dai tana da jiki ne"
Imran yace "naga alamar rigima kawai kike ji, ki kwanta seda Safe Allah ya tashemu lafiya, sena dawo"
Ya rufe datar sa, yai shiru yana sake nazarin hotunan Amira, ga video da aka bata kyautar mota, ga na rawa da tayi a gurin, yai ajiyar zuciya, gaba ɗaya ransa ya gama ɓaci yama rasa abunyi kwata kwata.
Da Asubar fari Amira ta bar Hotel ɗin nan, ta kakkarya ATM ɗinsa ta watsar, ta tafi tasha taje ta hau Mota, gaba ɗaya fargabar kar a saceta a hanya ta kau a zuciyarta, babban burinta kawai ta bar garin Abuja.
Ƙarfe takwas na safe tuni sun kamo hanyar Kano, suna tafe tana Addu'a Allah ya kaita gida lafiya.
Sultan ma tunda Amira tai masa gargaɗi, ana sallar Asuba suka hau motarta da aka bata suka bar Hotel ɗin da suka kwana, suma suka kamo hanyar Kano, Suna tunanin wace cakwakiya Amira ta haɗa haka, wadda ta sakasu barin gari ba shiri.
Shikuwa Ango yana banɗaki a rufe, ya jijjiga ƙofa ya buga ƙofar amma ba wanda yaji, saboda ta kulleshi Sannan ta kulle ɗakin, tun yana bugawa da ƙarfi harya haƙura ya nemi guri ya zauna a banɗakin nan ya kwana har gari ya waye, yana nan zaune yana tunanin yadda zeyi ya bar gurin nan, tare da zargin kansa yadda ya faɗa tarkon Amira da wuri haka, yayi mamakin Yadda Amira ta yaudare shi haka, babban abunda ya dame shi shine yadda yasan ana can ana jiransa gurin tafiya ɗaurin Aurensa.
Gurin ɗaurin Aure kuwa ana ta neman Ango, an nemeshi sama da ƙasa an rasa, an kira layinsa ba adadi amma taƙi shiga, ga lokaci yana neman ƙurewa ba wanda yasan inda ya tafi sam.
Amira kuwa kafin sha biyun rana tuni ta isa garin Kano, tana shiga Kano tayi kyauta da kayan Ango Hassan a danja, ta bawa mabaratan danja kayan, hatta kuɗinsa da ta kwashe a hanya tai kyautar su (sadaka da kayan Sata 🙄😲)
Ko gida bata je ba ta wuce gidan Anty Fa'iza, Anty Fa'iza ta kalleta tace "sannu"
Amira bata amsa ba ta ajiye kayanta, ta kamfaci ruwa ta shiga banɗaki, zuwa tayi ta watsa ruwa tai wanka, ta shiga Kitchen ɗin Anty Fa'iza ta zuba Abinci taci, seda ta ƙoshi ta samu guri tai kwanciyarta, bata kula Anty Fa'iza ba ita m bata kulata ba.
Se bayan azahar Sannan ta tashi, tai salla, Kiran Sultan ne ya shigo wayarta, ta ɗaga tace "ya ake ciki ne?"
Sultan yace "muna Kano tun ɗazu, amma meyasa kikace mu dawo haka ba shiri?"
Amira tace "ba ruwanka, tunda ka dawo lafiya shikenan, na zaci za'a kamaku a hanya ma, saboda ba'aiwa motar license ba, yanzu dai so nake ka samo me siye, a saida motar nan a bani kuɗi na"
"Amma meyasa zaki siyar?"
"Saboda ba tare aka bamu ba, ka saida mota ka aikomin da kuɗina, sannan ka haɗomin da kuɗina na gurinka"
"Shikenan, yadda kike so, za'a duba me siyan"
"Yawwa"
Amira ta katse kiran.
"Yanzu Amira seda kika je Abujan nan ko? Duk kafafen sada zumunta babu abunda yake yawo banda hotunan ki, Amira shifa rashin ji bashi da rana, Sannan kuma bashi da riba, yanzu hotunan ki se yawo suke gaki ga Arne, ga kyautar mota, ke bakya gudun bakin mutane Amira? Bazaki riƙe maraicinki ki tsuguna in da Allah ya ajiyeki ba ko Amira?"
Ko ɗaga kai Amira ba tayi ba, balle ta tankawa Fa'iza tai mata banza, kamar ba da ita take ba.
