alwala ta tada salla, bayan ta idar tana lazimi tana jin yadda su Sadiya keyi da ita.
Amina tace "hmm lalacewa ta ƙaru, likkafa ta cigaba, su O'o yanzu har kwana ake a waje"
Sadiya tace "kwanaki dai, yau kwananta nawa bata gidan nan, ni azo a gayawa Baba gaskiya a raba mana ɗaki da ita, baze yuwu ba, kar muje mu kwashi cuta wallahi"
Banza Amira tayi musu, ta ƙarasa laziminta, tana tunanin abunda zata fuskanta idan Baba ya dawo.
Tana cikin wannan tunanin ne akayi Sallama da Sadiya, saurayinta yazo ta tashi ta fita.
Baba ne yai Sallama ya shigo shida Usman, sun dawo daga masallaci, suna shigowa Maman su Sadiya ta fara kora bayani.
"Baba, se yau Allah yayi wannan mara albarkar ta dawo, kwana biyar cif bata gidan nan, Babu wanda yasan inda take kwata kwata, kaga alamu sun bayyana ƙarara tafi ƙarfin kowa yanzu, Babu alamar nadama a tare da ita balle asa ran tuba"
Baba yace "ni nama rasa abun faɗa akan wannan yarinyar wallahi, har kunyar shiga cikin mutane nake, saboda abunda take aikatawa"
Wata matar ce ta fito daga wani ɗaki tace "Ai Malam dole a san abunyi, tun bata kwaso mana abun kunya ba, ko ta kwaso wata cutar taje ta gama mana a gida ba"
Maman Sadiya tace "kokuma ta hana yaranmu auruwa ba, tunda gidansu ɗaya kar ace duk halinsu ɗaya"
Saboda tsabar ƙarfin hali irin na Amira, bata nuna tasan da ita suke bama, ta fito abunta zata wuce gurin da ake girki.
Tsawa Usman yai mata yace "Ke! Gidan ubanwa kika tafi tsawon wannan lokacin?"
"Gidan Uban mutum" ta bashi amsa
Amira ta bashi amsar cikin natsuwa.
"Ni kike zagi?' yai maganar yana nunata da yatsa.
"Kai ka ɗaine Mutum a gurin nan? Bana son kalen jaraba fa tom, ban kula kowa ba dan haka a sauraramin"
Baba ne ya kawo wuya, yace "ke wace irin yarinya ce mara albarka haka? Ke yanzu bakiji kunyar haɗa ido damu ba ma? Kin tafi gantali babu wanda yasan inda kike? Kwana biyar Amira ba wanda yasan inda kike?"
"Wai Baba sekai ta min iƙrarin abun Kunya, haryanzu fa ba cikin shege ba ɗan dakan kuka ba ƙanjamau, ba wanda na ajiye balle aji daɗin nunawa, amma kun isheni, nifa wannan abun da kukemin ne yasa na bar gidan nan naje na sarara na dawo"
Usman ya kai mata duka, yace "Amina, maza jeki ki rufe min ƙofar gidan nan, yau sena tattaka wannan ƙaramar mara mutuncin, yadda in akace gobe ta kuma fita bazata fita ba"
Be rufe baki ba, Amira ta dafe ƙeya tai waje, aikuwa Usman ya biyo ta, bata zame ko ina ba se inda Sadiya ke zance ita da saurayinta, tana ihu tana "na shiga uku, zasu kasheni, dan Allah yayanmu kasa baki"
Ta tattake daddumar da suke kai, taje bayan saurayin ta tsaya tana cigaba da ihu, miƙewa saurayin Sadiya yayi yana faɗin lafiya kuwa?
Usman ya ƙaraso yana "Wallahi yau zaki gane kurenki, tunda ke rashin mutunci shi kika saka a gaba, zaki yabawa aya zaƙinta"
Cikin marairaicewa da karairaya, Amira ta cewa Saurayin Sadiya "Yaya dan Allah kasa baki, dukana zeyi dan Allah ka hanashi"
Baba ne ya ƙaraso inda suke shima, wanda hakan yai daidai da shigowar Zailani, Zailani yana dubawa yaga Amira yaga su Usman a tsaye cirko cirko kamar zakaru.
