Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tsakaninsu, tunda baka san yakamata ba shiyasa nace ni bari inzo in ɗaukeka muje a sake duba jikinta" Imran yai shiru ya cigaba tuƙinsa. Suka isa gidan Alhaji Hashim, sukai parking sannan suka shiga, a falo suka tsaya sukai Sallama akayi musu izinin shiga. Anty na ganin Abba tare da Imran tace "gaskiya munyi fushi, fushi muke daku irin sosai ɗin nan, haka akeyi ai mana laifi amma ba ban haƙuri ba dubiya ko ta waya" Abba yace "tuba muke, Allah ya bada haƙuri" Alhaji Hashim ne ya shigo falon yana faɗin "Ƙyalesu zamu haɗe a Human rights tunda abun hakane" Abba yace "wannan kuma kai da shi, ɗanka ne yai maka laifi bani ba" Suka zauna suka gaggaisa, suka ƙara yiwa Imran Allah ya sanya Alkhairi, Abba yace "ina Amiran ne? Ya jikin nata?" Anty tace "'yar tawace akwai zuciya, ta bi ta damu kanta ba irin rarrashin da bana yi, amma ta damu kanta da koke koke, ga zazzaɓin nan ko sauka bayayi saboda damuwa, ina tsoron ta jawa kanta wani ciwon" Imran a ransa yace 'ni banyi kuka na sa abun a raina ba se ita, se taje taita yi ai" Abba yace "Yasalam, nasan a rina ai, yanzu tna ina?" Anty tace "Imran shiga ka taso ta tana ɗakin kusa da dining" Imran kamar yace baza shi ba, haka ya miƙe ya shiga ɗakin da Amira take, tana zaune akan gadon, ta rame sosai mussaman a fuskarta, ya ƙarasa cikin ɗakin gaban gadon da take, ɗago idonta tayi ta harareshi sama da ƙasa ɗauke kanta, se a lokacin ya lura da raunin dake gefen idonta, da tabon hannayenta da suka fara baƙi, a lokacin ya tabbatar da dukan da yai mata bana wasa bane. "Kizo ana nemanki a Falo" Ko gezau ba tayi ba balle ta motsa. "Ba kyaji ina miki Magana?" Kawai ta shige cikin bargo tai kwanciyar ta, wani takaici ya ƙule Imran, yana mata magana amma ta maida shi wani banza, kawai ya hau kan gadon ya janyota, aikuwa ta ware muryarta tace "Wayyo Allah ciwona! Dalla ni Ka cikani". Cikata yai da sauri yana kallonta da mamaki, Wannan ai salon Ace wani abun yai mata ne. Muryar Anty suka jiyo tana "Imran me kake mata ne? Kar muyi haka da kai fa" Amira kuwa hararasa tayi, ta sakko daga kan gadon ta fito falon, haka nan cike da kunya da takaici ya shima ya biyo bayanta, a ƙasa ta zauna ta sunkunyar da kanta tace "Abba ina wuni" "Lafiya ƙalau Amira, Amira haka zamuyi dake, kalli yadda kika rame fa, meyasa?" Aikuwa kamar ya fama mata inda yake mata ƙaiƙayi ta fashe da kuka tace "Abba ni bana son Auren nan, dan Allah a maida ni gida" Imran ji yayi Kamar yai tsaki, amma ya daure. Abba yace "haba Amira, ba muyi miki Auren nan dan cutar dake ba, kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki kinji, Muna so ki samu lafiya da wuri ki Tare a ɗakinki, Insha Allah Imran ze kula dake" Alhaji Hashim ya ciro sadakinta dubu hamsin a aljijunsa, ya miƙawa Imran yace ya bawa Amira. Ya karɓa ya ajiye mata akan cinyarta, Amira ta ɗago idanunta da suke ta zubda ruwa ta gallawa Imran harara, ji take tamkar tai masa Allah ya isa ta huta. Akai tayi musu Nasiha ita da Imran, sedai daga ita harshi ba wanda ya maida kai akan abunda ake gaya masa, kowa da abunda yake saƙawa a ransa, suka gama aka sallami Amira, ta miƙe zata tafi ɗaki Kuɗin jikinta suka zube ƙasa. Alhaji Hashim