Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tare da saurin tashuwa zaune ta ce, "A a Zahra, Haidar bai fi Yaya Sadeeq komai ba, kawai Yaya Sadeeq ya cancanci auren wacce ta fi ni komai ne." "Uhmn", iya haka kawai Zahra ta ce ba tare da ta ja maganar ba, ta fice a photon Yaya Sadeeq ɗin, tare da cewa, "Ki kiyaye dai wallahi, ya zama karo na ƙarshe kamun ma a ɗaura aurenki, kar ki bari ma ya kai bayan ɗaura aurenki, muddin da Haidar aka ɗaura, idan kika sake wannan kuskuren ƙura wa hoton Yaya Sadeeq ido, kina masa kallon da ya fice a musulunci, to wallahi ke da Allah, zunubi kuwa buhu-buhu za a rubuta miki, tunda duk kace nacenki, baki isa ki sauya cewa shi ba muharraminki ba ne." Sadiya numfashi ta sauƙe tare da ƙura wa Zahra ido, can kuma ta ce, "Zahra kinsan Haidar na fushi da ni? Rabona da magana da shi tun kamun a kawo lefe, ba ƙira ba saƙo, Zahra ya kyauta mini kuwa? Ya fa san hakan na iya yin sanadin numfashi na." Zahra dai ita ma zuba wa Sadiya idanuwa ta yi, a zuciyarta mamaki take yi, na abubuwan da Sadiya ke yi ka rasa alƙiblarta ka rasa gane ina ta dosa, a fili kuma ta ce, "Sadiya ki kama abu ɗaya dan Allah, mace fa ba ta auren maza biyu, ki nitsar da zuciyarki a kan mutum ɗaya sai damuwa ta miki sauƙi, na san kina cikin jarabawa amma wallahi wani abun har da laifinki ke kika ɗaura wa zuciyarki wata damuwar, ni wallahi har kin fara ba ni haushi." "Zahra zuciyata na ga Haidar, shi ne damuwata, Zahra ba ya ƙirana ba ya ɗaukan ƙirana." "To maganar Yaya Sadeeq da kallon hotonsa fa?" "Ya wuce Zahra na ƙarshe ne ba zan sake ba, Haidar shi ne babban damuwata, a haka za a ɗaura mana aure ya na fushi da ni?", Sadiya ta ƙarishe maganar hawaye na cika idanuwanta, saboda abun da ke mintsinan zuciyarta. Zahra taɓe baki ta yi tare da cewa, "Gwanda ya wucen ai, kuma batun Haidar ki bar ɗaga hankalinki ki na damun kanki, asali masu suna Haidar da zuciyarsu, ki gode wa Allah da aka ɗau lokaci yana lallaɓaki, sannan ki gode wa Allah da kika ga irin zuciyarsa yanzu, dan zuwa gaba ki kiyaye ko ma menene, tunda kin san me kika masa, kuma dai irin wannan normal ne, a na yin irin haka sosai, wasu har a ɗaura auren su na fushi da juna, kai wasu har a watse sai an bar su, su kaɗai sannan komai ya wuce su mori amarcinsu, ke dai ki cire komai a zuciyarki dan wallahi damuwa ya na lalata jikin mace." Ajiyar zuciya Sadiya ta sauƙe tare da jinjina kai, ta ce, "zan cire komai a zuciyata in sha Allah ƙawata, na gode sosai, kuma na yi wa Haidar uzuri." "Ya fi miki kam", Zahra ta faɗa tare da miƙewa ta wuce toilet, ta na jin tamkar ta shaƙo Haidar ya mutu ko za ta samu Yaya Sadeeq ya auri Sadiya dan sun fi dacewa, sai da tayi uzurinta ta fito sannan ta wuce ta yi addu'a ta kwanta ba ta sake bi ta kan Sadiya ba. Ita ma Sadiya banɗakin ta shiga ta yi uzurinta ta fito ta kwanta, amma dai tunanin ya ƙi bari ta runtsa, har dare ya raba, ta tashi ta ɗauro wani alwalan ta zo ta gabatar da nafila da addu'oi sannan ta kwanta, ba