Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
rubuta masa tasa tasai, duk aka kaishi a kai masa, sedai ya nuna babu Matsala a ƙwaƙwalwarsa partial stroke ne, sedai ana ta ƙoƙarin samu aga jinin sa ya sauka. Ammi hankalinta ya tashi, ganin Abba ya fita tun farar Safiya be gayamata in da za shi ba, gashi har ƙarfe sha ɗaya na dare, be dawo ba kuma baya ɗaga wayarta. Se sha ɗaya da rabi ya dawo, yana shigowa cikin damuwa tace "Abba meyasa zaka ƙi ɗaga wayata, kuma ba ka gayamin in da ka tafi ba, duk Hankalina ya tashi" "Imran ne ba lafiya, naje na ɗakko shi ne daga Lagos, yana nan Kaduna a Asibitin doctor Nura" A gigice tace "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Imran ɗina ba lafiya amma ka kasa gayamin? Meya sameshi haka?" "Kinga ki kwantar da hankalinki, ba wani abun tashin hankali bane, kawai dai damuwa ce ta ɗan masa yawa, amma yana samun kulawa ta mussaman" "A'a gaskiya se naje na ganshi, akan me zaka ɓoyemin kaƙi gayamin?" "A'a ba in da zaki fita, ki bari Allah ya kaimu gobe se kije ki ganshi" "To Yanzu waye ze kwana da shi?" "Khalid yana gurinsa, tare muka taho, shine ze kwana da shi" "Amma wace irin damuwa ce zata dame shi haka har ta kai shi ga shiga wannan halin?" "Ahh halin da matarsa ke ciki mana, idan ke be dameki ba ai dole shi ze dame shi, tunda yana zaune da ita tare suke kwana suke tashi, tana masa biyayya daidai gwargwado ai ta cancanci ya shiga damuwa saboda ita, yanzu da yake naki ɗan ne a kwamce ba lafiya, kalli tashin hankali ƙarara a fuskarki, kalli damuwa amma waccan da yake ba taki ba ce ba, seda nai surutu nai mita sannan ki ka je dubata, ban da tsangwama da takura da barazanar zaki sa a saketa da kike mata, duk ina sane Jamila kallon ki kawai nake yi, bata taɓa zuwa ta sameni ta cemin ga laifin ɗana ba, ko ga abunda kike zuwa kina musu ba, amma labari yana dawowa kunne na, ki ƙaddara Ba kya raye Imran yake kan gado Asibiti a kwance ba me temaka masa alhalin kina da ɗan uwa a raye, amma a barshi ba me kula da shi, kwatankwacin abunda ya faru da Amira kenan, har in koma ga Allah ba zan dena nanata matata da mu kai Aure sama da shekaru talatin da wani abu ta kasa min alfarma ba, duk da tarin Alkhairan da ni nai mata ba" Jikin Ammi ne yai sanyi, tai shiruu tana nazari, Yanzu kenan ace ba ta raye Imran ze iya shiga wani hali makamancin wannan ace bame zuwa kansa balle ya kula mata da shi? To amma ta yaya zata riƙe Yarinyar da ta gama lalacewa, bayan ga ta da ɗiya mace ita ma, idan ta koya mata Mugun hali fa? Haka tai shiru tana cigaba da tunani, ga batun Imran na kwance a gadon Asibiti ga wannan maganganun da Abba yai mata. Washegari tun da safe Ammi ta shirya, tai girki ta sanar da Minal halin da Imran ke ciki, ta kira Hadiza ma ta sanar mata, taita kiran wayar Ihsan amma ba ta shiga dan haka ta ƙyaleta. Abba a gajiye yake sosai, dan haka su Ammi ne suka fara yin gaba, yace ze zo daga baya. Cikin ikon Allah ko da suka je Asibitin suka tarar Imran ya farfaɗo, har Khalid ya kai shi yai alwala, ya Bashi Abinci ya kwanta. Ammi ta ƙarasa gaban gadon Imran da sauri, tace "Imran sannu ya jikin naka" Jinjina kai yayi alamar da sauƙi. "Kai kam Imran me kasa a ranka haka kake neman