Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
a cikinta, ranar da yaron wajen ka yazo nan ma, ba kaga yadda suka fafata ba, seda ta masa rashin Kunya ya bubbigeta, bayan tafiyarsa a garin yawonta ta kwaso juna biyu, ta sha magani ta zubar ya dinga wahalar da Ita, seda muka kaita Asibiti, idan ta bar gidan nan se tayi kwanaki fiye da goma Babu wanda yasan inda take, samari kuwa babu kalar wanda basa zuwa gurinta, lamarin nata dai ba arziki a cikinsa sam" Alhaji Ali ya dafe kansa cikin damuwa yace  "yanzu ina Amiran take ne?" "Eh to, yaron gurinka ya kira waya aka gaya masa ga abunda tayi, yace ze kaita makarantar kangararru, tun jiya da farar Safiya ta bar gidan nan ba wanda yasan ina ta tafi" Abba yai shiru na wasu 'yan daƙiƙu, yana tunani gami da nazari akan yadda ze ɓullowa lamarin, can yace  "Shikenan, yanzu dai duk yadda ake ciki dan Allah idan ta fawo, a kirani a waya a sanarmin, zanga abunda zanyi idan ta kama mu koma can Kaduna da ita shikenan, semu tafi ta koma can a nema mata makaranta" Baba yace "ai ta gama sakandare bana" Abba yace "eh high institution nake nufi" Yadikko tace  "amma bazamu so ka ɗauke mana ita ba, dukda rashin jinta bazamu so ka rabamu da ita ba, muma muna ƙaunarta" Abba yace "sedai yadda ta yuwun kawai" Ya miƙe da nufin ya tafi, Yadikko tace "to Yallaɓai sedai Amiran ta lalata min sabuwar wayata, idan ta dawo ban san dame zan kiraka in sanar maka ba" Abba yace "ai wannan ba Abun damuwa baane" Yasa hannu a aljihunsa ya ɗakko kuɗi ya ajiye mata yace "gashi nan, ki sai wata wayar sauran kici goro" Ta amshe tana washe baki tana dariya, suka fito tsakar gida, Su Sadiya suna gaisheshi, suma duk yabi ya basu kuɗi. Yadikko ta kuma karkacewa tace  "ai Yallaɓai wannan sune 'yan uwan nata, ba wadda ba tayi saukar alƙur'ani a cikin su ba, wallahi nutsatstsune gasu nan, baka ga yadda ake yaba tarbiyyar su a unguwa ba" Abba yace "Masha Allah, Allah ya ƙara tsare mana su gaba ɗaya" Yadikko ta sosa kai tace  "Ai naga shima yaron gurin naka ya girma sosai, masha Allah gashi nutsatstse ne" Abba yace "Au Imran, ai shi yanzu haka sojane" Yadikko tace "Soja marmari daga nesa, masha Allah, to Yallaɓai meze hana a ƙara ƙulla alaƙa da danƙon zumunci, a yaran nan yazo ya nemi ɗaya daga cikinsu ko Sadiya ko Amina?" Abba yai mutm yace  "Allah sarki, ai Imran ya kusa Aure, befi sati biyu ya rage bikinsa ba, za'a aiko muku da katin gayyatar ku har gida" Seda Yadikko ta canza fuska, amma ta maze tace  "Ahhh Alhamdilillah, kace mun kusa zuwa Kaduna garin gwamna, to Allah ya kaimu lokacin lafiya" Haka suka raka Abba har gaban motacinsu, ya shiga sukayi Sallama ya tafi, Yadikko ta koma gida tana mita, "yo ni tunda an kusa auren ɗansa base ko shi ya auri wata daga yaran nan ba, muma mu dangwali arziki amma shikenan daga ƙwauri se gwiwa, har yana batun ya ɗauke wannan watsatsiyar wato taje ta huta, mu mu zauna a wahala, daga nan ma a rufa ta samu wani hamshaƙin ya aureta, to wallahi baze yuwu ba, baze yuwu ta bar gidan nan ba, gara mucigaba da zama, taita gurza Rashin mutumcin, mu zauna a wahalar tare. Umma tace "Yadikko naso mutumin nan ya amsa ɗansa ya auri ɗaya daga yaran nan, ai da mun rage zafi da sun fita zakka, duk 'yan matan gidan nan ba wadda ta taɓa auren wani me ɗan abun