Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da zan dawo ba, nace in ba damuwa ko zata zauna a gurinki, kan inga yadda Allah zeyi damu, tunda babu me kula da ita a gidan" Anty tace "Ni da 'yata amma ka dinga cewa in ba zaka takuramin ba, ai gara da ka gayamin inje in ɗakko abata, yanzu Zamafaran aka turaku Imran?" "Wallahi kuwa Anty, kin ganmu a hanya ma" "Subhanallah, to Ubangiji Allah ya tsare mana ku, ya kaiku lafiya ya dawo da ku lafiya, Amirana kuma Allah yasa rabo muka samu" Imran yace "Rabon me kuma Anty?' "Rabon Baby mana, zan ɗau jika" "Hmmm Anty kenan, ai mana addu'a dawowa lafiya" "Insha Allah zamuyi, Allah ya tsare" "Ameen Anty nagode" Ya katse wayar. Duk da yasan Ammi tana jin haushin sa amma ya kirata a waya, suka gaisa ta amsa masa sama sama, yace "Ammi ina buƙatar addu'rki, ina hanyar Zamfara ne" Ba shiri ta ware murya tace "wace irin Zamfara kuma?" "An turamu aiki ne, na so in biyo muyi Sallama, amma kiran na gaggawa ne, kuma abokan tafiya ta suka zo, shiyasa kawai na taho" Ammi tace "Innalillahi wa innalillahi raji'un, To Imran Allah ya tsare mana ku, ya kiyaye ku, Allah ya dafa muku ya shiga lamarinku, Allah ya dawo mana daku lafiya" tana maganar se hawaye. "Ammina ki kwantar da hankalinki, ba abinda ze faru insha Allah" "Ai hankalina ba ze kwanta ba, se Allah ya dawo da ku lafiya, Allah ya tsare" "Ameen Ammi nagode" Ta ajiye wayar jikinta a sanyaye, Minal ta shigo ɗakin Ammi ta ganta wani iri, tace "Ammi meya sameki naga kamar kinyi kuka?" "Bari kawai, Imran ya tafi Zamfara yanzu mu kai waya da shi" "Zamfara kuma Ammi?" "Eh Wai Zamfara, suna hanya ma" "Mun shiga uku Ammi, kashe sojoji ake sosai a gurin faɗan nan fa" "Hmm, Nifa tuntuni bana son aikin sojan nan, Babanku ya goyi bayansa yaje ya nema masa, mutum yayi masters meye na wani aikin soja maimakon ya nemi aiki, duk wani abun tsiya babanku ke gayyato masa shi, ko taya shi aikatawa" "To Ammi yanzu haka ya tafi ya barsu a gida ɗaya, Anty Ihsan da wannan 'yar damben" Ammi tace "aikuwa, taɓ aikam baze yuwu ba, taje taiwa 'yar mutane lahani a banza" "Wallahi kuwa dan kin san zata aikata" "Aikuwa ta taɓa ta se ta bar gidan nan, bari kawai mayi Magana da Maman Ihsan ɗin ta koma gida kawai, ta bar mata gidan kafin ya dawo" "Aikuwa dai da yafi, ni dama anjima zanje gurin Mummyn". "Shikenan, bari inje gurin babanku inji meze ce, bana son inyi abu ya zo yanamin sababi, na ga kwanan nan tun da ya aurawa Imran Yarinyar nan yabi ya canza, amma canzawarsa ba ze canza ƙudurina akan Auren nan ba" Minal tace "nima dai na gani Ammi, bari inje in fara shiryawa" Anty se la'asar ta tashi daga gurin aiki, kai tsaye gidan Amira ta wuce, dan ta duba jikinta kamar yadda Imran ya buƙata. Da sallama ta shiga falon, amma shiru ba'a amsa ba, ga mamakinta Ihsan na falon a kwance tana kaɗa ƙafa. Anty tace "Barka da gida, ina sallama amma baki amsa ba" Ɗagowa Ihsan tayi ta kalli Anty, ta ɗan yatsina fuska tace "banji bane" "Allah sarki, ya gidan fatan kuna lafiya"? "Lafiya ƙalau" Ihsan ta amsa da mata da ƙyar. Anty tace  "Nace Amira tana nan ne?" "Bani da tabbas, tunda ba'a kaina take zaune ba" Mamaki ne ya cika Anty, tace "to Allah ya baki haƙuri" Ta wuce ɓangaren Amira, ta shiga da Sallama amma