Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
wuce muje ciki ni" Ai kawai Amira ta sa masa kuka, harda hawaye tace "gaskiya ni ba zan koma ba, haka kawai ni ban san kowa ba ka kawoni ka ajiye ni, se wani kallo na ake ana gayamin magana, ni gaskiya gidanmu zan koma, duk da bamu da komai Amma ni ya fiyemin nan" Imran ya ƙare mata kallo sannan yace "waye yake gaya miki maganar? Koda yake koma me akayi miki aike kika janyo, ubanwa yace kiyi abinda za'a gaya miki maganar, wuce muje ba gidan uban da zaki, in kinga kin fita daga gidan nan to ni ko Abba ne wani ya fita dake, amma daga nan har ƙarshen layin nan, kika fita zasu dawo dake, wuce mu koma" "Dan Allah kayi haƙuri, ni wallahi bazan iya zama a gidan nan ba, ka ƙyaleni in koma" Attention ɗin mutane ya fara dawowa kansu, wata mata tace  "Imran yau fa ranar farinciki ce a gareka, banda cin zali dan Allah, nam ba barikin soja bane" Imran kawai yai murmushi, matar na wucewa ya bugawa Amira wata irin tsawa, me matuƙar razanarwa, a gigice ta nufin cikin gidan da sauri, ya riƙo hannunta, yabi ta bayan gidan da ita zuwa sashin Abba. Minal kuwa da akan idonta, Amira ke kuka, Imran ya riƙe hannunta se cewa tayi "Ahha baɗala, kar dai Yaya Imran ake gwadawa karuwancin, aikuwa bari inje in gayawa Ammi" Sashin Abba suka shiga, Amira tana kuka amma tana ƙarewa gurin kallo, dan ita bara taɓa shiga gida me kyan wannan ba a rayuwarta. Abba yana ganinsu yace "oyoyo 'yar gidan Abba" Jin muryar Abban ce yasa ta dawo hayyacinta daga kalle kallen da takeyi. Taje ta samu guri ta zauna, Imran ma ya zauna, Abba yace "ki hau kan kujerar mana"  girgiza kai Amira tayi ta sunkunyar da kanta ƙasa. Abba yace "ai ni be gayamin ɗakko ki ya tafi yi ba, ai da tun daren jiya mun gaisa, se yanzu da safen nan fa ya gayamin" jikin Abba ne ya ɗanyi sanyi, ganin hawaye a idon Amiran. Abba yace "lafiya kuwa Amira? Imran ko kayi mata wani abun ne?" Imran yace "Niba abunda na mata" Amira ta ɗago ta harari Imran, Abba yace "gayamin me yai miki?" "Ni kawai yake ya ɗakkoni, ban shirya ba ban komai ba, ban taho da komai nawa ba, daga ni se kayan jikina,yazo ya ajiyeni ya tafi, tun a hanya nace ina jin yunwa Amma ya ƙyaleni yazo ya ajiyeni ya tafi, kuma banci Abinci ba, kuma ni dan Allah kace ya maida ni gida, ko tasha a kaini in hau mota in koma, ni bana son zama a nan gidan" tai maganar cikin kuka. Abba yace "yi haƙuri ya isa haka, besan baki ci Abinci ba, amma ga nawa cna kije ki zuba kici, za'a kawo miki kayan da zaki amfani dasu, kuma ki kwantar da hankalinki anjima 'yan gidanku zasu zo, ki bari suzo idan aka kammala biki sekuyi tafiyarku gida, kuma abunda yasa ya kawoki nan, kinga akwai rigimar da kika janyo, 'yan Sanda suna nemanki Wannan mawaƙin ya kai ƙararraki, kimga Yakamata muyi settling wannan mtsalar be kamata a ce an kama ki ba, kinga da baki je Abujan nan ba da duka haka bata faru ba" Amira ta share hawayen ta tace  "aini dama bance zan fito a waƙarsa ba, kawai nace masa zanyi tunani ne, kuma ni ƙarya yai min, bikin wannan Hassan ɗin, ɗan gidan ƙaramin ministan man fetur muka je, mun samu saɓani dashi, shine suka haɗa baki" Abba yace "saɓanin me? Kuma meyasa kika je Abuja?" Amira tace  "eh