yace "Zoki tafi da kuɗin mana, naki ne haƙƙinki ne" Amira ta durƙusa ta ɗau kuɗin kawai ta tafi jikin Anty ta ajiye mata kuɗin a jikinta, Anty ta rungume Amira ta cigaba da rarrashin ta, wato Amira sam bata gajiya da kuka. "Anty ni wallahi irin mijin Anty Fa'iza nakeso, wallahi wannan Imran ɗin cin zalina ze dingayi". Alhaji Hashim yace "A'a baze ci zalinki ba, Yayanki ne fa yana sonki ze kula dake sosai, Imran rakata ɗaki taje ta kwanta" Ya rasa meyasa aketa wani sake cuso masa Amira, Anty tace "tashi kije kuyi sallama" Tana tashi tai gaba abunta bata jira Imran ba, Imran yabi bayanta dan ba yadda zeyi. Suna zuwa ɗakin ya ƙarasa da sauri ya cinmata, ya kalleta yace "Ni kike cewa zan ci zalinki a gaban su Abba saboda makirci ko?" "Dukan da kayi min Adalci ne? Ka dinga dukana ka ƙyale ƙanwarka wallahi Allah yana kallonka" "Allah ya isa kike min kenan?" '"ni ban maka Allah ya isa ba" "Ƙarya nake kenan?" Ta girgiza masa kai, ya ƙare mata kallo daga sama har ƙasa yai tsaki ya juya ya fita. Domin Sharhi, gyara Ko shawara Ayshercool 07063065680. [1/23, 4:41 PM] Ayshercool: 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 WUTA A MASAƘA PERFECT WRITERS ASSOCIATION (WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS) https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P. W. A *Story and written by* AISHA ADAM (AYSHERCOOL) The experience writer of *ABDUL JALAL* * WATA KISSAR.... (SAI MATA) *BAƘIN TABO (Labarin gasa) *AƘIDATA (Paid Book) * WUTA A MASAƘA https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in ❌❌❌ Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.                                         25_26 Imran na fita Amira Tayi tsaki, ta kwanta akan gadonta taja bargo, kwata kwata da ta tuna dukan da Imran yai mata se taji ta tsaneshi bata ƙaunar ganinsa. Imran kuwa a harabar gidan ya tarar dasu Abba, sukayi Sallama dasu Alhaji Hashim suka tafi. Suna dawowa cikin gidan, Anty Nafisa ta tafi ɗakin Amira, tana shiga tai sallama Amira ta amsa, Anty tace Amira tashi zaune Magana zamuyi. Amira ta tashi zaune, Anty ta zauna kusa da Amira tace  "Amira wace irin sallama kukayi da mijinki ne?" Amira tace "mijina kuma?" "Eh mijinki Imran mana" ita Amira mantawa take wai Imran yanzu mijinta ne, idan ma aka faɗa se taji wani banbarakwai. Maimakon ta bata amsa se tayi shiru ta sunkuyar da kai. Anty tace  "Amira, duk da Imran ba sonki yake ya aureki ba kefa zaki nemo soyayyar nan da kanki" Ɗan tura baki Amira tayi a ranta tace "ji wata Magana mara ma'ana, ni zan bishi ya soni lallai" "Ki dena tura baki, kamar yadda na gaya miki ke zaki nemo soyayyar nan da kanki, sannan karki kuskura ki kuma ce masa mugu, ko yana cin zalinki yanzu mijinki ne shi, ki manta da abunda yafaru gaba ɗaya, ki fuskanci rayuwarki, banda gaya masa baƙar magana ko abunda ze tunzurashi, ko kin fiso ya sakeki ki zama ƙaramar bazawara?" Ba Kunya Amira ta ɗaga kai alamar eh, "au kin fiso ki zama bazawara, ya sakeki?" Amira ta kuma jinjina mata kai alamar Eh. "Lallai Yarinta na ɗawainiya dake, amma meyasa kike so ya sake ki?" "Ni wallahi ba irinsa nake so in aura ba, bashi da tausayi" "To ke wane iri kike so?" "Irin mijin Anty Fa'iza nake so" Anty tai murmushi tace "wane iri ne wai wannan mijin na Anty Fa'iza?" Amira ta gyara zama tace  "kinga fa shi mijin Anty Fa'iza yana lallaɓata sosai, gashi da sauƙin kai, yana da matuƙar haƙuri, kuma yana son yai abunda ze burgeta, gashi da fara'a da yawan murmushi, amma ba irin wannan Imran ɗin ba da ko dariya bayayi" Wani ƙasaitaccen murmushi Anty tayi, ta fuskanci Amira 'yar soyayyace tafi son wanda ze dinga lallaɓata yana biyewa taɓararata. Ta kalli Amira tace "Ai baki san wani abu ba, sufa maza tamkar yara suke a gurin mace, duk yadda kika so zaki sarrafa su, amma bata ƙarfin tuwo ba ta hikima da rarrashi, idan kin so seki maida Imran ɗin irin yadda kike so" "Taɓ, wannan sarkin hantarar baze taɓa zama irin Mijin Anty Fa'iza ba, inaga irinsu basu da yawa ma a duniya" "Ke waye ya gayamiki haka, kiyi tayiwa Imran Addu'a, ze zama irin yadda kike so insha Allah kinji yarinyar kirki" Amira ta gyaɗa kai ba dan ta gamsu ba, Anty tace "naga tunda kika ga Imran harkin ɗan sake, anya ba zamu tataraki mu kaiki ba?" Ɗan zaro ido Amira tayi tace "a'a ni kawai na ɗanji ƙwarin jikina ne, ba zuwan sa bane, in dan zuwansa ne bakiga yadda ya janyo ni akan gadon nan ba kamar wata kaza" Dariya Anty tayi tace  "bari in aiko Fadila ta kawo miki ko tea ne ki sha, seki samu ki sha magani" Fadila ƙanwar Alhaji Hashim ce, Aurenta ya mutu ta dawo nan gidan da zama. Amira tace "Aa karki sata aiki, bari inzo in karɓa" "Meyasa zaki ce kar in sata aiki, ƙanwata ce fa" Amira tace "Ai ta girmeni, be kamata ina zaune tayimin abu ba" Anty ta ɗan yi shiru tana nazartar Amira sannan tai murmushi tace "tashi muje Kitchen ɗin tare, ai nafison in ga kina tattakawa jiki yana ƙara ƙwari" Amira ta sakko daga kan gadon tabi Anty, tunda Aka kawo Amira gidan yaune ranar farko da ta ɗan saki jiki da Anty haka, har sukayi doguwar magana, amma da ba ruwanta dasu sam. Imran da ya koma gida har Ihsan tayi bacci, ya wuce ɗaya ɗakin yai wanka, ko ta kan Abinci baya bi, dan sam baya jin daɗin komai a bakinsa, ya bi lafiyar gado ya kwanta, sedai fara baccinsa ke da wuya Amira ta dinga masa gizo a cikin bacci, ya dinga mafarki da ita,farkawa yayi a hankali hankali ya buɗe idonsa, ya ɗakko wayarsa ya ga ƙarfe biyu da rabi na dare. Ya ajiye wayar yai shiru yana tunani, ya daɗe yana jiran ranar daze zama inuwa ɗaya da Ihsan dan nuna mata irin ƙaunar da yake mata, sedai kash ranar tazo masa da ƙalubale, be samu damar cika burinsa ba, Amira tayi kutse a ratuwarsa ta kassara komai, haka ya cigaba da juyi akan gadon nan, yana tunani ta ina ze ɓullowa al'amura, ga Ihsan sam taƙi saurararsa, miƙewa yai zaune a hankali ya sakko daga kan gadon, ya buɗe ƙofa ya nufi ɗakin da Ihsan take. Ya tura ƙofar a hankali, ɗakin ya gauraye da duhu, ya kunna fitilar wayarsa ya hangota kwance tana bacci, a hankali ya taka yaje ya hau kan gadon da take, ya kwanta ya hasakata da fitilar ƙaramar wayarsa zubawa kyakkyawar fuskarta ido, wadda tai fayau saboda kuka da damuwa. A hankali ya matsa inda take, ya janyota jikinsa, kamar a mafarki Ihsan taji Imran a jikinta, a zabure Ihsan ta farka tana neman ta kurma ihu, ta dire daga kan gadon nan da sauri tana zazzare ido. "Ihsan meye hak? Nine fa Imran ne kina nema kimin ihu a daren nan" "Akan