yace "to idan tazo Kadunan meye abunyi na gaba?"
*Zan gaya maka, idan na gama nazari"
Suna shirin shiga mota su tafi, Baba ya fito ya samesu yace "Masha Allah, Alhaji baku tafi ba kenan?"
Abba yace "eh, amma yanzu zamu wuce insha Allah"
"To amma nace ya batun Amiran, wani mataki zaka ɗauka akan lamarin nata"?
Alhaji Hashim yai sauri yace "karka damu, abunda muke tattaunawa kenan, idan mun tsaida maganar abunda ya dace zamu sanar muku insha Allah, amma dai a cigaba da haƙuri da ita dan Allah, mun san ana haƙuri amma a ƙara, zamu san abunyi a kai insha Allah"
"Amma ina fatan dai ba ɗauke mana ita zakuyi ba?"
"Haba dai, ya za'ayi ku raini yarinya ace za'a rabaku da ita, za dai a duba ne mugani tunda tana son karatu zamu maida ita makaranta, kuma a sama mata koda wata sana'ar ne"
Baba yace "shikenan, hakan babu laifi, Allah ya maida ku lafiya"
Suka amsa da Ameen, suka masa ihsani, sannan suka tafi.
Suna cikin tafiya Alhaji Hashim yace "amma wannan tsohuwar ba ita ta haifi baban yarinyar nan ba ko?"
Abba yace "Eh, kishiyar kakarta ce"
Yace "shiyasa no wonder"
Abba yace "meka gani?"
"A'a bakomai, ni wallahi yarinyar ma birgeni tayi, wannan ba zatayi wahalar saitawa ba da taimakon Allah da jajircewa, rashin ji ne kawai, amma tana da sauƙin hali, sedai akwai mulki" yai maganar yana murmushi.
Abba yace "wani sauƙin hali tana wannan aika aika haka?"
"Ai zata shiryu insha Allah"
Amira kuwa harta shiga gidan bata kula kowa ba, ta shiga ɗakinsu ta zauna tayi shiru tana saƙawa tana warwarewa, tana tuno abubuwan da suka wuce, da wanda suke faruwa a yanzu.
Jiki a sanyaye, ta tashi taje ta ɗauki buta ta shiga banɗaki, ta fito ta zauna a tsakar gida.
Amina ce ma ta taho zata shiga banɗakin, Sadiya tace "ke Amina, kisa gishiri da omo ki wanke banɗakin nan kafin ki shiga, karki je ki tsuguna ki kwashi cuta, dan yanzu likkafa ta cigaba, har da Arna ake iskancin"
Yafikko tace "ƙwarai kuwa, kisa Omo ko wanke banɗakin nan da kyau, Allah ɗai yasan me taje ta yayimo mana, karku tsuguna ku kwashi koren Sanyi"
Amira tai shiru, kamar bada ita ake ba.
"Yo banda rashin mutunci da Akuyanci, ace biye biyen ya wuce kan musulmai, sekin dan gana da kiristoci masu fitsari a tsaye, basa wankan tsarki, basa tsarkin gasu da biye biyen tsiya, amma suma kije kina binsu, Babu abunda ze hana ki shiga banɗaki a kwashi Sanyi, harda ma abunda yafi Sanyi"
Suka dinga cashewa Amira, tana zaune tana jiksu bata ce musu uffan ba, kuma bata tashi daga inda take ba.
Su Alhaji Ali kuwa, daga gidansu Amira, seda suka tsaya rabon IV ga Manyan mutanensu dake Kano, sannan suka kama hanyar Kaduna,Se bayan la'asar su Abba suka koma, Imran ya sauka a gida, su Kuma su Abba suka wuce wani gurin.
Imran ya shiga gida, kai tsaye cikin gidan ya fara zuwa, ya tarar da Ammi a falo, ya zauna yace "Ammi sannu da gida"
Ta ɗago ta kalleshi tace "daga ina kake?"
"Tare da Abba muke, munje Kano ne rabon IV"
"Ƙarya kakeyi, kunje gurin wannan yarinyar ne ko?"
Imran yace "Eh munje gurinta, daga nan kuma mukayi rabon invitation, Amma Ammi meya faru?"
