Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sha Allah", Sadiya ta amsa a sanyaye sannan ta juya ta fice tare da turo wa Mama ƙofan ɗakin. Da kallo Mama ta bi ƙofan, tare da girgiza kai, "Sadiya! Sadiya! Sadiya", Mama ta ƙira sunanta har sau uku a fili. Sannan ta ɗaura da faɗin, "Allah ka shirya mini wannan yarinya ka tabbatar da alkairi a rayuwarta, Rabbi ka sa ayi bikin nan lafiya ta zauna a gidanta lafiya har mutuwa." (Aminnnnn Mama). ⭐️ PLATEU SPECIALIST HOSPITAL. ABUBAKAR SADEEQ POV *** Sadeeq a nitse yake sipping kunun idanuwanshi a lumshe, yana jin ficewan su Umma har ficewan Umar, bai ko buɗe ido ba, saboda kunun Mama yana gaba a cikin jerin favourites nashi, a abun ci ko na sha. Sa'ad ƙarasawa yayi wajan flask na kunun ya ɗiba yana faɗin, "Abba na sako maka?" Abba fiska a ɗan haɗe amma muryanshi ba amo ya ce, "Kai Sa'adu, kunun mara lafiyan za ka shanye? Kai aka kawo wa ko shi?" Marairaice fiska Sa'ad yayi tare da cewa, "Wallahi Abba rai na ya biyaa da kunun nan, ƙamshinshi kawai da naji a take naji yunwa, ko da akwai wani a gidan na san na Yaya Sadeeq special ne Mama ta kawo mishi, zan taɓa", ya ƙarishe maganan da sigar magiya kuma cikin girmamawa. Abba bai kuma cewa da Sa'ad komai ba, ya maida idanuwanshi ga Sadeeq, a nitse ya ƙira sunanshi, "Abubakar." Sadeeq buɗe mayatattun idanuwanshi yayi, kallon Abba yayi, kallon da ke nuna girmamawa, sannan yayi ƙasa da idanuwanshi. Abba bai damu da rashin amsawan Sadeeq ba, tunda dai ya mishi alaman yana saurarenshi, cikin kamalalliyar muryanshi ya ce, "Fatan jikin naka da sauƙi sosai? Ko akwai abinda ke maka ciwo?" Sadeeq gently ya girgiza kai tare da cewa, "Am feeling better Abba." "Ok, gud, Allah kara ƙarfin jiki." "Amin Abba." Sa'ad kunun ya shanye, zai kuma ƙara wa Abba ya hana shi, Sa'ad ya marairaice, Abba ya haɗe fiska tare da cewa, "Tashi maza ka tafi gida, dama direba ne ya kawo ni kuma zai maida ni." Sa'ad kaman zai yi kuka haka ya aje kofin, tare da cewa, "Yaya Sadeeq Allah ya ƙara sauƙi, ƙarfin jiki kuma nasan in sha Allah kana shan kunun nan sau uku za ka koma kaman da har da faɗawan da kayi za ka ciko." Sadeeq da duk yake jin Abba da Sa'ad, bai ce komai ba bawai kuma dan zai ƙara kunun ba, kawai baya son yawan hayaniya ne, ƙirjinshi yanzu zai kama mishi, dan ya samu yanzu ya sake shi dama-dama, yana jin abinda Sa'ad ya faɗa ya bi shi da ido kawai, murmushi mai tsada da matuƙar kyau ya sakar mishi tare da lumshe idanuwanshi ya buɗe alaman, "Amin", da kuma Allah kai shi gida lafiya. Sa'ad dariya yayi tare da cewa, "Na sani ai, ga shi sau ɗaya ka sha har ka fara komawa kaman da", ya ƙarishe faɗa yana ficewa a ɗakin saboda kallon da Abba ya aika mishi, dariya kawai yake dan kallon na Abba bai dame shi ba, daɗi ya ji ƙwarai matuƙa da yanayin Yaya Sadeeq, dan wannan murmushin da alama ba na yaƙe ne kaman yanda yake musu kwanaki kamun ya faɗi ciwo ba, yana ficewa ya shige motarshi ya mata key ya kama hanyan gida, yana isa ya daidaita sawayen motarshi a ma'adana motoci, sannan ya wuce cikin gidan da sallama, palourn ba kowa wanda hakan ke nufin Umma na sama, Khalid kuma may be yana ɗakinshi ko kuma ya fita, shi