Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kin faɗa, kuma dai bansan a wanne gari ake haka ba, amarya ba ci ba sha sai sanya wa zuciyarta damuwa, duk kin zama ba kyan gani kamar ba ke ba, so kike Haidar ya tuhume mu ko? To ki saki ranki tun kamun gwaggwaninki su iso su rufe Mamanku da faɗa kin san su sarai." Ajiyan zuciya Sadiya ta sauƙe, sannan ta ɗage kanta a kafaɗan Umma ta ce, "Allah Umma na ci tuwo sosai a gidan Mama, har magani na sha, ki tambayi Yaya Khalid ko Mama." Jinjina kai Umma tayi tare da cewa, "Shikkenan, Allah ƙara mana ƙoshi, tun da kin sha magani sai ki yi abinda za kiyi ki kwanta da wuri." "To Umma, Allah tashe mu lafiya." Da, "Amin", Umma ta amsa, sannan ta miƙe ta fice da plate da ta shigo da shi. Sadiya tana ganin ficewan Umma,  ta sauƙe wani nauyayyan numfashi, sai da ta lumshe idanuwanta na mintuna, sannan ta miƙe ta shige toilet, ruwa ta watsa ta fito tayi shirin bacci, cikin dogon riga na bacci, ruwan ɗorawa, saboda yellow ya kasance ɗaya daga cikin favourite colors na Sadiya.    Sai da ta kammala komai ta kwanta, sannan ta laluɓo layin Haidar ta aika mishi da ƙira, ringing guda yayi ya katse ƙiran ya ƙirata, tana sakin tattausan murmushi ta ɗauka tare da kara wa a kunnenta, "Umn rankashidaɗe na Halimatu." ⭐️ ALIYU HAIDAR POV    *** Haidar wuni yayi fama da ayyuka, a gefe guda kuwa yana ta gwada layin Sadiya baya samun ta, hakan ya sanya aikinshi ya ja lokaci sosai, ya so zuwa wajan Sadiya dan tabbatar da lafiya take, musamman da ya kwana da sanin za ta je asibiti, shiyasa hankalinshi bai kwanta ba, amma ba yanda ya iya don kuwa lokacin da ya fito da niyan zuwa wajan Sadiya, lokacin ne Hajiya ta dabaibaye shi da aikenta, bai ma dawo ba yana hanyan dawowan kenan ƙiran Sadiya ya iske shi, hakan ya sanya ya parker motarshi suka yi waya, sai da suka kammala ta ba shi uzurin Umma na mata magana, sannan shi ma ya ja motan ya ƙaraso gida, sai da ya parker motar sannan ya fito tare da locking nata, cikin ƙasaitacciyar tafiyarshi yake taku cike da gajiya, domin tabbas yau ya gaji matuƙa, tun safe har yanzu bai huta ba.    Lokaci guda ya kai hannunshi jikin ƙofan da zai sada shi da main palournsu, ya danna door bell kuma ya murɗa handle na ƙofan ya shige, bakinshi ɗauke da sallama ciki-ciki, ba a amsa mishi sallaman ba saboda main palourn ba kowa, dan daman bai sa ran samun amsan sallaman ba, kaman yanda bai sa tsammanin ganin kowa a palourn ba, wannan palour ne da iya baƙi ake iya samu a ciki time to time, babban palour ne sosai iya ganin mutum, mai ɗauke da set uku na kujeru mist color, palourn yayi matuƙar ƙayatuwa duk da ba wasu abubuwan hayaniya a ciki sosai, plasma ne babba da ya kusa rabin bango wanda mutum ya ɗauka ko majiƙi ne, sai dogayen home theatre da ke a gefe da gefen plasman, sannan sauran part's na bangon ɗakin an manne su da frame masu girma na zane mabambanta masu kyau sosai da ɗaukan hankali, ga isashshen centre carpet milk color a tsakiyan kujerun, duk set guda na kujera da nashi madaidaicin centre table, banda sansanyar ƙamshi da sanyin ac ba abinda ke tashi a palourn.    