da aka ɗauko masu yin photo da kuma short video.
Bayan la'asar aka fara program ɗin wajajan ƙarfe huɗu.
Sadiya da ƙawayenta cikin burgewa da ɗaukar hankali suka shigo filin, abun sai ya ba da wani salo mai ban sha'awa, ga shi sai kashe musu hotuna ake yi, ana kuma ɗaukar video, ga wani rikitaccen kiɗa da ke tashi, mai sauti da shauƙi.
Bayan su Sadiya sun ƙarisa wajan zamansu da ƙawayenta, sai Henna artist suka shigo, waɗanda already Sadeeq ne ya yi mata booking na su, domin duk events ɗin, duk da Haidar ya ba da kuɗi da komai da za a yi hidima, amma wasu abubuwan Sadeeq ne ya ɗau nauyinsu.
Cikin nasu salon suka shigo da abubuwan aikinsu na lalle, kai tsaye kuma suka wuce wajan amarya da ƙawayenta, dama su huɗu ne Henna artist ɗin, sai mutum biyu suka wuce gefen amarya, sauran biyun kuma, guda ɗaya ta yi gefen ƙawaye uku da suke jere waje guda, ɗayar ma ta yi gefen saura ukun da suke jere waje guda.
Daga haka taro ya ɗau hanya, kiɗa na tashi su Khausar suka shigo da yaranta da sauran bataliya, Khausar da Najla da Nayla suka yi wajan amarya da ƙawayenta, inda ake cancara wa amarya jan Henna na gani na faɗa, su kuma ƙawayen da yake sun yi jan tun kamun a fara taron, sai ya zamana baƙi ake zana musu.
Ana yi wa amarya da ƙawayenta lalle, suna ganin takawar da duk waɗanda aka ƙira fili suke yi, ga spray na kuɗaɗe ana yi abun gwanin burgewa.
Cikin ƙanƙanin lokaci ƴammata biyun suka kammala wa amarya jan lalle, sai da suka bari ya yi wasu mintuna, sannan suka zana mata baƙi, ba ƙaramin kyau ƙunshin ya yiwa Sadiya ba, ga shi duk abinda ake yi, ana musu short video, dan masu ƙunshin ma da nasu mai musu video suka zo, dan live suke yin ɗaukar, gwanin burgewa sai likes da comments ake musu.
Bayan lallen amarya da ƙawayenta ya ɗan sha, haɗa hannayen nasu suka yi waje ɗaya, aka ɗauki hotuna kala kala, sannan video, sannan aka yi na ƙafafuwansu, sai kuma aka yi wa amarya nata ita kaɗai complete da kuma iya hannayenta, iya ƙafafuwanta, hotuna dai na gani na faɗa har suka shige fili ita da ƙawayenta, suka ɗan taka cikin burgewa da farinciki.
Wani irin henna party suka yi mai masifar haɗewa da aji, henna party ne mai matuƙar class da capacity, ayi wannan a yi wancan, ayi haka a yi haka har sai magrib sannan aka fara watsewa, amarya da ƙawayenta suka shige palourn Umma, kai tsaye upstairs suka wuce, a ɗakin da ke manne da na Umma, nan Sadiya ta musu jagora suka yi masauƙi, sai da suka yi sallan magrib, sannsn suka hau hira da shewa na yabon taron na su yanda ya haɗe, su Rukky sai zolayan Sadiya suke yi, ita kuwa sai murmushi, idan bai game ta ba kuma ta ba su amsa cikin nishaɗi, duk da a zuciyarta akwai maƙalallen damuwa, ta rashin ji daga Haidar da kuma ta Yaya Sadeeq, dan ba ta tunanin ta Yaya Umar, musamman da ta shiga hidimar yau.
Khausar ce ta turo ƙofar ɗakin da suke ciki, ta shigo da sallama, tare da cewa, "Ƙawayen amarya masu capacity ku fito ku ci tuwon Umma."
Amsa mata sallamar suka yi, Sadiya, Zahra, Hidaya da Safiyya suka amsa wa aunty Khausar batun abinci, Rukky da Salma da Nussy suka haɗa baki wajan cewa, "Bari mu dai mu kama hanya dare na yi."
