar iya haka, dan daman ta san fiye da haka na iya yiwuwa, Sadeeq da Umar sai Allah, a tsakankaninsu sai ka rasa wa ya fi wani son ɗan uwanshi da ji da lamuranshi da damuwa da damuwar ɗan uwan shi, shiyasa kullum cikin addu'an tsari daga mahassada da maƙiya da munafukai suke musu, Allah ya sa zumuncin ya ɗaure har jikoki da tattaɓa kunnuwa. # Hareeyh # 09161720046 # 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩 # 𝙇𝙞𝙠𝙚 & # 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚 [07/12/2025, 13:34] Uwar Batoorl✍️❤️🥰: 💔NAUYIN BAKI....👄💔 Na Uwar Batoorl. 𝗕𝗜𝗦𝗠𝗜𝗟𝗟𝗔𝗛𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗠𝗔𝗡𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗘𝗘𝗠 اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤🤍 🅿️ 16 _ 20 ⭐️ Kwana ɗaya, kwana biyu.... har aka ci kwanaki shida masu kyau, Sadeeq na a kwance maƙale da oxygen, ba abinda ya sauya kuma ba wani ci-gaba da aka samu, duk da kuwa likitoci na matuƙar ƙoƙarinsu, wajan kula da shi da ba shi duk wata taimako da ta kamata, kuma Umar na nan a tare da shi a ko da yaushe, sai Abba sun zo da dare sannan yake tafiya gida ya je yayi wanka yayi uzurinsa ya dawo, su kuma sai su tafi, dan shi yake kwana da Sadeeq ɗin, watarana Sa'ad ya taya shi, watarana kuma Khalid ke taya shi. A gefen ma'aikatarsu kuma, Khalid ke ƙoƙarin zuwa yana duba duk abinda ya kamata, Umar kuma daga asibitin yake duk abinda zai iya yi a waya ne, ko ko a system, don shi ne MD na companyn nasu dama. Ɓangaren su Umma kuwa suna iya ƙoƙarinsu wajan addu'oi, sadaka da sauransu, kuma daga ita har Mama suna kan gyara Sadiya wacce a yanzu bikin ke matsowa, ya rage sati biyu, sai dai a kwanakin kaf Sadiya bata da kuzari, duk fushi take, fama take da damuwa a kan rashin zuwa ta gano Yaya Sadeeq nata, Umma da Mama sun zuba mata ido ba wanda ya ce ta shirya a je da ita, hakan ba ƙaramin ƙara ƙona mata zuciya yake ba. Haidar ma yana amsan nashi rigiman, domin duk ta birkice mishi akan zuwa ta dubo Yaya Sadeeq, ya ƙoƙarta wajan ƙiran Yaya Umar a waya ya tambayi asibitin da suke zai zo dubiya, amma Yaya Umar bai sanar mishi ba dan Mama ta hana shi, sarai sun sani muddin aka sanar mishi to zai kwashi Sadiya ne su je asibitin, kuma ita da asibiti ba shiri suke yi ba sam-sam. Sadiya banda kuka da damuwa ba abinda ta sanya wa ranta, kuma fushinta da Mama ya fi yawa shiyasa ma ta tattara ta koma wajan Umma, duk da a can ɗin ma ko da yaushe tana ɗaki ba fitowa take yi ba, yau da ya kama Lahadi zai cika sati guda ciff da kai Sadeeq asibiti, Sadiya tana jin fitan Abba da Umma zuwa asibiti, ta fito palourn jiki ba ƙwari, a sanyaye take tafiya tana son ta tafi gidan Mama ne ta kulle kanta a ɗaki, ko in aka ga tana shirin mutuwa za a barta ta gano Yaya Sadeeq nata, tana ƙoƙarin ficewa a palourn ta tsinkayo muryan Khalid, dan shi yau bai je asibitin ba saboda a gajiye matuƙa ya dawo daga company jiya, wuni yayu hutawa yau, yana ganin Sadiya cikin zolaya ya ce, "Sady amarya sai ina? Kinsan dai Yaya Sadeeq ya hana ki sintiri da darennan ko? To a kunnenshi kuwa." Sadiya tana jin abinda Khalid ya faɗa sai ta fashe da kuka, kuka take na kewan Yaya Sadeeq da hanata zuwa ganinshi da