ka halaka kanka da kanka, da ƙuruciyarka amma ace jininka yai irin wannan hawan har abun ya kai ka ga faɗuwa" Shiru Imran yai ya lumshe ido be ce Komai ba, shika ɗai yasan meyake ji game da Amira, yana cikin tsananin fargaba da tashin hankali akanta, ga tausayinta da yake ji sosai, tun asalinta a wahala ta tashi, ya Aureta nan ma bata sauya zani ba, lokacin da yake ƙoƙarin ya bata farinciki iya iyarwasa kuma ga ƙaddara ta larura ta sameta, ga pressure Ammi da ta Ihsan, amma still a haka Ammi ke tambayar dalilin da yasa ya shiga damuwa. Aka dinga zuwa dubiyar Imran a Asibitin nan, wajen azahar Anty tazo duba Imran dan sam bata san Imran ba lafiya ba. Tunda Ammi taje Imran be Magana ba, sedai Anty na zuwa ya buɗe baki a hankali yace "Anty ya jikin mata ta?" Seda haushi ya kama Ammi, taji kamar ta kwaɗe shi amma ta dake ta basar. Minal kuwa sallama tai musu, ta tafi gida domin ɗora sanwar rana. Anty tace "jikinta da sauƙi Imran, ya naka jikin?" "Alhamdilillah" "Allah ya ƙara afuwa, ai se ɗazun nan Abban naka yake gayamin kana Asibiti, kuma an samu cigaba sosai a rashin lafiyar tata, tana ta tambayar ka" Murmushi Imran yai yace "yanzu tana son ganin nawa kenan?" "Ƙwarai kuwa, dan tana ta faman daru, ita ka tafi ka barta bari in kira maka ita a wayar Fadila" Ammi taxe "A'a Hajiya Nafisa, baya jin daɗi be kamata a sake ɗaga masa hankali ba" Da sauri Imran yace "A'a ni dai Anty kiramin ita" Ammi tace "a hakan kana kwancen zaka iya Magana?" "Eh Ammi, a kirata yau watana biyu rabona da ita, a kiramin ita dan Allah" Anty ta kira layin Fadila tace ta bawa Amira. Amira tana kwance tana wasa da gashin kanta, Fadila ta miƙa mata wayar. Amira ta karɓa ta kara a kunnenta, sedai shiru be ce komai ba, itama ba tace komai ba sukai shiru na wani lokaci, Imran ne ya fara sauke ajiyar zuciya, da fari Amira ba ta san waye akan wayar ba, seda taji yai ajiyar zuciya, tana jin ajiyar zuciyarsa ta fashe da kuka tace "Amran ka tafi ka barni ko" Lumshe idon sa yayi, sega hawaye na gangarowa daga idon Imran a hankali yace "Ai kece kika ce ba kya son ganina" "A'a ni bance ba, ƙadangaren jikinka ne bana son gani, amma ina son in ganka dan Allah ka dawo, mu koma gida dan Allah, na daɗe ban ganka ba" Ajiyar zuciya ya kuma yi, yana murmushi, duk da hawaye na bin gefen idonsa yace  "Nima ina son in ganki, ki bari idan na dawo daga Lagos zan zo har gidan Anty in ɗauke ki mu koma gida" Murmushi tai tace "to idan zaka dawo zan maka girki da kaina, zanje gida in wanke maka kayanka, in gyara ko ina nasan gidanmu yayi datti yanzu" A haka kamar ta fara dawowa hankalin nata, amma wani lokacin se tana cikin magana seta fara sako shirme. Imran yace "to shikenan, ki cigaba da yi mana Addu'a kinji, Sannan ki dena kuka ki dinga cin abinci sosai" "Ai ina cin Abincin, me kake yi Yanzu?" 