shi, wanda shi da kan shi yake kula da abunshi, ƙiran ya sanya shi miƙewa dan tafiya, magana yayi da Khalid ya ce, "Kai ma tashi maza duk mu tafi, ba zai yiwu a zauna haka ba wanda ya je wajan aiki ba."
Khalid ba musu ya miƙe suka fice tare da Abba, motar Khalid ɗin suka shiga ya ja su, sai da ya aje Abba a gidan man shi mai suna Salihu Waziri Ltd, sannan shi kuma ya wuce ma'aikatarsu wacce take ta Sadeeq sai masu hannun jari, ciki har da Umar da share nasa ya fi na kowa.
***MASU TALLA ƘOFA A BUƊE TAKE, KU HANZARTA DOMIN AYI INGANTACCIYAR TAFIYARNAN DA HAJARKU, KU KAWO TALLANKU CIKIN AMINCI A TALLATA MUKU SHI CIKIN ANNASHUWA DA SHAUƘI, KU TUNTUƁE NI A WANNAN LAMBA 09161720046.**
⭐️
RAYFIELD
SADIYA POV
***
Direba cikin kulawa ya ke tuƙi a nitse ba giggiwa, suna shiga anguwan nasu motar Sa'ad ta shigo ita ma, ganin haka ta sanya Sa'ad ya rage gudun motarshi yana bin su a sannu har suka ƙarasa ƙofan gidan su Sadiya, direba na fitowa shi ma Sa'ad ya fito, direban buɗe wa Sa'ad ƙofan bayan yayi, Sa'ad ya tattare hannun rigarshi ya sunkuya ya cicciɓi Sadiya, a hannu ya riƙe ta ya shiga gidan da sallama, yana tura ƙofan palourn ya sanya ƙafansa ciki, suka yi ido huɗu da Mama.
Waro idanuwa Mama tayi tare da cewa, "Subhanallahi! Sadiya kuma a hannu me ya same ta? Ba dai duk akan batun rashin zuwa asibitin ba?"
Sa'ad sai da ya aje Sadiya a kujera mai ɗaukan mutum uku, sannan ya ce, "Ai ma daga asibitin muke Mama."
"Ya Allahu!", Mama ta faɗi tare da wuce wa ta kawo ruwa, da kanta ta shafa wa Sadiya a fiskanta, cikin taushin murya take ƙiran sunanta, "Sadiya³", amma shiru Sadiya bata amsa ba.
Sa'ad numfashi ya sauƙe tare da cewa, "Bari na dubo likitan nata ko yana chemist."
Jinjina kai kawai Mama tayi tare da zama a gefen Sadiya ta ɗaura kan Sadiya a saman cinyarta, tana shafa kanta take faɗin, "Allah ya yaye miki wannan lalura Halima, ace muddin mutum ya je asibiti to ba shi ba lafiya, kuma sai likita ya duba ki sannan."
Sa'ad yana fita ya ce da direban ya koma asibiti kawai wajan su Abba, direba ya shiga mota ya mata key ya nufi asibiti, shi kuma Sa'ad ya shiga nashi motar ya yi reverse ya nufi ɗaya layin na bayansu, dan a can chemist ba likitan da ke duba Sadiya da yi mata jinya yake.
Ko da ya isa chemist ɗin a rufe ya samu, amma yana gama parker motarsa sai ga mamallakin chemist ɗin ya iso, sai da ya bari ya buɗe chemist ɗin, sannan ya fito a motar, da sallama ya tsaya bakin ƙofan chemist ɗin tare da bashi hannu suka yi musabaha, mai chemist ɗin yana ɗan murmushi ya ce, "Tunda dai na ganka, to nasan duk yanda za a yi, patient ta Dr Saddam ba lafiya."
Sa'ad murmushi guntu yayi tare da cewa, "Ai lamarin patient taka kaɗai ke kawo mutum nan, in ba haka ba chemist da asibiti ai ba wajajen zuwa cikin shauƙi ba ne, sai da dalili."
Dr Saddam ya ce, "Kuma fa haka ne, da wannan ma dan wannan, muma dole ke aje mu."
"Allah dai ya taimaka", faɗin Sa'ad.
Da, "Amin", Dr Saddam ya amsa, sannan ya shige ciki ya ɗau duk abinda ya kamata, yana citowa sai ga yaron da ke taya shi kula da chemist ɗin, gaisawa suka yi sannan ya ce, "Sageer bari na je layin bayannan na dawo ka kula."