muna harkar bukukuwa, mc da kaɗe kaɗe shine aka gayyacemu can, da mukaje anyi bikin kuma ya biyoni Hotel ɗin da nake muka samu Saɓani". zuciyar Imran kamar ta fashe, saboda maganar Ihsan data faɗo masa  "AN FASA AUREN, SABODA AN KAMASHI A BANƊAKI A HOTEL KARUWA TA RIFE SHI" Wani irin baƙinciki da takaici suka ziyarci zuciyar Imran, Abba yace "shikenan a bar maganar ta wuce, zanyi waya da mahaifin shi Hassan ɗin, Imran miƙo kayan breakfast ɗin nan ka haɗa mata" Imran ya kalli Abba zeyi magana, Amma Abba ya girgiza masa kai. Haka yana ɓacin rai ya haɗawa Amira tea, ga soyayyen dankalin turawa da ƙwai. Amira tace "ni bana cin wannan shayi kawai zan sha" Abba yace "saboda me?" "Ni ƙosai nake so, shi muke ci a gidanmu da Safe" Abba ya kalli Imran daya ɓata fuska yace  "Imran, ko za'a samu me ƙosai a nan kusa?" A ɗan hasale Imran yace "Abba kai ma dai kasan babu wata me ƙosai a unguwar nan, waye ze sai wani ƙosai? Sekace a ƙauye" Abba yace "cin ƙosan ne se a ƙauye?, idan aka ɗan zagaya ai za'a iya samu, ka duba ko zaka samo mata mana" Wani matsiyacin kallo Imran yaiwa Amira, ta ɗauke kanta kamar bata ganshi ba, ya miƙe yana mitar shi a ina ze wani samo ƙosai. Amira tace "ya barshi ma, zanci wannan ɗin". Abba yace "to shikenan, dawo ba se kaje ba" Imran kasa ya jinjina kai ya dawo ya zauna, cike da takaici da ɓacin rai. Amira ta dinga cin Abincinta, Abba yace "ai Munyi waya da 'yan gidanku, suma sun taho suna hanya, yanzu Imran zeje ya karɓo miki kayanki na fitar biki" Amira ba tace komai ba, ta cigaba da cin Abincin ta, yayin da Imran ya ɗaure fuska tam. Ammi ce ta shigo ɗakin Abba, tana zuwa tsakiyar falon tai turus ganin Amira zaune tana cin abincin Abba. "Ke me kike yi a nan gurin nan, har kike cin abinci a wannan kwanon?" Abba yace "Amiran ce baki gane ba, kokuma me?" "In ma na gane ta seme? Me take a nan nake tambaya?" Gaba ɗaya Amira taji Abincin ya fita daga ranta, saboda masifar Ammi. Abba yace "nine nace a kawon ita nan" "Amma inda mutane suke, be isa ta zauna a can ba se an kawota a nan?" Miƙewa Amira tayi tace "na ƙoshi" Abba yace "zauna ki ƙarasa cin Abincin ki" Amira tace "A'a na ƙoshi" Ta juya zata fita, Imran ya tashi yabi bayan ta, yace "ke karki koma cikin gidan nan, biyoni" Tabi bayan Imran, part ɗinsa ya nufa ta bishi a baya, suka shiga falonsa, suna shiga ya mai da ƙofa ya kulle yasa key ya kalleta yace "a nan na yadda ki zauna, karki kuskura kije ko ina daga nan, kinji na gaya miki, kuma wallahi kika min taɓe taɓen abunda ban saki ba, sena ɓata miki rai" Ba tace komai ba ta zauna akan kujera, tana ƙarewa ɗakin kallo. Har yai gaba ya juyo yace "kuma wallahi, idan kika sake kika kuma fito da wani iyayi a gaban Abba, wallahi a gaban nasa zan zaneki, sa'anki ne ni da zaki sa a aikeni siyo miki wani ƙosai, sa'anki ne ni?" Ya tambayeta cikin tsawa. Amira ta girgiza kai, yace "ki sake ki gani, zaki ga yadda zanyi dake, banza kawai". Shiru tayi bata ce masa komai ba, ya wuce bedroom ɗinsa, ya jima a ciki tana ita kuma tana zaune a falon, tayi shiru kamar mayya, be kula ta ba yazo ya fice daga falon, ya kulleta ta waje. Tsaki tayi, ta hau kan kujera 3seater, ta kwanta tai shiru tana tunani, gaba ɗaya ranta