Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
My Own, kishine ya rufemin ido, ina sonka sosai" "To yanzu me kike son ayi?" "Dan Allah ka dawo" "Na riga na dawo bakin aiki, se ƙarshen wata zan dawo" "Dan Allah kayi haƙuri, am missing You am sorry please" Imran yai ajiyar zuciya yace  "Shikenan naji, ki kwantar da hankalinki, zaki biyoni nan ne?" Da sauri tace "Eh zan biyo ka" "To shikenan, zan turomiki kuɗi ki biyo jirgi ki taho" "Alhamdilillah, insha Allah zan taho, amma kamar baka haƙura ba My Own" "Ya wuce mana, karki damu take a very good care" Ihsan taji daɗin ɗaga wayarta da Imran yai, nan da nan ta fara shiri, domin zuwa ta riski masoyinta a Ikko. Anty kuwa tana matuƙar jan Amira a jiki, hakan yasa ta saki jiki da Anty sosai, suna matuƙar mutunta ta da girmamata, ba hantara ba tsangwama ba Komai, Anty tana ta monitoring ɗin Amira da son gano matsalolin Amira, sedai a zaman da sukai Babu wata alama da ta gani da take nuna rashin jin da ake faɗa akan Amira. Tana girmama kowa, sedai kusan kullum setayi zancen dama irin Mijin Anty Fa'iza ta Aura. Yanzuma suna zaune a falo suna kallo, Fadila da Amira suna hira, Anty Fa'iza ta kira Amira  "Amarya bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida" Amira tace  "Malama uwargida dai sarautar Mata, ko kin manta ni aka fara ɗaurawa Aure"? Seda Anty ta kalli Amira tai murmushi, tare da girgiza kai. Fa'iza tace  "mara kunya, Allah ya baki haƙuri, Uwargida Imran, ya kike ya mutan gidan?" "Lafiya  ƙalau, ina 'ya'yana ina ɗan aljanna?" Fa'iza tace "duk suna lafiya, ɗazu ya gama zancenki kan ya fita, yace in kira ki ince yana gaisheki" "Allah sarki Yaya Bashir nawa, kice ina amsawa ya dena nemana ko?" "Haka kurum ya nemeki yai miki me? Ranar da Sultan yazo nemanki ya bani labarin shaƙar da Imran yai masa, haka kurum nima a shaƙen miji" Amira tai dariya tace  "haba dai, ai duk ke kika jamin wannan abun, da tun farko kin Auri Alhaji Yahaya, nikuma na Auri Abu Khairat da ba shikenan ba" Fa'iza tace 'mara mutunci, ai gara da aka miki Auren, na fuskanci da zaki samu dama sekin Auri mijina kin zama kishiya ta" "To tun yaushe ma, ke Allah ne yasa mijinki ne, da mijin wata ne ai da sedai taji wani zancen" "Taɓ kishi da irinki se macen da ta shirya ai, gara dai da kika Auri Imran ɗin shine dai dai dake" "Kyaji dashi dai, anjima zan kiraki ki haɗani da Khairat a waya, inji muryarsu" "Zan haɗaku Insha Allah, dan kusan kullum se sunyi zancenki suce min wai yaushe zakizo, gidanku kuwa sunata sababi wai an Aurar dake basu sani ba" "Mhmm, ni nama rasa me zance, kuma suna raina wallahi, duk cikinsu ba wanda ya kirani ko a waya, ni zan nemesu insha Allah zan kira su in gaishesu" "Shikenan, ds kin kyauta ki gaida mutan gidan". "Zasuji insha Allah"  Amira ta kashe wayar. Anty tace  "Amira wai ya kuke da Fa'izan nan ne?" "Yayata ce, cousin ɗina ce" "Amma kike gayamata  zaki Auri mijinta?" Amira tai murmushi tace  "tasan tsokanarta nake ai" "Anya baza taji ba daɗi ba, koda yake ai kema kinyi Aure yanzu". "Idan ma tana ji sedai tayi haƙuri, dan mijinta yayi a rayuwa, irin wannan mijin haƙurinsu idan baka musu biyayya ba se su kaika wuta, baya fushi sam da wuya, ko faɗa sukayi bata da gaskiya amma dan a zauna lafiya se yaita bata haƙuri, idan nike da mijin Anty