shiru ba kowa a falo, kiran sunan Amira tai, amma taji shiru, ta ciro wayarta ta kira Lambar Amira, amma bata ɗaga ba. Kai tsaye ta nufi bedroom ɗin Amira, tai Sallama sannan ta shiga, A duƙunƙune ta hango Amira akan gado, tana ta rawar sanyi ga sautin kukanta da yake tashi ƙasa ƙasa. Da sauri ta ƙarasa bakin gadon tana kiran sunan Amira, Amira da ƙyar ta iya ɗaga idonta ta kalli Anty. "Amira lafiya meya sameki haka?" Tai maganar tana yaye bargon jikin Amira, Amira dai kasa magana tayi se kuka, Anty tace "yi shiru ya isa kukan, bari in haɗa miki ruwa kiyi wanka, kin ci Abinci ma kuwa?" Amira ta girgiza kai. Anty ta jona ruwa a heater, ta haɗawa Amira ruwa, ta rakata banɗaki, ta dawo ta gyara mata gado ta canza mata bedsheet. Tayi mamakin yadda Amira ke Rashin lafiya har jikinta ya zama haka, kuma bata gaya mata ba, Amira ta rame sosai idanunta . Ta shiga Kitchen ɗin Amira, amma babu kayan Abinci a ciki, ta dawo ɗakin ta tarar Amira ta fito daga wankan. Ta kalli Amira tace "na duba Kitchen ɗinki, Banga komai na Abinci ba, se ɗan abunda ba'a rasa ba" Cikin muryar marasa lafiya tace "suna Kitchen ɗin falo" "Amma Amira ya akai kika bari jikinki yai haka bakije Asibiti ba, kuma baki gayamin ba? Ko dai ciki ne?" Amira ta girgiza mata kai alamar A'a. Anty tace "wani irin A'a, in ba ciki ba to wani rashin lafiya ne ze maida ke haka lokaci ɗaya duk kin rame, kamar bake ba, yanzun me kike son ki ci?" "Bakomai" "Kamar yaya bakomai? Gayamin abunda kike so maza" "Anty bana jin yunwa fa" "Aikuwa dolen ki kici Abinci" Anty ta tashi ta fita falo, Ihsan ta ɗaga kai ta kalleta, ta ɗauke kanta ta cigaba da kallo, tana faman hura hanci. Anty tace "Ashe Amira ba lafiya haka?" "Banda abunki Anty, ni na Aureta da zan san tana da lafiya ko kuma babu?" Anty ta sake tabattar da ba zaman lafiya Amira suke da Ihsan a gidan ba, ba ta kuma kula Ihsan ba ta wuce Kitchen ɗin, tuwon semovita da miyar ganye taiwa Amira, ta zo ta sa Amira a gaba da ƙyar taci Abinci, sannan ta ɗauki sample ɗin Amira na jini, tace zata tafi dashi, a kai lap a binciki meke damunta. Amira ta fashe da kuka tace "Anty dan Allah mu tafi tare" "Mu tafi tare saboda me, bayan ga ɗakinki, kuma ba muyi haka da mijinki ba?" "Anty ni dai dan Allah ki tafi dani" "Amira ina na taɓa jin anyi haka, ai bamu nemi Izini ba" "Anty in kin tafi waze kula dani? Kuma bani da lafiya sosai fa" Anty tai murmushi tace "shagwaɓaɓiyya 'yar gidan Anty, Amira in cikin ne ma haka za'ayi rainon cikin da wannan taɓarar? Bari in kira mijinki a waya, idan yake da network in tambayeshi inji me ze ce" Amira ta jinjina kai, Anty taiwa Imran missed calls sun kai biyar, amma wayar taƙi shiga. Tace "Amira wayar Imran ba ta shiga, yanzu meye abunyi?" Gaban Amira ne ya faɗi, kar dai har sun shiga daji? Wata irin ajiyar zuciya tayi, tare da faɗin Hasbunallahu wani'imal wakil. "Amira na lura akwai damuwa a tare da ke, mu tafi taren kawai, in wayar tasa ta shiga na masa bayani, ko in kira Abbanki in gayamasa" Cike da farinciki Amira ta jinjina kai, Anty ta ɗakko hijjabi ta bawa Amira ta saka, ta ɗaukar mata duk abunda take buƙata, suka fito. Ba kowa a falo, Anty tace muje mu yiwa abokiyar zamanki sallama, kan mu tafi" Amira ta girgiza kai tace "A'a