Yace "Wannan almirar uwar gantalin ta dawo kenan, shine daga zuwanta zata fara ɗagawa mutane hankali, tun daga waje ake jin ihunta, gidan ubanwa kika tafi?"
Saurayin Sadiya yace "dan Allah kuyi haƙuri, macece kubita a hankali karku daketa, zaku iyayi mata illa kuyi haƙuri dan Allah"
Usman yace "baka san halin wannan sheɗaniyar bane, shiyasa kake kareta"
Sadiya kam gaba ɗaya takaici ya cikata, ta rasa mema zatayi ta huce, kawai tana zaune tana tsinkar furen soyayya, wannan mahaukaciyar ta watsa komai, kuma ta zubar Mata da mutunci a gaban saurayin.
Amira kuwa kan saurayin ta kalla, ya sha uwar zanna bukar ɗinsa, kawai a ranata taga kansa ma ɗan dakon kara, ga dogon wuya kamar raƙumin dawa, ga yadin jikinsa duk ya tashi saboda tsufa, ji tayi kamar ta ƙyaƙyace da dariya, amma ta haɗiye dariyarta, saboda tasan a jazabar da take.
Yace "koma me tayi ina nema mata afuwa dan Allah, ayi haƙuri a ƙyaleta"
Suna can suna maganarsu tai cikin gidan, da sauri ta shige ɗakinsu ta banko ƙofar ta saka sakata.
Suka koma cikin gida, suna tunanin meye mafita akan Amira, dan lamarin nata sam ba sauƙi kullum ƙara taɓarɓarwa lamarunta sukeyi.
Amina taje zata shiga ɗakinsu, amma ta tarara Amira ta garƙame ƙofa da sakata, tai bugun duniya amma Amira taƙi buɗewa, tun tana bugawa harta koma magiya amma Amira tayi burus da ita.
Zailani ne yace "wai bakyaji ne? Bazaki buɗe ƙofar ba?"
Amira daga ciki tace "bazan buɗe ba, yau ni kaɗai zan kwana a ɗakin nan, kowacce ta tafi ɗakin uwarta ta kwana"
Amina tace "Ai naga ba ubankine ya gina gidan ba, danme zaki kulle ƙofa wane irin wulaƙancine wannan, dalla malama ki buɗe mana ƙofa"
"Bazan buɗe ba, kuma wallahi aka cigaba da takuramin a gidan nan, sena gangamo abunda duk zesa a haɗamu a kullemu"
Zailani yace 'anya wannan yarinyar ƙwaƙwalwarta bata fara samun matsala ba kuwa?"
Maman Amina tace "zunzurutun iya shege ne, ba wani taɓin ƙwaƙwalwa"
Amina kam tasan tunda Amira ta furta baza su kwana a ɗakin ba tasan bazasu kwanan ba, ba yadda ba'ayi ba Amira tace bazata buɗe ba.
Can Amina ta gama zancenta, ta dawo gida tana masifa "Wallahi idan Amira ta kuma shiga sabgata, sedai ayi mutuwar kasako, koni ko ita wallahi, wanne wane irin rashin mutunci ne? Tazo har kan sallayar da nake zance tana kurma ihu, ta nemi ta tattake mana ƙafafuwa, sauran ƙiris ta take masa cinya, gaba ɗaya ta zubarmin da mutunci yau, ji nayi kamar ƙasa ta tsage in shige wallahi"
Amira ta leƙo ta window tace "to maƙaryaciya, ɗuwawunsa na kusa takewa ba cinya, wani abu a tsomale kamar an jiƙa tsimma, zakizo ki ishi mutane yan yen yen, Wallahi in dai baza'a dena min cin kashi a gidan nan ba, kunya yanzu kuka fara jinta"
Sadiya tace "to dan ubanki ke ina naki tsomalallen? Waye yake zuwa gurinki banda 'yan iska irinki?"