aka yi, kuka take na kewan duk wasu kulawa da yake bata da dokoki da sauransu, a kwanciyansa ciwon nan ba za ta iya tuna dokarsa nawa ta take ba, ya hana ta fita daga zaran magrib tayi, amma kuwa tana fita daga gidan Umma zuwa na Mama, ya hana ta zama ba ɗan kwali amma haka take zama yanzu abinta tunda ba idonsa, ya hana ta yawan waya-waya da danne-danne, amma yanzu sai su raba dare suna waya da Haidar, maganan karatun Ƙur'ani kuwa ta kwana biyu bata taɓa ba ma, Islamiya kuma daman su Umma ne suka ɗaure mata wajan zama; a kan ba za ta je ba tunda suna gyaran jiki, duk da kuwa ya ce ta dinga sanya hijabi da hula p-cap ta je, dan p-cap ɗin zai tare mata ranan da ba'a so ya daki fiskanta, dokokin Yaya Sadeeq ba za su irgu ba, domin ya zame ne kaman uwa da uba a gare ta, yana shagwaɓa ta amma yana tarbiyartar da ita, babban yaya madadin uba. Khalid jin Sadiya bata bashi amsa ba sai kukanta da ya tsananta, da sauri ya ce, "Allah ya huci zuciyarki ƙanwar Yaya Sadeeq, ni a ta ya ma zan faɗa mishi bayan har yanzu bai farfaɗo ba." Sadiya ƙara kukan ta yi, tare da juyowa ta dawo ciki, a kan kujera ta zauna tana cigaba da kukanta, Khalid da ya ga kukan ba mai ƙarewa bane, sai ya ce, "Sady wai kukan me kike yi ne haka?" Sadiya cikin kuka ta ce, "Yaya Khalid su Mama sun hanani naje na kalli Yaya Sadeeqna." Numfashi Khalid ya sauƙe domin ya ɗauka ko wani abun ne ya faru, duk da ya san wannan wani abu ne ga Sadiya ko Yaya Sadeeq, saboda shaƙuwansu da yanda suka damu da juna, a kan Sadiya sai Yaya Sadeeq ya ɓata da kowa, sai dai kuma zuwan Sadiya asibiti ai ba mai yiwuwa bane, tunda ita ba ƙaunar asibiti take ba, dan akwai lokacin da Yaya Umar yayi hatsari, yanda ya jikkata ma an ɗauka ba zai rayu ba, domin motar da yayi hatsari da ita bata sake moruwa ba, ko da aka sanar da gida cikin tashin hankali da ɗimauta duk aka ɗugunzuma aka tafi FMC PLATEU har da Sadiya, amma da yardan Allah ana shiga asibitin tun ba a isa ɓangaren da Yaya Umar yake ba, Sadiya ta kama rawan jiki tana abu kaman wacce za ta shiɗe, sai da aka fice da ita a asibitin sannan ta dawo dai-dai, ita haka halittarta yake tana matuƙar tsoron asibiti sam-sam bata son asibiti, domin da farko an ɗauka ma ko aljanune gare ta, amma anmata ruƙiya ba komai, kawai bata son abu da asibiti ne ita, maimakon ta dubo mara lafiya sai ita ma ta kama yin cutar, dan muddin ta shiga cikin asibiti ta fito to sai tayi ciwo a gida, duk tsananin ciwonta kuma bata wuce chemist, ko me zai same ta to a gida ake jinyarta, har a gama treatment ta warke. Khalid bayan ya gama dogon tunaninsa, cikin sigar lallashi ya ce, "Sadiya kiyi addu'a kawai Yaya Sadeeq ya farfaɗo da wuri ya dawo gida, kin ga zuwanki asibiti wata matsalarce babba ma kuwa, kuma yanzu ke da kuke ganiyar shirye-shiryen biki in ba Allah ya aiko ba ya kama dole ai ba abinda ake so ya same ki, mutane sukan ce waɗanda suka kusa aure tsautsayi na bibiyarsu." Girgiza kai Sadiya tayi cikin kuka ta ce, "In sha Allah ba abinda zai faru Yaya Khalid, dan Allah ni ka kaini, ko ka faɗa mini inda aka kai shi sai Haidar ya kai ni, ko kuma ma naje da kaina na dawo lafiya." "A'a Sadiya, ni ba ruwana, idan wani abu ya faru