'bacci nayi na tashi" ya bata amsa "To ka gaishemin da kowa da kowa kaji" "Suwa kenan?" "Nima ban sani ba kowama kawai kace ina gaisheshi" "Allah ya baki lafiya Amran ɗina" Tace "Ameen" Duk yadda Imran yaso dakewa kasawa yayi, ya fashe da kuka a gurin, ta tabbata dai Amira ta na da taɓun hankali, jin kukan nasa yasa Amira itama ƙara sautin nata kukan. Ammi ta fizge wayar tace "meye haka Imran kamar wani shashasha, kalli fa kuka kake yi sekace wani sakarai" Imran be kula Ammi ba, ya ɗora tafukan hannayensa biyu a fuskarsa yana cigaba da kukan. Khalid yace "Ammi, tsakanin mata da miji ai se Allah, tun daga yarintar mu ban taɓa ganin Imran yana kuka haka ba, kin san lamarin ya kai a jinjina tun da kika ga yana kuka, kiyi haƙuri amma" Anty kuwa karɓe wayarta tayi a tanta tace "ai gara da Allah ya nuna miki irin son da ɗanki yake mata, wataƙila kya ɗagawa 'yar mutane ƙafa". Tunda Amira su kai waya da Imran, take murna. Anty na dawowa tace "Anty yau munyi yawa da Imran" Anty tace "haba, ya a kai wayar tasa ta shiga?" "Fadila ce ta kirashi a waya, yace min ze zo, ya kusa dawowa azo ai min kitso" Anty tai murmushin tace "inye ka ga matar mijinta, ai dole azo a nemo me kitso kam" Amira ta dinga murna, baki ya buɗe ai Imran yace ya kusa dawowa. Kwanan Imran uku a Asibiti, cikin ikon Allah ya warware gaba ɗaya, sedai abunda ba'a rasa ba. Se Ranar da aka sallame shi, sannan Ihsan ta san ba shi da lafiya, daga wayarta harta mamanta ba ta shiga. A kiɗime Ihsan ta tafi gidan su Imran, dan hankalinta ya tashi sosai da jin wai har kwanciya yai a Asibiti, Amma abun mamakin sam Imran ya ƙi kulata, yaƙi ko kallon in da take. Ammi ta ja ta ɗaki tace "Ihsan waike wace irin sokuwar mace ce ne haka? Ace mijinki ba lafiya amma wayoyinki sam basa shiga, kina me ki kai sake ya fara san Yarinyar nan haka harda yi mata kuka?" Zare ido tayi tace "kuka kuma Ammi?" "Kuka jiya a gabana sukayi waya, hadda kukan sa saboda ita yake Wannan rashin lafiya, ke kenan kullum ba kya nan wayoyinki a kashe, gaskiya ki canza hali" Ammi tai tayi mata faɗa, bayan sun fito Ihsan tace a maida shi gida tayi jinyarsa yace baya so, ba inda za shi ta barshi a gidansu. Maman Ihsan ma da 'yan uwanta duk sun zo duba Imran, sedai sam yaƙi sauraran Ihsan, ko ƙaunar ganinta ma baya yi kwata kwata. Yana ta magiyar a kai shi yaga Amira, ko a kawota amma Ammi ta share zancen. Alhaji Hashim ya dawo gari, dan ya samu labarin rashin lafiyan Imran da na Amira, Amira ya san da rashin lafiyarta dan yazo ya tarar da ita a gida wancan Zuwan da yayi. Jin da Amira tayi ana Maganar Imran, za'aje gurinsa yasa tace itama se anje da ita. Da Anty za tace a'a, Amma Alhaji Hashim yace "je ki shirya ina nan ina jiranki, tare zamu tafi" Amira cikin murna ta tafi ɗakinta. Anty tace "Daddy, ya zakace a tafi da ita, tana ganinsa zata birkice fa" Yace "to haka zata dawwama ba zata ga mijinta ba, ai se suna haɗuwar za'a gane an samu cigaba ko kuwa? Tunda aka samu take zancensa ma ai kinga an samu cigaba, munyi magana da wani malami akan matsalar ai, na kuma yiwa shi Alhaji Alin Magana, dan haka bakomai muje da itan" Amira ta fito sanye da dogon hijjabi, a haka kamar lafiyarta ƙalau ba abunda ke damunta. Suka shiga bayan mota ita da Fadila, Anty da Alhaji Hashim kuma a gaban motar. Suna zuwa gidansu Imran ta ga kamar wani baƙon guri sukaje daban, ita dai babban burinta shine ta ga Amran ɗin ta. Suka nufi cikin gidan, suna shiga falon suka tarar da Ammi da Minal, ga Ihsan da Anty Hadiza, se Imran da ke cin Abinci. Suna shiga akan Imran ta fara sauke idanunta, kallo ɗaya tai