Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Umma dubanta ta mayar ga Abba, cikin magana da ladabi ta ce, "Abban Sadeeq, kana ganin ba wata matsala a zuwan nata?" "To matsalar da rashin zuwan nata yake haifarwa ai ya fi na zuwanta, dubi yanda yarinya duk ta zama kaman ba ita ba, damuwa duk ya lalatar da kumarinta da kuzarinta, kawai ta je koma menene Allah ya kawo da sauƙi, balle ma a jikina nake jin in sha Allah ba abinda zai faru sai alkairi." Umma jinjina kai tayi ta ce, "Allah ya sa haka." "Amin Ya Rabbi Halimatu", faɗin Abba yana sauƙe numfashi. Daga haka duk suka yi shiru na mintuna, sannan Abba ya miƙe ya nufi haurawa sama, Umma ta tashuwan tayi ta rufa masa baya, suka wuce ɗakinsa kai tsaye. Sadiya cikin tsananin shauƙi da farinciki tayi waya da Haidar yau, kuma ya fahimci hakan a yanayinta, hakan ya sanya bai yi ƙasa a guiwa ba wajan tambayan dalilin farin cikin, ta sanar mishi Abba da Yaya Umar sun amince za ta asibiti, shi ma ya taya ta murna matuƙa, duk da gefe guda na zuciyarsa tunani ne na Allah ya sa kar komai ya same ta, dan shi ma ya san lalurarta ta zuwa asibiti, haka dai suka ƙarishe wayansu cikin ƙaunar juna, suka yi sallama, Sadiya ta kwanta cikin farinciki matuƙa, har mafarki tayi Yaya Sadeeq ya farka ya dawo gida. ***MASU TALLA ƘOFA A BUƊE TAKE, KU HANZARTA DOMIN AYI INGANTACCIYAR TAFIYARNAN DA HAJARKU, KU KAWO TALLANKU CIKIN AMINCI A TALLATA MUKU SHI CIKIN ANNASHUWA DA SHAUƘI, KU TUNTUƁE NI A WANNAN LAMBA 09161720046.** ⭐️ PLATEU SPECIALIST HOSPITAL ABUBAKAR SADEEQ POV *** Umar dama tun da safiya Sa'ad ya sanar da shi batun Sadiya, hakan ya sanya da ya koma ta yi rigimarta ya ce ta shirya, dan daman ko bata yi rigimar ba zai ce ta shirya ɗin. Bayan dawowansa su Abba sun tafi, shi da Khalid ne zaune a ɗakin da aka kwantar da Sadeeq, Khalid ya ce, "Yaya Umar." "Na'am Khalid", Umar ya amsa idanuwansa na kan system da ke gabansa yana dudduba ayyukan company. Khalid ɗan sosa kanshi yayi sannan ya ce, "Yaya Umar please a bar Sady ta zo ta duba Yaya Sadeeq, baka ga ba yanda ta koma ba, duk ta zama abin tausayi har Yaya Sadeeq da ke kwance jinya ma ya fi ta kyan gani, kuma ita da ake shirye-shiryen aurenta ai ya kamata a kalleta da kumari ta yi ɓul-ɓul, ba damuwa ya ramar da ita ba, dan Allah Yaya Umar ka yiwa su Mama magana su barta ta zo, na san idan kai kayi magana za su amince." Umar kallon Khalid yayi fiisha, sannan ya ce, "Da alama dai daman kai ka turo mini ita ta dinga yi mini halinta na kukan banzan nan ko?" Girgiza kai Khalid yayi da sauri yana faɗin, "Ba ni bane Yaya Umar, ni banma san ta fice a gidan ba, dan ko komawana daga wajan aiki na jiyo motsinta ne daga kitchen za ta wuce sama, amma ko magana ba muyi ba." "Ya yi kyau to, gobe kamun ka wuce wajan aiki za ku taho tare ka aje ta, ka amshi saƙonnan sai ka wuce", Umar ya faɗa har sannan idanuwansa na kan system da ke gabansa. Khalid washe baki yayi cikin murnan hankalin Sadiya zai kwanta, ya ce, "Allah ya kai mu goben Yaya, Allah ya bai wa Yaya Sadeeq lafiya wadatacciya." "Amin", Umar ya amsa a taƙaice ya cigaba da aikinsa. Khalid sosai ya