ai Umma kaɗai sai ta cinye ni ɗanye, idan Yaya Sadeeq kuma ya ji labari kinsan zai iya ball da ni a kan haka, kwanaki da kika sa na taimaka miki kika je gidan su ƙawarki har kika kai bayan Magrib, kina sane ai sarai marina Yaya Sadeeq yayi a kan haka, to ba ruwana." Sadiya kuka ta cigaba da yi tana roƙon Khalid, shi kuma ya dage ba ruwansa, daga ƙarshe cewa yayi, "Kinga kiyi maza ki tashi ki tafi gidan Mama, idan su Abba sun je to Yaya Umar yana dawowa gida yin wanka, dan haka sai ki mishi kukan ko zai tausaya miki ya barki ki je." Da sauri Sadiya ta miƙe tare da gode wa Khalid da dabaran da ya bata, ficewa tayi dai-dai tana isa ƙofan gidansu, dai-dai Umar ya fito a mota ya kulle zai shiga gida, da mamaki ya juya yana kallonta jin yanda take kuka kaman an mata mutuwa, ba tare da ya ce mata ƙala ba ya juya ya shige gidan, ita kuma ta mara masa baya tana kan kukanta, duk da a zuciyarta addu'a take Allah ya ɗaurata a kan Yaya Umar ya ce zai tafi da ita, dan ta fi kowa sanin halin Yaya Umar na zafi, sam-sam baya raga mata, idan ya raga mata to ta ci albarkacin Sadeeq ne, amma shi sam baya ɗaukan rigimarta da shiriritarta, shi da Mama, Umma da Yaya Sadeeq ne daman suka shwagaɓa ta, Yaya Umar bai sha mishi kai ba yanzu yayi ball da ita. Umar na shiga palourn, Sadiya ma ta shigo da kukanta, har zai wuce hanyan ɗakinsa sai kuma ya tsaya ya dakata, fiska a haɗe ya ce, "Ke kukan me kike wa mutane? Uban wa naki ya mutu?" Sadiya cikin ɗan tsoro-tsoro da shagwaɓa-shagwaɓa ta ce, "Ya..yayyy...Yaya Umar ina..ina..inaso ne naje na kalla Yaya Sadeeq, kuma..kuma..kuma sai Um..Umma da Mamaa suke ƙi, kuma wallahi inason na ganshi, inban ganshi ba zuciyata kuma zan mutu", ta ƙarishe faɗa cikin rawar murya, ga hawaye masu rauni da ke zubo mata. Umar kallon baki da hankali ya yiwa Sadiya, sannan ya wuce ɗakinsa, ya watsa ruwa ya sanya jallabiyansa ya feshe turaruka masu daɗin ƙamshi sannan ya fito, Umar ma ba baya ba wajan haɗewa da kyau da suffar jarumta, hasken fatan Umar irin na Sadiya, hatta da wushiryasu iri ɗaya dan wajan marigayin mahaifinsu suka gado, sai dai shi Umar bai da dimple, wannan kuma a wajan Mama Sadiya ta gado, Umar dogo ne mai tsayi da ƙaƙƙarfan jiki ga faɗin ƙirji, yana da ƙira matuƙa mai kyau da ɗaukan hankali, suna ɗan kama da yanayi na jini da Sadiya, amma dai kaman ba sosai ba, Umar yana da zafi sosai, kuma bai cika haƙuri ba, amma yana da biyayya, kuma yana da kiyayewa yayi abinda ya kamata, yana da magana sosai amma banda da Sadiya, domin a wajan Sadiya ganinsa take kaman dodonta, dan tana yin gar-gar zai make ta baya kuma son reni, albarkacin Sadeeq kawai take ci, amma duk da haka idan tayi wani abun idan ya aika mata da wani irin kallon za mu haɗu ne, a take za ta sha ruwan jikinta ta nitsu, sam-sam shi da Mama basa ɗaga mata ƙafa. Sadiya tana zaune a palourn tana kuka da kuma ƙarfi, dan ya jiyo, har ya fito tana kukan, bai bi ta kanta ba ya juya ya nufi fita, sai da ya kusa fita a palourn sannan ya dakata ya ce, "Ki rufe wa mutane baki kamun na ɓaɓɓallaki, in asibitin kike son zuwa to ki shirya maza gobe za a kawo ki, kuma idan kika yi halinki da kika saba a asibiti, ina mai tabbatar