a ɓace yake, hankalinta duk yayi gida, burinta kawai ta ganta a gida, dan gaba ɗaya gidan nan da mutanen cikin su ba suyi mata ba, Sannan ta ƙwafe Minal akan abun da tayi mata, abun ya ɓata Mata rai sosai. Ammi kuwa sam Abba ƙim biye mata yayi, taita mitarta harta gaji ta haƙura, daga baya tace  "Nayi waya da  Babar Ihsan, tace min ance mata an canza gidan da za'ayi jeren kayan amarya, zuwa gidanka na Bamako, shine nace meyasa aka canza? Bayan naga gidan Imran ɗinma babban gidane ya ishe su, ya zasuyi da wannan uban gidan su biyu?" Abba yace "Eh akwai dalilin yin hakan" "Meye dalilin?" Ta tambayeshi tana kallonsa. "Zakiji a nan gaba kaɗan" "Nifa na kasa gane kanka tunda bikin nan ya ƙarato, meye bazaka gayamin yanzu ba, ni me zance musu suna nan suna jirana in gayamusu dalili, zau tafi jeren kaya?" "Suma zasu san dililim ba da daɗewa ba, sannan ba wani abun tashin hankali bane"  yana gama maganar ya miƙe ya fita ya barta a falon. Kusan mintuna talatin da fitar Imran, se gashi ya dawo, ya buɗe falon ya ajiye mata leda a gabanta yace  "gashi nan, kayan wanka ne a ciki da tooth brush, ga toilet nan a Falo ki shiga kiyi wanka, idan kin ga dama kiyi abunda ban saki ba, in dawo kiga yadda zanyi dake" Maimakon ta motsa sema lumshe idanunta da tayi, tai masa banza, be sake kulata ba, ya ɗau abunda yake buƙata ya kulle bedroom ɗinsa ya barta a falo, ya kuma kulleta yai tafiyarsa. Gaba ɗaya suka gama shirinsu, Anty Fa'iza bata ƙara so ba, suka kirata a waya tace musu kayanta da nauyi, dan haka su haɗu a tasha gurin hawa mota. Yafikko tace "nikam ban so tafiyar nan babu ni ba, amma duk yadda zakuyi Ke Sadiya da kuma ke Amina, kuyi duk yadda zakuyi, ku janyi hankalin yaron nan kanku, ko shi ko kuma mahaifinsa, mu samu ko wata daga cikinku ne ku aura muma, mu huta, kai Amma Amira ta cuceni da ta ka dani ba damar inje gurin nan, shegiya watsatsiyar Yarinya, mara hankali, ko da yake ta yiwa kanta itama, tunda ta tafi gantalinta ba wanda yasan inda take, ita ma ba taje ba, nima banje ba da kunje ku gaywa Alhaji Ali kar ya ga ba 'azo da ita ba, tana can ta tafi iskancinta, sannan dan Allah duk abinda kuka samo ku ɗan ragomin nima" Haka taita musu zantuka, daga nan suka kama hanya suka tafi tasha, suka haɗu da Fa'iza a can, suka hau Mota. Dasu Umma sukaje gidan su Imran, suma ba wani takansu Ammi tabi ba, amma duk da haka an basu masauki, an kai musu Abinci, Minal se wani gani gani take musu, kamar taga wani abu na daban. Amira wuni tayi a cikin falon Imran, ga yunwa ta isheta, ga waya ba caji ta rasa abunda za tayi taji daɗi kawai ta hau kuka, tayi me isarta sannan ta Share hawayenta. Imran kuwa, suna gurin Bridal shower, shida abokansa dan ya ma manta da wata Amira, shagalinsa kawai yake, sedai lokaci lokaci gabansa ya kan faɗi idan ya tuna mata biyu za'a aura masa, kuma haryanzu daga Ammi har Amaren Babu wanda ya sani. Se bayan isha'i sannan Imran ya dawo gida, shima a gajiye yake sosai, a harabar gidan 'yan mata matan nan na family ɗin su Ammi suka dinga tsokanarsa, wai dama she yana soyayya gashi harzeyi Aure. Amina ce ta hango shi, ta tuni da huɗubar Yadikko, ta tsaya 'yan matan nan suka ragu, sannan ta nufi inda Imran yake, tana