Khausar cewa ta yi, "To ku shirya bayanin yiwa Umma, dan ba za ku tafi ba ku ci abinci ba", ta na gama faɗin haka ta fice.
Sadiya harara ta aika musu duka,sannan ta ce, "Nussy da Rukky idan kun tashi tafiya ku wuce Jos, ke kuma Salma ki fire sama ƙarshen tafiya kenan."
Zahra ta ɗaura da cewa, "Salma muna nan da ke a gidannan har ƙarfe tara dan ki ji, ku kuma ko ma menene sai kun ci abinci ku tafi, in za ku tashi mu fita ku ci ku samu ku tafi, ku tashi ku bar ɓata lokaci, dan ko ƙarfe sha biyu za ku kai sai kun ci abinci atou."
"Ƙyale su Zahra, su fi ruwa gudu", Sadiya ta faɗa ta na aika musu da harara, ta tashi ta fice ita da su Hidaya.
Su Rukky su na dariyan Sadiyar suka rufa musu baya duka, duk kusan a tare suka sauƙo a benen, kai tsaye tsakiyar palourn Umma suka nufa, inda abinci ke ajiye Khausar ta saka musu, sai da suka sake gaishe da Umma da ke ƙoƙarin shigewa kitchen, sannan duk suka zauna suka fara ci da bismilla, bayan sun kammala, suka yi wa Umma godiya, Nussy da Rukky suka yi musu sai da safe Zahra ta raka su suka tafi, bayan fitansu, Salma ta miƙe tare da marairaice fiska ta ce, "Amarya mai maganar sugar, ta Al-Sad a mini afuwa, kin san yau muka dawo Allah akwai uzurin da zan je na yi."
"Ba damuwa Salamatu darling, mu kwana lafiya, ki huta gajiya, ki gaishe da su Umma da gajiyar hanya, sai kin shigo goben", faɗin Sadiya ta na murmushi.
Amsawa Salma ta yi, ta yi wa sauran ma sai da safe sannan ta juya ta fice a palourn, a bakin ƙaramar ƙofar gidan ta shigowa suka haɗu da Zahra wacce ta dawo daga rakiyar su Nussy, Salma ƴar dariya ta yi ganin irin kallon da Zahra ke mata, ta na dariyar ta ce, "ƙawar amarya mu kwana lafiya."
"Kin rantse dai yanzu za ki tafi ko?"
"Allah ku mini afuwa, kun ga yau dawowarmu, hanyar nan ba daɗi ne da shi ba", Salma ta faɗa ta na marairaicewa.
Zahra ta ce, "Shikkenan ai, mu kwana lafiya ki huta gajiya, a gaishe da su Umma, sai goben."
Murmushi Salma ta yi, tare da cewa, "Amin Ya Rabbi, ƙawar amarya a huta gajiya", daga haka Salma ta fice ta nufi gidansu, ita kuma Zahra ta shigo ta wuce ciki, da sallama ta shiga palourn, su Sadiya suka tambayeta har ta dawo, kuma su Nussy sun samu machine, ta amsa musu, sannan Zahra da su Hidaya suka haura sama, suka wuce ɗakin da suka samu masauƙi, dan gabatar da sallar isha'i da aka yi tun suna cin abinci.
Bayan wucewan su Zahra ba jimawa Abba ya shigo, sannnu da shigowa su Sadiya suka masa, Sadiya sai duƙar da kai take yi.
Abba ƴar murmushi yayi bayan ya amsa musu, sannan ya ce, "Madalla da autar Abba amarya, Allah ya muku albarka ya sanya alkairi auta, Allah ya sa a kammala hidima lafiya."
Ciki-ciki Sadiya ta amsa da, "Amin Ya Rabbi."
Abba na murmushi ya haura sama, Khausar ta yi ƴar dariya ta ce, "Su small Mum manya amarya, ana kunyar Abba."
Umma ta ce, "To ƙanwar ta ki ce ta koma abokiyar wasanki Khausar?"
Khausar ƴar dariya ta yi, ta na ƙoƙarin yin magana, ƙira ya shigo wayarta, ganin layin mijinta ta ɗauka tare da barin palourn, ya rage Umma da Sadiya kawai.
