ba na nufin auta ta kai shekaru ko wayewar da ta wuce a zaɓar mata miji, kawai abu guda ne ke a tsakaninsu kuma shi ne Aliyu, sannan duk Abubakar shi ya ja komai tun farko, dan haka ni ba zan aura wa Sadiya ɗan ki Abubakar ba."
Daga Mama har Umma shiru suka yi, Umma sake hango abinda Abba ke nufi take yi, sannan abinda yake gudu duk tana sake hango su, kuma tana goyon bayan shi, gwanda Sadeeq ya ɗau na Annabawa yayi haƙuri, auta da Haidar kuma a bi su da addu'ar alkairi.
Ita kuma Mama a nata ɓangaren ta tabbata maganar Abba daidai ce, amma kuma bata hangi matsalar komai daga Sadiya ba, kawai Abba ya kasa fahimta ne, dan haka zuciyarta har yanzu bata nitsu a kan a bar maganar Sadeeq ba.
Abba da ya ji Mama ta yi shiru, sai ya muskuta ya sake cewa, "Maman Abubakar, da girmanmu da komai bai ma kamata mu mai da kanmu ƙananun mutane ba, yanzu wannan fa kayan lefe mutanen nan suka kawo, so kike da kayan lefen da komai da suka kawo a haɗa a tattare a maida musu abinsu? Kuma sai a cewa ƴan uwa an fasa aurar da auta ga wanda take so, Abubakar za a aura mata? Wannan bai zama son kai ba? Ko kina tunanin mutane ba za su zage mu ba?"
"Ba wani zagi Abban yara, in dan baffanunta da kawunanta ne, duk ƴan uwa ni zan musu bayani su fahimta in sha Allah, Abban yara na fahimceka na kuma fahimci manufarka da abinda kake gudu, amma kai ka kasa fahimtata", faɗin Mama da sassauƙar murya.
Duk ta inda Abba ya fito, Mama sai ta ɓille masa, ta kasa yarda a ajiye maganar Sadeeq a gefe, hakan ya sanya daga ƙarshe kawai Abba ya jinjina mata kai tare da miƙewa tsaye, "Allah ya kyauta, ya tabbatar mana da abinda yake mafi alkairi", iya haka ya faɗa ya nufi bene ya wuce ɗakinsa.
Umma da kallo ta bi Abba har ya ɓace wa ganinta, sannan ta numfasa tare da juyowa ga Mama ta ce, "Maman Sadeeq, kin kasa fahimtar Abban yara, ya kamata kuma ki fahimce shi, ni da ke duka mata ne, munsan ya ciwon a raba ka da wanda kake so a aura maka wani yake, ciwo ne wanda idan baka yi sa a ba, to haka za ka fama cikin jinyarshi har ƙarshen rayuwarka, ko da kuwa ƴaƴa ɗari za ka haifa da wannan..."
Da sauri Mama ta tari numfashin Umma ta hanyar cewa, "Idan baka yi sa a ba kika ce Umman yara, amma Sadiya sa a za ta yi kuma dacewa za ta yi in sha Allah, mai babban suna ne fa, na aminta da shi da irin riƙon da zai yi wa Sadiya."
"Ba ta Sadeeq ake yi ba Maman Sadeeq, ta auta ake yi, ko da auta bata fito fili ta ce ba ta son Sadeeq ba, dan na san ba za ta iya furta haka ba, musamman wa mu, amma na tabbata ke za ta iya faɗa miki abinda ke zuciyarta, sai dai kawai ki ɓoye ko ki shashantar da lamarin, amma auta tana yi wa Sadeeq kallon da take yi wa Umar ne, aurar da su ga juna ɗaukan alhaƙinsu ne duka, ba lallai su sake su samu nitsuwa da juna ba", Umma ta ƙarishe maganar tana sauƙe ajiyar zuciya, dan lallai tana hango fiye da abinda Abba ke hangowa.
Ƴar murmushi Mama ta yi, tare da cewa, "In sha Allah har jikokinmu daga gare su za mu gani, Allah dai ya tabbatar da alkairi."