me zaka zomin ɗaki ban sani ba, kawai ka fara rungumeni haka akeyi?" "Dama na Aureki ne dan inzo mu dinga kallon juna? Ihsan meyasa haka ne? Ina tarin ilimin addinin dana sanki dashi?" "Idan ba Aurena kayi dan ka kalleni ba, ai naga bani kaɗai ka Aura ba, kaje gurin karuwar da aka aura maka mana, dan Allah Imran ka ƙyaleni ni babu wani sauran abu ko fahimta daya rage tsakanina da kai, ka ƙyaleni inyi jinyar zuciyata akan yaudarar da kaimin" Maganganun Ihsan sun ɓatawa Imran rai matuƙa, ya ƙare mata kallo tsaf, dudu Ihsan idan yai niyya duk Wani abunta baze hana shi abunda yai niyya ba, sedai baya son cutar da ita, ya rasa wace irin zuciya ce da ita haka, yadda sukai soyayya be taɓa tunanin dan wani abu ya gifta na ƙaddara zata masa haka ba. Be ce mata uffan ba, ya ɗauki wayarsa ya fita ya bar mata ɗakin, saboda tsabar takaici a Falo Imran ya kwana, ya rasa abunda yake masa daɗi, ana Aure a samu nutsuwa da kwanciyar hankali, amma shi banda damuwa ba abunda ya fuskanta a Auren. Ƙarfe tara na Safe Ihsan tana can tana baccinta, ya shirya ya fice ba tare da yabi ta kanta ba, be zame ko ina ba se gidan su Khalid. Yaje ya tarar da Khalid yana breakfast, Khalid na ganinsa ya fara murmushi "Angon biyu, Kai angwaye na ƙyalli suyi ƙiba kaikuma naga kamar ramewa kayi, lafiya kuwa?" Imran kawai ya nemi guri ya zauna yai shiruu, yama rasa ta ina ze fara. "Kayi shiru, ko da akwai matsala ne?" "Khalid a satin nan zan koma gurin aiki insha Allah" "Kamar yaya zaka koma gurin aiki? Harka gama hutun angwancin ne?" "Wane hutun angwanci Khalid? Na rasa mema zanyi inji sanyi a raina, gara in nesa da Ihsan, kwata kwata taƙi saurarata, ta sawa kanta damuwa da tashin hankali akan Amira, taƙi saurarata taji wani uzuri daga bakina gaba ɗaya, jiya Abba yasani a gaba wai dol se munje mun duba Amira, itama mukaje ta cazamin Kai, se koke koke take wai an Aura mata Mugu, ni dana san hakane da tunda fari banyi Auren nan ba, gara in nesa dasu in bar musu garin, suje su ƙarata" Khalid ya ɗanyi murmushi yace "Imran kenan, tun yanzu fa kenan, ina ga in Amira ta tare suka zama su biyu, a gaskiya Ihsan ta bani mamaki sosai, ban zaci za tayi maka haka ba, amma ka sake bata chance kayi haƙuri kasan tana da matuƙar kishi sosai, amma ka jinkirat tafiyar nan ko zaku daidaita" "Khalid ba abunda zan jinkirta, Insha Allah bakin aikina zan koma suje su ƙarata, zan nunawa Ihsan ko babu ita zan iya rayuwa saboda na fuskanci kamar lallaɓata da nake ne yasa take nema ta wulaƙanta ni, dama ita waccan bata tata nake ba, da ita da babu duk ɗaya" "Kaga Imran ina rabaka da nuna halin ko in kula ga Amira, karka bari ta gane kana ƙinta, in ba haka ba ba ruwana, karkazo nan gaba Allah ya jarabceka da soyayyar ta" "Soyayyar wa, wannan mara Kunyar banzan fitsararriya, kai kaga abunda ta dingayi jiya, bata da ta ido sam, a gabana take cewa bani da imani, zataga rashin imani kuwa" "Ita wannan da ta san kai me Imani ne kake kyautata mata ai gashi tana baka wahala, itama Amiran dan baka janta a jikine yasa take maka kallon mara Imani, kuma ga yadda kake treating ɗinta babu tausayi, dole tace baka da imani ai" Imran ya miƙe yace "malam niga mota ta nan zan bari a gidanku, zan ƙarasa gida inje ɗakin