ma kai tsaye ɗakin shi ya wuce, sai da ya watsa ruwa sannan ya ɗaura alwalan isha'i, fitowa yayi dining ya ɗibi abinci ya ci sannan ya wuce ɗaki ya ta da sallahn isha'i. Abba da kallo ya bi Sa'ad har ya fice sannan ya mayar da idanuwanshi ga ha Sadeeq, wanda ya gama shan kunun, ya aje kofin, Abba in a serious way ya zuba wa Sadeeq idanuwanshi, domin baya jin zai iya yin shiru akan shawaran da likita ya basu, "Abubakar menene ke damunka da kake ɓoye ma mutane, har mu iyayenka, da har damuwan yayi sanadin faɗuwanka?", Abba ya ƙarishe maganan tare da tsare Sadeeq da idanuwa. Wani irin harbawa zuciyar Sadeeq tayi, da sauri ya runtse idanuwanshi duk da kuwa yana jin alaman tsare shi da idanuwa da Abba yayi, amma baya jin ko da bulala Abba ya tsare shi zai iya faɗa mishi abinda ke a zuciyarshi, kai ko wuƙa ma ba bulala ba, shi yanzu idanuwan wa zai iya kalla ya ce ga abinda ke a zuciyarshi, he has no confidence for saying what's in his mind, ba zai taɓa faɗa ba tunda har yayi loosing opportunityn shi, ba zai rusa farin cikin Sadiya ba, domin ya san buɗe bakin shi da nufin faɗan abinda ke a zuciyarshi to kaman rusa farin cikin Sadiya ne, domin bazai taɓa mance furucinta gare shi ba, a lokacin da ya samu tabbacin soyayya take tuƙuru da Aliyu, his heart was broken into billions pieces that time, he was very shocked, har gobe yana mamakin ikon Allahn da ya sa a lokacin bai haɗiye zuciya ya mutu ba, yana sonta yana ƙaunarta yana planning duk wani budget na rayuwarshi da ita, saboda yana ganin his future in her, a very good and amazing future, but a lokaci guda komai ya lalace ya rushe, yayi ƙoƙarin nusar da ita cikin hikima da dabara amma amsanta ya kuma dulmiya shi ne a cikin tafkeken duniyan da ba zai iya making a cikinshi ba, he can't make anything without her, including his life, he's miserable without her, she's his whole world, he can't do without her.... Maganan Abba ne ya katse zancen zucin da yake, wanda zancen zucin ke sake kame mishi zuciya ya damalmale da ciwo. Abba idanuwanshi a kan Sadeeq da yayi ƙasa da kanshi ya kasa mishi magana balle ya bashi amsa, ɗan sassauta murya Abba yayi, cikin siga mai kama da lallashi ya ce, "Abubakar faɗuwa ka yi ka daina numfashi balle motsi, ka san adadin irin tashin hankalin da mahaifiyarka ta shiga kuwa? Kar a ce ma ni, ƴan uwanka Sa'ad da Khalid, Amininka Umar da mahaifiyarshi waɗanda suka ɗauke ka kaman jininsu, Sadiya yarinya baiwar Allah da take ƙaunarka fiye da yayanta da suka fito ciki ɗaya, a haka ma ƙanwarka Khausar bata san halin da ake ciki ba da tashin hankalin namu ya fi haka, amma a sati guda da ka kwashe ba ka a hayyacinka Allah ne kawai ya taimaka mana wajan yiwa Khausar ƴar hanya-hanya cewa kana lafiya, Sadeeq duk mun damu da kai, kuma idan ka faɗa abinda ke damunka za mu taimaka ƙwarai matuƙa bakin rai bakin fama wajan ganin mun yaƙi wannan abun, idan kuma wani abu kake so, to wallahi ko da duka dukiyata za ta ƙare ne zan nemo maka shi Abubakar na maka wannan alƙawari." Cikin hanzari Sadeeq ya ɗago gajiyayyun mayatattun idanuwanshi da suka rine, saboda azabar zuci da kuma ciwo, kallon Abba yake without blinking his eye's, kallon