Fa'iza, ai binsa zan yi sauda ƙafa, bazan bari ma yai fushi ba, itama ta sha wahalar rayuwa Allah ya musanya mata da mafi Alkhairi" Fadila tace  'to shi Imran ɗin da Allah ya baki, ba zaki bishi sau da ƙafan ba?" Murguɗa baki Amira tayi ta ɗauke kai, alamar ba wannan maganar. Anty tace "A'a shina zata bishi sau da ƙafan mana, ai Amira Yarinyar kirkice, next week insha Allah Ina son muje dake Kasuwa ki zaɓi abunda kike buƙata, amma za'a kirashi ki fara tanbayarsa tukuna" Amira tana jin abunda Anty ta faɗa amma ta basar kamar bata ji ba. Ranar juma'a da yamma, Ihsan ta sauka a garin Lagos, Imran da kansa yaje ɗakkota a airport, tana ganin Imran ta tafi da gudu ta runguneshi, shima rungumetan yayi yana murmushi yace 'i miss You my Ihsan". "Miss you too Hubby" Suka shiga motarsa suka tafi, tun kan ta sauka tuni yasa anyi order Abinci ya ajiye mata. Gidansa a cikin Barrack yake, flat ne madaidaici me kyau sosai, gidan ya burgeta sosai, tai wanka ta canza kaya suka zauna suna cin Abinci, tana sake lallaɓa Imran tana bashi haƙuri, dan ta lura be huce gaba ɗaya ba. Ihsan an haɗu da maza, dan yau Imran ya samu abunda yake so a gurin Ihsan, hakan yasa ta wanke duk laifin da tayi masa, sedai Ba laifi ta ji jiki, gaba ɗaya Imran ya manta sunyi faɗa, suka jone suka shiga sabuwar Rayuwa shida Ihsan, me cike da soyayya da kulawa, gaba ɗaya ya manta da wata Amira a rayuwarsa, se daga baya ma Ammi tasan Ihsan tabi Imran. Amira tai waya da Anty Fa'iza tace "taje gidansu ga kwasar mata kayanta gaba ɗaya, ta haɗa mata dana wajenta ta ajiye mata" Da la'asar Amira ta fito ta samu Anty a Falo tace  "Anty, ina son zani wankin kai, dan Allah kisa a rakani" Anty tace  "Eh gaskiya yakamata kam, dam kuma nayi miki zancen zuwa kasuwa, bari a kira Imran ki nemi izninsa" Haɗe rai Amira tayi tace "Izini kuma?" "Eh mana ba mijinki bane, seda izininsa sannan zaki fita" Amira ta ɗan kumbura fuska, wai mijinta tunda sukazo da daddare shi da Abba, be ƙara bi takanta ba, ko ya kira yaji halin da take ciki ba, se yanzu za'a wani kirashi wai a tambayeshi zata fita, fan tana jin nauyin Anty ne da wallahi ba zata kulashi ba itama. Ganin lambar Anty tasa Imran ya ɗaga wayar, dan seda yaga lambar Antyn ne Amira ta faɗo masa, ya ɗaga da fatan Allah yasa ba wani abun tayi musu ba. Anty tace "Ango wannan shiru haka, ba amo ba labari baka ko waiwayar matar taka" Cikin jin nauyi Imran yace "wallahi Anty Nafisa abubuwa ne suka ɗanmin yawa, harkar aikin namu ne ba sauƙi" "Ka koma bakin aikin kenan?" "Eh na koma tuni" "Ahh to masha Allah, kace Ihsan ɗinma tana nan ka barta?" "A'a Ihsan tana tare dani, da ita na taho muna nan gaba ɗaya" Kasancewar wayar a hansfree take, Amira tana jin maganar da suke, aikuwa nan da nan Amira ta haɗe rai. Rainin hankali, ita am barta a nan bata ga tsuntsu bata ga tarko, ita ba matar Aure ba ita ba sakakkiya ba tana zaune a gidan mutane, dan ita bata ma san zaman me take a gidan ba, Amma ya ɗau matarsa sunyi tafiyarsu, irin zaman da zataje tayi a gidan nasa kenan? Ta tambayi kanta. Anty tace "dama Amira ce tana son taje gyaran kai, kuma ina son taje Kasuwa zamuyi 'yan saye saye, nace bari in kira mu nemi Izini" Imran yace "seta dawo" "A'a bari in baka ita ku gaisa, ta tambayeka da kanta" Anty ta miƙawa Amira wayar, Amira kamar karta karɓi wayar nan, zuciyarta se wani tafasa take kamar ta tsaga ƙirjinta ta fito. Tasa hannu ta karɓi wayar, ta danne fushinta tace "Yayana barka da yammaci ya aiki?" Imran a ransa sabon salon rainin wayo. Ya basar yace "Alhamdilillah" "Dama zanje a gyaramin kai ne, Shine nake neman Izini" "Sekin dawo" Imran ya bata amsa. 