Jinjina kai Sageer yayi, sannan Sa'ad da Dr Saddam suka ƙarasa ga motan Sa'ad ya ja su sai gida, ko da suka iso, Sa'ad ne ya fara shiga ya sanar da Mama isowan Dr Saddam, sannan ya fice ya mishi iso, Dr Saddam cikin girmamawa ya gaishe da Mama tare da tambayan ya jikin mutuniyar tashi, Mama tana murmushi ta ce, "Dr ga mutuniyarka nan jiki sai godiya, wannan lalura tata ta asibiti sai godiya kawai."
"Wataƙila zuwa gaba da yardan Allah abun zai ragu sosai ko bata daina duka-duka ba", Dr Saddam ya faɗa yana ƙoƙarin bai wa Sadiya taimakon da ya dace.
Mama jinjina kai kawai ta yi, a ranta take faɗin da wuya dai Sadiya a ce ta daina wannan lalura gaba ɗaya, sai dai kaman yanda ya ce raguwa to wataƙila ya ragu sosai, tunda a kwanakin baya abinda take yi ya fi haka.
Dr Saddam duk abinda ya kamata yayi ya yi, Sadiya ta farfaɗo daga suman da tayi, amma da matsanancin ciwon kai, kuma tana farfaɗowa abu na farko da ta fara ambata shi ne, "Yaayaana ka tashi mu tafi gida bazan iya cigaba da jure wa ba."
Dr Saddam allura ya mata ya kuma maƙala mata drip, ba jimawa bacci yayi gaba da ita tana ƴan sumbatunta na ambatan Sadeeq, sai da ya kammala komai sannan ya yiwa Mama sallama tare da addu'an Allah kara sauƙi, suka fice tare da Sa'ad, har chemist nashi ya mayar da shi, sannan ya biyasa kuɗin aikinsa ya mishi sallama ya koma gidan, sai da ya tabbatar komai dai-dai ba matsala, har ya gwadawa Mama yanda za ta kashe ruwan idan ya ƙare, sannan ya mata sallama ya fice, asibiti yake son ya koma, amma ya fi son sai ya fara zuwa wajan aikinshi tukunna, sunan gidan man da yake kula da shi S² & K² Ltd, wanda ya kasance mallakin Abba ne.
***MASU TALLA ƘOFA A BUƊE TAKE, KU HANZARTA DOMIN AYI INGANTACCIYAR TAFIYARNAN DA HAJARKU, KU KAWO TALLANKU CIKIN AMINCI A TALLATA MUKU SHI CIKIN ANNASHUWA DA SHAUƘI, KU TUNTUƁE NI A WANNAN LAMBA 09161720046.**
⭐️
PLATEU SPECIALIST HOSPITAL.
ABUBAKAR SADEEQ POV
***
Umma da Umar suna nan a zaune har aka kira azahar, Umar ya miƙe ya fice zuwa masallaci, yayinda ita kuma Umma ta mike ta shiga ɗakin da Sadeeq ke kwance, a sannu a hankali ba tare da making wani sound ba dan kar ta dame shi, ta ɗau pure water ta fice, a waje ta yi alwala, sannan ta dawo ciki tayi sallah, tana idarwa ta naɗe darduma ta maida shi kan drawern gefen gadon da Sadeeq ke kwance, komai a sanɗaɗe take yi, har ta samu ta fice, wajan da suke zaune ta koma ta zauna, ba jimawa Umar ya dawo, bayan ya zauna yake cewa, "Umma kun duba har yanzu bai tashi baccin ba?"
Jinjina kai Umma ta yi tare da cewa, "Na leƙa fiskanshi kamm, ban ga wani alama na ya farka ba, wataƙila sai zuwa anjima."
"Awanninsa uku fa yana nemann huɗu, Allah dai ya yayewa Sadeeq wannan cuta", Umar ya faɗa cikin yanayi na tausayawa abokin nashi.
Umma da, "Amin", ta amsa.
Sannan ta ɗaura da cewa, "Ya kamata ka ƙira mana Mamanku mu ji ya jikin Auta kuma, dan ni na mance tawa salular a gida."