zuwa ta zube ƙasa ta gaisheshi. Fuskarsa ba yabo ba fallasa ya amsa mata yace "she kunzo?" Tace "eh munzo tun ɗazu, sedai ba'azo da Yadikko ba, tunda Amira ta hankaɗeta ta faɗi ƙasa bata iya tashi, kuma ita ma Amiran ba'azo da ita ba, babu wanda yasan inda take, tunda ta fice yawonta ba wanda yasan inda take" Imran yace "Ba yawo ta tafi ba, ni naje na ɗakkota jiya" be kuma cewa komai ba yai gaba abunsa. Ya bar Amina a tsaye tana mamaki, gurinsu Fa'iza ta koma, tace "wai dama Amira tana gidan nan?" Fa'iza tace "eh tana nan, tun da muka zo nake zuba ido inga a ina zan ganta, tun jiya Imran yaje ya ɗauketa suka taho" Sadiya tace "wai shi Imran ɗin da kansa?" Fa'iza tace "eh mana, har gidana yaje nemanta". Gaba ɗaya mamaki ne ya cikasu, Amma sukayi shiru, basu kuma cewa komai ba. Imran yana zuwa ya buɗe falon ya shiga, ya sha Manyan kaya se ƙamshi yake, Amira tana zaune tai tsuru da ita kamar kyanwa, be kulata ba ya wuce ɗakinsa, yaje yai wanka ya canza kaya, ya fito falon yaje ya buɗe fridge ɗinsa, komai yana nan yadda yake, bata taɓa komai ba, ya kalleta babu alamar taci Abinci tun breakfast. Ya ɗakko wani ƙaton cake, da lemo ya Kawo ya ajiyemata a gabanta, yakuma ɗaukar kayansa yai waje ya kulleta a ciki. Khalid na ganin Imran yace "Angon biyu lafiya kuwa? Yau a nan zaka kwana ne?" "Eh waccan yarinyace tai ƙoƙarin guduwa da safe, Allah yasa na nunawa security ita, da tuni ta gudu da safe, shine na kulleta a ɗakina" Khalid yaita dariya yace "Yaseen kafi son Amira akan Ihsan, irin wannan tattali haka?" "Nifa daɗina da kai rashin hankali wasu lokutan, ni na gaya maka ina son wannan yarinyar ne? Kawai ba yadda zanyi ne, nasan idan ta gudu nine a wahala, ni za'a sa in tafi yawon nemanta" Khalid baya son yaja zancen suyi faɗa, dan haka ya ƙyale Imran. A daren Amira ta cire kayan jikinta, ta wankesu a banɗakin falon Imran, da yake akwai liquid soap a ciki, ta saka sabuwar  doguwar rigar jallabiuar daya kawo mata, taƙi yin Bacci saboda kar tana bacci, Imran ya shigo ya shiga toilet ɗin nan yaga kayanta a ciki, dan harda underwears ɗinta ta wanke. Seda kayan nan suka bushe, ta kwashe su daga banɗakin, Sannan hankalinta ya kwanta, ta kwanta akan doguwar kujera bacci ya ɗauke ta. Da safe Imran yazo ya kawo mata Abinci, sedai be kulata ba, ya ajiye mata ya tafi, ya maida ita kamar wata ɗaurarriyar Akuyarsa. Ranar Alhamis yakama za'ayi dinner, kowa nata shiri ana hada hada amma an kulle Amira a ɗaki. Gashi ance mata 'yan gidansu zasu zo, amma Imran ya kulleta, gashi tana tsoron masa rashin kunya ya casa ta, dan ba kowa a gurin daga shi se ita. Imran na shiga cikin gida yana son ya karɓi abu a hannun Ammi, Anty Hadiza tace masa "Imran nikam ina Amira ne? 'yan gidansu suna nemanta amma basu ganta ba tunda suka zo" Imran yace "eh zasu haɗu a gurin dinner, tana ɗakina" "Me takeyi a ɗakinka?" "Jiya guduwa taso tayi, shiyasa na rifeta a ɗakin na koma gidansu Khalid, akwai magana fa, naso in samu lokaci in ganki amma ba time" "Labarta min, meye maganar?" Imran ya ɗan taɓe baki yace "zaki ji very soon, Yanzu dai nemomin Ammi" Da ƙyar aka gano Ammi cikin jama'a, ya karɓi abunda ze karɓa ya fita. Mutane wasu duk sun watse sun tafi