'Nagode, ka gaishemin da ƙanwata kuma Yayata, wato Amaryata" Daga nan ta kashe wayar, ta sake haɗe rai ta miƙawa Anty wayarta. Ba ƙaramin mamaki Amira ta bawa Anty ba, ga kishi nan ƙarara a fuskarta, amma ta danne taiwa Imran magana cikin nutsuwa. Anty tace  "Amira kishi haka?" "Anty wane irin kishi kuma? Ni ba kishi nake ba" "To me kikeyi?" "Bakomai" ta faɗa kamar za tayi kuka. Anty ta jinjina kai tace "lallai gidan Imran akwai kallo, Amira kishi ne gashi nan ƙarara a fuskarki, sedai kin birgeni da kika ɓoye kishin naki, baki nuna masa ba" Amira kasa magana tayi, kawai ta tashi ta tafi ɗakinta, danji take kamar an ɗora mata dutse a ƙirjinta, jin Imran na can shi da matarsa, ita kuma an barta a nan. Anty ta jinjina kai tace "taɓɗijan Amirana kishi tun yanzu?" Amira kam tana zuwa ɗakin ta rufe ƙofa ta tsaya tana sauke numfashi, tace  "Lallai ma an rainamin hankali, zaman da zanje inyi a gidan nasa kenan, ita yana sonta ya bata kulawa ni kuma ina kallonsu? Baze yuwu ba, ba zanyi boranci a gidamu, inzo gidan miji ma inyi boranci ba, dani suke zancan da shirina zan tare a gidan Imran, ba zan ɗau kowane kalar cin kashi ba, zan nuna musu WATA KISSAR..... Sai mata!!! (Wanda be karanta littafin wata kissar sai mata ba, an barshi a back 😜😜😜🤪) Gaskiya ba ƙaramin jin daɗin sharhin ku nake ba, shiyasa nake muku dogon page, ina godiya da kulawa masoya 🥰😍😍😍😍🥰 Share Please Follow me on watpad@ Ayshercool7724 Domin gyara, Sharhi ko shawara 07063065680 [1/25, 8:34 PM] Ayshercool:       🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 WUTA A MASAƘA PERFECT WRITERS ASSOCIATION (WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS) https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P. W. A *Story and written by* AISHA ADAM (AYSHERCOOL) The experience writer of *ABDUL JALAL* * WATA KISSAR.... (SAI MATA) *BAƘIN TABO (Labarin gasa) *AƘIDATA (Paid Book) * WUTA A MASAƘA https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in ❌❌❌ Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.                          27_28 Imran kam seda ya ƙarewa wayar kallo, tare da jinjina kalmar Yayana da Amira ta kirashi da shi, yasan wani sabon iyayin ne yasa ta faɗi haka, wani gajeren tsaki yaja, ya ajiye wayar ya cigaba da aikinsa. Amira kam tunda ta shige ɗakin nan bata sake fitowa ba, ta zauna ta dinga saƙawa tana warwarewa, tana tunanin irin zaman da za tai a gidan Imran, daga Imran har matarsa da danginsa babu me ƙaunarta. Imran kam ya samu nutsuwa sosai, hankalinsa a kwance yake sosai, cin amarcinsu kawai suke da Ihsan. Yana kwance yana kallo, Ihsan ta fito tana yamutsa fuska, ya kalleta yace "My beb, ya dai naga kina ɓata rai?" Ƙarasowa tayi ta kwanta a jikinsa tace  "yau bana jin daɗin jikina gaba ɗaya" Murmushi yai ya shafa dogon gashinta yace  "kodai kodai?" Ihsan tace "kodai me?" "Ko an gamune, kin sama mana Baby?" Gaban Ihsan ne ya faɗi, a ranta tace ji wata Magana, daga