jimawa ɓarawon bacci ya yi gaba da ita. Washe-gari da suka tashi ya kama Alhamis, shirye-shiryen Nupe day suka tsunduma. **** Umar ko da ya rabu da Sadeeq ya wuce gida, kwantawa ya yi bacci, shi ne bai tashi ba sai da takwas ta gota sosai ana neman tara, da ya sauƙo gadonsa ya tarar da abun karyawa an jera masa a mini centre table nasa, ya san aikin Mama ne ba na kowa ba, sai ya murmusa tare da yiwa Allah godiya da irin mahaifiyar da ya azurtasu da ita.   Toilet ya wuce ya yi wanka ya fito ya shirya a gaggauce, shigar black suit trouser da army green long-sleeve ya yi, ya sha necktie da wristwatch nasa, ya sanya half cover shoe, bayan ya yi stocking da black belt na shi, kyau Umar ya yi sosai sai tashin ƙamshi yake yi, sannan ya je wajan sofan ya zauna ya jawo table na breakfast na shi ya karya a nitse, ya na kammalawa ya miƙe tare da ɗaukar duk abinda zai buƙata ya fice a ɗakin, sai da ya gaisa da Mama da sauran jama'a sannan ya fice, motarsa ya shige ya mata key ya nufi ma'aikatar su, bai tsaya bi ta kan gidan Abba ba, dan yana da tabbacin Sadeeq ya jima a office, tunda ya san seriousness irin na Sadeeq a kan aiki, ga aiki kamar agogo. Sai dai ko da ya isa ya yi mamakin da bai ga Sadeeq ba, daga ƙarshe ma da ya tambaya aka tabbatar masa Sadeeq bai shigo ba, kuma ya ƙira layin Sadeeq ɗin ta shiga ba a ɗauka, da ya yi ƙira uku kawai sai ya haƙura, ya bari a kan ko yana bacci ne, tunda jikin da saura, kawai ya mayar da hankalinsa kan aiki, har dai lokacin tashi ya yi, sannan ya koma gida lokacin su Sadiya su na program na su, bai bi ta kai ba ya shiga gidan wajan Sadeeq, sai Umma ke sanar masa ai ya yi tafiya, bayan sun gaisa sun ɗan taɓa hira da Umma ya mata sallama ya fito, ya na ƙoƙarin dialing layin Sadeeq sai ga saƙon shi ya shigo, bayan ya karanta kuma sai ga ƙira, ya ɗauka ba tare da ya tsaya yin sallama ba ya ce, "Yanzu ina ka tafi dan Allah, bayan ba ka gama warkewa ba?" Sadeeq a ɓangarensa murmushi ya yi mai sauti, sannan ya ce, "Assalamu alaikum." "Wa'alaikassalam, fatan ka na lafiya?", Umar ya amsa tare da sake aika masa da tambaya. "Lafiya lau har na fi ka lafiya, ka wani daina mini abu kamar yaro ƙarami mana." "To dama yanzu da nake shirin zama yayanka ai yaro kake a wajena, dan haka ka kula, fatan dai ba driving ka yi ba?" "Shi nayi ƙanin uba na." "Amma dai wallahi ka na son kasada da lafiyarka, ina laifin ka bi flight, to da Allah a dawowa ka bar motar a can ka biyo jirgi, zan zo na ɗauko ka a airport na Abujan." "Da kaina zan dawo ƙanin uba na." Sai sannan Umar ya yi ƴar dariya tare da cewa, "Ba ka yi da gatse ba ai, ko ka mance ni mai sunan ƙanin Abba ne?". "Au ashe haka fa, to Abba zan yi yadda ka ce." Duk dariya suka sanya Sadeeq da Umar ɗin,  sannan suka kama wani hiran a kan issuen da Sadeeq ya ce shi ya kai shi Adamawa, sun jima suna waya, sai da magrib ta yi sannan suka yi sallama, Umar ko da ya yi sallar magrib suna tare da su Abba a masallaci har isha'i, sannan suka fice Abba