ji daɗi, dan a duniya suna ji da Sadiya suna sonta, kwatankwacin yanda Yaya Sadeeq ke son ta da kulawa da ita, a cikin Abba su huɗu ne kawai, Yaya Sadeeq, Aunty Khausar, Yaya Sa'ad sai kuma shi Khalid, sam basu da ƙaramar ƙanwa mace, shiyasa shigowan su Sadiya rayuwansu, ya sa duk suke ji da ita suke ƙaunarta. Har kaman zai ƙira Sadiya ya mata albishir, sai kuma ya fasa ya cigaba da danna wayarsa kawai. Washe-gari da wuri Khalid ya tattara abinda zai tafi gida da su, ya tafi, yana zuwa ya samu har an kusa kammala abun karyawa, kasancewan yana son shiryawa da wuri, bai tsaya bi ta yiwa Sadiya albishir ɗin ba tukunna ya wuce yayi wanka ya shirya cikin ƙananun kaya, Khalid mai kyau ne, matashin saurayi mai kimanin shekaru ashirin da huɗu. Khalid ya kammala ya fito kenan, ya samu Abba, Sa'ad da Sadiya har Umma su ma sun fito a shirye tsaf, gaishe da Abba da Umma yayi, sannan Sa'ad, sai ya dubi Sadiya yana faɗin, "Ke kuma irin wannan gayu haka sai ina haka? ƙanwar Yaya Sadeeq Amaryan Haidar." Sadiya washe baki tayi tare da ɗaga ma Khalid babban yatsanta, alaman jinjina shawaransa ta jiya tayi, tana murmushi mai kyau ta ce, "Sai wajan Yaya Sadeeqna." "Au! Wa ya riga ni yi miki albishir ɗin Yaya Umar ya amince ki je, ya ce ma na kai ki." Sadiya murmusawa tayi, tare da yi masa nuni da Abba amma da ido, kamun Khalid ya ce wani abu sai Abba ya ce, "To wannan dai zuwan Abbanta ne ba na Umar ba." Khalid ƴar dariya yayi tare da cewa, "Congrats ƙanwar Yaya Sadeeq." Daga haka Sadiya ta ɗauki basket, Umma ta miƙa wa Khalid flask Sa'ad ya riƙe sauran abubuwan suka fice. Umma da Abba da Sadiya mota guda suka shiga direba ya ja su, Sa'ad da Khalid kowannensu ya shiga tashi motar dan daga asibiti duk wajajan aikinsu za su wuce, shi Sa'ad shi ne ke kula da gidan man Abba, shi kuma Khalid a companyn Sadeeq yake aiki. Umma da Abba hira suke a kan Khausar da ta ƙira tana shirin zuwa biki, kuma tana tambayan Yayanta Sadeeq dan tana ƙiransa baya tafiya, Abba ya ce lallai shi ma ta ƙira shi akan haka, amma daman ya kwaɓi su Sa'ad har Umar, akan kar wanda ya sanar mata Sadeeq ba lafiya, a barta kawai sai ta zo bikin, in zuwa lokacin ya ji sauƙi shikkenan, idan bai ji ba kuma to ta zo ta gani, Umma ta jinjina kai dan ita ma daman hakan ta tsara. Sadiya tana lafe a jikin kujera, tana jin hiran su Abba sama-sama, tana addu'an samun nitsuwa a zuciyarta har bacci yayi gaba da ita, har suka isa asibitin tana bacci, sai da direba ya parker a gefen ward da Sadeeq yake, sannan Umma ta dubi Abba, tare da cewa, "Auta fa bacci take yi." "Ki ƙira sunanta da bismillah da addu'a sannan ki taɓa ta, ta taso mu shiga ciki", Abba ya faɗa yana ficewa a motan, tare da zagayawa ɓangaren da Sadiya take ya buɗe ƙofan. Umma bismillah ta yi, murya a tausashe sosai ta ƙira sunan Sadiya, sannan ta ɗan taɓa kumatunta tana maimaita sunanta, "Auta³, tashi mu shiga ciki ki kalli Yaya Sadeeq ɗin naki." Sadiya cikin bacci ta soma jin tsikan jikanta na tashi, kamun ta nisa a hakan ta tsinkayi muryan Umma na ƙiran sunanta, bismillahn da Umma ta yi shi ya dirar mata a kunnenta, ya ankarar da