"Amin Ya Rabbi", iya haka Umma ta amsa, tana jinjina irin ƙaunar Mama ga Sadeeq, ƙaunar da ya sa har bata hango ko Sadiya za ta iya cutuwa a haɗin, Sadeeq kawai take hanga zai samu farincikin shi, tunda Sadiya ce farincikin shi, kuma zai samu lafiya, dan ta fahimci Mama har da batun rashin lafiyar Sadeeq ya sa ta dage, kuma babu ƙarya ko ita ma tana tsoron rasa Sadeeq, kar a dalilin rasa auta ya rasa rayuwarsa.
"Ni kam na wuce Umman amarya da ango."
Maganar da Mama ta yi shi ya katse zancen zucin Umma, hakan ya sa Umma ta murmusa tare da yi wa Mama a huta lafiya, daga haka Mama ta fice, a compound na gidan ta haɗu da Khalid da Sa'ad, suka gaisheta cikin girmamawa, ta amsa, sannan Khalid ya ce, "Mama wai autar Umma kam ɓoyewa take yi ne tun yanzu? Sama ƙasa na nemeta na rasa, kuma maganar ƙawancen nan za muyi."
Mama dariya tayi tare da cewa, "Kana babban yaya me ya haɗa ka da ƙawance Khalid."
"A a Mama, ajiye Yaya za a yi a gefe, sai mun kammala hidima sannan za a yi batun Yaya."
Sa'ad hararan Khalid ya yi, sannan ya ce, "Autar na gida ne Mama?"
"Ni yanzu ɗaya bansan ina Sadiya take ba, tana ciki wajan Ummanta, ko tana can gida, Allah masani, ɓoye kanta take", faɗin Mama.
Khalid ya ce, "Indai Aunty Khausar na nan, to wataƙila ita ma tana ciki, bari mu dubo ta."
Amsawa Mama ta yi, tare da sanya musu albarka ta wuce, su kuma suka yi cikin palourn.
Da sallana suka shigo, suka iske Umma zaune da kayan lefe a gabanta ta zuba musu idanuwa, da sauri Khalid ya ƙarasa yana faɗin, "Ma sha Allah, auta ta yi goshi, irin wannan akwatuna haka."
Sa'ad zama yayi tare da zuba wa akwatunan idanuwa, maganarsu da Umma na ranar ne ya faɗo masa, hakan ya sanya a sanyaye ya ɗago yana kallon Umma, sannan ya ce, "Umma daga gidan su Haidar aka kawo?"
"Eh Sa'ad, ɗazu aka kawo kuna wajan aiki", Umma ta amsa.
Khalid kallon rashin fahimta ya yiwa Sa'ad, sannan ya ce, "Dama idan ba daga gidan su Haidar ba, daga ina za a kawo Yaya Sa'ad? Ko auta na da wani mijin bayan Haidar?"
Har Sa'ad ya buɗe baki zai yi magana, sai kuma yayi shiru, da ya tuna Umma ta kwaɓe shi.
Umma ta ce, "ku tattara ku gyara musu zama a wancan gefen, Abbanku bai gani ba tukunna, kuma sauran baƙi idan sun iso za su shigo suke kalla, idan an kammala za a kai ɗaki, kamun ranar da za a kai mata gidanta."
Sa'ad na ƙoƙarin miƙewa dan jan akwatin, Khalid yayi saurin dakatar da shi ta hanyar cewa, "A a Yaya Sa'ad, bari mu ma mu kalla."
"Yau na ga ikon Allah ni Halimatu, namiji da kallon lefe, Allah ya shirya ka Khalid", iya haka Umma ta faɗa ta wuce ta bar musu palourn ta haura saman bene.
Sa'ad girgiza kai yayi tare da cewa, "Allah ya taro ka Khalid."
"Amin wa addu'ar Umma da taka Yaya Sa'ad", Khalid ya faɗa yana buɗe akwati.
Sa'ad zamanshi ya gyara tare da fidda wayarshi yana dannawa, shi bai san me zai gani a lefen ba, balle ma da yake jin ba daɗi sosai a zuciyarsa na ganin alamar dai Yaya Sadeeq ba zai samu auta ba.