Haidar sai da ya ɗan shaƙi daddaɗan iskan main palourn, sannan ya cigaba da takawa, wani ƙofan ya kuma buɗewa inda ya sada shi da asalin palourn da masu gidan suke, wannan palourn ya fi palourn da ya wuce kyau da ƙayatuwa, sai dai bai kai wanda ya wuce da farko girma ba, wannan madaidaicine dan set na kujera ɗaya ne, a haka ma suna a manne da juna, saboda daga gefe akwai step's da zai sada mutum da upstairs inda ɗakunan yaran matan gidan yake, a ɗan gefen step's ɗin kuma ƙofan kitchen ne, a cikinshi akwai ƙofa biyu, ɗaya na store ɗaya kuma ƙofan baya ne, wanda in ka bi shi za ka fita compound na gidan ta baya ba tare da ka bi ta main palour ba, daga ɗaya gefen step's ɗin kuma ɗan corridor ne wanda ke ɗauke da ɗakuna biyu, na Hajiya da kuma na Alhaji, wannan palourn ma kaman wancan dai ɗauke yake da tambatsetsen plasma da sauran abubuwa da ke ƙawata wajan zaman TV, ga showglass da ke ɗauke da mazubin turarukan wuta different type's with different scents, airfreshners, burner's, humidifier's da sauransu, sinadaran ƙamsasa gida, sannan a ko wanne ɓarayi na bangon palourn akwai frames, wani na Alhaji da Hajiya da yaran nasu duka, wani iya Alhaji da Hajiya, wani yaransu mata kawai, wani kuma duka yaran nasu, a side da ƙofan da zai sada ka da sashin Haidar, a nan ne frame na Haidar shi kaɗai ke manne, yana sanye da ƙananan kaya yayi masifaffen kyau, wannan ƙofan da ke a side ɗin ne idan ka shige shi zai sada ka da gajeren corridor sai palourn Haidar wanda ke ɗauke da ɗakuna biyu, ɗaya normal ƙofa ne mai kyau da kuɗi, ɗaya kuma glass door ne, nan ne kuma bedroom na Haidar, sashin shi ma ya gaji da ƙayatuwa har bedroom nashi, sai dai ɗaya bedroom ɗin ba furniture a ciki, kuma wannan aikin Hajiya ce, ta ce ba za a sanya komai a ciki ba, daga shi har Alhaji ba wanda ya tamka mata a kan hakan, sun dai zuba mata ido ne su ga me take nufi da hakan, dan sun san duk tsawon lokaci dai dole abinda take nufi ya fito ko kuma idan Haidar ya tashi saka furniture ɗin ta ƙyale shi ya saka. Da sallama ƙasa-ƙasa Haidar ya shigo wannan palourn ma, sai dai a nan kam jama'an da ke a palourn kaf sun amsa mishi, Hajiya, Nihal, Nimra da Husna, ƙannen nashi sannu da dawowa suka mishi bayan amsa sallaman, amma Haidar bai ko kallesu ba balle ya amsa, har ya ƙarasa gefen  Hajiya da take zaune a kujera mai ɗaukan mutum uku, Husna ta yi matashin kai da cinyan Hajiyan. Daga ɗaya gefen Hajiyan ya zauna tare da cewa, "Hajiya barka da dare." Fiska ba yabo ba fallasa Hajiya ta ce, "Yauwa Haidar, sannunka da dawowa ko, fatan ka duba komai da komai lafiya?" "Eh na duba komai ya iso yanda kika ba da lissafin." Sai sannan Hajiya ta ɗan washe baki tare da cewa, "Ma sha Allah, nima gobe zan leƙa da yardan Allah, kwana biyu ban je ba tun da na amso list na abubuwan da ya kamata Nadiya ta shigo mana da su." Haidar bai kuma cewa komai ba ya miƙe tare da nufan hanyan da zai sada shi da ƙofan sashin shi, maganan Hajiya ne ya dakatar da shi. "Dinnern fa? A kawo maka sashinka ne?" "No Hajiya am okay, Nihal ta kawo mini coffee kawai", yana gama faɗin haka ya murɗa handle