ita yin bismillah tare da addu'an farkawa a bacci, a nitse ta wara idanuwanta suka sauƙa kan Abba da ya zuba musu ido yana murmushi, motsawa tayi tana ƙoƙarin yaƙar tashuwar tsikan jikinta da rawan da jikinta ke ƙoƙarin ɗauka, a haka ta lallaɓa ta fito a motan, tana arba da haraban asibitin a take wani juwa ya ɗibeta, tayi baya za ta faɗi, da sauri Umma ta tallafota jikinta tana faɗin, "Ki yi addu'a Auta, za ki samu nitsuwa da ƙwarin guiwa." Jikin Sadiya rawa yake da gaske idanuwanta na ƙoƙarin tara ƙwalla, taku ɗaya biyu kawai hawayen suka fara gangarowa jikin ya kama mazari sosai, Umma kiɗimewa tayi ta juya ga Abba tana faɗin, "Abban Sadeeq ko za a haƙura ta koma motan direba ya maida ta gida kawai?", Umma ta faɗa idanuwanta na tara ƙwalla, dan rawan da jikin Sadiya yake ya yi yawa. Abba kamo kafaɗan Sadiya yayi daga jikin Umma, a nitse ya ce, "Halimatus-Sadiya, wajan Yaya Sadeeq naki za ki je fa, maza ki daure kinji yarinyar kirki ƴar albarka, ki ta maimaita Innalillahi wa Inna ilaihiraji'un." Sadiya jikinta na rawa ta gyaɗa wa Abba kai, sannan ta koma jikin Umma ta lafe, duk da har lokacin jikinta na rawa, a haka suka cigaba da takawa har suka shige ciki, ruwa lokacin Sadiya ta kusa ficewa a hayyacinta, kuka take mara sauti, har wani jajjan numfashi take kaman za ta shiɗe, Umma a gigice ta ce, "Dan Allah a maida ta Abban Sadeeq, wallahi yarinyar nan tausayi take bani." Abba jinjina kai yayi alaman su juya, da sauri Sadiya ta girgiza kai, tana buɗe baki da nufin magana sai sautin kukanta ya fito, cikin kukan take faɗin a barta dan Allah, suna cikin haka sai ga Umar, tana ganinshi ta soma miƙa mishi hannu, cikin kuka take cewa, "Yaya dan Allah ka kai ni wajan Yaya Sadeeqna, dan Allah." Umar amsanta yayi a hannun Umma, a haka jikinta na rawa ya riƙeta a jikinsa har suka ƙarasa cikin ɗakin da Sadeeq yake, tana kuka tana a kai ta wajan Yaya Sadeeq. Har gaban gadon Umar ya kai ta, a dake ya ce, "Za ki iya tsayuwa?" Da sauri Sadiya ta jinjina kai alaman za ta iya, sai Umar ya sake ta yana faɗin, "To maza ki rufe wa mutane baki......", maganan bakinsa ne ya maƙale sakamakon na'urar da ke saƙale a jikin Sadeeq da ta ba da sauti, da sauri Umar ya juya, idan ba gizo idanuwansa ke masa ba yatsun Sadeeq ke motsi, ai da sauri ya hanzarta ya fice dan ƙiran likita, Umma da Abba da su Khalid da suke tsaye a waje, ganin Umar ya fito a hanzarce, da sauri hankali tashe suke tambayansa lafiya? Umar yana tafiya yake faɗin, "Idan ba gizo idanuwana suka mini ba to Sadeeq ya motsa." Bai gama rufe baki ba, Khalid da Sa'ad suka rufa masa baya dan ƙiran likita, Umma da Abba kuma suka shige ɗakin da sauri suka yi wajan gadon da Sadeeq ke kwance. Sadiya dama Umar yana sake ta, ta riƙe ƙarfen gadon tare da runtse idanuwanta dan ta tattaro iya ƙarfin guiwanta, idanuwanta a kulle take faɗin, "Yaayaa nah, dan Allah ka tashi, Yaayaana ka daina wannan zaman asibitin bana so bazan iya jure abinda nake ji ba", cikin matuƙar karaya da gajiya da sarewa tayi maganan, tare da fashewa da matsanancin kuka ta ɗaura kanta a saman ƙirjinsa tana kuka jikinta na kan rawa