Fa'iza ta kira Usman a waya ta gaya masa ga Amira ta dawo tana gidan ta, suna gama wayar, Usman yaje ya gayawa Yadikko.
Baba yace "bari a kira kawunta a gayamasa, gata ta dawo"
Yadikko tace "kul, kar wanda ya sake ya kirashi ya gaya masa, idan fa kuka gaya masa yazo, to ɗauketa zeyi ya tafi da ita, idan kuma ya tafi da ita shikenan, nikuma sonake wannan ɗan nasa ko shi su dinga zuwa, saboda a samu su Auri wata daga cikin yaran nan"
Umma tace "to yanzu Yadikko baza'a ce musu gata ta dawo ba?"
Yadikko tace "baza'a faɗa ba, ai gara ta ƙara baƙin jini a idonsu, yadda bazasu ɗauketa su haɗa da 'ya'yan su ba"
Haka kuwa akayi, babu wanda ya kira su Abba yace ai Amira ta dawo, sedai tuni hotunan ta sun zaga ko ina, ta zama topic of discussion, ko ina zancenta kawai akeyi, labari ya cika inguwarsu hadda batun motar da aka bata.
Ango Hassan kuwa an bada cigiyarsa har gurin 'yan sanda, ana zaton ko sace shi akayi.
Ma'aiktan Hotel sukaje da safe gyara ɗakin Amira, Amma suka tarar a rufe, sun zaci ta fitane, suka tafi, da yamma ma ɗakin a rufe har dare, aka ɗakko mukullin ɗakin aka buɗe sedai ba kowa a cikin ɗakin.
Jin an buɗe ɗakin yasa Hassan a dinga jijjiga ƙofar banɗakin yana ihu, wanda zeyi sharara ya fita da gudu, yaje ya tattaro ma'aikatan Hotel ɗin, akazo aka buɗe sega Hassan a cikin banɗaki, daga shi se gajeren wando, jikinsa se tsuma yake saboda wahala.
Nan aka shiga kallon kallo, dan gaba ɗaya labarin ɓatansa ya fara zaga gari, gashi ba wanda be san anyi bikin ba, kasancewarsa shahararrene, amma abun mamaki se gashi a Hotel, ya kwana a banɗaki.
Haka aka samo masa kaya ya saka, yana ƙudurce irin wulaƙancin da zewa Amira idan ya haɗu da ita, shikenan mutuncinsa ya zube a idon duniya.
Abba kam komai ya ƙwace masa, ya rasa mene mafita akan wannan lamarin, yana son yasa a duba masa Garin Abuja a nemo Amira, Amma yana tsoron a gane suna da alaƙa da ita, ko ta fuskanci ana nemanta ta gudu.
Imran kuwa tuni ya sauka a Kaduna, ya sauka cike da takaicin yadda Amira ke nema ta zubar musu da mutunci, dan shima yaga yadda hotunanta dana Mahaifinsa ke yawo, ana tambayar anya ba 'yarsa bace.
Koda Imran ya koma gida ya lura da damuwar dake kwance a fuskar mahaifinsa, sedai be masa maganar Amira a gaban Ammi ba, dan kar tayi faɗa, dan tun da ya dawo take masifa akan Amira, Abba dai be tanka mata ba, se tunanin mafita da yakeyi.
A masallaci Imran ya samu Abba suka taho tare, Imran yace "Abba naga kana cikin damuwa, meke faruwa ne?"
Abba yace "Imran maganar Amira ce, wai yanzu har arnan nan na kudu mawaƙa take hotuna dasu, gashi ana haɗa hotuna na da nata, ana tambaya anya ba 'yata bace? Idan abu ya fito zanji kunya na gaza kula da yarinyar nan harta zama haka"
Imran yace "wai dama Abba kai ma ka gani?"
