Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels [12/30/2021, 8:13 PM] Ayshercool: .🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 WUTA A MASAƘA Page 1 PERFECT WRITERS ASSOCIATION (WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS) https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P. W. A *Story and written by* _*AISHA HUMAIRA (Daddy's girl)*_ The experience writer of *ABDUL JALAL* * WATA KISSAR.... (SAI MATA) *BAƘIN TABO (Labarin gasa) *AƘIDATA (Paid Book) * Anda no WITA A MASAƘA SADAUKARWA GA ƘUNGIYAR PERFECT WRITERS ASSOCIATION, DOMIN TAYA MURNAR CIKA SHEKARU BIYU DA KAFUWA jinjina ta musamman ga Swt Sisyna (Nanatou) Allah ya bar ƙauna. Me gayya me aiki shugaba a bar koyi Safna Aliyu Jawabi. Sa'adatu Abdullahi Madubi (My red) Anty Asmy Jafar Mummyna Nafisa Ummu ɗahira Da dukkan membobin ƙungiyar perfect writer's association Godiya ta musamman ga, iyayena ƙawayena 'yan uwa da abokan arziki, tare da masoyana a duk inda kuke a faɗin duniya. Alhamdilillah, ina miƙa Godiya ta ga Ubangiji maɗaukakin sarki, yadda na fara a sa'a Allah yasa in gama a sa'a. https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in Domin gyara, sharhi ko shawara 07063065680              _ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH, GASHI YA DIRA DA ZAFINSA, GAJEREN LABARINE ME TARIN ILIMANTARWA DA NISHAƊANTARWA KAFIN ZUWAN LITTAFIN RUƊUN ƘURUCIYA, COMMENTS ƊINKU KAWAI NAKE BUƘATA, BAZAN DINGA POSTING KULLUM BA, SANNAN BABU LALLAI IK DINGA DOGON PAGE, SANNAN DAN ALLAH BANDA BIYONI PC ANA DAGA FARKO, ZANYI IYA ƘOƘARINA INYI SHARING GROUPS, KUMA KU DINGA TAYANI SHARE PLEASE, COMMENTS ƊINKU KAWAI NAKE BUƘATA, GA WANDA BASU KARANTA LITTAFIN AƘIDATA BA, KARKU BARI A BAKU LABARI, KUZO IN BAKU PART1 KYAUTA KU SAI 2&3 AKAN FARASHI ME SAUƘI, TAKU HAR KULLUM AYSHERCOOL_ BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM Da misalin ƙarfe goma na dare, Gari yayi shiru, wasu daga cikin al'umma sun adana kawunansu a cikin gidajensu, domin hutawa rayukansu hidindimun da akayi da Rana. Sedai a ɓangare guda kuma sautin kiɗane ke tashi a wani ƙaton ɗakin taro, mutane nata shiga da fita kamar Rana, se kaiwa ake ana komowa da Abinci da abin sha kala kala, da gani base ka tambaya ba kasan bikine ake na masu hannu da shuni, duba da haɗuwa da tsaruwar ɗakin taron, da kuma kalar mutanen dake zarya a gurin, da uwa uba danƙara danƙaran motocin dake fake a harabar gurin taron. Ango da amarya na kan high table suna kallon wanda suka halarci bikin nasu, Yayin da ƙawayen amarya da abokan ango, dangi 'yan uwa da abikan arziki keta cashewa a filin rawa, anata bajinta gurin zuba musu kuɗi, dj se ƙara zigasu yake suna ɓarin kuɗi yayin da matan keta cashewa. MC ne ya fara magana ta speaker yace "Masha Allah, gaskiya na yadda wannan bikine na masu arziki, madalla ƙawayen amarya da abokan ango ina godiya da wannan bajinta da ku ka nuna, da kuma kara da ku ka yiwa Amarya da ango, sedai ana tsaka da wannan shagali na samu sanarwar, isowar wasu hamshaƙan jiga jigan baƙi da suka amsa gayyata domin tayamu nishaɗi a wannan biki na 'ya'yan gata, wannan baƙin ba kowanne bane face DJ Sultan, tare da 'yan tawagarsa na rawa, ciki hadda wannan tauraruwar taku, wadda ludayinta ke kan dawo, tauraruwarta ke haskawa a cikin manyan yara da suka yadda da kansu wajen iya cashewa, wato gimbiya Amira, nasani ga dukkan wanda suka saba zuwa