hannu, duk se talakawa" Yadikko tace  "waccan makirar Fa'iza, ba yadda ba'ayi da ita ba ta auri Alhaji Yahaya amma taƙi fafur, da ko ba komai ko umarar nan naje, da an rage wasu wahal halun, shiyasa nakeson ko Sadiya ko Amina wata ta samu me ɗan maiƙo" Umma tace "to Ubangiji Allah yasa a samu ɗin" "Bari kawai, ai idan suka kawo katin bikin nan, dole ne mu tafi gaba ɗaya harsu ɗin, idan yaso ko a cikin manyan mutanen fa zasuje a samu su samo miji nagari, ba wannan samarin da suke binsu ba, basu ajiye komai ba basu bawa wani ajiya ba, banda ƙaddara aisu Sadiya kalar manyane" Nan kansu ya dinga kumbura, Sadiya ta fara raya abubuwa a ranta, fan harga Allah Imran yayi mata musamman zuwan nan da yayi, ya burgeta sosai. Amira na kwance a ɗakinta na Hotel, tayi shiru tana tunani, taji ana knocking, tashi tayi taje ta buɗe ƙofar, Sultan ne tare da wani mutum, bata ce komai ba ta saki ƙofar suka shigo, a nan falo suka zauna, ita ma ta nemi guri ta zauna a wata kujerar. Mutumin ya kalleta yace  "gimbiyarmu, fatan kinzo lafiya?" "Ƙalau" ta bashi amsa a taƙaice. Ya ɗan gyara zama yace  "A gaskiya naji daɗin amsawa da kikayi, har kika baro Kano kika taho Abuja halartar taron bikina, naji daɗi sosai nayi farinciki" Se yanzu Amira ta gane ashe shine wanda ya gayyacesu bikin, oho ita bata san waye bama, ita dai babban abunda yasa ta ƙarfafa ta taho garin Abuja shine tazo a huta, ta rage baƙin cikin dake damun ta a zuciya. Ta dubi mutumin tai murmushi tace "Naga saƙonka an bani waya, harna fara amfani da ita, nagode sosai kuma insha Allah zamuyi iya ƙoƙarin mu mu nishaɗantar a gurin nan, Allah ya sanya Alkhairi ya baku zaman lafiya" Yace "Ameen ya Allah gimbiyarmu, ko zaki iya bani lambar wayarki?" Amira ta girgiza kai tace "No need, duk abunda kake buƙata ka gayawa Sultan ya gayamin" Ya jinjina kai yace  "Shikenan yadda kike so haka za'ayi, sedai zan gayamiki garin Abuja garine na samun kuɗi sosai, performance ɗinki ze janyo miki mutane sosai, dan haka ki dage ki ƙara shiri" Amira tai murmushi tace "bana buƙatar wani shiri, wanda nazo dashi ya isheni". "I like your confidence dear, Akwai manyan mawaƙa daga kudancin Nigeria suma zasu halarci taron bikin, amma gaba ɗaya nafi farinciki da zuwanki akan kowa gurin nan, nasan ba zaki bani kunya ba" Amira tace "Allah yasa" "Kamar yaya Allah yasa?" Sultan yace "Ai zuwanta garin Abuja bashi ne ba, kayi addu'a taje gurin taron, dan wannan gimbiyar, gimbiyarce ta gaske, komai nata ganin dama ne" Mutumin yace  "Ahh tofa kace aiki be ƙare ba, dan Allah gimbiyarmu ki halarci bikin nan Please, kece gishirin bikin nan Please" Murmushi tayi seda haƙoranta suka Bayyana, tace  "idan har ina raye kasa a ranka naje taron bikinka, dan bana karya alƙawari" Ba laifi sun sha hira sosai, Sannan mutumin nan ya tafi. Abba kuwa shiru shiru, ya dinga sauraren kira yaji ance Amira ta dawo, amma shiru gashi haryanzu yana yawan mafarki da Ƙanwarsa, akan ya kula da 'yarta karta lalace, abun se damunsa yake ya rasa inda zesa ransa, gashi ta kasa ta tsare akan lallai ita baza'a kawo mata Amira gidanta ta zauna ba, shi dai Abba bece komai ba ya cigaba da yiwa iyayen Amira addu'a, da fatan duk inda take Allah ya karkato hankalinta ta koma gida, dan yana nadama akan rashin tallafar rayuwar