ya wuce gida, nan ma sai da Umar suka ɗan yi hira da su Khalid sannan suka shige gida, shi ma ya wuce gida, abubuwan da zai yi yayi sannan ya kwanta, cike da ƙudurin da yardar Allah gobe zai samu Haidar da maganar sun fasa ba shi auren Sadiya, ya yi haƙuri kawai. *** Za ku iya samun littafin a waɗannan manhajoji. ●BAKANDAMIYA HIKAYA. ●WATTPAD @Uwarbatoorl96 ●AREWABOOKS. @Uwarbatoorl96 ●WHATSAPP 09161720046 a kan Naira #500. Idan littafi ya zama completel 1k yake in sha Allah. # Hareeyh # 09161720046 # 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩 # 𝙇𝙞𝙠𝙚 & # 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚 [07/01, 11:14] Uwar Batoorl✍️❤️🥰: 💔NAUYIN BAKI....👄💔        Na Uwar Batoorl. 𝗕𝗜𝗦𝗠𝗜𝗟𝗟𝗔𝗛𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗠𝗔𝗡𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗘𝗘𝗠     اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤🤍 End of book1. Last free page. 🅿️ 49 _ 50 ⭐️ Umma ta na haurawa sama ɗakin Abba ta same shi har ya yi shirin kwanciya, sallamar da ta yi ya amsa yana ɗan sakin murmushi ya ce, "Umman amarya." Da murmushi Umma ta ƙarisa wajan Abba ta na faɗin, "Barka da hutawa uban amarya, rankashidaɗe mijin Halimatu." Jinjina kai Abba ya yi alamar ya amsa, sannan ya ɗaura da faɗin, "Wai yaronnan Abubakar ƙaura ya yi saboda maganar auta?" Murmushi Umma ta yi tare da cewa, "Abbansu ni ma ban sani ba gaskiya, duk da ba na tunanin maganarta ne, dan mun yi magana da shi bayan dawowarku masallaci, daga haka kuma duk bamu san da tafiyar ba, sai da Khausar ta ƙira shi sannan muke jin wai ya tafi Adamawa, kuma kamar lamarin aikinsu ne ya kai shi." "Shikkenan ai, Allah ya taimaka ya musu albarka duka, Allah ya kare shi ya dawo da shi lafiya, sai ya dawo za mu yi magana in sha Allah." Da, "Amin", Umma ta amsa, sannan suka cigaba da tattaunawa a kan batun Sadeeq.        ⭐️     SADIYA POV Ƙayataccen Nupe day suka yi, an sha kyau, an sha hotuna da videos, an sha bidiri, duk wani abu na al'adun yaren sun yi, Sadiya amarya ta sha kyau kamar a sace ta a gudu, ƙawaye sun daddafi busy. Washe-gari Juma'a aka gabatar da walima, inda aka gayyato fitacciyar malama ta zo ta gabatar da nasiha, jan hankali da shawarwari ga amarya da ma ɗaukacin mata, masu aure da marassa aure har ma zawarawa, sosai malamar ta yi nasiha mai ratsa zuciya da jiki, musamman akan yacce mutuwar aure ke yawaita, sai a rasa daga mazan ne ko matan ne, kuma ko ma daga waye ne, ana so dai mutum ya kiyaye haƙƙoƙin da ke a kansa, kabarin kowa daban, dan haka ba a tsammanin mace ko namiji wai ɗaya ya ce shi ma zai yi kaza tunda ɗayan na yi, kowa ya kiyaye kuma ya gyara tsakaninsa da ubangijinsa, lokaci ba ya jira, rayuwa gudu take, Allah ya datar da mu duniya da lahira, ya azurtamu da zaman lafiya da ta haƙuri, ya raya zuri'a ya albarkacesu, marassa aure daga zawarawa har budurwaye Allah ya kawo na gari, ya ba da haƙurin zama. An raba kyautuka na gani na faɗa a wajan walimar, yayyun amarya su ne suka