"To ai da sauƙi, tunda dai ana zuwa ɗin, ina zaune zaki sha mamakin wanda ze Auri Amira, ƙasaitaccen mutum dan ni me tsadace"
"A gidan ubanwa wani me tsada ze kwasheki? Kara da kiyashi, ya kwashi cuta?"
Bata kulata ba, ta jefowa Amina wayarta ta window tace "ke kuma ga wayarki nan, wannan matsiyacin saurayin naki Na'ibi yake ko liman ya ishi mutane da kira, be iya komai ba bashi da ko sisi se kiran wayar tsiya, ƙazami me yawo da silifas"
Maman Sadiya ce da suke cewa Ummma tace "dan Allah ku ƙyaleta, idan ba hakaba a banza ranku ze cigaba da ɓaci, bazata canza hali ba"
Sadiya tace "malama ni buɗe ƙofa zan canza kaya"
Amina tace "tun wuri ki nemi nayi, dan tace bazata buɗe ƙofar nan ba"
"Saboda me bazata buɗe ba"
Tace "kowa sedai ta kwana a ɗakin uwarta, yau ita kaɗai zata kwana a ɗakin"
"Saboda ɗakin na ubanta ne? Wallahi seta buɗe"
Sadiya taje ta shiga jijjiga ƙofar, tana wani irin mahaukacin bugu, da gudu Baba ya fito daga ɗaki yace "Au Halima, kema biye mata zakiyi kuyi? Shikenan maza biye mata ku taru ku haukatani, koku ɗoramin wani ciwon daze ajali na"
Amira tace "ko ciwo be kamaka ba zaka mutu, dama gashi ka tsufa, ai da ka ƙyaleta, wallahi naso ta jijjige ƙofar ɗakin nan yau, dama ga damuna ta kusa, nikuma in jijjige tagar kowama ya huta, in damuna tazo kowa yaji jiki"
Suna ji suna gani haka suka yiwa Amira Allah ya isa, suka tafi ɗayan ɗakin cikin ƙanensu, wanda harda masu fitsarin kwance a cikin yaran, haka suka shiga suka kwanta, dan Amira bazata taɓa buɗe ƙofar ba kome zasu yi, dan idan ta furta zatayi abu se tayi, sedai ai mata duk abunda aka ga dama.
Sadiya tai ƙwafa tace "ai dai bazata dawwama a ɗakin ba, wallahi gobe in Allah ya kaimu sena mata dukan tsiya kona samu in huce, yau bala'in nata kusan a kaina ya sauka, gara mu daku a kece raini dan uwatta"
Amina tace "kedai bari, wallahi ina da abubuwan yi da yawa a ɗakin nan, amma saboda hatsabibanci tai mana wannan iskancin, wallahi karki saurara mata ki mata shegen duka, zan tayaki , dan ni kaina yau na gama ƙulewa, tafa fasamin waya jefomin ɗin da tayi"
"Kema seki fasa mata baki ki huce, naga gidan nan kamar tsoronta akeji, zamu koya mata hankali"
Ɗakunan iyayensu duk da ƙannensu, ga kakarsu bata nan balle su kwana a ɗakinta, haka suka kwanta cikin yara, shimfiɗar banda zarnin fitsari ba abun take, ƙarshe a ƙasa suka kwana, Sadiya nata tsinewa Amira tana mata Allah ya isa.
Da Asubar fari, Kafin kowa ya tashi, Amira ta tashi, taje tai alwala ta ɗau sallaya tai waje, ta bar gidan, ta koma soron kusa da ƙofar gida ta shimfiɗa tai zamanta, seda aka kira sallar Asuba taji alamar mutanen gidan sun fara tashi, ta zare sakata tai waje abunta da daddumarta kame me zuwa tuhajjud.