Anty, mu tafi kawai, ki ƙyaleta" "No ba za'ai haka ba, ba ze yuwu mu tafi ba muyi Mata sallama ba" Anty na cikin Maganar se ga Ihsan ta fito, hannunta riƙe da plate ɗin Abinci, kallo ɗaya tai musu ta ɗauke kanta. Anty tace "Ihsan, zan tafi da abokiyar Zamanki, bata da lafiya sosai, zan kaita Asibiti, idan da halin dawowa zan dawo da ita, idan babu kuma zan riƙeta se ta warke" "To ni kuma meye nawa a ciki?, Naga bani na Aurota ba kuma ba zamana take ba, ai ba lallai senaji in da zata ba" A ɗan hasale Amira tace "Anty dan Allah ki rabu da ita, taho mu tafi ni jiri nake ji" Ihsan tace "Allah ya raka taki gona, yasa daga nan ba zaki dawo ba" Mamaki ne ya cika Anty sosai, Lallai zargin ta ya tabatta, babu zaman lafiya tsakanin Amira da abokiyar zamanta. Anty ba ta kuma cewa komai ba, suka ƙarasa mota ta saka Amiea a mota suka tafi, suna tafe Amira na ta kuka da ciwon kai da jiri, hakan yasa suka wuce Asibitin da Anty take aiki. A kai mata duk tasa tasan da za'ai mata, amma ba'aga komai ba, babu ciki ba malaria Babu typhoid. Antu ta saka aka gwada BP ɗin Amira, sedai tayi mamakin sakamakon da aka gaya mata, seda ta karɓa ta sake yi da kanta, But still thesame result. Anty ta kalli Amira tace "Amiea, zan tambayeki wani abu, kuma gaskiya nake so ki gayamin, idan kikamin ƙarya, zan ɓata miki rai" Amira tace"to insha Allah ba zan miki ƙarya ba" "Meke damunki haka da yasa jininki ya hau?" "Bakomai" Amira ta bata amsa. "Bance karki min ƙarya ba? A baya an taɓa cewa kina da hawan jini"? Amira ta girgiza kai alamar a'a. "To ne yake damunki da har zaki haɗu da hawan jini a wannan shekarun naki haka? Ki gayamin me kike ciki a gidan Imran?* "Anty bakomai fa, kawai an turashi Zamfara ne, shine na damu kuma ana kashe mutane a can" Anty ta ƙura mata ido tace "ina jinki se kuma me, dan ban yadda wannan ne dalilin da ya sa ki kai wannan ramar ba, lokaci ɗaya haka, ga kuma jininki ya hau ba, da fari na zaci ciki ne, amma tunda ba shi bane, ki gayamin meke damunki" "Anty zan gayamiki, amma kimin alƙawarin idan na gayamiki dan Allah karki gayawa kowa" Anty tace "Naji, ba wanda zan gayawa" Amira ta share hawayen ta tace  "Anty, ni marainiya ce, na tashi ba uwa ba uba, mahaifiyata ita ta fara rasuwa, ina da shekaru huɗu gurin haihuwa, da ta rasu babana be sake Aure ba, babana shikaɗai mamansa ta haifa, abokiyar zaman Yadikko, shima yana matashi mamansa ta rasu ta barshi, dama babansu ne kakana ya fara rasuwa, bayan rasuwar iyayena, Yadikko ce ta riƙeni abokiyar zaman kakata, sedai a zaman da Yadikko tai da kakata, mace ce me bala'in kishi, ta tsani kakata ta azabtar da ita sosai a yadda na samu labari, wannan ƙiyayyar da takewa kakata da iyayena, ita ta shafeni na tashi a wahala, Yadikko ba ta ƙaunata ko ƙaunar cigabana, taso in fi haka lalacewa in tagayyara a rayuwata, katsam akaimin wannan Auren, abun ya tsaya a zuciyarta ita da iyalanta matuƙa, da naso yin bore akan Auren, amma na nutsu nai tunani naga shine rufin Asiri na, duk da zafi da rashin haƙuri irin nawa, amma na danne zuciyata na ƙudiri a niyar zaman Auren, duba da nasihohin da ku kaimin, sedai mahaifiyar mijina ba ta sona, tace in zauna cikin shiri a kowane lokaci zata iya kashe Auren nan, Banda cin mutunci da