Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
"Sannu Imran, ka ga yadda ka koma kuwa?" Murmushi kawai Imran yai Yace "to Ya za'ayi, tunda mun riga mun shiga aikin" Alhaji Hashim yace "gaskiya ne, Allah ya ƙara muku ƙwarin gwiwa, se ka samu isasshen hutu kuma" Imran yace "Yallaɓai ai ba hutu, nan da sati biyu insha Allah zan koma Lagos" Abba yace "Lagos kuma?" Imran yace"eh Abba" Ammi tace "nifa gaskiya na gaji da wannan aikin, haba dan Allah kaga yadda ka koma kuwa?" Abba yace "ki gode Allah tunda yana raye" Imran yaita zuba ido amma be ga Ihsan ba, suka hau mota domin komawa gida, Abba yace "gaskiya wannan karon in zaka koma Lagos, ka tafi da Amira, tunda wancan karon da Ihsan ka tafi, wannan tafiyar a tafi da ita!!!... SHARE PLEASE! AMIN AFUWA BAN EDITING BA ABUBUWA SUNYI YAWA (Ina ɗimbin godiya ga Comments ɗin da kukemin, nagode ƙwarai, sedai batun in dinga posting kullum baze yuwu ba, abubuwa sunmin yawa, ga sabon littafina na RUƊIN ƘURUCIYA zan fara, masu tambayar document na WUTA A MASAƘA ban kammala littafin ba, yanzu nake kan rubuta shi, ina godiya da kulawa" Ayshercool 07063065680 [2/6, 7:35 PM] Ayshercool:         🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 WUTA A MASAƘA PERFECT WRITERS ASSOCIATION (WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS) https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P. W. A *Story and written by* AISHA ADAM (AYSHERCOOL) The experience writer of *ABDUL JALAL* * WATA KISSAR.... (SAI MATA) *BAƘIN TABO (Labarin gasa) *AƘIDATA (Paid Book) * WUTA A MASAƘA https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in ❌❌❌ Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.                                                                                      39_40 Shiru Imran yai be ce komai ba, Ammi ma ba tace uffan ba, jira take suje gida ta tabbatar idan da gaske Abba yake Wannan maganar. Gidan Imran suka nufa kai tsaye,aka ajiye Imran da Amira, Amira tace zata bi Alhaji Hashim su koma gida, yace "wani gidan kuma Amira?" "To ai ban gayawa Anty zan zauna ba, kuma bani da lafiya" "Ai ga magnin nan ya dawo, kije ki kula dashi, zamu dawo muyu masa sannu da zuwa ta mussaman". Ammi se hararar Amira take, Amira ta nuna kamar bata ga me Ammin take ba. Suka shiga cikin gidan, ɓangaren Ihsan a rufe na Amira ma haka, Amira ta duba Kitchen ɗin falo, ta ɗakko mukulli, ta buɗe part ɗinta, ta kalli inda Imran ya zauna a kan kujera, tace "Naga Ihsan bata nan, bari in haɗa maka ruwa kai wanka". Jinjina mata kai yayi, ba tare da yace komai ba, taje ta haɗa ruwan ɗumi a banɗakin bedroom ɗinta. Ta fito falo tace "Captain bisimillah na haɗa" Ya miƙe yabi bayan ta, yana cike da mamakin ina Ihsan ta tafi haka? Ba ta san da dawowarsa bane ko kuwa me hakan yake nufi? Duk da ta kwan biyu ba ta gidan, amma komai nata tsaf da shi, Imran ya samu ruwan ɗumi, yai wanka kan ya fito har ta shiga Kitchen, ya zauna a gaban mudubi yana ƙarewa kansa kallo, shi kansa yasan ya rame, saboda anyi gwagwarmaya a dajin nan. Amira ta shigo zata masa magana amma tai turus tana kallonsa, se taga kamar ba shi ba, ya zama wani ƙato sosai. Ya kalleta yace "Ya dai?" "Amm bakomai, da..daama zance