Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
bar ƙauna, ina jin daɗin sharhin da kuke akan labarin_*                             22_23 A fusace Amira ta sake cewa "inji ubanwa? Ke waye ya gaya miki wannan shirmen dan Allah bana son wasan banza, ni mu tafi kawai" Haɗe rai Fa'iza tayi tace "duk wasan da muke dake na taɓa miki irin wannan ne? Ni karɓi wayoyinki da sauran kayanki, suna waje suna jirana zamu tafi" "Can ta matse musu su da wanda suka ɗaurawa Auren ba dai Amira b, kuma wallahi bazan kwana a garin nan ba" Kan Fa'iza tai magana tuni Amira tai waje abunta, Anty dake Falo ta tashi da sauri tace "A'a, Amira ya haka? Ina zakije kuma?" Amira tace "gida zamu koma, an gama biki ga mota can a waje zamu tafi gida" Anty tace "wani gida kuma Amira? Ai babu ke ba komawa gida baki san an ɗaura miki Aure bane? Kiyi haƙuri ki koma ki kwanta kin san baki da lafiya" Aikuwa Amira ta ɗora hannu a ka tace "Na shiga uku ni Amira, wai dama dagaske An ɗauramin Aure da wannan Mugun? Meyasa za'amin haka? Dan anga ni marainiya ce shine za'a Auran wanda ya kusa kasheni? Wato idan ya kasheni ba wanda yake da Asara? Meyasa za'amin Auren dole? Ni wallahi gida zan tafi, gara zaman gidanmu da zama da wannan Mugun mara imani, wallahi ni gida zan koma" Ta rirriƙe Fa'iza tana rusa kuka, tuni hawaye ya wanke mata fuska, Alhaji Hashim ya sakko daga kan benensa, jin kukan Amira da yayi. Yana zuwa ya tarar Amira ta riƙe Fa'iza tana kuka, itama Fa'iza seta saka Kuka ta rungume Amira tace "Amira kiyi haƙuri, ki rungumi ƙaddara kinji, dan Allah karki kuma aikata wani abun daze rusa rayuwarki, ina miki fatan Alkhairi da fatan Imran ya zame miki Mijin marainiya" "Wane mijin marainiya Anty Fa'iza? Kalli jikina fa kalli dukan da yaimin, babu tausayi ba imani, ni wallahi bana sonsa, meyasa za'amin Auren dole dan babana ya mutu, Fa'iza kinfi kowa sanin wahalar dana sha, yanzu na cancanci sake faɗawa wata wahalar? Meyasa kuka bari akamin wannan Auren? Meyasa?" Kasa magana Anty Fa'iza tayi, ita kanta Anty jikinta sanyi yayi dan Amira ta bata tausayi sosai. Alhaji Hashim ya ƙarason inda suke, yace "Amira cikata su tafi kar suyi yamma a hanya" "Dan Allah ku barni in koma gidanmu, wallahi niba matar Aure bace bana son wannan Auren, karku rabani da 'yan uwana alhalin bani da kowa a nan se Allah, wanda kuka saka ya Aureni baya ƙaunar ko ganina, ku dubi maraicina ku rabu dani dan Allah" Alhaji Hashim ya haɗe rai sosai yace "ki cikata su tafi nace" Amira ta saki Mayafin Fa'iza, ta durƙushe a gurin ta sake fashewa da kuka, Anty Fa'iza tanayi tana waigowa harta kai ƙofar falon. "Dan Allah Anty Fa'iza karki tafi ki barni a nan, dan ƙaunarki da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam" Da sauri Fa'iza ta bar falon tai waje tana goge hawaye. Tana zuwa mota su Amina suka shiga rattaɓo mata tambayoyi, 'Ina Amiran? Mutuwa tayi kike wannan kukan haka?" Fa'iza ta goge hawayenta tace "mu kaɗai zamu tafi ba Amira" Sadiya tace "Saboda ne kuma?" "An ɗaura mata Aure" Umma tace "Aure kuma? Kamar yaya kenan?" "Kiran da akayi min ɗazu kenan, mata biyu aka Aurawa Imran, da ita da waccan Yarinyar". Amina tace "ita wa wai?" "Ita Amira mana" ta basu amsa Suka haