Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sosai Iya Bola" ya karɓi flask ɗin ya shiga dasu, ya ajiye ya kalli Amira yace "bagidajiya baki iya gaida Mutane ba ko? Kina kallonta tana kallonki amma ki kasa gaisheta" "To ni me zance mata, ni iya turanci nayi? Ni ba wani gane me take faɗa nake ba" "Ai dama ina zaki gane, tunda ki ka ajiye makaranta kika dena zuwa, ki ka kama shirme" Amira tace "ni wallahi ban ajiye makaranta ba, dan nayi Candy kuma Anty tace min ma zan cigaba da makaranta, naga ma dai a makarantar tamu ba irin wannan turancin ake ba" Ta ƙarasa Maganar hadda murguɗa masa baki, gajeren tsaki yayi yace "Nan barrack ne ba inda kika saba haukanki ba, idan kika kuskura ki kayi shirme casaki za suyi kuma ba abunda ya shafeni, ta shi kije Kitchen ki ɗakko plate kizo kici Abinci" Tashi tai tana yatsuna fuska, ta shiga Kitchen ɗin duk yayi ƙura, ta ɗauki plates ta ɗauraye ta fito falon. Ya karɓa ya buɗe flask ɗin Abincin, teba ce da miyar shuwaka, ta sha bushshen kifi da ganda, se ƙamshi take. Imran ya ɗibi nasa ya tura mata sauran, yaje ya wanko hannunsa yazo ya zauna, ita dai se binsa take da ido kamar wata sokuwa, ya fara cin Abincin yaƙi kulata, Yunwa ta isheta dan haka ta  matsa  gabansa ta sa hannu, be kulata ba ya cigaba da cin Abincinsa. Loma ɗaya tayi da ƙyar ta haɗiye, ga tsamin garri, ga miyar ɗan banzan yaji ga ɗacin shuwaka,  ja da baya tayi tana suɗar baki saboda yaji "ni gaskiya ba zan iya cin wannan Abincin ba, ba daɗi ga yaji, ni gaskiya bana cin teba" Imran sake jan plate ɗinsa yayi, ya cigaba da aika tebarsa, Amira ta koma gefe ta zuba masa ido, ya gama ci yaje ya wanke hannunsa, ya fita ya barta. Ta gaji ga yunwa tana ji amma ta tashi ta shiga ɗakin da ya nuna nata, sauran kayan Ihsan ta gani a ɗakin, ta kwaso kayan ta ƙulle ta ajiyesu a gefe ta shiga aikin gyaran gidan nan, tun daga ɗakunan, har zuwa banɗakuna falo da Kitchen, haka ta gyara ko ina yai fes. Se da Imran yai sallar isha'i sannan ya dawo Gidan, ya sissiyo kayan Abinci da kayan amfani, yai makin ganin uban aikin da Amira ta sha, yaje bakin ƙofar ɗakin da take, yai knocking. "Yes come in" Ya ɗaga labule yace "ga kayan Abinci can na kawo, ki tashi ki dafa wani abun ki ci" Tace "to in dafa da kai ne?" "A'a zan ƙarasa wannan tebar" "Zafa ta ɓata maka ciki, ka bari in dafa Abinci da kai" "Nace miki zanci wancan" "Shikenan" ta bashi amsa. Duk wani abu da yakamata Amira tana yiwa Imran, gyaran gida yi masa girki, ruwan wankansa da duk abunda yakamata tana masa, sedai gurin kwanan kowa daban, Kwanakin su Huɗu a Lagos, amma Ihsan bata taɓa kiransa a waya ba ko da wasa, ya zuba ido yaga iya gudun ruwanta amma, ko flashing ba tayi masa ba. Ya ɗau wayarsa da kansa ya kirata amma taƙi ɗagawa, yai mata missed calls sun kai goma amma taƙi ɗaga ko guda ɗaya, haushi ya kamashi ya harzuƙa yai jifa da wayar cike da jin zafin abunda Ihsan tai masa, hakan yai daidai da fitowar Amira da kwanuka. Ta kalli Imran tace "lafiya kuwa?" Banza yai mata ya cigaba da sauke numfashi, ajiye masa Abincin tayi tace "Koma meye Allah ya baka haƙuri" ta ajiye masa Abincinsa ta bar masa falon dan kar koma meye ya huce a