Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels [07/12/2025, 13:34] Uwar Batoorl✍️❤️🥰: 💔NAUYIN BAKI....👄💔 Na Uwar Batoorl. Marubuciyar:- ƳAR SARKI CE MAFARKI NAH JAHILCI KO AL'ADA ƳAR KARUWA SHAAMEEƘH 𝗕𝗜𝗦𝗠𝗜𝗟𝗟𝗔𝗛𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗠𝗔𝗡𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗘𝗘𝗠 اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤🤍 Ina mai miƙa dubban godiya ga Allah maɗaukakin sarki da ya bani ikon fara rubuta wannan labari NAUYIN BAKI, ina addu'a da fatan Allah ya sa na kammala lafiya yanda na fara lafiya cikin aminci, duk wasu fitintinu da wasu abun ƙi Allah maɗaukakin Sarki yayi mana katangar ƙarfe da su, mu kammala cikin ikonsa da amincewansa da yardansa lafiya. Duk wasu kura-kurai da za su wanzu bisa kuskure Allah ya yafe mu gaba ɗaya ni mai rubutawa da ku masu karatu, Allah kuma ya bamu ikon kiyaye dai-dai ya haɗa mu a kan ladan alkairan da labarin ke tafe da su. SADAUKARWA Wannan labari kacokam nashi na sadaukar da shi gare ki HAJIYA AYSHA, Hajjatyna, ina roƙon Allah ya saka miki da mafificin alkairi, domin ba dan ke ba, to da tabbas wannan labari babu shi, Allah ya azurtaki da zuria'a masu albarka, waɗanda kike riƙonsu Allah ya musu albarka, Allah ya ƙaro miki zaman lafiya da ta soyayya da haƙuri a gidanki, Allah ya ƙara mana haƙuri da dangana har mu iske namu rabon na Haihuwa. TUKUICI A ko da yaushe muddin Uwar Batoorl za ta ɗauki alƙalami da sunan rubutu, to tabbas zai kasance tukuici ne a gare ka SIR ABUBAKAR SADEEQ, CEO LAFAZI WRITERS ASS. Tare da ɗaukacin members namu, Allah ya agajemu a lamuranmu ya talkafa mana alƙalumanmu. GORO Littafina goro ne a gare ku Iyayena da Mijina, Allah ya jiɓanci lamuranku duniya da lahira, Rabbi ya muku buɗi ta alkairin duniya da lahira, yanda kuka tsaya kuma kuke kan tsayawa a lamurana, Rabbi ya tsaya muku duniya da lahira. YABO A kullum littafina zai kasance ne yabawa gare ki ƴar uwa ta gari HAUWA'U SALIHU ISAH, babbar ya madadin Uwa, Allah ya ƙaro miki zaman lafiya a gidanki, ya raya miki zuria'a ya musu albarka, Rabbi ya kawo masu zuwa nan gaba lafiya cikin aminci. GAISUWA DA FATAN ALKAIRI Mariya(mai jego) Hajiya Aisha(Maman mhm'd) Balkisu (Ammin sheikh) Surayyatu (Ƙawar arziƙi) Ecleemart (Uwa ga amintacce) Hajiyar Makeup Hafsat Umar (Amarya mai capacity) Ummu Adeel (Mutumiyar arziƙi) Dr seeyert (Bestyna) Haj. Maryam Adam (Ummul baiti) Madam Khadija (Maman Abdallah) Haj. Saddiƙa (Mom Sani). Inai muku gaisuwa da fatan alkairi, har ma waɗanda ban ambaci sunansu ba, masoyan Uwar Batoorl, mutanen Amana na Uwar Batoorl, don kun wuce Fan's kun zama Fam. JINJINA Ni Uwar Batoorl ina gaisuwan jinjina ga duk masoya masu ƙwarara guiwa da ƙarfafa guiwa a gare ni, a saya littafina a yaba mini, a alkairanta mini a kuma a bi ni da addu'o'i, ina jinjina a gare ku, Allah ya muku ninkin wanda kuke mini daga addu'o'i har abin arziƙi, Allah ya taya ni gode muku, madallah da ku. ***MASU TALLA ƘOFA A BUƊE TAKE, KU HANZARTA DOMIN AYI INGANTACCIYAR TAFIYARNAN DA HAJARKU, KU KAWO TALLANKU CIKIN AMINCI A TALLATA MUKU SHI CIKIN ANNASHUWA DA SHAUƘI, KU TUNTUƁE NI A WANNAN LAMBA 09161720046.