ka riƙe Min amana, wallahi bazan iya jure sharing ɗinka da wata ba, ina matuƙar sonka da kishin ka dan Allah karka ci amanata, ban san ya zanyi ba randa na buɗi ido naga kana zaman Aure da Amira ba"
"Kwantar da hankalinki, Ni ke kaɗaice tawa, ke kaɗai zuciyar Imran ke so da ƙauna, Auren Amira Auren biyayyane da bin umarni, ke kuma Auren soyaya mukayi dake" yai maganar yana sake hugging ɗinta a jikinsa.
Da haka ya lallaɓa Ihsan, kalamansa sukayi tasiri a zuciyarta, harta haƙura ta biye masa.
(🙄🙄🙄)
Washegari Amira ta shirya, Fadila zata rakata gurin kitso, Anty tace "Yawwa Amira, Abbanki yamin waya Imran zasu dawo very soon insha Allah, ana so ki faɗi kalar kayan da kike so a samiki, koma muje dake ki nuna wanda kike so, se kuma kayan Kitchen duk Abbanki ya turomin kuɗi ki kirashi ki masa godiya, sannan kuɗin kitsonki ma nayiwa Imran magana, shine yakamata ya biya kuɗin, ya turo dubu biyar, shima ki kirashi ki masa godiya"
Tura baki Amira tayi tace "Nifa bani da lambarsa"
"Eh ni ina da ita ai, kije ku dawo zan baki"
Amira bata kuma cewa komai ba, tai gaba abunta.
Sukaje saloon, akai mata kitson attachment ɗinta kamar Yadda ta saba, tai ras da ita sannan suka dawo gida.
Taje ta tarar Anty tayi baƙuwa, an kawo mata wasu kaya, bata damu da ta san komeye ba suka gaisa da baƙuwar Amira tai wucewarta.
Bayan tafiyar matar Anty ta kira Amira ɗakinta, tace "baki nunamin kitson ba"
Amira ta cire hular kanta, kitsone ƙanana na attachment yayi matuƙar yi mata kyau.
Anty tace "masha Allah, kitso yayi kyau sosai, i wish mijinki yazo yaga kitson nan, amma Amira kin san ba kyau kitson ƙari ko? Gashi kema kina da gashi kiyi ƙoƙari ki dena"
Amira ba tace Komai ba se sunkuyar da kai da tayi, Anty ta ɗakko wasu manyan robobi se ƙamshi suke ta ajiyewa Amira a gabanta tace "ga wannan kayan sabulai ne nasa aka haɗo miki, ga na wanka nan dana mayukan shafawa, ga turarukan wanka nan dana shafawa, dan Allah Amira karki wasa, ki kula kiyi amfani dasu yadda yakamata, na kashe kuɗi sosai akan kayan nan, sonake kiyi tsaf dake kafin ki tare in gyaraki Sosai, dama gashi naga kema 'yar gayu ce, kayanki gobe in Allah ya kaimu za'a karɓosu daga gurin tela, ki dage da kayan gyaran jikin nan sosai kinji Amira"
"Insha Allah zanyi Anty, nagode Sosai Allah yasaka da Alkhairi"
Ta ɗebi kayan nan ta tafi dasu ɗakinta, yanayin robobin kawai sun isa kasan an kashe kuɗi sosai akan kayan nan ba kaɗan ba, daga sabulan mayukan zuwa kayan turaren, Banda kayan mayukan gyaran jiki da suka siyo a kasuwa.
Hatta Abincin da Amira take ci seda Anty ta daidaita mata shi, ganye yafi yawa a cikin Abincin da take ci, da kayan fruit mussaman data lura Amira ma'abociyar kayan marmari ce.
"Minal, wai kinji babanku ko? Wai next month Yarinyar nan zata tare a gidan Imran wai lallai lallai su dawo"
Minal tace "Wai dan Allah dama dagaske Abba yake akan Auren nan?"