kanta. Hankalin Amira ya ɗan kwanta, duk da ba shiga shirginta yake ba amma ta sarara da ɓacin ran da take shiga saboda Ihsan, da yadda yake wulaƙantata saboda Ihsan. Da safe Amira ta na cikin aikace aikacenta Imran ya shiga gurin da yake motsa jiki, ta kammala breakfast ta bishi ɗakin bata taɓa shiga ba se yau, manyan ƙarafa ne a gurin da yake Gymming da su, a ranta tace "taɓɗijan bayan wahalar da ake basu gurin training, har wani Gymming yake saboda tsabar wahala" ta zuba masa ido tana kallonsa, ya ɗago ya kalleta yace ya dai. "Bakomai na gama girki" "Ok ina zuwa" ya bata amsa ya cigaba da abunda yake. "Ka dai ɗaga ƙarfen nan a hankali, kar ƙirjinka yai ciwo" ɗan murmushi yai bece mata komai ba. Wasu lokutan idan Imran ya fita tun safe se dare yake dawowa, kaɗaici yafara damun Amira, taji gaba ɗaya zaman garin ya isheta, ga maƙotanta duk ƙabilu ne taji gaba ɗaya zamab garin ya isheta, ga Imran ba ruwansa da ita. Yau be dawo da wuri ba, dan harta gaji ta kwanta bacci, can ta farka taji motsin Imran a Falo, ta taso ta fito ta sameshi a Falo, yana kallon Ball. Taje ta zauna a kusa da shi tace "Baby ashe ka dawo, bacci ne ya ɗaukeni" Yamutsa fuska yai yace "Baby kuma?" "Eh mana Baby" Hmm kawai yace, yana ƙara volume ɗin TV. "Wai meyasa yau baka dawo da wuri ba?" "Kinfa isheni, ki ƙyaleni da wannan surutan naki" Ɗan rausayar da Kai tayi tace "hmm shikenan, nasan da Ihsan ce ba zakace mata haka ba, ban san dalilin da yasa ka tsaneni haka ba, shikenan good night"ta tashi jiki a sanyaye ta tafi ɗakinta. Kawai se yaji be kyauta ba, yaji tausayinta, tana ta ƙoƙarin yin abunda ze faranta masa amma yana gwasale ta, se yaji ba daɗi. Kashe Kayan kallon yayi, ya tafi makwancinsa, ya zauna ya ɗakko System ya shiga dube dube, sedai ko mintuna goma be ba da shiga ɗakin, Amira tayi Sallama. Ya amsa mata, ta shiga ta zauna amma tai shiru ba tace Komai ba, "ya akayi ne?" "Alfarma nazo nema a gurinka" "Ina jinki" Hawaye ne ya fara bin fuskarta tace "dan Allah ka barni in koma gida, ka kaini inda zan hau ko motace, ban san  in takuraka da yawa, naga kamar biyoka garin nan na takura maka da yawa, kuma dama kace ba wani amfani zan maka ba, dan Allah kayi haƙuri zan koma in yaso se matarka ta biyo ka, kuma dan Allah kan in tafi Imran ka sakeni dan girman Allah, tunda nai Auren nan na buɗe sabon shafin ƙaddara a rayuwata, ban taɓa jin daɗin Auren nan ba, dan Allah ka sakeni" Ƙura mata ido yai yana kallon yadda take kuka, "na miki kama da namijin da ze Auri mace ya saka?" "Ni dai koma mene kawai ka sakeni dan Allah, banga amfanin Auren nan ba, na gaji! Na gaji! Am tired wallahi, duk da nasan ni ba wani zurfi nayi a ilimin addinin ba, amma nayi iyayina gurin yin biyayyar Auren nan, amma zuciya ta ta fara rayamun wani abu daban, baka ƙaunata baka tausayina hankalinka yana kan Ihsan, ka sakeni in samu wanda ze Aureni duk da laifin da nai a baya tunda na dena yanzu" Kashe System ɗin yai, yai kwanciyar sa yaja bargonsa, yaƙi kulata. Aikuwa ta ƙule, ta janye bargon daga jikinsa "Imran wallahi ba zaka maida ni mahaukaciya ba, am so much tired na gaji, dan girman Allah ka sakeni tun da ba ka ƙaunata, ni ka ƙyaleni in samu