ne, in kawo maka Abinci nan in na gama?" "No zan zo nan falon in ci"  ya faɗa a taƙaice. Ya fito Falo, ya buɗe jakarsa ya fito da wando na sojoji da shirt ya saka, Amira ta zo ta ajiye masa kayan Abinci, ta haɗa masa tea, da dafaffiyar doya da miyar ƙwai. Yadda Imran yake zura Abincin nan a tumbinsa, zaka san lallai ba ƙarama wahala yaci ba, Amira se kallonsa take kamar ba ta taɓa ganinsa ba, ita tausayinsa ne ma ya dinga kamata, duk yai duhu. Amira tace "Sannu" Imran ya jinjina mata kai kawai, ya cigaba da zura Abincin sa. Kallon gefen kafaɗarsa tai tace "meya sameka a nan?" "Bullet ne" ya bata amsa. "Harbin ka akayi?" "Eh harbi ne" Ta jinjina kai, can ya ture kayan Abincin yace "ya ƙoshi" Amira ta kwashe kayan Abincin, ta kai Kitchen, taje bedroom ta ɗakko masa bargo da fulo, ta fito tace "ga fulo ka kwanta kafin ta dawo daga gurin aikin" Imran ya karɓa ya kwanta tare da lumshe idonsa. Har ta miƙe zata tafi yace "Amira" Seda tsigar jikinta ta tashi, ta waigo tace "Na'am" "Ya jiki?" "Naji sauƙi ai" Ɗan ƙura mata ido yai, dan sabon salo ta saka uban hijjabi taƙi cirewa, amma duk da haka kana iya gane ta rame sosai, kamar wanda a kaiwa dole yace "Meya sameki ne?" "Bakomai, kawai rashin lafiya ne" ta bashi amsa, Yai ajiyar zuciya be kuma cewa komai ba. Ta koma ɗakinta, tana cigaba da hamdala, kasancewar Imran yana raye. Anty kuwa tana ganin Alhaji Hashim shikaɗai tace  "yaya, ina Amiran lafiya dai ko?" "Lafiya ƙalau, Mun ɗakko Imran, ya dawo lafiya ƙalau" "To ina Amiran"? "Na baro ta a gidan mijinta" Anty tace "Daddy why? Ya za'ai ka bar musu ita?" "To Anty ya kike so ayi?" "Gaskiya ban niyyar ba da Amira Yanzu ba, sena san meye matsayinta a gurin Imran" "A'a matarsa mana" "A'a fa Daddy, nifa ban gane kan wannan abun da kayi ba, nan na zauna na baka labarin irin abunda ke faruwa kuma seka bar masa ita" "Calm down Madam, yarinya ba ta da lafiya, ita ta fara hango mijinta taje ta taro abunta tana murna, ga sirikanta kawai se in taho da ita, haba Antyn Yara" "Gaskiya ni dai banji daɗin abunda kai ba Daddy" "To Allah ya baki haƙuri, amma gara da na barota a can, dan Yarinya na kewar mijinta, ai tsakanin miji da mata se Allah, ki ƙyale sha'anin yaran nan kawai" "A'a dole in dinga saka ido, saboda baza'a mayarmin da 'ya bora ba" "Koma dai menene, kiyi haƙuri" Anty tace "ba wani inyi haƙuri, ka yi min laifi kawai" "Naji kuma ai na bada haƙuri, ai nima 'ya ta ce" yai maganar yana murmushi. Ammi kuwa bayan sun koma gida, ta samu Abba a part ɗinsa, ya kalleta yace "ya dai sarkin ƙorafi?" "Magana nazo muyi" "Maganar me ne?" "Wai dagaske kake da Yarinyar nan ze tafi Lagos?" "Eh dagaske nake" "Amma saboda me?" Abba yace "ban gane saboda me ba, Saboda matarsa ce, wancan lokacin ya tafi da Ihsan, wannan karon ya tafi da Amira" "Amma.... Abba yace "bana son Amma nan dan Allah, na gama Magana wannan karon da ita ze tafi" Ammi ta harzuƙa, amma ta dake tace "naji da ita ze tafi, amma ina son kayi tunani a raba musu gida, dan gaskiya Yarinyar nan ba ta da cikakken tunani, kan Imran yai tafiyar nan ta kama Ihsan ta daketa, harta fitar mata da jini" Abba ya kalleta yace "ban gane ta daketa ta fitar mata da jini ba?" "Ai shine bayanin da