gurin make up. Amira tana  kwance tayi shiru, tayi kukan ta gaji, Imran ya buɗe ɗakin ya shiga. Ya kalleta yace "kinyi wanka?" Ba tare da ta kalleshi ba tace nayi "Kuma shine kika zauna haka busu busu baki shafa mai ba?" Sekace ya bata man da zata shafa ɗin, banza tai masa kamar bata ji ba. Ya kuma ajiye mata kaya yace "tashi ki shiga bedroom ɗin nan kisa kayan nan ki ɗauki mai akan mirror ki shafa ki zo ina jiranki yanzun nan" Ta karɓi kayan ta shiga ɗakin nasa, ta rufe ƙofa se tsaki take tana zumɓura baki, ta ƙarewa dressing mirror ɗin kallo, mayuka kamar na Mace. Ta buɗe ɗakin ta kalleshi tace "babu me gurguwa a ɗakin" Ya kalleta yace "wace gurguwar?" "Shine man da nake shafawa, ni bana shafa irin wannan" "Kin wuce ko sena zo nayi ball dake? Me kuturwa kike shafawa bame gurguwa ba" Ta bugo ƙofar da ƙarfi ta koma cikin ɗakin tana tsaki, wani danƙareren less ne, dark blue a cikin ledar, an ɗinka shi riiga da skirt, ko ina aka samu size ɗinta oho? Se takalmi da jakarsa, da mayafi da kayan yari da sarƙa. Amira ta saka kayan nan tsaf a jikinta, fuskarta babu makeup ba komai, ta ɗaura ɗankwalin tai wani irin kyau, ta kalli gadon Imran, tsaf dashi tai zamanta a kai. Tana jin yana masifar ba zata fito ba, Amma tai masa banza, a fusace ya buɗe ƙofar bedroom ɗin, ta ɗago idanunta ta kalleshi, kamar ba ita ba, kayan nan sun mata cif a jikinta. Dama  Abba ne yasa yayi wa  Usman waya, yace ya  bashi lambar Fa'iza yace a taho da size ɗin kayanta da takalmi, shine aka ɗinko mata. Tana zaune akan gadonsa, "bazaki taso ba kenan? Waye yace ma ki haumin gado?" Tashi tai daga kan gadon, tana ɗan tura baki, ya kai idonsa kan turarukansa yaga yadda tai masu aiki, ko ina ƙamshi kawai yake. Kawai ya girgiza kai, dan ya gaji da magana, duk taku ɗaya idan tayi, cike yake da ɗaukar hankali, haka ta taho kamar zata bangaje shi ta fito falon ta tsaya, tana hararsa ta gefen ido. Suka fito harabar gidan, mayafin kayan na riƙe a hannunta, bata yafa ba, ta riƙe jaka da hannu ɗaya, wani soja ta hanga da uniform a tsaye a jikin wata mota, sukaje bakin motar, Imran yacewa Sojan "gata nan ka kula da abunda nace maka" Sojan ya jinjina kai, Amira ta kalli sojan ta kalli Imran, Imran Ya haɗe rai yace "idan ta maka rashin Kunya ko taurin kai, ka harbeta ni na saka ka kawon gawarta!!! Amira tace "Na shiga uku, harbi kuma kamar wata 'yar fashi!!! Share Please (🤣🤣 Me Oga Imran ke shirin yine haka? Da cakwalkwalin cakwakiya fa, Ina jiran jin Comments ɗinku) Please don't come to my inbox, And start telling me from page 1 please. Wanda yake nema daga farkon, ya duba watpad @ Ayshercool 7724 Domin gyara, Sharhi ko shawara Ayshercool 07063065680 [1/17, 12:46 PM] Ayshercool:          🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥                 WUTA A MASAƘA PERFECT WRITERS ASSOCIATION (WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS) https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P. W. A *Story and written by* AISHA ADAM (AYSHERCOOL) The experience writer of *ABDUL JALAL* * WATA KISSAR.... (SAI MATA) *BAƘIN TABO (Labarin gasa) *AƘIDATA (Paid Book) * WUTA A MASAƘA https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in ❌❌❌ Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.                                                                     