guraren taron biki, birthday da makamantan su, da duk wanda yasan dj Sultan da tawagarsu nasan sun san wannan gimbiya, kai ga wanda bema santa ba yau ze santa, zatazo ta baje mana baiwarta ta nishaɗantar damu, ina fatan kuma zaku nuna mana farincikinku ta hanyar nuna bajintarku, DJ idan ka shirya, Sultan da jama'arka muna buƙatar ganinku akan stage" Wata waƙa aka saka me sanyi, wasu mazane suka dinga fitowa, suna sanye da baƙaƙen wanduna da fararen riguna, bayanta an rubuta Dj Sultan, sekuma sunayen su a ƙasa, su huɗu haka suka zo suka jeru a tsakiyar filin, suka sunkuyar da kai, kamar masu jiran umarnin wani, sumarsu duk ta sha dying, kowanne da kalar askinsa, wanine ya kuma shigowa filin shima, sanye da shiga irin tasu, ga uwar suma akansa se ƙyalli take ya tsaya a cikinsu suka zama su Biyar. Mutane sun zuba ido  suna jiran ganin gimbiya Amira, kowa ya zuba ido wasu tyni sun zaro wayoyi zasu ɗauka, amma aka shafe wasu mintuna bata bayyana ba, se jan rai da ake yi, har wasu suka fara ƙosawa. lokaci ɗaya aka canza waƙa, aka saka wani kiɗa me sauti da ɗaukar hankali, Ta wata ƙofa ta fito, sanye da crazy jeans, da baƙar riga, ta ɗaure kanta da siririn ɗan kwali ta zubo kitson gashin doki da tayihar ɗuwawunta, ƙafarta sanye cikin wani uban takalmi kamar na sojoji, tana da matsakaicin tsayi, idanunta kamar na Japanese, tana da dogon hanci, sedai ba fara ce tas ba, tana da shape ɗin jiki me kyau, dan kayan sun zauna a jikinta sun kamata tsam tsam a jikinta, kana ganin duk wani shape na jikinta, kallo ɗaya zaka yi mata kaga yarinya ce ɗanya, dan dudu ba zatafi shekaru sha shida zuwa sha bakwai ba, amma tana da jiki me kyau da ɗaukar hankali. Yanayin tafiyar da take, yana tafiya daidai da sautin kiɗan dake tashi, shewa mutanen hall ɗin suka shiga yi, suna tafa mata dan yadda take tafiyar cike da ɗaukar hankali da burgewa, tsakiyar mazan nan taje ta tsaya, tana tsayuwa suka ɗago kansu daga sunkuyarwar da sukayi. Wani irin kiɗa aka saki, aikuwa suka fara rawa a tare, sedai yadda Amiran take rawa kamar ba jikin ɗan Adam ba, Kamar me jikin roba, tafi mazan nan iya sarrafa jikinta cikin ƙwarewa da jan hankali, duk inda ta karya jikinta kota lanƙwasa haka mazan nan keyi, duk wani tsalle da juyi haka itama ke yinsa, attach ɗin kanta na bajewa. Nan da nan hall ya ɗau shewa, masu video nayi Masu hotuna nayi, nan aka shiga ɓarin kuɗi akan Amira. Sunyi rawa kala kala Babu alamar Amira ta gaji da rawar nan, suka nishaɗantar da mutane sosai, agogon hannunta ta kalla, ta silale daga kan stage ɗin, se nemanta akayi aka rasa. "Mungode mungode, DJ Sultan da tawagarsa, jinjinar ban girma ga Gimbiya Amira, munagodiya da wannan gudunmawar da aka bamu, Muna fatan Allah ya maida gimbiyarmu gida lafiya" Amira kuwa zuwa tayi ta canza shiga, ta saka doguwar riga akan kayanta, kamar ba ita tayi wannan uwar rawar ba. Zagayawa tayi inda dj suke zaune, tace  "Sultan, yau mun samu kuɗi sosai, bani 10k zan hau Mota, senaji alert" Sultan ya kalleta Yace "ke Amira, har 10k?" "Eh ko ba zaka bayar bane?" Sultan yace "A'a, ni na isa ince bazan bayar ba? Ni a wa?" "Dalla ka hanzarta ka bani, zan tafi gida inje mu fafata, kuma fitar yau tayi kyau, dan mun samu kuɗi wallahi maga ba dai dai ba zanyi dirar mikiya a Chamber inyi rashin mutunci" Sultan yai murmushi yace "ki huta gimbiya, bame miki ba daidai ba ai girmanki ne, in bake babu mu" ya ƙarasa