Umar ba musu ya fidda tsararriyar wayarshi, sannann ya laluɓo layin Mama da yayi saving da WorldBest, ya aika ƙira, ringing biyu yayi ta ɗauka, ba tare da yayi magana ba ya miƙa wa Umma wayan, Umma ta amsa suka gaisa da Mama tare da tambayar jiki Sadiya, Mama ta jaddada mata da sauƙi an yi abinda aka saba yi idan haka ta faru, ga ta ma tana bacci, sannan Mama ta tambayi jikin mai babban suna, Umma ta shaida mata shi ɗin ma jiran tashinsa a bacci suke, fatan afuwa da sauƙi suka yi ga yaran nasu, sannan suka yi sallama, suna katse ƙiran sai Umma ta miƙa wa Umar wayarshi, ya amsa tare da maidata aljihu, Umma ta sauƙe numfashi tare da cewa, "Wannan lamari na Auta sai du'a'ee."
"Har da kuma rashin duka ke damunta Umma, kuma duk Sadeeq ne ya bata lasisi take yin waɗansu abubuwan", Umar ya faɗa cikin yanayi na nuna taƙaicin wasu abubuwan da Sadiya ke yi.
Ƴar murmushi Umma tayi tare da cewa, "Allah ya so Sadeeq ɗin bacci yake yi, amma da nasan ko yanzu ya farka to sai kun raba hali a kan haka, yanzu kam tunda za ku aurar da ita ai shikkenan magana ya ƙare, Haidar zai raba muku gardama."
Umar ƙwafa yayi kawai bai ce komai ba, amma a gefe guda fatan farkawan amininsa cikin aminci yake yi.
SADEEQ.
Slowly ya fara motsa gashin idanunshi, yayinda eyes balls nashi ke ɗan jujjuyawa.
Buɗe idanuwanshi yake son yi, amma baya son ya buɗe kuma bai yi tozali da kyakkyawar fiskarta ba kaman dai ɗazu, ga shi yanzun wani irin nauyi yake ji a ķirjinshi sosai-sosai, ji yake kaman dutsen dala aka ɗaura mishi, yana neman hana shi yin numfashi cikin salama.
Ƙasa-ƙasa ya motsa jajayen laɓɓansa masu sheƙi da burgewa, duk da sun ɗan bushe saboda rashin lafiya da yake yi, "ALHAMDULILLAHILLAZI AH-YANA BA'ADA MA AMATANA WA ILAIHIN-NUSHUR", ciki-ciki sosai yayi addu'an, ta yanda shi kaɗai ya ji abinshi.
Daga haka sai yayi shiru, matsakaitun ƙofofin dogon hancinshi yake buɗewa da kyau, ko zai shaƙi ƙamshinta kaman yanda ya saba a duk sanda ta shiga inda yake ko kusa da inda yake, amma sam-sam babu ƙamshinta da zai mishi nuni da tana waje, sai disashen ƙamshin da ke tabbatar mishi da ta wanzu a wajen kamun wannan lokacin, da classic voice nashi ya furta sunanta, "Sa'adiyahhhhh", ya ƙarishe ƙiran sunan nata a fili yana kuma furzar da iska mai zafi, saboda nauyin da ƙirjinshi ya mishi.
Shiru yayi na wasu ƴan mintuna bayan ya ƙira sunanta, sai can ya soma ƙoƙarin tashuwa zaune duk da idanuwanshi har sannan bai buɗe su ba.
***
Umma suna zaune da Umar suna hira jefi-jefi game da maganan likita, Umar ɗago kaurarran hannunshi yayi, wanda ke maƙale da tsadaddiyar agogonshi ƙirar apple, irin agogon da ake connecting nashi da waya ake operating na waya da shi, har WhatsApp har call.
Umar yana ganin lokaci ya ɗan ɓata fiska, a taƙaice ya ce, "Umma har la'asar fa ta kusa, bari na dubo Sadeeq ɗin nan, yanzu awa biyar ake nema, kar ya farka muna nan bamu sani ba."
"To dubo shi Umar, Allah ya sa ya tashi", Umma ta faɗa tana gyara zamanta.
"Amin Umma", faɗin Sadeeq tare da miƙewa ya nufi ɗakin da Sadeeq ke kwannce, da sallama ya murɗa handle na ƙofan ya shiga, sai da ya maida ƙofan ya kulle sannan ya lura da kyakkyawar ganin da maganenshi ke gane mishi, ai da sauri ya ƙarasa bakin gadon, tare da sanya hannayenshi duka ya tallafo Sadeeq, sai da ya jinginar mishi da pillow ya kuma ɗan ɗaga gadon da abinda ake murɗawa ta ƙasa, yanda matun zai ɗan yi resting da kyau ya huce kwanciya ko zama, sai ya jingina Sadeeq yana faɗin, "Sorry bros."