na sashinsa ya shige, tun daga gajeren corridorn ya soma cire p-cap nashi da wristwatch nashi, da sallama ya shige palourn shi, kai tsaye ya wuce cikin ɗakinshi, a nan ya ƙarisa rage kayan jikinshi ya shige closet nashi ya wuce toilet, ya ɗan ɗau mintuna sannan ya fito sanye da rigan wanka(bathrobe), yana ƙoƙarin tsayawa tsane jikinshi ya sanya pyjamas sai ya jiyo sautin wayarshi, hakan ya sanya ya fito tare da ɗaukan wayan, katse ƙiran nata yayi ya ƙira ta, tana ɗauka ya ce, "Assalamu alaiki natsuwar ruhin Aliyu Haidar." Lumshe idonshi yayi tare da sakin numfashi mai tattare da gajiya, lokaci guda kuma murmushi na mamaye haɗaɗɗen fiskarshi, saboda amsar da Sadiya ta ba shi a ɓangarenta. "Haidar na Halimatu in ba da kai na a sare na je gida na ce da Alhajina faɗuwa kan yayi ko?", ya ƙarishe maganar da murmushi mai sauti yana ɗage gira guda kaman tana kallonshi. *** A ɓangaren Sadiya dariya ƴar gajeriya tayi, amma irin dariya mara sauti kuma mai tafiyar da ƙunci da damuwan da ke a zuciya, sannan ta ce, "Ah abun bai kai har haka ba Al-Sad." "Ya kai har ma ya fi", faɗin Haidar yana murmushi wanda ya kore mishi duk gajiyan da yake a ciki, da kuma damuwar wuni kewarta da yayi. "Uhmn, to ya gajiyan ayyukan yau ɗin? Fatan gajiyan ya sake mini angon nan da ƴan kwanaki, ko kuwa dai sai an zane gajiya?" "Nope, gajiya dai tun da ya jiyo muryarki yake ƙoƙarin ƙyale ni, amma dai da za a zane shi da tausa da zai fi tafiya da kyau." Ƴar murmushi Sadiya ta yi bata ce komai ba, sai juyi da tayi a kan gadon Umma tana jin ƙaunar Haidar na sake huda duk wata magudanar jini, ruwa da numfashi na jikinta. "Sweet Al-Sad...", maganan da yayi niyan yi ya katse saboda knocking ƙofarshi da ake yi, hakan ya sanya ya ce, "Excuse me sweet Al-Sad, bari na amshi coffee a wajan Nihal." Gyaɗa kai Sadiya tayi tare da murmushi  kaman yana kallonta, bata katse ƙiran ba saboda ya hana ta, muddin ba ita ta ɗau excuse na katse ƙira ba, ko shi da kan shi ya nemi ta katse ƙiran, to dan ya ce bari yayi wani abu to ya hana ta katse wa, haka ita ma indai abinda za ta yi ba wani na buƙatan ta katse ƙiran bane to bata katsewa zai jira ta har ta kammala sannan sa cigaba da wayarsu. Haidar sanin Nihal ce ya ce ta kawo mishi coffee, sai bai damu da bathrobe da yake sanye da shi ba, kawai ya gyara zaman shi a kan kujeran da yake zaune wanda ke gefen gadonshi, wayan na maƙale a kunnenshi ya ce, "Hey Nihal come in." Husna da ke tsaye a bakin ƙofar ɗakin Haidar ɗin, hannunta riƙe da tray na tangaran madaidaici mai ɗauke da coffee cup da murfinshi, fari tas mai yalƙi da ɗaukan ido,  tiriri da ƙamshin coffee sai tashi suke suna dakar mata hanci, knocking guda tayi bayan mintuna ta ji ya ce ta shigo, sunan Nihal ta ji ya ƙira ba ita ba, hakan ya sanya jikinta ya ɗan kama kerma, dan ta san wannan ma wani hukuncin za ta amsa, na kawo abinda ba ita ya aika ba, balle kuma ita da ya hana ta shiga ɗakin shi, yanzu kuma ga shi ya ce ta shigo tunda a tunaninshi Nihal ce, rashin shigarta kuma wani bala'in ne a wajan Ya Haidar, idanuwanta ne suka ciko da ƙwalla. "I said come in, ko ni