"Gashi kuwa kina gani, ai tunda aka ɗaura Auren an gama, dole in san abunyi akan lamarin nan"
"Nifa Mummy tsorona Allah, tsororna kar taje idan baya nan ta cutar da Anty Ihsan, dan nika ɗai nasan dukan da naci a hannunta, ƙarfi ne da ita kamar gardi, tsaf zataiwa Anty Ihsan dukan tsiya, dan tafi ta girma"
"Aikuwa wallahi bazan laminci ta daki 'yar mutane ba, duk ran da ta daketa seta koka inda ta fito kuma yanzunma ina nan akan bakana, sena kashe wannan Auren tun kan Imran ya fara tunanin wani abu a kanta, duk da ya tabattar min da shi babu son yarinyar nan a tare da shi, a yanzu na yadda amma namijine ba tabbas garesu ba, suna dawowa zanyiwa tufkar hanci, zanje gidan nasa da kaina"
"Aikam dai gara ki ɗau matakibda wuri Ammi, dan idan kika bari aka cutarwa da Mummy 'yarta zata ga ba'ai mata adalci ba"
"Ai bama zan fara bari hakan ta faru ba"
Amira ta dage da gyaran jiki kamar yadda Anty ta buƙata a gurinta, nan da nan fatar Amira ta fara sheƙi, dama tana da haske sedai ba fara ce ba, irin chocolate ɗin nan ce, tai ras da ita kai baka ce wani abu na damunta ba, an karɓo mata ɗinkunan ta, ta shiga wannan ta fita wancan tai ƙalau da ita, idan akace maka Amira ce ma baka yadda ba, saboda wata nustuwa da ta ƙara yi, duk inda ta gifta se ƙamshi kawai takeyi.
Yanzu ma Amira ce ta fito, ta soka wani uban ɗaurin ɗan kwali a gaban goshinta, dayake megidan ma duk a Abuja suke aiki da Abban Imran, dan haka takan sake tai shigar da take so, da yake Anty ba tada ɗa namiji.
Anty tana falo tana yiwa wata mata Nutritional counselling, da illar yawan cin Abinci mai da yaji da mata keyi.
Anty Nafisa na matuƙar burge Amira, mussaman yadda patient ɗinta kan biyota har gida, gashi ba hantara ba tsangwama, ta iya tarairayar su da jansu a jiki, tai musu bayanin abubuwan da basu gane ba, gashi ta san kan zaman rayuwar duniya, komai nata sannu a hankali take binsa.
Amira taje ta zauna tana sauraren yadda Antyn take bayani, wani abun in Anty ta faɗa se kunya ta kamata, wani kuma tayi dariya.
Haka Anty ta gama ta sallami matar sannan ta kalli Amira tace "Uwargida sarautar Mata, irin wannan kyau haka"
Amira tai murmushi tace "Antyna kenan, nikam ina son Aikin Asibiti yana matukar burgeni sosai"
"Dagaske kina so Amira?".
"Dagaske Anty"
"Kai amma naji daɗi sosai, kin san aikin Asibiti yana da mahimmanci musamman ga 'ya mace, bari Abbanki ya dawo zamuyi magana dashi insha Allah, naji daɗin hakan, ɗazu Imran ya kira amma kina bacci, bari a kira shi yanzu"
"A'a Anty base kin kirashi ba, idan kin kira ma ban san me zance masa ba"
Haɗe rai Anty tayi tace "ƙaniyarki zaki ce masa, nifa bana son shirme Amira, ki kiyayeni fa akan Imran, idan kuma zuba masa ido zakiyi ki zama 'yar kallo in kin tare shikenan ni ba ruwana"
Anty ta ƙarasa maganar tana kiran lambar Imran, ta miƙawa Amira wayar, Amira ta karɓa tare da sake tura ɗaurinta gaban goshi ta harɗe ƙafa tana tura baki"
"Hello wake magana?" Taji muryar Ihsan ta daki dodon kunnuwanta.
Haushi ne ya kama Amira, Amma tace "Amira ke magana, mijinmu yana kusa ne? Ohh Sorry bamu gaisa ba kina lafiya, ya amarci?"
Anty ta ɗagawa Amira babban yatsanta alamar jinjina 👍.
Tsaki Ihsan tayi tace "ke ƙaramar Karuwa ki kiyayeni ki kiyayi mijina, mijinku keda wa? 'yar alfarma har kika da bakin cewa ina mijinku, mijinku keda wa? Mijin Ihsan dai kuma karki sake kiran wayarsa na gayamiki"
Amira a zaune take ga sanyin AC, amma nan da nan ta fara gumi, ta miƙe tsaye, Anty taji abunda Ihsan ta faɗa, dan haka ta shiga girgizawa Amira kai.