Lunguna ta dinga bi tai nisa da gidan, ta samu guri tai sallar Asuba, sannan ta cigaba da bin lunguna ta tafiya hankalinta a kwance, tai tafiya me nisan gaske sannan ta samu masu Napep suka fara fitowa, ta tsare wani ta kwatanta inda ze kaita.
Gidan Anty Fa'iza ne, safiya ce sosai lokacin da taje, ta ƙwanƙwasa ƙofa Ta ɗan daɗe tana ƙwanƙwasawa kafin a buɗe.
"Anty Amira kece?" Cewar Bashir daya buɗe ƙofar.
"Eh nice Abban Khairat"
Ya bata hanya ta shige, Fa'iza dale tsakar gida ta kalli Amira ƙafafunta duk sunyi ƙura, ga sallayarta a hannu
"Lafiya kuwa Amira?"
"Lafiya lau" ta bata amsa
*Amma na ganki da sassafen nan"?
"To ba dole ki ganni da sassafen nan ba, ana shirin yadda za'a naɗamin duka yau a gidanmu, shiyasa tun Asuba na gudo, dan bazasu dakeni ba kamsr jaka"
Bashir yace "Shiyasa tuntuni nace ki dawo gidan nan mu zauna, ki bar musu can ɗin amma kika ƙi, banda abunsu meyasa zasu ce zasu dakeki?"
"Abban Khairat, baka san ita me ta aikata ba, wani lokacin harda halinta itama, ban gayamaka abunda tayimin jiya ba a gurin biki da mukaje ba, daga inda ta gama tiƙar rawarta daga nan ta gudu gida, ban sake ganinta ba se yanzu da taje ta kunno wata wutar a gidan"
Zumɓura baki Amira tayi, ta shige ɗaya ɗakin tai kwanciyarta.
Fa'iza zatayi magana, Bashir ya girgiza mata kai, tare da yi mata alamar tayi shiru, tayi haƙuri.
Ya jata zuwa ɗakinsu.
Gidansu Amira kuwa se gani sukayi ƙofar ɗakinsu Amira a buɗe ta kama gabanta, Baba yace "wannan yarinyar yaushe ta bar gidan nan?"
Umma tace 'waya san mata?"
"Kenan cikin dare ta fice, kokuwa ya akayi?"
"To waye ya sani?"
Suka cigaba da salallami, da jinjina rashin jin Amira.
Baba yace "ni mamakina ko ina ta tafi, a wannan cikin daren oho?"
Umma tace 'ina kuwa zata banda yawon iskancinta data saba?"
Haka Baba ya fita Masallaci yana tunanin ta ina ze ɓullowa lamarin nan.
Amira kam bata farka ba se shaɗaya na rana, hankali kwance ta sha baccinta, ta farka taje ta haɗa Abincinta ta karya, ba tare da ta gayawa Fa'iza laifin da tayi za'a zanetan ba a gida.
Sadiya tana wankin kayanta tace "Allah ya temaki wannan jakar bata kwana a gida ba, wallahi da ta kwana a gida da yau na saɓa mata kamanni"
Amina tace "ina zata kwana a gidan, tunda tasan abunda ta aikata, ta kwana a waje wajen iskancinta"
Sadiya tace "aikuwa da, dan masifa tsakar gida ta bar gidan nan saboda wulaƙanci"
Wata dattijuwace tai Sallama hannunta ɗauke da kaya, suka amsa gaba ɗaya suna "Yadikko sannu da zuwa, Yau Allah yayi an dawo kenan"?
Tace "eh fa, na sha ƙauye sati Uku kenan"
Suka karɓi kayan hannunta, ta ciro kuba a jakarta ta buɗe ɗakinta, Umma ce ta fito daga ɗakinta tana "Sannu da zuwa Yadikko, ya hanya?"
"Alhamdilillah duk suna a gaisheku"
"Muna amsawa, amma da sassafe kika taho? Naga kin ƙarado da wuri?".