yin Auren se maganar ciki. "Ya naji kinyi shiru ne?" "My, daga yin Aurenmu se ciki kuma, ko gama cin amarcin banba se ciki, kasan fa ciki yana bawa mata wahala sosai" "To meye a ciki Ihsan? Ai Arziki ne da yawa suna nan suna nema basu samu ba, ina fatan Allah yasa ciki ne, ko biyu ki haifamin sekiyi planing ki huta" "My D Service ɗina fa?" "Bakomai, Allah baze hana mu yadda zamuyi ba, Allah ya bamu masu albarka" Yai maganar yana kissing goshinta, murmushi kawai tayi ta rungumeshi sosai ta lula duniyar tunani. Amira ta kai kwana biyu kafin ta sake sakin ranta, dan duk batun Imran ta dameta, Anty kuma tana ankare da ita, ta tausaya Amira matuƙa, ta fuskanci Amira nada kishin gaske sedai kuma ta iya siyasa sosai da sosai. Amira tana cin Abincin Safe tana ta cakala, ba wani ci take sosai ba, Anty tace "Amira, anjima ki shirya zamuje kasuwar, idan yaso gyaran kan gobe in Allah ya kaimu se Fadila ta rakaki" Amira tace "to Anty, bari in gama se in fara shiri"  ta kammala cin Abincin, amma maimakon ta tashi seta ɗakko wayarta ta kira layin Yadikko, amma bata tafiya, seta kira ta Usman. Seda ta kusa katsewa sannan ya ɗaga yai Sallama. "Yaya Usaman manyan gari, ko nemana ma ba'ayi ko, wato Allah ya rabaku dani babu me neman inda nake, bakomai rayuwa ce" Usman yace "Ni mamakine ma ya kamani a ina kika samu lambata?" "Ji wata tambayar rainin hankali, dama can ina da ita ai" "Kina da ita amma baki taɓa kirana ba ai, kuma wake da lambarki a gidan nan? Ba wanda yake da lambar ki" "Hmm duk da haka wannan ba uzuri bane, ai da kukaji labarin Aurena haka ba shiri, kwace bari kuji ya wannan marainiyar take ciki, meyakamata ayi mata? Koda yake ai ba sona kuke ba, nice dai duk inda na shiga kuna raina, yanzu ya kake ya gidan?" "Lafiya ƙalau Alhamdilillah, ya amarci ina mijin naki?" "Yana Lagos gurin aiki" "Naji ance ai baki tare ba ko?" "Eh ban tare ba, amma nakusa insha Allah, Ina su Sadiya da Yadikko uwar faɗa" "Kowa lafiya ƙalau" "Kai musu wayar mu gaisa, na kira ta Yadikko bata shiga" 'to bari in kai musu" Ya shiga cikin gidan da wayar a hannunsa, ya tarar da Yadikko na shan koko da ƙosai, ya miƙa mata waya yace "gashi za'ai magana dake" Ta kalleshi tace "waye?" "Karɓi kiji mana" Yadikko ta krɓi waya ta saka a kunnenta. "Hajiya Yadikko me abun mamaki, ba faɗa meya kawo gaba? Har labarin Aurena ya riskeki amma ki gaza nemana, ko kice ya nake ciki? "To in nemeki ince miki me? Ko in miki me?" "Ba abunda zakimin, amma ko yaya ai kyanuna kin damu dani, amma dai shikenan ya kuke yasu Baba da kowa da kowa?" "Ji yadda kike wani tambaya ya suke, irin kin damu dasu ɗin nan, aifa kin damu dadu da baki haɗa kai da wan uwarki anmiki Aure ba izininmu ba" "To ni meye nawa a ciki, yadda baku san da labarin Auren ba nima ban sani ba, sama taka naji wai an ɗauramin Aure da Imran" Yadikko tace "to amma kuma kika zauna? Aida seki ce masa bakya son sa, akanme za'a miki Auren dole, ni kik ban mamaki m, ina bakin nakinda tsiwar taki, da har zaki bari a miki Aure ba saninki kuma ki zauna kiyi shiru?" "To Yadikko idan ban zauna nayi shiru ba me kike son inyi?" "Ai irin haka ski ce masa bakya so, ko kina son Imran ɗin ne? Ina kwanaki har nan gida yazo ya sameki ya dinga tamaula dake a gidan nan, kuma nan akazo aka bania labarin ana