** 🅿️ 1 _ 5 ⭐️ PLATEU STATE, NIGERIA. PLATEU SPECIALIST HOSPITAL Da misalin ƙarfe goma na dare, hayaniya da kai kawon jama'a ya tsagaita a harabar asibitin, sai hasken fitilar Sola da ke haske ko ina a farfajiyar asibitin gwanin sha'awa kaman ba dare ba, shiru ba sautin komai sakamakon lokaci da ya ja, ga kuma walƙiya da ke haskawa, wanda hakan ke nuni da akwai hadari a garin. Ƙaran shigowar wani haɗaɗɗen hamshaƙin mota a matuƙar guje, shi ya mamaye gurbin shirun da farfajiyar asibitin ya ɗauka, daga irin mugun gudun da matuƙin motar ke yi ka san tabbas ba lafiya ba, matuƙin motar shi ne bai dai-daita sawayen motar ba, kuma bai tsagaita gudun ba sai a gaban emergency ward, tun matuƙin bai gama dai-daita sawayen motar ba, mazaunin kujeran da ke a gefensa ya buɗe cikin sauri ya fito, a rikice a hargitse ya kutsa kai cikin asibitin, nurses da ke a ɓangaren ya yiwa magana a kiɗime, cikin hanzari suka gunguro gadon ɗaukan mara lafiya(Stretcher) suka nufo waje, shi kuma da ɗan gudu-gudu ya fice, ko da ya koma wajan motar tasu samu yayi waɗanda suka taho tare da su suna ƙoƙarin kinkimar mara lafiyan, ƙarasawa yayi kusa da dattijon cikinsu, cikin murya da ke nuni da tsantsar damuwa ya ce, "Abba ku matsa bari na riƙe shi, ga malaman asibitin ma da stretcher." Dattijon ɗan baya yayi ya bai wa wannan matashin mai suna Umar space ya tallafawa sauran suka ɗago mara lafiyan da kyau, suka ƙarasa fito da shi a motar dai-dai malaman jinyan asibitin sun iso, ɗaura mara lafiyan aka yi akan gadon sannan suka fara tura gadon da sauri-sauri, su ma duk suka mara musu baya cikin hanzari. Kai tsaye emergency aka shige da mara lafiyan, a dai-dai matsayar masu kula da mai jinya suka tsaya, wannan matashin da ya ƙira malaman jinyan asibiti; shi ne ya kuma jawo kujeran roba tare da aje wa a bayan dattijon, cikin girmamawa ya ce, "Abba ku zauna." Dattijon zama yayi tare da gyara zaman tabarau nashi a idanuwanshi yana sakin ajiyan zuciya lokaci guda, sannan cikin dattijuwar muryansa ya ce, "Umar, Khalid, Sa'ad duk ku zauna ku ma, in sha Allah za a fito da Abubakar Sadeeq lafiya cikin aminci da yardan Allah", ya ƙarishe maganan yana haɗa hannayensa a zuciyarsa yana mai addu'an Allah ya tashi kafaɗun yaron shi, Allah ya kawo musu koma menene da sauƙi. Matasan samarin duka uku ƙarisawa suka yi wajan kujerun asibiti irin na silver waɗanda ke mammanne da juna duk suka zauna, Khalid da Sa'ad jingina suka yi da jikin kujeran suna jan numfashi kowa da abinda ke yawo a zuciyarshi, yayin da