"Eh Imran na gani, an nuna min tunda na gani na kasa samun nutsuwa, har Kano naje bata gidansu, nace in ta dawo a kirani, kawai naci karo da hotunanta a gurin biki a Abuja, bikin ɗan Professor Latif"
Gaban Imran ya faɗi, ta tabbata Ihsan da Amira ta haɗu kenan? Ya dake yace "to yanzu Abba meye abunyi kenan? Yakamata a samu mafita da gaggawa"
Abba yace "munyi maganar da Alhaji Hashim, yace in saurareshi kuma naji haryanzu bece komai ba"
"Abba ba zamu tsaya jira ba, yakama yarinyar nan duk inda take a nemo ta"
Abba yace "A'a, bana son garaje Imran, mubi komai a hankali ka bari zuwa Gobe in Allah ya kaimu inyi magana da Alhaji Hashim, nasan yasa a duba ta a Abuja ne"
Imran yace 'to shikenan Abba, bari muji me zece ɗin, amma ina tsoron taje ta kuma janyo mana wani abun tereren"
"Karka damu, insha Allah ba zata kuma wani abun ba, muyi mata Addu'a Allah ya shirya ta"
Ai shi Imran ba shiriyar Amira ce ta dameshi ba, yadda ze hukunta ta kawai yake tunani, suna zamansu lafiya zata janyo musu abun faɗa a duniya.
Koda suka shiga gida, Imran ɗakinsa ya wuce Abba kuma ya shiga cikin gidan.
A falo ya tarar da Ammi da Minal, suna hira Ammi na kallonsa ta share shi, Minal ce tace "Abba sannu da zuwa"
Yace "Yawwa Minal sannunki"
Tace "Abba me invitation ya kawo fa, an kai maka ɗakinka, saura zanje in karɓo gobe in Allah ya kaimu zamu karɓo namu, zamu kaiwa Anty Ihsan"
Abba yai murmushi yace "Masha Allah, to Allah ya kaimu goben Lafiya"
Daga nan ya wuce ɗakinsa, Minal tace "Ammi wai meyasa baki kula Abba ba?"
"Ke ƙyaleni da maganar uban nan naku, yana nema ya jajubo mana Matsala"
"Ammi matsalar me kuma?"
"Wannan yarinyar ce ta tsaye masa a rai, take gagara shine nima zezo ya ɗagamin hankali, naga yana take taken yaje ya ɗakkota ya dawo da ita gidan nan, shiyasa na ja da baya na zuba masa ido, in ga iya gudun ruwansa karma yaga fuskar daze kawo min wannan yarinyar gidan nan"
Minal tace "taɓɗijan, Ammi cewa fa ake karuwanci take, kinga hotunan ta kuwa a media"?
"Ai shiyasa na zuba masa ido inga iya abunda zeyi"
Minal tace "Wallahi Ammi karki yadda akwo miki karuwa wallahi"
"Barni da shi kawai, ai ya dena ganin walwalata har sena ga matakin daze ɗauka a kan lamarin"
Imran se tunani yake akan meye mafita akan lamarin Amira, kar maganar ta cigaba da bazuwa a ɓata siyasar mahaifinsa, kuma kimarsa ta zube duniya ta zage shi.
Wayarsa ce ta fara ringing, yana jin ringing ɗin yasan Ihsan ce.
"Hello Masoyi"
Imran yace "Na'am masoyiya"
"Ka wuni lafiya?"
"Lafiya ƙalau Alhamdilillah, ya kike?"
"Lafiya ƙalau masoyi, ya naji muryarka wani iri ba lafiya ne? Ɗazu ma da mukayi waya muryarka wani iri, still yanzuma haka"
"Bakomai Baby, don't mind ba abunda ke damuna"
"Baby ya shirin bikinmu? Ɗazu munyi waya da Meenal, tace an kawo katin ɗaurin Aure ko?"
"Eh Ihsan an kawo, za'a kawo miki naki, ina jiran a kawo na party ne in haɗa in kawo miki"
"Yanzu ba zaka zi gobe in Allah ya kaimu ba"?
"Baby kiyi haƙuri, ina ta shirin bikinmu ne"
"My own, naga a gajiye kake bari in barka se Allah ya kaimu gobe, ka kwanta ka huta kaji nawan"
"To cwt heart, have a nice dreams Baby" yai mata kiss ta waya.
Ihsan ta lumshe ido tace "I love You my Imran".
"Love you too baby, am missing you Baby, zan shigo gobe in Allah ya kaimu in ganki"
"Wow nice to hear that My Own, wallahi naji daɗi sosai, Allah ya kaimu kazo kaga yadda na fara canzawa saboda gyaran da nake"
"Allah Babyna, Allah ya kaimu goben, inzo in gani"
"Ameen have a nice dreams Honey" ta ƙarasa maganar tana
Sukayi Sallama ya kashe wayar yana murmushi, sedai Amira na faɗo masa ya haɗe rai gaba ɗaya takaici ya mamaye shi.
