Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ita, amma ni nafi ƙarfin shekaru biyar rabona da ita" "Shikenan my Own, i trust you, na yadda da dukkanin maganganun ka, amma yaushe zaka dawo?". "Da wuri zanje in dawo, yaushe zanje in kwana a garin mutane, da wuri zanje in dawo Insha Allah" "Allah ya kaika lafiya, ya dawomin da kai lafiya my own, Amma zakazo muyi sallama ko?" "Ai da sassafe zan tafi Ihsan, bana zo muku gida da sassafe ba" "Ni dai kazo dan Allah My" "Ƙarfe bakwai fa zanzo" "Eh dan Allah kazo ni dai" "Shikenan, Insha Allah zanzo kan in tafi ɗin" "Allah ya kawomin kai lafiya, ya tsaremin kai, ya yafe maka kura kuranka, Allah ya sada ka da dukkanin Alkhairin duniya dana ƙiyama" "Ameen ya Allah abar ƙaunata, shiyasa nake matuƙar ƙaunarki nake alfahari dake, Allah yayi miki albarka matar Imran" "Ameen my love, i love You" "Love You too babyna" ya ƙarasa maganar tare da yi mata kiss ta waya. Ihsan ta sauke wayar a hankali ta ɗorata a kan ƙirjinta, ta lumshe idonta tana jin yadda ƙaunar Imran ke ratsa lungu da saƙo na zuciyarta, ta lumshe idanunta tare da tunani kala kala, ji take tamkar ta janyo lokacin auren nan, saura befi watanni biyu ba ya rage, amma tana jin tamkar saura shekaru biyu ne, dan gani take kamar ba zasu zo ba. "Ihsan! Ihsan! Ta ji muryar Mummynta, "Na'am  Mummy gani nan" "Na kiraki ya kai sau biyar, amma baki amsa ba" Ihsan ta tashi zaune tace "yi haƙuri Mummy, waya nake ne banji ba" "Sarkin waya, ke ko gajiya bakyayi, Allah dai ya kaimu ayi bikin nan kowama ya huta" Ihsan tai murmushi ba tare da tace komai ba. Mummy ta zauna a kusa da Ihsan tace "Ina fatan kin sha maganin nan?" Ɗan tura baki Ihsan tayi tace "mhmm ni gaski Mummy.... "Ke gaskiya me?" "Maganin ne ba daɗi, kuma fa ɓatan ciki yake" Mummy tace "to dama ana shan magani ne dan daɗi? Haka zakije gidan Auren ba gyara?" Tura baki Ihsan tayi tace  "Mummy ai ina sha" "Inma ba kya sha kyaji dashi, Hajiya Ramatu tana Dubai, ta turomin samfiran lesussuka, tace ki zaɓi wanda za'a kawo miki na dinner" Ihsan tace "Mummy ni duk wanda aka kawo shikenan" "A'a zan turomiki ta what's app ki zaɓa, bazan zaɓa miki ba kice beyi ba' "Shikenan Mummy, in kin turomin Zan zaɓa din" ******************** Amina na tsaka da baccinta, tan enjoying baccin sosai kasancewar dare yayi sosai, tana cikin abun rufarta, tana ta kwasar bacci. Ji tayi kamar an jefata a kogi, sakamakon jin ta tsundum a cikin ruwa me tsananin sanyi, cikin razani da tashin hankali tai firgigit ta tashi tana kurma ihu. Amira ta gani a tsaye a kanta da bokiti. "Me nayi miki zaki jiƙani da ruwa haka? Wane irin wulaƙancine haka?" Amira tace 'na miki hakane dan in tasheki in ja miki kunne, ɗazu da magariba ina salla ina jin kina wai ina gama yawon iskancina, sannan inzo ina salla, naso na baki amsa a ɗazun, sedai nace bari in bari se cikin dare daga ni seke in baki amsa, shiyasa na tasheki, idan ubanki