gibe ɗaurin Aure ya kamaki ya zane, to da irin wannan zaki zaman Aure, ai irin haka kamata yayi ki gayawa babansa bakya son sa" Amira tai murmushi tace "Yanzu Yadikko, kawai se in dubi tsabar idon Abba ince masa bana son ɗansa, to ai duk isaknacina wasu lokutan nasan abunda yakamata da wanda be kamata ba" "To Yanzu dai zama zakiyi dashi kenan? Ya dinga muzguna miki yana dukanki? Nifa da cewa nayi ko ƙararsa zamuyi, ya Aurar dake ga ɗansa ba izininmu, kuma ɗan nasa ma har dukanki yakeyi dan a ƙwatar miki haƙƙin ki, idan yaso ko raba Auren ne ayi, ki fito ki auri wanda kike so yake sonki" "Taɓɗijan aikuwa da kun kai ƙara da kunji Kunya, dan bazan yadda a kashemin Aure ba, kinga kajin da nake ci kuwa, Allah ya hutar dani ya rabani da Karuwanci da kuke faɗa ya rufan Asiri in tonawa kaina, ai ba dani ba, zamana zan in lumui a gidan, koda ze dinga dukana kuwa, balle ba duka ba zagi tsakanina dashi, lallaɓani ma yakeyi, kin san Karuwa da shiga rai, mussaman yadda na goge a iya duniyanci, nan komai available baki ga da kazar dana karya ba yanzu haka, ga shayi me kauri falo da AC, ga luntsumemen gado, anjima in tashi in saka matsatsun kaya, koma tsirara in taka masa rawar gala a gabansa ya kalleni yana murmushi, yaushe zan yadda amin sagegeduwa, an rabani da bin kwararo da wannan gidan namu gidan tashin hankali, aini Allah ya rufan Asiri, su Sadiya ma ina musu Addu'a Allah ya ɗaga su daga wannan gidan ko dan tijararki"  Amira tai maganar tana wani makirin murmushi. "Yanzu Amira ni kike gayawa, kina rawar gala tsirara a gaban miji?" "Au nayi a gaban wasu banzaye ma balle mijina, meye amfanin ƙirar da Allah yaimin in dai bazan juyasu a inda ya dace ba, gari banza ma naje nayi an min liƙi, balle yanzu da nake me dalili na ibada" Yadikko tace "Amma kuwa idan hakane wannan Imranan munafuki ne, yaita nuna yana jin haushinki, baya ƙaunarki amma ya aureki, harma ya saki jiki dake?" "Au kina mamakine Hajiya Yadikko, Amira ce fa ai bari kawai wani abun baze faɗu a waya ba, kusa lokacin da za kuzo kema kici kajin nan da nake ci, da ina kusa da sena dinga aiko miki ki adana tsufanki, yanz idan nace na gaji da naman kaza, anjima Imran ze aiko da na zabi, aini Alhamdilillah Allah ya 'yanto ni" Wani irin baƙin ciki ne ya tikare zuciyar Yadkko, wato Amira ma jin daɗinta takeyi, taso ace tana can tana wahala amma taji saɓanin haka. "Yadikko ya naji kinyi shirune? Ki gaida Mutan gidan gaba ɗaya, zanje in ɗorawa Mijina sanwar rana" "Amma naji kina da kishiya ko?" "Eh, ina da kishiya mana" "Kuma lafiya kuke zaune da ita?". "Ai ba ruwan wani da wani nida ita, kowa zaman kansa yakeyi, Yadikko se anjima, zanyi girki in gyara jikina, sannan Anty Fa'iza zata zo ta ɗebar min kayana na nan gidan Please, duk abunda aka san nawane kar a taɓamin" Amira ta katse wayar, ta ɗan tsurawa wayar ido, wasu hawaye suka cika idonta, ta rasa meyasa Yadikko bata son ganin duka wani abu na cigaba ya raɓeta, ta fison ta ganta a wahala da tashin hankali, tafi son taga ta wulaƙanta, sama batayi murna da jin abunda Amira ta faɗa ba, so tai taji Amira tace tana cikin wahala. Amira tace "ya Ubangiji Allah, ka jiɓanci lamurana, kaimin ɗauki akan zaman da zanyi a gidan Bawan Allah nan, Allah karka kawo dalilin da zesa maƙiya suga hawaywna ko su ganni