masa ta gane ba shi da lafiya ne, ya ɗago ya kalleta ya miƙe cikin sauri yace "Amira" Kallonsa ta tsaya tana yi, kamar ba ta gane shi ba, sedai ba gane shi ne ba tai ba, a tsorace take kar ta je ta kuma ganin abunda ba ta so. Ba kunyar Komai Imran ya ƙarasa inda take yace "Amira baki gane ni bane?" Ɗan hararsa tayi tace "gani nai ka tsufa" Be bi takan mutanen da ke falon ba ya rungume Amira, yaji yadda cikinta ya tokare shi. Sedai zeyi ya yaji jikinta ya fara rawa, kan yai wani yunƙuri tuni ta suma. Jiki a sanyaye ya zauna da ita a jikinsa, yana hawaye. Ammi da Ihsan ji su kai kamar su rufe shi da duka. Alhaji Hashim ya shigo falon, suka gaisa da Su Ammmi, yaga yadda Amira ke sume a jikin Imran jikinta yana rawa yace "ka kwantar da hankalinka, munyi magana da Abbanka, Akwai makamin da ze zo ya dubata kayi haƙuri, zata warware insha Allah, ina Alhaji Alin yake?" Imran yace "yanzu ze fito insha Allah" Ihsan kuwa tayi mamakin ganin yadda cikin Amira ya girma haka, dan gaba ɗaya zatonta cikin ya zube, gabanta ba ƙaramin faɗuwa yayi ba jin ance Malami ze zo ya duba Amiran. Abba ya fito suka gaisa da Alhaji Hashim, suka cigaba da tattaunawa akan yana yin larurar Amiran. Aka kunnawa Amira karatun Alqur'ani, suna nan zaune megadi yazo ya sanar da isowar malamin. A kai masa iso ya shigo, aka gaggaisa ya kuma tambayar Imran yadda Amira ta fara Rashin lafiyar. Yasa kowa ya bar gurin, se Imran kawai da Anty se Abba, yasa aka kawo ƙaton bedsheets, aka rufe Amira da shi, Imran yana rungume da ita. Malamin ya bawa Imran tofi a jarka yace ya shafa mata a fuska, ayoyin faƙƙu sihir ne a ciki. Imran ya karɓa ya shafa mata, sannan malamin ya fara karanta Alqur'ani, sedai farawarsa ba wuya Amira ta fara miƙa, ta finga rawar sanyi kamar me jijjiga. Cikin wata irin wahalalliyar murya kamar me gudu Amira tace "dan Allah kayi haƙuri, ka ƙyaleni haka" Malamin yace "meye dalilin ka na shigar wannan baiwar Allah?" "Eh na daɗe a jikinta, na shiga jikinta saboda yanayin shigar da takeyi ne, kuma asali turani a kai jikinta, ni ke sakata raye raye da jin kiɗa, aka kuma bani aiki akan in haukata ta, nace ba zan iya ba saboda ina sonta, shine aka bawa wani jinin baƙaƙen kaji, aka rubuta sunanta da na wani aljani da sunan mijinta, a kai mata Asiri da ƙadangaren, ba danni ba da hauka za tayi sosai" Abba yace  "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Innalillahi wa innalillahi raji'un, wace irin masifa ce wannan?" Malamin yace "ba wani ba dan kai ba, Allah ne kawai ya kiyayeta, be kuma ɗora mata wahala ba, yanzu ina son kaje ka bar jikinta kuma kaje ka tone abunda kukai mata, sannan ina maka nasiha da kaji tsoron Allah, ba abunda tai maka amma ka shiga jikinta kuna cutar da ita, baka tunanin ita ma halittar Allah ce kamar kai?" "Dan Allah kayi haƙuri, wallahi ba dani aka mata Asiri ba, ni dai kawai ina jikinta ne ina sa ta rashin ji, amma insha Allah yau zan bar jikinta, tunda ka ga nima musulmi ne, kuma ina son gamawa da duniya lafiya" Malamin yace "Naji, ai shiyasa zan maka adalci in ƙyaleka, saboda albarkacin musulunci, kaje abunda kai Allah ze hukunta ka, amma sonake a karya wannan sihirin sannan ka bar jikinta" "Yanzun nan ma kuwa