Amira, dukda a yadda ya gani dangin mahaifinta sunyi ƙoƙarinsu akan taribiyyarta amma ta lalace, ƙila suna takurawa ne gurin tarbiyyar shiyasa ta kangare musu. Rana bata ƙarya sedai uwar ɗiya taji kunya, hall ya kai hall, ƙaton hall ne wanda yaji kayan ado sosai, ba ƙarya ma halarta taron 'yan hutu ne, ankon dake jikin 'yan matan dana iyaye ze tabattar maka da masu kuɗi ne, gashi da yawansu farare ne tas kamar basa shiga rana. Tuni manyan mawaƙa suka fara baje kolin baiwar murya da Allah subhanahu wata'ala yai musu, Ango da amarya tuni suka iso, tun a hanya yake kiran waya yaji idan su Amira sunje, amma aka sanar masa basuje ba. Ango da Amarya na zuwa gurin taron, hall ya ƙara yamutsewa, da ɗaukar hotuna da shagulgula kala kala. Da mota akaje aka ɗakko su Amira, harabar gurin kawai abun kalloce, Amira ta tsaya tana ƙarewa harabar gurin kallo, doguwar rigar abayace a jikin Amira, ta yafa mayafin a kanta, sannan ta saka face mask ba a iya gane fuskarta, suka sakko daga motar, har zasu shiga gurin wayar Amira ta fara ringing, tace su shiga zata biyo bayan su. Ta ɗaga wayar ta saka a kunnenta "Hello Amira, ina kika shiga ne, naje gida yau ance bakya nan, gashi Abban  Kaduna yanata kiran waya yana tambayar kin dawo?" Amira tace  "meye nasa na inda na tafi? Meye damuwarsa bayan ɗansa daya tura shine kuma ya wanke ƙafa yaje da kansa?" "Amira Yanzu dai kina ina ne? Nazo gida ance kwananki huɗu bakya nan, ina zuwa akace an san ina da lambar ki, in kira inji kina ina?" Amira tace "somewhere in the world" "Wane Irin somewhere in the world? Amira kina ina?" "Anty Fa'iza kin dameni fa, ina ruwan wani da inda na tafi naje in huta ne" "Malama ɗan matsa kinzo kin cikewa mutane hanya" wata siririyar murya ce tai maganar, Amira ta ɗago ta kalleta daga sama har ƙasa, ta ɗauke kanta ta cigaba da wayarta. "Malama Magana fa nake miki" Budurwar ta sake maimaitawa, Amma Amira tai burus da ita. Yunƙurin sake yiwa Amira magana tayi, amma Amira cikin tsawa tace "ke dalla karki isheni, jiki a bushe ke ba ƙiba ba, amma kin isheni wai na cike hanya, in bazaki wuce ta nan ba shikenan" Ta kalli Amira tace  "ke ɗan saurara mana, wama ya gayyaceki gurin nan har kike nema ki gayamin Magana ne iyee?" Amira cigaba da wayarta tayi, dan yadda ranta yake a ɓace ɗin nan zata iya buga wannan shashashar da ƙasa. "Amira keda wa kike magana ne?" "Anty Fa'iza, dan Allah kiyi haƙuri, sanin inda nake bashi da amfani, idan kin sani ma ranki ne ze ɓaci, se anjima kawai" Ta kashe wayar ta shiga hall ɗin, ashe tunda su Sultan sukazo ake mata kirari, ake koɗata Sultan na hangota ya ƙarasa inda take yace  "Amira ki hanzarta mu ake jira tun ɗazu fa" Bata tanka masa ba, taje ta cire abayar jikinta, seda aka kashe fitala na wasu 'yan lokuta sannan aka kunno fitilar. Amira ta bayyana akan stage, kamar kullum idan zatayi rawa, a tsuke take a cikin riga da wando, Attached ɗin nan har ƙugunta, nan fa aka saki kiɗa Amira ta shiga baje kolin rawa, ita da tawagar Sultan, gurin ya ɗau sowa da ihu, nan aka dinga bajakolin kuɗi akan Amira, sam bata jin jikinta, rawata kawai takeyi. Tunda tai tozali da Amira gabanta yai Wata irin mummunar faɗuwa, saboda tsananin kamanin da take da Imran, nan ƙirjinta ya shiga dukan uku uku, wannan yarinyar tana da