Yadikko tace "ai ana idar da sallar Asubahi, gari ya fara haske nace a kaini tasha in hau Mota, ina magajine d ban ganshi ba?"
Sadiya tace "Baba yanzun nan ya fita, amma ze dawo"
Nan suka shiga hira tana basu labarin hanya, Babane yai Sallama suka amsa gaba ɗaya yana ganin ƙofar ɗakin Yadikko a buɗe ya ƙarasa ɗakin yana "Yadikko, ashe kin dawo?"
"Eh magaji na dawo"
Ya shiga ɗakin yana "Sannu da zuwa, ya kika barosu?"
"Lafiya ƙalau Alhamdilillah, waini ina wannan Amira ne? Ban ganta ba tunda na dawo, na saba ana shigowa gidan nan da hayaniyarta ake fara cin karo, amma naji shiru tazo ta sharemin ɗakik nan dan yayi ƙura"
Umma tace "taɓɗijan wace Amiran? Ai Yadikko se fatan Allah ya shirya, dan jiya kwananta biyar bata gidan nan ba wanda yasan inda take"
Zare ido Yadikko tayi tace "ban gane kwana biyar ba, ina ta tafi?"
Baba yace "gantalinta na banza ne, abun ya ƙaru fiye da kima, dan na kira Baffa yazo ya mata faɗa ta shura takalmanta, ta gudu se data kwan biyar bata nan, se jiya ta dawo jiyanma, daga dawowarta ta shiga neman magana, tsakar dare ta buɗe ƙofa ta bar gidan nan, ba wanda yasan inda take, a gaskiya ni Yadikko na gaji da halin wannan yarinyar, an daka an daka amma ba canji, an zaga anyi barazanar amma kullum sake lalacewa take, yanzu har kunyar fiya nake cikin mutane, saboda nunani ake"
Umma tace "bama wannan ba, kar muje ta kwaso mana cuta ta gama mana ita a gidan nan"
Yadkko tace "lallai, Amadu ya mutu ya bar mana jaraba, kace iskancin nata gaba yake ƙarayi, to baze yuwu ba, tun kan ta ƙarsa fanɗarewa ta ɗakko mana abun magana gara asan abunyi"
Umma tace "to Yadikko meye abunyin da za'ayi?"
"Ni nasan abunyin, ke Sadiya koke ko Amina, ingo wayar nan lalubomin lambar wan uwarta, shima yasan abunyi tun wuri, in yakama ya ɗauketa shi ya riƙeta, ai yafimu arziki"
Amina ta karɓi wayar tace "da wani suna akayi saving lambar?"
Yadikko "inaga kamar Ali ne, Alin Kaduna haka zakiga sunan"
Baba yace "Nikam Gwaggo kinga wannan tunanin sam be zomin ba"
"Aini gashi yazomin, tun wuri yazo asan yadda za'ayi da ita kowa ya huta"
Aka lalubo lambar aka miƙamata.
********************
Kamar a mafarki yaji wayarsa tana ringing, ya buɗe idanunsa ya janyo wayar, seda yayi murmushi sannan ya ɗaga ya kara a kunnensa, amma yai shiru yana sauke numfashi.
Cikin muryarta me daɗin sauraro a kunnuwan Imran kamar me raɗa tace "My Own"
"Mmmm" ya amsa ba tare da ya kuma cewa komai ba.
"My own" ta kuma maimaitawa.
"My heart" ya amsa.
"Yawwa, dama so nake naji ka amsa, bacci kake ne?"
"Bacci nake Baby, wayarki ce ta tasheni"
"My own ɗan hutu, bacci da ranar nan, ina fatan kayi salla?"