me sona in Aura" kuka take iya ƙarfinta Imran yace "A hakan zaki samu me son naki ya Aureki? Waze Auri 'yar gala?". "Eh a hakan wani ze Aureni ya zauna dani, ya soni a yadda nake" Cikin son cusa takaici Imran yace "au haba?" Fashewa ta sake yi da kuka, hadda sheshsheƙa, sosai ta bawa Imran tausayi, ya miƙe zaune ya shiga ƙoƙarin sake janyo bargonsa, amma ta riƙe bargon tana kuka. Haɗawa yai da ita da bargon a jikinsa, yace "rufemin baki ki dena min kuka, me nayi miki zaki dinga min kuka a daren nan? Saboda tsabar baƙin kishi da ke damunki zaki ce sena soki, to baza'a sake ki ɗin ba, zama kuma yanzu kika fara" Kuka ta cigaba da yi kamar wata ƙaramar Yarinya. Amira ta fuskanci kunnata kawai Imran yake. Tsaki tayi ta miƙe daga jikinsa, "ni kike wa tsaki?" "Na maka tsakin, mugu mara adalci kawai, wallahi Allah yana kallonka, kuma wallahi sena gayawa Abba duk abunda kake min, na dena rufa maka Asiri, Baka da adalci Imran ina ga baƙin cikin ka ne da na matarka ze kasheni, dannewa kawai nake ina maka biyayya dan cika umarnin Ubangiji, Amma wallahi na gaji" "Ni kike cewa mugu mara adalci?" "Na faɗa na kuma, mugu mara adalci! Mugu! Na faɗa Allah ya sakamin abunda kuke min" Miƙewa zaune yai ya fizgo ta da ƙarfin gaske yace "bari in gwada miki adalcin da kike so ɗin...... 🙄🙄🙄🚶🚶🚶) Ina Ganin sharhinku yana sani nishaɗi godiya nake 🥰🥰🥰😂 masu zagin Ihsan kuma, zan cireku a group ɗina dan a team ɗinta nake 😎😎😎 Gyara Sharhi ko shawara Ayshercool 07063065680 [2/11, 3:25 PM] Ayshercool:   🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 WUTA A MASAƘA PERFECT WRITERS ASSOCIATION (WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS) https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P. W. A *Story and written by* AISHA ADAM (AYSHERCOOL) The experience writer of *ABDUL JALAL* * WATA KISSAR.... (SAI MATA) *BAƘIN TABO (Labarin gasa) *AƘIDATA (Paid Book) * WUTA A MASAƘA https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in ❌❌❌ Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.                             43_44 Se da Amira ta saki ƙara, sakamakon yadda Imran ya janyo ta da ƙarfi sosai. Ba sani, ba sabo, ba tausayi, ko sassauci Imran ya aikata abunda zuciyarsa ke raya masa akan Amira, ya aikata abunda yake so kansa tsaye, ba tare da wani tausayi ko rangwame ba, sedai kash duk yadda ya zaci abun ba haka yake ba, saboda abunda ya tarar ya girgiza shi ya bashi mamaki matuƙa, he never thought that Amira was virgin. Seda ya dawo hankalinsa yaji wata irin nadama ta saukar masa, dan kusan abunda ya aikata ba shi da maraba da Fyaɗe, sedai kawai dan matarsa ce, ya kalli in da Amira ke kwance kukan nata ma ba ya fita, se sheshsheƙa da ajiyar zuciya kawai da take yi. Hannu bibbiyu ya sa ya dafe kansa, yai shiru yana tunani daban daban a zuciyarsa, kunya da tarin Nadama suka baibaye shi. A hankali ya kuma kallon Amira, jiki a sanyaye yace "Sannu" Bata ko motsa ba balle ta amsa, ta cigaba da kuka. Ya janyo bargo ya lulluɓe ta, ya miƙe jiki a sanyaye ya bar ɗakin. Gaba ɗaya Amira ta kasa banbance a halin da take ciki, a sume take ko a farke ta kasa ganewa. Ɗagota Imran yai daga kwanciyar da