zan taso na amsa? Ko sai ya huce tukunna za ki shigo?" Maganar Haidar shi ya dawo da ita daga tunanin da take yi, sannan shi ya ƙara sanya wa ta daburce, amma sam hakan bai sanya ta yunƙura da niyar shiga ba. Haidar da ranshi ke a ɓace na manna mishi hauka da Nihal tayi, a tsawace ya ce, "Don't let me come and meet you there." Sanin halin Haidar ya sanya Husna yin saurin tura slice glass door ɗin, ta sanya ƙafanta ƙirjinta na bugun ɗari uku da tamanin, tana ambatan sunan Allah kawai, dan ta san yau sai ɗan buzunta. *** Za ku iya samun littafin a waɗannan manhajoji. ●BAKANDAMIYA HIKAYA. ●WATTPAD @UwarBatoorl96 ●AREWABOOKS. @Uwarbatoorl96 ●WHATSAPP 09161720046 a kan Naira #500. Idan littafi ya zama completel 1k yake in sha Allah. # Hareeyh # 09161720046 # 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩 # 𝙇𝙞𝙠𝙚 & # 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚 [07/12/2025, 13:34] Uwar Batoorl✍️❤️🥰: I just published "Page 51 _ 55" of my story "💔NAUYIN BAKI👄💔 Na Uwar Batoorl"::https://www.arewabooks.com/chapter?id=69255c2f36d95e13db2789e8 💔NAUYIN BAKI....👄💔        Na Uwar Batoorl. 𝗕𝗜𝗦𝗠𝗜𝗟𝗟𝗔𝗛𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗠𝗔𝗡𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗘𝗘𝗠     اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤🤍 🅿️ 21 _ 22 ⭐️ Husna kanta a ƙasa ta shigo ɗakin, bakinta ɗauke da sallama cikin siririyar muryarta, amma ƙirjinta banda bugu ba abinda yake yi, hakan ya sanya ta tsaya a tsakiyar ɗakin tare da ƙara sunne kanta ƙasa ta kasa ƙarasawa inda yake. Haidar da tunda ya jiyo sautin sallaman ya gane ba Nihal ba ce, ran shi idan ya kai dubu to ya ɓaci, duk da ya san wannan ba zai wuce aikin Hajiya da ke son cusa mishi Husna a lamuranshi ba, amma ita ma mahaukaciyar yarinyar da nata, idan ba hauka ba mai zai sa ta ke kutsa kanta tsakanin masoya guda biyu waɗanda aka halicce su dan junansu, rai a ɓace ya kalleta tare da taune leɓenshi na ƙasa alaman zai yi maganinta, a ɗan tsawace ya ce, "Idan kika kuskura ya huce, hmmn!", iya haka ya faɗi tare da sanya wayarshi a loudspeaker, ya saisaita muryarshi tare da cewa, "Pardon me sweet Al-Sad." Daga ɗaya ɓangaren haɗaɗɗiyar tattausar muryar Sadiya ce ta ratso wayan, cewa tayi, "Jiranka ka kammala duk abinda za ka yi, abu ne na alfahari gare ni, domin na hidimta wa so, dan haka bana buƙatan ba da haƙurinka." Tattausan murmushi Haidar ya saki tare da cewa, "Allah kawo mana kwanakin da suka rage cikin aminci." "Amin", Sadiya ta amsa tana lumshe ido. Husna da take jin duk musayan kalamai da Haidar ke yi da Sadiya, wani abu ne ya soki zuciyarta tabbas mai zafi ne da ciwo, amma ta san ko karen hauka ne ya cijeta to ba za tayi kishi da Sadiya ba, dan wargi ma waje ya samu, ina ita ina kishi da Sadiyar da Haidar ya gama mallaka mata zuciya da ganganar jikin shi, wasu irin hawayen tausayin kanta da ƙaunarsa ne suka ciko idanuwanta, hakan ya sanya ta ɗan ɗago kanta ta saci kallonshi, amma ganinshi da bathrobe ba ƙaramin kiɗimata yayi ba, hannunta ne ya fara rawa, firgici da tsoro suka dirar mata na ganin wasu ɓangare na jikinshi, duk da ma dai Allah ya taimaketa ya malmale jikinshi da kyau, daga wuyarshi zuwa abinda ya kai guiwarshi a kulle ruf, amma duk da haka ba ƙaramin kiɗima ta yi ba, shiyasa tayi saurin sake sadda kanta ƙasa.     Haidar da ke waya da Sadiya cikin nishaɗi, amma idanuwanshi na kan Husna yana bin ta da mugun kallo, ganin abinda take shirin yi ya sa a tsawace ya ce, "Don't you dare try to let what in your hand fall down", ya faɗi yana kan bin ta da mugun kallo, dan shi da kanshi haushin shigowanta yana sanye da bathrobe yaji, shiyasa ya hanata shigar mishi ɗaki saboda privacy nashi, gwanda su Nihal ma. Husna ƙwallan da take maƙale su a idanuwanta ne suka zubo, sake satar kallonshi ta yi, amma kallon da ya aika mata da shi ya sanya tayi saurin sharewa, ta kuma sadda kanta ƙasa, daurewa tayi ta ƙarasa inda yake zaune cikin sauri-sauri, a kan mini centre table da ke gabanshi ta ajiye trayn coffeen, tana ƙoƙarin miƙewa ya ce, "stay on your kneel and wait for me." Daram! Haka zuciyar Husna ta buga, wani irin hukunci Ya Haidar ke shirin mata? da ta zauna yana waya da Sadiya a gabanta ta gwammace ya mata ɗan banzan duka kai ya karyata ma, domin karayar hannu ko ƙafa ya fi mata sauƙi sau dubu a kan karayar zuciya, domin fata-fata Ya Haidar ke shirin yi da zuciyarta, ta yanda zuciyar will never be heal. "Al-Sad, me Nihan kuma ta yi? a barta ta tafi please a yafe mata", faɗin Sadiya a nata ɓangaren, domin taji tsawan da Haidar yayi, dan har ita ma ta tsorita, duk da idan da sabo ya kamata ta saba da halin Haidar na yiwa ƙannenshi tsawa da faɗa, amma ta kasa sabawa saboda ko Yaya Umar da ke hantararta ba ya mata tsawa sosai, kallo ne kawai idan ya mata to ya isa ta shiga taitayinta. Haidar lumshe ido yayi tare da yin baya ya jingina da jikin kujeran da yake zaune, murya cike da tulin ƙaunarta ya ce, "An yafe mata Sarauniyata, mamallakiyar Haidar da Zuciyarshi, ai duk abinda kike so ayi, to kawai ki faɗi cikin umurni, your wish is my command your majesty." "Zan kasance Sarauniya ne a fadar da ka kasance Sarkinta, idan babu kai to babu ni, duk inda kake kuma to tabbas akwai ni, ko da gangar jikina baya wajan, to zuciyata da ruhina za su kasance a wajan, don kai ne zuciyar tawa, duk inda za ka Halimatu na a tare da kai ƙafa da ƙafa." "Ina matuƙar ƙaunarki Al-Sad, bana muradin ganin ranan da zan kasance babu ke, idan babu ke to rayuwata fanko ce, ni da kaina ba za ta amfanar da ni ba balle wani ya amfana daga gare ni, ke ce komai tawa." "Da numfashi dai ba abinda zai farraƙa Halimatu da Haidar in sha Allah, kai ko babu numfashi ma ni taka ce, da a ce wannan rayuwan za ta ƙare mu kuma dawowa a wata rayuwar, to kai zan kuma zaɓa a wanda nake so na kasance tare da shi har ƙarshen rayuwar, kai ne farin ciki na kai ne muradina Al-Sad, zan zaɓe ka sau dubu a rayuwa dubu." "Ke ce duniyata duniyar da aka halitta domin ni, ke ce mafarkina mafarkin da har abada bana son farkawa daga shi, ke ce zahiri na zahirin da nake son tabbata a shi har ƙarshen numfashi na, ke ce addu'ata addu'ar da bana taba gajiyawa da yi ko da na second bana hutawa wajan