***
Sadiya kanta a ƙasa ta shiga gida, ta ci sa'a lokacin sallar isha'i ne, ba wanda ya kula da ita, har ta shige ɗakinta, kai tsaye ta wuce toilet ta ɗauro alwala ta zo ta gabatar da nata sallahn, tana idarwa ta shafa addu'a ta laluɓi wayarta ta fice a ɗakin, wajan su aunty Kulu ta je, ta gaishe da sauran baƙin da aka yi yau, su kuwa suka dinga tsokanarta tana amsawa cikin yaƙe, har ta samu ta sulluɓe ta fice a palourn, a madaidaicin harabar gidan nasu ta samu gefe can ta bayan motar Yaya Umar ta zauna kan wani dutse, wayarta ta fidda ta laluɓo layin Haidar, last call nasu take kallo wanda ya kasance tun jiya da suka yi maganar lefe, da ta ƙi faɗa masa abinda ke damunta, shikkenan yayi fushi, hargitsin da take ciki tun jiya da Mama da Yaya Umar suka mata faɗa, ya hana ta samun sukuni ta ƙirasa, shi kuma da alama ya hau dokin zuciya sosai, tunda bai ƙira ta ba har yanzu.
Ɗiss-ɗiss!, ruwan hawayenta suka ɗiga a samar screen na wayarta da take riƙe da shi idanuwanta a kan numbern Haidar, kamar wacce ke ƙoƙarin haddace numbern, ɗigar hawayen nata ne ya sanar da ita shaɓe-shaɓe da fiskarta ya jima da yi da hawaye wanda sai sannan take jin ɗuminsu, dan bata san da zubowansu ba, hakan ya sanya ta yi saurin lumshe idanuwanta, wani irin ciwo take ji a zuciyarta, ji take numfashinta na ƙoƙarin barin jikinta, ta buɗe baki da niyar yin kuka mai sauti ko za ta ji salama, sai ta ji dirar muryar Umar a kunnenta.
"Ke Sadiya", Umar ya ƙira sunanta fiska a haɗe.
A hankali Sadiya ta ɗago idanuwanta da suka gama jiƙewa da hawaye, lashes ɗin ƙasa na haɗewa da na sama, amma idanuwan nata basu sauƙa a kan Umar ba, sai a kan Sadeeq da ke daga gefenshi ya zuba mata idanuwa.
Wani irin tsinkewa zuciyar Sadiya tayi, ta buga da ƙarfin da sai da ta kai hannunta ta dafe saitin zuciyarta, har sannan idanuwanta na a kan Sadeeq, kuma hawaye na kan bin kuncinta.
Umar da duk wata annurin fiskarshi ta gama fecewa, fiska a haɗe ya yi ƙwafa tare da cewa, "idan kin gama kukan ki zo ki same ni a ɗaki", iya haka ya faɗa ya juya ya bar wajan, ran shi a ɓace ya nufi cikin gidan, bai tsaya bi ta kan jama'ar da ke palourn ba ya wuce ɗakinsa kai tsaye, dama da cikinta da haushinta ya dawo office, tun da ya shigo gidan ya tarar da bajakolin lefe, wanda ya tabbatar daga gidan su Haidar lefen yake, tun sannan ransa ke a ɓace yake nemanta, dan yaji dalilin da zai sa Haidar ya kawo lefe, bayan maganar Sadeeq ake yi yanzu ba na shi ba, kuma a yanzu ji yake da kan shi zai sanar da Haidar, Sadeeq za su aura wa Sadiya ya yi haƙuri, dan ya ga alamar idan aka tsaya ta Abba to ba za a samu abinda ake so ba har sai an rasa Sadeeq, dan yana kule da shi har yanzu komai cikin ƙarfin hali da dauriya yake yi.
Maganar Umar shi ya dawo da Sadiya hayyacinta daga nisa da ta yi a duniyar kallon Sadeeq da tunani, hakan ya sa ta yi saurin janye idanuwanta sannu a hankali daga kan shi, ƙasa ta yi da kanta tana mai ƙoƙarin danne kukan da ya zo mata maƙoshi.
Sadeeq yana tsaye idanuwansa a kan ta, har sai da ya ga Umar ya shige cikin palourn, sannan ya sauƙe hannayensa ya zuba su a aljihu, sannu a hankali cikin haɗaɗɗiyar tafiyarshi ya fara takowa zuwa gare ta, inda duk taku guda yake jin zuciyarshi na matuƙar tsinkewa, kamar yana tunkarar ƙarshen rayuwarshi.