Sadeeq idanuwanshi a lumshe ya gyara kishingiɗar shi yanda zai zamana comfortable gare shi, sanna ya jinjina kai wa Umar na sorryn da ya mishi.
Umar ya san haka kawai ma ba amsa sorryn Sadeeq zai yi ba, balle kuma da bai da lafiya, sam Sadeeq baya ƙaunar kalmar sorry, ko da kuwa laifi aka mishi.
"Let me call Dr", Umar ya faɗa idanuwanshi na a kan Sadeeq.
Jinjina kai Sadeeq ya kuma yi, sannan Umar ya juya a hanzarce cikin takun sassarfa ya fice a ɗakin, daga annurin da ke a fiskarshi to ka san yana cikin farin ciki, yana isowa wajann Umma ta buɗi baki da niyan magana kenan, sai ya dakatar da ita ta hanyar taran numfashinta ya ce, "Umma ku shiga ciki ya farka, bari na kira likita."
Da sauri Umma ta miƙe bata jira Umar ya ƙarishe magana ba, ɗakin ta nufa har tana harɗewa saboda sauri, Umar kuma ya wuce office na likitan, ya samu akwai mutum a ciki, sai da ya ɗan jira wanda ke ciki ya fita, sannan ya shiga bayan an bashi izini, yana shiga ya sanar da likitan farkawan Sadeeq, tare suka fito da likitan suka nufo ɗakin da Sadeeq yake.
Umma tana sallama ta shiga ɗakin, kai tsaye ta nufi waja Sadeeq tana faɗin, "Alhamdulillah! Ma sha Allah! Mun gode wa Allah, sannu Sadeeq."
Sadeeq idanuwanshi har lokacin a lumshe ya jinjina kai, Umma sannu ta cigaba da jero mishi tana jin kaman ta maida shi ciki saboda farin ciki, cewa tayi, "Akwai abinda kake buƙata ne Sadeeq?"
"Umma Ina Sa'adiyah?", muryanshi ƙasa-ƙasa, cikin kamewa da aji yayi maganar, idan ka kasa kunne ka saurari taushi da haɗuwar muryar, kai ka ce ba ta mara lafiya ba ne.
Umma da ta riga ta san halin ɗan ta da yanayinshi da yanayin maganarshi, daga motsawan laɓɓanshi ta fahimci abinda ya ce, tana ƴar murmushi ta ce, "Auta bata jima da komawa gida ba ai Sadeeq."
Numfashi Sadeeq ya ja tare da sauƙewa, yana ɗan ƙara runtse idanuwanshi, saboda ƙirjinshi da ya ɗan kama mishi, Sadiya yake son fara tozali da kyakkyawar fiskarta mai gusar mishi da cuta da damuwa, yayi kewanta over, ji yake kaman ya shekara one five bai sanyata a idanuwanshi ba, dan ji yake kaman ya jima ya kwashe kwana da kwanaki yana bacci.
Shiru ya yi na ƴan wasu mintuna, sai can wani tunani ya faɗo mishi, abinda Umma ta faɗa ya maimaita a zuciyarshi, «Auta bata jima da komawa gida ba», doest that means she have came to the hospital? Is she really fine? What about her problem with hospital?, yayi wa kanshi wannan tambaya a zuciyarshi, ya buɗe baki zai yi magana sai shigowan Umar da likita ya dakatar da maganar shi, duk ƙarasowa suka yi wajan gadon da yake, likita ƙoƙarin yake ya gyara mishi kishingiɗan kamun ya duba shi, Umar ya taimakawa likitan, sannan likitan ya ce, "Za ku iya fita, idan na kammala duba shi sai ku shigo."
Umma juyawa ta yi dan ficewa, Umar ma ya juya zai mara mata baya sai ya ji an riƙe hannunshi, wanda baya da ko haufi Sadeeq ne, a nitse ya juya tare da zubawa haɗaɗɗiyar fiskar Sadeeq ido, wanda har yanzu idanuwanshi suke a lumshe.