son gano tabbacin alƙawarin da Abba ya mishi yake, tabbas ya gano hakan a idanuwan Abba, kuma Abba ma da ya fahimci kallon da yake mishi, sai ya jinjina mishi kai alaman tabbatarwa akan abinda ya ce, lumshe ido Sadeeq yayi yana busar da zazzafan iskan da ke tafe daga jinyatacciyar zuciyarshi, he made a decision, zai faɗa wa Abba, ko da alƙawarin Abba bai cika ba lallai zai samu sassauci a zuciyarshi, zai faɗa abinda ya kwashe shekara da shekaru yana riƙe da shi a zuciyarshi, shekaru goma sha takwas masu kyau yana wannan dakon, kuma zuciyarshi bai taɓa bari ko da lallaɓanshi su furta ba balle ma kunnuwanshi su ji, kar a kai ga wasu kunnuwan. Ajiyan zuciya mai sauti da nauyi ya sauƙe, calmly ya buɗe idanuwanshi, ƙasa ya kuma yi da kanshi, in a lower sound ya buɗe bakinshi ya ce, "Abba......" * Za ku iya samun littafin a wannan manhajoji. BAKANDAMIYA HIKAYA. AREWABOOKS. @Uwarbatoorl96 WHATSAPP 09161720046 a kan Naira #500. Idan littafi ya zama completel 1k yake in sha Allah. # Hareeyh # 09161720046 # 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩 # 𝙇𝙞𝙠𝙚 & # 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚 [07/12/2025, 13:34] Uwar Batoorl✍️❤️🥰: 💔NAUYIN BAKI....👄💔        Na Uwar Batoorl. 𝗕𝗜𝗦𝗠𝗜𝗟𝗟𝗔𝗛𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗠𝗔𝗡𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗘𝗘𝗠     اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤🤍 🅿️ 41 _ 45 ⭐️ "Abba..." Ɗif maganan da yayi niyan yi ya ɗauke saboda maganganun Sadiya da suka yi clashing a kunnuwanshi kaman lokacin take mishi maganan. «Yaayaana Allah da gaske da wayo na da hankali na, am 18yrs fa Yaayaa, na san me so nasan me shirme ko yaudara, Yaayaa ina son Haidar da dukkan zuciyata, irin soyayyan da ba dan tsoron Allah da imani ba, da kuma kasancewanka a tare da ni, da kuma kasancewan Haidar mutumin kirki, ba dan duk waɗannan ba, da ace Haidar mutumin banza ne to a irin yanda nake jin shi a zuciyata da ya jima da cika burinshi na banza a kaina, ko da kuwa a ce in bi shi mu gudu ne in aka ce za a hana shi ni, amma kasancewanshi mutumin kirki kuma da aure yake so na to dukkan yardata da amince wa ta ɗari bisa ɗari na damƙa wa Haidar, na amince ya zama mijina kuma uban ƴaƴana, amma fa Yaayaana sai kai ma ka amince dan ba zan yi abinda ba goyon bayanka ba da albarkanka", ta ƙarishe maganan tana rufe kyakkyawan fiskanta da kyawawan hannayenta da yatsun suka sha ado da zanen baƙin lalle, tana sanye ne da dogon riga ruwan ɗorawa na shadda wanda ya sha ado da zubi na zamani daga sama har ƙasa,  da kuma a bakin hannayen rigan da wuyan rigan, ɗaurin ɗankwali ta yi simple, kasancewan suna a cikin gidan Abba ne, kuma a ɗan gefe da ya kasance kaman wajan shan iska ko kuma karatu ga mai buƙata, hakan ya sanya duk da Sadeeq ya ce ko da compound na gida za ta fita ta sanya hijabi,  amma yau ta sako gyale mai ɗan girma fari ƙal, ya amshe ta tayi kyau sosai. Sai da ta gama rufe idanuwanta da murmushin wai tana kunyan Sadeeq,  sannan ta ɗan wara yatsunta ta yanda za ta kalleshi ta tsakankanun yatsun, tun da ta ji yayi shiru bai bata amsa ba, kuma amsanshi take jira, ganin  kaman yanayinshi da