nake maka, shiyasa ni tun farko da kai shawara dani ba zaka yanke Wannan hukuncin ba, yana zaman zamansa yana da wadda yake so ka ƙaƙaba masa Auren Wannan yarinyar mara kunya mara ta ido, gaskiya a raba musu gida, kar ta yiwa 'yar mutane lahani" "Kinga saurara, da na yanke hukuncin Auren nan, seda naji ta bakin Imran kan ayi Auren nan, kuma zanje gidan zanji abunda yake faruwa, da kaina inga akwai yiwuwar raba musu gidan, ina son Imran yai zama me adalci a tsakaninsu shiyasa na haɗasu, amma zanje Gidan da kaina" Gabanta ya ɗan faɗi bayan tayi tunanin idan ya samu labarin taje Gidan taci mutuncin Amira fa? Lallai ita ma se nata ran ya ɓaci. Da sauri tace "Amma ai da ba se kaje ba, kawai dai na gaya maka ne kasan hukuncin da ya dace ka ɗauka, kuma ai be kamata a bar Ihsan ita kaɗai ba, tunda lokacin da ya tafi da Ihsan ita Amiran ba ta gidan" "Nifa na gama yanke hukuncin da naga ya dace dan haka ki rabu dani" Yai Maganar tare da miƙewa ya bar mata falon nasa gaba ɗaya ta raka bayansa da uwar harara. Ammi ɗakinta ta koma, ta ciro wayarta ta kira Ihsan, Ihsan na ɗagawa Ammi tace "ke wai kina ina ne?" "Ina nan Ammi, meya faru ne?" "Kina nan a ina, yau mijinki ze dawo, suka tafi da waccan shashashar gurin taro shi, ke ba kya nan, muka biya muka ajesu a gidan su, nan ma ba kya nan, ke wace irin mara wayoce ne haka?" "Au Ammi dama yau ze dawo? Ai ni babu wanda ya gayamin fa, Yanzu yana ina?" "Ke kina zaune harse an gayamiki, ita ya a kai ta sani? To ki hanzarta ki tafi gidan, dan kin bari ta fara tararsa, Allah ya kiyaye dai amma ki hanzarta ki koma ki karɓi mijinki" "To Ammi Insha Allah" Ihsan ta katse wayar tace "Kai, taɓɗijan, Lallai banga ta zama ba, ta shiga harhaɗa jakarta zata koma gida. Sosai bacci ya kwashe Imran, lokaci lokaci Amira ta kan leƙo ta duba taga yana lafiya, sannan ta koma ɗakinta. Ƙarshe ta dawo falon ta zauna, tana karatun littafi a wayarta. Se azahar ya tashi daga baccin, ya cewa Amira zeje masallaci, seda ya fita Sannan maƙotansa suka san ya dawo, a nan suka gaggaisa suka masa Barka da zuwa, tare da yi masa barka da arziki. Ya koma gida ya tarar har Amira ta ajiye masa Abincin Rana, ya nemi Guri ya zauna akan kujera ya lumshe idonsa. Ƙarar buɗe ƙofar Amira ne ya sa shi buɗe ido ya kalli inda take, crazy jeans ta saka, da wata fitinanniyar riga, attachment ɗin nan har ƙugunta, kamar za tayi rawar galar, hannunta riƙe da ƙaton robar popcorn. "Captain ka dawo? Ga Abinci fa" Seda Imran ya ɗan shagala da kallonta, can ya dawo hayyacinsa amma bece Komai ba. Kusa da shi Amira taje ta zauna tace "wai ko wani abun yana damunka ne?" Girgiza mata kai yai alamar a'a. "To sakko kaci Abincin, in dai Ihsan ce ta kusa dawowa tana gurin aiki ne, nasan tunaninta kake" Da sauri Imran ya kalleta, itama ta ƙureshi da ido, babu ko ƙiftawa, zuciyarsa ta shiga bugawa da saurin gaske, a jere ya dinga ajiyar zuciya, ya miƙe ya zauna a ƙasa, ta zuba masa Abinci. Ya miƙe ƙafa yaci abunsa, dan ba ƙarya Amira ta iya girki, sedai yana ci yana satar kallon Amira, duk da ta rame amma kayan sun mata kyau sosai, sun zauna a jikinta. Ta maida hankali tana kallon TV kamar ba ta san yana kallonta ba, seda ya gama yace "Am done, zoki