Umma cikin raha ta ce, "Wai auta wannan duƙe-duƙen kan fa? Ko dai akwai wani abu ne na zo mu saka labule?"
Sadiya ajiyar zuciya ta sauƙe cikin sanyin jiki, ta sake duƙar da kanta, idanuwanta na cikowa da ƙwalla, wani iri take jin kanta, gaba ɗaya a tsarge take, ta na ganin laifin kanta ne sosai, kunyar su Umma ya damaimayeta, ta rasa me ke ɗawainiya da rayuwarta, ta rasa wani irin ƙaddara ce ke bibiyarta ta lamarin aurenta, Yaya Sadeeq ya cancanta ko ba dan kowa ba, balle kuma in za a ce saboda Umma da Abba, ga aunty Khausar da su Khalid, wannan shi ne tsaka mai wuya, mafi ƙololuwar girma da ta shiga a rayuwarta, ga zuciyarta da gangar jikinta sun kasa amsan Yaya Sadeeq, Haidar kawai suke gani, da shi suke burin rayuwa, ƙwaƙwalwarta kawai ke iya lissafa alkairan Yaya Sadeeq da lissafin kunyan iyayensu, hakan ba ƙaramin damunta yake ba...
"Auta", Umma ta ƙira sunanta cikin kulawa ta na dafa kafaɗarta, hakan ya sa zancen zucinta ya katse, ta ja dogon numfashi, a take kuma hawaye suka fara zubo mata, ashe har ta yi nisa a tunani ba ta ma san, cewa wai Umma har ta taso daga inda take zaune ta zauna a gefenta ba, hakan sai ya sake sanyaya jikinta.
Umma sauƙe ajiyar zuciya ta yi, sannan cikin kamalalliyar muryarta, a tsigar kulawa da rarrashi ta ce, "Autar Abba da Umma menene ya faru? Wa ya taɓa ki? Me aka miki? Ke da wa?", Umma ta jero matar tambayar cikin raha, a sigar da ta san dole Sadiya sai ta faɗa mata damuwarta.
Sadiya da take jin tamkar ta tura baki yadda ta saba, ta kuma ce ai Yayanta Sadeeq ne, amma sai ta kasa yin hakan, domin kunyar Umma da kunyar ambatan sunan ɗan ta, a matsayin damuwarta, ta san hakan ba zai yi wa Umma daɗi ba, dan su ɗin masu tarin alkairi ne da kuma kara.
"Auta yau ba za a sanar wa Umma wa ya taɓa mata shalelenta ba?"
Da sauri Sadiya ta girgiza kai, ta na ƙoƙarin mai da hawayenta, cikin rawar murya ta ce, "Ummata dan Allah ku yafe mini ku yi haƙuri."
Umma ta ce, "Auta me ya faru na neman yafiya kuma ni Halimatu? Me kika mana?"
Cikin sheshsheƙan kuka Sadiya ta ce, "Umn umn, dan Allah Umma ku fahimce ni, wallahi ba na nufin butulci, ba na nufin komai Umma, na faɗa wa Abba Yaya Sadeeq nake nufi", daga haka kawai Sadiya ta fashe da kuka mai sauti.
Umma jawo Sadiya jikinta ta yi, ta soma bubbuga bayanta alamar rarrashi, ta na kuma shafa bayanta, murya cike da ƙaunar Sadiya da tausayinta ta ce, "Ke ba butulu ba ce dama auta, ke ƴar adam ce, kuma ajiza, sannan duk wanda ya san mutum tara yake bai cika goma ba, to zai miki uzuri, dan haka ki kwantar da hankalinki auta, abinda duk kika ce shi kike so, da yardar Allah za mu miki shi, muddin muka hangi alkairi bayan mun miki addu'a, ki bar damun kanki auta, kina gani duk kin bi kin zabge, kamar ba ke ce kwanaki da kumarinki ba, dan Allah ki cire komai a ranki auta, ku yi hidimarku cikin nishaɗi, Allah ya muku albarka ya sa ku kammala komai lafiya, Allah ya kuma sanya alkairi da albarka."