a rana, Allah yadda suke ƙina kar bani ikon ƙinsu ko cutar dasu, Allah ka shiryesu ka ganar dasu ka maida su kan tafarkin ka madaidaici" ta ƙarasa addu'ar a hankali cikin karaya. Yadikko kuwa cewa tai "ni ungo wayarka, munafukar yarinya 'yar hau, ni zata kira ta gayawa daɗin Aure, dan ubanta tun kan a haifi uwarta nai Auren nan nima, amma dan fitsara harda gayamin tana zama tsirara a gabansa, yo aikin banza ma, tsirara nawa tayi a gaban ƙarti daban daban, shima shashasha soloɓiyo, namijin hotiho ya rasa wadda ze Aira se Wannan karuwar, dama tana tafiya tuɓi tuɓi da mazaunai ai dole su tsole masa ido ya Aureta, duk wannan hantarar da zagin da yake mata ahse kurin banza ne" Amina tace "ai bazaki san kurin banza bane, se kinga irin shegen dukan da yayi mata daren da za'a ɗaura musu Auren nan, ya farfasa nata jiki da duka, ke bakyace Aurarta ze ba" Sadiya tace "nifa ban yadda da abunda ta faɗa ba, wannan Yarinyar makirace maƙaryaciya, ya za'ai mutum yana sonkabya maka wannan dukan" Amina tace "ke bar maza da gulma, kin san uwarsa fa ba son ta take ba, se iya dukan nata dan yai pretending, amma ai a ɗakinsa ta dinga kwana, kuma takanas yazo har garin nan ya ɗauke ta, ke ƙaddara ma baya sonta, Yarinyar da ta saba bik mazama, ina ga shi, shima barikin zata masa ya manne mata" Yadkko tace "dan abun takaici, kalli koko nake sha babu ko sikri, ƙosan nan kamar a jefi gardi dashi dan tauri, shi kansa yajin ƙosan kafi zabi yasha babu maggin kirki a ciki, amma wai tana can tana cin kaza, kai Allah ya isa, yanzu da kuke Auren yaron nan, ai da ɗaki za'amin a gidan wallahi inje in tare nima in ɗan murmurw" "Yanzu dai ki dena cin zarafin ƙosan nan, ki daure ki cigaba da tura abunki" cewar Aminaa. "Ke barni ni takaici baze bari in ƙarasa cin wannan gardin ƙosan ba, 'yar banza Allah yasa duk lokacin da taci kazar taita zawayi, ya zamana ba ita ba cin kazar gaba ɗaya. Haka Yadikko taita soko burutsunta, taita bayyana hassadarta ƙarara akan Amira, ba tare da kunya ko tsoron Allah akan hakan ba. Amira kuwa wanka taje tayi, ta shiraya a cikin riga da skirt da dogon hijjabi. Ta fito domin su tafi kasuwa, suna tafe a hanya suna hira, Anty tace  "Amira, me kike ganin za'a saimiki da sadakin ki ne?" "Bakomai" ta bata amsa. "Kamar yaya bakomai, ki faɗi me kike so, inya kama ayi ciko a saimiki, Abbanki ne yaimin waya yace a tambayeki" "Nifa Anty kome kuka siya yayi shikenan" "Ke a ranki babu wani abu da kikeso?" "Eh, bana son komai ni dama ki riƙe na bar miki" "Tunda tare zamuyi zaman Auren dake ko? Yarinya gara kici Sadakinki, Addini ne ya halarta miki abunki" Amira bata sake cewa komai ba, ta dinga kallon titi da gurare, tana sake ƙarewa garin kallo har  suka kai wani ƙaton shagon saida kayayyaki. Bayan sun isa ne Anty tace "muje duk abunda kike so ki ɗauka, banda alkunya naga wasu lokutan akwaiki da kawaici, An bada isashen kuɗi ayi miki siyayya" Amira tace "to" Suka shiga, sukayi siyayya sosai, suka taho hanya aka bada kayan Amira ɗinki, da wanda Antyn ta siya suka nufi komawa gida. Misalin ƙarfe tara na dare, Ihsan ta gyara gado ta shiga wanka, ta fito sannan Imran ya shigo ɗakin, ya nemi guri ya kwanta yana kallon Ihsan tana shiryawa. Ta kalleshi tace "ya da kallo hakane?" "Au to kar in kalleki? Idan ban kalleki ba