in huta, bana son Abba yasan nazo" Khalid yace 'Yadda kace Angon biyu" Imran be kula shi ba yai waje, gidansu ya nufa kai tsaye, yana zuwa ya wuce sashensa yai kwanciyar sa ba tare da kowa yasan yaje gidan ba. Jikin Amira da sauƙi sosai, ta tashi tai wanka ta canza kaya a cikin wanda aka bata, ta fita falo seda ta gama ƙarewa falon kallo, sannan ta nufi inda Kitchen yake, ta tarar da Fadila nata aiki tana ƙoƙarin haɗa abun karin kumallo ita da Me aikin gidan. Amira tace "Anty Fadila ina kwana?" Fadila ta kalli Amira da fara'a tace "Alhamdilillah, 'yar gidan Anty jiki yai sauƙi, ya ƙarfin jiki kuma?" "Alhamdilillah, naji sauƙi sedai ina kewar gida sosai" "Allah sarki, haka Aure yake Amira ki kwantar da hankalinki zaki saba ne" "To wai a nan zan ta zama?" Fadila tace "A'a haba dai, kin matsu ki tare a gidanki ko?" Amira ta zare ido tace "rufamin Asiri, kawai tambayarki dai nayi" "Ba a nan zaki zauna ba, zaki tare a gidanki nan da wani ɗan lokaci insha Allah" Amira ta ɗan taɓe baki tace  "ni dama an ƙyaleni na tafi gida, in yaso daga baya na dawo" "Zama da mune bakya so kenan ko?" Tai saurin girgiza kai tace "A'a wallahi, ina da kaya a gida da nake buƙata" "Karki damu, duk abunda kike buƙata kiyi Magana" Amira bata amsa ba tace  "bari in tayaku aikin" Fadila tace "A'a, kar Anty ta fito tace an samata ke aiki" Amira tai murmushi tace "ba abunda za tace, ta karɓi ferayr dankali a hannun Fadila" Wayarta ce ta fara ringing, wayar da se yau ta kunnata tunda aka kawota gidan, tana son ta kira su Anty Fa'iza amma taga yayi Safiya da yawa ta fasa. Ta ɗaga tace "Hello My blood" "Gimbiya kina lafiya kuwa?" Amira ta murmusa tace "lafiyata ƙalau Sultan, ya kake ya aiki?" "Amira wai da gaske An miki Aure?" "Eh Sultan, an min Aure" "Amira wane irin Aurene haka ba shiri ba labari? Dagaske kuma wannan da yazo ya tafi dake ɗin shiya Aureki?" "Eh Sultan shine, ɗan uwana ne" "Anya Amira an miki adalci kuwa? Wallahi ina tsoron mutumin nan karya dinga cutar dake, sam bashi da tausayi wallahi shaƙar da yaimin lokacin da yazo Office ɗin ji nai kamar na mutu wallahi" Ƙwallace ta taru a idon Amira, Sultan ya damu da ita sosai, ta kalli tabon dukan dake jikinta, ta haɗiye kukan dake shirin ƙwace mata tace  "Karka wani damu, babu wata matsala lafiya zamu zauna dashi insha Allah" "Anya Amira, kina ganin babu Matsala?" "Babu wata matsala malam, Baza'a zaɓamin abunda ze cutar dani ba, ya labari harka tana garawa kokuwa?" Sultan yace "ina wata harka babu ke, nifa tunda ya tafi dake ban sake samun nustuwar zuwa gurin wani sha'ani ba, harga Allah bana baƙinciki da Aurenki Amira, hasali ma ina murna kin samu miji kinyi Aure, sedai naso ace kin samu miji nagari me sonki sosai, bana son ki sake wahala a rayuwarki" "Allah sarki ɗan uwana rabin jikina, bani da wata alaƙa ta jini da kai, sedai ka damu dani sosai Sultan, karkaji komai Zan zauna lafiya da Imran insha Allah" "Shikenan Amira, Ina miki fatan Alkhairi, Allah ya baku zaman lafiya, Amira banda rashin ji da taurin kai kinji, kiyi haƙuri kiyi masa biyayya, Allah ya baku haƙurin zama da juna" Duk da hawaye ya cika idon Amira, amma ta ƙaƙaro murmusa tace "Nagode sosai Sulty guy, karka damu zan zauna lafiya da mijina