"Chance na samu, dole inyi bacci idan na koma bakin aiki bana samun hutu sosai, shiyasa nakeyi yanzu kan in koma"
"Hakane, Amma ya sallar kayi kuwa, kasan Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yace salla ginshiƙin Addini ce, wanda ya tsaida ita ya tsaida Addini, wanda ya barta ya bar Addini"
Imran yace "Allahu Akbar, Sayyadata shiyasa nake matuƙar ƙaunarki, nayi salla My Ihsan kwanciyata kenan, bacci ya ɗaukeni kika kirani"
Ihsan tayi ajiyar zuciya tace "bari in ƙyaleka, kwanta kayi baccinka kaji abun sona"
"No, aini jin muryar nan taki ta isheni, ta fiyemin baccin nan da zanyi, ni ji nake da ma kina kusa dani, ki min tausa, jikina ciwo ya ke"
"Mhmm I hope kaci Abinci?"
"Ba kya son zancen kenan? My Ihsan Allah dai ya nuna min ranarvda zaki zama tawa, inyi maganin wannan kunyar taki"
Tace "bafa ka bani amsa ba, kaci Abinci?"
"Wallahi Ihsan banci ba"
Cikin shagwaɓa tace "wato wahalar mim da kanka kake, se ulcer ta kama ka? To nayi fushi"
Ransa a ɗan ɓace ya murɗa ƙofar ɗakim dake cikin falon ya fito, tana zaune tana rubuce rubuce ta ɗago kanta ta kalleshi tace "Abba lafiya kuwa?"
Ɗan girgiza kai yayi yace "lafiya amma ba lau ba, aika Minal ta kiramin yayanta yanzun nan"
"Amma lafiya kuwa Abba? Meke faruwa ne?"
"Saka a kiramin shi dai"
Minal ta tashi ta tafi ɗakin Imran, taje ta tarar da shi a kwance a akan gadonsa yana waya, yana kallon Minal, Amma be kulata ba ya cigaba da wayarsa
"Babyna karki fushi dani mana, baccine ya hanani cin Abinci, haba my" yai maganar cikin shagwaɓa kamar ƙaramin yaro.
Minal mamakine ya kamata, yadda yake waya Amma su idan yana musu magana kamar wani dodo, se da ya kammala wayarsa, sannan yace "ke meye haka kikazo ki ka sani a gaba kina kallona?"
"Dama Abba ne yace yana son ganinka, yanzun nan a falo"
Imran yace 'naji jeki ki bani guri"
Minal ta juya ta na mamakin yayan nata.
Minal na shiga falon ba daɗewa, sega Imran ya shiga da sallama ya samu Guri ya zauna, kusa da Abba a kan carfet yace "Abba gani"
Abba ya kalleshi yace "Imran kasan meyasa na kira ka?"
"A'a Abba"
"Ina zaune a ɗaki, aka kirani a waya akace min wai ƙanwarka rashin ji take yi"
Mummy cikin Rashin fahimta tace "wai wace ƙanwar tasa?"
"Yarinyar nan Amira, ɗazu kakarta ta kirani, wai rashin ji take musu, se ta bar gida tafi sati bata gida, abun ya ɗagamin hankali matuƙa, da kaina naso inje gobe in Allah ya kaimu, amma ina da tafiya ta gaggawa gobe in Allah ya kaimu, ina son ka wakilceni kaje ka jiyomin meke faruwa ne?"
Mummy tace "Abba, wai ina yarinyar nan tana hannun dangin uban ta? Ai sune a haƙƙu su kula da ita, amma wani labarin za'aje a jiyo maka kuma?"
"Yarinyar nan nima 'yata ce, dole hankalina ya tashi, gaba ɗaya na shiga damuwa, Amira 'yata ce gatse gatse kakarta ta gayamin wai yanzu karuwanci take, kuma harta bar gida tayi kwanaki ba a san inda take ba"
Imran ya ɗago da sauri ya kalli Abbansa yace "Wai Abba wannan'yar yarinyar ce take karuwanci? Wannan yarinyar 'yar mitsitsiya?"
"To Gashi nan dai, haka akace min, wai duk ta gagaresu bata jin maganar Kowa, yawonta takeyi"
Imran ya jinjina kai yace "Shikenan Abba, zanje goben in Allah Ya kaimu, inga meke faruwa"
Abba yace "yawwa Imran, Allah yayi maka albarka"
Me kuke tunanin ze faru, idan Imran yaje gidansu Amira, za'a magamce matsalar ko kuma zata masa halin.