wa zan kalla?" "Babu, gara kaita kallona" Yai murmushi yace "yakamata ki tsahirata wannan shafe shafen, kizo ki kwanta haka" "Ka barni in kinatsa a hankali kayi baccinka ban hanaka ba" "Bazan iya bacci ba kya jikina ba" Wani murmushi ta kuma yi masa sannan tace "to shikenan my D, gani nan" Ta saka night gound ɗint, sannan ta nufo gadon tana masa murmushi, tana ƙarasowa ya janyota kan gadon yana murmushi yace "the beautiful lady my eyes ever saw in the earth" "Kaji ka, duk kyawawan matan da suke garin nan?" "Ihsan kawai idanun Imran ke iya hangowa, Ihsan ce kawai macen da Imran ke iya gani a cikin dubabbanin jinsin da ake kiransu da suna Mata" Kalaman Imran suka dinga Ratsa kwanya da jinin jikin Ihsan, wayarsa ce ta fara ringing, yan ɗago wayar yaga My Dad, seda gabansa ya ɗan faɗi yai fatan Allah yasa lafiya. Ya tattara dukkanin nutsuwarsa yace "Abba yana kira, bari in amsa wayar" Ihsan ta jinjina masa kai, ta gyara kwanciyarta a jkinsa. "Salamau Alaikum, Abba barka da dare" "Yawwa barka, kuna lafiya?" "Lafiya ƙalau Alhamdilillah Abba" "Ya wajen aikin naka, ya Ihsan ɗin kuma?" "Komai lafiya ƙalau Abba, ya aiki" "Lafiya ƙalau Alhamdilillah, ai ban san da Ihsan ka tafi ba, munyi Magana da Hajiya Nafisa akan kayan ɗakin Amira, tace akwai buƙatar a bar wancan dana zaɓa a sauya da wani, ya danganta da tsarin ɓangaren Amiran, a samo kayan da zasuyi kyau, kasan sha'anin  mata da tsarabe tsarabe, wayarka bata shiga na kira ema inji ko kana gida yacemin ai baka nan daga kai har Ihsan ɗin, ina son jin yaushe zaku dawone? Za suzo su duba ɓangaren Amiran" "Amm....amm Abba da ni cewa nayi, se Allah ya kaimu ƙarshen next month zamu dawo" "No Amira zata tare before then, kuma ina son ka dawo kan lokacin tariyar, saboda su duba abunda zasu duba kana nan" "To Abba, insha Allah za'ayi yadda kace, amma Abba nace meze hana ita Amiran ta zauna a gidana da zan zauna da farko, kowacce ta zauna gidanta daban?" "A'a, ai nan gidanma yalwatacce ne, ze isheku karka raba kan iyalinka, ni anya makuwa kana kira kaji halin da take ciki kokuma kaji lafaiyarta?" "Eh Abba, muna waya da Anty" "Ba kana waya da Anty ba, da Amira ya kamata kayi waya tunda itace matarka, kaji lafiyarta tunda tana da hakki akanka" "To Abba insha Allah, zan kira" "Idan na tuntuɓa naji baka kira ba zan ɓata maka Imran" "Insha Allah hakan ba zata faru ba, zan dinga kiran" "To shikenan, ka gaisarmin da Ihsan ɗin dan Allah" "To Abba zataji insha Allah" Ihsan kuwa tuni ta bar jikin Imran, jin ana masa maganar Amira, da batun Amira zata tare, ta juya masa baya. Imran ya ajiye wayar ya matsa kusa da ita yace  "My dear meyasa kika juyamin baya?" Banza tai dashi kamar ba taji meyake cewa ba. "Ihsan magana fa nake miki" A ɗan hasale tace  "to me kake so ince maka? dan Allah ni ka ƙyaleni " "Yanzu meye abun fushin kuma Ihsan? Ya kike son inyi, Abba ya haɗamin zafi kema ki haɗamin me kikeso inyi in bijire masa?" Kawai Ihsan ta fara kuka, hadda sheshsheƙa. Rungumeta yayi a jikinsa yace  "is Ok, na gane kiyi haƙuri in dai Amira ce ni ba ruwana da ita, ba dai gida bane tazo ta zauna, nike ce kawai mata ta ke nake so Ihsan, ni tsakanina da Amira ido, dan Allah karki ɗaga hankalinki kinji my wife" Yai maganar yana share mata hawaye. "Imran dan Allah

Chapter 15 of 31