shigo gidan suna tambayar ba'asin kukan Yadikkon.
Cikin kukan take cewa "waze sani kuka idan ba wannan makirar Yarinyar ba? Kullum burinta taci mutuncina da tsufana da komai, nasan da kakarta ce ni ba zata mata haka ba, ta kalli tsabar idona ta zageni tsaf taimin wankin babban bargo, ko tsufana bata duba ba, yarinyar nan bata da mutunci, bata san darajar furfira ba sam.
Kalaman Yadikko sunyi tsauri kuma sun tsaya a zuciyar Amira, tamkar ta haɗiyi ƙayar kifi me dafin gaske haka take ji a ƙirjinta, Yadikko makirar tsohuwace ta gaske, ta iya shirya kalamai da Magana, ƙarya da ƙarairayi ba wanda bata iya ba, gata da daɗin baki da fuska biyu dan haka babu wuya ta ƙulla maka sharri.
Amira ta buɗe akwatinta ta shiga gyara kayan ciki, yayinda Hawaye ke zuba ba ƙaƙƙautawa a cikin idonta, tana jik zafin addu'oin da Yadikko take mata, ba tayi yunƙurin kare kanta akan abunda Yadikko ta faɗa ba, saboda a gurin Amira basu isa ta tsaya tana gaya musu abunda ya faru ba.
Sadiya tace "ji munafuka, wai itama kukan take Jahila wadda bata san darajar furfura ba"
"Furfura me daraja, ita ta cancanci girmamawa, ba furfurar banza ba me son zuciya"
Amira ta bawa Sadiya amsa.
"Ke dan uwarki Yadikko ce me furfurar banza? Baki da mutunci Amira?" Zailani yai maganar yana kallonta.
Ko kallon inda yake Amira ba tayi ba, ta cigaba da kukanta, Zailani ya ƙule ya fita tsakar gida ya ɗakko ice, Yadikko cewa take rafkawa shegiya a muƙamiƙinta, tunda bata da mutunci.
Yana shiga ɗakin yai kan Amira ya soma sauke mata icen nan, ji tayi kamar kafaɗarta ta cire, take Amira ta ciro ƙaramar wuƙa a rigarta, tana kuka tace "wallahi ka kuma dukana da icen nan, sena yanke ka da wuƙar nan, sena maka kaciya da ita ince fyaɗe zakamin.
Da sauri Yadikko tace "ƙyale shegiya Zailani, karta maka halin karuwan, dama ta saba ganin tsiraicin maza, tunda ba abunda ta hango seyi maka kaciya, karta kassaraka dan idan tayi maka kaciya da wuƙa ta kashe ka kuma bata da Asara"
"Ni zaki kalla kice zaki yiwa kaciya? 'yar daba kika koma bayan karuwanci?"
"Nace ka ƙyaleta kar tayi maka illa a banza"
Sukai waje, Amira kuwa ta zauna a gurin ta cigaba da rusa kuka kamar an mata mutuwa, ga zafin dukan data sha, ga zafin irin rayuwar da ake mata, me cike da ƙalubale da cin zarafi.
Imran se bayan goma na dare ya ƙarasa gida, dama ya riga yayi dama, yana zuwa wanka kawai yayi ya hau kam gadonsa ya janyo waya, ya kira Ihsan suka cigaba da waya da, kamar zasu cinye juna, kowannen yana nunawa ɗan uwansa irin yadda yake ƙaunar ɗan uwansa.
Abba kuwa ya rasa yadda ze tunkari Imran da wannan maganar, saboda gani yake idan yayi haka kamar bewa Imran ɗin adalci ba, da ita kanta yarinyar daze aura ɗin, Amma yayi tunanin yayi tunanin ya rasa ina mafita akan lamarin banda wanda Hashim ya gaya masa, gashi sam shima ya fita sabgar Ammi, dan yasan idan taji maganar nan za'ayi tashin hankali ba kaɗan ba.
Amira kuwa yau kusan kwana tayi ba tayi bacci ba, ta sha kuka ta sha kuka, kamar ta shiɗe, ta dinga tunani daban daban, ji take kamar ta gudu ta bar gidan nan, amma idan ta gudu ina zata?
Haka taita wannan tunani har Asuba tayi.