wulaƙanci da Ihsan takemin, kinga dole inyi haƙuri tunda gidanta ne, ita Miji yake so bani ba, Anty yanzu idan Auren nan ya mutu, haka mariƙiyata take fata, amma ko Auren be mutu ba, ni zan mayarwa Captain abunda ya kashe a Aurena ya sawwaƙe min, tun kan mahaifiyarsa tasa yaimin korara wulaƙanci kamar yadda ta taɓa yimin lokacin da aka kawoni ina ƙarama akace ta riƙeni" Hawaye na zuba Amira take gayawa Anty maganar, jikin Anty yai sanyi ƙwarai, tayi mamakin abunda Ammi tayi, a haka gata wayayyiar mace, amma ya zama na banza, ba tace Komai ba taje ta haɗo wasu allurai ta yiwa Amira, ko mintuna ashirin ba'ayi ba bacci ya kwasheta, Anty ta zauna ta zubawa Amira ido, wani irin tausayin yarinyar yana ratsa zuciyarta. Tafiyar su Amira babu daɗewa se ga Ammi taje gidan, Ihsan ta tashi da fara'arta tana "Ammi sannu da zuwa" "Yawwa Ihsan" "Ammi ba ki gayamin zaki zo ba ina Minal?" "Minal tana gidanku gurin Mummy, ɗazu babansu ya koma gurin aiki, tace min zata ta kwana biyu ba taje ba, mu kai waya ɗazu da Imran ashe kuma zamafara aka tura shi?" Jiki a sanyaye Ihsan tace "wallahi kuwa Ammi, kin ganni nan gaba ɗaya na kasa sukuni, haka na wuni jikina ba daɗi, ina ra masa Addu'a Ubangiji Allah ya dawo dashi lafiya" "Ameen, ni kaina hankalina a tashe yake da wannan tafiyar, sedai ina fatan Ubangiji Allah ya dawo da shi lafiya, amma sam hankalina yaƙi kwanciya ƙarfin hali kawai nakeyi, naji kina kin wuni jikinki ba daɗi Allah yasa jika na kusa na ɗauka" A kunyace Ihsan ta sunkunyar da kai tace "ina cikin damuwar tafiyarsa ne kawai" "Ai shikenan, idan ma ɓoyewa kike dole ze fito a gani, nace ina wannan Yarinyar take ne? Na zo ne inga yadda za'ayi, idan zamanku a tare ze yuwu bayanan, kar inje na saki baki a can ta miki illa" Kwaɓe baki Amira tayi tace "ɗazu uwarta ta titi tazo ta tafi da ita wai bata da lafiya" Ɗan zaro ido Ammi tai tace  "kamar yaya ba ta da lafiya, ba dai wani abune ya faru ba tsakaninsu ba?" "Taɓ, ai Ammi ba wannan zancen, tunda kika zo jiya da daddare take kuka, shine Matar Alhaji Hashim tazo ta tafi da ita wai ba ta da lafiya" "To ai yayai kyau, suje can su ƙarata, sekiyi zamanki ma ki huta, ai na zaci tana nan ne musan abunyi" "A'a sun tafi ɗazu" "To ai hakan ma yafi ai, se mu cigaba da Addu'a, Allah ya tsareshi ya dawo da shi lafiya" "Ameen, insha Allah" Amira kam seda ta kwana ɗaya a Asibiti, Anty ba ta sake yi mata maganar abunda yake damunta ba, aka sassaka mata ruwa da allurai, washegari da Anty ta tashi daga gurin aiki ta tafi da ita gida. Fadila na ganinsu tare ta tarosu, tace "Sannu Amira banje na duba ki ba, ina makaranta Anty tace yau za'a sallame ki" "Bakomai Anty Fadila ai na warkema" "Duk da haka kin rame sosai Amira, amma kin daɗe kina rashin lafiya?" "A'a, ban daɗe ba, kawai dai na rame ne" Anty tace "Fadila kawo mata Abinci" "Aka zubawa Amira Abinci shime da kyar ta ci Abincin nan" Anty tace karta koma ɗaki, tasan idan ta shiga ɗaki kwanciya za tayi, dan haka Fadila ta kaira tayi wanka, ta dawo falo ta zauna. Haka kuwa akayi, tai wanka ta dawo falo ta zauna, Fadila na tai mata hira amma sam hankalin Amira baya kan Fadila, ta ƙurawa TV ido amma ba kallon take ba. Anty ta fito daga ɗakin ta, tace "sannu Amira" "Yawwa Anty" Anty ta