ba da gudumawar kyautukan, Khalid da Sa'ad. Hidima ake da bidiri ba kama hannun yaro, kowa bai da burin da ya wuce, gobe ta yi cikin yardar Allah, a ɗaura aure a miƙa amarya gidanta a ƙarisa shagali. A ɓangaren amarya da ƙawayenta sai raha da zolayarta suke yi, kowa da abinda yake faɗa, tijara irin ta ƙawaye duk sai cika Sadiya suke yi da shi, ita kuwa baiwar Allah wunin ranar gaba ɗaya tun da aka gabatar da walima cikin sanyin jiki take, ta rasa me ke mata daɗi, Haidar har sannan bai neme ta a waya ba, illa iyaka saƙon da ya turo mata wanda ya tabbatar mata da lallai Yaya Umar ya masa maganarta da Yaya Sadeeq, hakan ba ƙaramin damunta ya yi ba, duk yadda ta so ta samu yin magana da shi ya hana ta wannan damar, saƙon da duk take tura masa ba alamar ya buɗe balle arziƙin reply, ƙira kuma ba ya shiga ma layinsa ko ta ƙira, ta rasa me ke mata daɗi, ko da ta yiwa Zahra maganar haƙuri ta bata kawai, dan ko ita ta rasa ya za suyi, dan da alama Haidar ya hau dokin fushi sosai, sun ƙirasa ta wayar Zahra ma bai ɗauka ba. Duniya ta yiwa Sadiya matuƙar zafi, har take lissafa ranakun shirye-shiryen bikinta, a cikin ranaku mafiya ciwo da ƙalubale a gare ta, gabas da yamma abubuwan ba sauƙi ba daɗi, har kowa ya yi bacci idanuwanta biyu ta kasa bacci, ga shi gobe ɗaurin aure amma Yaya Sadeeq ma bai dawo ba, ya na lafiya? Ya jikinsa? Da sauransu kaf yawo suke a kanta, zai samu zuwa bikin ma balle walicci, Yaya Umar da yayi shiru ya zuba mata idanuwa shi da Mama sun haƙura ne ko kuwa akwai abinda suke shiryawa? Waɗannan tambayoyi da suka mata caa a ka da zuciya ya sanya ta tashi ta ɗauro alwala kawai, ko da ta fito banɗaki, salla ta gabatar har dare ya raba, sai can wajajen asuba, ɓarawon bacci ya yi gaba da ita. *** Kansancewar ana ida sallan Azahar za a ɗaura auren, tun kamun a ƙira salla Salma ta cancarawa mini ƙayataccen kwalliya mai muminin kyau, na haɗe cikin leshi ruwan sararin samaniya, wanda ya sha ɗinkin riga half gown da straight skirt, manyan duwatsun da aka yi adon leshin da su jefi-jefi, ba ƙaramin sake ƙawata leshin suka yi da ɗinkin ba,  tamkar matashiyar ɗawisu haka na fito saboda haɗuwa da kyau. Hira da dariya muke yi da ƙawayena, suna tsokanata, wai yanzu kam na girma na fita sahun ƴammata na koma sahun matan aure. "Muna nan muna jiran Al-Sad ɗin ya ƙira ya shaida miki an ɗaura", faɗin su Nussy ƙawaye, da su ma suke a shirye, so suke su yi mini video wai idan ina waya da Haidar ɗin. Daga cikin ɗakin da muke muka fara jiyo hayaniya-hayaniya a cikin gida, a maimakon sanarwar an ɗaura aure sai salati da koke-koken wasu jama'a, hakan ya sanya ƙawayena kaf suka miƙe dan ficewa su jiyo me ke faruwa, ni ma da nake zaune zuciyata na mugun bugawa, gabana na faɗuwa tamkar numfashina zai yanke, ganin shiru ba wacce ta dawo ɗakin a cikinsu, ga tsanantar hayaniyar fiye da ɗazu, sai na miƙe da sauri dan na fice na gano wa kaina abinda ke faruwa, saboda na cika da tsoro da kuma fargaba, gidan aure da ya kamata ya