Koda Ammi ta shiga ɗakin Abba, kwanciyar ta tayi bata kula shi ba, Abba ya dudduba invitation na ɗaurin Aure da aka kawo, ya fara tunanin yadda za'a fara rabon invitation ga manyan mutane, wayarsa ce ta fara ringing ya ɗaga
"Assalamu alaikum Alhaji Hashim"
"Wa'alaikum salam, Alhaji Ali yarinyar nan fa ta bar garin Abuja, na sa Anyi bincike a ɓoye, bata Abuja, nace kuma can gidan nasu ba'a ce maka ta dawo ba?"
Abba yace "Gaskiya basu kirani ba"
"To yanzu dole mu nemi abunyi da wuri, ka shirya gobe in Allah ya kaimu ka shirya muje Kanon muje mu san yadda za'ayi a neme ta a Kanon, kuma ina son inga yarinyar nan dan a gano meye bakin zaren"
Abba yai ajiyar zuciya yace "Shikenan, Allah ya kaimu goben, zamu haɗu insha Allah se muje muga yadda za'ayi"
Alhaji Hashim yace "to Allah ya bada goben".
Ammi tana jinsu tai juyi taja tsaki, ta gyara kwanciyarta.
Abba ya kalleta ya ɗauke kai, shima yaja Guri ya kwanta.
Seda Safe Abba ya sanar da Imran, zasu kuma tafiya Kano, Imran be musawa Abba ba, ya shirya suka biya ta Gidan Alhaji Hashim, suka ɗauke shi suka kama hanyar Kano.
Suna cikin tafiya Ihsan ta kira Imran a waya, yana ɗagawa tace "My Own ka tahone? Ka ganni nan na maka kwalliya, na maka girki ka taho da wuri Please"
Imran yace "Amm, amm very Sorry Ihsan, Na tafi raka Abba Kano ne"
"Kano kuma?"
"Eh Kano Ihsan, zamuje gurin wannan cousin ɗin tawa dana gayamiki"
"Again, Amma Imran me kuma zaka kuma zuwa yi gurinta? Me zakayi mata hakane? Nikam kodai akwai abunda kake ɓoyemin ne?"
"Calm down mana, ba abun ɗaga hankali bane, ki kwantar da hankalinki kina jina?"
'kaga ƙyaleni dan Allah, nida tun farko baka cemin zaka zo ba da duk ban sa rai ba"
Kawai ta kashe wayarta, Alhaji Hashim da Abba hankalinsu na wani gurin, basu san me Imran yake a waya ba, da yake na gaba a kusa da direba, su kuma suna baya.
Imran ya ajiye wayar ya dafe goshi, baya son ɓatawa Ihsan rai, kuma da alama tana kishi ne sosai, gaba ɗaya haushin Amira ya ƙara kamashi, duk a dalilinta komai nasa na kwaɓewa, kamata yayi yanzu yana can ya fara rabon IV, amma yana nan yana gantalin inda za'a gano ta.
A ɗakin Yadikko aka sauke su, Su Amina se kaiwa suke suna komowa, a tsakar gidan nan saboda su Imran, Amma gaba ɗaya abunda ya kawosu shine a gabansu, wato yadda za'a ga Amira.
"Alhaji Ali, batun wannan yarinyar fa se Addu'a kawai, dan haryanzu babu wanda zece ga inda take, sedai a koma gefe a cigaba da Addu'a"
Alhaji Hashim yace "to yanzu ina da ina take zuwa, kamar ƙawaye ko 'yan uwa haka, dan gaskiya akwai buƙatar a gano inda take a nan kusa, saboda idan hotunanta suka cigaba da yawo, kuma ta cigaba da fitina akwai matsala, na farko siyasar Alhaji Ali zata taɓu, kuma ita kanta yarinyar yakamata a temaki rayuwarta"
Yadikko tace "to yanzu waya san inda a tafi? Kufa kuka zo da labarin a Abuja tai wannan hotunan, har da kyautar mota ta samu, mufa gaba ɗaya ta gagaremu tafi ƙarfinmu, bata ganin kowa da gashi, dan da tana ganin mutuncinmu da bata tsallake ta bar gidan nan ba tare da ta sanar da inda zata ba, zubar da ciki tayi ko warkewa ba tayi ba tasa ƙafa ta kuma tafiya"
Dukda Imran a ƙule yake da Amira, amma yaji hasuhin yadda Yadikko ke ƙara tonawa Amira Asiri a gaban Alhaji Hashim.