kalan idanuwanshi sun sauya, hakan ya sanya ta yi saurin cire hannunta a fiskanta, cikin damuwa da kulawa ta marairaice a shagwaɓe ta ce, "Yaayaana what's wrong? Ko na ce ba dai-dai ba? Yaayaana wallahi in baka amince ba na haƙura, duk da Haidar shi ne farin cikina, ina son shi ina ƙaunarshi, kuma rabuwa da shi tamkar rabuwa da farin cikinane, amma wallahi ka ji na rantse in baka amince da shi ba zan rabu da shi Yaayaana, kai ne duniyata ko da kuwa shi farin ciki na ne", ta ƙarishe maganan a yanayi na karaya da ban tausayi, idanuwanta kyawawa da suka ji ƙwalli suna cikowa da ƙwalla.» A matuƙar sanyaye Sadeeq ya ce, "Ba zan raba ta da farincikinta ba, bazan kuma bari a raba ta da farin cikinta ba, shi ne farin cikinta and i can dedicate the whole world to her not only my life." Abba da yayi shiru yana kallon Sadeeq, ya dai ga motsawan laɓɓun Sadeeq amma bai ji abinda ya ce ko guda ba, don a ƙasan maƙoshi Sadeeq yayi maganan, shi kaɗai ya ji abinda ya faɗa, hakan ya sanya Abba jan gauron numfashi, ba tare da ya ce wa Sadeeq komai ba ya miƙe saboda sallahn isha'i da aka ƙira ya fice a ɗakin ya wuce masallaci. Sadeeq lasan lip nashi na ƙasa yayi tare da kai hannunshi ya dafe saitin zuciyarshi, murmushi yayi wanda ya fi kuka da ihu ciwo, murmushi na azaba, cikin dakiya kaman yana magana da wani, a taƙaice ya ce, "Ba mai ji, sirrina ne ni ƙadai, na sadaukar da rayuwata da zuciyata wa farincikinki", daga haka ya lallaɓa ya miƙe ya wuce toilet, kuskure baki yayi sannan ya dawo ya ta da sallahn isha'i shi ma.   Yana addu'a Abba ya dawo, kamun ya shafa sai ga sallaman Umar da Khalid,  shafa addu'an yayi tare da taya Abba amsa sallaman nasu, amma ciki-ciki ya amsa, ya miƙe ya sanya slippers nashi ya ƙarasa kan gadon ya kwanta, ba tare da ya kalli inda Umar ke tsaye ba, saboda har yanzu haushin amshe wayan da yayi ya kashe yake ji. Umar ne ya fara yiwa Abba sannu ya amsa, sannan Khalid,  Abba ya amsa yana faɗin, "Ya wajan aikin?" Khalid da aka taɓo mishi inda ke mishi ƙaiƙayi, marairaice fiska yayi tare da cewa, "wajan aiki ba daɗi Abba, ayyuka kaman za su halaka maka autanka, dan Allah ka tayani ba wa Yaya Umar haƙuri ya koma zuwa ni na kula da Yaya Sadeeq,  idan ya warke sai mu cigaba da zuwa tare." "Ai ko babu Sadiya goɗai-goɗai da kai ba ka zama auta ba Khalid." "Allah yaro ne ni Abba,  am just 24 fa, Abba ban fa wuce a goyani ba, nidai ayyukan nan sun fi ƙarfin shekaruna." "Wa zai goyaka? Amma dai ba matata ba ko? Dan addu'a nake Umman taku ta haifo wani ɗan, dan dai kai kam ka wuce auta ka wuce goyo, aure ma zan maka ba jimawa." Khalid ɓata fiska yayi tare da cewa, "Abba kana cewa Umma za ta haifo wani ɗan sai inajin haushi, kishi nake a barni a auta kawai atou." Ba iya Abba ba har Umar sai da ya dara jin abinda Khalid ya ce, girgiza kai Abba yayi tare da faɗin, "Allah ya shirya ka Khalid, amma dai soon zan aurar da kai." "Amin Abba, 24 kam ai wacce aka aurawa ni sakina za tayi dan ni yaro ne." Umar ƴar murmushi yayi tare da cewa, "Ka bar cewa 24 kawai fa, age is not just a number, from second, minute, hour, day, week, month and year a haka har ka aje ashirin da huɗu." "Amma ai dai ko