Sadiya kukan ta cigaba da yi, amma ta rage sauti, a haka Umma ta ci gaba da bata baki, ta na rarrashinta har sautin kukan ya ragu, suna a haka sai ga Khausar ta dawo, Umma ta ce, "Maza zo ki rarrashi autata bari na je wajan Abbanku ya na ƙira."
Sadiya murya a dishe da kuka ta riƙe hannun Umma tare da cewa, "Ummata na gode, Allah ya saka muku da aljanna, Allah ya ji ƙan magabata."
"Amin autar Umma, Allah ya miki albarka ya ba ki zuri'a masu albarka", Umma ta faɗa da kyakkyawar murmushi ta na shafa kan Sadiya, sannan Sadiya ta sakar mata hannu, ta wuce ta haura stairs ta yi wajan Abba.
Khausar zama ta yi a gefen Sadiya, a wajan da Umma ta tashi, cikin kulawa ta ce, "Kukan me kuma small Mum ke yi, bayan kina daf da sake girma, ana miƙa wa uncle H ke, shikkenan you're not more auta kuma, sai dai mummy auta", cikin zolaya Khausar ta ƙarishe maganar.
Sadiya kwantar da kanta a kafaɗar Khausar ta yi, da disashsshiyar muryarta ta ce, "Aunty Khausar kowa haka yake fuskantar ƙaddara da damuwa, ya shiga tsaka mai wuya yayin da yake shirin yin aure?"
Murmushi Khausar ta yi, tare da cewa, "Fiye da haka ma small Mum ana shiga, a wajan wasu ma ai ke a rahama kike dumu-dumu ba ki da damuwar komai, ke ƴar gata ce ai, kin san kalar taskun da wasu suke fiskanta kamun a yi auren? Ke dai Allah ya sake rufa mana asiri kawai small Mum, amma dai ta ki mai sauƙi ce, wasu fa har auren ana iya fasawa, saboda wani mugun sharri ko wani abu na su na sirri da ake bayyanawa lokacin auren, wasu ga soyayya kamar za su kashe kan su, amma gwajin jini ya zame ya raba wannan soyyya ana raye ba a mutu ba, wasu kuma mutuwar ɗaya a cikinsu ke yi ana tsaka da hidima, abubuwa masu ciwo da taɓa rai da dama, wasu jinkiri auren ma ke musu, wasu kuma gaba ɗaya Allah bai rubuto su cikin masu yin aure ba, amma fa duk ƙaddara ce da jarabawa, duk wanda ya yi haƙuri ya rungumi ƙaddarar shi to zai ga sakamako mai kyau."
Sai da Khausar ta numfasa sannan ta ɗaura da cewa, "Small Mum, ke naki mai sauƙi ne, musamman da ya kasance kowa na son farincikinki, Yaya Sadeeq ya zaɓi ki yi farinciki ko da zai mutu, Umma da Abba sun zaɓi farincikinki ko da za su rasa nasu, haka ni da kowa ma, dan haka ki kwantar da hankalinki, komai da ya faru a ƙanƙanin lokaci, Allah ya rubuto zai faru ne tun asali, ki yi haƙuri ki mayar da hakan ba komai ba, ya wuce kamar ba a taɓa yi ba, na yi waya Yaya Sadeeq ya sanar mini komai ya wuce, yana so ki saki jiki ki yi hidimarki yadda ya kamata."
Sadiya kuka ta fara mara sauti amma mai taɓa zuciya, da muryar kuka ta ce, "Aunty Khausar wallahi ba na ƙin Yaya Sadeeq, aunty Khausar ina jin kunyar Yaya Sadeeq ina jin nauyinsa, aunty ba zan iya masa kallon miji ba, matsayi nake ba shi tamkar ta mahaifi ba iya babban Yaya ba."
"Ba wanda ya isa ma ya ce ba kya ƙaunar Yaya Sadeeq ai small Mum, an fahimceki an miki uzuri, Allah ya tabbatar da alkairi, shi kuma Yaya Sadeeq, Allah ya ba shi haƙuri da ikon riƙe matsayin da kika ba shi da kyau da amana, amma duk da haka ina kwaɓarki da maganar danganta Yaya Sadeeq da mahaifi."