Gari na fara haske Amira ta kintsa tai ficewarta, ta tafi gidan Anty Fa'iza, can ma da taje bata kula kowa ba, ta samu guri tai kwanciyarta, zuciyarta na mata raɗaɗi akan irin rayuwa da takeyi.
Imran ya fara zama busy, saboda hada hadar shirin bikinsa, dan an shiga satin biki, amma Abba yana jin nauyin gayawa Imran matakin daya ɗauka a game da Aurensa da Amira.
Abba yana shirin fita, sega kiran Alhaji Hashim, Abba ya ɗaga suka gaisa Sannan yace "Alhji Ali ya ake ciki ne? Ka sanarwa da yaron kuwa?, Zuwa yanzu yakamata ace an tsare yarinyar nan ta fara istubra'i fa"
"Hashim na kasa sanar masa, ba dan ina shakkarsa ba, ba kuma dan baze abunda nake so ba, sedai ina tunanin ita kanta mahaifiyarsa yadda zata ɗau maganar"
"Aikuwa idan baka faɗa musu yanzu ba, komai ze kacame maka, ko kana nufin se ranar ɗaurin Auren zega an ɗaura masa aure haka ba saninsa, an shiga satin biki, ita kanta yarinyar daze aura ɗin akwai buƙatar ka samu aje a sanar da magabatan yarinyar nan suma su sani"
Abba yace "to shikenan, zan san yadda zanyi Insha Allah"
Alhaji Hashim yace "to babu laifi, nima zanyiwa Meɗakina Magana, seta zauna a gurinmu, har gwaje gwajen da yakamata se ayi mata"
"Nagode sosai Hashim, Allah ya bar zumunci"
Abba ya ajiye wayar, ya ɗanyi shiru Sannan ya fito, ɗakin Imran ya nufa, yana zuwa yai knocking, Sannan ya buɗe ya shiga.
Imran ya shirya cikin dogayen kaya, da alama fita zeyi, yana ganin Abba yace "Abba da kanka, da ka kirani ai se inzo da kaina"
"Ni na kira ango, ai gara inyi tattaki inzo da kaina"
Imran yai murmushi cikin jin kunya ya sunkunyar da kai.
Abba yace "Imran magana nazo muyi"
Imran yace to Abba.
Suka zauna Abba na kan kujera, Imran yana zaune akan carfet.
"Imran wata alfarma nazo na nema a gurinka, sedai ban san yadda zaka kalli abunba"
Imran yace "Abba wannan wace irin alfarma ce haka? Wadda kake tunanin bazan iyayi maka ba? Ba abunda baka mana ba a rayuwa, mezesa in kasa maka wani abu da ka buƙata a gurina?"
"Imran bana son kaga dan ni na haifeka zan maka dole ko in cutar da kai, shiyasa na kira abun da alfarma, ba dole zan maka ba, alfarma ce zan nema idan kaga zaka cutu base kayi ba, ba zan maka dole ba"
"Abba dan Allah ka dena kiran alfarmar nan, amma me kake so inyi maka haka?"
"Imran, munyi magana da Alhaji Hashim ne akan wannan yarinyar Amira, kuma muka cinma matsaya aurar da ita, ko hakan zesa ta nutsu, sedai mun duba babu wanda ze iya riƙeta da mutunci da amana idan ba kai ba, kaine ɗan uwanta zaka iya rufa mata Asirin abinda tayi a baya, saɓanin idan ta auri bare, a taƙaice dai ina son zaka auri Amira ne, ka haɗa ta da Ihsan, amma ba dole zan maka ba, Kamar yadda na gaya maka a fari, amma hakan kamar jihadi ne, da ceto rayuwar yarinyar daga tarwatsewa gaba ɗaya, ban yanke wannan hukuncin dan in cutar da rayuwarka ba, amma me kace?"
Wani irin gumi ne ya shiga ratsa Imran, duk da sanyin AC daya cika ɗakin, amma wata irin zufa yake, tabbas ya shiga tsaka me wuya, dan sam ba shi da ra'ayin zama da mata biyu, saboda baya son fitina da damuwa, kuma ga wadda ake so ya aura, fitinanniya lamba ɗaya, wadda a zahiri ma shi ƙyamarta yake yi, amma ance ya aureta ya haɗa da Ihsan, anya kuwa ze iya? Can wata zuciyar tace 'kai har akwai alfarmar da Abbansa ze nema a gurinka ka kasa yi masa? Bayan haihuwarka da yayi ya sadaukar da lokacinsa, ƙarfinsa dukiyarsa gurin gina taka rayuwar?.