zauna kusa da Amira, suka fara hira da Fadila, can Amira tace  "Anty, wai idan sojoji suka tafi daji, a ina suke kwana ne?" Anty tace "Amira kenan, banda abunki ni ba soja ba ya zan in san inda suke kwana? A dajin dai suke kwana" "Anty waye yake basu Abinci kuma?" Anty ta kalli Amira tace "Amira tunanin mijinki kike kenan?" Amira ta girgiza kanta tace "A'a kawai na tambayeki ne" "Hmm Amira kenan" Har sunyi shiru Amira ta kuma cewa "Anty lambar Captain ta na shiga kuwa?" "Amira, Imran yana nan lafiya fa, kin san jininki ya hau amma kina ta sake ɗaga hankalinki, munyi waya da shi jiya ma, ki kwantar da hankalinki kinji Amira" "To Anty" Gaba ɗaya tausayin Amira ya kama Anty, lallai Amira ta damu da Imran matuƙa. Haka Anty taita ƙoƙarin kwatarwa da Amira hankali, kwanan Amira uku a Gidan Anty, Alhaji Hashim ya dawo gida, yai mamakin ganin Amira a gida. Yace "Amira lafiya dai ko, naga kin rame haka?" Amira tace "lafiya ƙalau Daddy, bani da lafiya ne kawai" "Subhanallah, to Ubangiji Allah ya sawwake" "Ameen Daddy" Seda suka shiga ɗaki Daddy ya nutsu yaci Abinci, sannan yace "Naga Amira a gida, tace min dai bata da lafiya, ina fatan hakane" Anty tace "to kusan hakane Daddy, Sau ɗaya Allah ya bani haihuwar yara tagwaye, amma ji nake kamarni na haifi Amira, duk da na riƙe yara da yawa kan Amira, amma ƙaunarta daban ce a raina, saboda ina matuƙar tausayinta fiye da yadda kake zato, nasan maraici nasan zafinsa, abokinka Alhaji Ali ya aurawa ɗansa Amira bisa ga yin katanga ga lalacewar da tayi, amma ka sani ba'a gyra ɓarna da ɓarna, shekaranjiya Imran ya tafi Zamfara, ya kirani akan cewar Matarsa ba lafiya, naje na tarar tayi rama sosai, na zata laulayi ne, sedai bisa ga binciken da nai damuwa ce cunkus a zuciyar yarinyar nan, ta yadda ta kai jininta ya hau fiye da tunani, a abunda ta gayamin, uwarmijinta na barazanar zata kashe mata Aure, bamu haifeta ba amma tayi biyayya ga maganarmu ta rungumi zaman Aurenta, amma mahaifiyar Imran da kishiyarta na muzguna mata, duk da ta ɓoye laifin Imran ba ta gayamin ba, amma nasan tabbas shima akwai tasa gudummawar a abunda ake mata, tana gudun mutuwar Aurenta, saboda inda ta fito suma ba ƙaunarta suke ba, duk da bakomai ya gayamin ba, na lura tana da ɓoye sirrinta, amma banji daɗin abunda Hajiya Jamila takeyi ba, itana fa uwace ta haifa, ni idan abun baze yuwu ba, idan Allah ya dawo da shi, ya rubuta takarda ya saketa, ni ina so zan riƙe kuma insha Allah, duk da abinda suke zargin tayin zata samu miji nagari, mata nawane sukai karuwanci aka Auresu, aka zauna da su suka dena abunda suke, Ihsan 'yar gwal ce ta ba zata zauna da kishiya ba, to idan baya so ya saketa ni zan riƙeta, ba yau na fara riƙe 'ya'yan wasu ba, acikin hamshaƙan mutanen nan zan samo mata miji, wanda ze riƙeta" Bilhaƙƙi Anty take faɗa, dan seda ƙwalla ta taru a idonta, Alhaji Hashim yace "easy Maman Yara, kwantar da hankalinki mana, ai abun duk be kai haka ba, ki kwantar da hankalinki, zanyi magana da Alhaji Alin, abun baze kai ga saki ba" "Gara dai kuyi maganar, tun wuri yasan matakin da ze ɗauka, dan idan hawan jini ya kasheta matarsa ce da matar ɗansa suka kasheta" "Allah ya baki haƙuri maman Amira" Alhaji Hashim yaita bawa Anty haƙuri yana rarrashin