"Au tambayata ma kake ko? Za'a haɗa kai da kai a munafurceni, yana son ya ɗakko yarinyar nan ya dawo da ita gidan nan, to baze yuwu ba wallahi, bame ajiyemin Karuwa a gida, ina da 'ya Mace a lalatamin ita a banza, baze yuwu ba"
"Ammi bafa cewa yayi zata dawo gidan nan ba, hasali......
"Rufemin baki" tai maganar a hasale.
Naga kafi goyon bayan ubanka a kaina, kome zeyi seka dinga rufa masa Asiri, koma dai menene a baya ban karɓeta ba ba zan karɓeta a yanzu ba data zama 'yar gagara"
Imran dai yai shiru, bece komai ba, taita mita tana faɗa, harta gaji tayi shiru, Sannan ya tashi ya bar falon.
"Kai kai kai kai! Waye ya kashe wutar girkin nan? Umma! Umma! Waye ya kashe wutar girkin nan wai"
Umma daga ɗaki tace "kamar yaya? Ki iza wutar mana, amma se ƙwalamin kira kike"
Sadiya tace "bafa mutuwa wutar tayi ba, jiƙa murhun akayi da ruwa"
Umma ta fito da sauri, ta nufi gurin murhun, an jiƙeshi sharkaf da ruwa Babu yadda ma ze kama, ga itacen da yake ajiyema wanda ake girkin dashi an jiƙashi da ruwa.
Yadikko ce ta fito da carbi a hannunta tace "wai meke faruwa ne, Abincin haryanzu be gamu ba?"
Sadiya tace "wane irin Abinci ya gamu an jiƙe murhu da ruwa"
Yadikko tace "innalillahi wa innalillahi raji'un, Yanzu ɗan wakem be dahu ba?"
"Ina fa ya dahu, yanzu na gama jefawa fa na shiga inyi salla"
"Ina Amira take?"
Sadiya tace "waya san mata?"
"To wallahi itace da wannan aikin, Babu wanda zeyi wannan Haukan idan ba ita ba, shikenan Abincin nan ya ɓaci dan baze ciwu ba" cewar Umma da ranta ya gama ɓaci.
Yadikko tace "yanzu idan an siyo wani icen baze ba?"
Sadiya tace 'ta yaya zeyi? Tafa jiƙe murhun gaba ɗaya, ta jiƙe itacen da ruwa, yanzu kafin a siyo wani, a hura wutar ai aiki ne jawur, ɗan wake dai ya riga ya gama ɓaci, se a nemi abunyi"
Yadikko tace "wannan yaro ko matsiyaciya, an mutu an barmu da jaraba, da masifa ita duk wani abun da za'a ce mata Allah wadaranta shi takeyi, shegiyar yarinya watsatsiya, ta sani sarai babu wanda yaci ko Abinci rana a gidan nan, ni ji nake kamar an kwashemin hanji saboda yunwa, shine ta mana wannan baƙin zaluncin, Allah wadaran wannan sheɗaniyars yarinyar"
Usman yace "to ance a lallaɓa wan uwarta ya ɗauketa kowa ya huta, kimce ba haka ba, baza'a ɗauketa taje ta huta ba, dan haka dole mu haƙura mucigaba da kwasar baƙin ciki da takaici, yanzu dai ɗan wake ya ɓaci, sedai a bawa Awaki, kowa kuma yayi ta kansa"
Amira kam bayan tayi wannan aika aika, ficewarta tayi tai nata guri, tasan koba komai ta haɗa musu zafi da takaicinta zasu kwana, duk da abunda tayi musun, besa ta huce daga abunda suka yi mata ba, na zagi da cin mutuncinta da suke ba yau ba gobe ba.
Imran kam gaba ɗaya beji daɗin Abunda Ammi tayi ba akan maganar Amira, idan bata yadda Amira ta dawo Gidan nan ba an tsareta an sa mata ido ba, to lalacewa kam Yanzu ta fara, duk da shima baya goyon bayan dawowar Amiran gidan nasu, saboda kar tayi silar lalacewar ƙanwarsa, amma be kamata a ƙyaleya ta cigaba da wulaƙanta ba.
Gefe guda kuma ga tunanin Ihsan, wadda a wayar da sukayi ya lura ranta yayi matuƙar ɓaci, dan ya kirata bata ɗaga ba, yana yin Sallar isha'i, ya canza kaya ya tafi gidansu Ihsan.