ma menene Yaya Umar sai kun yi auren kamun nayi, kuma dai aiki na manya ne." Abba ya ce, "Duk lokaci guda zan aurar da ku In sha Allah, bari na samu na sallami auta." Khalid sake ɓata fiska yayi, Umar kuma ya murmusa cikin jin kunyan Abba dan yasan maganarsu da Abba a kan hakan. Khalid sai sannan ya kai dubansa ga Sadeeq, ya ce, "Alhamdulillah sannu da tashuwa Yaya, Allah ƙaro sauƙi da ƙarfin jiki." "Amin", duk suka haɗa baki wajan amsawa, har da Sadeeq ɗin amma shi ciki-ciki ya amsa. Abba miƙewa yayi tare da cewa, "Bari na wuce ko, Abubakar Allah ƙara sauƙi, Umaru mu kwana lafiya, Allah ya muku albarka ya ƙara haɗa kawunanku." "Amin summa amin Abba", Umar ya amsa cikin girmamawa. Sadeeq ma murya a tausashe cike da girmamawa ya ce, "Allah kai ku gida lafiya." Amsawa Abba yayi sannan ya nufi ƙofa, Khalid ya mara wa Abba baya suka fice tare, har wajan mota ya raka Abba,  sai da direba ya ja motan suka fice a asibitin sannan Khalid ya koma ciki. Umar yana ganin ficewan su Abba ya juya ga Sadeeq tare da cewa, "Da gaske fushi kake?" Sadeeq haɗe rai yayi tare da yin banza da Umar bai ce mishi ci kanka ba, saboda haushinshi yake ji sosai. "To dai ba zan ce sorry ba indai akan rubbish ɗin Sadiya ne, how dare she da za ta saka ka agaba tana kuka bayan baka da lafiya." A ɗan fusace Sadeeq ya ce, "So what? Kai ta yiwa kukan ko ni? Ina dai lafiyata ce?" Umar taɓe baki yayi tare da cewa, "Allah kai ka ɓata yarinyar nan take duk shirmen da ta gama dama, tana abu kaman ba wacce ake shirin aurenta ba, yarinya ta koma kaman goyon gauro......", Umar cigaba yayi da surutu kaman wanda Sadiyar ke gabansa zai bubbugeta. Sadeeq na kwance idanuwanshi a lumshe yana jin duk abinda Umar ke cewa, ranshi na ƙara ɓaci, guntun tsaki ya ja tare da yin ƙwafa duka masu sauti, amma bai sake tanka wa Umar ba, har Khalid ya dawo cikin ɗakin, sannu ya kuma yiwa Sadeeq,  amma Sadeeq ko kallonshi bai yi ba balle ya amsa, Khalid da ya so a yanzu ya samu ya haɗa su a waya sai kuma ya sha jinin jikinshi ya samu waje ya zauna a gefe, kan ɗaya single bed ɗin. Umar fidda wayarshi yayi yana dannawa ya ce, "Ya kuka yi da Faransawan nan?" Khalid ya gane da shi Umar ke magana ba a waya ba, hakan ya sanya ya gyara zama tare da koro mishi bayani, baƙi suka yi daga Faransa, akan contract na wani katafaren gini da za su yi, sun ba da duk details na yanda suke son komai, an daidaita maganan kuɗi yanda za su biya, an zana musu yanda suke buƙata, sai daga baya kuma suka zo suna faɗin a musu ragin kuɗin, already Sadeeq kuma ya ce musu baisan zancen ba, in ba za su biya yanda aka shirya da su da fari ba, to zai sayar wa wasu zanen, hakan ya sanya suke sintiri a companyn,  duk da kuwa Umar na magana da su through system ko waya, amma sai sun kamo hanya sun zo, yanzu wannan zuwan nasu dai a ƙarshe sun dai-daita, "Za su biya amount ɗin da aka yi da su tun farko", Khalid ya faɗa yana fidda wayarshi a aljihunshi. Umar jinjina kai yayi tare da cewa, "That's good for them." "Ai kam ya fi musu, in ba haka ba dama renin wayo ke damun mutanen nan amma sarai suna da kuɗin", faɗin Khalid. Umar ya buɗe baki zai yi magana sai ringing na wayarshi ya