Jinjina kai Sadiya ta yi alamar ta ji ta bari, sannan ta ce. "Aunty Khausar ku yafe ni, ki taya ni nemar yafiyar Umma da Abba da kuma ba su haƙuri."
Khausar share wa Sadiya hawaye ta yi, tare da girgiza kai ta ce, "Indai Abba da Umma na buƙatar haƙuri da neman yafiya daga gare ki, ashe su ba iyaye ba ne, dan haka ki kwantar da hankalinki ki kuma cire komai a zuciyarki small Mum, farincikinki shi ne burin Yaya Sadeeq, idan kina tauye wa kanki farinciki cutar da shi kike yi, gani yake ya gaza, sannan zai ga kamar mutuwa kawai kike so ya yi, sai ki yi farinciki."
Da sauri Sadiya ta girgiza kai, tare da share hawayenta, ta ƙaƙalo murmushin dole, ta ce, "Indai farincikina shi ne burin Yaya Sadeeq, to zan tabbata ina yi in sha Allah har ƙarshen rayuwata, ko ina cikin ciwo da ƙunci zan yi farinciki saboda Yaya Sadeeq na ya kasance cikin salama."
Murmushi Khausar ta yi a zahiri, wanda a zuciyarta kuma kuka ya fi sa ciwo, saboda tausayin Yaya Sadeeq har ma da ita Sadiyar, amma duk da haka ba za su yi ƙasa a guiwa ba, za su ci gaba da yin addu'a, Allah ya tabbatar da abinda yake mafi alkairi.
Rarrashi sosai da hira ta fahimta Khausar da Sadiya suka yi, har sai da Sadiya ta ji dama-dama a zuciyarta a zahiri, amma a baɗini lissafi ne tirim, musamman a kan mutuwar da ake yawaita ambatawa Yaya Sadeeq, sai abun ya maƙale a zuciyarta, ta na tunano condition da ya shiga a asibiti na unconsciousness, da kuma abubuwan za ranar Khausar ta faɗa mata, wannan tunani shi ke sake dulmiya Sadiya a duniyar damuwa, ko da kuwa ta yi tsalle dubu ne domin ta yunƙura ta fice, to ba ta iyawa.
Khausar ƙiranta aka kuma yi, ta tashi tare da yi wa Sadiya bari ta amsa ƙiran ta na zuwa, ta na barin wajan sai ga Sa'ad da Khalid sun shigo, sannu da shigowa ta musu, Sa'ad ya amsa ya na murmushin yaƙe, ƴar tsokana ɗaya biyu ya mata, sannan ya wuce ɗakinsa, saboda ita ma daga kallonta kuma da muryarta ya fahimci akwai damuwa a tattare da ita, kamar dai Yaya Sadeeq da yau sai tashi suka yi babu shi, kuma har sai yamma suke samun labarin tafiyar da ya yi, hakan ya sa Sa'ad yake tausaya musu duka tare da musu fatan alkairi.
Khalid ƙarasawa palourn ya yi, ya zauna a kujerar da ke kallon ta Sadiya ya ce, "Amaryar Aliyu ƙanwar Abubakar sai da ke, amarya mai capacity."
Sadiya ƴar murmushin yaƙe ta yi, tare da cewa, "Yaya Khalid ka ce ka na cikin ƙawaye, to ina taka lallen?"
Ƴar dariya Khalid ya yi tare da cewa, "Raba ni da jibgegiyar bala'i, idan na yi lalle ai gabas da yamma daga gidan Mama har na Umma, haka za a mayar da ni jakin Kano dan jibga, ko kuwa na ce sakwarar legas dan bugu."
Ƴar darya Sadiya ta yi, tare da cewa, "To babu kai a ƙawance kenan Yaya Khalid?."
"Na haƙura, yanzu ni Yayan amarya ne, amma fa maganar sallama musamman zan samu Haidar da ni za a sallami ƙawaye, za a ba ni rabona."
Murmushin yaƙe Sadiya ta yi, tare da miƙewa ta ce, "Gwanda kai Yaya Khalid ka yi salla, ni ban yi ba bari na je na yi."