"Amm yanzu ba batun wannan ake ba, ina da ina take zuwa, suwaye ƙawayenta"?
"Ai ita ta san inda suke haɗuwa da ƙawayen nata, dan duk irinta ne ita tasan inda take zuwa ta haɗu dasu, dan babu iyayen arzikin da zasu bar yaransu suyi mu'amala da ita tunda ga rayuwar data zaɓa, yanzu haka bance tana garin nan ba tana can inda ta tafi gantalin nata data saba, dan da.....
"Assalamu alaikum"
Amira tai sallama.
Domin gyara Sharhi ko shawara
Ayshercool
07063065680
.
[1/10, 2:59 PM] Ayshercool:
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
WUTA A MASAƘA
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P. W. A
*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA)
*BAƘIN TABO (Labarin gasa)
*AƘIDATA (Paid Book)
* WUTA A MASAƘA
SADAUKARWA GA ƘUNGIYAR PERFECT WRITERS ASSOCIATION, DOMIN TAYA MURNAR CIKA SHEKARU BIYU DA KAFUWA
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in
❌❌❌
Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.
Afuwan banyi Editing ba
11_12
Amsa mata Sallamar sukayi, ta shigo ɗauke da jakarta ta matafiya, Imran na jin muryarta ya miƙe ze fito, Alhaji Hashim ya riƙe shi yace
"Imran, kabi komai a hankali"
Imran ya jinjina kai ya fito, Abba cewa Yake "Imran yi a hankali, banda fushi nan naka"
Imran Yana fitowa sukayi ido huɗu da Amira, seda cikinta ya juya amma tai banza kamar bata ganshi ba, tana ƙoƙarin shiga ɗakinsu.
"Ke daga ina kike?!"
Yai mata wata razananiyar tsawa, seda ƙirjinta ya buga da ƙarfin gaske, amma tai banza da shi, ta fasa shiga ɗakin ta ajiye jakarta a tsakar gida, ta samu guri ta zauna tana tauna cingam ɗin bakinta, tana jiran Imran yai mata duk abinda yaga dama.
Alhaji Hashim ne suka fito tare da Abba, Amira ta ɗaga kai ta kallesu, sedai kallo ɗaya tai musu ta ɗauke kanta, saboda yadda take jin haushin Abba daga shi har iyalansa, haushinsu take ji.
Alhaji Hashim yayiwa Imran alama da ido sannan ya kalli Amira yace "Masha Allah, ashe wannan ce 'yar tawa da kake bani labari, tubarkallah gata me kyau kamarka ɗaya da ita, a bamu tabarma mu zauna daga nan mu gaisa da ita"
Yai maganar yana nazarin Amira, kasancewar sa masani a fannin kimiyar sanin halayen ɗan Adam.
Kana ganin shigar jikinta zakaga fitinaniya, bata kuma kallonsu ba ta ɗauke kanta tana wasa da yatsun hannunta, Imran kam kamar ya ɓarar da ita haka yake ji.
Aka miƙo tabarma Abba ya shimfiɗa suka zauna, ita kuma Amira na kan turmi, ganin sun zauna ita kuma tana sama, yasa ta miƙe zata bar gurin.
Alhaji Hashim yace "ina kuma zakije?"
"Ɗakinmu mana" ta bashi amsa kai tsaye, shi dai Abba yakasa cewa komai se binsu da ido.
Alhaji Hashim yace "haba Amira muda muka zo ganinki se kuma ki tafi ki barmu?"
Amira tace "Niba gurina kuka zo ba, kunzo gurin mutanen gidan nan ne, dan a gaya muku halina kuma an zauna an gaya muku komai, kuma in zuwane ai a baya Yakamata azo a ganni ba a yanzu ba"
Tai maganar ƙwalla na taruwa a idonta.
A hasale Imran yace 'Ke ana miki magana zaki yiwa mutane rashin Kunya?"
"Karka ƙara yimin tsawa na gaya maka, akan me ina ruwanka dani? Tunda kazo ban kulaka ba meye nayimin tsawa" Amira tai maganar cikin tsiwa.