maganar Tare Da ƙirgo kuɗi ya bata. Yayin da aka cigaba da shagalin biki, ita kuma ta silale tai waje abunta, agogon hannunta ta kalla, sha biyu saura na dare, kuma gurin bikin ma basu da niyyar tashi yanzu. Cikin hanzari ta fita titi, duk babu masu abun hawa, se  ɗaiɗaiku, ji take tamkar ta rufe ido ta ganta a gida, dan ta san yau da drama. Wata uwar ƙatuwar motace ta alfarma tayi parking a gabanta, aka sauke glass ɗin motar. Wani Babban mutum ne a ciki, wanda a ƙalla ze kai shekaru hamsin da biyar, ya kalli Amira Yace "Baby ina zuwane muje in sauke ki?" Ƙare masa kallo tayi, ta ɗauke kanta. "Haba Me kyau, be kamata kiyi ta tsayuwa a gurin nan ga dare ba, ina zakiyi". "Hausawa zanje" ta bashi amsa. "Ok shigo in saukeki Mana" Ba tunanin komai, Amira ta buɗe gaban motar ta shige abunta, wani sanyi da ƙamshin turaren jikinsa sun gauraye cikin motar. Ya fara jan motar a hankali, ya kalleta Yace "Gimbiya Amira, kinci sunan naki gimbiya fa, gaskiya kin nishaɗantar damu sosai, na daɗe banga 'yar baiwa ba kamarki" Ɗauke kai tayi kamar bata san meyake cewa ba, ya ɗan kalleta Yace "magana fa nake Gimbiya" Maimakonsa ta bashi amsa, se tace "Idan kaje zoo road zan sayi abu" "Meye abun?" "In munje ka gani" ta bashi amsa Yaita surutunsa amma taƙi Magana, suna zuwa gurin masu gasa kaji tace "yawwa ɗanyi parking, zan sai kaza" Yace "haba Amira, aiba girmanki bane, bari inje in siyo miki" Bata kuma cewa komai ba, ya fita daga motar, ya ɗan jima sannan ya dawo motar, hannunsa ɗauke da manyan ledoji, ɗaya na kaza ɗaya kuma na abun sha, ya miƙa Mata. Tasa hannu ta karɓe tace tagode. Tai tayi masa kwatance har sukazo bakin wani layi, ta kalleshi tace "Nagode fa a nan zan sauka" "Ahh haba dai, mu ƙarasa inga gidannaki mana" Ta kalleshi tace "gidana kuma? Kaga a nan zan sauka zan ƙarasa" "Amma Yakamata muyi exchanging number, sannan ai Yakamata muyi sallama" Amira tace "Yallaɓai wace sallama kuma?" Ya wani matso daf da ita yana ƙasa da murya Yace "haba Gimbiya, wannan ai ƙwalele ne, duk yadda kikaje kikayi wannan karairayar kice zamu rabu ba sallama haba Baby" Yai maganar yana ƙoƙarin naniƙar Ameera, hannu tasa zata buɗe motar amma taji a rufe, ta juyo a fusace tace "malam ka buɗemin in fita, bana son iskanci fa" "Wane irin bakya son iskanci, nifa bana son wani kame kame, meye na wani damuwa ko ɓoye ɓoye, bayan kin nuna wace ke, kinyi talla na biyo kuma kiƙi siyarwa, kinga in dai kuɗine baki da Matsala, zan kashe miki ko nawa ne" Zaro ido tayi tace "dagaske?". Da sauri ya jinjina kai Yace  "ƙwarai dagakse mana" Kamar abun arziki ta zira hannu a rigarta, ba zato ba tsammani ta zaro wata 'yar ƙaramar wuƙa, se ƙyalli take ta kalleshi tace "Wallahi, idan har baka buɗemin motar nan na fita ba, sena yanka wannan ubsn tumbin naka da wuƙar nan, kuma in toshe duk wata hanya da za'a gane nina yi". Zaro ido yayi Yace 'ke kina mace kike yawo da wuƙa haka, har kike iƙrarin zaki kasheni?" "Saboda irinka nake yawo da ita ai, dan naje nayi talla se akace maka kowane jaki nake sayarwa, ko ana ciniki ta dole ne, na kasa ka taya, nace bazan siyar ba, base ka ƙyaleni ba, ni harƙallata ba kowa nake siyarwa ba seme rabo ina fatan ka gane?". Yadda Amira ke maganar cikin ɓacin rai da zazzaro ido, suka tabbatar da zata iya aikata Abinda tace, cikin hanzari ya cire lock ɗin, ta buɗe motar da sauri, ta ɗauki ledar kazarta ta shige wani layi me duhun gaske. Tana