Ya kirata a waya Amma bata ɗaga ba, ya tura mata saƙo "Ina gidanku yanzu, ina jiranki"
Tana ganin message ɗin kamar ta share, amma taji ba zata iya ba, dan haka ta zira hijjabinta ta fito, yana tsaye a jikin motarsa, ya ƙarasa inda take, ta cigaba da tafiya yana bin bayanta har sitting room ɗin da suke zance.
Ta samu guri ta zauna, amma ba tace komai ba, seda ya ɗan ƙura mata ido na wasu lokuta Sannan yace "Mu Ihsan dama zaki iya fushi dani haka? Har in kiraki ki ɗaga wayata? Why"
Kasa Magana tayi, sedai ta girgiza masa kai.
"Anya kuwa kina sona, har naje Kano na dawo tunanin yadda zan ɓullo miki nakeyi, duk na shiga damuwa, kinƙi ɗaga wayata balle inji muryarki hankalina ya kwanta, baki san muryarki ce cikamakim nutsuwata ba? Gaba ɗaya wunin yau haka na wuni ba daɗi, kin dena sona ko?"
Da sauri ta girgiza masa kai, "to meyasa kika ƙi ɗaga wayat? Kina fushi dani ko?"
Tai shiri ba tace komai ba.
"Kiyi haƙuri kinji Babyna, nima ban san da tafiyar bane, ina Bacci da Safe Abba yazo ya tasheni yace in shirya zan rakashi Kano, na kira wayarki a kashe, shiyasa ban sanar miki ba, ko kinfi son in saɓawa Abba ince ba zanyi abunda yace ba?"
Girgiza masa kai tayi tace "ba haka nake nufi ba, wallahi My haka kurum duk lokacin da kace min zaka Kano se inji gabans yana faɗuwa, bana son zuwa kanon da kake yi, kawai se inji kamar wani abu mara daɗi ze faru, wanda ze zama barazana ga Soyayyata da kai"
Imran yai murmushi yace "My Wife, kishi kawai ke damunki fa, yarinyar nan na gayamiki halin da takeyi, ta yaya ina da mace kamarki zan kalli wata, duk wasu qualities da manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya lissafa game da mace tagari kina dasu, Ubangijin Allah ya baki, tayay zanyi tunanin kallon wata mace? Kinfi kowa sanin bana kalle kalle, kuma ta yaya zan kalli wadda take yawace yawace, kawai Yarinyar ko bana son ƙanwata ce, kuma mun haɗa jini da ita, kinga ba yadda na iya, Akwai alaƙa me ƙarfi a tsakaninmu, amma ni ba wani abu mummuna daze faru akan Soyayyar mu, nibke nake so kawai, kuma ni bayan ke bazanyi wani Auren ba, kin san bana ra'ayin ajiye mata fiye da ɗaya, ke ɗin kawai kin isheni, Amira ƙanwata ce kawai"
Gaban Ihsan ya faɗi tace "Ameera kuma?"
Yace "Eh sunanta kenan"
Tunawa tayi da Yarinyar da tayi rawa a Abujan nan, kuma itama sunanta Amira, ga kuma kaminin da suke ita da Imran, anya ba itace wannan Amiram ba?.
To amma ai ta nunawa Imran ɗin hoton yarinyar, yace shi be santa ba, bashi da wata alaƙa da ita, kawarda wannan tunanin kawai tayi daga ranta, ta barwa ranta cewar, suna ne kawai yazo ɗaya.
Ta kalleshi tace "to ya kuka dawo ya hanyar?"
"Alhamdilillah, mun kai invitation ma, Minal tacemin Mummy taje gidanmu Ɗazu ta taho da naku"
"Eh taje ɗazu, akan maganar gurin Dinner ne, kuma anyi settling komai"
"To Alhamdilillah, ya biki kuma da kikaje, kinyi kyau sosai a hotunan da kika turomin, seda naji kishibya kamani kar wani ya gani ya ƙyasa"
Ihsan tace "hmm ai daga dinner ɗin nan, akayi mother's event washegari, aka fasa auren nan"
Ya kalleta da mamaki yace "kamar Yaya aka fasa Auren?"