miki da sai na yi ƙuli-ƙulin kubura da ke, tun da ance miki zaman daɗi ake a asibitin da muke fama", yana gama faɗa ya fice, cikkn jin haushin iyayinta, akan me simple and short ta buɗe baki ta roƙa za ta asibiti, sai ta kama kuka kuma akan me? Me aka mata? Uban wa ya mutu? Yarinya kawai ta zama kaman wata goyon gauro. Sadiya hamdala tayi tare da saurin haɗiye kukanta, farinciki take gobe za ta je ta gano Yaya Sadeeq nata da yardan Allah, da haka ta miƙe ta wuce ɗaki, bata jima ba da shiga ɗakin ba ta jiyo sallaman Mama, fitowa tayi tare da mata sannu da dawowa, Mama da ido take binta da kallo har ta fice, sannan ta girgiza kai tana addu'an shiriya ga tilon ƴar tata, tare da fatan Allah ya sa idan ta shiga gidan aurenta ta gyaru kuma ta shiga ne sai mutuwa. Sadiya tana shiga palourn ta samu Abba da Umma a zaune, Sa'ad na daga gefe, don yau shi ne a gida, Khalid sun koma tare da Yaya Umar za su kwana can. Sadiya kanta a duƙe ta shigo da sallama, duk suka amsa mata, ɗan rusunawa tayi tare da faɗin, "Sannunku da dawowa Abba da Umma da Yaya Sa'ad." Amsawa duk suka yi suna murmushi, ita kuma ta miƙe ta cigaba da tafiya za ta haura saman bene, Abba ne ya dakatar da ita, yana murmushi ya ce, "Auta zo nan abinki." Idanuwanta cikowa suka yi da ƙwalla, sannan ta juyo a sanyaye kanta a ƙasa har ta ƙaraso gaban Abba, tsugunawa tayi tana ƙoƙarin mai da hawayenta, amma sai da suka gangaro. Abba ɗagota yayi tare da zaunar da ita a gefensa, yana faɗin, "Share hawayenki Auta, faɗa mini wa ya taɓa ki, dan anga Yayanki ba lafiya za a ke cin zalinki ko, to Abbanki yana nan." Sadiya fashewa tayi da kuka, tana kuka ta ce, "An hana ni naje na ga Yaya Sadeeq Abba." Shafa kanta Abba yayi, tare da cewa, "Kwantar da hankalinki Auta, ai baki sanar da Abba ba shiyasa, amma kinga yanzun da magana ta iske Abba, ai zuwa ya zama dole, babu kuma mai hana ki, kije ki kwanta kiyi bacci hankali kwance, gobe in sha Allah ni da kaina zan kai ki, ki gano Yayanki, wa ya isa ma ya hana Sadiya zuwa ga Sadeeq." Ɗiff! Haka kukan nata ya ɗauke ta ja ajiyan zuciya, tare da sakin murmushi, da siririyar muryanta da kukan da ta kwashe kwanaki tana yi ya cinye, ta ce, "Nagode Abba, Allah ƙara rufin asiri da arziƙi." "Amin Auta, Allah ya muku albarka." Da amin duk suka amsa, sannan Umma tana murmushi ta ce, "Shikkenan fushi da ƙunci sun ƙare, Abba ya kashe case ko?" Sa'ad dariya yayi ya ce, "Ai kuwa dai Umma, dan tun da Yaya Sadeeq ya kwanta a asibiti, Sady ke fushi da ƙunci, ƴar dariyarnan tata da tsokana duk babu, ƴar rawan kai irin ta amaren da suka kusa aure duk babu, wa zai kalli Sady ya ce aurenta nan da 2 week's?" Abba danƙwalon Sa'ad yayi tare da cewa, "Mai anguwan garinku Sa'adu, ka ƙyale mini Auta da zolayarka, kuma Abbanta yana kallonta ya hangi ƙyalƙyalin alaman da ke nuna ta kusa aure." Sadiya hannayenta ta sa ta rufe fiska cikin jin kunya, sannan ta miƙe ta haura sama tana ƴar murmushi, ga farin cikin za ta je ta gano Yaya Sadeeq, ga batun aurenta da Haidar nata, da idan mutum yayi sai taji kaman ta mishi kyauta. Sa'ad ma miƙewa yayi ya shige ciki yana dariya, dan ya kwana biyu bai ga Sadiya a irin shauƙin ba.

Chapter 4 of 32