ta. Amira kuwa wayar Anty ta ɗauka, ta ɗau lambar Imran, ta koma ɗakinta ta dinga kiran wayarsa, amma a kashe bata shiga, hakan ya ƙara ɗagawa Amira hankali, ba ta taɓa tunanin Ta damu da Imran haka ba, bata iya baccin kirki, haka zata tashi tai nafila cikin dare tana addu'a Allah yasa yana lafiya. Da safe Anty ta aika Fadila akan lallai Amira ta fito falo, ta karya tare dasu, dan in aka kai mata ɗaki baci take ba. Haka Amira ta fito, har ƙasa ta durƙusa ta gaida Daddy ya amsa cikin sakin fuska yace "'yar Antyn ta ya jikin naki?" "Naji sauƙi Daddy" "Masha Allah, Allah ya ƙara sauƙi" "Ameen Daddy, Anty ina kwana?" "Lafiya ƙalau, maza zauna a zuba miki Abinci". "Anty Azumi nake ai" "Azumin me baki da lafiya?" "Azumi nake Allah yasa Imran ya dawo lafiya, ana ta kashe su a daji" Tai maganar hawaye na zubawa daga idonta, Anty ji tai kamar tayiwa Amira kuka, tabbas Amira ta fara son Imran ne. Daddy yace  "banda abunki Amira, ke da baki da lafiya ina ke ina Azumi? Addu'a ma da kike masa ta wadatar, yana nan lafiya insha Allah, zauna kici Abinci" Suka tursasa Amira, tana ci tana goge hawaye, ita kanta bata san ta damu da Imran haka ba, se daya tafi wannan Yaƙin. Bayan ta gama Anty ta bata magani ta sha, ta koma ɗakinta ta ɗau wayarta ta kuma kiransa amma a kashe, message ta rubuta masa kamar haka. "Assalamu alaikum warahmatullah, duk da bani da tabbacin a wani hali kake yanzu, na kira wayarka ba ta shiga, amma ina fatan kana cikin ƙoshin lafiya, Ubangiji Allah ya tsareku, ya baku nasara akan abunda kuka je yi" Ta gama rubuta message ɗin ta ajiye wayar a hankali, tare da lumshe idonta, ta na addu'ar Allah ya dawo da Imran lafiya, duk da baya sonta, amma tana jin kamar yana da mahimmanci a rayuwarta, rashin sa shima ze sake barin wani babban giɓin a rayuwarta. Kamar yadda Alhaji Hashim be yiwa Alhaji Ali maganar nan ba, saboda yasan Alhaji Ali da haƙuri amma yana da zuciya sosai, yasan yadda Alhaji Ali ke murna da Auren Amira da Imran, yana jin hakan kamar wanke laifinsa na baya ne, muddin yaji wani abu na Ammi na ƙoƙarin kashe Auren, tabbas za'ayi ba daɗi, dan haka yai shiru da bakinsa ya ƙuduri se Allah yasa Imran ya dawo lafiya ze zauna da shi. Ihsan kam hankalinta kwance take zuwa service ɗinta, ita kaɗaice a gidan ba kowa, taje inda take so ta dawo sanda ta ga dama, wataran ma ta kwana a gidansu. Seda Imran ya shafe kwana Ashirin da biyar babu wanda yaji daga gareshi, Amira duk ta sukurkuce, ta dami kanta ta gaza nutsuwa sam, se aikin koke koke da take fama da shi. Alhaji Hashim ya gayawa Alhaji Ali, cewar Amira tana gidansa ba lafiya, Alhaji Ali baya gari amma ya kira babbar 'yarsa Hadiza taje ta duba Amira, bayan ita Babu wanda yaje dubata. Ranar da Imran ya kwana Ashirin da takwas, Alhaji Hashim ya shigo ya tarar da Anty a Falo yace  "Maman Yara, Alhaji Ali ze shigo garin nan cikin dare insha Allah, an bada sanarwar gobe in Allah ya kaimu tawagar su Imran zasu dawo, da yawa daga cikin su sun rasa rayukansu, dan haka gobe in Allah ya kaimu zamuje mu gani, yana rayen ne ko kuma ta Allah ta kasance, dan tunda suka tafi sau ɗaya babansa yai waya da shi" "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Allah yasa ba abunda ya sameshi, wayyo Allah na" Gaba