alaƙa da Imran ne kokuwa dai kawai kamanni ne? Tasan dai Minal sam bata kama da Imran, amma wannan kamanin nasu sun ɓaci sosai. Nan ta shiga tunanin wacece wannan take rawa haka? Meye alaƙarta da Imran. Aka bawa su Amira hutun taƙaitaccen lokaci, kafin a sake kiransu kan stage kowa se jinjina mata yakeyi, na iya ƙwarewarta a rawa. Aka sanar da isowar wani shahararren mawakin kudancin Nigeria, wanda sunansa ya zaga ciki da wajen Nigeria harma da wasu sassa na duniya, shima aka dinga tafi ana masa sowa. Amira tai shiru tana tunanin irin kuɗin da aka liƙa musu, yanzu akwai irin wannan mahaukatan kuɗin, amma idan ba da dalili makamancin wannan ba, baka isa ka cisu ba, an gwammace a zubar dasu a gurin taro dan a faɗa ace anyi, ire irenta masu rangwamen gata, sedai in zasu sauka daga hanyar da ta dace shine zasu samu irin wannan kuɗaɗen. Tana cikin tunanin ne taji an dafata ta baya, ta juya taga yarinyar ɗazuce da suka haɗu a bakin ƙofa, sedai bata gane Amira ba saboda ɗazu Amiran ta saka mask. "Sannu da ƙoƙari 'yar uwa gaskiya kin burgeni sosai" Amira tace "Nagode" "Amma dan Allah ko zan iya tambayar ki wani abu?" Amira tace "No ba shi nazo yi ba" Tai gaba ta bar Ihsan a gurin a tsaye. Aka kira wannan shahararren mawakin ya hau kan stage, ya karɓi mic ya fara zuba waƙa shima, mawaƙin na daga cikin manyan mawaƙan da Amira ke sauraren waƙoƙin sa, from no where Amira ta fara bin salon waƙar tasa tana rawa, aikuwa abun ya ƙayatar dan rawar ta hau sosai da waƙar da yake yi. Ba ƙaramin burgeshi Amira tayi ba, ƙarshe dai tare sukayi performance ɗin shi da Amira, shi yana bake basirarsa ta waƙa Amira na baje tata a fannin rawa. Biki yayi biki, Amira ta samu kuɗi sosai da sosai, mawaƙin nan yazo ne yayi mintuna talatin ya tafi, amma se gashi ya zarce lokacin daze bar gurin. Ya karɓi mic yaiwa Ango da amarya fatan zaman lafiya, sannan ya yabawa Amira irin baiwar da take dashi, haryake cewa be kamata ta ɓoye baiwar da Allah yai mata ba (🙄🙄🙄 masu ziga mutane suna tamɓele, duka wata baiwa idan ba ta addini ba shirme ce) Ya ƙara da cewa zata iya zama wani abu da wannan rawar da ta iya haka, ya jinjina mata ya yabawa ƙoƙarinta da yadda ta burgeshi sosai. A take ya nemi yaga Amira a kan stage, Amira ta basar ta fito kan stage ta tsaya, mawaƙin yai alama da a miƙo masa wani abu, aka miƙo masa abu a ƙaramin kwali. Yana buɗe kwalin ya fito da mukullin mota, ya miƙwa Amira seda ta tsaya tana kallonsa ya sake miƙa mata, murmushi tayi sannan ta miƙa hannu ta karɓa, ya miƙa mata hannu su gaisa, amma ta girgiza masa kai tace  "I am Muslim" Nan ma aka cigaba da cecekuce, da taya Amira murnar kyautar mota data samu a gurin, banda kuɗin liƙi, dan son bajinta haka wasu masu kuɗin suka cigaba da bata kyaututtuka. (Ina jin takaicin irin wannan kyauta da ake bawa makaɗa da mawaƙa, bayan tarin malaman da muke dasu, da masu ilimin addini, Yanzu anfi bawa mawaƙa da 'yan film mahimmanci fiye da manyan malamnmu) Mawaƙin nan yasa aka kira masa Amira, suka sake gaisawa yace "a gaskiya nayi mamaki da kikace ke mususlma ce, dama akwai wani video na waƙata da zanyi shooting next week, yarinyar da zan saka tana min wasa da hankali, idan bazaki damu ba ina son inyi featuring ɗinki a waƙar, hakan zesa duniya ta sanki sosai" Amira ta