Umar kuma ya ɗan zauna a baki-bakin kujeran ya ɗaura guiwowin hannayensa a kan cinyarsa, ya tallafe goshinsa da tafukan hannayensa duka biyu, cikin tsantsar damuwa. Shiru ne ya ratsa wajan ba ƙaran komai sai sautin iskan da fanka ke badawa kawai, ƙaran ƙiran waya shi ya katse shirun wajan, Umar da ke a matuƙar rikice ya ɗauka wayarsa ce sai ya fara laluɓa, sai ya ji ashe ma ya bar wayar tashi a gida, wayar Abba ke ringing. Abba ciro wayar yayi a aljihun gaban jallabiyan jikinshi, "Halima", sunan da wayar ta nuna ɓaro-ɓaro na wanda ya ƙira shi, sai da ya ja numfashi sannan ya ɗau ƙiran tare da kara wayan a kunnensa, cikin tashin hankali dattijuwar muryan da ke nuni da ta babbar mace ce ya ratso cikin wayan, ba tare da tayi sallama ba ta hau magana cikin damuwa, saboda ba ta da nitsuwar yin sallaman. Cikin damuwa take faɗin, "Alhaji ya jikin Sadeeq ɗin? Fatan ba abinda ya same shi? Fatan Ɗa na yana a raye ba mutuwa yayi ba?, Alhaji wani asibiti kuka kai shi direba ya kawo ni, wallahi ba zan iya bacci ba kuma ba zan iya kasancewa cikin salama ba idan ban ji ko ganin halin da Sadeeq yake ciki ba", dattijuwar ta ƙarishe maganan tana kuka tana faɗin kar Sadeeq ya mutu. Dattijon numfashi ya sauƙe, duk da a yanayin damuwa da yake ciki shi ma da tashin hankali, amma hakan bai hana shi magana cikin kamala ba, cewa yayi, "Halimatu yanzu kukan naki shi zai bai wa Abubakar lafiya? Halima da zuwanki da rashin zuwanki duk ba abinda zai ƙara kuma ba abinda zai rage, zai fi kyau a ce yanzu haka kin tashi kin kai wa Allah kukanki ne a kan wannan kururuwan da kike, kar ki je ma ki faɗi abinda bai kamata ba, cuta ba ta kawo mutuwa indai lokaci bai yi ba, kaman yanda lafiya bata hana mutuwa muddin lokaci yayi, Halimatu ki kwantar da hankalink, ki yiwa Abubakar addu'a Allah ya tashi kafaɗunshi, da yardan Allah ba abinda zai samu Abubakar kin ji", ya ƙarishe maganan cikin tausasa murya a sigan lallashi. Dattijuwar jinjina kai tayi a ɓangarenta kaman tana a gaban dattijon, daga haka kuma ya katse ƙiran tare da mayar da wayarsa aljihu, suka ci gaba da zaunawa jiran fitowan likitocin. Sa'ad cikin tsantsar damuwa musamman da ya ji yanda mahaifiyarsu ta ɗaga hankalinta, a ladafce ya ce, "Abba menene ya sa Yaya Sadeeq ɗin ya faɗi?", Sa'ad yayi wannan tambayar ne saboda shi baya gida, yana shigowa da motansa kenan ya samu ana hada-hadan fito da Sadeeq, shi ne Abban ya ce ya ja su zuwa asibiti. Abba numfashi ya ja, murya ba amo cikin damuwa ya ce, "Sa'adu nima dai bansani ba, mahaifiyarku ce ta shiga ɗakinsa sai kuma ta fito hankali tashe tana kuka wai ta same shi a yashe a ƙasa ba ya motsi." Sa'ad a sanyaye ya sauƙe ajiyan zuciya tare da cewa, "Allah ya tashi kafaɗunshi." "Amin Ya Rabbi", Abba da Khalid suka haɗa baki wajan amsawa. Khalid ya ce, "Allah ya tashi kafaɗun Yaya, domin daga shi sai