kwashe kwanukan" Maimakon ta amsa, juyowa tai da Wani irin kallo, ta ɗan lunshe idanunta, seda Imran ya ɗan dirirce, cikin rangwaɗa ta zo gabansa ta kwashe kwanukan, ta dawo falon ta zauna, ta kalleshi tace "ko kana buƙatar wani abun ne?" Ya girgiza mata kai alamar a'a. Suna nan zaune kamar kurame, Anty ta kira Amira a waya, Amira ta ɗaga wayar tasa a kunnenta tace "Assalamu alaikum, Anty" Anty tace "wa'alaikum salam, shine kika biyewa Daddy ya maida ke gidan Imran ba tare da ɗaukar wani mataki akan abunda ake miki ba ko?" A shagwaɓe Amira tace  "Ba haka bane Anty, shine yace in zauna fa" "To ni ba ruwana tunda kika koma, ba tare da ɗaukar mataki ba, in wani abu ya faru zance Allah ya kyauta ne kawai" "Subhanallah, Anty bafa haka bane, Allah Daddy ne yace sena zauna" "To shikenan naji, naji yacemin dake Imran ze koma Lagos ko?" "Eh nima haka naji yace" "That's very good, zan ganki kafin ku tafi Insha Allah, ko dai inzo ko kuma ke kizo" "To Anty nagode sosai, insha Allah zan zo ma" "To shikenan, hmm Amira kenan, har kin ware daga rashin lafiyar ko saboda kinga mijinki" Gaba ɗaya kunya ta kama Amira, Bata sake cewa komai ba har Anty ta kashe wayar. Ta ƙasan ido yake sake kallon Amira son ransa, gaba ɗaya bata da makusa, tana da ƙira me kyau ga iya gayu, ga shagwaɓa, gata 'yar wanka sedai abunda ɓata masa rai dai ɗaya ne, Amira was prostitute before. Ihsan ce ta buɗe ƙofar falon, ta shigo fa Sallama, ta na shiga ta tarar da Imran a zaune, da gudu ta ƙarasa in da Imran yake ta faɗa jikinsa tana faɗin "oyoyo my heart, you are welcome" Rungumeta shima yai yana murmushi yace "Thank you sweetheart, ina kika tafi haka? Baki je taroni ba, kuma na dawo ba kya nan?" "Am sorry my, naje gurin aiki ne, kuma ba wanda ya gayamin yau zaka dawo, i really miss you my dearest love" Tai maganar ta na sake maƙalƙale Imran, shima maƙaletan yai a jikinsa, yana shaƙar daddaɗan ƙamshin turaren da ke tashi a jikinta. Ɗaga kai tai ta kalli Amira dake zaune, tana ta watsa popcorn ɗinta a baki, ga shigar dake jikinta, ta nuna kamar ita kaɗaice a falon bata san sun wanzu a gurin ba, haka kurum taji a ranta yanzu idan wani abu ya shiga tsakaninsu fa? Take ƙirjin Ihsan ya buga da ƙarfi, amma ta daure tace "let's go in My dear, i really miss you, muje ciki in nuna maka irin yadda nai missing ɗinka My D" Ba kunya se ga Imran ya ware yana murmushi, ya rungume Ihsan suka shiga part ɗinsu, Amira ta bisu da kallo tai wani murmushi me ciwo tace "da ni kuke zancen, ni dai tunda Allah ya dawo da kai lafiya Alhamdilillah" Tana shiga part ɗinta, kiran Fa'iza ya shigo wayarta, rabon da suyi waya da Fa'iza tun tafiyar Imran da Anty ta zo ta tafi da ita. "Anty Fa'iza, yau kin tuna dani ne?" Fa'iza tace "ban sani ba, sena ɗura miki ashar tukuna, kira nawa na miki ba kya ɗagawa, kuma ba zaki biyo ba, ni na fara tunanin ko wani abun ne ya sameki ma, na kira Abban su Imran yace kina lafiya ba kya jin daɗi ne kawai, nace ko kalar naki laulayin kenan na wulaƙanci" "Wai ba damar Mutum yai rashin lafiya, se a fara wani laulayi a'a naƙuda nake" "Bar ganin ba kya kusa dani, kikamin iya shege sena zageki" Amira tace "to Allah ya baki haƙuri, ya kike ya gida ya Yayana?" "Kowa