ɗanyi shiru sannan tace  "A ina za'ayi shooting ɗin?" Yace "eh to, zamuyi wani a nan Abuja wani kuma a Lagos, amma ina son zamu fara cover na waƙar, zamuyi hotuna tare za'a saka" "Shikenan, na yadda za'ayi hotu nan, amma fitowa a waƙar se nayi nazari" Yai murmushi yace "zamu iya zama abokai"? Amira ta girgiza masa kai alamar A'a, ta wuce ta barshi a gurin, nan aka finga hotuna da Amira, da ƙyar ta zame suka bar gurin. Abba ba yadda ya iya haka ya koma Abuja, yana sauraren ta ina za'ace masa Amira ta dawo. Yana zaune a Office yana aiki, amma yana ta zancen zuci, buɗe ƙofar Office ɗin akayi tare da sallama, ya ɗago ya amsa. Alhaji Hashim ne yace  "Alhaji Ali, kasan meke faruwa kuwa?" "A'a seka faɗa" "Wallahi hoton wata yarinya ne yake yawo a social media, me matuƙar kama da kai, wani mawaƙi yasaka hotunanta wai ze saka ta a sabuwar waƙa, se haɗa hotonka ake da nata wai anya ba 'yarka bace?" Alhaji Ali yace "Ni kuma?" "Ƙwarai kuwa kamar ku ɗaya sosai, kuna kama, sedai kana ganin yarinyar kaga fitsararriya" Alhaji Ali yace "ni kuwa wacece haka?" Alhaji Hashim ya ɗakko wayarsa ya daddana ya miƙawa Alhaji Ali. Yasa hannu ya  karɓa yana dubawa cikin tashin hankali yace "Innalillahi wa innalillahi raji'un" Share Please Masu Comments ina godiya sosai da sosai, ina jin daɗin Comments ɗin yana bani ƙwarin gwiwa sosai. Domin gyara, Sharhi ko shawara 07063065680 [1/8, 9:33 PM] Ayshercool:    🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 WUTA A MASAƘA PERFECT WRITERS ASSOCIATION (WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS) https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P. W. A *Story and written by* AISHA ADAM (AYSHERCOOL) The experience writer of *ABDUL JALAL* * WATA KISSAR.... (SAI MATA) *BAƘIN TABO (Labarin gasa) *AƘIDATA (Paid Book) * WUTA A MASAƘA SADAUKARWA GA ƘUNGIYAR PERFECT WRITERS ASSOCIATION, DOMIN TAYA MURNAR CIKA SHEKARU BIYU DA KAFUWA https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in ❌❌❌ Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba. Afuwan banyi Editing ba                                                               9_10 Abba ya nanata innalillahi wa innalillahi raji'un ya kai sau goma, Alhaji Hashim yace  "Aliyu ya dai? Koka santa ne?" "Hashi akwai damuwa fa" "Damuwar me?" "A game da wannan yarinyar, ba wai wai bane, 'ya ce a gurina, 'yar ƙanwatace data mutu ta bari, gaskiya bazan ɓoye maka ba nafi shekaru biyar rabona da ita, tana hannun dangin mahaifin ta, kawai se a tsukin  kwanakin nan akamin waya akace, tana rashin ji na tura Imran yake ya gano min meke faruwa, yaje ya mata faɗa da jan kunne, ranar da nace maka zan koma gida kano zan tafi, ai gurinta naje ina zuwa suka cemin kwananta kusan huɗu bata gida bsu san inda take ba, na bar saƙon da zarar ta dawo a kirani a waya a sanarmin, kawai se gashi kazo min da wannan hoton, kuma wallahi kwanakin nan kusan kullum senayi mafarki da mahaifiyar ta tana min magiya a kan kar in bar 'yarta ta lalace, nayi Nadamar rashin bawa yarinyar nan mahimmanci, kuma abunda ya janyo haka naga dangin babanta na matuƙar ƙoƙari akanta" Alhaji Hashim yace "aikuwa da matsala, dan abokan adawa zasu iya amfani da wannan damar gurin yamaɗiɗi da kai a bakin duniya, musamman za'abi diddigi a gano alaƙarka