ɗaya suka juya inda Amira take, ashe tana Kitchen basu sani ba. Da sauri Anty tai kanta tana faɗin "Amira calm down ba fa mutuwa yai ba" "Anty i give up, dan Allah Daddy ya gayamin in ya mutu' Daddy yace "ba mutuwa yai ba, zuwa zamuyi mu ɗakko shi" "To dan Allah zan biku" "Naji, amma ki kwantar da hankalinki kinji, Allah ya kaimu goben" Da ƙyar suka lallaɓa Amira, ta haƙura. Alhaji Hashim yace "Ina ganin ikon Allah, gaskiya Yarinyar nan ta tashi hankalinta da yawa". Anty tace  "hakane, ni fatana Allah yasa kar ya gane tana masa wannan son, ya dinga wahalar da ita, amma yanzu ka amsa mata da itan zaku tafi?" "To idan ban amsata ba ya zanyi, kina ganin zata sume a gurin" "Allah yasa yaron nan yana nan ƙalau," Ya amsa da "Ameen" Amira tunda ta idar da sallar Asuba take zaune, tana lazumi gari na fara haske tai wanka, ta saka kaya ta fito Falo. Daddy na fitowa tare da Anty suka ganta zaune a Falo, Anty jinjina kai kawai tayi dan mamaki. Daddy yace "to Amira taso mu tafi, sedai ki zama me tawakkali da koma me zamuje mu tarar kinji ko?" Amira ta jinjina kai, ita dai Anty ba ta so aje da Amira ba, saboda ba ta san me zasu tarar ba. Haka ta shiga mota, suka tafi gidan Alhaji Ali suka fara zuwa, suka tarar Ammi tana ta kuka, tace itama da ita zasu tafi. Abba yace "Hashim ya na ganka da Amira, haka kika rame haka?" Alhaji Hashim yace "ba dole ka ganni da ita ba, ta tashi hankalinta da yawa shiyasa nace gara mu tafi tare" Suna nan suna tattaunawa, Ammi ta fito ita da Minal, sedai tana ganin Amira tai turus ta haɗe rai tamau, Amira ta gaisheta amma tai banza da ita. Suka ɗunguma a mota suka tafi, suna tafe kowa da abunda yake saƙawa a zuciyarsa, Amira ta shiru tana ta addu'a a zuciyarta. Motocin sojojine da yawa a gurin, ga sojoji manya da ƙanana da mutane a gurin, kowa yana duba nasa, ga gawarwaki ana ta firfito dasu. Suka firfito daga Mota, ƙirjin kowa na dukan uku uku, dan basu san me zasu tarar ba. Alhaji Hashim yace "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Ubangiji Allah ya jiƙan musulmin ciki da suka rasu" Jiki a sanyaye Abba yace "Ameen" Ammi se kuka take ita da Minal, Amira kam zuciyarta harta bushe, hawayen sun dena zuba. Amira ce ta tafi da gudu, ta kutsa cikin sojojin nan, Abba yace "Subhanallah, ina zata kuma? Tana hayyacinta kuwa?" Babu zato yaji an rungumeshi ta baya, be motsa daga inda yake ba, kuma be waigo ba, sun kwashi wasu daƙiƙu a haka, a hankali yasa hannu ya janyota daga bayansa, sake rungumeshi tai tana hawaye tace "Alhamdilillah, You Are alive Captain" Jikinsa gaba ɗaya a sanyaye, ganin Yadda Amiran tai wata uwar rama, Amirama mamakin ramar da yayi take, yai baƙi Uniform ɗin  jikinsa sunci ƙaniyarsu suma, wani gurin duk ya yayyage, kallo ɗaya zakayi masa kasan an fafata a filin daga. Ɗan murmushi yai ya ɗagota daga jikinsa yace "ke da wa kuka zo?" "Da su Abba, da Ammi" "To ki dena kukan mana tunda ban mutu ba" Murmushi tayi amma hawayen suka ƙi tsayawa, yasa hannu ya goge mata hawayen yace "ɗagani, karki ɓata kayanki da datti" "Bakomai zan wanke" Ya riƙo hannunta, suka fito inda su Ammi suke, Abba yai murmushi yace "Alhamdilillah" Ammi da Minal suma suka tafi inda yake suka rungumeshi. Alhaji Hashim yace

Chapter 21 of 31