har ƙafafuwanta suna ƙoƙarin gaza ɗaukanta. Umma da Abba a haka suka shigo suka samu Sadiya, ga Sadeeq nan har ya wara idanuwansa, amma wani irin kai da da kawowa alaman da ke a jikin na'urarsa ke yi da mugun sauri, wanda hakan ke dai-dai da bugun zuciyarsa, da sauri Umma ta kamo Sadiya da niyan ɗago ta, amma Sadiya ƙam-ƙam ta ƙanƙame Sadeeq, Abba na ƙoƙarin kai hannu, sai ga shigowan likitoci da su Umar, da sauri likitan ya ce a ɗaga Sadiya a fice da ita cikin faɗa, saboda barinta da aka yi har ta kwanta a ƙirjin mara lafiyan, kuma a saitin da zuciyarsa take, sam hakan bai yi ba. Umar ne ya ƙaraso, caɗak ya ɗage Sadiya ya nufi waje da ita, wacce zuwa lokacin ta sume, su Umma duk suka rufa musu baya, bisa umurnin likitoci a kan duk su fita, dan tun kan a ɗage Sadiya ma suka fara bai wa Sadeeq taimakon da ya kamata. Sadeeq da tun da muryan sautin kukan Sadiya ya dirar masa a ƙwaƙwalwa da zuciya, a take ya motsa yana jinta a jikinsa kuma ya ƙoƙarta ya buɗe idanuwansa, wani irin gudu da ƙarfi zuciyarsa ke masa kaman za ta faso ƙirjinsa ta fito, ji yake Sadiya da ta kwanta a ƙirjinsa saitin zuciyarsa to taimakonsa ta yi da zuciyar ta fito, duk kuka da maganganun Sadiya yana jin su sarai, amma ba zai iya motsa komai nasa ba bayan idanuwansa da ya ƙoƙarta ya buɗe ko zai kalli kyakkyawar fiskarta, da Umar ya ɗage Sadiya a jikinshi, cikin rauni da nauyin da hannunsa ya masa ya motsa da niyan ya kamo Sadiya, amma sai hannun ya saki ya ɓingire, idanuwansa ya karkata ya bi su Umar da kallo har suka fice, amma bai samu ganin fiskanta, idannuwansa ya maida ya lumshe, ciki-ciki murya ba sauti ya buɗe tsadadden bakinshi ya ƙira sunanta, "Saa..dii..yaaaa", a rarrabe ya ƙira sunanta kuma ƙasa-ƙasa sosai, domin indai ba kunnenka ka kai wajan bakinsa ba, to ba za ka ji sautin ba, sannan in idanuwanka ba sa ganin bakinsa ba za ka gane me ya faɗa ba, daga haka sunanta na ɗaukewa a bakinsa, bugun zuciyarsa ya tsaya, numfashinsa ya ɗauke ɗiff. *** Za ku iya samun littafin a wannan manhajoji. BAKANDAMIYA HIKAYA. AREWABOOKS. @Uwarbatoorl96 WHATSAPP 09161720046 a kan Naira #500. Idan littafi ya zama completel 1k yake in sha Allah. # Hareeyh # 09161720046 # 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩 # 𝙇𝙞𝙠𝙚 & # 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚 [07/12/2025, 13:34] Uwar Batoorl✍️❤️🥰: *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.}``` ✏️ ____________(✪)______________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• 💔NAUYIN BAKI....👄💔 Na Uwar Batoorl. 𝗕𝗜𝗦𝗠𝗜𝗟𝗟𝗔𝗛𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗠𝗔𝗡𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗘𝗘𝗠 اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤🤍 🅿️ 21 _ 25 ⭐️ Numfashin Sadeeq na ɗaukewa, na'urorin suka dakata. Likitocin azama suka kuma badawa tare da duƙufa ka'in da na'in wajan ceto numfashinsa, duk wani abu da ya kamata sun yi amma numfashin Sadeeq ya ƙi dawowa, sun yi zufa, sun gaji, sun sare, har suna sadakar da ran majinyacin nasu yayi halinshi, ɗaya daga cikin likitocin ne yayi ƙasa da face mask nasa, ya kai dubansa ga wanda