malam, Nagode sosai da adalcin ka" Imran yace "ke tanbaye shi waye yai mata Asiri yake ƙoƙarin haukata min mata?" Malamin ya girgiza kai Yace "ka kuwa san babu halittar da ta kai aljani ƙarya, ze iya yiwa wani sharri, koma waye kawai ka barwa Allah kar kai bincike, Allah ya bata lafiya kawai" Ya cigaba da karantawa Amira Alqur'ani, amma babu wani reaction da ta kuma yi, se bacci da ya ɗauke ta. Ya bada Addu'oin da za'a bawa Amira ta dinga karantawa, da wanda za'a karanta mata a ruwa ta dinga sha, da dokoki da za'a kiyaye dan samun lafiyarta. Abba ya kawo alheri me yawan gaske ya bawa malamin, tare da yi masa godiya. Abba sun daɗe suna jimanta abunda sukaji game da Amiran. Imran kam ɗakin Minal ya kainAmira ya kwantar, ya kasa motsawa ko nan da can, ya zuba mata ido kamar wata sabuwar halitta daban. Ihsan kuwa ta cika ta batse, ganin yadda hankalin kowa ya koma kan Amira, ta kwashi jakarta tai tafiyarta daga gidan. Imran yana nan zaune kusa da Amira, ta motsa a hankali tana, ya zuba mata ido a hankali tayi miƙa tare da yin salati. Imran ya matso kusa da ita yace "My Amran ya jikin?" Ta kalli Imran tai murmushi tace "bacci nayi ne haka me nauyi?" Imran yace "eh kusan haka" "Ina su Antyn ko sun tafi sun barni?" Imran yace "kin san lokacin da kuka zo ne?" Tace "Na sani mana" "Amira baki missing ɗina ba ko?" Ya ɗan faɗa a shagwaɓe. 'ni na isa ince bana kewar ka, tsoro nake ji kar in taɓaka inji wani abun" Janyo ta yai jikinsa yace "ba abun da za kiji ai kin warke" "Wallahi tsoro nake ji" ta faɗa kamar za tai kuka. Nan Imran ya warware mata abunda yaf faru gaba ɗaya. Sosai ta fashe da kuka tana tunanin laifin me tayi wa wani haka, da za'ai mata wannan abun. Imran ya rungumeta yana ƙoƙarin kawar mata da damuwar da ta tsinci kanta a ciki. Ya kalli cikinta yace "Allah sarki yarona ya sha wuya, Allah yasa karki haifeshi da lotsatsen kai, saboda yadda ki ka dinga faɗuwa da cikin nan, Alhamdilillah yana nan be zube ba" Tai murmushi tare da shafa cikin nata. "Imran yaya ta farka ne?" Suka ji muryar Anty na nufo ɗakin, a sukwane Imran ya sakko daga kan gadon, ya gyara yace "eh ta farka" Kallo ɗaya anty tai musu ta maze tace "Alhamdilillah, Amira ya kike jin jikin naki yanzu?" "Alhamdilillah Anty" "Kin warke dai ko yanzu ba ƙadangarun?" Sunkuyar da kai Amira tai tana murmushi. Anty tace "Abba ya tura ai muku saukar Alqur'ani a gida, ki fito jama'a su ganki aji daɗi, kin samu sauƙi". Imran yace "Anty amma zamu iya tafiya gida ai ko?" "A'a seta ƙara murmurewa" A marairaice Imran yace "Anty, ina cikin damuwa sosai, sedai na barwa Allah komai amma dan Allah ki sa baki a bani Amira mu koma gida yau tunda taji sauƙi Please" "Kai amma dai ba haka naso ba gaskiya, naso ka bari muga improvement ɗin da za'a samu, amma ban san dalilinka ba, zanwa Iyayen naka Magana, daga nan kawai ku tafi" Imran yace nagode sosai Anty, Allah ya biya ki da aljanna. Ammi kamar taiwa Imran dukan tsiya haka take ji, saboda wannan rawar kan da yake akan  Amira. Kamar yadda ya buƙata, da magariba ya ɗau Amira suka tafi gida tare, dan ba kunya ya nuna yana buƙatar matarsa a tare da shi. Da suka je gidan ma, nan nan ya cigaba da yi da Amira, tamkar mata ɗaya