Ga mamakinta Seji tayi Amira tace "Allah ya huci zuciyarki ƙanwata kuma Yayata, sanin mijin waye tsakanin nida ke wannan lokacine ze banbanece mana, ki bari in tare, dama ba wani abu bane ba, ya kira ɗazu ina bacci ne, shine Anty ta kira shi zan masa godiya, naga saƙo ina godiya Allah ya ƙara Arziki"
Da sauri Ihsan tace "Saƙon menene?"
"Sirri ne tsakanin mata da miji meye naki na sekinji? Ki miƙamin wannan saƙon kawai shiya san godiyar ta meye"
Daga nan ta kashe wayar, tazo ta miƙawa Anty ran nan nata a ɓace.
"Anty tace Amira nace miki kishi na damunki kin musa min, shikenan dai na jinjinawa dauriyarki da ɓoye fushi, ki ƙara haƙuri nasan zaki fuskanci ƙalubale a gidansa, amma kiyi haƙuri ki daure, naji maganganun da ta gaya miki, ki rabu da ita ko zata gayamiki karki kulata wataran se labari kinji, amma fa ba ziga ba kin burgeni da amsar da kika bata" Anty ta ƙarasa maganar tanawa Amira murmushi.
Amira kam ɗakinta ta koma, ta garƙame ƙofa, tace "kan uba ni wannan daskararriyar Yarinyar zata cewa Karuwa 'yar alfarma, ashe za'ai ƙaramin yaƙi duk ranar da muka haɗu ido da ido tace min 'yar alfarma, nafi ƙarfin a Aureni dan amin Alfarma, zata ga Karuwa ganin idonta, da na aje karuwancin a gefe, amma naga bazamu daidaita da su ba, se naje gidan nan da karuwancina, zan nuna mata hatsarin da Karuwa ke dashi, na zata kira da 'yar alfarma da Amira kuke zancen"
Nan Amira ta cigaba da masifa ita kaɗai a ɗaki, dan ranta yayi matukar ɓaci.
Ihsan kuwa zubawa wayar Imran ido tayi, tana jujjuya maganganun Amira, Imran ya fito daga wanka ɗaure da towel yana goge ruwan wankan jikinsa yace
"sweetheart, zoki shafa min mai tunda ma fito daga wankan"
Gani yai Ihsan tana binsa da kallon tuhuma, ga wayarsa a hannunta ya kalleta yace "lafiya kuwa?"
"Meye haɗinka da Amira har take kiran wayar ka?"
Ƙarasowa yayi ya karɓi wayar yace "kamar yaya, ni bani da lambarta ƙila a wajen Anty Nafisa ta karɓa"
"Amma har take gayamin ince maka taga saƙo ta gode, Imran anya ba yaudarata kake ba?"
Shiru yai yana kallon Ihsan, shi dai yasan babu wani abu daya haɗa shi da Amira, Anty ce tace ya turo da kuɗi Amira tai gyaran kai, shima dan yana kunyar Anty ne ya tura, amma yanzu Ihsan zata ɗaga masa hankali"
Share Ihsan yayi yaje ya fara ƙoƙarin saka riga, dan be san me ze gayawa Ihsan kuma ta yadda dashi ba.
"Au banza ma zakayi min?"
'to me zance miki ne? Ban san me zan gayamiki ki yadda dani ba, tunda kin yadda da abunda ta gayamiki shikenan, seki tayi ai"
Yana gama maganar yai waje abunsa, Ihsan tabi bayansa da kallo, tana jin kamar zuciyarta ta tsaga ƙirjinta ta fito.
Tofa!!!
Domin gyara, Sharhi ko shawara
http://wa.me/+2347063065680
[1/27, 6:30 PM] Ayshercool:
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
WUTA A MASAƘA
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P. W. A
*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA)
*BAƘIN TABO (Labarin gasa)
*AƘIDATA (Paid Book)
* WUTA A MASAƘA
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in
❌❌❌
Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.
29_30
Bayan fitar Imran, Ihsan ta rasa abunda yake mata daɗi, gaba ɗaya ta rasa meke mata daɗi, shigowar Amira rayuwarsu babbar barazana ce ga farin cikinta, gaba ɗaya taji ta tsani Amira wani mugun haushinta take ji.