Baba Lawan, shike karɓar salla idan nayi, dan Allah ki tashi Yanzu ki wanke ƙafa, kije ki ƙwanƙwasa masa ƙofa kice masa, daga yau idan na kuma salla karya karɓa, shine zaki tabbatar min da kin isa. Idan kuma bashi yake karɓa ba, daga yau kika kuma shiga sabgata, duk abunda na miki ke kika siya, ki fita hanyata tun wuri, idan ba haka ba wallahi duk wanda ya taɓani sena ɓata masa rai" "Amma Amira yakamata ki zubamin wannan uban ruwan a daren nan ina bacci?" "Ni ba ruwana daya kamata kobe kamata ba, ke kin duba yakamatan ne kika gayamin abunda kika gayamin ɗazu, daga yanzu seki dinga yiwa bakinki linzami akan Amira" Amina ta kalli yadda ruwa har gudu yake a tsakar ɗakin, ta jiƙe katifar nan sharkaf da ruwa, Sadiya ce tayi juyi ta jita camɓal a ruwa, a razane ta miƙe zaune ta zaci fitsarin kwance tayi, taga fitila a kunne, ga Amina a zaune Amira tsaye a kansu, taga ruwa yana gudu a tsakar ɗakin. "Lafiya meye haka?" Amina cikin tsananin takaici tace  "Jiƙamu tayi da ruwa" Sadiya tace "akan me?" Amina ta rasa amsar da zata sake bawa Sadiya. Sadiya tace "yanzu meye ribar abunda kikayi mana? Kawai ki tayar mana da hankali ki hanamu bacci" "Idan har bazaku dena shiga sabgata ba, nima bazan fasa ɗaga muku hankali ba" Ta juya ta fita da bokitin, haka suka tashi suka fita da katifar waje, tana ɗigar da ruwa. Amira ta samu guri tai zamanta akan bokiti, a tsakar gida kamar aljana, tana jiran su gama gyara ɗakin taje ta kwanta. Baƙin ciki ya ishi Sadiya, suka gama gyara ɗakin, suka tsane ruwan duk da ya jiƙa ɗakin, Sadiya ta ciko bokiti da ruwa itama ta wankewa Amira jikinta da ruwa nan a tsohon daren nan. Amira ta gigice saboda yadda taji zubar ruwan sanyin ba zato ba tsammani, ta miƙe a gigice, tana ɗigar da ruwa ta kalli Sadiya ta kalli jikinta, ta jiya ta kandamo ruwa ta dinga antaywa a cikin ɗakinsu. Nan da nan rigima ta kacame a wannan uban daren, faɗa da bokitai, da ɓarnar ruwa, Zailani ne ya fara shigowa cikin gidan, ya tarar dasu suna ta faɗa, suna neman suyiwa Amira taron dangi, amma se buga musu bokiti take sun kasa taɓata, ga shi sunyi kaca kaca da ruwa a gidan. Tuni su Yadikko ma suka fito tsakar gida, suka tarar da wannan aika aika a cikin wannan uban daren. Yadikko tace "masifar yarinyar nan ta isheni, nagaji wallahi wace irin yarinyace ke haka mara hankali?" Kowa Amira yake bawa laifi, banza tayi musu ta shiga ta canza kaya, ta wuce ɗakin Yadikko. "Ke dan ubanki fitomin daga ɗaki, ba zaki je nima ki ɗagamin hankali ba, fito ƙaramar sheɗaniya, masifarki bata tashi se cikin dare kowa na bacci" Baba yace "Yadikko dan Allah ki ƙyaleta, wannan yarinyar se an dangana da malaman ruƙiya, dan wannan aikin tabbas akwai hannun sheɗanu a ciki" A taƙaice dai yauma ba wanda yayi baccin kirki a gidan, saboda halin Amira na rashin kirki. Gari na wayewa ta canza kayanta ta fice, ta bar gidan gaba ɗaya. Da safe Imran ya tashi ya shirya