Imran ya harzuƙa, amma Alhaji Hashim ya girgiza masa kai yace "Yaya Imran gaskiya ka dena yi mata tsawa, kai baka san lallaɓa ƙanne akeyi ba, ai nan ba barikin soja bane, zoki zauna mu gaisa mana"
Tana zumɓura baki tazo ta zauna a ƙasa akan takalmanta.
"Ya kika zauna a ƙasa? Hau kan turmin ki zauna mana" inji Alhaji Hashim.
"A'a ai bekamata kuna ƙasa ina sama ba" tai maganar tana share hawayen da take ta ƙoƙarin riƙewa.
Shiru Abba yayi yana kallonta daga baya yace "Amira ina wuni"
Shiru tayi ta sunkunyar da Kai, ya kuma maimaitawa amma bata ɗago ba kanta na ƙasa.
Alhaji Hashim yace 'Abbanki yana gaisheki baki amsa ba"
Shiru ta sake yi ta ƙi ko ɗago kanta, Imran yaji kamar ya tashi yayi ball da ita, ana mata magana ta yiwa mutane banza.
Kamar wadda aka yiwa dole ta kalli Abba tace "ina wuni?"
Yai murmushi yace "lafiya ƙalau, kin dawo lafiya?"
Tace "eh"
Yace "masha Allah"
Alhaji Hashim yace "naji ance har kyautar mota aka baki, ina motar ne mu shiga a maida mu gida a ciki" yai maganar yana murmushi.
Ita dai Amira bata san wannan mutumin ba, amma ya fara isarta da magana, amma ta maze tace
"Ai nace a saida motar a bani kuɗina, ni bana son Mota"
"Eyya baki bari munzo mun gani ba, shikenan tunda kin siyar, da cewa zanyi Allah ya tsare yasa a kashe lafiya, amma tunda kin siyar ba damuwa, amma meyasa kika siyar ba zaki dinga hawa ba ki ragewa kanki zirga zirga, gashi ance ma zaki fara fitowa a waƙa ko?"
"Nifa ba wata waƙa da zanyi, kawai dai munyi hotuna ne, kuma ni nafi buƙatar kuɗin akan motar shiyasa na siyar da ita"
Abba yace "Amma Imran ya gayamin ya baki kuɗi, meyasa baki kirani kince in ƙara miki wasu ba kika tafi Abuja"
Imran ya ƙure ta da ido cike da takaicim yadda ake wani lallaɓata, ita kuma tana Magana tana tura baki, aikuwa ta ɗago ido sukayi ido huɗuda Imran ta galla masa harara, Sannan tace "Ni bana roƙo"
"To ai babanki ne, babu laifi dan kin roƙe shi"
Yadikko kuwa tuni ta ƙule, dan a zatonta za'ai ƙuli ƙulin Kubura da Amira ne, tana zuwa su dirar mata da zagi da cin mutunci, amma taga saɓanin hakan, Alhaji Hashim se lallaminta yake yi, ko Imran ya yunƙura ze mata wani abun, seya hana shi yi.
Amira tun tana ɗaure fuska tana amsa tambayoyin da ƙyar, a hankali seta fara sakin jikinta, musamman da Alhaji Hashim, saboda yadda yake mata magana a nutse cikin rarrashi.
A hankali Abban ma da take basarwa ta fara ɗan sakin jikinta dashi, amma da sunyi ido huɗu da goga Imran seta Galla masa harara.
A nan take gaya musu "ai ni da banyi niyyar zuwa Abujan nan ba, dole ce ta sani naje"
Abba yace "wace irin dole?"
"Kuɗi nake tarawa, wanda zasu isheni in tafi ƙasar waje karatu"
Alhaji Hashim ya ɗago ya kalleta yana nazarin amsoshin da Amira take basu, dsga bisani yace "Masha Allah, ai wannan tunani ne me kyau, Allah ya bada sa'a, yanzu dai mun taho da katin bikin Yayanki, mun bawa mutan gidan nan nasu, kema ga naki musamman aka taho miki dashi, ai zakije ko?"
Amira ta kalleshi tace "waye kuma Yayana?"