Allah ne kawai suka san me ke damunshi, amma sam-sam daman kwana biyunnan Yaya ya zama wani iri sosai, ba'a gane mishi ko kaɗan, ko murmushi da yake yiwa mutane duk na ƙarfin hali ne, miskilancinshi da rashin son hayaniya da saurasu duk sun ƙaru a kwanakinnan." Jinjina kai Sa'ad yayi tare da cewa, "Wannan haka yake Khalid, domin kuwa nima na lura bakina ne kawai yayi nauyi wajan tambayarsa ko lafiya, amma ina tunanin Umma ma ta lura dan ranan zan fita naji suna maganan, tana tambayarsa amma ya ce mata ba komai." Abba yana gyara zamansa ya jingina a jikin kujeran ya ce, "Ƙwarai Ummanku ta mini maganan, sai da tayi magana sannan nima na lura da hakan, kuma duk mun tambayesa dalili amma ya ce ba komai, shiyasa daga ni har ita muka tattara kashinsa muka aje a gefe tunda ba ƙaramin yaro bane shi." Khalid ne ya taɓa Umar da har yanzu kansa ke a ƙasa, tare da cewa, "Yaya Umar kar ka sanya damuwa a ranka wani abun kai ma ya same ka fa, in sha Allah zai tashi lafiya." Umar da yayi nisa cikin tunani da zaƙulo da lissafo me zai sa har aboki kuma Aminin da ya zame masa ɗan uwa ya faɗi lokaci guda haka farat ɗaya, jin maganan Khalid sai ya ja dogon numfashi tare da ɗago kansa ya jinjina alaman in sha Allah, dai-dai lokacin kuma walƙiya mai matuƙar kaifi ya haska tare da cida mai matuƙar sauti. Duk addu'a suka karanto na wanƙiyan da kuma tsawar, duk a zuciyoyinsu, Abba ne ya ɗaura da na tsawan a zahiri, "Subhanallazi yu sabbihul ardi bi hamdihi, wal mala'ikatu min kifatihi." Sai da Abba ya numfasa, sannan cikin lallashi ya ce, "Umaru ba abinda zai samu Amininka Abubakar da yardan Allah, ka kwantar da hankalinka." Jinjina kai Umar yayi a yanayi na damuwa ya ce, "Allah ya amince Abba." Daga haka wajan ya kuma ɗaukan shiru, duk suka zauna sauraran fitowan likitocin da suka shiga kan Sadeeq, ba jimawa ruwa ya soma sauƙowa, yanayi yayi matuƙar sanyi da ɗari. ***MASU TALLA ƘOFA A BUƊE TAKE, KU HANZARTA DOMIN AYI INGANTACCIYAR TAFIYARNAN DA HAJARKU, KU KAWO TALLANKU CIKIN AMINCI A TALLATA MUKU SHI CIKIN ANNASHUWA DA SHAUƘI, KU TUNTUƁE NI A WANNAN LAMBA 09161720046.** ⭐️ RAYFIELD AREA. HALIMATU SADIYAH POV *** Kwance take a gado mai matsakaicin girma, a madaidaicin ɗakinta, sanye take da short gown mai sulɓi irin yadin palazzo, rigan mai hannun vest ne tsayinsa bai wuce guiwanta ba, rigin-gine take kwance ta ɗaura pillow a saman ƙirjinta ta ƙanƙame idanuwanta a lumshe banda murmushi ba abinda take yi, ga waya a maƙale a kunnenta wanda hakan ke nuni da koma menene a wayar to shi ne dai dalilin murmushin nata, tana ciccilla ƙafafuwanta sama, cikin siririyar muryanta cike da shauƙi da shagwaɓa take langwaɓe kai gefe, cewa take, "Uhmn! Ni kwanakin ma fa sun mini kaɗan, gani nake suna isowa da wuri, zan yiwa Mama magana su Baffa su ƙara", ta ƙarishe faɗa tana cunna baki, wanda kana ganin