gareshi, ko da wasan wasa be kalli sashin da Ihsan take ba. Amira ta fuskanci ko zancen Ihsan baya son ji. Bata dame shi ba itama, ta shiga hidima da mijinta, Imran kuma fafur ya hanata aikin komai, shima ya shiga lallaɓata. Duk da shima yana fama da kansa, ita ma warkewar ta kenan, amma tabbas sunyi missing juna Sosai da sosai. Tun Amira na tsoron kar wata matsalar ta sake faruwa, amma taga ba abunda yafaru, tun tana fargaba harta haƙura ta saki jikinta da shi. Imran ya dage akan kula da Amira, da Addu'oin da aka bata da sauransu, da kansa yake kaita Asibiti gurin awon ciki. Se dai tunda Amira ta koma gidan kuma take munanan mafarkai da Yadikko, ta ja bakinta tai shiru ba ta gayawa kowa ba. Tuni ta gyara wayarta, ta shiga waya da su Anty Fa'iza, da sauran abokan arziki, a ƙasa da sati guda tai ras kamar ba ita ta sha wannan wahalar ta watanni ba. Imran na zaune a falo, yana bawa Amira Abinci a baki tana ta zuba taɓararta. Ihsan ta faɗo falon kamar korarriya, Imran ko ɗaga kai be ba balle ya kalleta. Ihsan tace "wallahi Imran Allah ya isa tasakani na da kai, mugu Azzalumi kawai, abunda ka ke min se Allah ya saka min, kuma insha Allah se alhakina ya kuma kama ku, ba iya aljanu se tayi hauka tuburan ta bi bola". Amira tace "da ikon Allah ba zanyi hauka ba Ihsan, kema kuma ba zaki ba" Imran yace "Ihsan ni kike cewa Allah ya isa ko?" "Eh na faɗa, Allah ya isa azzalumi mara adalci" "Ni ban hukunta ki saboda naki halin ba, ni zaki zo kaina ki gayawa wannan miyagun maganganu haka ko? Lallai nayi ganganci na kuma godewa Allah da ya sa ban zamo daga masu butulci ga iyaye ba, Mahaifina ya zaɓa min mata ina hangen tasowar Wuta a Maƙera katsam se ga WUTA A MASAƘA, kallonki kawai nake Ihsan, na miki talala ne, akwai Ranar da dubun ki za ta cika" Be tsaya saurarata ba ya tashi ya bar falon, Amira tabi bayansa da sauri, tana ganin rashin kyautawar abunda Imran yayi. Sedai tana shiga bedroom ɗin taci karo da wayarta tana ringing. Sunan Sisto ne akam wayar, ta ɗaga wayar ta kara a kunnenta, "Amira Yadikko fa babu lafiya, ita da Amina, an kasa gane kan abunda yake damun su, Yadikko na ta kiran sunanki" "Innalillahi wa innalillahi raji'un" shine abunda Amira ta faɗa ta fashe da kuka. Imran yace "ke lafiyarki kuwa?" "Yadikko ce babu lafiya, gobe in Allah ya kaimu Kano zanje" "Kano kuma, ga tsohon cikin zaki tafi Kano?" "To kana ji Yadikko ba lafiya, idan kuma ta mutu fa ban ganta ba?" Shi mamaki ne ma ya isheshi, yanzu dui da tarin abunda Yadikko tai mata, amma tana kuka saboda Yadikko ba lafiya, sosai ta birkice da koke koke. Imran yace "kwantar da hankalinki, naji da kaina ma zan kaiki, ai kinyi ƙoƙari tunda aka kawo ki Garin nan baki je gida ba" Ko bacci bata iyayi ba, da ƙyar ta iya haƙuri zuwa wayewar gari. Wajen ƙarfe goma, suka nufi hanyar Kano, Imran ya sai kayayyakin da za su je dubiyar da su, suna tafe tana kuka Imran yana kwantar mata da hankali. Se azahar suka isa Kano, suka tarar da mutane sosai a gidan su Amira, da sauri Amira ta shiga gidan, ta shiga ɗakin Yadikko, tana zuwa ta tarar da Yadikko a kwance, duk fuskarta ta kumbura suntum tayi baƙi, duk gashinta ya kaɗe ta zama kamar wata horror. Ga su Baba da Kawu duk a