tsaf, cikin ƙana nan kaya, ya tafi falon Ammi, ya durƙusa ya gaisheta ta amsa masa sama sama Sannan tace "har zaka tafin ne?" "Eh Ammi, zanje ina son in dawo da wuri ne" 'shikenan, kome ze faru ban yadda a haɗa kai da kai a kawomin wannan yarinyar gidan nan ace in riƙe ba, taje can dangin ubanta su riƙeta, aisu Yakamata su riƙeta ba wani ba, dan haka ka kula" "To Ammi insha Allah, ki cewa Abba na tafi idan ya tashi" "Shikenan, Allah ya kiyaye hanya" "Ameen, Ammi Nagode" Ya tashi ya fita, a ƙofar gidan su Ihsan yai parking, ya kirata a waya da sauri ta ɗaga wayar tace "my own ka tashi?" "Gani a ƙofar gidanku, leƙo muyi sallama zan wuce kano" Ihsan tace "da wuri haka? To gani nan zuwa" Yana nan tsaye sega Ihsan ta fito, ta sanya zumbulelen hijjabi tun daga sama har ƙasa, ta ƙaraso inda yake tsaye tace "good morning" "Morning Beb, how are you?" "Fine Alhamdilillah, kayi kyau sosai" Yai murmushi yace "Nagode sosai, kim damu inzo muyi sallama kafin in tafi, shine na biyo gani nazo, ina fatan shikenan" 'hmm kusan shikenan, But am so much jealous, bana son kaje wata ta kallarmin kai, wannan kyan da kayi kamar ka zauna inta kallonka nikaɗai" Yai murmushi yace "Ihsan kishinki yayi yawa a kaina" "Kenan yin hakan laifine?" "Ni na isa ince laifine, nasan ƙaunace tasa kike kishina, amma ki sha kuruminki, ni nakine har abada Ihsan, kuma na gayamiki yarinya ce ƙarama ba babba ba, ki kwantar da hankalinki kinji my wife" "Shikenan na kwantar, tunda naji tabbaci daga bakinka Mijina, Allah ya tsaremin kai ya kiyaye hanya, ga wannan ka dinga taɓawa a hanya" Ta ƙarasa maganar tana miƙo masa leda, yasa hannu ya karɓa ya kalleta yace "Nagode sosai My Wife, take a very good care of yourself kinji Babyna" "Insha Allah, sannan da naso muyi Maganar kayan da zamu saka na dinner, Amma kaje kawai mayi magana ta chat" "Shikenan, bari inje sena dawo" "Allah ya tsaremin kai habibina" "Ameen" Ya shiga motar ya kunna, tana ɗaga masa hannu, yaja motar ya tafi, seda ya bar harabar gurin Sannan ta juya ta koma gida. Amira kam da sassafiyar nan, restaurant ta tafi taje taci Abincin ta ta ƙoshi, wajen ƙarfe goma na Safiya, ta tafi office ɗin su Sultan. Suna ganinta suka fara shewa, suna mata barka da zuwa, cikin sakin fuska ta amsa musu, ta ƙarasa ciki Sultan ya saki fuskarsa yace "Sannu da zuwa gimbiya" "Yawwa Sannu, nazo ka bani wayata da kace an bani" Sultan yace "Gimbiya ikon Allah, ke tunda muka rabu a gurin bikin nan baki sake zuwa office ba se Yau" "Kai dai bari kawai, ɗakkon wayar in gani" Ya tashi yasa mukulli ya buɗe wata drower, ya ɗakko wayar a kwali ya miƙa mata. Tasa hannu ta karɓa, ta buɗeta tace "Wow, yanzu Sultan wannan tawace?" "Ƙwarai kuwa taki ce, wanda ya baki itane kuma ya gayyacemu bikinsa, kin san kuwa idan mukaje bikin nan abunda zamu samo da yawa" Ɗan shiru tayi tace "gaskiya zuwana Abujan nan babu tabbas, kamar yadda na gaya maka, sedai idan na