(Idan ba'a comment akwai gaɓar da zanje in ajiye in dena rubutawa tabbas🙄🙄🙄 kokuma me so sedai yabi watpad)
Domin gyara, Sharhi ko shawara
Ayshercool
07063065680
[1/4, 9:26 PM] Ayshercool: 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
WUTA A MASAƘA
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P. W. A
*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA)
*BAƘIN TABO (Labarin gasa)
*AƘIDATA (Paid Book)
* WUTA A MASAƘA
SADAUKARWA GA ƘUNGIYAR PERFECT WRITERS ASSOCIATION, DOMIN TAYA MURNAR CIKA SHEKARU BIYU DA KAFUWA
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in
❌❌❌
Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.
4
Imran ya miƙe ya koma ɗakinsa yana sake tunanin Amira, duk da anyi shekaru rabon daya ganta, amma yasan ba babba bace ba yarinya ce ƙarama, amma ace wai harta san ta fara yawon banza, ta bar gida taje tayi kwanaki a wani guri, lallai zamanin nan ya zama se Addu'a kawai.
Amira ta na kwance akan doguwar kujera tana game a wayarta, Sultan ya kirata a waya.
Seda ta ɗanyi tsaki sannan ta ɗaga tace "kiran me kake min haka?"
Yace "na turo miki kuɗinki, Amma kinƙi zuwa ki karɓi wayarki, kuma satin nan muna da aiki fa, akwai bukukuwa hadda dinner"
"Tom naji, se kuma me?"
"Ko zaki zo ki bada training ne? Ina son a baje basira sosai, ga wanda ya baki wayar nan yana ta min tuni, yana nanata min zuwa Abujan nan gurin bikinsa fa"
"Kai ka rabu dani da wannan Abujan"
"Amira meyasa?"
"Ina tsoron inje wani abu ya sameni a hanya fa"
"Insha Allah babu abunda ze sameki Amira, dan Allah ki yadda muje, zamu samo kuɗi sosai fa"
"Gaskiya zuwan nan nawa Abuja ƙila wa ƙala ne, babu tabbas sedai insha Allah gobe in Allah ya kaimu zan shigo, zan bada training"
Sultan yace "Dan Allah Amira kiyi tunanin, ina jiranki".
Tace "abunda na yanke zakaji, karka damu"
Sukayi Sallama ta ajiye wayar, Fa'iza ta kalleta tace "Amira, wai har yanzu baki bar maganar zuwa Abujan nan ba? So kike ki ƙarawa kanki abun faɗa ko?"
Amira tace "An daɗe ba'a faɗa ba, ko naje ko banje ba baza'a fasa faɗa ba, dan haka ni be dameni ba"
"Amira ba yanzu nake jiye miki ba, gaba akeji musamman idan Allah ya baki miji, ko bayan kin haihu a dinga faɗin abunda kikayi"
"To waini kinji nace miki zani ne, bafa zuwa zanyi ba"
"Gaskiya ce dai, ko ba kyaso dole in gaya miki ita"
Amira ta miƙe tace "Ni tafiya ma zanyi"
"Allah ya kiyaye hanya" Fa'iza ta bata amsa
Khairat tace "Anty Amira dan Allah ki zauna karki tafi"
Amira tace "Sorry daughter na, ai zan dawo insha Allah, ina son nima naje gidanmu ne, amma ina dawowa"
"To ki dawo da wuri"
"To Shikenan, Insha Allah zan dawo da wuri, ki gaishemin da Abbanku"
Fa'iza bata kulasu ba, Amira ta fice ta kama hanyar gidansu.