Ɓangaren Amira ma tunani kawai take akan irin zaman da zatayi a gidan Imran, dan ta ƙudirce a ranta ba zata juri wulaƙanci ba ko kaɗan.
Ihsan seda ta wuni cir Imran be dawo gida ba, dan se bayan tara n dare sannan ya dawo Gidan, da ya dawo ɗin ma be bi ta kanta ba, ya nemi guri yai kwanciyar sa ya bi lafiyar gado abunsa.
Mamaki ya cika Ihsan, ita da akaiwa Laifi amma shine yake fushi, yai watsi da Ita, gani tayi Imran ba shi da niyyar saurararta.
Har wayewar gari ya shirya yai ficewar sa gurin aiki, koda wasa bata taɓa kawo akwai abunda ze kawo mata tangarɗa a rayuwar auren da suka tsara yi ita da Imran ba, se gashi katsam Amira ta kutso rayuwarsu.
Ihsan gaba daya ta shiga damuwa da tunanin idan Amira ta shigo gidan wani irin zama zasuyi, dan yau da gobe se Allah, Amira ta cika macen da zata wuce a kalla, tai shiru tana tunanin ina mafita.
Se magariba sannan Imran ya dawo, kuma ba wannan ne lokacin da ya saba dawowa ba, ta tashi ta karɓi ƙatuwar jakarsa ta sojoji, be kulata ba ya wuce ɗaki abunsa, yai wanka ya fita sallar magariba, be dawo ba se isha'i, bayan ya dawo yace "My a kawo Abinci ne?"
"No karki damu naci Abinci"
"Haba my D ban cancanci haka daga gareka ba, kana nufin kar inyi kishi akanka kenan? Wani kalar zama zamuyi kuma ranar da ta tare? Akwai yiwuwar ka juyamin baya kenan?"
"Ihsan ba haka bane, na rasa ya ki ke son inyi ne, na miki bayani amma kin kasa ganewa, kishi yana rufe miki ido da yawa, kin kasa fahimta ta gaba ɗaya, ni ba wani abu tsakani na da Yarinyar nan, na gaya miki komai da yadda aka yi na Aure ta, amma kin kasa fahimta, ta yaya zata gaya miki magana ki yadda, baki san halin yarinyar nan bane, idan har ki kace zaki biye abun da zata dinga faɗa, to tabbas za mu dinga samun saɓani, ni ba burina bane in dinga ɓata miki rai ba, ina sonki Ihsan meze sa in muzguna miki? Amma kishi yana rufe miki ido da yawa Why Ihsan?"
"Kayi haƙuri Please, ba zan sake ba insha Allah"
"Yawwa ko ke fa my deari, I miss you fa"
Yai maganar yana rungumeta, tare da faɗaɗa murmushinsa, da haka suka shirya suka sake jefa babin Amira a kwandon shara.
Amira kam ita kanta ta san fatar jikinta tayi kyau, kamar bata shiga rana, ta ƙara ƙiba hutawa kawai take, kusan kullum tana tare da Fadila, tana koyon girke girken 'yan gayu wanda bata iya ba, sam Amira ba ta da ƙyuya, Akwai gyara bata son ƙazanta kwata kwata.
Wasa wasa seda Imran ya shafe watanni biyu shi da Ihsan a Lagos, Abba ya kira zeyi faɗa akan rashin dawowarsa, Anty tace "ita tace bakomai su bari sa dawo daga baya saboda wasu dalilai"
Nan kuwa tayi hakan ne dan tabattar da Amira ta ɗau gyara yadda ya kamata, kuma duk iya nazari da binciken da Anty tayi akan Amira ta kasa tabattar da abinda ake zargin Amira na karuwanci gaske ne ko ƙarya ne, ita dai a barta da shirme wasu lokutan da taurin kai, amma sam ba ta ga wani abun ashsha ko aibu a tare da Amira ba.
Tunda Imran yai zancen za su dawo Kaduna Ihsan ta shiga damuwa da faɗuwar gaba, saboda yadda ta tsani Amira ko zancenta ba ta son ayi, se ta ji gaba ɗaya hankalinta ya tashi.