canza shawara zakaji" "Dan Allah Amira kiyi wani abu da gaggawa, wallahi zamu samo kuɗi sosai, kuma tamkar sake tallata kanmu ne, tunda manyan mutane ne zasu je gurin bikin" "Kai ƙyaleni, se yadda ta yuwu kawai, Yanzu haka ina da gurin zuwa ne" Sultan yace "haba dai, bayan munyi dake yau akwai training, satin nan fa muna da biki" "Ka basu training ɗin bakomai fa, akwai inda nake gaggawar zuwane, kasan ni dai baka da Matsala dani" "Amma Amira" Ai bata jira ba taja jakarta tai waje, dan karma ya lallaɓata yace seta tsaya. Gurin Saloon taje, aka gyara mata kai, akayi mata kitson attachment ƙanana,  se azahar Sannan ta bar gurin, taje ta kuma siyan Abinci, ta cika cikinta sannan ta wuce gida. Imran kuwa tuni ya sauka a garin kanon dabo, seda ya sake kiran Abba a waya yayi masa kwatancen gidansu Amira, sun masa kyakkyawar karɓa, sedai ya tarar Amira bata nan, nan suka saka Imran a gaba, suka dinga gaya masa abunda akayi da wanda ba'ayi ba akan Amira, sedai Sadiya se wasu abubuwa take dan ta ɗau hankalin Imran, amma yaƙi kallonta. Baba yace "gantali iri iri ba wanda yarinyar nan bata yi, ga tara maza banda raye raye, da tashin hankali da take janyo mana a unguwar nan, banda idan iskancinta ya tashi ta hana mutanen gidan nan bacci da takeyi" Imran yai shiru, gaba ɗaya abun ya ɗaure masa kai, yace "yanzu ina Amiran take?" Yadikko tace  "ai tunda tai tijararta ta cikin dare, tun duku duku tasa ƙafa ta bar gidan nan, ba wanda tayi wa sallama" Imran yace "Amma ya kai aka bari har abun nata yai nisa haka ba'a sanarwa Abba ba? Kuma naga ga manyan maza samari a gidan nan, suma ta gagresu kenan?" Baba yace "mun zaci abun nata zamu iya shawo kansa da wuri, amma abu ya gagara, duka, zagi kurari ko faɗa baya tasiri a kanta, ko jinjirar jaka na ta ganta akan taurin kai da rashin ji" Sadiya tace "wallahi Yaya baka san halinta ba, jiya bakaga yadda ta jiƙamu da ruwa ba cikin dare, ta hanamu Bacci wulaƙanci kala kala ba wanda bata mana, zagi dagamu har iyayenmu bamu tsira ba" Imran yai shiru yace "ku bani lambar wayarta" Amina tace "ai babu wanda yake da lambar wayarta a gidan nan, si bamu kai ta bamu lambarta ba" Abun ya ɗaurewa Imran kai sosai, abun nasu kuma harda sakaci, Amma ya za'ati ace yarinya ɗaya tal ta gagaresu?ya sha mamakin abunda aka gaya masa akan Amiran. Yana nan zaune Baffa Salahu ma ya shigo, shima yana tarar Da Imran ya zauna yana sake kora masa abubuwan da Amiran takeyi. Kamar daga sama sukaji Sallamar Amira, Amina dake tsakar gida ta amsa tana dariyar mugunta, Amira ko a jikinta, tana ta tauna cingam. Yadikko tace "kaji ta can ta dawo, tun farar Safiya da ta fita se yanzu Allah yayi mata dawowa" Imran yace akira masa ita, Sadiya ta tashi jiki na ɓari ta fito tsakar gida tace "Ke Amira kizo ana kiranki" Amira tace "wace ke ɗin taki? Karki sake ki kuma kirana da ke, kin san bana son raini" "To ai cewa akayi in kiraki" "Kuma wanda