Sadiya tana jin sautin takun Sadeeq ne kamar yana shirin tafiya da numfashinta, ta yadda take jin ba za ta iya ci gaba da riƙe kukan ba, numfashinta har wani tsere yake kamar idan ya tafi ba zai dawo ba, idanuwanta a kan ƙafafuwan Sadeeq har ya ƙaraso inda take zaune, daga gefe ya zauna a wani dutsen, har sannan idanuwanshi na kan ta.
Da giant cool voice na shi ya ƙira sunanta, "Sa'adiyahh."
Daga shi har ita lokaci guda zuciyoyinsu suka buga, ta yadda sai da ya lumshe haɗaɗɗun mayatattun idanuwanshi, ciki-ciki ya furta, "Auch", saboda zuciyarshi da ta kama, ya ɗan taune leɓenshi.
Sadiya kuwa zuciyarta na bugawa, kawai ta fashe da kuka mai sauti, kuka mai cike da rauni, ƙunci, damuwa, rashin madafa, tsaka mai wuya, kuka ne wanda ke tafe daga ƙasan zuciyarta.
***
Za ku iya samun littafin a waɗannan manhajoji.
●BAKANDAMIYA HIKAYA.
●WATTPAD
@Uwarbatoorl96
●AREWABOOKS.
@Uwarbatoorl96
●WHATSAPP
09161720046
a kan Naira #500.
Idan littafi ya zama completel 1k yake in sha Allah.
# Hareeyh
# 09161720046
# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚
[25/12/2025, 19:45] Uwar Batoorl✍️❤️🥰: 💔NAUYIN BAKI....👄💔
Na
Uwar Batoorl.
𝗕𝗜𝗦𝗠𝗜𝗟𝗟𝗔𝗛𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗠𝗔𝗡𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗘𝗘𝗠
اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤🤍
🅿️ 43 _ 44
⭐️
Sadeeq shiru yayi yana saurarar sautin kukanta, wanda yake jin tamkar ana watsa wa zuciyarsa ruwan narkakkiyar dalma ne, hakan ya sa ya sanya hannunsa a aljihu, cikin sa'a ya laluɓo handkerchief, miƙa mata yayi ba tare da ya ce komai ba.
Sadiya amsa ta yi ta sanya a fiskarta, tana share hawayenta, wasu hawayen na kan zubowa tana ci gaba da yin kukan ba tare da ta rage sautin ba.
"Please Sa'adiyah it's okay, kiyi shiru, share hawayen haka kin san ba na son kukanki, right?"
Jinjina kai Sadiya ta yi alamar, "eh", sannan ta rage sautin kukan, ta kuma share hawayen ta fece hanci, handkerchief ɗin na riƙe a saitin hancinta, ta na shaƙar daddaɗar sassanyar ƙamshin Yaya Sadeeq da ke sanya mata nistuwa da kuma faɗuwar gaba lokaci ɗaya.
"What's wrong with you Sa'adiyah? Why are you crying? Tun jiya da na shigo wajan Mama, na ji Najla ta ce kina kuka, don't tell me kukan tun jiya shi ne har yanzu kike yi? Me yayi zafi har haka sosai? Kin ga yadda kika faɗa kuwa? a haka kike so a kai wa Haidar ke..?" Sadeeq ya ƙarishe maganar yana ɗan kau da kansa, saboda zuciyarsa da ta sosu, amma duk da haka a sigar lallashi ya yi maganar.
Sadiya sai da ta ɗan saita muryarta, sannan ta ce, "Ba komai Yaayaana."
Lumshe ido Sadeeq yayi, yanda ta ƙira shi da sautin kuka, sai ya ji zuciyarsa ta narke kamar ya jawota jikinsa ya lallasheta, amma ba dama, sai ya ɗan furzar da iska tare da basarwa ya ce, "Kukan jin daɗi?", da sigar tambaya ya yi maganar.
