Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Allah ya kyauta, tunda lokacin da suka ƙulla wannan sharrin ban sani ba, Allah ya kyauta kawai zance" Ihsan tana kuka, haka mahaifiyarta ta sa ta a gaba suka bar gidan. Ammi ta tashi zata sake rufe Minal da duka Abba yace "A'a ki ƙyaleta haka, kema magninki ki ɗau yadda ki bawa ƙawa, har in bana gari ki barta taje ta kwana a gidan ta, wake me ƙawa, Allah yasa hakan ya zame miki darasi" Haka suka tafi gida, Anty kuwa riƙe hannun Amira tai tace "Congratulations my dear, Allah ya wanke ki yau" Amira murmushin yaƙe kawai tayi, suka tafi gida. Ranar kusan kwana sukai Amira na rarrashin Imran, dan kuka ya dingayi sosai kamar ƙaramin Yaro, ya rungume Amira yana  "Am sorry my wife, ko yafemin Amira, nayi zaton wuta a maƙera ne, ta shammace ni ta tashi a MASAƘA, ki yafemin Amira" "Amran, mungama wannan maganar ai, ni ba abunda kai min" Ammi tayi kuka sosai da sosai, akan abunda Ihsan ta aikata mata na lalata mata 'ya. Khalid ya taɓa nuna yana son Minal, Ammi ta nuna se tayi karatu me zurfi. A satin Abba yaiwa Khalid magana, akan in dai haryanzu yana sonta suzo ayi Magana. Aikuwa Khalid jiki na tsuma ya sanar da iyayensa aka aika gidansu Minal. Sati guda da zuwan su Amira Kano, Yadikko ta rasu, sedai mutuwar ta girgiza Amira sosai, Imran yace ba inda zata ta'aziyya. Amira tace "nima bance se naje dole ba, amma na yafewa Yadikko duniya da lahira, Allah ya yafe mana gaba ɗaya" Imran ya jinjinawa haƙurin Amira da tausyi, Ammi kuwa sosai take son wanke laifukan ta a gurin Amira, dan haka mussaman take zuwa ta rakata awo, tayi mata girki tai ta bata haƙuri tana neman yafiyar ta. Da Imran ya koma Lagos kuwa, Ammi tace Lallai Amira ta koma gidanta da zama, Anty kuma tace bame ƙwace mata 'ya, da ƙyar a kai sulhu Anty ta ƙyale Amira a gidan Ammi. Sosai Minal ta dinga jin kunyar Amira, Amira kuma ta nuna mata tamkar ba abunda ya taɓa faruwa, kamar bata san Minal ta aikata wani abun ba. Da fari Ammi ta dena shiga sabgar Minal gaba ɗaya, amma Amira ta nuna mata illar yin hakan, Minal ta nemi afuwar Amira, Amma Amira tace ta manta da Wannan zancen, ta ɗauka ba wani abu da ya taɓa faruwa. Watan cikin Amira tara da kwana uku ta fara naƙuda, Ammi ta kaita Asibitin su Anty, aka karɓi haihuwar ta a can, ta haifi kyakykyawar 'yarta mace wadda ta ɗebo kamannin Ammi sosai. Washegarin haihuwar Imran ya dawo Kaduna, yai murna sosai da haihuwar, yaiwa Jaririyar huɗuba da sunan mahaifiyar Amira Fatima zahra. Haihuwar tai daidai da lokacin bikin Minal, dan haka aka haɗa bikin da Sunan. Ihsan kuwa komawa tsohuwar harkarta tayi gaba ɗaya, ta koma gurin wannan mutumin da ya fara ɓata ta, wanda ya kwaso cutar ƙanjamau itama ta samu, ƙarshe tazo kyan da take taƙama da shi ya gushe, saboda larura, kuɗin da suka tara ta wannan mummunar hanyar suka ƙare, ga rashin lafiya ga babu. Imran kam Seda Amira ta sake haihuwa, sannan ya nema mata makaranta, ta samu Admission taje tai karatun midwifery. Suka zauna cikin kwanciyar hankali da ƙaunar juna, ga zuriya da Allah ya albarkace su da ita, kuma suka shirya da uwar mijinta suka zauna lafiya, Minal ma ta Khalid yana sonta, sedai itama Allah ya jarabceta da fitinar ƙannen miji, duk da ga gida ga gida suka zauna, amma suka sata a gaba basa ƙaunarta. Zumuncin su Amira ya ɗore, ita da Fa'iza, Abba ya samawa Bashir aiki a wani babban kamfanin abokinsa a Kano, kasancewar yana da degree yayi karatu. Sultan ma ya bar sana'ar DJ, ya koma makaranta. Amina kuwa harta koma ga Allah, tana hauka tuburan, Sadiya ta samu wani me mata uku ita ta huɗu ta aura, kishiyoyi da 'ya'yan miji suka maida ita tamkar baiwa, sedai duk da abun nan da sukaiwa Amira, baya hanata temaka musu. Jajircewar Imran da gaskiyarsa akan aiki, yasa ya kai har muƙamin General na Sojoji, gefe ga kasuwancin sa yana yi, ga mace ta gari da tarin zuriya. TAMMAT BI HAMDILLAH, DUK DA NACE GAJEREN LABARI N, SE GASHI YA KAIMU IN DA BAN ZATA BA, INA FATAN AN AMFANA DA DARUSSAN DAKE CIKIN LABARIN, KUSKUREN DAKE CIKIN LABARIN KUMA INA FATAN UBANGIJI ALLAH YA YAFE MANA BAKI ƊAYA. HAR ILA YAU ƘOFATA A BUƊE TAKE DOMIN GYARA, SHARHI KO SHAWARA KO TUNTUƁENI KAI TSAYE AYSHERCOOL 07063065680 KAR KU MANTA LITYAFIN RUƊIN ƘURUCIYA SHIMA YAZO DA NASA SALON NA MUSAMMAN, DAN ZAN IYA CEWA NASA SALON YAFI WUTA A MASAƘA MA, KU HAZARTA KUYI SUBSCRIBING AKAN NAIRA 300 KACAL KAR AYI BABU KU. NAGODE ƘWARAI DA ƘAUNAR DA KUKA NUNAMIN AKAN LITTAFIN NAN. KU KASANCE DANI DON CIGABA DA SAMA MUKU DA LITTATAFAI MASU ILIMANTARWA DA FAƊAKARWA. TAKU HAR KULLUM AISHA ADAM (AYSHERCOOL) 0706306568. An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 31 of 31