yace ki karani yace kice min ke? Waye yake kiran nawa?" "Kije ɗakin Yadikko ki gani" Ta kalli ƙofar ɗakin taga takalma, ta kalli Sadiya tace "wannan uban takalman fa? Me aka ƙulla in shiga a cinyeni, wai tukuna ma wannan ƙaton takalmin me kyan nan na waye? Dan nasan gidan nan babu me arzikin wannan takalmin" Sadiya tace "Yaya Imran ne fa yazo" "Waye kuma Yaya Imran? Ke dalla ke kika sanshi, bazani ba" Ta shige ɗakinsu abunta, Imran yana jinsu duk yadda suka yi da Sadiya, ya fito daga ɗakin Yadikko ya kalli Sadiya yace "tana ina?" Sadiya ta nuna masa ɗakinsu, yasa kai ya shiga, yana shiga ya tarar da Amira a tsaye sanye da doguwar rigar material, wadda ta kama jikinta sosai, kamar idan tayi kyakkyawan numfashi rigar zata buɗe, ga attachment ta saki har ɗuwawunta, yayi matuƙar mamakin ganin yadda Amiran ta girma haka, tai tsawo tayi fresh kamar ba ita ba, fuskarta ba kwalliya amma tsaf da ita se tauna cingam take. Ɗagowa tayi tai tozali da Imran, take gabanta ya faɗi, dan ita ta manta dashi gaba daya a rayuwarta, tsayawa yayi suna kallon kallo da shi. "Zauna magana zamuyi" Imaran yai maganar yana kallonta. Ta samu Guri ta zauna ta harare harare, ya kalleta yace "daga ina kike?" Ta sunkunyar da kanta tace "daga sana'a" "Wace irin sana'a?" Amira tace "ta neman kuɗi" "Ai sunan sana'ar nake son ji" "Sana'a nake da jikina, ina neman kuɗi" ta bashi amsa. Mamakine ya cika Imran, ba kunya ba tsoro ta bashi wannan amsar. "Ke bakiji kunyar abunda kika faɗa ba?" Zumɓura baki tayi tace "ai ba sata nayi ba, da zanji Kunyar faɗa" "Meye dalilinki na fita a haka? Da wannan shigar" "Nifa gaskiya ka dameni da tambayoyi, na gaya maka a saye na rufa, amma se wani sake tambayata kake, to karuwanci nake kamar yadda kake sonji, ko aka gaya maka kafin in dawo" Wani ranƙwashi da Imran ya sakar mata a tsakiyar kanta ne yasa ta kurma ihu a gigice. Imran yace "Ke bakiji kunya ba kike cewa karuwanci kike? Banza mara kamun kai, harkije waje ki dinga kwana saboda baki san darajar kanki ba kamar Saniya?" "Ya za'ayi in san darajar kaina, bayan tun tasowata ba'a nunamin ni me daraja bace" tai maganar tana kuka, saboda seda fitsari ya cika mata mararata saboda azabar zafin ranƙwashin da yayi Mata. "Wace irin magana kikeyi haka? Baki san Akuyace take bada jikinta ga kowane banza ba, ke Akuyace ko karya da kike tallar jikinki, dan maza du biyoki su biya buƙatar su su baki kuɗi, kamar motar haya" Amira taji zafin maganganun sa amma tace  "Ai nima ba kowa nake bawa jikin nawa ba, dan haka niba Akuya bace, ka iya bakinka karka sake kirana da Akuya, karuwancina me lasisi nakeyi, kuma baka da bakin magana akan abunda nakeyi" Tana rufe baki zuciya ta tinziro Imran Yasa ƙafa yai Ball da Amira, abunka da soja duk girmanta, seda ta gara har kanta ya bugu da ƙafar keke, Amira ta sake fashewa da kuka tana "karka kuma dukana, bani da me kula dani dan me bazan fita inda zan samu ba, idan ka kuma dukana Allah ze sakamin, ka ɗau hakkina karka kuma dukana" Imran ya cigaba da mammake Amira, tana kuka tana kwakwazo, amma bakinta yaƙi mutuwa, yasa hannu ya riƙe kunnenta, azaba tasa jikinta ya hau rawa, ta haɗa gumi ga hawaye, kamar kunnenta ze cire. Hannunsa riƙe da kunnenta yace "meyasa kike abunda kike aikatawa?" "Kuɗi nake so" ta bashi amsa tana kuka. "Dan kina son kuɗi seki dinga karuwanci, bazaki sana'a ba?" "Ni bazan iya ba kuɗin kawai nakeso, fame kula dani kuma bame bani" "Dole ne ki riƙe kuɗin? Meyasa bazaki kira Abba ki gaya masa ya dinga tura miki kuɗin ba?" "Ni bana roƙo" "Amma kin iya yawon banza ko, yawon befi roƙon abun kunya ba?" Dukda a cikin azabar da take, amma be hanata cewa "wallahi yawon da nake ya fiye min, in roƙi wani abu ko a gurin waye, ka sakarmin kunne na malam karka illatamin kunne" Imran ya sakar mata kunne ya miƙe tsaye, ya zare belt ɗin wandonsa, beyi niyyar dukanta ba, amma yaga abun nata bana ƙare bane ya rufe ƙofa, da niyyar yai mata dukan tsiya, Amma Amira ta fashe da kuka ta shiga magiya. "Dan girman Allah kayi haƙuri, karka dakeni bazan ƙara ba, wallahi yanzu ma inaga ka karyani dukana da kayi da wannan ƙafar taka, dan Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama kayi haƙuri, wallahi na dena bazan kuma ba" Da ƙyar muryarta take fita, saboda kuka, fuskarta tai jawur. Imran yace "Ƙarya kikeyi bazaki dena ba, naga alamar kina da taurin kai" "Wallahi bani da taurin kai, kaina me laushi ne,bazan sake ba ninace maka bazan kuma ba, Allah na dena" "Rufemin baki, ko in saki tsallen kwaɗo a tsakar gida yanzun nan" Amira tai gum da bakinta, se hawaye kawai dake cigaba da zuba. "Idan aka kuma kiran Abba, akace gashi kinyi wani abu, in miki me?" "Wallahi kazo duk abunda kamin nina janyowa kaina, bazan kuma ba daga yau insha Allah" Ya saka hannu a aljihunsa, ya ɗakko kuɗi ya watsa mata, yace "in dai kuɗine gasu nan, idan sun ƙare kiyi waya a baki wasu, idan na kuma samun labarin kinyi wani abu makamancin wannan, wallahi nazo zakiga abunda zan miki, Enugu zan kaiki aikin soja, in kaiki barrack su azabtar dake tunda baki da kai, wawiya shashasha kawai" Amira ta sunkunyar da kanta, jikinta nata zugi, yayi ya gama ya buɗe ƙofar ya fita. Yana fita Amira tabi bayansa da harara, jikinta se zugi yake mata, saboda yadda ya dinga balla da ita, ga ranƙwashi da murɗe kunne. Imran yaje sukayi magana da su Baffa, ya dawo ƙofar ɗakin ya tarar da ita tana nan zaune tana kuka, yace "am going for now, lokaci lokaci zan dinga zuwa, kuma na bada lambar wayata, da kinyi wani abu amin waya a gayamin, wallahi kika bari ska kirani akace kinyi ba dai dai ba, zakiga yadda zanyi dake" Amira bata cemasa komai ba, harya gama sababinsa ya juya ya yai sallama da mutan gidan yace ko waje kar a sake barin ta fita, idan aka hanata abu ko tayi gaddama a kira shi, suka tabattar masa za'ayi yadda yace , daga