yanayinta kasan ta gama matowa a kogin soyayyan wanda take waya da shi. A ɗaya ɓangaren, wani haɗaɗɗen murya ne da kana ji ka san mamallakin muryan haɗaɗɗene na ajin ƙarshe kuma maƙura kaman dai muryan ta shi, "Wai just 3 weeks da suka rage ne suka miki kaɗan? To dan kiji ba mai ƙara kwanakinnan idan ba nine na so hakan ba, ai miji shi ke yanke date dama bisa ga ƙarƙon shungullolinsa, amma ni kinsan ko nan da 1 week aka mayar ai a shirye nake, kai ban ma ƙi a ɗaura gobe a miƙo mini ke a goben ba", ya ƙarishe maganan ne yana lumshe idanuwa a ɓangarensa, shauƙin soyayyanta ke fisgarshi yana ratsa shi ta ko ina. Juyi Sadiya ta kuma yi ta kifa ƙirjinta a kan pillown, tare da yin sama da ƙafafuwanta tana kaɗa su, tana sakin murmushi har yanzun, dan tasan zolayarsa ta yi kuma ya zolayu, cikin son shafe zolayar ta kuma runtse idanuwanta da kyau, cikin salon magana mai jan hankali da nitsuwa, kaman mai bust ta ce, "Ko da kuwa ba miji ke yanke kwanaki ba, bazan taɓa bari wani ya ƙara kwanakin ba, domin na gama shiri tsaff jira nake kawai igigoyin mallakarka su harɗe ni su sarƙafeni su ja ni har gidanka, ta yanda kamun na kwanta zan kalli haɗaɗɗiyar fiskan mijina, haka ina tashi a bacci fiskarshi zai zamana abu na farko da zan fara tozali da shi domin daidaitar lafiyar zuciya da ta gangar jikina." "Daga na mallakeki an kai ki gidana, fiskana sai ya ishe ki da kallo, zan kasance a tare da ke a ko da yaushe muddin ba aiki ko wani abu mai muhimmancin bane zai fiddani, kuma ko da wani uzurin ya sanya nayi nesa da ke, to a duk sanda kika buƙaci ganin mijinki, za ki ganni da yardan Allah, sweet Al-Sad ina miki son da baki ba zai iya faɗan adadinsa ba, ban taɓa son wata ƴa mace ba sai a kanki, kuma bana fatan ƙaddaran da za ta kawo wata cikin rayuwata ta riskeni", murya a shauƙance yayi maganar, yana mai cusa yatsunsa cikin gashin kansa. Sadiya sanya tafin hannunta tayi ta rufe fiskanta, cikin jin kunya ta ce, "Allah ya tabbatar mana da alkairi Zakina." Murmushi mai matuƙar sautin da zai iya sanya mutum ɗauke wuta ya saki a ɓangarensa, yana ƙoƙarin yin magana sai Sadiya ta miƙe tare da cewa, "Mama ta shigo bari mu gama magana zan ƙira ka", tana gama faɗa ta kashe wayan, tare da tunkarar mahaifiyarta da ta shigo ɗakin duk jiki a sanyaye wani iri, tana isa gabanta ta ce, "Mama mai ya faru na ganki haka?." Girgiza kai Mama tayi, cikin damuwa ta ce, "Ai komai ma ya faru Sadiya, yanzu Yayanki ya fice hankali tashe wai an ƙirashi mai babban suna ba lafiya." Wani irin waro idanuwa Sadiya tayi, cikin tashin hankali ta ce, "Shi Yaya Sadeeq ɗin ne ba lafiya? Wai me ya same shi Mama? Suna ina yanzu haka? Mama bari naje gidan nasu na duba yaya jikin nashi", faɗin Sadiya tana ƙoƙarin raɓa gefen Mama ta fice. Mama kallon Sadiyar kawai take tare da mara mata baya har suka fice a ɗakin, kamun