take, ya ɗaura mata towel, yana ƙoƙarin ɗaukanta amma ta bige hannunsa ta sakko daga kan gadon. "Ki tsaya in taimaka miki mana, na kai miki ruwa toilet ɗina" Wani banzan kallo tai masa tace "bana so" Ta lallaɓa jikinta, ta shiga ban ɗaki, ta nemi guri ta zauna, tana zubar da hawaye. Imran kuwa sake zama yayai yana tunani, ta yaya Amira zata zama virgin? Dama haka tana faruwa ko kuwa dai dama duk abubuwan da take ba ta aikata Zina?. Nan damuwa ta tarar masa, ya dinga tunani daban daban, yana cikin tunanin ta buɗe ƙofar banɗakin ta fito. Imran ya tashi da sauri ya tafi inda take, yana jera mata sannu, sedai a sannun nasa ko ɗaya ba ta amsa ba. Ta nufi ƙofar fita daga ɗakin. Da sauri yace "ina kuma zaki? Ki zo ki kwanta a nan, in duba first-aid box ɗina, in baki magani" "Bana so, ba zan sha ba ka riƙe abunka Imran, ai ni be kamata ka tausayamin ba, saboda Karuwace ni da aka tirsasa ka Aura dan ka taimaka Mata, Alhamdilillah yau burina ya cika, kaine ɗa namiji na  farko da na fara sani a rayuwata, kuma kaima ka sheda hakan, dan haka daga rana me kamar irin ta yau, kar ka sake kirana da Karuwa, kuma ka sanar da matarka da 'yan uwan ka ni ba Karuwa bace, abunda yake hanani maida martani idan an gayamin Karuwa, shine bani da hujjar kare kaina, Yanzu kuwa na samu wallahi duk wanda ya kuma cemin Karuwa dai dai nake da shi, zan mayarwa mutum daidai da abunda ya gayamin, ni ba Mazinaciya bace, bana aikata zina ban taɓa ba kuma ba zan fara ba, Imran kome na zama A duniya duk lalacewar da nayi a duniya da sa hannunku a ciki kune sila, kasan irin baƙar wahalar da na sha kuwa? Ka san irin raɗaɗi da zafin maraici kuwa,? Maraici na rashin uwa da uba, kuma na tashi a tsakanin maƙiya, mahaifiyarka taƙi karɓata, na tashi ina gararanba a gari wasu lokutan abunda zanci ya gagarrni, bayan tulin aikin da nake kamar jaka, ba wanda ya damu da ina jin yunwa, ƙishirwa ko bani da lafiya, ba wanda ya damu da wani kalar Abinci zanci a ina zan kwanta, saboda na rasa babban jigo abun jigina wato iyaye, ina da ɗan uwan mahaifiya a raye me tarin dukiya, amma na kasa samun gata, kiyayewar Ubangiji ita ta tsareni har na kawo wannan lokaci, amma idonku ya rufe kun gaza ganin naku laifin, kullum se jifana da muguwar kalma me muni, me ɗacin gaske Karuwa, hmmm don't try to pretend that kana jin tausayina yanzu, a baya na fi buƙatar tausaya wa, da ja a jiki amma ban samu ba, se baƙin wulaƙanci da na fuskanta a gidan ka, bakomai Allahn da ya ɗauki iyayena ya na ƙaunata kuma baze bari in taɓe ba" Tai maganar hawaye wani na bin wani, tai ficewarta da ga ɗakin, ta tafi ɗakinta ta faɗa akan katifa ta sake fashewa da kuka. Imran kuwa kasa motsi yai, Lallai an Cutar da Amira da kalma me munin gaske, amma koma da maraici wani abun ita ta janyowa kanta, dan babu yadda Za'ayi mutum yana aikata abunda takeyi ace ba Iskanci take ba, ga raye raye, ga shigar banza da gantali ga tsantsan fitsara da rashin kunya, ba wanda ze yadda ba karuwa ba ce. Haka Imran yaje yai wanka, duk jikin sa a saluɓe, ya gyara gadon ya nemi guri ya kwanta, tunani duk ya cika masa zuciya tare da matsanancin tausayin Amira. Da gari ya waye, da kansa yai gyare-gyaren