"Ni dai wahsegarin Dinner, Mummy tace lallai mu dawo gida saboda shirye-shiryen namu bikin, se waya akayiwa Mummy ranar ɗaurin Aure wai ba'a ga Ango ba ya ɓata, ana ta cigiya se bayan kwana biyu aka ganoshi a Hotel, yaje gurin Karuwa ta kulleshi a banɗaki"
Imran yace "Subhanallah, banda ganganci ga Matarka za'a kai maka, meya kaishi zuwa gurin Karuwa? Meyasa mutane bamu maida Zina komai bane? Muke rintse ido ga bala'in dake cikinta muke abunda muka ga dama?"
"Mhmm kaima dai ka faɗa, yanzu duk zancen ya bazu, dan baka hawa social media ne sosai, da ka gani"
Imran yace "Abun ba daɗi gaskiya, Allah ya kyauta"
Ta amsa da Ameen.
Ya sake kallon Ihsan yace "My kinga yadda fatarki ke sheƙi kuwa? Me kike shafawa hakane se ƙyalli kike fa"
Rufe fuskarta tai tana murmushi.
"Gaskiya nima a bani kayan gyaran jikin im dinha gyarawa, ko kinfi som a kawo miki ni a haka?"
Dariya Ihsan tayi tace "kaji ka, tome zaka gyara ai a gyare kake already my Own"
Nan suka cigaba da hirarsu cike da nutsuwa da farantawa juna rai.
*****************
"Alhaji Ali, mafita ɗayace ta rage maka akan yarinyar nan, idan ba haka ba wallafa idan abokan adawa suka ɗagoka, to tabbas se sunyi me yuwuwa sun zubar maka da mutunci a idon duniya, se sun watsa siyasar ka"
"To meye abunyi yanzu?" Abba ya faɗa cikin damuwa.
"Abunyi ɗayane, kaga a yadda na lura da yarinyar nan, kulawa take buƙata, da wanda ze dinga saurararta, tana da ambition me kyau a ranta, tana son karatu, kuma ni banga alamar wannan gidan nasu ana kula da ita ba gaskiya, ni gaba ɗaya Tsarin mutanen gidan bemin ba, da alama ka banzatar da ita a baya, kuma rashin gata yasa ta zama haka, amma idan ta samu gata da janyowa a jiki, ta samu tsayayyen me kula da ita, insha Allah zata nutsu"
"To banƙi ta taka ba Hashim, amma wallahi Jamila ba zata bari yarinyar nan ta zauna a gurina ba, tun tana ƙarama akace in ɗauke ta, Jamila yace bazata riƙe ta ba, kuma na lura haryanzu abun yana ran Amira, kuma a yanzu haka ma, bata shiga sabgata saboda kar ince zan kawo Amira gidan nan ta zauna, gaba ɗaya kaina ya kulle"
"Ai Ali ka sakarwa matar nan da yawa, ba gidanka bane ko kuɗi kuka haɗa kuka siya, kana da ikon da zaka kawo wanda kakeso ya zauna, amma tunda ka saba mata a haka ba yadda zakayi, seka samu ka aurar da ita nan kusa, inba haka ba kuma wallahi lalacewar da zatayi nan gaba se tafi ta Yanzu, kana ji tana tara kuɗi take zata tafi ƙasara waje karatu, me kake tunani idan ta tafi? Kuma ko a nan ƙasara ka barta, aka nema mata makaranta idan ba ayi dagaske ba, lalacewa zata cigaba dayi, dan haka kodai ka dawo da ita gidanka ta zauna koka aurar da ita"
"Ya salam, Hashim wa zan aurawa Amira? Bana son in aurawa wanda ze mata gori ko ya dinga wulaƙanta ta, wallahi ban san ina ƙaunar yarinyar nan ba se yanzu da aka cemin ta lalace, kuma nasan ina da laifi a lalacewar tata, kuma yanzu kullum se nayi mafarki da mahaifiyar ta, tana min magiya"
Alhaji Hashim yace "kaga, Asiri a rufe ka Aurawa Imran, ka haɗa masa biyu ai yana da kuɗin riƙesu, in yaso a ɗaura auren karta tare se tayi Istbra'i, ta zauna ko a gidana ne, bani da matsala da maiɗakina, zata fuskanta, a mata gwaje gwajen da duk yakamata"
Alhaji Ali yace "Mata biyu lokaci ɗaya, idan nai haka nawa Imran adalci kuwa?"