"Kayi shiru ba kace komai ba Imran"
Cikin sanyin jiki Imran yace "bakomai Abba, yadda kace haka za'ayi"
Abba yai murna yace "Alhamdilillah Masha Allah, dama nasan ba zaka bani kunya ba Imran, zanje in samu magabatan Ihsan suma muyi magana dasu, Sannan za'ayiwa Amira daukkan gwaje gwajen da suka kamata, insha Allah nasan ma Babu wata matsala"
Imran kam gaba ɗaya kansa ya gama kullewa, a ransa yace ko wani gwaji za'ayi mata ba ruwana, dan bazan iya haɗa jikina da Yarinyar data gama raba jikinta ga maza a titi ba.
Bema san me Abba yake cewa ba se jin muryar Abba yai yana "Nagode, Nagode sosai Imran, Ubangiji Allah yayi maka albarka, Allah ya haɗa kanka da iyalinka, ya zaunar daku lafiya, yadda kayi min biyayya Ubangiji Allah yasa yaranka su bika haka, sannan zan canza maka gidan da zaku zauna, seku zauna a gidana na Bamako gaba ɗaya, bana son ka rarraba kan iyalinka, insha Allah baza kayi dana sani ba a rayuwarka na gode sosai my Son"
Ya shafa sumar Imran, Sannan ya tashi ya fita cike da farinciki da annashuwa a ransa.
Imran kuwa zaman daɓaro yayi yana tunani, da wani idon ze kalli Ihsan, meze fara gayamata, ba abunda ze hana tayi masa kallon mayaudari, kimarsa zata ragu a idonta, taya ze fara zama da wannan Yarinyar, mara ta ido da shegiyar fitina, Amira ta rasa qualities da yawa da ake nema a gurin mace, tabbas daba Abbane ya nemi wannan alfarmar ba, da kowaye ya nema baze yi ba, dan sam Amira ba ta dace da tsarin rayuwarsa ba.
Yana nan zaune, Khalid ya shigo ɗakin Imran, cike da mita ya kalli Imran yace "kai ka rainamin hankali gaskiya, kaje ka shanyani ina zaman jiranka, kawai kazo nan kayi zamanka kana tunani haka akeyi?"
Imran yai shiru bece komai ba, se tagumi da yayi da hannunsa bibiyu.
"Wai ba magana nake maka ba ka shareni? Ka wani yi uban tagumi kamar ance Ihsan ta mutu"
Imran ya sauke hannayensa yai ajiyar zuciya, tare da sake dafe kansa.
"Wai zaka tashi mu tafi ne kokuwa?"
"Kaga a fasa fitar nan kawai"
"Saboda me, wai kai meke damunka ne, ka wani nustu kamar marayan muzuru, ka tashi mu tafi malam lokaci yana ƙurewa"
"Kaga a fasa fitar nan kawai"
Khalid ya kalleshi da mamaki yace "Kamar ya a fasa? Ban gane ba"
Imran yace "Khalid ina cikin damuwa ne, bazan iya fitar ba".
"Damuwar me, kai da zakayi aure, ai damuwa semu gawauraye"
"Khalid mata biyu wai zan aura lokaci ɗaya"
"Kamar yaya?" Khalid ya tambaya cike da rashin fahimta.
Nan Imran ya warwarewaa Khalid komai.
Khalid yace "lallaai kana cikin tsaka me wuya mutumina, amma Allah yasa haka shine mafi Alkhairi, insha Allah zakaga sakamakon biyayya, kayi haƙuri Imran, inaji a jikina zaka samu Alkhairi a sanadin Aurenta"
Imran kawai ya tashi ya tafi ɗakinsa yaje ya kwanta, dan yama rasa abunda zeyi gaba ɗaya.
Alhaji Hashim kuwa tuni yayiwa matarsa bayani akan Amira, kuma ta bashi tabbacin ita a kawo mata Amira zata riƙe, dan gaba ɗaya yarinyar tausayi ta bata da Alhaji Hashim yayi mata bayani.