gidan nan gaba ɗaya, ya dafa tea da yake ba wani iya girki yai ba yavfita ya siyo bredi. Sedai har ƙarfe goma Amira ba ta fito ba, wanda ƙa'idar ta bata wuce ƙarfe takwas duk baccin da za tai, ɗakinta ya nufa ya shiga da sallama, ya hangota kwance akan katifar dake ɗakin a cikin bargo. Ya ƙarasa ya ɗan janye bargon, ya daddaki filon da ta ke kai yace "Amira ki tashi ki karya, rana ta fara yi, idan yaso in kin karya se muje ko Asibiti ne" Ƙare masa kallo tayi tace 'meye naka a ciki, da in karya ko kar in karya? Ina ruwanka dani Karuwa ka ƙyaleni mana" "Naji amma kiyi haƙuri ki tashi, se muje ko Asibitin Barrack ne a duba ki" "Muje Asibiti kace musu me, You rape your wife because you thought she's not virgin? Haka zaka gaya musu? To ni ba haka nake ba, ko da nake karuwa na san daidai, ba zan taɓa fallasa Asirin Aurena ba" Imran yace "Amira rape kuma?" Cikin hawaye tace "akwai maraba da rape da abunda kaimin jiya ne? Babu maraba ai, kuma ka dena wani pretending kana lallaɓani, dan ka samu wani abu daga gareni, seka sakeni daga Garin nan Kano zan koma na gama Aurenka" Haɗe rai yai yace "dan kinga ina lallaɓaki shine zaki dinga gayamin Magana?" Tashi zaune tayi tace "An gaya maka ɗin, na faɗa kaji haushi ka rabu dani" "Naji, amma muje ki karya" "Ba zanci ba" Tai maganar tana Share hawaye, Ƙarshe Imran se tashi yai ya bar mata ɗakin, abun duniya ya ishi Imran, tabbas anwa Amira ba daidai ba, mussaman yadda ya dinga dizgaya da kalamai marasa daɗi. Wunin ranar haka dinga koke koke, kuna taƙi saurarar Imran. Imran yana ɗakinsa ya kira Khalid a waya. "Kai lafiya kake kirana a daren nan? Ya kake ya Lagos?" "Lafiya ƙalau Alhamdilillah, Amma fa akwai matsala ina cikin damuwa" "Sarkin matsala, meke faruwa Kuma?" "Khalid, Amira ce, naiwa Yarinyar nan ba daidai ba, Amira ba Karuwa bace, abun ya bani mamaki, how could this be possible, and worse part of it is that, ta dage wai sena saketa ta koma Kano, ni wannan be dameni ba, ina jin kunya akan abunda nai mata" Khalid yace "kaga abunda na dinga gaya naka kenan a baya, amma kai kunnen uwar shegu dani Imran, na gaya maka ka sassauta ƙiyayya akan Yarinyar nan, duk da dama can kan son ta, son zuciya ne ya rufe maka ido, kawai seka haƙura ku rabu tunda haka take so, da ka cigaba da gallaza mata" "Wane irin in saketa kuma? Kaifa ka fiye abun haushi wallahi, wane irin in saketa?" "To in baka saketa ba me zaka mata? Ace ka Auri yarinya over 4_5 month, amma baka taɓa sauke hakkinta na Aure ba, da lafiyar ka da Komai ka tare a gurin mace ɗaya, gaskiya ba kayi adalci ba, kuma wallahi na goyi bayan ka sawwaƙe mata, tunda ba ka da adalci" Tsaki Imran yai ya kashe wayarsa, dan kalaman Khalid sun fara fusata shi. Yai shiruu yana zancen zuci se ga kiran waya, yayi mamakin ganin lambar Ihsan, ya sa hannu ya ɗaga, "My" "Na'am Ihsan" ya kira sunanta. "My ka manta dani baka ta tawa ko?" Tai maganar cikin kuka. Imran yace "Ihsan me zance, ko ya zan dake? Na taho amma kika kasa kirana a waya, ni ban fushi ba na kiraki a waya, amma nai miki miss calls kusan goma, amma ki ka gaza ɗaukar ko guda ɗaya, ya ki ke son inyi?" "Wallahi ina kishinka da kewar ka Imran, na kasa