da alama shi ne babba a cikinsu, da harshen turanci ya ce, "Sir, kaman fa ya cika." Likitan da ya kasance babban, girgiza kai kawai yayi idanuwansa na a kan na'urar da ke jone da ƙirjin Sadeeq, gyara hannun rigan shi ta likitoci yayi tare da yiwa ɗaya nurse magana, ya miƙa wa nurse ɗin sirinjin da ke a hannunshi, da iya ƙarfinshi ya soma danna ƙirjin Sadeeq da duka hannayenshi biyu, a take Sadeeq ɗin ya ja wani dogon numfashi, ba tare da ɓata lokaci ba kuma suka cigaba da yi mishi abinda ya kamata. Sun ɗau lokaci ƙwarai matuƙa sannan suka samu komai ya dai-daita, numfashinsa ya saitu suka mishi alluran bacci saboda ya ɗan huta, dan zuciyarshi ta yi bugun da ya wuce ƙa'ida, dole ana buƙatar ya ƙara hutawa. A ɓangaren su Sadiya, Umar na fitowa da ita a ɗakin bai tsaya ba, kai tsaye in da su Abba suka yi parking ya nufa, da sauri direba da ke a tsaye kusa da motar ya buɗe ma Umar ƙofa, a gidan baya ya kwantar da Sadiya, sannan ya dubi direban ya ce, "Ka kai ta wajan Mama", iya haka ya faɗa a taƙaice ya juya, Umma da ke tsaye a bayanshi ta ce, "Ita kaɗai za a mayar gidan?" "Eh Umma, su je Mama za ta kula da ita, bai kamata daga ku har Abba ku bar asibitin ba, ya kamata mu ji me ake ciki tukunna", Umar ya faɗa cikin ladabi, duk da babu nitsuwa sam a muryarshi. Umma jinjina kai tayi, tare da jaddada wa direba ya kula, sannan ta musu addu'an isa lafiya, ita da Umar suka juya suka koma cikin asibitin, a tsattsaye suka samu su Abba a inda suka bar su. Abba da mamaki yake kallon Umma da Umar har suka ƙaraso inda suke, sannan ya ce, "Ina ita Auta?" Umma ta ce, "Direba ya mai da ita gida." "Halimatu ita kaɗai kuka bari aka tafi da ita? Kuma a cikin wannan halin da take? Wannan wani irin lissafi ne?", Abba ya ƙarishe maganan cikin nuna ɓacin ran shi da hakan. Umar ne ya yi ƙasa da kai, cikin biyayya da girmamawa ya ce, "Ayi haƙuri Abba, ni ne na ce direban ya tafi da ita Mama ta kula da ita, yanzu mu ya kamata mu san halin da Sadeeq yake ciki tukunna." "Sadeeq shi kaɗai ne ɗa? Ba dan Sadeeq ɗin ta samu kanta a wannan yanayin ba? Duniyar yanzu duk yardanka da mutum, banda a kan kuɗi da kuma ɗa, ɗan ma musamman ƴa mace, dan kuɗi nemansu ake ko ta wanne haya haram ko halal, ƴaƴa kuma kana tsare da su a gida ma sai a zo a ɗauke maka ɗa, kuma a buƙaci maƙudan kuɗaɗe, ko a cutar maka da ɗanka, wasu ma su kashe, ba wai ban yarda da direba bane, amma yana da kyau mu kiyaye, sannan sai Allah ya kiyayemu daga sharrin shaiɗan, da son zuciyar mutane, amma dai duk ba laifinku bane, da na sako ta a gaba na kawo ta dole ku bar wa direba ita kaɗai ya maida gida, kai Sa'adu tashi maza ka bi bayansu, ka je ka taimaka wa Maman taku ku shigar da Auta gida", Abba ya faɗa yana mai dai-daita idanuwansa a kan Sa'ad. Sa'ad da sauri ya juya ya fice, a hanzarce ya shige mota ya mata key ya rufa musu baya. Abba ƙwafa yayi tare da jingina da kujerar da ya zauna a kai. Umar cewa yayi, "Ayi haƙuri Abba." Abba bai ce komai ba, haka duk suka yi shiru jigum-jigum, kowa da abinda yake lissafawa a ran shi, amma duk kusan akan batun Sadeeq ne. Sun jima sosai a zaune suna jiran