cika da shewa da guɗa, ya na ƙoƙarin komawa gidan makokin da ba ma fata, hakan ya sanya na fita na fara tambayar me ke faruwa, amma ba wanda ya ba ni amsa saboda kusan dukka jama'ar kuka suke, wasu kuma salati suke yi, hakan ya sake birkita ni na kiɗime, mayafin da nake rufe da shi ma sake shi nayi ya faɗi, ban tsaya bi ta kan shi ba kai tsaye na nufi wajan da na hangi a Mama zaune ta na kuka, ga jama'a ana bata haƙuri, cikin damuwa da muryar da ke nuni da ina gaf da fashewa da kuka na ce, "Mama menene? Me ke faruwa?", na faɗa ina durƙushe a gabanta, hannayena a saman guiwanta. Mama cikin kuka ta ce, "Sadiya mun rasa mai babban suna, Babana ya tafi ya barmu, Sadiya Yayanki Sadeeq ya rasu." Wani irin zaro idanuwana na yi, cikin rashin fahimta da gasƙata abinda Mama ta faɗa, na miƙe tsaye na juya da nufin dubo Umma, a cikin cunkosan jama'ar da firgici ya sa na kasa shaida su balle banbance su, domin na san ko da Mama za ta ce Yaya Sadeeq ya rasu saboda ba ɗanta ba ne, ai Umma ta san zafin shi, ita ta haife shi ba za ta faɗa hakan ba, sai dai ban yi taku uku cikakku ba, wasu jama'a suka shigo cicciɓe da mutum a cikin taburma a naɗe, cikin mutanen har da Sa'ad, Khalid da Abba da Yaya Umar, kana ganin idanuwansu ka san suna cikin damuwa da alhini,  Khalid da Sa'ad hawaye ma suke yi, Umar kuma jijiyoyin kansa sun yi mugun tashuwa, Abba ba a magana, domin tashin hankali ne da dammuwa kwance ƙarara a kan fiskarsa. "Jama'a ku gyara a ajiye gawan", wani bawan Allah ya faɗa hakan cikin waɗanda suka cicciɓo gawar. "Abubakar Sadeeq mutumin kirki ne, addu'a yake buƙata ba kuka ba, halinsa na gari ya bi shi", wani mutumin ya kuma faɗan haka. Idanuwana a kan su har suka shumfiɗe mutumin da suka shigo da shi cikin taburma a ƙasa, a mugun haukace na yi wajan dan a ganina ƙarya kawai ake yi, kawai an yi wa Yaya Sadeeqna haka ne don ba'a son shi, in ba haka ba ya za'a yi a ce ya mutu.     Ina isa kan gawan kamun na tsugunna, Yaya Umar ya sha gabana, ba tare da na ankara ba sai jin sauƙar gigitattun maruka na yi hagu da dama, bai jira na gama dawowa hayyacina ba, ya nuna ni da yatsa, cikin yanayin da ke nuni da baƙin ciki da damuwa gami da tsanata da yake yi, ya ce, "Ke ce kika kashe shi, ke ce silar mutuwarsa, ke ce ajalinsa, me za kiyi kuma a kan gawarsa? burinki ya gama cika kin auri wanda kike so, shi kuma da ba kya so kin zama sanadiyar mutuwarsa, Sadiya babu mu babu ke, ki je ga ki ga duniya ga Haidar, tunda kika zama sanadin na rasa Aminina to a wajanmu ke ma matacciya ce." Mama cikin kuka ta taso daga inda take zaune ta nufo mu, ta na isowa bata yi wata-wata ba ita ma ta kwashe ni da mari, ta kuma rufeni da duka, sannan ta ce, "Na yafe ki Sadiya, na yafe wa Aliyu ke, ke ce sanadin rasa mutum mai karamci da mutunci irin babana, ki je ki zauna da wanda kika zaɓa, domin baki zaɓemu ba kuma ba ki ɗauke mu a komai ba, da kin ɗauke mu a komai, to tabbas za ki ji shawarar mu ki auri wanda muka so ki aura, amma tunda kika