Kwanansu Biyu da dawowa Kaduna, amma ba taji anyi zancen tariyar Amira ba, ta cewa Imran tana son Zuwa gida za ta je ta gaida Mummy, da ga nan kuma za ta je ta gaida Ammi, Imran da kan shi ya kaita gidan su, ya shiga su ka gaisa da Mummyn Ihsan, sannan yace ta bari da daddare ze zo ya ɗauke ta suje gidansu ta gaida Ammi.
Ihsan tayi murna sosai zuwanta gida ta ga Mummynta, saboda tayi missing ɗinta sosai.
"Ihsan kinyi ƙalau abunki, lallai Ikko ta karɓe ki"
Ihsan tai murmushi tace "Mummy kenan, ni nifi missing ɗinki akan Komai fa"
"Wane missing ɗina, bayn kin bi mijinki Lagos ba labari, se da ki ka je can da kwana biyu sannan na sani"
Jiki a sanyaye Ihsan tace "Mummy tafiyar ce ta zo min babu shiri fa"
"Kamar ya ya babu shiri, nima nayi mamakin wannan tafiya taki cikin gaggawa"
"Mummy zama na da Imran a tsorace na ke, yanzu nake sake gane wasu da ga halayen sa wanda ban sani ba a baya, ban taɓa sanin yana da fushi haka ba, idan nai masa laifi se yayi watsi dani gaba ɗaya ya shiga yin ratuwarsa shi kaɗai"
Mummy tace "to ke da ga Aurenku me ze sa harki fara masa abunda za kuyi faɗa?"
"Mummy kin manta ba ni kaɗai bace ?"
"To se me dan bake kaɗai bace? Meye ruwanki da ita?"
"Hmm, Mummy wallahi Karuwa bala'i ce, Imran ya tabattarmin da ni ka ɗai yake so, amma Yarinyar nan tana nema ta zama bara ga soyaya ta da ma Aurena da Imran"
"Ke fito kimin bayani dalla dalla mana, yi min Magana kai tsaye, naga dai bata tare ba haryanzu"
"Mummy, ni da Imran bama taɓa samun matsala se idan anyi zancen yarinyar nan, ni ba na iya ɓoye fushi na da kishi, shi kuma da nayi fushi akan ta seyai banza dani wai ya nake son yayi, kuma mahaifinsa ne yake matsawa akan al'amuran ta, shi ba sonta yake ba ba kula ta yake ba, amma idan har mahaifinsa ya cigaba da tura mas ita akwai matsala Mummy"
Mummy ta ja ajiyar zuciya tace "kwantar da hankalinki, ai ba a banza na yadda aka kai ki ɗakin nasa duk da wannan cin amanar da akayi mana ba, idan ubans yana tura masa ita, ni kuma zanwa tufkar hanci ta ɓangaren mahaifiyarsa, ki kwanta kiyi baccinki a ɗakin Aurenki, ba zan zuba ido wani Abu mara daɗi ya faru dake saboda wani Babansa ba, ni na san abunyi"
Ihsam ta rungume Mummynta tana "Yawwa Mummy na, shiaysa nake sonki Sosai, amma da hankalina duk a tashe yake wallahi"
"Ki kwantar da hankalinki, miƙomin wayata, tun yanzu zan mata magana, yadda in kunje can ɗin zata san me za tayi"
Cikin murna Ihsan ta miƙa mata wayarta, ta karɓa ta kira Ammi, wayar tana fara ringing Ammi ta ɗaga tai sallama tare da faɗin "Hajiyata manyan ƙasa, ya gida ya business?"
"Lafiya ƙalau Alhamdilillah, ya aiki ya Meenal, kwana biyu ba ta zomin ba"
"Tana lafiya, harkar school ce ta sako ta a gaba, nace ba dan ba dan ba ai se a fasa school ɗin nan, duk tabi ta ranar min da ita, dama gata ba jiki ba gaba ɗaya ya zabge saboda harkar makaranta ba ta da lokacin kanta"..
"Allah sarki, ai ba'a fasa makaranta ba, se haƙuri, Allah ya bada sa'a ace ina gaisheta"
"Za ta ji insh Allah"
Mummy tace "kin sam su Ihsan sun dawo, gata ma ta zo min"
"Eh na sani ya gayamin, dan shi ya zo ma jiya, ya cemin anjima insha Allah ze suzo mu gaisa, dan son kai shine ta fara zuwa gurinki ko?"