ds ita, da kuma yadda ka gaza kulawa da ita, harta zama haka, dan wannan yarinyar tana kama da kai fiye da yadda take kama da 'ya'yanka" "Hashim yanzu meye abunyi dan Allah?" "Abunyi dai kam dole a nemo shi da gaggawa, yanzu duk yadda za'ayi a tabattar an samo inda yarinyar nan take, dan ance jiya akayi hotunan a gurin wani biki a Abuja, kuma shi mawaƙin ya bata kyautar mota" Alhaji Ali yace  "A Abuja akayi bikin?" "Eh a can ne, a gurin akayi hotunan" "To yanzu a ina zan gano yarinyar nan ni kuwa, bana son inyi wani kyakkyawan motsi daze sa 'yan Adawa su farga da halin da ake ciki" Alhaji Hashim yace "kabi komai a sannu, zamu shawo kan matsalar Insha Allah, zan sa a duba min nan Abujan, za'a ganta insha Allah" "To Allah yasa" Ɓangaren Amira kuwa, sunyi hotuna da mawaƙin nan, sedai sunyi hotunan ne tana sanye da atamfa da kuma jallabiya, sunyi kyau sosai, sedai wanda akayi agurim party ne take sanye da riga da wando. Sultan yana ta sake zigata akan ta amince da maganar mawaƙin nan, a fara haskota a cikin raye raye, zatayi kuɗi da kuma suna a duniya, ita dai bata amsawa Sultan ba, ƙarshe ma cewa tayi ya bata guri zata kwanta dare yayi. Kamar yadda ta buƙata, bayan fitar Sultan, ta shiga tai wanka ta saka kayan baccinta, ta hau gado ta kwanta, Amma gaba ɗaya kewar gida ta dameta sosai, dukda gidan nasu ba wata tsiyar suke tsinana mata ba, amma tana son komawa gida gaba ɗaya garin ya isheta. Ji tayi ana knocking ɗin ƙofarta, ta duba agogo ƙarfe sha ɗaya da rabi na dare, tayi zaton Sultan ne dan haka ta miƙe ta zira hijjabi, ta tafi buɗe ƙofar, tana zuwa bakin ƙofar tace  "waye?" Daga waje taji muryar namiji yace "buɗe ki gani" Ba fargabar komai ta buɗe ƙofar, Ango ne da kansa a wannan daren, ta kalleshi tace "lafiya na ganka a nan a wannan daren?" "Haba ki bari in shigo mana Magana zamuyi" Ta bashi hanya ya shiga, yana ƙoƙarin shiga bedroom ta tsayar dashi tace "karka shigarmin bedroom, meya kawoka a wannan daren?" "Haba Amira meye na wani kar ins higa bedroom, anyway harkar arziki ce ta kawoni" "Ina jinka" ta amsa tana ƙare masa kallo. "Kinga jiya a gurin nan ba ƙaramin kasuwa kikayi ba, manyan mutane nata naman contact dake, ciki hadda manyan masu muƙami a ƙasar nan, wanda zaki samu kuɗi fiye da wanda kika samu jiya a gurin bikin nan" Amira tace "ina jinka" 'to shine mazo muyi yarjejeniya" "Tame fa?" "Zan haɗaki da manyan mutane a garin nan, amma sekin yadda dani tukuna?" "Yadda kamar yaya kenan?" "Waike seki ta wani abu kamar ba 'yar hannu ba, kawai ki amince dani ehh kin gane karatun dai" Amira tai murmushi tace "wannan ai me sauƙi ne, muddin zaka haɗani da Manyan mutane, kuma gashi za'a kai maka amarya gobe in Allah ya kaimu Amma ka taho gurina, Nagode ƙwarai dama ina neman me tayani kwana, damuwa ta isheni" Yai murmushi yace "Allah my mirat?" Yai maganar yana matsowa kusa da ita da ƙoƙarin taɓa ta, Amira tace  "Yanzu ace duk yadda amaryarka ta sha gyara, wani ya kai mata farmaki kamar yadda kake shirin yi yanzu ya zakayi?" Yace  "ahh haba dai, ai babu me yasa n wannan gangancin, duk wanda yaima zan iya hallaka shi" "Amira ce banza kenan ko?" "Ahh no, Amma aike kin saba yi shiyasa nima nazo, kuma ai hanyar Alkhairi zan miki" Amira tace "ƙwarai kuwa nina saba yi kam, dan san'ata ce