shiga ta cire takalmanta, ta riƙe a hannu ta kasa da gudu tai cikin layin, a bakin ƙofar wani gida tai birki, ta dinga sauke numfashi, seda ta dawo hayyacinta sannan ta shiga gidan cikin sanɗa. Babu kowa a makeken tsakar gidan, dan haka ta ajiye takalmanta ta shiga cikin wani ɗaki ta ajiye jakarta da ledar hannunta ta fito tsakar gidan. Hanyar banɗaki ta nufa, cikin sanɗa amma taji ance  "daga ina kike dan ubanki?". Cak ta tsaya ta juyo a hankali, wani matashine a tsaye yana huci, da zazzare ido. "Nace daga ina kike?" Matashin Ya maimaita tambayar cikin tsawa. "Daga neman na kaina" ta bashi amsa kai tsaye. "Ni kike gayawa neman na kanki kika tafi? Kin tafi yawon karuwancinki shine se yanzu zaki shigo mana gida, kina ta zubar mana da mutunci a idon duniya, to bari kiji in gayamiki daga yau se yau idan kika kuma tafiya yawon iskancinki kikayi dare, to karki shigo mana gida, ko kuma ki tarkata kayan ki ki shiga duniyar gaba ɗaya ki bar mana gida, zefi miki kwanciyar hankali" "Ai wallahi tallahi babu ɗan matar daya isa ya koreni daga gidan nan, dan gidan ubanane, kuma karuwanci sana'ane, wani idan ya kasa nasa kasuwancin ba'a siya, nikuwa Alhamdilillah, idan na kasa har wawa ake, kuma wallahi yanzu na Fara" A harzuƙe yace "ni kike gayawa haka?" "An gaya maka ɗin, haifata kayi da bazan gaya maka ba?" Cikin zafin nama ya kai mata mari, ta goce da sauri, ta ware muryarta a wannan daren ta shiga kurma ihu, ga gari yayi shiru saboda dare amma ta dinga kurma uban ihu. Wani dattijo ne ya zare sakatar wani ɗaki ya fito Yace "idan kanawa ma'aikin Allah Usman ka ƙyale yarinyar nan, karta tara mana jama'a ni wallahi lamarinta tsoro yake bani yanzu" Usman yace "wallahi Baba dan taga ana ƙyaleta ne, duk ta zubarwa da mutane mutunci maimakon tayi iskancin nata a ɓoye amma seta nuna duniya ta sani, shegiya karya" Amira tace  "wallahi niba karya bace, kuma wallahi ka kuma yunƙurin dukana sena maka illa, ko in sa a zanemin kai wallahi, dan yanzu ba da bace" Usman Yace "kana gani ko Baba?" "Ƙyaleta duniya ce, wanda bezo bama jiransa take, rabu da ita abokin yi take nema" Haka suka koma ɗakunansu suka ƙyale Amira. Ta shiga banɗaki ta fito, taga yadda kowa ya rufe ɗaki yana bacci, ta nufi inda ake girki, ta bubbuɗe kwanuka, amma ba'a bar Mata Abinci ba. Ta kalli kwanukan, ta sake kallon yadda kowa ya rufe ƙofa yana bacci, tace 'wallahi tunda aka ƙi ajiye min abinci se kowa ya tashi" Ta ɗakko ƙaton murfin tukunya ta fito tsakar gida, ta saita ƙofar ɗaki ɗaya ta jefi ƙofar da ƙarfi da murfin babbar tukunya, nan take ya bada wani razanannen sauti, wanda ya sanya wanda suke ɗakin kurma ihu, kafin su gama ihun ta sake jefa wani murfin, nan da nan ta tashi da yawa daga ilahirin mazauna gidan, ba iya na cikin gidan ba harda maƙota, suka tashi a firgice. "Amira, baki da hankali? Wane irin dabbanci ne wannan? Meye haka kika yi?" "Ba dole inyi rashin mutunci ba, dan wulaƙanci ace baza'a ajiyemin Abinci ba, sedai ayita sani aiki kamar jaka a gidan nan, wallahi idan ba'ayi wasa ba sena tada balli, a raba gidan nan a bani gadon ubana a ciki, idan yaso in dinga ci da kaina, tunda an maida ni mara galihu a gidan nan" Wata matace ta ɗora hannu a ka tana faɗin "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, wannan wane irin bala'i ne? Wace irin annobace wannan? Shikenan bamu da kwanciyar hankali a gidan nan, saboda wannan sheɗaniyar