roƙo ki, ke ce rayuwata, ke ce komai nawa sweet Al-Sad, ina fata da addu'an idan Allah ya mallaka mini ke, na maida ki mace mafi sa'ar aure da miji a rayuwarta, ki zama abin fata da buri ga ko wacce mace, na yalwata ki, na wadata ki, na riritaki, na ƙaunace ki, na yi haƙuri da ke a ko wanne yanayi da hali na rayuwa." Wani irin abu da ya fara fisgar Husna ji take kaman daga zaunen ma jiri zai ka da ita, hannunta ta kai ta dafe kanta da ke juya mata yana sara mata, ɗiff ta dena jiyo musanyan kalaman da Haidar da Sadiya ke yi, ta tafi tunano ƙaddarar da ya kawo ta ɗakin. *** «Da kallo Hajiya ta bi Haidar da ya ce Nihal ta kawo mishi coffee, taɓe baki tayi tana faɗi a ranta, "Tunda kai ka haifa mini Nihal ɗin za ta kawo maka, wacce baka son ganin ita zan aiko, idan ka so ka kasheta, kuma ko gawarta sai ka aura, yaro sam baya ji sai taurin zuciya da kunnen ƙashi kaman na mutan farko." Sanyin da Hajiya ta ji a ƙafanta ne ya katse mata zancen zucin da take yi, tana duba wa sai ta kalli Husna ke hawaye, kuma idanuwanta na a kan ƙofan sashin Haidar, hakan ya sanya cikin tausayin marainiyar ƴar tata ta kai hannu ta share mata hawayen, sanna ta ɗago dan yiwa Nihal magana, sai ta samu Nihal ta jima da barin palourn,  hakan ya sanya Hajiya ta ce, "Tashi ki wanke idonki bana son ganin hawayenki kin sani, kuma idan baki daina hawaye a kan Haidar ba zan cire hannuna a batun aurenki da zai yi." Da sauri Husna ta miƙe daga kwancen da take, ta sa hannu ta share idonta, ta kuma wuce wajan dinning area, inda ke maƙale da mirror da tap na wanke hannu ta nufa, ta tari ruwa ta wanke fiskarta sanna ta koma palourn, tana ƙoƙarin zama Nihal ta fito daga kitchen ɗauke da madaidaicin tray na coffeen Haidar, hakan ya sanya Hajiya dakatar da Husna daga zama, sannan ta ce, "Nihal bai wa Husna cofeen ta kai wa Yayan naku." Da sauri Husna ta zauna tare da girgiza kai ta ce, "A a Hajiya, nidai ta kai ai ita ya ce." "Ni kuma ke na ce ki kai, da ku da shi ɗin duk ni na haifeku, dan haka abinda na ce na gaba da wanda kuka ce, Nihal miƙa mata ta kai, ke kuwa idan baki amsa kin kai ba to babu ni babu ke." Da sauri Husna ta miƙe tare da ƙarasawa gaban Nihal ta miƙa hannunta tare da cewa, "Aunty Nihal kawo na kai." Nihal kallon Husna tayi sannan ta kalli Hajiya, fiska a marairaice ta ce, "Amma dai Hajiya kin san halin Ya Haidar sarai ko, yanzu ke kika ce amma a kan haka sai ya zane ni bai dame shi ba." "Ya kashe ku duka ba iya zanewa ba, miƙa ma ta kai kamun raina ya ɓaci." Nihal na tura baki ta miƙa da Husna trayn, ita kuma ta amsa, duk da tana cike da tsoro, amma tana cike da ɗaukin za ta kalleshi da kyau, a haka ta nufi sashinshi da sallama, sai dai tun da ta ga ba ya palournshi, ta sha jinin jikinta sanin ya hana ta shigar mishi ɗaki, hakan ya sanya ta tsaya daga bakin ƙofa tayi knocking.» *** Dai-dai ta kammala tunano yanda aka yi bayan barin Haidar palourn, da kuma tsautsayin da ya sanya Hajiya ta dage sai ta kawo Coffeen, dai-dai sannan Haidar kuma ya kammala wayarshi da Al-Sad ta shi, juyowa yayi ga Husna fiskar nan tamau a haɗe ba alamar rahama ko