insha Allah, take care of yourself kaji" "Rufan Asiri kar mijinki yaji kina faɗin haka, yasa azo a casani se anjima" Amira ta kashe wayar tana murmushi, Fadila tace "Amira wannan kuma waye? Hala saurayinki ne?" "Ba saurayi na bane, kuma ba ɗan uwana bane, kawai Allah ne ya haɗani dashi, abokin kasuwanci na ne, yana jin tausayina ne sosai, ya sha shiga riski saboda ni, bazan manta da Sultan ba" "To Amma dai kiyi a hankali, kar Mijinki yaji kina waya dashi ya zaci wani abune a tsakaninku" Amira tai murmushi tace  "Ya daɗe be zata ba, ai yasan wadda aka aura masa, dan haka meye na zargi ko wani tunani" Fadila tace "Amira, Aure fa ba abun wasa bane ba, rayuwar da kikayi a baya daban, wadda kika shiga daban, karki kuskura ki ɓatawa kanki suna a sameki da wani mummunan aiki da Aurenki, dan Allah ki kiyaye" Amira tai murmushi me cike da ma'anoni daban daban tace  "to insha Allah zan kiyaye" "Yawwa ko ke fa" Ba Anty ba hatta Alhaji Hashim yaji daɗin yadda Amira ta fara sakewa, ba kamar da yadda ta takure kanta ba. Yadikko kuwa baƙin cikin duniya yabi ya ishe ta, wai Amira tayi Aure, duk da yawon ta zubar ɗin da tayi amma ta samu danƙareren miji kamar Imran ta aura, da fari cewa tayi su Baffa Salahu su kai ƙarar Abba, wai akan ya Aurar da Amira, ba da izininsu ba alhalin suke da hakkin Aurar da ita tunda mahaifinta baya raye, dangin uba suke da maganar Aure bana Uwa ba. Usman ne ya ankarar da ita yace "Yadikko, ki rufawa kanki Asiri tun wuri, Allah kaɗai yasan meya tsara tunda akayi Auren nan faka faka haka, kuma idan kika sa suka kai ƙarar me kikeso ayi? Na farko dai Aure ya ɗauru tunda ya cika dukkan sharuɗan da addini yazo dasu, sedai ace anyi ba daidai ba daya aurar da ita, na biyu Kuma kin san dai ba raba Auren nan za'ayi ba, ga uwa uba shi wanda ya aurar da ita ɗin wani ne a sama, baki da kuɗin da zakija dasu, kawai kiyi haƙuri ki koma gefe kiyiwa su Amina Addu'a suma Allah ya basu maza nagari wanda yafi na wanda Amira ta samu" Yadikko tai ajiyar zuciya tace 'ni babban abun takaicin, yadda suka dinga sintiri a gidan nan shida ɗansa, amma aka rasa wanda ze buɗe baki yace mana ga abunda ake shiryawa, da kunturun makirci, suka auri karuwa suka bar na ƙwarai" "To ke meye naki a ciki, suje su ƙarata an rage mana Matsala ma" "Wane rage matsala, ni ba gara ace tana gidan nan a cigaba da matsalar ba, su Sadiya su Auri yaron ba" "To koma dai yane, Yanzu jabbal ƙalam, tunda an riga an Aureta se haƙuri" Haka Yadikko ta kasa ɓoye bƙin cikinta da Auren Amira, Sosai take nuna tana adawa da Auren, yayinda labarin Auren Amira ya cika gari, kiwa ya dinga mamakin irin yadda Amira tai Aure lokaci ɗaya haka, duk da irin tarin fitinarta da rashin jinta. Tafi tafi rayuwa na cigaba da tafiya, Imran sam ya dena shiga sabgar Ihsan, yai watsi da ita ya dena nuna yasan da zamanta a gidan, wataran da sassafe kafin ta tashi ya fice, baze dawo ba se dare, ya ajiyemata duk wani abun buƙata, amma fa ba ruwansa da ita. Ranar wata laraba da Safe, Ihsan ta tashi daga bacci ta fito falo taga takadda akan Centre table na falonta, ta ɗauka ta duba taga Imran ne ya ajiye mata saƙo  "Na koma gurin aiki, in kina buƙatar wani abu na bar kuɗi a wardrobe ɗina" Gaban Ihsan ne ya