anyway, shiga ka watsa ruwa kafin nan na shirya" Ba tunanin komai ya shiga murna, ya tuɓe daga shi se gajeren wando ya buɗe toilet ya shiga, yana shiga ta maida key ta waje ta rufe shi a cikin banɗakin Ta tattara kayanta tsaf a Akwatinta, tana jin yadda yake jijjiga ƙofar ze fito amma yaji a rife, ta haɗa kayanta tsaf, ta kwashe agogonsa takalamansa, hula wayoyi da mukullin motarsa da komai na aljihunsa, na kuɗi da ATM cards ɗinsa ta bar ɗakin ta kulleshi ta waje a ɗakin, tai ficewarta. Ta fice daga Hotel ɗin, ta dinga tafiya ba tare da tasan inda zata ba, seda tayi nisan gaske da Hotel ɗin sosai sannan ta tsaya, ta cire sim cards ɗin wayoyinsa ta kakkarya ta zubar, ta kira wayar Sultan, tai sa'a kuwa ya ɗaga yana ɗaga wa tace  "Sultan, duk abunda kuke ku bar Hotel ɗin nan, Asubar fari ku hawo motar da aka bani ku bar garin nan, dan ni bana Hotel ɗin yanzu haka" Cikin mamaki Sultan yace "Amma saboda me? Meke faruwa?" "Akwai matsala ne, idan kuma kuka zauna za'azo a kamaku a banza ba ruwana" Tana gama maganar ta kashe wayarta, tayi searching a wayarta, inda wasu Hotels ɗin suke, ta samu abun hawa ta tafi wani Hotel ɗin can nesa da gari sosai, taje ta kama ɗaki ta kwana a ciki. Ɓangaren Ihsan kuwa duk yadda taso samun Imran a waya abu ya gagara, tun ranar da taga Amira hankalinta yaƙi kwanciya sam. Yanzu ma gwada layinsa take amma baya shiga, ta koma what's app ta masa Magana. Kamar mintuna biyar dayi masa magana taga ya amsa. Ta sake tura masa saƙo kamar haka "Ina ta trying layinka amma baya shiga, baka kirani ba kuma' "Am sorry, muna cikin daji ne, amma muna hanyar fitowa zamu kwana, gobe insha Allah da safe zamu fito dajin ne ba network sam" "Shikenan, ina fatan kana lafiya ƙalau" "Lafiyata ƙalau, jibi in Allah ya kaimu zan dawo gida, zan ɗau hutu na Aure da zanyi" "Kai amma nayi farinciki my own, Allah ya kawomin kai lafiya" Imran yace "Ameen, kin koma gida daga gurin bikin ne?" "A'a, ranar laraba zamu koma, dama ina ta son tambayarka wani abu, wallahi wata nagani a gurin bikin nan, me matuƙar kama da kai, hankalina ya tashi sosai dana ganta" "Ni kuma? Wacece wannan haka? Kuma meyasa hankalinki ya tashi?" "Kawai ji nayi ba tayimin ba, bana ƙaunarta sam, wata fitsararriya da ita kuma ni ban taɓa ganinta a Family ɗinku ba, sedai kamar da kuke ta ɓaci" Imaran yace "ikon Allah se kallo, nikam ban san wata me kama dani ba, da zata Abuja gurin biki" "Ka zata wasa nake ko? Bari in turo maka hotonta ka gani" Nan Ihsan ta tura masa hotunan Amira, da videos harda wanda tayi da wannan mawaƙin. Imran ya jiya hotunan nan, babu ko tantama Amira ce, hotunan ta ne ba wata ba, take yaji ransa ya ɓaci sosai zuciyarsa har tafasa take, gantalin nata harya kai ta tafi Abuja? "Ya naji kayi shiri bakayi reply ba?" Imran yace "gaskiya ban santa ba, kawai dai ikon Allah ne nima naga muna kama sosai, amma gaskiya ban santa ba" Ihsan tace  "har hankalina ya ɗan kwanta, dan nayi zaton wannan cousin ɗin taka ce da kace min tana Kano" Gaban Imran ya faɗi, amma yace "meyasa kikayi zaton itace?" "Naga kuna kama sosai ne, kuma kace min tana yawo bata jin Magana shiyasa" Imaran yace "hakane, amma ai na gayamiki ita waccan yarinya ce, bsta kai wannan ba" "To ai itama wannan ɗin ba wata babba bace, dan

Chapter 6 of 31