Tura baki Sadiya ta yi, idanuwanta na cikowa da ƙwalla, murya na rawa ta ce, "Yaayaana...", sai kuma ta kasa ƙarisa maganar kawai ta cigaba da share ƙwallanta, domin da matuƙar kunya ta dubi Yaya Sadeeq ta yi masa wannar magana, da a ce a kan wani ne, ba shi a karan kan shi ba, to da za ta iya masa maganar ya taimaka mata ta samu mafita, amma yanzu da kunya ta yi maganar, tunda ga shi, shi da kansa bai yi mata maganar ba, kai anya ma kuwa ba haɗin su Yaya Umar bane? Anya da gaske Yaya Sadeeq zai ce yana son ta? Yaya Sadeeq dai da bata taɓa jin maganar wata hamshaƙiyar mace a bakinsa ba, sai ita ƴar tatsitsiya.
"Uhun, ina jin ki Sa'adiyah, ko kin daina sirri da ni ne?" Sadeeq ya faɗa a yanayin zolaya.
Ƴar murmushi Sadiya tayi, sannan ta girgiza masa kai alamar, "A a."
Daga haka shiru ya biyo baya na wasu mintuna, kowa da abinda yake lissafasawa a zuciyarsa, sai can Sadiya ta katse shirun ta hanyar cewa, "Yaayaana."
"Na'am Sa'adiyah."
"Ya ƙarjin jikin?"
Wani guntun murmushi Sadeeq ya yi, tare da kallon Sadiya ta wutsiyar ido, ya ji daɗi ƙwarai har ran shi, duk da already ya san ta damu da shi da lafiyarsa, amma tambayar da ta yi a yanzu ya fi komai faranta masa, sai yake jin kamar ya fallasa mata sirrin zuciyarsa, kamar ya sanar mata ita ce cikar samun sauƙin shi, soyayyarta ce samun ƙarfi da ƙwarin jikinsa, ita za ta tallafa masa ta agaji ruhi da gangar jikinsa ya ci gaba da rayuwa cikin salama a duniyarta, kamar yadda kowa ke rayuwa a duniyarsa, amma sai dai gefe guda na zuciyarsa na hana shi furta mata, haka kawai yake jin kamar shi ne sanadin kukanta na ɗazu, yanzu da ya samu ta daina, kar ya sake ɓata zuciyarta.
Wannan tunani ya sa Sadeeq ya share batun zuciyarsa, ya ce mata, "Am okay Sa'adiyah, ke ce dai na ga kamar kin amshi ciwon, it seems like you're not okay, kin rame."
Sadiya da ta mance da damuwar da take ciki da batun Haidar, ji take kamar a lokutan baya ne suke hira da Yaya Sadeeq, hakan ya sanya ta shagwaɓe fiska tare da cewa, "Ba dole na rame ba Yaayaana yana asibiti an hana ni zuwa."
Ƴar murmushi Sadeeq ya yi, tare da cewa, "Really?"
Tura baki Sadiya ta kuma yi tare da gyaɗa kai alamar tabbatarwa.
Madaidaicin sumar kan shi ya shafa, tare da kawar da maganar, gudun kar a je bigiren da ba zai iya danne abinda ke zuciyarsa ba, cewa yayi, "Ina jin raɗeraɗin maganar result's naku sun fara fitowa, so as soon as your result is out, I'll talk to Haidar, so that za muyi arranging na komai ki ci gaba da zuwa school immediately."
"In sha Allah Yaayaana, kuma ni kai nake so ka mini waliyyi a auren....", da sauri Sadiya ta haɗiye maganar, saboda sai yanzu ta tuno da asalin situation da suke ciki, satar kallon Yaya Sadeeq ta yi, ba zato suka haɗa ido, ta kuma kasa kawar da nata har ya karanci abinda zai karanta, hakan ya sanya ya saki murmushin yaƙe tare da miƙewa tsaye, hannayensa ya zuba a aljihu tare da cewa, "Fatan alkairi Sa'adiyah."
Ƙwalla ne suka ciko idanuwanta, bakinta na rawa cikin muryar da ke nuni da tana shirin fashewa da kuka ta ce, "am sorry Yaayaana, ina maka kallon Yayan da muka fito ciki ɗaya ne, wanda ba aure tsakanina da shi..", kuka ne ya suɓuce mata mai ciwo, ta ma kasa ƙarisa maganar.