dakatar da shi, «Sister Khausar», sunan wacce ta ƙira shi, sai da ya sauƙe ajiyan zuciya sannan yayi picking call ɗin yana sakin guntun murmushi, jin muryan wacce ta yi sallaman ya sanya shi faɗaɗa murmushin nashi, ya amsa sallaman tare da cewa, "My girl, how're you doing?" A ɗaya ɓangaren kuma, siririyar murya ne na yarinya ƙarama ta amsa ta hanyar cewa, "Am doing great Uncle U, and you." "Am fine too my girl, how's Daddy, Mummy and Baby Nayla?" "They're all doing good, Ya granny's namu and uncles? How's little Mum?" "They're all fine, where is your Mummy?" Yarinyar shagwaɓe siririyar muryanta tayi tare da cewa, "Uncle U, she's with baby Nayla." "Kin kira ni bata sani ba?" "Umn", yarinyar ta faɗa tana yin ƙasa-ƙasa da murya. Umar na ƙoƙarin yin magana, sai ya jiyo muryan Khausar, na salati tare da yiwa Najla faɗa a kan ƙiran da tayi bata sani ba, sannan ta kara wayan a kunnenta tana faɗin, "Uncle U." Umar murmushi yayi tare da cewa, "Sister ki daina yiwa my girl faɗa, laifinki ne, da baki aje wayan a inda za ta gani ba ai da ba za ta ɗauka ba balle ta ƙira kowa." Khausar girgiza kai tayi tare da cewa, "Uncle U baka san karambani da manyance irin na Najla bane, yanzun nan fa na shiga toilet da Nayla zan shiryasu su kwanta shi ne ta ɗau wayar, yarinya shekaranta biyar kawai amma kaman uwar mata, ban fa isa tayi ido huɗu da wayata ba." Guntun dariya Umar yayi ya ce, "Smart girl kenan, Allah ya musu albarka ya raya su." "Amin Ya Rabbi,  ya gidan? Ya kowa da kowa? Ina Yaya Sadeeq?" Umar miƙewa yayi ba tare da ya amsa mata ba ya ƙarasa har gaban gadon Sadeeq ɗin, yana ƙoƙarin cire wayar a kunnenshi ya jiyo muryanta tana faɗin,  "Uncle U, are you there?" "Yeah, ga shi nan ku gaisa", ya ƙarishe faɗa yana miƙa wa Sadeeq wayan. Sadeeq amsan wayan yayi tare da kara wa a kunnenshi ya amsa sallaman Khausar,  cikin girmamawa ta gaishe shi ya amsa,  ya tambayi ya mijinta da yaran, ta shaida mishi kowa lafiya, sannan ta tambayeshi ya taji muryanshi haka kaman bai da lafiya, ya ce mata gajiya ne kawai, basu yi wani dogon magana ba suka yi sallama,  Umar da ke gefe ya amshi wayanshi suka cigaba da magana. "Uncle U, Yaya Sadeeq na lafiya kuwa naji muryanshi haka?" Ta tambaya cikin nuna kulawa da damuwa na yanayin da taji muryan ɗan uwan nata. "Lafiyanshi ƙalau kawai stress ne." "Okay, Allah taimaka." "Amin, yaushe za ku shigo ne? Naji Mama ta ce a week ɗin nan." "In sha Allah on Saturday." "Allah kai mu da rai da lafiya,  Allah ya kawo ku lafiya, a gaishe da Officer." "Amin Uncle U,  officer zai ji, mu kwana lafiya, byee." Amsawa Umar yayi tare da katse ƙiran. Khalid ko da ya ga Sadeeq ya amshi waya yayi magana da Khausar,  sai ya sauƙe numfashi tare da samun confident na cika wa Sadiya alƙawarin da ya mata, gwada ƙiran wayanta yayi amma ya ji busy, hakan ya sanya ya dakata ta gama call nata, sannan ya ja plastic chair ya koma kusa da gadon Yaya Sadeeq,  murya a tausashe tare da fatan amincewan Sadeeq,  ya ce, "Yaya Sadeeq ayya Sadiya tana son jin muryanka." Sadeeq idanuwanshi a lumshe,  yana jin Khalid amma bai ce mishi ci kanka ba, har sai da Khalid ya kuma cewa, "Please Yaya Sadeeq,  wallahi