"Ali baka da wata mafita idan ba wannan ba, Duk wanda zaka aurawa Amira Asirinka baze tonu ba, tana jin tsoron Imran, kuma yin hakan kamar Jihadi ne, tunda Addini be haramta ba, amma idan ba haka ba ban san meye abunyi ba"
(😂😂😂 Godiya ga masoya, Comment ɗinku ke bani ƙarfin gwiwa da nishɗi, Wato idan kukayi Comments daya girgizani, bana gajiya da typing, amma idan nai posting naji shiru, da na fara typing nake fara hamma in ajiye)
Ayi share saboda Allah.
Ayi following ɗina a watpad akan
Ayshercool7724
Ina maraba da sharhi gyara ko shawara, banda biyoni ace in bada page kaza 🙄
07073065680
.
[1/12, 2:04 PM] Ayshercool: 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
WUTA A MASAƘA
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P. W. A
*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA)
*BAƘIN TABO (Labarin gasa)
*AƘIDATA (Paid Book)
* WUTA A MASAƘA
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in
❌❌❌
Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.
Afuwan banyi Editing ba
KAMAR YADDA NA FAƊA TUNDA FARI, BA LALLAI IN DINGA SAMUN YIN POSTING KULLUM BA, IDAN AN GA BAN POSTING BA AMIN HAƘURI
13_14
Abba yai shiru yana nazarin
maganganun Alhaji Hashim sannan yace
"banƙi maganar ka ba Hashim, amma duk da ni na haifi Imran, idan na tursasa masa ya auri Amira, kamar ban masa adalci ba, da ita yarinyar daze aura da fari ba, kuma ina gudun ya wahalar da ita tunda ba sonta yake ba"
"Eh to, da wannan dan wannan, amma ka sani, da kai da kaya mallakar wuyane, zaka iya tursasa shibya kyautata mata, kuma koba komai ka isa dashi, saɓanin ka aurawa bare ita, wanda baka isa dashi ba, ni da ina da ɗa babba wanda ya isa aure, ba abunda ze hana in sa ya auri Amira, hakan Jijadi ne se Allah yai maka Rahama, ya goge maka laifin watsi da zumunci da kayi a sanadin hakan"
Alhaji Ali yace "hakane maganarka, amma yadda zan tunkari Imran da wannan maganar nake tunani, da kuma mahaifiyarsa, kasan Yarinyar daze aura ɗin yarinyar ƙawartace, kar inje shiya amince, su kuma su ɗagamin hankali"
"Da ita da ɗanta a ƙarƙashinka suke, dan haka ka tunkare shi da maganar kaji me zece, nasan baze baka kunya bama"
Alhaji Ali yai ajiyar zuciya yace "shikenan Ubangiji Allah ya wuce mana gaba"
"Ameen"
Ammi na zaune suna hira da Minal, akan yadda Abba ya fita harkarta shima, gashi bata san meyake shiryawa game da Amira ba, tana ta mita tana wassafawa Minal, wayarta ta fara ringing, Minal ta ɗakko wayar ta miƙa mata.
Maman Ilham ce take kiranta, ta karɓi wayar ta ɗaga "Hajiya Jamila, maganar kajin nan nayi magana da me kajin, yace 50 pieces zamu samu kawai a gurinsa"
"Maman Ihsan a sake dubawa, mu samu su cika ɗari mana, bana son muyi bikin da za'a tafi damu a baki, sonake ayi biki na kece raini, naji Babansa ma ze sai mana sa, wanda za'a saka a Abinci, wannan kaji na dinner ne, ina son sake masa magana, amma kwana biyun nan bama jituwa, shiyasa na ƙyaleshi, amma tun yanzu yakamata a sai san a ajiye"
Maman Ihsan tace "Subhanallah, lafiya dai ko?"
"Barni kawai Laɗifa, Magana ce akan wata Yarinya, 'yar ƙanwarsa, ƙanwar fa ta mutu yace ze ɗakkota in riƙe nace bazan iya ba, shine yanzu ta girma yarinyar ta zama fitinanniya shine yaketa take taken, wai ze kawomin ita gida, gani da yarinya mace, salon ta ɓatamin ita, shiyasa na ɗauke masa wuta inga iya gudun ruwansa"
Maman Ihsan tace "gaskiya idan yayi haka be miki adalci ba, ya zaki zauna da ƙatuwar budurwa karuwa a gida, kina mata kallon biri tana miki na Ayaba, gasky idan yai haka be kyauta ba, amma gara ki lallaɓashi ayi auren yaran nan ba Tare da wata matsala ba"
"Shikenan, zan san yadda za'ayi, zan tuntuɓeshi ki gaida Ihsan ɗin".