Sadeeq da yake tsaye ya bata baya, yana ji har ta ƙarisar maganar, wanda yake jin tamkar zuciyarsa take kekketawa da zazzafar aska, abinda ya guda kenan tun farko, abinda bai so ya ji ba tun farkon fari, domin wataƙila zai iya jure rashin auren Sa'adiyah kuma ya rayu, amma jin tabbacin Sa'adiyah ba ta son shi daga bakinta, to abu ne da zai iya sanya zuciyarsa yin bindiga a take, wannan zafin da yake ji a zuciya shi ya ɗan ja hankalinsa, sautin kukanta ne ya dawo da shi daidai, kuma a take ya nufi ƙofar fita a harabar gidan, cikin takun sassarfa, saboda so yake ya daina jiyo sautin kukanta da ke neman zauta shi, gwanda ya fama da abinda yake ji a zuciyarsa, wanda ya riƙe masa ƙahon zuciya.
Sadiya idanuwanta a kan bayan Sadeeq har ya fice a gidan, kukanta ta tsananta kamar za ta shiɗe, domin tabbas tana ganin rashin kyautawanta, tana ganin wautan da tayi, lallai kalmar ɗan adam butulu ya tabbata a kanta yau...
Ƙarar shigowar ƙira a wayarta shi ya sa ta ɗan tsagaita kukan, cike da ɗaukin ko layin Aliyu ne ta laluɓo wayar a tsakankanin cikinta da cinyotinta, amma tana dubawa zuciyarta ta kuma bugawa, saboda ganin layin Yaya Umar, hakan ya sa ta ƙara sautin kukanta tare da cewa, "Ni kam na shiga uku, gaba kura baya siyaki, wannan wace iriyar rayuwa ce Allah na tuba, haka kowacce mace ke fiskanta ko ni ce kawai kalar tawa ƙaddarar haka? Allah ga ni gare ka", ta ƙarishe maganar tana ƙoƙarin saita muryarta da ke rawa, saboda kukan da tayi, gabanta na faɗuwa ta amsa ƙiran da ya sake shigowa, dan na farkon ya katse, numfasawa ta yi tare da kara wayar a kunnenta, kamun ta yi sallama, muryar Umar daga ɓangarenshi ya ce, "Yaushe na zamo abokin wasarki da zan ƙira ba za ki ɗauka ba har ya katse? Ƙiran nawa ma sai kin yi ra'ayi za ki ɗauka ko?"
Sadiya tana ji ne tamkar ta ƙwalla ƙara saboda taƙaicin abubuwan da Yaya Umar ke yi mata, gaba ɗaya kamar ba ɗan uwanta na jini kuma Yayanta ba, Yaya Umar ba ya tausayinta sam-sam kuma ba ya ƙaunarta, yanzu ƙira ɗaya da bata ɗauka ba shi ne abun masifa, kuma dan gujewa masifarshi ne bata ɗauka ba ta tsaya saita muryarta, amma ashe bata tsira ba, dan a ko da yaushe Yaya Umar kamar jiranta yake yi da ƙiris ta yi kuskure ko laifi, shikkenan ta shiga uku, cike da tausayin kanta siraran hawaye suka zubo mata, da sauri ta sa hannu ta goge, tana ƙoƙarin yin magana ta jiyo shi yana kuma cewa, "Tunda shi maganar ma sai kin ga dama za ki yi, to maza zo ɗakina ki same ni, rubbish girl kawai", ya faɗa cikin hasala tare da katse ƙiran.
Sadiya da kallo ta bi wayar nata na wasu daƙiƙu, sannan ta sauƙe nauyayyar ajiyar zuciya, ta miƙe tsaye tana tattaro duk sauran ƙwarin jikinta, ta fara takawa har ta isa bakin ƙofar palourn nasu, sai da ta tsaya ta sake saita kanta sannan ta tura ƙofar palourn ta shiga da sallama, mutanen ciki suka amsa mata tare da tambayarta ina ta shiga, Mama sai nemarta take yi, murya a sanyaye fiskarta ɗauke da murmushin yaƙe ta ce, "Ina harabar gida, yanzu ma Yaya Umar ne ya ƙirani", cikin sanyi tayi maganar, tare da wucewa hanyar ɗakin Umar, tana isa bakin ƙofar ta ja ta tsaya, da sansanyar muryarta ta yi sallama, sai da ya ɗan ɗau wasu daƙiƙu sannan Umar daga ciki ya amsa mata, tare da bata izinin shigowa.