yarinyar?". Usman Yace "ka gani ko Baba, daka bari ɗazu na jiƙa mata jikinta da duka, da duk haka bata faru ba" Baba yace  "duka kuma na nawa? Wane irin dukane ba'a mata ba, wannan yarinyar bata da rabon shiriya, kamar jaka haka take, wallahi ina ga gurin 'yan Hisba zan kaita bazan iya ba taf" "Kokuma ka tattara ka maida ita gurin wan uwarta ba, tunda yafi mu arziki" Amira tace  "ba gidan uban da zanje in zauna, nan ne gidan su Ubana wallahi ba inda zani, in kun gadama ku Kaini prison, ku zaku tonawa kanku asiri ba ruwan Amira". Abun takaici ta shige ɗakinsu ta rufo ƙofa, harda saka sakata, ta barsu a tsakar gida suna cigaba da masifarsu suka ɗai, ɗaya daga cikin wanda suke kwance a ɗakin ta kalleta tace  "dan Allah karki shigo muma ki tayar mana da hankali, ki buɗe mana ƙofa zafi mukeji" Amira tace "bazan buɗe ba, wallahi idan baki wasa ba, zamu zauna ba bacci yau se Asuba" "Allah ya baki haƙuri" Ɗayar kuwa da take cikin bargo tsaki tayi tace  "wallahi Allah ya isa hanamu baccin da kika yi" "Asiya kika yiwa Allah ya isa bani ba" A fusace ta yaye bargon ta tashi zaune tace "karki kuskura ki sake zagarmin uwa" "To uwatace da bazan zageta ba, an zageta Asiya kikayiwa Allah ya isa, Allah ya ban haƙuri da ake zagin tawa uwar" Zata kuma magana ɗayar tace  "dan girman Allah Sadiya ki ƙyaleta, abokin yi take nema, ƙyaleta da halinta" Sadiya tayi ƙwafa tace  "matsiyaciya kawai" Amira tace  "nice ma Usman, ba sana'a se zaman banza da sa ido da kurin dukan mace" Haka suka ƙyale Amira, dan yanzu kusan ƙarfe biyu da rabi na dare ne, idan suka biyeta baza suyi bacci ba. Ta gyara zamanta, ta ɗakko ledar kazarta ta shiga ci tana korawa da sassanyar madara, suna jin ƙamshi da yadda take tauna ƙashi, amma ba wanda ta bawa. Seda ta kammala, tayi gyatsa sannan ta nemi gurin kwanciya, Allah ya isa kam ta sha ta a gurin mutan gidan harda maƙwabta. Da Asubar fari ta tashi, ta gabatar da sallar Asuba, ta koma cikin bargo tai kwanciyarta. Bayan gari yayi haske mutanen gidan suka dinga fitowa ɗaya bayan ɗaya, kasancewar gidan family house ne, me ɗauke da mutane da dama a ciki, ɓangare ɓangare ne a gidan, amma duk 'yan uwane. Sashin su Amira suka dinga haɗuwa, suna maida yadda akayi na hanasu bacci da Amira tayi daren jiya, fitinar Amira ta fara addabawa mutan gidan nesa ba kusa ba. Suna cikin tattaunawarne wani babban mutum yai sallama shida wannan dattijon na jiya da daddare wato Baba, suna ganinsa suka ce "Yawwa, barka da zuwa dama kai muke jira Baffa" Sadiya tace "Ai wallahi Baba gara da kaje ka taho da Baffan, tunda shi tana jin tsoronsa, haka kurum duk mutuncinmu ya zube a idon mutane saboda Amira, ta addabi kowa bata jin maganar Kowa, ai gara da kazo daren jiya ko rintsawa bamuyi ba, saboda tijararta" Wanda aka kira da Baffa yace "ku barni da ita, ina makirar take?" "Tana ɗaki tana bacci" cewar mahaifiyarsu Sadiya. Baffa yace  "tasomin ita dan ubanta, yau zata yabawa aya zaƙinta" Sadiya ta tafi ɗakinsu da rawar jiki, "Ke Amira ki tashi ana kiranki" Tai maganar tana dukan katifar Amira, maimakon ta tashi sema taja tsaki, ta sake shigewa bargonta. "Ke Amira kirankifa ake yi" "Ke dalla malama ƙyaleni, in kinga na amsa wani kira tona Allah ne, babu 'yar ƙatuwa ko ƙaton dazesa in fita tsakar gida Yanzu" Sadiya tace "jar uba, Baffa salahun ne ɗan ƙatuwa"? Zumbur Amira ta tashi zaune, kafin tayi magana Baffa Salahu ya shiga bubbuga