"Ai amare idan suna hidimar biki ba sa salla, subscription suke yi."
"Banda Sadiya a wannan tsabga, sai da safe Yaya Khalid."
"To Allah ya tashe mu lafiya amarsu ta ango."
Sadiya ta na ƴar murmushi ta haura stairs, ta na haurawa kuma murmushin ya gushe, ji take kamar ta ƙwala ihu ko kowa zai fahimci halin da take ciki, rashin magana da Haidar tamkar rashin wadatacciyar numfashi ne a gare ta, Haidar bai taɓa mata haka ba, bata kuma san abu mai zafi da ta masa har ya ɗau wannan fushin ba, da shi za ta ji ko da lamarin Yaya Sadeeq da ya ƙi gusawa a tunaninta daidai da second ɗaya, hawaye ne suka silalowa Sadiya yayin da ta tura ƙofar ɗakin, a maimakon sallama sai cewa ta yi, "Ya Rabbi kada damuwa ta haukatani", ciki-ciki ta yi maganar, ba tare da ta bi ta kan su Hidaya da suke mata magana ba ta wuce toilet, ta bar su da baki sake suna tambayar ba'asin hawayenta, sai Zahra ne ta ce, "Wataƙila dai an fara mata nasiha ne tun yanzu, kar ku wani damu."
Jin abinda Zahra ta ce sai suka ƙyale maganar, suka ci gaba da danna wayoyinsu, Zahra ma danna nata take yi, inda ta yi posting wasu hotunansu aka cika ta da like da sharhi.
Sadiya ba ta san hawaye take yi ba sai da ta shige toilet, ta yi tozali da fiskarta a madubin gaban sink na alwala, hakan ya sa ta tsaya tare da fashewa da kuka mara sauti, sai da ta yi mai isarta ta na jera ajiyar zuciya, sannan ta ɗauro alwala ta fito, kai tsayeta wuce inda darduma ke shumfiɗe ta tayar da sallah, ta jima ta na addu'a sosai bayan ta idar, sannan ta shafa addu'ar, a kan darduman ta kwanta ba ta cewa su Zahra komai ba, ta laluɓi wayarta, saƙon Sadeeq ta sake karantawa fiye da sau shurin masaki, sannan ta shiga layin Haidar ta ƙura masa ido, daga nan ta laluɓo photon Haidar nata da yake mata murmushi cikin shauƙi, ya zo hira ne ta ke ce masa ya yi kyau ya tsaya ta masa photo, ya kuwa tsaya ya na murmushi tare da ce mata, «Murmushin da kike buƙatar gani a fiskar Al-Sad naki, za ki ta ganinsa har ƙarshen numfashi da yardar Allah, domin ke ce sanadi, mahaɗa kuma silar murmushin, ke ce nishaɗina sweet Al-Sad, zuciyata ba za ta iya yin fushi da ke ba har abada.»
Ƙasa-ƙasa kuma cikin rawar murya, Sadiya ta ce, "So soon haka Zakina, har ka fara fushi da ni, ka karya alƙawarin wadata ni da murmushinka, ina kewarka Al-Sad, zuciyar Sadiya ta na cike da begenka da ƙaunarka, ka na shirin kassara ruhin da ta dogara da soyayyarka, amma duk da haka ta kasa ganin laifinka, ƙaunarka sun makanta duk wata sassa ta Halimatu daga na jiki har na zuci, kai kawai suke kallo da soyayyarka."
Sai da Sadiya ta gama wannan sambatu, sannan ta fice a hoton Haidar ta na hawayen kewarshi, ta na son sake ƙiransa ko tura masa saƙo, amma ta na ƙoƙarin hana kanta, ta na son ta riƙe kanta ta kama kanta, ta koyi juriya da dauriya, hakan ya sa ta laluɓo photon Yaya Sadeeq, wanda ya haɗe cikin dalleliyar jamfa ruwan hoda, kan shi ba hula, kwantaccen gashin kansa mara yalwa a bayyane, a kwance ta sha gyara sai sheƙi take yi, dariya yake yi har kyawawan fararen haƙoranshi a bayyane, wani irin abu ke sukar zuciya da ganganar jikin Sadiya, kallon ƙur kallon da bata taɓa yi wa Yaya Sadeeq ba take yi ma hotonsa yau, haka kawai ta tsinci zuciyarta da murmusawa har kuma kan laɓɓanta da fiskarta, kyawun Yaya Sadeeq ya tafi da hankalinta da imaninta fiye da duk sanda ta gan shi a baya, Yaya Sadeeq ƙarshe ne, ƙure aji ne da misali shi ɗin.