Mama ta iso tsakiyan palourn nasu har Sadiya ta isa bakin ƙofa saboda kiɗimewa, murya a kaurare Mama ta ce, "Ke Sadiya bana son hauka fa, in ma suna a gida haka za ki fice da ɗangalallen riga ba hijabi? Zan ci mutuncinki da abu da kike yi watarana kaman ƙaramar yarinya." Sadiya fiska a marairaice da damuwa ta juyo ta ce, "Kiyi haƙuri Mama, wallahi na rikice ne, bari na sako hijabin sai naje." "Da ya fi miki kam, dan wannan hadarin da ke a gari ma kaɗai ya ishe ki, balle kuma a ce mai babban sunan suna hida sai ya saɓa miki ai", Mama ta faɗa tana nufan nemo nata hijabin. Ɗaki Sadiya ta koma ta sako zumbulelen babban hijabinta, ko da ta dawo palourn samun Mama tayi ita ma da nata hijabin, gaba Mama tayi Sadiya ta bi ta a baya, kulle madaidaicin gidan nasu suka yi, sannan suka taka har ƙofan wani tangamemen katafaren gidan da ke manne da gidansu, bakin shirgegen gate na gidan wanda ya ci kuɗi suka tsaya, Sadiya ce ta yi knocking, mai gadi daga ciki ya ce, "Waye?" Sadiya da siririyar muryanta mai ɗauke da damuwa ta ce, "Sadiya ce." Da sauri mai gadin ya buɗe ƙofan yana musu sannu tare da basu haƙuri bai san su bane, Sadiya dai bata tsaya sauraransa ba ta wuce ciki, Mama ce ta tsaya suka gaisa sama-sama sannan ta ce masa bakomai ta wuce ciki ita ma, kasancewan alaƙa ta maƙwabtaka da abokantaka da ke a tsakaninsu da mamallakan gidan, shiyasa kai tsaye suke shigowa gidan tamkar ƴan gida, kuma shiyasa ma'aikatan gidan suke girmamasu suke darajasu kaman mutanen gidan, dan umurni ne daga mamalllakan gidan. Sadiya da sallama ta shiga palourn, duk da kuwa ba zuwan lafiya bane, amma hakan bai hanata ƙwala wa Umma ƙira kaman yanda ta saba ba muddin ta shigo, faɗi take, "Ummanmu na tafi wajan Yaya Sadeeqna", ta ƙarishe maganan tana shiga sashin Sadeeq da sallama, zuciyarta a matuƙar zaƙe dan ganin halin da yake ciki. Ƙamshinsa mai matuƙar sanyi da daɗi da sanya nutsuwa, shi ya ziyarci hancinta a farko, kamun idanuwanta suka sauƙa a kan tangamemen frame na photonsa da ke maƙale a bango, sanye yake da suit arsh colour, amma iya wandon da white ɗin da falmara ke a jikinsa, top ɗin ya riƙe a hannunsa da ya saƙala a kafaɗansa kaman ya rataya, hannunsa guda na dafe da kujerar da ke gefensa, ya harɗe ƙafafuwansa, a ta ƙasan frame ɗin an rubuta sunansa da manyan baƙi ENGNR. ABUBAKAR SADEEQ SALIHU WAZIRI. Haɗaɗɗene kuma kyakkyawa matuƙa, yana da tsayi dai-dai da matsakaicin jiki haka ma hasken fatarsa ba za a ce masa fari kai tsaye ba, kaman yanda ba za'a sanya shi a jerin baƙaƙe ba, yana da suffa da sura irin ta zaratan maza kuma jarumai, yanda ya haɗe a frame da ke da girma sai ka ji kaman ka ƙira shi ya amsa, musamman da ya kasance kamilin miskilin murmushi ke shumfiɗe a zaƙwaƙurar fiskansa ta ingarman namiji. Sadiya numfashi ta sauƙe tare da janye sanyayyun idanuwanta a kan