19_20 Imran yace "Eh ka harbeta idan tayi maka rashin mutunci ka harbeta a ƙafafumta" Amira ta tsaya tana kallon Imran, aka buɗe mata ƙofar motar ta shiga, Sojan yaja suka fita, seda Imran yaga fitar motar Sannan ya juya ya nufi gidansu Khalid. Ƙofar wani katafaren gurin gyaran jiki da kwalliya sojan nan yai parking, ya fito ya buɗewa Amira ƙofa, Amira taƙi fitowa ta kalli gurin sannan ta kalli sojan tace "nan kuma ina ne?" "Eh nan ne yace a kawoki, bari in mata Magana" Taɓe baki Amira tayi, ta cigaba da kalle kallenta. Ya koma gefe yai waya, mimtuna kaɗan sega wata farar mata ta leƙo, tai murmushi tace "tana ina?" Sojan yace "gata nan a cikin mota, ki fito ki shiga' Seda Amira taja aji sannan ta fito daga motar ta shiga gurin, matar ta bawa Amira guri ta zauna. Katafaren gurin gyaran jiki ne da guaran kai na mata, gurin ya haɗu sosai. Matar ta nunawa Amira wata kujera a gaban mudubi tace "zoki zauna a nan mu fara kar lokaci ya ƙure" Amira tace "wai me zakiyi min ne?" "Yi haƙuri, ba wani abu zan miki ba, kwalliya ce akace zan miki" "Kwalliya kuma, waye yace kiyi min?" "Kai kekam akwai daru da tambayoyi, daga gidan Alhaji Ali ne" Taɓe baki Amira tayi tace "ki bari inyi salla tukuna, dan idan akayi lokacin salla yayi wanketa zanyi ba ruwana" Me kwalliyar tai murmushi tace 'to ta salla" Haka kuwa akayi seda Amira tayi Salla sannan aka fara kwalliyar, harta samu Guri ta saka cajin wayarta. Se magariba aka gama kwalliyar, sedai Amira ta haɗu tayi kyau sosai, me kwalliyar taita ɗaukarta hotuna, har sukayi musayar lambar waya. Sojan nan na waje ba inda yaje yana jiran Amira, dan ba ƙaramin warning Imran yai masa a kanta ba. Dukda haka seda ta saka ya tsaya, ta cire kuɗi a POS, yana yi yana kaffa kaffa karta tsere. Ihsan ma tana can kai ya ɗau caji, tana gurin kwalliya, tana son ayi a gama kan Imran yazo ɗaukarta, dan baya son jira. Amira kuwa tuni ta isa gurin dinner ɗin, seda ta tsaya a bakin ƙofa ta ƙarewa ko ina kallo sannan ta shiga, tana ta waige waige, can ta hango Anty Fa'iza da su Amina, da gudu ta ƙarasa inda suke ta rungume Fa'iza tana 'oyoyo" Fa'iza tace "kai Amira wannan kwalliyar fa?" 'hmm kedai bari kawai" tai maganar tana janyo Khairat jikinta, tace "Sadiyayye ya hanya" Sadiya ta ɗan kwaɓe fuska tace "Alhamdilillah, ashe ke tuntuni kina nan?" "Wallahi kuwa, har gurin su Sultan yaje ya ɗaukeni na sha tijara, kai mitumin nan bashi da imani, seda na kwana biyu a ɗakinsa, a rufe kamar wata Akuya sedai ya kawomin Abinci ya kulleni yai tafiyarsa, ai naga tasku" Amina da Sadiya suka haɗa ido, suka ɗan jinjina kai a tare, Fa'iza tace "Ai gidana ya fara zuwa nemanki, tun daga Kaduna yake tracking ɗinki, yana zuwa gidana kuma ki bar gidan shine ya biki can gurin Sultan" "Aini nan Alla Alla nake a gama bikin nan in koma gida na gaji da zaman garin nan sam babu daɗi" Suna cikin hirar ne sega Minal da tawagar ƙawayenta sun shigo, ana ta sanar da cewa ango ya kusa isowa shi da Amaryarsa. Minal suka zauna akan kujerun bayan su Amira. Can Amira tace 'nifa na ƙagu inga wace me tsautsayin ce zata auri wannan