nan ya  tafi. Amira tai watsi da kuɗin daya bata zuciyarta na ƙuna, ga baƙaƙen maganganu da yayi mata, ga kuma wahala ta sha, da ƙyar ta ja jikinta ta ɗakko wayarta, ta kira Sultan. Ringing biyu ya ɗaga yace Allah ya temaki Gimbiya. "Ka gayawa mutumin nan, ina nan zuwa garin Abuja, zanje gurin bikin nan!!! In ba'a comment zan dena posting gaskiya Share Please Follow me on watpad@ Ayshercool7724 Or what's app 07063065680 . [1/6, 5:20 PM] Ayshercool: . 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 WUTA A MASAƘA PERFECT WRITERS ASSOCIATION (WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS) https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P. W. A *Story and written by* AISHA ADAM (AYSHERCOOL) The experience writer of *ABDUL JALAL* * WATA KISSAR.... (SAI MATA) *BAƘIN TABO (Labarin gasa) *AƘIDATA (Paid Book) * WUTA A MASAƘA SADAUKARWA GA ƘUNGIYAR PERFECT WRITERS ASSOCIATION, DOMIN TAYA MURNAR CIKA SHEKARU BIYU DA KAFUWA https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in ❌❌❌ Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.                                  5_6 Sultan da ƙarfi yace "wow, that's my Queen, Gaskiya kin gama birgeni Amira, zan gaya masa nasan zeyi farinciki da jin haka sosai" Amira ta share hawaye tace "Ka gaya masa kawai, kaga idan ma be biya kuɗin jirgin ba ni zan biya, zan tafi ku sameni a can" "A'a me yayi zafi? Tare ma zamu tafi ai, amma naji muryarki wani iri kamar kina kuka, lafiya kuwa?" Ɗan gajeren tsaki tayi tace "manta kawai, ni dai na gaya maka ne kawai, tafiyar nan dani za'ayi ta insha Allah" Tana gama maganar ta katse kiran, ta shafa kunnenta dake ta zugi, da jikinta da keta mata raɗaɗi tai ƙwafa tace "wallahi tunda akamin haka an taɓo masifa, sena ɓatawa kowa rai kuma sema tabattarwa wannan sakaran be isa ba, nize wulaƙanta ga duka ga miyagun maganganu, dani kuke zancen" Tai maganar tana goge hawayen dake bin fuskarta, Amina ta shigo ɗakin ta kalli yadda Amira tai zaman dirshen tana kuka, ga kuɗin da aka bata tayi watsi dasu, fuskarta tayi jawur. Amina ta kwashe da dariya tace "yau Allah ya dubemu ya karɓi Allah ya isarmu, Allah ya kawo mana maganinki, ni dama ya ɓallaki kowa ya huta" Sadiya ta biyo bayan Amina tana faɗin "kedai bari, ai gara da aka mana maganin banza, ashe iskancinta na ƙaryane sega shi tana ihu tana ayi haƙuri, ballagaza kawai" Amira tai shiru ta cigaba da kukanta, gaba ɗaya taji ta tsani komai ma, ya zubar mata da mutunci a gaban mutane, bebi ba'asin komai ba yaci zalinta yai gaba, take taji haushi da tsanar Imran sun mamayeta gaba ɗaya. Ranar wuni sukayi bakinsu shiru, saboda uwar hayaniyar ta sha wuya, zuwa yamma zazzaɓi ya rufeta saboda kukan da tayi, da kuma ciwon da jikinta yakeyi ga ciwon kai, haka ta shiga bargo tana rawar sanyi, sedai dulk da haka saƙawa take tana ware abunda zatayi ta huce abunda akayi mata, amma Zuwa Abuja kam sedai idan