lafiya ƙalau, ya jikin naki?" "Naji sauƙi Alhamdilillah" "Wai meya sameki ne?" "Mhmm, bani da lafiya ne kawai, kuma a ka zi aka turamin miji Zamfara, dole hankalina ya tashi in kasa lafiya ai" Fa'iza tace "ba shakka daɗi miji, sannu Amira wai yaushe kuka daidaita ne haka, har ake Wannan kewar da ɗaga hankali a kansa?" "Kinji Anty Fa'iza da wata Magana, mace da mijinta ai se Allah harki dinga tambaya ta wai yaushe muka shirya, kin manta lokacin da kike min iyayi ke ga me miji, to nina yanzu na hau layin ai" "Ke bana son Iskanci irin naki, nifa Yadikko ta matsa akan lallai se sunzo gidan ki, nifa na rasa ya zan mata, in ma ki sa musu lokaci, kokuma ki gansu ko kin shirya ko baki shirya ba" Amira tace "Akan me zasu zo ko na shirya ko ban shirya ba, hak akeyi? Kice musu bana gari kawai" "Ta yaya, bayan Abba yace musu kina nan, gara ki san abunyi, zuwa za suyi nan kusa" Amira tai ajiyar zuciya tace 'ke ba zaki zo ba?" "Amira bani da lafiya, kuma bani da kuɗin mota ne" "Zan turomiki, kuzo a ranar ku juya a ranar, kuma ki taho min da su Khairat ɗina" "Iyee dan wulaƙanci, aikuwa ba zan zo ba" "Anty Fa'iza ba haka bane, zaman da nake a gidan nan ba ni kaɗai bace, ina da kishiya kuma ba zaman lafiya muke ba, bana son su zo su samu abun faɗa, ko suyi wani abu daze zubarmin da mutunci a gabanta" Anty Fa'iza tace "Eh to kuma hakane, shikenan zan biyo su muzo tare, mu taso da Asuba, nasan takwas zuwa tara munzo, a dawowa ma mu taho da wuri, shikenan, in sun tsaida ranar na miki Magana" "To shikenan, in zaki taho ki taho min da kayan daɗi kin san mara lafiya" "Mijinki be san in da ake sai da kayan daɗin ba ne? Ba zan siyo ba, kina ta wani kwana kwana Allah ya raba lafiya". Murmushi kawai Amira tayi, ta kashe wayar ta kalli cikinta tace "wai wa ya ga Amira da ciki, ko ya zanyi oho min?" Ihsan ta kalli Imran a shagwaɓe tace "my Own naga ka rame sosai" "To ya ba zan rame ba, wata guda a daji, bamu daɗe bama, duk da an karkashe wasu, But Alhamdilillah muma mun samu gagarumar Nasara" "Allah sarki My, ai ban san yau zaka dawo ba, amma gayamin me kake so in dafa maka kaci?" Tai maganr tana shafa gefen fuskarsa. "Ai naci Abinci" ya bata amsa "Kamar yaya kenan?" "Amira ta dafa Abinci ta bani" Jiki a saluɓe ta kalli Imran tace "saboda me zata dafa abinci ta baka kaci?" "Saboda na dawo a galabaice, ke kuma ba kya nan, dole ina buƙatar Abinci" "Amma my meyas baka kirani a waya ba?" "Da wace wayar? Ni wayata ba caji a ciki" "Dan Allah My kar ka sake cin Abincin ta, ni wallahi bana son mu fara faɗa daga dawowar ka, amma gaskiya banji daɗi ba, ina fatan wani abu be faru tsakaninku ba yadda na tarar da ita daga ita se kai a gidan nan da wannan shigar" Imran yace "Look Ihsan, don't add me another stress please, I need to rest, ban shirya fara jin complains ɗinki ba, tunda har yanzu baki yadda da ni ba shikenan" A shagwaɓe tace "no is not like that at all My, na yadda da kai have a rest my Dear" Tai maganar tana shafa fuskarsa. Se zuwa magariba sannan Imran ya watstsake gaba ɗaya, kamar ba shiba sedai ramar nan tana nan da yayi. Bayan ya dawo daga sallar isha'i, Abba ya kira wayarsa suka gaisa, Abba yace "Imran ya jiki ha gajiya?" "Abba komai