Sadiya ba awa ta ɗauka a wannan yanayi ba, awanni ta ɗauka, photon Yaya Sadeeq da ya kasance abu na ƙarshe da ta laluɓo, ta ɓata lokaci a kan shi fiye da a numbern Haidar da text message na shi Yaya Sadeeq ɗin.
Hidaya da Safiyya sun gama komai har danna wayoyinsu, sun yi addu'a sun kwanta bacci, Zahra da ke ankare da su, sai da ta tabbatar baccinsu ya yi nisa, sannan ta lallaɓa ta sauƙa a gadon ta ƙarasa wajan Sadiya, ta na zuwa ta fisge wayar Sadiya, har za ta danna botton na kashewa sai idanuwanta suka sauƙa a kan photon Yaya Sadeeq da ya yi bala'in kyau, da ɗan mamaki da kuma kallon tuhuma da ta neman ba'asi ta bi Sadiya, sai da ta kuma kallon photon, sannan ta juya shi ga Sadiya da ke hawaye a kwance duk da fiskarta cike yake da murmushi, murya ƙasa-ƙasa Zahra ta ce, "Wannan fa?"
Sadiya share hawayenta ta yi, tare da dakatar da murmushin ta sauƙe ajiyar zuciya, murya a dishe ta ce, "Zahra ina kewar Yaya Sadeeq, ina kewar Haidar, duniyata ta ɗau caji ta ɗau zafi, Zahra ina jin kamar rayuwata ta zo ƙarshe na mutu na huta kawai, Zahra na haƙura da rayuwar har Haidar, Zahra ni kaɗai na san zafi da abinda nake ji a zuciya, kowa gani yake lamarina mai sauƙi ne, ƙaddarata da sauƙi wai, amma Zahra wallahil Azim ni kaɗai na san irin ciwon da nake ji a zuciya, ƙaddarata mai zafi ce a gare ni da duk wanda ya fahimcce ni, ni ɗin abar a tausayawa ce a zubar mata da hawaye, na gode wa Allah lamarin su Umma da sauƙi kaf na su, amma na san kara suke mini kawai, Mama da Yaya Umar a yanzu ba na ganin laifinsu, duk da ba lallai zuciyata ta ba da haɗin kai na yi abinda suke so kuma na jure ba, dan ta jima da mallakawa Haidar kanta, Zahra Yaya Sadeeq duniyata ne, shi ɗin komai ne a wajena, Zahra ina jin da ina da dama zan samawa Yaya Sadeeq matar da ta fi ni komai da komai, na kuma sanya musu soyayyar junansu fiye da yadda yake so na, Yaya Sadeeq ya fi ƙarfina Zahra, Yaya Sadeeq ya wuce ajina, aura masa ni ma cutar da shi kawai za a yi, Zahra Yaya Sadeeq ya wuce duk inda kike tunani, na san duk banda damar haka, amma na yi alƙawain sadaukar da tsayuwan dare na ga Yaya Sadeeq, zan masa addu'a zan kuma yi kamar shi kaɗai gare ni kuma na sani a duniya in sha Allah."
Zahra da kallon kin zare ko ba kya hayyacinki ta ke bin Sadiya da har sannan take kwance a darduman, cikin son dawo da ita hayyacinta ta ce, "Amma dai lafiyarki kike wannan magana a kan Yaya Sadeeq? Shi da kika zaɓi Haidar a kan shi, ai kinsan Haidar ya fi shi komai a nufinki, dan haka ki bar wani cewa ya fi ƙarfinki."
Girgiza kai Sadiya ta yi
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 30 Chapter of 32