jarababen mutumin mara tausayi" Ɗagowa Minal tayi ta kalli Amira, amma Amira ta cigaba da maganar ta. "Dan wallahi duk wadda ta kwashi Wannan, ta shiga uku, banjin ko ɗan rarrashin nan ya iya, banda tsawa da hantara be iya komai ba" Fa'iza tace "kai Amira ki bari mana, ɗan uwanki ne, kuma kina cikin 'uan uwansa be kamata ki faɗi haka ba" "Na faɗa aje a gaya masa, dan baki san da yadda ya ɗakkoni daga Kano ba, yadda kika san dabba haka yaimin, yana jana ina kuka ina masa magiya, amma ko a jikinsa sema zagina da yake" Minal da ta fara ƙulewa da maganganun Amira, wanda dama Amiran tana sane takeyi ta ja tsaki tace "Ai dabbar ce ke, dole ai treating ɗinki kamar su" Maimakon Amira ta nuna taji haushi, kota rama seta ɗakko wayarta tace "hey guys let's snap pics" Nan ta shiga yin hotunanta hankali kwance, can tace "Nifa jikina tsuma yake, zanje a sakarmin sauti in cashe" "Dan girman Allah kiyi haƙuri, ki rifa mana Asiri mu koma gida lafiya" Anty Fa'iza tai maganar tana riƙe skirt ɗin Amira. Amira tai murmushi tace "cikani tunda ba ɓarauniya kika kama ba" Aka sanar da isowar Amgo da Amarya, wanda sojojine zasu shigo dasu da bridesmaids. Suna nan zaune aka saki wani kiɗan parrate, sega sojojin nan sun shigo cikin shigarsu ta ɗamara, suna taku daidai da kiɗan dake tashi, abun gwanin burgewa. Haka suka rakasu har kan high table, Ihsan ta sunkunyar da kanta a cikin mayafi, shiyasa Amira bata ganta sosai ba. Seda aka ɗan jima sannan Imran ya ɗagewa Ihsan mayafin kanta, ta sha make up gata fara sol, tayi kyau matuƙa. "Taɓɗijan dama Wannan ce matar daze aura ɗin, ai na taɓa ganin wannan a Abuja, duk iyayin nasa ya ƙare a wannan skelaton ɗin, aba kamar bata cin Abinci, ga wani make up an mata kamar tsohuwa, gaskiya me kwalliyar nan ta cuceta" Minal ta kuma waigowa tana kallon Amira, se cin zarafin Imran take da Ihsan hankalinta kwance, kuma ga wasu daga cikin 'yan uwan Ihsan ɗin a gurin a zaune. "Da kike kushe Ihsan, kin san ko banza ta fiki komai, ita kamilalliya ce ba irinki ba watsatsiya, wadda bata san darajar kamta ba" Maimakon Amira taji haushi se cewa tayi "matan ma dai suna suka tara, yo wannan idan tai kwalliya ta fito gaban miji maimakon ta burgeshi ai tausayi zata bashi, ya zata ko bata da lafiya, ai mace tai juyi aga tana da abun kallo shine take mace, amma wannan se kace tana cin ƙanzo, gaskiya wannan Imran ɗin bashi da wayo be iya zaɓen mace ba, gata wata busu busu da ita kamar zabiya" Amina tace "haba Amira, dan Allah kidena mana, waike duk inda kika je sekin nemi magana, ina ruwanki ne" Anty Fa'iza tace "Ai shine, dan Allah Amira ki bari, Minal kiyi haƙuri please" Minal tace "ita zaki gayawa ta bari, wallahi idan bata dena zagin Anty Ihsan ba, nima bazan bar gaya mata magana ba, ina ruwanta damu, ita ya gani yace yana so, iya har tana da bakin magana, kota kushe wani, ita da take da abun faɗa, karuwar banza ballagaza" Amira bata rama ba, sema bin waƙar dake tashi Yanzu take, sojojin nan sukaje suka canzo kaya, suka cika kan stage suna rawa, se ihu suke suna cashewa, suka janyo Imran daga kan kujera, suna ɗaga shi sama. "Kai gaskiya ma dai wasu sojojin mahaukata ne, kalli abinda sukeyi kamar basu

Chapter 10 of 31