fitowan likitoci, cike da ɗauki da yaƙinin jin kyakkyawan labari, likitocin na fitowa tun kamun su iso gare su duk suka miƙe, guda na yi musu magana, duk suka rufa musu baya, Abba dakatar da Umma da Khalid yayi, hakan ya sa suka tsaya basu bi su ba, Umma ƙarisawa tayi bakin ƙofan ɗakin da Sadeeq yake kwance, daga ƴar space da ke da glass wanda za ka iya hango na ciki take kallonsa, gaba ɗaya ya koma kaman ba Sadeeq ba, jinya ba wasa ba, a fili ta furta, "Allah ka sa iya wahalan Sadeeq kenan, Rabbi ka sa ya farka kenan, Rabbi ka wadata wannan bawa naka da lafiya mai inganci." Abba a baya suka bi likitan har office nashi, kusan a tare da shi suka zauna, hannu ya bai wa su Abba suka yi musabaha, sannan ya ɗaura da faɗa na meyasa aka bar Sadiya ta faɗa jikin patient nasu, cikin faɗan yake cewa, "Tun farko dama na faɗa muku, yanayin bugun zuciyarshi ba dai-dai ba, sannan kuma ta kwanta a gefen saitin zuciyarshi, hakan sam-sam bai kamata ba, a tabbatar irin haka bai sake faruwa ba ko da wasa, yana da kyau a kula sosai." "In sha Allah za a kiyaye likita", Abba ya faɗa cikin tabatarwa. Numfashi likitan ya ja tare da cewa, "To da farko dai Alhamdulillah, patient namu ya farfaɗo cikin ikon Allah, yanzu haka yana bacci, dan akwai buƙatan ya huta sosai, saboda ya samu nitsuwa, da dai-daituwar bugun zuciyarshi, domin yana daga dalilin da ya sanya ya yanke jiki ya faɗi, akwai wani abu da yake riƙe da shi a zuciya, wanda shi ke assasa sauyawar bugun zuciyarshi zuwa mataki mai hatsari, kuma lallai-lallai idan ya tashi a shawarceshi a kan ya kiyaye riƙe abu a zuciyarshi ko yawan tunani, in abu yake buƙata ya sanar muku kusan yanda za ku yi ku samar mishi, idan kuma wani abun ne ya dame shi, nan ma ya sanar muku ku nema mishi mafita, amma zuciyarshi ta raunata sosai da abinda yake riƙe wa, kuma akwai wani abu guda ɗaya, da fari ya faɗa dogon suma ne wanda a ko wanne lokaci zai iya farfaɗowa yanda Allah ya so, sai kuma cikin ikon Allah ga shi yau sati guda cif da kawo shi asibiti, kuma cikin ikon Allah ya farfaɗo, amma sakamakon ya nuna farfaɗowanshi na da dangantaka da wani abu, wanda ya same shi wanda yake so ko yake ƙi, lallai wannan yarinyar da ta faɗa jikinshi, tana daga dalilin farfaɗowanshi cikin ikon Allah, walau ta kasance maganin cutarshi ko kuwa cutar tashi gaba ɗaya", Likitan ya ƙarishe bayanin nashi tare da miƙa wata ƴar takadda gaban Abba. Ya ɗaura da cewa, "A nemo wannan magun-guna kamun ya tashi a bacci, dan yana tashuwa za ku iya shiga wajan shi, amma yanzu ba a son kowa ya shiga, kada motsinku ko hayaniya ya hana shi samun sukunin da ake so ya samu." Abba amsa yayi tare da miƙa wa Umar takardar, sannan ya kuma bai wa likitan hannu suka yi musabaha, cikin kamala ya ce, "Mun gode sosai-sosai Likita, Allah ya saka muku da alkairi ya baku lada, in sha Allah za mu kiyaye, sannan kuma za mu shawarce shi a akan abinda ke a zuciyar tashi." Jinjina kai likitan yayi ya ce, "Allah ya taimaka ya ba shi lafiya." Da, "Amin", Abba da Umar suka amsa, sannan suka miƙe suka fice suna kuma godiya tare da yiwa likita ya huta lafiya. Abba suna fitowa