samun nutsuwa ko Abinci ba na iya ci, gani nake komai ze iya faruwa, hankalina yaƙi kwanciya sam" "Ihsan dan Allah ki kwantar da hankalinki, ki dena ta da hankalinki kar ki saka wani ciwon a kama min ke dan Allah" "Imran ba zan iya ba, zuciyata kamar zata tsaga ƙirjina, dan Allah ka dawo please" "Ihsan ta yaya zan dawo? Aiki fa nake yi a nan ɗin" "Imran zuciyata ta kasa jurewa, dan Allah ka dawo gida" "Ihsan, kin san ba abune daze yuwu ba, in baro aiki na in dawo ba, kuma kin san nam kusa baza'a bani wani pass ɗin ba" "Au haka kace? Shikenan nagode Imran, ka dena sona ka dena damuwa dani, koma meye inje baka damu ba ya sameni, shikenan"  ta katse wayarta. Imran yabi wayar da kallo, be taɓa zaton Ihsan na da wannan halayen ba, na tsananin kishi haka da ƙorafi ba, a waje sam ba ta nuna masa wannan halin ba se yanzu, shikam a yanzu duk sedai kowa ma yai haƙuri dan aikin gama ya gama. Amira kuwa zuwa kwana uku ta samu sauƙi, da ƙwarin jikinta, sedai sam ba ta shiga sabgar Imran, ko girki idan tayi a Kitchen take ajiye masa nasa, ko gaisheshi ta dena yi, harkokinta kawai take, ga fitinanniyar shigar da takeyi ko yana nan ko baya nan, hakan ba ƙaramin hana Imran sukuni yake ba, sam baya jin daɗin yadda take shareshi, take nuna halin ko in kula a gareshi, gefe guda ga wata irin fitana dake damunsa akan Amira, amma yana jin nauyin tunkararta, saboda yasan iya Rashin kyautawa ya aikata mata. Imran ya dawo daga gurin aiki a matuƙar gajiye, ya zauna a falo da shi da takalminsa da jakarsa, ba wanda ya kai ɗaki ya kashingiɗa ya lumshe ido, Amira ta fito daga ɗakinta sanye da mini skirt da kuma vest, hannunta riƙe da cup taje ta zauna. Imran ya buɗe ido yana ƙarewa surar jikinta kallo, ya ɗanyi gyaran murya yace "Sannu da gida" "Yawwa sannu da zuwa" "Ko zan iya samun Abinci?" Yana Kitchen ta bashi amsa. "Dan Allah ki kawomin, na gaji sosai" Da farko shiru tayi kamar ba taji meya yace ba, se kuma ta tashi ta kawo masa, tana gama ajiyewa ta miƙe zata tafi yace "Ki dawo ki zauna mana" "A'a zanyi abu a ɗaki ne" Imran yace "ok shikenan, amma dan Allah ina neman wata alfarma ne" "Ok ina jinka" "Dan Allah ina son zaki rakani wani taro ne, in Allah ya kaimu Ranar Saturday" Kallonsa Amira tayi tace "ba inda zani, wake ado da Karuwa har ya ɗauketa ya shiga da ita taro, wannan ai aikin Ihsan ne matan ƙwarai, ta biyo jirgi ta taho ta raka ka" "Eh ai yanzu ke nake so ki rakanin tunda ba ta nan, kowa zeje da wani nasa, nikuma kinga daga ni seke a nan" "Ni da bani da amfani, me zanje in maka? Ko ka manta kace idan kazo dani ba wani amfani da zan maka, idan ka manta ni ina sane" Tana gama Maganara ta wuce ɗakinta tana cigaba da mita. Imran yai shiruu, Amira ƙanwarsa ce, gari banza ba ta isa gaya masa Wannan maganganun ba, amma da yake yasan shike da laifi ba abunda ze iya yi mata sedai ido. Ba yadda be da Amira ba akan ta rakashi, amma tace ko me zeyi ba zata ba. Haka Imran ya dinga fama da Amira, gefe ga Ihsan da ke kiransa tana sake sauke masa nata shirmen, harya ka ya dena ɗaga wayarta, saboda ɓata masa rai da take yawan yi. Ranar da Imran zeje taron, bayan ya dawo daga sallr magariba ya shirya ya fito, sedai