Da sallama ta shiga Kamar yadda ta saba, sedai duk da akwai mutane a tsakar gidan babu wanda ya amsa mata, itama bata damu ba ta wuce ɗakinsu, ta cire hijjabin jikinta ta fito tsakar gida, da niyyar yin alwala sakamakon kiraye kirayen sallar magariba da akeyi, Yadikko ce ta fito daga banɗaki, tana ganin Amira tace "Ke Daga ina haka?"
Amira tace "ni yakamata in tambayeki saukar yaushe?"
"Ban sani ba, ina tambayar ki kina tambaya ta"
"Daga waje mana, naje wani gurine" Amira ta bata amsa.
"Wato ke abun naki cigaba yayi, har ki bar gida sati guda ba wanda yasan inda kike ko? Wallahi Amira iskanci ba abunyi bane"
"Yadikko, tun a baya Yakamata a gayamin haka, ba a yanzu ba da nai nisa, Iskanci yana kaimin yana min rana, dan haka bame zuwa rana tsaka yace in dena in hanu"
Yadikko tace "Hakama zaki ce? Baki da ta ido ko Amira? Kike faɗin Iskanci ya miki rana"
"To da dare yaimin, ai rana yayi min, ina zaune waze dinga bani kuɗi, Iskanci ma sana'a ne na kasa na samu, dan haka yamin rana".
Tana gama maganar taja butarta tai banɗaki, bayan tayi alwala taje ta tada salla.
Amina tace "aikin banza, dama dena wannan sallar kikayi, dan ba karɓuwa take ba, kije ki gama bin maza a waje kiyi saɓo san ranki, dan munafunci kuma kizo ki tada salla ƙaryar banza kawai"
Amira tai mata shiru, ta cigaba da sallarta, ta idar tayi adddu'ointa ta koma gefe ta kama wayarta, ba tare da ta sake tankawa kowa ba.
Shikam Imran gaba ɗaya abun duniya ya tsaye masa, daya tuna Wai Amira ke karuwanci, meta sani a sha'anin rayuwa, yaushe ta san ciwon kanta da har zata kai jikinta ga maza, a biyata kuɗi har ta fita tayi sati bata gida dan abun takaici.
Yana cikin tunanin ne Ihsan ta kira shi, yasa hannu ya ɗaga wayar, ya saka a kunnensa tare da yin Sallama.
Ta amsa masa sannan tace "My kana Lafiya?"
"Lafiya ƙalau my heart, ya kike ya mutan gidan?"
"Lafiya ƙalau, But it seems like something is wrong with you?".
"No, Babu wata damuwa dama zanje kano n gobe in Allah ya kaimu"
"My me zakayi a kano kuma?"
"Eh Abba ne ya aikeni, zanje ganin wata cousin sister ɗina ne"
A sanyaye Ihsan tace "cousin sister kuma My? Na zaci cousins ɗinka duk mazane? Baka taɓa gayamin kana da cousin ba mace ba"
Imran yace "ta ɓangaren Abba ina da cousin mace, mazan da kika sani duk na ɓangaren Ammi ne"
"Amma ba zaka daɗe ba ko?".
"Ihsan, yarinya ce fa ƙarama, Abba ne yace inje in duba masa ita, kuma dan yana da inda zashi ne goben in Allah ya kaimu, da da kansa zeje ya ganta, ki kwanatar da hankalinki Yarinya ce ƙarama sosai, dan nasan kishi ne yake damunki"
Ihsan tai nannauyar ajiyar zuciya tace "My own, tabbas kishine ke damuna, ina sonka sosai shiyasa nake kishinka, Allah karya kawo lokacin da zan buɗe ido in ganka da wata, bazan iya jurewa ba My"
Ta ƙarasa maganar a raunane, kamar za tayi kuka.
"Ihsan meye abun ɗaga hankali kuma? Imran naki ne ke kaɗai, kin san halina bana kule kule, musamman idan kikayi duba da yadda soyayyarmu ta fara, kuma na gayamiki yarinyar ƙanwata ce, yarinyace sosai, wata matsala ce ta taso Abba yace inje in duba masa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 31