ta mutu, amma muddin tana raye se taje. Imran kuwa har ya shiga garin Kaduna, yana tunanin Amira da abunda take aikatawa, abun ya ɗaure masa kai gaba ɗaya yarinyar nan ta fitsare, wai harta kalli tsabar idonsa ta gaya masa wai karuwanci takeyi da jikinta dan ta samu kuɗi. Ya daki sitiyarin motarsa da ƙarfi yace "wace irin rayuwa ce wannan? Yarinyar da Yakamata ace tana makaranta, amma itace ke yawon ta zubar ba kunya ba tsoro ƙaramar yarinya kamar wannan ta ɓata image ɗinta, ga fitsara da rashin ta ido, take yaji wani mugun haushinta da ƙyamarta sun kamashi. A haka ya ƙarasa gida da tunani kala kala, seda yai sallar magariba sannan ya shiga gida. A falo ya tarar da Ammi, ya nemi guri ya zauna, Ammi tace "Imran ya hanya? Na kiraka bata shiga fa, har hankalina ya fara tashi" "Alhamdilillah, inaga rashin network ne, tun ɗazu na dawo na tsaya nayi salla ne kum.... Be ƙarasa ba wayarsa ta fara ringing, ya ɗakko wayar yaga sunan Abbana a kai, ya saita nutsuwarsa sannan ya ɗaga wayar "Salamu Alaikum Abba Barka da yamma" Abba yace 'yawwa Imran, yaya ka dawone?" "Eh Abba na dawo, Yanzu na shigo gidan ma" "To Alhamdilillah, yaya ka barosu ya ake ciki ne?" Imran yace "to Abba, maganar ce dai Babu daɗi, dan yarinyar nan ta riga ta kangare kusanma zan iya cewa tafi ƙarfinsu, kuma da bakinta ta amsamin tana yawon banza, wai kuɗi take so babu me bata, ba kaga shigar da ta dawo da ita a jikinta ba, abun dai se Addu'a kawai" Abba yace 'innalilallahi wa inna ilaihi raji'un, garin yaya suka bari yarinyar nan ta lalace hakane? Kuma naga kamar da ba haka take ba?" "To Abba, abun nata ne dai se Addu'a kawai, amma ta zama muguwar fitsararriya, na bata kuɗi kafin in taho nace idan tana buƙatar wasu, ta kira ka a waya a tura mata, amma akwai buƙatar kaje da kanka, ko makaranta ce a nema mata, dan bani da tabbacin ma ko makarantar secondary ta gama, idan Kuma wani abun ne yakama ayi mata, se a duba a gani" Abba yai ajiyar zuciya me ɗauke da damuwarsa yace "Shikenan Imran, idan na dawo ma ƙarasa tattaunawa, amma banji daɗin labarin nan ba, amma Nagode sosai, zan san abunyi Insha Allah" "To Abba, Allah ya dawo da kai lafiya" "Ameen Son" Ya katse wayar, tuni Ammi ta yamutsa fuskarta tace "ko meye ze ɗaga hankalin sa kuma, bafa shiya lalata yarinyar nan ba, laifin dangin ubanta ne bana wani ba, ai suke da alhakin riƙeta ba shi ba, kuma wallahi ka kuskura kasa ya kawomin wannan yarinyar gidan nan se ranka ya ɓaci, baza'a lalata min tawa 'yar da na daɗe ina gina tarbiyyar ta ba" "Ammi ai bance ya kawota gidan nan ba, Amma Abba yakamata yayi wani abu akan yarinyar nan" "Kai dalla rufemin baki, Gobe in Allah ya kaimu kaje Hana boutique, nayi Magana dame gurin, ka karɓo wasu riguna, da za'a saka a lefenka" "To Ammi Nagode sosai, Allah ya ƙara Arziki" Ya miƙe jiki a sanyaye ya tafi masallaci dan gabatar da sallar isha'i. Bayan ya dawo ya tarara an

Chapter 4 of 31