ya ce, "Yanzu Umar ka je ka sayo maganin sai ka kawo." Jinjina kai Umar yayi, sannan ya juya ya ɗau hanyar da zai sada shi da pharmacyn su na asibiti, shi kuma Abba ya nufi wajan su Umma, ko da ya isa a zaune ya samu Khalid a inda ya bar su, Umma kuma tana jikin ƙofar ɗakin da Sadeeq yake kwance, tun bai ƙarisa ba ya fahimci hawaye ne a fiskanta, girgiza kai kawai yayi, yana isowa dai-dai inda Khalid yake zaune, Khalid ya ce, "Sannunku da fitowa Abba." "Yauwa Khalid sannunmu", faɗin Abba yana ƙarisawa wajan Umma. A gefenta ya tsaya shi ma yana hango Sadeeq ta ƴar space da take hango shi, murya a tausashe cikin rarrashi da ƙarfafa guiwa ya ce, "Zan faɗa kaman ko da yaushe yanda na saba faɗa miki Halimatu, kukan iyaye ga yaransu ba alkairi bane a rayuwarsu, musamman hawayen uwa, ko mutuwa Sadeeq yayi baya buƙatan kukanki, balle a yanzu da yake a raye kuma a halin lafiya sai godiya, kina gani dai yanzu an cire mishi oxygen da aka maƙala mishi, Sadeeq ya farfaɗo cikin ikon Allah, yanzu haka bacci yake na hutawa, ki kwantar da hankalinki kar kukanki ya kuma jawo mishi wani abun." Da sauri Umma ta juyo tare da cewa, "Sadeeq ya farfaɗo da gaske?" Jinjina kai Abba yayi cikin tabbatarwa, sannan ya ɗaura da mata bayanin da likita ya musu, yana ɗaurawa da cewa, "Ni nafi tunanin ƙaunar da yake wa Auta ne ya sanya yana jinta ya farfaɗo." "Daman ai babu ma mahaluƙin da ya isa ya ce Auta ce cutar Sadeeq, bata cikin jerin abinda yake ƙi, sai dai ma abinda yake ƙauna ya wuce so", Umma ta faɗa tana sake juyawa ta hangi Sadeeq. Abba murmusawa yayi tare da cewa, "Sadeeq son da yake wa Auta ai ko kece kika haife ta, iya soyayyar da zai mata kenan, kinaji ai bayan an yanke date na aurenta, kwana uku kamun ya kwanta ciwon nan muka yi magana, da shi da Umar akan abubuwan da za a yi na biki, amma Abubakar ya ce shi zai yi komai, kuma ko me ake buƙata a tuntuɓe shi, ni ko na ce mishi sannu uban Auta na biyu tunda ya ƙwace mini matsayina ko nace ya mai da ni bana raye da zai ce komai zai yi." Umma na ƴar murmushi ta ce, "Babban wa uba ne ai." "Wani bin ma har da uwa yake kasancewa ba uba ba, don irin amsarki suka bani, shi da Umar ɗin duka, shiryayyun yara ƴan albarka", Abba ya faɗa cikin alfahari da hamdala ga Rabbi na ba shi su a matsayin yaransa. Umma murmusawa tayi tare da cewa, "Sadeeq da Umar ikon Allah, in ka ji suna kace nace to akan Auta ne." "Shi Umar ya cika tsauri a kanta, to ta ina za su shirya ta wannan ɓangaren, Allah dai ya musu albarka duka, Allah ya tashi kafaɗun Abubakar, ya nuna mana wannan biki da rai da lafiya." "Amin dan isar Annabi", Umma ta faɗa. "Sallallahu Alaihi Wasallam", suka haɗa baki wajan yi wa Annabi salati. Umar ko da ya je pharmacyn yaɗan samu layi, a hanzarce ya jira har aka sallameshi ya biya komai ya dawo wajan su Abba, buɗe ƙofan ɗakin yayi a nitse ya shiga ya aje yana addu'an Allah yasa amininsa ya tashi baccin da wuri, dan ba ƙaramin kewanshi yayi ba, basu taɓa kwashe sati guda basu yi magana da juna ba, komai rintsi, hatta da lokacin da duk suke a makaranta. Ƙiran Abba da aka yi daga gidan man

Chapter 5 of 32