yana fitowa yaga Amira ta sha Kwalliya cikin doguwar riga dark blue, wadda taji aikin stone Sosai, se walwali suke, ya tsaya yana kallonta, tace "muje ko?" "Zaki rakani ne?" Tace "eh" Imran yai murmushi yace "Masha Allah, muje" Suka fito tare, Imran ya rufe gida, suka shiga motarsa suka fita. Tunda Amira ta zo garin nan bata taɓa fita ba ko sau ɗaya se yau, duk da duhu ya fara yi amma hakan be hanata yin kalle kallenta ba, wani Guri suka je Imran yai parking ya fito, amma ita bata fito ba. Imran yace "munzo ai, ki fito" "Ina ne nan?" "In da zan saida ke ne?" Ya bata amsa. Ta fito tare da faɗin "ai ko ka saida ni ba daraja zan ba, Saboda kasan na gama bin kwararo" Imran bece komai ba, ya rufe motarsa yai gaba tana binsaa baya. Wani ƙawataccen ɗakin taro suka shiga, mutane na ta shiga suna fita, wasu da shigar hankali wasu da ta ban haushi, kasancewar gamayyar musulmi ne da wanda ba Musulmi ba. Imran ya kai Amira wani teburi yace "ki zauna a nan ki jirani, zanje in canza kaya" Ƙin zama tayi tace "haka kurum, wallahi ba zaka tafi ka barni b, muje tare" Haka ta bishi har inda ze canza kayan, ta jirashi ya canza ya fito, suka zo suka zauna. Suna zama ba daɗewa aka fara Rabon Abinci da drinks, Amira tace "wai me za'ayi a nan ɗin ne?" "Walima aka shiryawa wanda suka samu ƙarin matsayi, da wanda sukai ƙoƙari agurin yaƙi" Suna maganar aka kawo musu Abinci, da lemuka aka ajiye musu, shinkafa ce fried rice, ta sha kayan lambu ga danƙwaleliyar kaza akan kowanne. Amira tace "gaskiya nifa ci zanyi" "Ai dama dan kici aka baki, nima zanci ai" Amira ta kalli Abincin Imran, ta sa cokali ta ɗauke kazar kan Abincin Imran tace "Wannan kazar dani ta dace, kai ba'a so kayi ƙiba, ni kuma kaga dama can ina da ƙibata" Imran yace "haka akeyi, a baki taki a bani tawa kice se kin cinye da tawa?" "Eh ɗin, duka zan cinye na bar maka shinkafar" "Amira muna da kaji a gida fa, karki ba da mu mana Please" "Abunka da 'yar ƙauye ai sedai kayi haƙuri kawai, kuma ma aini baka saimin kazar amarci ba, amma ka saiwa Ihsan" Imran yace "hmm rigumammiya, ai seki cinye" Yaja shinkafarsa ya fara ci, wasu couples a kusa dasu, duk da basa jin hausa amma su Imran sun burge su, dan ba ƙaramin dariya suia basu b, kai kace wasu masoyane da suka daɗe suna shan soyaya. Wata soja ce tazo wucewa, ta kalli Imran tace "ya na ga kana cin Abinci ba nama, garin yaya" Imran ya nuna mata plate ɗin Amira yana murmushi, matar tayi dariya tace "kace anfi ƙarfinka ne, bari akawo maka wata" Amira tace "ya ƙoshi" Imran yace "ba se kin kawo wata ba, wannan ɗin ta isa"  matar ta wucesu tana musu dariya. "Kin sa ana kallonmu, muna faɗa akan  kaza" "Eh munyi ɗin ina ruwan wani, wai wannan matar me kama da maza itama soja ce, na ganta da wandon sojoji" "Allah yasa taji ki, zaki bayani" Kamar kasan da tana min magana, kawai hangowa nai ta nausheni, dan na ɗauke maka kaza, wai da daga nan se Asibiti emergency, dan wannan hannun nata kamar itace, kamar ba na mace ba, kuma ta na da miji?"  tai maganar tana dariya. Imran kallon Amira yake, she's very Funny and jovial. Yace "tana da miji hadda yara" "Taɓ lallai" Ta sa fork da spoon tana yanko

Chapter 24 of 31