sassauci, "Ke ina wasa da ke? Ke ce Nihal? Ko salon haukan naki ne ya motsa da zan ce Nihal ta kawo mini abu ki amsa ki kawo, ni sa'anki ne?" Ya faɗa cikin tsawa yana aika mata da mugun kallo. Husna da bata san sadda hawaye ya wanke mata fiska tas ba, buɗe bakinta da ke jiran ƙiris ya ba da sautin kuka tayi tare da cewa, "Ka..ka..kayi haƙuri Yaya, wallahi Hajiya ce ta ce na kawo dole", ta faɗi cikin rawan murya da sauri kaman wacce ta ga dodo. Haidar ƙwafa yayi dan ya san za a rina wai an saci zanin mahaukaciya, wannan dama ai sai aikin Hajiya, sake haɗe fiska yayi tare da cewa, "Idan Hajiya ta ce ki shiga wuta za ki shiga ne? To wallahi kika cigaba da kutso haukarki cikin lamurana zan saɓa miki kamanni shashasha kawai, ai dai ban miki kama da sa'an kulaki ba ko?" Husna sanin idan ta buɗe baki da niyan amsa mishi, to sautin kuka ne zai fito, hakan ya sanya ta gyaɗa mishi kai kawai hawaye na kan gangaro mata. "Bakinki ciwo yake da ba za ki iya buɗewa ki amsa mini bane? Ko na fara wasan haka da ke?" "A...a..a a Ya Haidar ka yi haƙuri" ta faɗa cikin kukan da sautinshi ya riga ya fito. "Mtswww!, dalla malama tashi ki ɓace mini a gani kamun na tattakaki, kuma ki kuskura ko by mistake ki ƙara tako mini ɗaki ki ga abinda zan miki, wawuya kawai mara hankali da tunani." Kamun Haidar ya ida faɗan, tuni Husna ta miƙe da ƙyar da ƙafafuwanta da suka yi tsami, jiki na rawa tana kuka ta fice da sauri ba tare da ta ko waiwaye shi ba. "Maza ki ƙara sautin kukan naki ki je ki cewa Hajiyan kashe ki nayi kika dawo, mahaukaciya kawai, in ba hauka ba me zai sa ka so wanda ke son wani, ai ko Hajiya ce ta zuga ki za ki yiwa kanki faɗan hakan, balle kuma nasan wannan munafurcinki ne kika sanya Hajiya ta hau kai ta zauna", cikin ɗaga murya ya yi maganan, ta yanda za ta jiyo shi, sai da ya tabbata ta fice mishi a sashinshi,  sannan ya miƙe yana jan gajeren tsaki, ya wuce closet nashi ya sanya kayan bacci, zuciyarshi fal haushi wannan shashashar yarinyar ta kalleshi da rigan wanka, salon ta sake raina shi, to yana dai-dai da ita.   Yana kammala shirinshi ya wuce ya bi lafiyan gadonshi ya kwanta, dan already ya sha Cofeen tun yana waya da Sadiya, kuma sun riga sun yi sallama sai da safe, bacci zai yi tun yanzu ya huce gajiyan ayyukan yau. Husna tana ficewa a ɗakin ta rage sautin kukanta, a gajeren corridorn sashin ta tsaya ta share hawayenta tare da dai-daita kanta, duk da tana jiyo abinda Haidar ke faɗi wanda ke sake ƙona mata zuciya, haka ta tura ƙofan ta fice a sanyaye, Hajiya da Nimra ta samu yanzu a zaune a palourn, amma bata bi ta kansu ba ko tsaya sauraran maganan Hajiya da ƙiran sunanta da Nimra ke yi, da gudu-gudu ta haura stairs, ɗakin da yake mallakin su ita da Nimra ta shige tare da kullo ƙofan ta sanya sakata, kan madaidaicin gadonta ta wuce ta faɗa tare da fashewa da sabon kuka, cikin kukan take cewa, "Me laifi na? Wallahi banda laifi, ba laifina bane, laifin zuciyata ce, amma zuciyata meyasa za ki mini haka? Meyasa za ki zaɓi azabtar da ni da son wanda bai taɓa kallona da idon rahama ba balle ta soyayya, tun ina yarinya

Chapter 12 of 32