zazzaune suna share hawaye. Amira tace "Yadikko meya sameki haka?" Yadikko ta fashe da kuka tace "Amira dan Allah ki yafemin" Amira tace "Ni ba abunda ki kaimin Yadikko, meke damunki ne?" "Amira tun tasowarki nake cutar da rayuwarki, na kasance me biye biyen malamai, tun lokacin zamana da kakarki, bana ƙsuanarta sam, malamai suka gayamin idan kin girma zaki zama wata, shine hankalina ya ƙi kwanciya, na sa aka haɗaki da aljani, dan ki lalace amma abu ya ƙi yiwuwa, shine na dinga haɗawa da makirci ina ce miki karuwa, Auren nan da ki kai a raina yake, jikokina naso mijinki ya aura ba ke ba, da naje gidanki naga daular ki ke ciki, abun ya sake ƙuleni, shine naje nasa a kai miki Asiri da ƙadangare, gashi yanzu abun ya dawo kaina ni da Amina, tana can an kulleta tana hauka tuburan, dan Allah ki yafemin Amira!!! Domin gyar, sharhi ko shawara Ayshercool 07063065680. [2/28, 6:24 PM] Ayshercool: 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 WUTA A MASAƘA PERFECT WRITERS ASSOCIATION (WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS) https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P. W. A *Story and written by* AISHA ADAM (AYSHERCOOL) The experience writer of *ABDUL JALAL* * WATA KISSAR.... (SAI MATA) *BAƘIN TABO (Labarin gasa) *AƘIDATA (Paid Book) * WUTA A MASAƘA https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in ❌❌❌ Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba. *_Assalamu alaikum warahmatullah, ina miƙa saƙon ta'aziyya ga ɗaukacin dangi na bisa ga rashi da mukayi na Kakana, ina fatan Ubangiji Allah ya jikansa da rahama, ya gafarta masa. Ina miƙa saƙon godiya ta ga wanda suka kirani a waya, da wanda suka turamin saƙonnin ta'aziyya, na gani Nagode sosai Ubangiji Allah ya bar zumunci ya bada lada, Nagode sosai_*                            53-54 Rawa jikin Amira ya fara yi, ta matsa gefe daga kusa da Yadikko tana bin ta da ido kamar ta ga wata aba daban. Baba yace "dan Allah Amira kiyi haƙuri, ki yafewa mahaifiyata, tabbas nasan mun biye mata gurin muzgunawa rayuwarki da tsangwamar ki, wanda haka kakarki ta fuskanta daga gare mu zuwa mahaifinki da ke kanki, amma ban zaci Yadikko zata iya yi miki Aisiri haka ba, amma dan girman Allah ki yafewa Yadikko Amira" Amira kam kasa magana tayi, se fashewa da wani irin kuka na tausayin kanta, Yadikko ta cutar da ita cuta me munin gaske, ba dan Allah ya temake ta ba da yanzu tana can tana hauka. Imran da yake tsaye a bakin ƙofa ya ji komai, ya tako cikin ɗakin ya kalli Yadikko yace "da yawa abun da mu bayi ke mantawa da shi shine, ita duniyar ba matabbata bace ba, ita wadda ki kai kishin da ita yau tana ina? Shi wanda ki kai kishin akansa yana ina? Shi mahaifin Amiran shina da kika azabtar yana ina? Tunaninki ke kiyi gadin Duniyar kenan? Meye a cikin duniyar gaba ɗayanta, meye laifin da Amira tai miki a rayuwa? Ba ita ta tsarawa kanta irin ratuwar da za tai ba, Allah ne ya tsara mata dan me zaki ce se an canza? Ke da Allah dan ƙarshen cutarwa kin mata, tunda kika so haukata ta, kuma ko da Amira ta rasa hankalinta ba zan taɓa yadda in auri jikokokin ki ba, saboda na gane duk abunda kike faɗa akanta sharri ne kawai da makirci Amira

Chapter 29 of 31