"Hope she's doing good?" Sadeeq yayi tambayan a taƙaice, kuma muryanshi ciki-ciki hallau dai kaman an mishi dole ne ko kuwa farilla ne tambayan.
Umar sarai ya ji tambayan Sadeeq kuma ya gane abinda yake nufi, tsuke fiska yayi tare da ƙwace hannunshi ya juya zai tafi.
Sadeeq jin Umar ya ƙwace hannunshi, sai ya buɗe manyan haɗaɗɗun mayun idanuwanshi, Umar ya bi da kallo cikin sigar gajiya da kuma ciwon da yake ciki, a sanyaye ya ƙira shi, "Bro!"
Umar jin yanda Sadeeq ya ɗan ɗaga murya kuma ya yi ƙiran da tabbas ya san da shi yake yi, juyowa yayi tare da sake tsuke fiskan nashi, duk da kallon da Sadeeq ke mishi da mayun idanuwanshi, bai hana shi aika mishi da nashi kallon ba, na ka ji da kanka tukunna, ka damu da lafiyarka ba ta shiritacciyar yarinyar nan ba da ka gama sakaltawa.
Wani irin miskilin haɗaɗɗen guntun murmushi Sadeeq ya saki na iya fatar baki kuma da gafen baki, domin ya fahimci kallon da Umar ke mishi duk da kuma idanuwan nashi dishi-dishi suke dan dauriya ya sanya shi buɗe su da jarumta, amma ya fahimci kallon tun da wannan sababben abu ne tsakaninsu, wato magana da ido, duk yanda ɗaya zai motsa idonsa to ɗaya zai fahimci nufin ɗayan, sun san kansu sosai fiye da tunani, ko iyayensu basu gane musu yanda suka gane wa junansu ba, wani irin amminta da shaƙuwa ne tsakanin Umar da Sadeeq.
Umar sake tamke fiska yayi ya juya ya fice, shi ya rasa irin shiga ran Sadeeq da Sadiya ta yi, ko shi da suke uwa ɗaya uba ɗaya da ita bai damu da ita da lamarnta kaman yanda Sadeeq ya damu ba, Sadeeq ko a gargaren mutuwa yake to fa ta Sadiya yake ba ta kanshi ba balle wani, domin ba zai taɓa mance wani tsautsayin hatsari da ya kusa faruwa Sadiya ba, lokacin tana ƙarama tana zuwa school da rashin jin ta, mota ce ta kusa bige ta, amma Sadeeq cikin hanzari da azama da jarumta ya samu ya kawar da Sadiya ga motan, shi kuma motar ta buge shi, abubuwa da dama dai na sadaukarwan Sadeeq ga Sadiya.
Sadeeq da gajiyayyun jinyayyun idanuwanshi ya bi Umar da kallo har ya fice, sannan ya mai da haɗaɗɗun mayun idanuwanshi ya lumshe a ranshi yana addu'an Allah yasa tana a halin lafiya fiye da shi.
***
MASU BUƘATAR A TALLATA MUSU HAJARSU, ZA KU IYA TUNTUƁAN WANNAN LAMBA.
09161720046
Za ku iya samun littafin a waɗannan manhajoji.
BAKANDAMIYA HIKAYA.
AREWABOOKS.
@Uwarbatoorl96
WHATSAPP
09161720046
a kan Naira #500.
Idan littafi ya zama completel 1k yake in sha Allah.
# Hareeyh
# 09161720046
# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚
[07/12/2025, 13:34] Uwar Batoorl✍️❤️🥰: 💔NAUYIN BAKI....👄💔
Na
Uwar Batoorl.
𝗕𝗜𝗦𝗠𝗜𝗟𝗟𝗔𝗛𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗠𝗔𝗡𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗘𝗘𝗠
اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤🤍
🅿️ 26 _ 30
⭐️
Duk abinda ya wakana tsakanin Umar da Sadeeq, a ƴan mintuna suka yi shi, kuma likita na kan aikin shi na dudduba Sadeeq.