faɗi, tai shiru tana tunani To yanzu idan gurin Amira ya tafi fa? Take taji wani gumi yana tsatstsafo mata, jiki na rawa taje ta ɗakko wayarta ta kira shi, sedai be ɗaga ba, se a yanzu take tunanin wautar da tayi na share Imran, hakan ze iya bashi damar tafiya gurin Amira. Tana nan tana wannan zulumin taji ana buga gate, ta saka hijjabi taje ta buɗe ƙofar, tana buɗewa taga Ammi ce da Minal suka zo. Murmushi tayi tare da yi musu sannu da zuwa, ta jagorancesu zuwa falonta. "Ammi sannunku da zuwa, da kun kirani na ɗora muku wani abun ai" Ammi tace  "A'a sauri mukeyi, nace mu biyo inzo in dubaku zamu wuce ta wajen gidan nan nace bari in leƙoku, ina Imran ɗin?" "Ammi ai ya koma aiki yau". "Kamar ya ya koma aiki yau? Amma ya akayi be gayamin ba? Hutun nashi ya ƙare ne?" Ihsam tace "kiran gaggawa akayi masa shiyasa ya tafi be miki sallama ba" Ammi tace  "shikenan, na biyo ne dama inga komai lafiya kafin inyi zuwa na musamman, sannan ki kula ki kwantar da hankalinki, waccan Yarinyar da ita da babu duk ɗaya, karma ki a ranki kina da kishiya, ki sake kiyi rayuwarki a gidan mijinki, na yiwa Imran kashedi sosai akan Yarinyar nan, jira nake ta tare inga ta inda zan ɓullowa lamarin in kashe Auren ba tare da mahaifinsa ya zargi wani abuba, karki kuksakura ki bata damar da zata ga kafar da zatai masa shishshsigi, kin san karuwai a waje ma ƙwacen miji suke balle tana matarsa, duk ds na lura shima ba shi da interest akanta, mahaifinsa ne duk ya haɗa wannan kwamacalar, shiya tursasashi ya Aureta, shikuma ya amince ba tare da ya nuna baya so ba, kowane ɗa yafi son uwarsa amma shi kam, yafi son ubansa a kaina" Ihsan ji tayi kamar Ammi tai mata allura, tabbas idan tai wasa hankalin Imran ze iya karkata kan Amira, Dan haka dole tayi wani abu a kai, ashe dagaske dai takura masa akayi ya Auri Amira ba dan yana sonta ba. A gurguje Ammi tayi sallama ds Ihsan suka tafi, tunda suka tafi abun duniya ya ishi Ihsan, ta ɗau waya ta kira Imran kusan 5missed calls anma yaƙi ɗagawa sam. Baƙin da ta dingayi ne suka dinga ɗauke mata hankali, amma wani sashi na zuciyarta na can tunanin mafita, dan bata zaci Imran ze iya watsi da ita haka b, harta kirashi yaƙi ɗagawa ba. Ɓangaren Abba ma hankalinsa ya kwanta, mussaman daya sake zuwa gidan Alhaji Hashim ya tarar da Amira ta saki jikinta, ta dena koke koke da damuwa, yanzu bashi da wata fargaba na za'a kirashi ace masa ga Amira ta aikata wani lafi, dan haka ya samu nutsuwa harya koma bakin aikinsa. Ihsan kam abun duniya ya isheta, kwanan Imran biyar da tafiya amma yaƙi ɗaga wayarta, ta tura masa message ba adadi amma beyi responding ɗin ko guda ɗaya ba. Rana ta shida da Safe ta sake jarraba kiran wayarsa, Babu tsammani taji ta ɗauka, kawai ta sa masa kuka. "In kuka zakimin zan kashe wayata, meyafaru?". "My meyasa zaka tafi ka barni dan Allah?". 'saboda ba kya buƙata ta, babu amfani cigaba da zaman namu shiyasa na bar miki Gidan" "Haba My, kishinka ne yasa nai abunda nayi, But i regret it, Ammi tazo ranar da ka tafi, ta gayamin takura maka akayi ka Aureta, dan Allah kayi haƙuri, wallahi ina sonka mijina". "Ina tantama akan son da kike min Ihsan, tunda kika gaza yimin uzuri ki saurareni" "Dan Allah kayi haƙuri

Chapter 14 of 31