bijire har haka ta faru, ki je ga ki ga Aliyu nan, ba na son na sake kallon fiskar mai kama da ke balle ke Sadiya, ko mutuwa nayi ba na buƙatarki kan gawata", ƙarishe maganar Mama ta yi tare da yanke jiki ta faɗi. Ban samu damar magana ba, daga Yaya Umar har Mama ba wanda ya barni na ja numfashi da niyar yin magana, hakan ya sanya cikin tarin ciwon abinda nake ji a zuciyata, na buɗe baki da niyar sakin ƙara, amma ban kai ga yin ƙarar ba zafin wani abu da ya daki bakina ya katse ni, ko da na kai dubana sai kuɗaɗe na gani, ina ƙoƙarin ɗago kai na, sai kalaman Yaya Umar suka dirar mini a kunne, kalaman da ke nuni da shi ne ya jefe ni da kuɗin.   Ya na nuni da hanyar ficewa a palourn ya ce, "Ga ƙudin sadakinki nan, ki tattara naki ya naki, ki fice a gidannan, kar ki yi kuskuren zuwa kan gawar Aminina balle na uwar da ta yafe wa wanda kike so ke, kika sake kika waiwayo gidannan to ke ma gawarki za a fitar wallahi, ki je mun yafe ki matacciya kike a wajanmu daga yau." Kuka kawai na fashe da shi mai cin zuciya, ina ƙoƙarin durƙushewa a wajan, sai Yaya Umar ya yi saurin riƙo hannuna ya fara ja na ya nufi ƙofa dan fitar da ni a gidan, duk kukan da nake yi da ƙoƙarin turjewa kamar ba na yi, abinda ya daɗa tsorata ni da fitar da ni a birki, bai wuce ganin kowa da kowa na tsaye amma an rasa mai cetona, an rasa mai ba wa su Yaya Umar haƙuri, an rasa mai saka baki a barni, na je ga Yaya Sadeeqna da ake masa kallon ya mutu, an rasa mai taimaka mini na je kan mahaifiyata da ta faɗi ban san a mace take ko a raye ba, su Abba su aunty Kulu kowa ma ba wanda ya ce komai, Umma ta na durƙushe gaban gawar da aka ce ta Yaya Sadeeq ne, ta na kuka ita da Aunty Khausar, ko ɗagowa su kalleni ba suyi ba balle su tausaya mini. "Wayyo Mama, Umma ku taimakeni, Abba, gwaggo na, auntyna, Yaya Umar ka yi haƙuri na tuba, ka ƙyaleni na yi magana da Yaya Sadeeq, Yaya Umar Mama kar ta tafi ta barmu, ka barni na yi magana da Mama ta yafe mini, wallahi na fasa auren Haidar, Yaya Sadeeq nake so, shi zan aura, na tuba zan auri wanda kuke so na aura, Yaya Umar kar Yaya Sadeeq ya mutu bai aureni ba wallahi ina son shi, na tsani Haidar, Yaya Umar zan mutu, zuciyata.....", sumbatu da kuka kawai nake yi, ta inda nake shiga ba ta nan nake fita ba, neman agaji da magiya ba kalan da ban yi ba, amma sai da Yaya Umar ya kai ni har ƙofar gida, sai sannan ya tsaya tare da ƙwaɗa mini wani mahaukacin mari, ya nuna ni da yatsa bai ce komai ba, yayi ƙwafa kawai ya hankaɗa ni ya tura ƙofar gidan ya rufe bayan ya shige.    Durƙusawa na yi a wajan ina dafe da kunci saboda azahar marin, don marin da Yaya Umar ya mini ya tafi da ji na da ganina na wasu daƙiƙu,ko da na ga ya garƙame ƙofar gidan, hakan ya sa cikin wani mahaukacin karaji na ɗaura hannuwana duka biyu a kai na, sannan na tsala wani irin razanannen ihu mai ratsa dodon kunne da gusar da ji na wasu daƙiƙu. *** "Sadiya, Sadiya, Sadiyaaaaa", Umma ta ƙira sunanta da ƙarfi ta na jijjigata. ⭐️ ALIYU HAIDAR POV    *** Hajiya ce a zaune ta tusa Alhaji a gaba, ta na masa bayani, shi kuma sauraranta yake da dukka na zomayensa, bai ce komai ba har sai da ta kammala bayaninta ta yi shiru dan kanta, sannan Alhaji ya muskuta tare da jan gauron numfashi ya ce, "Hajiya duk sai bayani kike yi, wanda sam ba na fahimta wallahi, na kasa gane me kike nufi." Hajiya ɓata fiska ta yi ba sosai ba, sannan ta ce, "Magana ta gaskiya kuma ta domin Allah, ka san me nake nufi Alhaji, ai ba tun yau ba nayi maka maganar." "In ma na sani to na mance", Alhaji ya faɗa murya ba amo, saboda ba son jan maganan yake yi ba, ba ya son abinda zai sa Hajiya ta dage sai ta takurawa Haidar, amma yana ganin alamar ta yi nisa kuma ta gama shirinta. Hajiya ba ta damu da yanayin amsar da Alhaji ya bata ba, ta ce, "Ai mai nema ba ya fushi Alhaji, ko me kai da ɗanka za ku ce it won't bother me, damuwata kawai a yi auren duka biyu lokaci ɗaya, tun sanda muka yi maganar lefe da kai na sanar maka, so nake ya auresu lokaci ɗaya, ko da bata tare ba to kawai dai a haɗa auren, yanzu ana satin biki, jiya har an kai lefen ita Sadiya, na san kuma ya gama sallamarta da kuɗaɗen hidindimun da za ta yi, amma mu nan ko sisi ba a bai wa Husna ba, hakan kuma bai kamata ba." Guntun murmushi Alhaji ya yi, sannan ya ce, "Idan ban yi ƙarya ba ai maganar lefe, ce mini kika yi, kin raba musu su biyu, duk da ba haka ya kamata ki yi ba amma na yi shiru ban ce miki komai ba, Hajiya bansan meyasa kike dagewa har haka ba, amma dai ina binku da fatan alkairi, ni ba ni zan bayar da kuɗin hidima ba, shi zai bayar da kansa, sai ki same shi ku yi magana, maganar lefe ce ke kaina dama, da an kai wa sadiya set uku yacce muka yi, to da yanzu ita ma ukun za a haɗo mata, amma tunda kin raba musu, shikkenan kuɗaɗena sun huta, Aliyu ya yi sauran hidimar matansa tunda shi zai zauna da su ba ni ba, maganar gida ma duka kin hutar da ni." "Amma ai Alhaji mun yi da kai za ka masa magana idan lokaci ya yi." "Lokacin ai ina nufin bayan bikinsa da Sadiya ne, amma tunda kin dage yanzu sai dai a haɗa sai ki masa magana da kanki, ni dai ina muku fatan alkairi duka, Rabbi ya ba da zaman lafiya da ta haƙuri ya haɗe kawunansu." "Amin Ya Rabbi", Hajiya ta amsa rai ba daɗi, domin ta san za su kai ruwa rana ne kawai da Haidar, tunda ita ba iya ɗaukar kuturun zuciyarsa za ta yi ba, abinda ya sa kenan ta ce Alhajin ya yi masa magana, tunda shi Alhaji ya na iyawa da zuciyar Haidar ɗin, amma tunda haka ne ba matsala ai ita ta haife shi ba shi ya haifeta ba, za ta san yadda za ta yi. Daga haka Alhaji ya ci gaba da aikin da yake yi a na'urarsa, Hajiya kuma ta tashi ta fice a ɗakin ta wuce nata ɗakin, ta na shiga wayarta na soma kukan neman agaji, kai tsaye inda ta ajiye sa a kan bedside drawer ta nufa, amsa ƙiran ta yi, tare da zaunawa a bakin gadon, ta kara wayar a kunnenta, ba ta ci wasu mintuna ba ta gama wayar, sai da ta tura wa matar da suka yi magana, kuɗin da ta buƙata, sannan Hajiya ta aje

Chapter 31 of 32