Likitan ƙara sanya abin gwajinshi yayi Sphygmomanometer(abun gwada hawa ko sauƙan jinin mara lafiya) cuff ɗin ya soma ɗaura wa Sadeeq a lafiyayyen murɗaɗɗen dantsenshi, sannan ya maƙala Stethoscope a kunneshi, ya sanya Gauge ya matsa Valve, sai da ya matsa iska yanda ake matsawa, sanan ya sake Valve ɗin har ya gama reading, ƴan rubuce-rubuce yayi, yana kammala wannan ya kuma maƙala Stethoscope a ƙirjin Sadeeq ɓangaren zuciyarshi, nan ma ƴan rubuce-rubuce yayi, kana ya cire abin a kunnenshi ya rataya a wuyanshi, murya a tausashe cike da kulawa ga patient nashi kaman yanda likitoci ke yi ga marassa lafiyansu, cewa yayi, "Sir bayan ƙirjinka akwai wani abu da ke maka ciwo?"
Sadeeq idanuwanshi a lumshe ya ɗaga hannunshi tare da yin nuni da kanshi, alaman kan shi ma yana mishi ciwo.
Likitan sake ƴan rubuce-rubucenshi yayi, sannan ya kuma cewa, "Amma ƙirjin ya yake maka."
Sadeeq cikin rashin son magana ya buɗe tausasan laɓɓunsa, a taƙaice ya ce, "It hurts me soo much."
Jinjina kai likitan yayi, ya kuma yin rubuta tare da cewa, "iya zafi yake maka?"
Sadeeq ciki-ciki ya ɗan ja guntun tsaki, bayason yawan magana balle yawan tambaya, he hate's attending to doctor's and lawyer's, saboda silly question's nasu, mutane ne they'll keep on asking thesame question's in different way's, what's the difference between the first, second and the third question in ba son sa mutane yawan magana ba? A zuciyarshi yake wannan mita.
Likitan sake maimaita tambayan yayi jin Sadeeq yayi shiru, sannan ya ɗaura da cewa, "Ko da kuwa mun gwada ka mun ga wani abinda ke damunka, amma yana da kyau mu ji bayani daga bakinka muddin za ka iya bayanin, dan asan action da za a ɗauka", liktan ya ƙarishe maganan yana ƙoƙarin duba magun-gunan da ɗazu ya sa aka sayo.
Sadeeq murya cike da gajiya da magana ya ce, "Yana mini zafi sosai, inajin nauyi sosai and inajin ciwo."
Likitan sake rubuce-rubucenshi yayi, sannan ya miƙe da file ɗin a hannunshi, yana kallon ruwan da ya maƙala wa Sadeeq wanda ya kusa ƙarewa yake faɗin, "Sir akwai abinda kake riƙe da shi a zuciyarka, yake damunka ko kuma kake so, mun yi magana da relative's naka, so you have to say your mind, let them know what's in you, may be they can provide it or they can help."
Sadeeq a zuciyarshi wani irin faɗuwa gabanshi yayi da ya tuna wani abu, wanda shi ne dalilin faɗuwarshi ma, ƙirjinshi ne ya ɗan kama, ƙasa-ƙasa ya ɗan ɓata fiska tare da sake runtse ido, ciki-ciki ya furta, "Achhhh!".
Likitan da sauri ya ce, "Wani abun ne?" Saboda ya ga yanda Sadeeq yayi reacting alaman alwai abinda ya motsa mishi.
Sadeeq girgiza kai yayi, murya ba amo cike da ciwon da yake ji ya ce, "I want to ease my self."
Likitan ya gane nufin Sadeeq saboda motsa hannunshi da yayi mai saƙale da drip, sannann yayi maganar, ba ɓata lokaci likitan ya cire mishi ruwan, sannan ya mishi fatan samun sauƙi ya juya ya fice, a bakin ƙofan ya samu Umma da Umar, sanar da su yayi za su iya shiga ba damuwa, amma idan yayi Umar ya zo office ya same shi, daga haka ya wuce abinshi, wata nurse ce ta amshi file na hannunshi da sauran abubuwan cikin girmamawa, sannan ta rufa mishi baya har office nashi, sai da ta aje mishi file ɗin da komai a kan table sannan ta juya ta fice, shi kuma ya zauna tare da cire Stethoscope da ke maƙale a wuyanshi.
Sadeeq sai da ya ji fitan likitan, sannan ya sanya hannunshi na dama a gefen saitin zuciyarshi, a fili ya ce, "You mentioned both Dr, what's in my mind aches me and i loved it, but i don't have any option..."
"Sadeeq ƙirjin ne? Ko a ƙira likitan ne?", maganan Umma ya katse wa Sadeeq nashi, cikin damuwa da kulawa ta yi maganan, saboda ta ga yanda ya dafe saitin zuciyarshi.