photon, cikin sanyin jiki tana jin wani iri, wanda ko da yaushe a photo ko a zahiri idan ta ɗaura idanuwanta a kan Yaya Sadeeq sai taji wani abu na tsarga mata zuciya tun daga ƙoƙon ranta, na matuƙar ƙaunarsa a matsayin Yayanta kaman yanda yake ƙaunarta a matsayin ƙanwarsa, sosai take masa addu'a da fatan samun mace tagari, bata taɓa ɗaga hannayenta da sunan addu'a kuma ta sauƙe su ba tare da ta sanya Yaya Sadeeq a ciki ba, bata kuma taɓa ambatan Allah a zuci ko a fili da niyan ta kai ƙoƙon baranta gare sa ba, dai ta jai ƙoƙon Yaya Sadeeq gare sa na Allah ya taya su gode masa, dan Yaya Sadeeq mutum ne har da ƙari sai dai fatan Allah ya amsa addu'o'i, yanda yake alkairanta musu shi ma Allah ya ninka masa nashi alkairan ta duniya da lahira. Kai tsaye ta nufi ɗakin da ta san shi ne na baccinsa, bakinta da sallama ciki-ciki ta tura ƙofan ɗakin a hankali, idanuwanta da suka gane mata ba mahaluƙi a ɗakin ne ya sanya ta ƙarisa buɗe ƙofan da sauri, lungu da saƙo ba kowa, nan ɗin ma dai sai ƙamshinsa da photos nasa kaman dai a palourn, da sauri ta juyo zuciyanta na tsananta bugawa, Mama ta ce mata Yaya Umar ya zo wajan Yaya Sadeeq ba lafiya, to ina suke? Kar dai asibiti aka kai Yaya Sadeeq? Wani irin bugawa da mugun ƙarfi zuciyarta tayi, saboda a rayuwarta ba abinda ta ƙi jini irin asibiti, sam-sam bata son maganan asibiti. Da sauri ta juya ta koma main palourn, Umma da Mama ta samu a tsaye curko-curko, daga yanayin yanda ta ga Umma, to tasan lallai bata buƙatar tambaya dan halin da ake ciki ya gama nunawa a yanayin Umma, a sanyaye ta rage tafiyanta jiki ba laƙa kaman mai tambayan ƙasa kamun ta taka, idanuwanta cike da ƙwalla ta ƙarasa wajan Umma ta faɗa jikinta, hawayen idanuwanta ne suka fara gangarowa, cikin muryan kuka ta ce, "Umma an tafi da Yaya Sadeeqna asibiti ko? Umma meyasa aka kai shi asibiti? Zai warke a gida fa", ta ƙarishe faɗa hawaye na zirya a kumatunta gudu-gudu. Umma cikin jumriya da kalaman Abba suka ɗan sanya mata, ta sanya hannunta ta shafa kan Sadiya zuwa bayanta ta cigaba da bubbuga bayanta alaman rarrashi, sannan ta ja hannunta suka zauna a kujera mai ɗaukan mutum uku, a sanyaye Umma ta ce, "Kar ki damu auta, in sha Allah Yayanki lafiya lau zai dawo da ƙafansa ma, kar ki tashi hankalinki kin ji ko, Abbanku ma ya ce mini jikin da sauƙi likitoci suna tare da shi." Sadiya kanta a lafe a jikin Umma tana kukanta ta ce, "Umma kin san aisibitin nan ba son sa muke ba ni da Yaya Sadeeqna." Umma jinjina kai tayi tana faɗin, "Na sani auta bakwa so, amma komai ai kamawa take, Allah ya bashi lafiya shi ne za muyi addu'a ko....", Umma ta cigaba da rarrashin Sadiya, dan kuka take da gaske, damuwan Sadiyan ma shi ya rage wa Umma nata har ta samu ƙwarin guiwa. Mama ajiyan zuciya ta sauƙe a zuciyarta tana yiwa Sadeeq ɗin fatan samun sauƙi, dan yanda take

Chapter 1 of 32