Sadiya sai da ta runtse idanuwanta, tana ambaton sunan Allah, sannan ta ɗaura hannunta a kan handle na ƙofar, da bismilla ta murda ta tura, ta shiga tana yin wata sallamar.
Ciki-ciki Umar da ke zaune a bakin gadonsa ya amsa mata, idanuwansa a kan wayarsa da yake dannawa.
Sadiya cikin sanyin jiki ta ƙarisa shigowa, a kan lailayayyen carpet na ɗakin mai taushi ta yiwa kanta matsugunni, zama tayi dirsham tare da yin ƙasa da kanta, cikin muryar da ke nuni da tsoronsa da take ji, ta ce, "Yaya ga ni nan."
Umar shiru yayi na wasu mintuna, sai can ya aje wayarsa tare da mayar da idanuwansa kanta, ita kuma sake duƙar da kanta ƙasa tayi ƙirjinta na bugawa, ƙwafa Umar yayi tare da cewa, "Mun fara wasar ɗaukar wayar ganin dama da ke ko?"
Da sauri Sadiya ta girgiza kai, murya na rawa ta ce, "Ka yi haƙuri Yaya."
Umar cewa yayi, "Kayan me na gani yau a gidan nan?"
Sadiya da take hamdalar ya haƙura da maganar waya, jin maganar da yayi wanda take da tabbacin na kayan lefen ne, ba ƙaramin ruɗewa cikinta yayi ba, kuma daman tun da aka kawo kayan take zullumin Yaya Umar da kuma Mama, domin yana daga dalilin da ya sa ta samu Abba da maganar da ta masa ɗazu, duk da ta san muddin hakan ya tabbata to tamkar ta ɗauki wuƙa ne ta daɓa wa kanta da kanta.
Umar jin Sadiya ta yi shiru ba ƙaramar harzuƙa yayi ba, cikin ɓacin rai ya ce, "Sadeeq za ki aura ko kin ƙi ko kin so, ni da kaina zan samu Haidar, zan sanar masa an fasa ba shi ke, kuma da kaina zan mayar musu da kayakinsu, ko da kuwa su sun ƙi zuwa su ɗauka."
Siraran hawaye ne suka zubo wa Sadiya da kanta ke a ƙasa, lokacin da ta ji furucin Umar, jin wai da kanshi zai mayar da kayan kuma ya yiwa Haidar magana, yau ita da wanne ido za ta kalli Haidar?, an masa aldalci kuwa? Ji take tamkar ta yi ihu ta yi kuka ta roƙi, ko ma me zai faru kar a tunkari Haidar da wannan maganar, balle kuma ta a mayar musu da kaya.
"Ina magana kin mini shiru, wato ga mahaukaci ko?", Umar ya faɗa yana katse zancen zucin da take yi.
Da sauri Sadiya ta girgiza kai tare da buɗe baki da niyar yin magana dan ta ba shi haƙuri, amma shigowan Mama da sallamarta suka katse ta, sai ta kuma yin ƙasa da kai tana kukan zuci wanda ya fi na fili ciwo.
Mama da sallama ta shigo ɗakin, tana ganin Umar da Sadiya sai ta sauƙe numfashi, dan tun dawowanta daga gidan Abba take leƙa Sadiya lungu da saƙo a gidan, sai yanzu da ta fito a ɗakin Sadiya kenan wanda yake sawunta kusan na uku, sai su aunty Kulu ke sanar mata, Sadiyar tana ɗakin Umar, shi ne ta nufo nan ɗin, kuma ta samu salama da ganin Sadiya a ɗakin nasa, dan nan ne ya fi sirri a kaf gidan, tunda ko ina cike da jama'ar biki.
Umar cikin girmamawa ya ce, "Sannu da shigowa Mama."
"Yauwa Umar, ashe kuna nan ina ta bulayin nemanku", faɗin Mama da ta ƙarisa shigowa, ta wuce wajan sofan da suke ɗakin ta zauna a guda ɗaya, dan dama biyu ne kuma duka masu ɗaukar mutum ɗaya ne wato one seater.
"Eh Mama muna nan, na ƙirawota ne ina tambayar ba'asin kayan da na gani dawowana, wato share maganar da aka mata tayi, ta girma wuyanta ya isa yanka, bata ɗau maganar da aka mata a bakin komai ba, har
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 27 Chapter of 32