Sadeeq a kame ya wara haɗaɗɗun mayun kyawawan idanuwanshi, kallo guda ya yiwa Umma sannann ya janye idanuwanshi a kanta cikin son ɓoye ciwon da yake ji, idanuwanshi ya mayar ga Umar wanda yake tsaye daga gefen Umma shi ɗin ma ya zuba mishi idanuwa.
Umma cikin damuwa ta ce, "Umar ko za ka ƙira likitan?"
"No Umma, am okay", Sadeeq ya faɗa tare da lumshe idanuwanshi.
Umar yana ganin aminin nashi ya mai da idanuwanshi ya lumshe sai ya dubi Umma ya ce, "Umma bari na je naji ƙiran likitan."
"To Umar, daga nan ka sanar mishi kaman ƙirjin Sadeeq ɗin na damunshi", faɗin Umma.
Umar juyawa yayi ya fice yana faɗin, "In sha Allah Umma."
"Allahu ya muku albarka", Umma ta faɗa tana zama a plastic chair da ke a gaban gadon, ba jimawa ta miƙe ta ɗau ledan pure water ta fice ɗan ɗauro alwala saboda la'asar an ƙira har an shiga, tana dawowa daga alwalan ta shimfiɗa darduma ta tada sallah.
Umar ko da ya je office na likitan, bayani likitan ya kuma yiwa Umar, akan lallai-lallai su binciki patient nashi, amma akwai abinda ke a zuciyarshi, tun kamun ciwon ƙirjin nashi yayi tsamari ya kai matakin da ba a so, tun kamun bugun ƙirjinsa ya buga mafi muni da hatsari da kan iya kawo ƙarshen rayuwarshi, to su tabbata sun shawo kan abun sun yi abinda ya kamata.
Umar ya jaddada wa likita in sha Allah za su yi abinda ya kamata da yardan Allah, za su shawo kan koma wace matsala ce, sannan likitan ya miƙa mishi ƴar pepper ya ɗaura da cewa, "A sayo waɗannan, idan ya samu ya zaga toilet ya dawo, sai a bashi abu ya sanya a cikinshi, sannan a haɗa da sauran magun-gunan da wannan duk a bashi, duk akwai prescription nasu a jiki."
"Okay Doctor, mun gode sosai", Umar ya faɗa yana miƙewa daga zaunen da yake.
Murmushi likitan yayi tare da cewa, "It's my pleasure."
Jinjina kai alaman yabawa Umar yayi, sannan ya juya ya fice a office ɗin, sai da ya saya maganin sannan ya koma wajan su Sadeeq ɗin, yana shiga ya samu Umma na sallah, Sadeeq kuwa na a kwance yanda ya bar shi, fiskanshi na fiskantar saman pop na ɗakin, amma idanuwanshi a lumshe, sai dai daga yanda ƙwayan idanuwanshi ke juyawa za ka gane idon shi biyu, dan lallai idanuwanshi biyu kawai ya lumshe idon ne, kuma yana jin motsin Umma duk har ta tada sallah, har shigowan Umar, sai da Umar ya tsaya a gefen shi, sannan ya buɗe gajiyayyun idanuwanshi, da ido yayi wa Umar alama da zai zaga, ba ɓata lokaci Umar ya aje abinda ke a hannunshi ya matsa jikin gadon, taimakawa Sadeeq yayi ya tashi ya zauna, sai da ya ɗan ja iska na sekonni sannan Umar ya taimaka mishi ya tashi tsaye, Ingarman Namiji!! ashe duk yanda wancan frame ya nuna suffan Sadeeq da surarshi to ya wuce haka, duk yanda ake hangenshi daga kwance ma ya wuce haka, Sadeeq dirarren namiji ne kuma tsayayayye jarumi ingarma.
Sadeeq bai cika tsayi zololo kaman falwaya ba, amma yana da tsayinshi dai-dai, jikinshi a kakkame a mummurɗe irin ta jarumai majiya ƙarfi ma'abota motsa jiki, irinshi ne in suka kasance cikin sojoji to kallo guda zai wa ɗan ta'adda ya sanya shi tsurewa ya shiga taitayinsa, dan yasan lallai da maza yayi ido huɗu.
Wata iriyar kamalalliyar fiska mai cike da ƙwarjini da haiba da kamala yake da, kamalalliyar fiska
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 32