Mummy tai murmushi tace "to wannan kuma i taku keda 'ya'yan naki, sedai ta zo min da batun wai wannan Yarinyar zata tare ko?"
"Hmm kedai bari, Yarinyar nan yadda ki ka san a kaina zata tare wallahi, nayi nayi da babansa ya yadda a raba musu gida amma yaƙi, kwata kwata na rasa abunyi wallahi, baban su na da haƙuri sedai akwai taurin kai"
"To ni dma ba wani abu baane ba, dama cewa zanyi dan Allah idan sunzo anjima a ƙara ja masa kunne, kar azo ana samun matsala, kin ga dai na farko yarinyar nan tayi yawon ta zubar, kuma Hajiya Nafisa ita ta yiwa yarinyar nan test, zasu iya haɗa baki da ita ace yarinyar nan lafiyarta ƙalau, alhalin baza'a rasa wani abun a tare da ita ba, a dai ja masa kunne ya kula, kar a samu matsala"
"Ki kwantar da hankalinki, na daɗw da yi masa wannan takarar, babu abunda ze faru insha Allah, dan nima ban shirya amsar jika a gurin karuwa ba, kuma shima ya tabattarmin da babu abunda ze faru, na zubawa babansa idone dan in bi komai a hankali, amma zanyi duk me yiwuwa raba auren nan zanyi ba inda zashi"
"A' Hajiya Jamila, kar ace mun haɗa kai an kashe masa Aure a zagemu fa"
"To base aita zagi ba, aimu mafitar yaranmu kawai kuke nema, karki damu ki kwantar da hankalinki, zan sake jan kunnensa insha Allah"
"To shikenan Nagode sosai, se sunzo ɗin".
"To shikenan Allah ya kawo su Lafiya"
Mummy na katsae kiran, Ihsan tace "haba Mummy, naji ana za'a kashe Aurensa da ita kuma kina cewa kar ace kun kashe Aure?".
"Au so kike in nuna ƙarara ga abunda nake so? Ke baki san rayuwar duniya'yar siyasa bace, ai ina sane na faɗi hakan"
"To shikenan, ni Allah yasa kar ta tare ma a kashe Auren"
"Ameen, nima da na fi son hakan ai"
Haka Ihsan suka cigaba da hirarsu da Mummyn ta, suna tsara irin rayuwa da kuma zaman da Ihsan za tayi da Amira ko da ta tare ɗin.
Se bayan sallar magariba sannan Imran yaje ya ɗakko Ihsan suka tafi gidansu Mummy ta bata magunguna da sauran abubuwan gyara.
suna zuwa gidan su Imran Minal ta rungume Ihsan tana murna tace "Anty Ihsan shine kika fara zuwa gurin Mummy kika wuni se yanzu zaki zo mana ko? Ni na mayi fushi ki koma kawai "
Ihsan tai murmushi tace "lallai, ni banyi fushi ba seke, sau ɗaya fa kika zo gidana, shima Ammi ki ka rako, ba dan haka ba ba zan ganki ba"
"Kai Anty Ihsan kwanan ki nawa a gidan ku ka tafi lagos, kuma shi Yaya Imran fa yana faɗar baya son a dinga zuwar masa gida idan yai Aure"
"Haba My, shikenan mu ba za'a zo inda muke ba"
Hararsu Imran yayi yace "cigaba da biye mata tana miki shirme"
Ammi ce ta fito daga ɗaki tana faɗin "mutanen Lagos"
Ihsan ta zube ƙasa tace "Ammi ina wuni"
"Lafiya ƙalau Ihsan, ya gida ya kika baro Mummyn"
"Lafiya ƙalau Ammi"
Tace "Masha Allah, Imran ya aikin"?
"Aiki Alhamdilillah Ammi, ya gidan"
"Gida gamu a cikinsa, Minal kawo musu Abinci su ci a nan ko su tafi da shi, dan da ku mu ka saka sanwa"
Imran yace "ai idan ma ba'a sa ka damu ba a ɗora wata, ina Abba ko be dawo ba?"