lafiya ƙalau Alhamdilillah" "Kaje Asibiti kuwa?" "Ai Abba lafiyata ƙalau ba wata matsala" "No, duk da haka yakamata a bincika lafiyarka, ban so daga dawowarka in fara maka surutu akan gidanka ba, amma kayi haƙuri ba yadda na iya ne, nace mahaifiyarka tai min magana akan tana so a raba musu gida, wai Amira ta daki abokiyar zamanta harda ji mata rauni, ya a kai ban san Maganar ba?" Imran yai ajiyar zuciya yace "Abba, misunderstanding ne kawai tsakaninsu, kuma na sasantasu tun kan in tafi, dan haka ba wata matsala Abba" "Yawwa ɗan gidan Abba, haka nake son ji dama, Ubangiji Allah yai muku albarka gaba ɗaya" "Ameen ya Allah Abba, nagode sosai" Ya taka ya ƙarasa gida, dan bejin ze iya zuwa ko ina, yana buƙatar yaje gida ya huta. Duk da yadda Imran yake a gajiye, ga raunuka da suke jikinsa, amma ya ɓoye ga rashin cikakkiyar lafiya, amma ba Wanda ya gayawa, haka ya suka sha soyayyarsu shi da Ihsan, yana mamakin yadda har yanzu Ihsan bata taɓa fashin period ba, yana fatan ubangiji Allah ya dube shi kar ya jarrabe shi da rashin haihuwa, mussaman ga irin aikin da yake yi, duk da ita mutuwa ba ruwanta da aikin da mutum yakeyi, amma kowani lokaci ze iya rasa ransa saboda aikin nan, gashi bashi da wani ɗa, be sani ba ko Allah zesa ya samu nan kusa. Ya shafa kan Ihsan dake kwance a jikinsa yace "My, haryanzu babu wani labari ko, ina son Yara sosai Ihsan" Gaban Ihsan ya faɗi tace "My ka fara ƙosawa ko? Ni kaina ban san meyafaru ba, Amma dan kayi haƙuri ka tayani Addu'a, Ni kaina ina fatan in samu ɗin" "Ba ƙosawa nayi ba, ki kwantar da hankalinki, Allah yana sane damu ze bamu very soon insha Allah" "Allah ya amsa" "Ameen Swtheart" Imran soyayyar su kawai suke sha da Ihsan, sam Amira ta nuna bata damu da zamansu bama, ta dinga ɗauka tamkar ita kaɗai take rayuwarta a gidan. Imran yai kamar ya manta da zaman Amira, amma ƙasan zuciyarsa yana saƙa abubuwa da dama a kanta, yana mamakin kulawa da tausayawa da take nuna masa lokuta da dama, haka nan seya dinga jin tausayinta, mussaman idan ya tuna ranar da take cewa ta barshi da Allah, ita marainiya ce, duk da abun da yake mata hakan be hana daze tafi tai hawaye ba. Kuma be hana ta dinga tura masa messages na fatan Alkhairi ba, be hana da ya dawo ta karɓeshi hannu bibbiyu ba. Ya sauke ajiyar zuciya, ya kalli agogo yaga dare yayi sosai, Ihsan na ta faman baccinta, ya miƙe a hankali ya ɗau system ɗinsa ya fita falo ya zauna. Amira kam idonta biyu a lokacin, tana falonta Salla, ta idar da Addu'onita, ta cire hijjabin zata koma bedroom, amma jin motsi a babban falo yasa ta ɗan tsorata, ta Ajiye hijjabin ta lallaɓa za taje ta rufe ƙofar falonta, karma in wani abun ne ya shigo mata ɗaki. Sedai tana leƙawa ta hango Captain yana danna System, ajiyar zuciya tayi, ta fito falon, ɗan ɗaga kai yayi ya kalleta, ya mayar ya sunkuya yana aikinsa. A kusa dashi ta zauna, ta kalli System ɗinsa, taga samfuran bindigogi ne kala kala, yake dubawa. Ta ɗan jingina da jikinsa tace "ka bani tsoro fa" Be kalleta ba yace "tsoron me?" "Motsin ka naji, naji tsoro sosai" "Meyasa baki bacci ba har yanzu?" "Baccin ne be zo ba" Ya jinjina kai yace "yakamata ki kwanta, mussaman da baki da lafiya kinyi rama sosai" Amira ta