"To shikenan zataji, seda Safe"
Ihsan data shigo tun ɗazu ta tsaya tana jiran Mummy ta gama waya, ta kalleta tace "Mummy da Ammi kike waya ko?"
"Eh da ita ne har Imran ɗin ya tafi ne?"
"Eh ya tafi" ta samu Guri ta zauna Sannan ta kuma cewa "Mummy, naji kamar tana ce miki wai wannan ƙanwar tasa zata dawo gidansu ne ko?"
"Kai Ihsan, yanzu dama kasa kunne kikayi kina jin abunda nake faɗa?"
Ihsan ta girgiza kai tace "ba haka bane Mummy, Imran ya bani labarin yarinyar, sedai a duk lokacin da za'ay zancenta se inji gabana yana faɗuwa, sama bana ƙaunar maganarta, gashi Yanzu ana zancen zata dawo gidansu"
"To ke meye haɗinki da ita da zaki damu kanki akanta? Inma gidansu zata dawo da zama akanki zata zauna? Ina gidanki daban?"
"Mummy, Yarinyar cousin ɗinsa ce kuma kamar yana nuna damuwa akanta fa" tai maganar cike da karaya.
Mummy ta riƙo hannunta tace "haba Autan Mummy, tun kan ki shiga gidan Aure kin fara da karaya haka? Ki kwantar da hankalinki sekin so wata zata raɓi mijinki, kuma yarinyar da take yawon banza ina zatayi kima a idon Imran bayan gaki" tai maganar tana murmushi.
Ihsan tace "hakane Mummy, amma kin san mazan yanzu ba'a iya musu fa"
"Ke dallcan, don't put that in your mind Baby, ba ruwanki da wata kanki kawai zaki kafa, kuma Imran yana sonki sosai baze yi abunda ze saki damuwa ba"
Ihsan tai ajiyar zuciya tace "Shikenan Mummy, na dena damuwa insha Allah"
Shikuwa Imran kamar kullum sannu a hankali yake tu(insa harya shigo layinsu, wani matashine tsaye a jikin wata Mota yana danna waya, Imran ya ƙara gudun motar ya tafi yai kan matashin kamar ze bigeshi sannan yai wani wawan birki.
Matashin seda ya ja da baya, Imran ya fito daga motar yace "kai yaushe ka dira ba labari?".
Matashin yace "ban sani ba, takeni da mota dan ubanka, kayi jinyata a Asibiti, sedai kaci amarcin a nan Asibitin gurin jinyata"
Imran ya kwashe da dariya yace "kaifa ₦an iska ne wasu lokutan, to ya? Ya ake ciki ne ka diro ashe?"
"Ba dole in diro ba, tunda ka addabeni in dawo gani na dawo, ka bani uwar da zaka bani"
Imran yace "wace uwar zan baka kuwa? Kawai dama danka dawone ka tayani hidimar bikina'
"Ɗan rainin hankali, nima ina hanya na samo wata zazzafa, kuma insha Allah wuf zan da ita"
"Karma dai kayi, ka zauna kaita ruwan ido"
"Ai nayi mamakin lokacin da ka fara soyayya, har kake shirin Aure ka barni, dole in zuciya Yaseen, kamarni Khalid ace Imran ya rigani Aure, gaskiya wannan ci bayane a gareni".
Imran yai dariya yace "wai yaushe ka shigo ne?"
Khalid yace "da magaribar nan ne, nake gidanku Ammi tace min baka nan, shine naje nai Salla sekuma gaka ka dawo"
"Fatan ka dawo lafiya, ya hanya?"
"Alhamdilillah, mushiga cikin gidan se muci Abinci mucigaba da tattaunawa"
Daga nan suka shiga gidansu Khalid.
Hajiya Amira kuwa, tunda ta lalata musu ɗan wake tasa ƙafa ta bar gidan nan, ta tafi nata garari a gari da wannan magaribar, sedai duk inda ta wuce wasu na nunata, ana cewa itace wadda aka baiwa mota, wadda zata fito a videon raye raye, ita kam ko a jikinta hakan sam be dameta ba, sabgar gabanta kawai takeyi.