Kasancewar mahaifin Ihsan ya rasu, Alhaji Ali da waliyan Imran, a ranar sukaje suka samu wan mahaifinta akan mata biyu za'a aurawa Imran a gurin ɗaurin Aure, Ihsan da kuma 'yar uwassa, shima wan mahaifin nata be nuna fushi ko ɓacin ransa ba, sedai yace musu "komai muƙaddari ne, kuma bawa baya wuce ƙaddararsa, Allah ya basu zaman lafiya ya haɗa kansu, amma kun san halin mata, se Addu'a, dan haka karku sanar musu da zancen, ni zan sanar musu idan lokacin da yakamata yayi, idan aka gaya musu yanzu ba zasu bari ayi bikin lafiya ba"
Abba yace"Allah ya wuce mana gaba, mungode sosai da wannan karamcin naka, Allah ya albarkaci yaranmu gaba ɗaya"
Imran kam bacci ma gagararsa yayi, yana kallon Ihsan tana kiransa amma ya kasa ɗaga wayar, saboda zatonsa An sanar mata ai ita da Amira ze aura.
Amira kam ta dena shiga sabgar mutanen gidan, duk wulaƙancin da sukayi mata, amma suna ta shirye shiryen zasu bikin ɗan uwanta Kaduna, Amira kallonsu kawai takeyi, 'yan gidansu akwai son abun duniya fiye da kima, basa iya ɓoye zalamarsu sam.
Amira Ta fito tsakar gida, Sadiya nata wanke wanke, ta baje kwanuka gashi ta zubar da dagwalon ƙanzo da komai, Yadikko tazo wucewa Amira ta kauce ta bata hanya, kawai ta taka ruwan omo, santsi ya kwasheta ta faɗi ƙasa, cikin kwanuka da dagwalon wanke wanke, ta buge ƙeya da tukunyar ƙarfe.
Take ta kurma uban ihu, ta dafe kanta wai Amira ta hankaɗeta, ko takanta Amira bata biba, tai gaba abunta.
Baba ya fito ya dinga yiwa Amira tijara, yana faɗin ya gaji da wannan tashin hankalin, baza'a kashe masa uwa a banza ba, Amira seta bar musu gida.
Ko kallaonsa ba tayi ba, ta ɗauki gyalenta da jakarta ta fice ta bar musu gidan.
Da safe Imran yana kwance, yana ta tunani ranar ne za'a fara bikinsa, Amarya za tayi henna day amma baya cikin nutsuwarsa, still Ihsan tana ta kiransa amma yaƙi ɗagawa ƙarshe ma ya kashe wayarsa gaba ɗaya, dan be san meze ce mata ba.
TV dake bedroom ɗinsa na tayi ita kaɗai, can aka nuno mawaƙin nan da Amira tayi hotuna dashi a Abuja, wai ze kai ƙarar Amira kotu, sunyi yarjejeniya zata fito a waƙoƙinsa, amma tai tafiyarta bema san inda ta shiga ba, dan haka 'yan sanda suna nemanta, duk inda take.
Imran ya tashi zaune, ya dafe kansa yama rasa me Yakamata yayi.
Wai wannan itace wadda ake son ya aura, wannan watsatsiyar Yarinyar.
Ya ɗakko wayarsa ya kira Baba a waya, Baba ya ɗaga lokacin yana tsaka da banbami akan Amira.
Imran yace "Ina Amira take?"
"Ai lamarin wannan yarinyar banma san me zance ba, kwana biyun nan masifa kawai take janyo mana, ta saka ƙafa ta fice ta tafi gantalinta, shekaranjiya tayiwa Yadikko zagin cin mutunci, dan an mata magana ta ɗakko wuƙa kamar wata 'yar daba, yau kuma ta hankaɗa Yadikko cikin tukwane ta kusa suma saboda yadda ta bugu a kanta, gaskiya na gaji ba.....
Imran da maganganun Baba ke sake kunnashi yace "kaga ba kira nayi ka wassafamin wannan takicin ba, duk inda take ku nemota, koku turomin lambarta inyi tracking ɗinta, zan shigo Kano anjima, idan ba haka ba ta gangamo wata rigimar, wadda ba iya kanta zata tsaya ba harku zata shafa, dan haka duk inda zaku samo labarta ku nemo ku turomin, zanyi tracking in nemota, tun kafin abun data janyo ya zama out of control"
Imran ya katse wayar yai jifa da ita akan gadonsa ya furta "Oh My God, Allah ka dubeni wai wannan ce zata zama matata, wannan yarinyar yasalam, am Sorry My Ihsan, baki cancanci haka daga gareni ba, amma dole inje in ɗakko Yarinyar nan kan 'yan sanda su kamata, abun kunyar zemin yawa, ace matar da Imran ze aura a hannun 'yan sanda, Sunan Abba ze ɓaci nima mutuncina ya zube"
Ya ɗau wayarsa ya kira Khalid, Khalid ya ɗaga, Imran yace "Khalid ka shirya zaka rakani Kano yanzu Please!"