sake kwanciya a jikinsa tace "ai ni dama nafi son in rame ɗin" "Meyasa kike so ki rame?" Tana sane tace "Na fi son in koma kamar Ihsan nima" "No, gara ki zauna yadda kike kinfi kyau" Ɗan ƙura masa ido tai, tai murmushi tace "dagaske ina da kyau Captain?" "Eh kina da kyau mana, tunda kike kama dani, kuma kinga ni kyakykyawa ne" Sosai Amira take dariya, tace "ji yabon kai, ka bari a faɗa mana, ba fa wani kyau ne da kai ba fa" "Ki bari mata ta ta jiki, kina cewa bani da kyau, duk abunki tunda mata ta tace ni me kyaune nasan ina da kyau, kika bari ta jiki faɗa zakuyi, kuma ki ka mata rashin kunya in zaneki" Tsaki Amira tayi tace "dan Allah wai zaman me nake da kai, tunda baka sona, dan Allah ni ka sakeni in Auri wanda yake sona". Kallonta Imran yai yace "so kike Abba yai fushi da ni kenan?" "Ai cewa zan nina ce ka sakeni, dan Allah ka sakeni, wallahi bayan tafiyar ka hawan jini seda ya kamani saboda ɓacin rai" tai maganar tana hawaye "In jinin ya hau Akwai magani ai" Kallon Imran take, sam be damu da damuwarta ba, miƙewa tai ta tafi ya barshi a gurin. Yabi bayanta da kallo har ta shige, seda ya ɗanyi murmushi, daga ƙarshe ya koma ɗaki ya kwanta, amma da yayi juyi se Amira ta faɗo masa rai, Gaba ɗaya tunaninta ya hanashi bacci, Abincinta me daɗi, muryarta ma me daɗin sauraro. Ihsan ta shiryawa Imran breakfast, ta fita gurin aikinta, da yake Imran be tashi daga bacci ba, ta tafi gurin aiki, Ihsan na fita, Amira ta kwashe kayan Abincin Ihsan, ta jera masa nata. Da Imran ya tashi daga bacci, yai wanka ya fito, ya zauna ya kwashi Abincinsa, ba tare da sanin wanda yai girkin ba. Se la'asar Ihsan ta dawo, ta shiga Kitchen da hanzari ta ɗora girki, daf da magariba ta kwaso Abincin ta kawo dining ɗin babban falo, sedai ta tarar da kwanukan Abincinta a ƙasan dining. Mamakine ya kamata, ta bubbuɗe taga yadda ta zuba masa Abinci be taɓa ba, tana tsaye tana tunani sega Imran ya shigo, ya ƙarasa dining ɗin yana faɗin "My kin dawo? Ya aikin?" Ta kalleshi tace "ya a kai nai maka girki ba ka ci ba?" Imran yace "ni ɗin naci mana". Ta buɗe foodflask sega Abinci a ciki, babu alamar an taɓa. Yace "Aini ba wannan flask ɗin na gani da safe ba" "Kaga irinta ko, inyi magana ace na fiye neman Magana, wanne na ajiye idan ba Wannan ba" Amira ta fito daga sashenta, hannunta riƙe da ɗan ƙaramin kwandon shara na Kitchen, Imran yace "Amira, meyasa kika ɗauke Abincin Ihsan kika ajiye naki? Haka akeyi" Amira tace 'Ai ba Ihsan ce kawai matar gida ba, nima matarka ce, akan me sedai ta dafa ta baka ni zaman me nake, to nagaji shiyasa nai mata haka, rashin adalcin da akemin ya fara isata saura ma raba kwana" "Shut up!" Imran ya daka mata tsawa, "ke duk yadda za'a lallaɓaki sekin nemi magana, meyasa ki kai haka? Ko dan kin ban Abinci ranar da na dawo naci, shine ki kai haka? Ke idan baki nemi Magana ba ba kyajin daɗi ko? Waye ya saki? Kuma da ubanwa zaki raba kwanan fitsararriya mara Kunya"? Wata uwar harara Amira ta watsa masa tace  "koma da ubanwaye" "Ni kike gayawa haka?" "Tsakanin wuta da Aljanna wacce mallakinka da zaka sani, wanda zesa inji tsoron gaya maka magana?" Take ta koma masa ainihin Amiran ta, mara jin magana. Cikin zafin nama

Chapter 22 of 31