"Yana gurin aiki, se Allah ya kaimu sati me zuwa ze dawo"
Nan suka dinga hira, Minal ta kawo musu Abinci, Imran ya zage yana ci amma Kunya ta hana Ihsan cin abincin, duk da kuwa ta saba da gidan sosai, amma haka nan ta dinga jin nauyin cin abincin.
Ammi ta shiga ɗaki yin sallar isha'i, Imran ya kalli Minal yace "ba mu guri zan bawa mata ta Abinci"
Minal miƙewa tai tana ɓoye dariya a ranta tace "Lallai ka ga masoya"
Tana tafiya ya janyo Ihsan jikinsa yace "kin wani ƙi cin abinci, Gara tun wuri ki saki jiki kici Abincin nan, oyo open Your mouth"
Haka Ihsan ta lafe a jikinsa yana bata Abinci, tana amshewa, Ammi ce ta fito daga ɗaki Da hanzari Ihsan ta bar jikin Imran cike da kunya, Ammi tai murmushi tace "Ihsan kenan"
Imran kam basarwa yayi kamar ba wani abu da ya faru, Ihsan kam kamar ƙasa ta tsage ta shige dan Kunya.
Ammi ta zauna sannan tace "Imran naji daɗin yadda na fuskanci kuna zaman lafiya, nasan lallai a wannan dawowar ta ku Mahaifinka ze ce se waccan Yarinyar ta tare, to ina son in sake ma ka jan kunne ne, kar ka sake zuwan Yarinyar nan ya zama barazana ko silar rushewar farincikin da nake gani a Tare da ku, kasan irin zaman da za kuyi, ba kai ba shiga sabgar yarinyar nan, kuma na ga a tsaye take idanunta ba bu alamar mutunci, kar ka kuksakura ka bada ƙofar da za ta saka Ta raina maka mata, tsakanin ka da ita ido, tun da ubanka ya dage ka Aureta ka Aireta ga gida nan taje ta zauna, ni ba zan lamunci in haɗa zuriyata da Karuwa ba, ka kula kuyi hankali da ita.
Ke kuma Ihsan, karki kuskura ki biye mata, dan ba cikakken hankali ne da ita ba, zata iya yi miki illa idan kika ce zaki biye mata, ba ruwanki da ita, ki bi mijinki ku zauna lafiya duk yadda zanyi zanyi inga Auren nan beje ko ina ba, goyon bayan ku kawai nake buƙata nan kusa zan mitstsike Auren nan"
Da ƙarfi ƙirjin Imran ya buga, kawai se ya saki Amira, da wani idon ze kalli Abba idan ya sake ta?
Ammi tace "Naga kayi shiru, ko ka nada Magana ne?"
"A'a kawai ina zancen zuci ne, ba damuwa Ammi insha Allah zan kiyaye abunda kika faɗa"
"Yawwa Allah yayi muku Albarka, ina ƙara gaya muku baku ba yarinyar nan ko shiga shirginta, kuyi rayuwarku daban tayi tata"
Haka Ammi taita jaddada musu, suka tashi tafiya ta kawo kyautuaka ta bawa Ihsan.
Ko da suka koma gida Ihsan ta riga Imran yin gaba, Abba ya kira wayar Imran, Imran ya ɗaga suka gaisa da Abba.
Abba yace "Imran naji kun koma ko?"
"Eh Abba yau kwananmu uku da dawowa"
"Yawwa to dama bugowa nayi in roƙi alfarma, dan nasan idan ban nema ba baza'ayi min ba, ina so aje a duba 'uar marainiyata, kaji ko da abunda suke buƙata saboda tariyarta"
"To Abba insha Allah, kuma dama nayi niyyar gobe in Allah ya kaimu zanje gidan Antyn insha Allah"
"Yawwa yaron Kirki, haka nake son ji, ba danni ba kuma ba dan Amira ko halinta ba, a daure a taimaka a kulamin da marainiyar nan dan Allah Imran, ka ta ya ni wanke laifin da na aikata a baya, ka riƙe Yarinyar nan da mutunci, ka manta da irin nata laifukan ita ma dan Allah"
Gaba ɗaya jikin Imran yayi sanyi yace "Insha Allah Abba, zanyi ƙoƙarin kula da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 16 Chapter of 31