(Oga Imran za'aje a ɗakko mana amarya 😂😂😂)
Share, Share, And share as much as you can please, masu nema daga farko yana nan a watpad a account ɗina
Ayshercool 7724
Ayi vote, ai following please
Masu san what's app group kuma ga link nan, mata kawai banda maza Please, Sannan akwai dokoki a group ɗin, in kina ɗaya daga groups ɗina karki joining please
https://chat.whatsapp.com/EAYHhAEJQPk8uGg2IeCQhX
07063065680.
[1/15, 6:38 PM] Ayshercool: 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
WUTA A MASAƘA
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P. W. A
*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA)
*BAƘIN TABO (Labarin gasa)
*AƘIDATA (Paid Book)
* WUTA A MASAƘA
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in
❌❌❌
Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.
KAMAR YADDA NA FAƊA TUNDA FARI, BA LALLAI IN DINGA SAMUN YIN POSTING KULLUM BA, IDAN AN GA BAN POSTING BA AMIN HAƘURI
17_18
Imran ya kalleta a fusace yace "nan yai miki kama da gidan karuwai ne?" Murguɗa masa baki tayi ta ɗauke kai.
Khalid yace "Amira gidansu Imran ne fa, ki shiga bakomai, baki ga 'yan biki suna shiga suna fita ba"
Ta ƙarewa gidan kallo, sannan ta kalli Imran tace "muje"
Idan Imran ya biyewa Amira, ze iya yi mata dukan tsiya a gurin nan, kawai ya wuce yai gaba, Amira tabi bayansa.
Mata nata tsokanarsa suna ango ka sha ƙanshi.
Cikin gidan suka shiga, ya wuce Falo Amira na biye da shi.
Minal suna zazzaune a falo da ƙawayenta, da babbar Yayarsu Khadija wadda daga Ita se Imran, ita tayi Aure tuntuni.
Khadija ce ta fara ganin Imran da Amira, ta kallesu tai murmushi tace "Imran kai da wa nake ganinka haka kamar Amira?"
Amira dai tayi turus, tana kallon Anty Hadiza.
Jin ance Amira yasa Minal waigowa, duk yadda ake faɗar rashin jin Amira da yadda ta ganta a hoto, ba ta zaci zata ganta a haka a fili ba, tafi kyau da class Sosai a fili.
Imran yace "eh ita ce"
Hadiza tace "masha Allah, Nikam yaushe rabon da inga Amira tun tana ƙarama sosai, yanzu waze ce ita ce, ta zama hamshaƙiyar mace"
Wata a ƙawayen Minal tace "wannan ba ita ce wani mawaƙi yace zata fito a vidon waƙarsa ba?".
Minal ta kwaɓe baki tace "ita ce"
"Wow Gaskiya naji daɗi dana ganta, ashe 'yar uwakku ce, wallahi ni burgeni tayi"
Cikin isa Imran yace "ke minal, ki bar abun da kike kije ki kaita ɗakinki, ki nuna mata toilet tayi salla, Sannan ki bata babban hijjabi"
Amira kuwa kamewa tayi a gefe, tana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya.
Minal ta zumɓura baki, cikin ƙunƙuni tace "ɗakina, toilet ɗina, kuma kayana, taɓɗijan Allah ya kiyaye inyi sharing da wata"
Cikin muryarsa me razanarwa wasu lokutan yai mata tsawa "dan ubanki me kike cewa? Ni nake miki Magana kike min ƙunƙuni?"
A hargitse Minal tace "A'a Yaya, dan Allah kayi haƙuri, wallahi ba da kai nake ba"
"Kai Sarkin masifa, tun daga ciki ake jiyo hargowarka, lafiya kake wa 'yata shouting haka?" Ammi ce ke maganar lokacin da ta fito daga wani ɗaki.