"Imran mana gashi a kusa dake"
Ɗan ja da baya tayi nesa dashi tace "Aikuwa wadda zata aureshi zata kwashi mara Imani, kuma ni ba Yayana bane ba, dan nasan baze ci zalin ƙanwarsa da suke ciki ɗaya ba kamar yadda yayi min ba, hadda ze kainin Enugu Sojoji su koyamin hankali, ni bazan zo ba"
Tai maganar tana satar kallon Imran, seda Abba yai murmushi yace "ƙyaleshi, dan ƙaniyarsa an gayamasa kowama irinsa ne, taya za'a kaiki wani Enugu, rabu dashi, yakamata ki halarci taron bikinsa"
Amira tace "ni gaskiya bana son zuwa inda za'amin wulaƙanci, ko a dinga gayamin magana, bana mantuwa ko an shekara dubu idan ina raye, in dai aka ci mutuncina bana mantawa, shiyasa bana son zuwa, kuma ni gaskiya wannan kallon da yake min tsoro yake bani, wallahi idan naje gidansu ze iya dukana, dan bashi da tausayi"
Ba Abba ba shi kansa Alhaji Hashim seda yayi dariya banda Imran da ya sake shan kunu, Alhaji Hashim yace "haka yake wannan fuskar shanun ai, ki ƙyaleshi ai ba gurinsa zaki zo ba, kuma ba dan shi zaki ba"
"Amira tace Ai da dan tashi ne cewa zanyi Al'yasa a fasa Auren, dan bashi da tausayi, ranar da yazo nan ya dinga ball dani da ƙafarsa, kuma nasan bazewa ƙanwarsa ba" tai maganar tana sake yiwa Imran kallon banza.
Abba yace "Allah ya baki haƙuri, ni dai fatana kizo ɗin kinji yarinyar kirki, ni zan aiko da mota ma a ɗakkomin ke"
Amira tace "shikenan, naji zanzo insha Allah"
"Kin tabattar zaki zo dai ko?"
'bana saɓa alƙawari" ta bashi amsa.
Imran kam ya cika yai fam, gashi an hana shi magana, maimakon su Abba su ɗau mataki, sun biye Mata se lallaɓata suke tana shirme.
Haka suka cigaba da hira da Amira, mutan gidan ma gaba ɗaya abun haushi ya basu, sun saka ran za'aiwa Amira rashin mutunci da tijara, amma an wani sata a gaba se rarrashinta ake kamar ƙwai akan Dutse.
Suna fita Yadikko tace "Kai Magaji tashi maza ka bisu, kaji me zasuce karka kuskura ka bari a tafi da yarinyar nan, maza jeka kaji me suke cewa"
Aikuwa Baba ya tashi, ya biyo bayansu.
Amira ta rakasu har gaban danƙareriyar motarsu, Banda Wadda jami'an tsaro suka rakosu da ita.
Abba yace "zan saimiki kayan anko kema a ɗinka miki, za'a ajiye miki idan kinzo seki saka kema"
Tace "Hmm gayyar soɗi kenan fa, zanzo da tsummokaran da Allah ya bani, abun masu kuɗi ina ni ina saka kayan da masu kuɗi zasu saka"
Amira akwai abun takaici, ana lallaɓata a shawo kanta, tana sake buɗewa, a fusace Imran ya daka mata tsawa yace
"ban gurizan shiga mota, Shashasha kawai"
Seda ta ɗan ruɗe saboda ko yaya yai mata tsawa seta razana, Imran yana mata kwarjini sosai, shiyasa daya mata tsawa jikinta yake tsuma.
Kallonsa tayi ranta a ɓace, annurin fuskarta ya ɗauke ta juya zata koma gida, Abba ya fara yiwa Imran faɗa, ya taka inda Amira take ya ɗakko kuɗi a Aljihunsa ya bata, Amma taƙi karɓa, sema hawaye data farayi kawai ta shige gida.
Jikin Abba gaba ɗaya yayi sanyi, Alhaji Hashim yace "Imran da alama tana shakkarka, amma be kamata ka dinga mata tsawa ba, yarinyar da ake lallaɓawa a gano bakin zaren zaka dinga yiwa tsawa haka? Irin wannan yaran ba kowane lokaci ne tsawa ko kurari ke aiki akansu ba, sema dai ya tunzura su, ita tarbiyya ba ko yaushe take buƙatar tsanani da takura ba, wani lokacin seda rarrashi da jan yaro a jiki, wannan yaro faɗa da zare ido baze mata aiki ba, attention take buƙata da rarrashi, yanzu babban abunda yakamata shine mu samu ta zo Kaduna, kar ace za'abi ta tashin hankali da hayaniya, mu bita a sannu, da tazo shikenan"
Abba
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 31