duk ta bi ta damu sosai, da ƙyar ta ci abinci ta sha magani, dan sai da na mata alƙawarin haɗa ku a waya ma.......", ya kwashe komai da ya sani ya faɗa wa Sadeeq har da wuni kukan da tayi. Sadeeq nauyayyan numfashi ya ja, sannan ya sauƙe a hankali, sai da ya wara idanuwanshi sannan calmly ya ce, "Call her." Khalid cikin hanzari ya sake dialing layin Sadiya, ya kuma ci sa'a yanzu her line is not busy, dan ringing guda yayi ta ɗau call ɗin. ⭐️ RAYFIELD      SADIYA POV         *** Cikin natsuwa Sadiya ta fito a gidan nasu, kanta a ƙasa take tafiya cikin yanayin rashin ƙarfin jiki, domin kaman wacce sai ta tambayi ƙasa kamun ta taka haka take tafiyan. A sanyaye ta fidda hannunta da ke a cikin hijabi, ta yi knocking na ƙaramin ƙofan gidan ta kuma tura a lokaci guda, kasancewan ba a kulle ƙofan ba tukunna tana turawa ya buɗe, da sallama ta shiga, mai gadi ya taso yana mata sannu tare da barka da shigowa, a sansanyar yanayinta ta amsa mishi tare da wucewa ciki ba tare da ta tsaya amsa dogon gaisuwan da yake niyan mata ba, still tafiya take gently har ta tura ƙofan shiga main palourn masu gidan. "Assalamu alaikum", murya a ɗan sake ta yi sallaman. "Wa'alaikissalam", Sa'ad da isowanshi cikin palourn kenan ya amsa mata. Sai da ta ɗan ja numfashi, sannan ta shigo a nitse, kanta a ƙasa ba tare da ta kalli inda Sa'ad ya zauna a palourn ba ta nufi upstairs, tana faɗin, "Barka da dare Yaya Sa'ad." "Yauwa Auta Amarya, barkanmu, ya jikin naki kuma?" "Alhamdulillahi da sauƙi." "Allah ya ƙara afuwa, sannunki da shigowa ko." "Ah ma sha Allah,  Auta jiki yayi dama-dama har an lallaɓo an shigo", maganan Umma da ya katse na Sadiya da ke shirin amsawa Sa'ad. "Umn Alhamdulillah Umma", Sadiya ta faɗa idanuwanta na cikowa da ƙwalla. Umma ƙarasa sauƙowa a stairs ɗin tayi tare da ƙarasawa wajan Sadiya, ta ɗaura hannunta a kafaɗar Sadiya suka taka har wajan rantsattsun haɗaɗɗun kujerun palourn,  sai da suka zauna ta kwantar da kan Sadiya a kafaɗanta, tana shafa kanta take faɗin, "Sannu ko Auta, Allah baki lafiya ya yaye miki wannan lalura, daman yanzu sauƙowa na zan shiga wajanku kenan, ashe kin lallaɓa kin taho wajan Ummanki." "Umma da sauƙi." "Fatan dai kin sha magani?" "Eh Umma." "To yayi kyau Allah ya ƙara afuwa,  Yayanki Sadeeq na gaishe ki sosai." "Ina amsawa, Allah ya ƙara mishi lafiya shi ma." "Amin autana." Sa'ad ne ya ce, "Ai Yaya Sadeeq ya warke ya ma fi ki lafiya da alama, yanda daga ganinki jikinki ba ƙwarin nan." "Ma sha Allah", faɗin Sadiya da take jin kaman ta rufe ido ta ganta a gaban Yaya Sadeeq ɗin. Umma murmushi dai tayi kawai bata ce komai ba, amma in ba haka ba kowa ya ga Sadeeq ya san dauriya ce kawai irin ta maza da jarumta, domin kana kallon yanda yake kulle ido ka san akwai abinda ke mintsininshi kawai ƙarfin hali yake yi. Sadiya a hankali ta janye kanta a kafaɗan Umma,  sannan ta miƙe tana faɗin, "Umma wayata." "Ai kuwa yana a ɗaki, sai ki haura ki ɗauko", faɗin Umma tana yiwa Sadiya murmushi. Jinjina kai Sadiya ta yi, sannan ta juya ta nufi upstairs cikin takunta na nitsuwa a sanyaye. Sai da ta haura, sannan Sa'ad ya juyo ga Umma yana faɗin,  "Umma ya kamata Sadiya

Chapter 10 of 32