Ba tsammani ta kalli inda Amira take, sukai ido huɗu da juna, ko za'a naɗe ƙasa a dawo, Amira ba zata manta fuskar Ammi ba, da wasu abubuwa da suka shuɗe shekarun da suka gabata ba.
A wulaƙance ta ƙarewa Amira kallo ta kalli Imran tace "lafiya wannan fa?"
"Abba ne yace inje in taho da ita yau, a fara biki da ita"
"Saboda bikin nata ne, kokuma na ƙanwar uwatta?"
Amira ta ɗago ta kalli Ammi, ta maida kanta ta sunkunyar.
Anty Hadiza tace "Ammi, Amira ce fa ko baki ganeta bane?"
"Ke zam cewa baki ganeta ba, baki da labarin rashin jin da yawon ta zubar ɗin da takeyi, babu inda hotonunata da rashin kunyarta basu shiga ba, kawai se a ɗebo jiki a kawomin ita cikin gida, saboda me to baze yuwu ba, ba a gidan nan ba sedai wani gurin"
Hadiza tace "Haba Ammi, koma menene dalili ne ya kawota, kuma na ɗan lokacine, ana gama biki fa zata tafi"
Gaba ɗaya hankalin mutane ya dawo kansu, aka dinga bawa Ammi rashin gaskiya da nuna mata illar abunda tayi, jin mutane nata surutu ba yadda ta iya, haka ta ƙyale Amira, saboda gudun surutan mutane.
Imran ya kuma kallon Minal yace "bakiji me nace bane?"
Miƙewa Minal tayi, Imran ya kalli Amira yace "ki bita kije ta baki masauki, a baki hijjabi ki rife jikinki"
Duk da sanyi da jikin Amira yayi, hakan be hanata zumɓura baki ba, dan da ta san gidansu Imran ze kawota, da duk tunballen tsiyar da za'ayi sedai ayi ba zata yadda taje gidansu ba.
Minal tai gaba Amira tabi bayanta, suna shiga ɗakin Minal ta juyo ta gallawa Amira harara tace "ga toilet nan ki shiga, kuma ki kula karki sake kimin taɓe taɓen abunda ba shikenan ba, kuma karki min fitsari a ƙasa, kinji na gaya miki"
Amira ba tace uffan ba, dan ta san kome akayi mata Imran ne ya janyo da ya kawota gidan, dan da tana gidansu babu me mata wannan rashin mutunci haka.
A masallaci Imran ya sake haɗuwa da Khalid, suka wuce gidansu Khalid, a hanya Imran ya bashi labarin irin karɓar da Ammi tayiwa Amira.
Khalid yace "ai nasam za'ai haka, ni babbar fargabata ma suzo su san wannan maganar, akwai fa sauran rikici"
Imran yace "bari kawai, aini na zubawa sarautar Allah ido kawai, dan ban san abunyi ba"
"Ka kwantar da hankalinka, Allah ze baka mafita insha Allah"
Seda suka raba dare suna hira, Sannan Imran ya tafi gida, lokacin duk an rurrufe ko ina, kuma be haɗu da Abba ba sam balle ya gayamasa ya ɗakko Amira, dan haka kai tsaye ɗakinsa ya wuce yaje ya kwanta.
Amira kam duk a takure take, ba wanda ya kulata balle ya bata Abinci, ga gajiyar hanya data ɗebo, gashi bata san ko ina ba, Minal da ƙawayenta se wulaƙanci sukewa Amira, Minal tana gaya musu ai Amira karuwace, se wannan guda ɗayar ta farko da tace Amira tana burgeta itace bata biye musu ba.
Da daddare akazo gurin kwanciya, Minal ta kalli Amira tace "kinga, me aiki zata shigo yanzu ta kai ki inda zaki kwana, nan ɗakin zamu kwana ne nida ƙawayena, bama son takura ina fatan kin gane?"
Amira ba tace komai ba, ga kaya tana son canzawa, bata ɗakko komai nata ba, kawai Imran ya kawota ya ajiye yai tafiyarsa, taji kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu dan takaici.