Se wajen sha ɗaya saura na dare se gata ta dawo Gidan, kamar kullum yauma da Sallamar ta ta shiga gidan, sedai ba wanda ya amsa mata, saboda a ƙule suke da ita.
Ta turo ɗaurin ɗan kwalinta gaban goshi, alamun itama daidai take da kowa, duk wanda ya kawo mata rainin tana daidai da shi ta wuce ɗakinsu, su Amina na zazzaune kamar marayu, sedai sun cika sunyi fam se harare harare sukeyi, ta share su ta ajiye 'yar ƙaramar jakarta da ledar hannunta.
Yadikko ta fito daga banɗaki, ta nufo ɗakin su Amira, ta ɗaga labule ta kalli Amira tace "tauraruwa me wutsiya ganinki ba Alkhairi ba"
Amira tace "yau kuma kirarin da zakimin kenan? Naji na karɓa kuma nagode sosai"
"Yanzu banda rashin imani da tausayi, Abincin da zamuci ki ɓata kika jiƙe murhun da itacen, saboda rashin tsoron Allah, Amira kina son ki gama da duniya lafiya kuwa? Ke kwata kwata bakya neman Albarka kullum cikin kalen jaraba kike"
"Yadikko, idan nazo gamawa da duniya lafiya ki hana, idan ke zaki saka in gama da duniyar lafiya ki hana dan Allah, ni kuna so ku gama da duniyar lafiya kuka zauna kuka dinga kwashemin Albarka kuna zagina jiya, duk cikinku aka rasa me cewa Allah ya shiryi Amira, se masu kiramuk watsewa da kwaso cuta, dan nayi hoto da mutum shikenan Iskanci nake dashi? Ƙaddarama hakanne idan su Amina ne haka zaki zauna kina kwashe musu Albarka kokuma Addu'a zakiyi musu?"
Amina tace "ke saurara, karki kuksakura ki kuma gwada misalin rayuwar da kike akanmu, muba irinki bane kike can kiyi abunki Amma ki dena misali damu"
Yadikko tace "gaya mata dai, ai ba kowane irinki ba, babu yadda za'ayi su Amina suyi abunda kikeyi, ban sani ba ko a can tsatonku ne da irin haka, shine kema kika tsotso a nono aka barmana masif......
"Ya isheki haka Yadikko!
Amira ta faɗa cikin tsawa "wasa yayi wasa Amma banda zungurin uwar miji da taɓarya, karki sake ki zagarmin iyaye, gaba ɗaya ba wanda yake raye sun mutu, iyaye da kakkannina, kuma ke kin san a tsatsonsu Babu wanda yai karuwanci, karki ƙara sako su a ƙazamar maganarki, in ba haka ba zan ɗau mataki, ni ɗin dai da kika saba yiwa kiyi tayi, Amma ban yadda ki taɓa iyayena ba tunda basa raye, ba abunda sukayi miki dan haka baki da hujjar da zaki dinga danganta abunda nake dasu"
Yadikko ta hangame baki jin yadda Amira ke tatala mata rashin mutunci, saɗara saɗara.
"Yanzu Amira ni kike gayawa wannan maganar haka?"
"Na gayamiki ɗin, kika kuma zagin iyayena ko kakata wallahi sena miki rashin mutunci, nagaji wallahi"
Yadikko ta fashe da kuka, tana "Innalillahi wa innalillahi raji'un, yau na shiga Uku, 'ya'yana da jikokina babu wanda ya taɓa sani kuka, babu wanda ya taɓa sani magana seke, daga taimako na riƙeki kin zame min bala'i, tir da halinki Amira, Allah ya kwashe miki albarka mara mutunci mara imani, da ikon Allah Se karuwanci ya zama silar jefaki cikin bala'in da bazaki iya fita ba"
Jikin Amira ne ya fara tsuma, hawaye na bin fuskarta, ta tabatta da Yadikko ta haifi iyayenta babu yadda za'ai tai mata wannan fatan, kullum burinta taga Amira ta tozarta, tai tayi mata miyagun Addu'oi da jan alkaba'i.
Su Sadiya ne suka shiga rarrashin Yadikko, suna bata haƙuri, jin kukan Yadikko yasa su Usaman suka
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 31