ƙofar ɗakin yana cewa  "zaki fitone kizo kiran da nake miki ko sena shigo?" Cikin zumɓura baki Amira ta sakko daga kan katifarta, ta ɗau wayarta ta saka a aljihu, ta ɗau kuɗaɗen ta suma ta saka a aljihun wandon dake jikinta  ta fito, maimakon ta nemi hijjabi ta suturta jikinta, amma ta fito a haka, gajeren wando ne a jikinta, da wata matsatsiyar vest, ta baje kalbar attach dake kanta. Baffa Salahu yace "Ke baki da hankali baki da ɗa'a ko? Shine kika fito a haka saboda baki da Kunya?" "To waini ya zanyi? Idan na tsaya saka hijjabi masifa zakayi min, yanzuma kuma ban tsira ba". Baffa yace "nine nake masifar ko? Amira ba kiwa kanki adalci ba wannan mumunnar rayuwar da kika ɗauka, kina 'ya mace da iliminki da komai amma kika zaɓi yawon ta zubar, duk danginmu bamu taɓa samun wanda yai abunda kika aikata ba, abun kunya kamar wanda kike ba'a taɓa samu ba wallahi". Amira tace "Baffa wane irin abun kunya kuma? Nifa ban taɓa cikin shege ba" "Ni kike gayawa baki taɓa cikin shege ba? To je kiyo cikin shegen karki fasa dan ubanki, idan akace a rayuwa 'yar Habiba zata yi karuwanci, za'a ƙaryata hakan amma segashi kina zubar mana da kima da martaba a idon duniya, daga uwarki har ubanki babu mutumin banza kaiconki Amira, kaico". Wani irin abune ya tokarewa Amira a zuciyarta, taji kamar ta fasa ihu, amma tai shiru ta sunkuyar da kai, Baffa nayi Baba nayi, su Yaya Usman ma suka saka baki, aka dinga mata faɗa da tashin hankali a ka, gashi Amira ta tsani faɗa a rayuwarta. Seda suka yi me isarsu, Baffa yace  "duk ranar data kuma fita gantali tayi dare, ko Usman ko Zailani a cikin mazan gidan nan, a samu wani yai mata dukan tsiya, sannan duk randa ra kuma yiwa wani rashin kunyar ko iyashege azo a gayamin, se naci mutuncinki Ja'ira mara kamun kai, kuma daga yau ko ƙofar gida kar a sake bari ta fita, wuce kije ki tattare wannan kwanukan ki wanke, ki ɗora abincin safe, dan matan gidan nan ba bayinki bane suda yaransu, a wanke a ɗora a dafa a baki kici, kuma ki cika musu ciki da iskanci ba" Amira ta kalli uban wanke wanken dake zube a gurin, da uwar tukunyar da ake ɗorawa a gidan dan girka Abinci, ta kalli furfurar dake kai da gemun Baffa Salahu, tabbas ba dan wannan furfurar ba da seta yanka masa rashin mutunci. Amma lokaci ɗaya ta sauya kamar ba ita ba, cikin ladabi tace  "zanyi insha Allah, zan wanke kwanukan sannan zan dama kunun karyawar, Allah ya baku haƙuri" Kamar gaske ta nufi inda murhu yake, masu zagi na cigaba da zaginta, suna faɗar albarkacin bakinsu, taje ta iza wuta ta miƙe tai hanyar banɗaki, tana zuwa ta suri hijjabi a jikin katanga, tai waje da gudu.... Ayshercool 07063065680 [1/2, 11:06 AM] Ayshercool: 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥                 WUTA A MASAƘA                                         Page 2 PERFECT WRITERS ASSOCIATION (WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS) https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P. W. A *Story and written by* _*AISHA HUMAIRA (Daddy's girl)*_ The experience writer of *ABDUL JALAL* * WATA KISSAR.... (SAI MATA) *BAƘIN TABO (Labarin gasa) *AƘIDATA (Paid Book) * Anda no WITA A MASAƘA SADAUKARWA GA ƘUNGIYAR PERFECT WRITERS ASSOCIATION, DOMIN TAYA MURNAR CIKA SHEKARU BIYU DA KAFUWA https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in                          Page2 Amira na jin yadda aka biyo ta ana ƙwala

Chapter 1 of 31