Me aikin ta shigo ɗakin ta kalli minal tace "Anty gani"
"Yawwa, dama zaki wanke min banɗakina ne bana son sharing da jagwalgwalo, kin sanni da ƙyama, kuma an shiga banɗakin But before that, ki kaita inda na gayamiki za ta kwana"
Me aikin ta kalli Amira tace "taho in rakaki"
Ba musu Amira tabi bayan me aikin nan, sedai inda me aikin ta kaita ne ya bata mamaki, abun ya ɗaure mata kai, da faɗi da girman gidan nan, a rasa inda za'a kaita se Kitchen, kitchen ɗinma a cikin store, duk ga kayan Abinci a jibge kamar abun banza, an saka mata tsurara katifa wai ta kwana a gurin.
Amira ta ƙarewa gurin kallo, ta ja tsaki ta fice ta koma falo ta bar me aikin a gurin, ta samu guri a gefen kujaerun falon ta zauna.
Mutane kowa ya samu gurin kwama amma Banda Amira.
Haka ta kwana a falon nan a zaune, ga garin da sanyi ga baƙunta, da Asuba can waje ta fita tai alwala, tana ƙarewa gidan kallo da yadda zata bar gidan nan, ko Imran ya sani kobe sani ba, ta ƙudirce gari na yin haske zata gudu, ta koma Kano.
Yadikko kam ta bugu sosai, dan se an rirriƙeta take iya tashi, amma sam bakinta yaƙi mutuwa, banda zagi da kwashewa Amira albarka ba abunda takeyi, wai itace tai silar faɗuwarta ƙasa.
Umma da su Sadiya suna ta haɗa kaya, zasuje biki ita kuwa tana kwance, duk jiki yayi tsami.
"Wai yanzu niba yadda zakuyi dani, a lallaɓa a tafi dani gurin bikin nan?"
Zailani yace "ina za'a kaiki, ki zame musu kaya? Ya zasuyi dake? Jinyarki za suje suyi kokuma bikin zasu? Kawai ki haƙura ki zauna, a yaran gidan Baffa Salahu ko su Habiba ne suzo su dinga tayaki zama, kafin su dawo Amma wallahi kikace zaki bisu ma wahala zaki sha"
Haka sukayi ta fama da Yadikko, akan lallai se an tafi da ita gurin biki, seda taga ba sarki se Allah ta haƙura da zuwan.
Washegari da Safe suka gama shiri tsaf, suna jiran Fa'iza taje su haɗu a nan gidan su tafi gaba ɗaya.
Amira kuwa gari na fara hasake, wajen ƙarfe takwas na Safe tana tunanin idan ta fita ina zatayi, Anty Hadiza ta fito daga ɗakin Ammi tace "Amira, ya baƙunta?"
Amira ta kalleta tace "lafiya ƙalau, ina kwana?"
"Lafiya ƙalau Amira, naga kina ɗari ɗari ki saki jikinki fa, nan gidanku ne, ki saki jiki da kowa duk 'yan uwanki ne"
"Gidansu a gidan ubanwa? Gidana dai gidan mijina, gidansu yana Kano, kuma 'yan uwan 'yan uwana ne, ta nemi nata 'yan uwan ba nawa ba, mu babu kalarta a 'yan uwana"
Amira tai shiru ta sake sunkunyar da kai, zuciyarta na tafasa, Hadiza tace "Ammi why?"
"Ke dalla rufemin baki ko in zageki yanzun nan"
Suna barin falon Amira ta miƙe daga inda take zaune, dama jakarta na jikinta, ta zira takalmanta tai waje.
Mutane nata shiga suna fita, Amma tana zuwa bakin gate, ɗaya daga masu gadin ya taso ya kalleta yace "ina zaki?"
"Fita zanyi" Amira ta bashi amsa.
"Zuwa ina?" Ya tambayeta.
"Kamar yaya? Su sauran wanda suke fitan tambayarsu kake yi?, Kokuma ni ka raina, dan Allah ka bani guri in fita"
"Gidan ubanwa zaki idan kika fita?" T muryar Imran taji ba tsammani, waiwayowa tayi da sauri ta ganshi a tsaye, sanye da jallabiya fara.
Haɗe rai tayi sosai tace "Ni gida zan tafi, gidanmu zan koma"
"Hmm tunda dama ke kika kawo kanki ko? Kin ɗauka haka nan na kawo ki nan ɗin kina da damar da zaki fitane? Da kin matsa kin fita da se sun harbe ƙafarki da bindiga, sakarya kawai
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 31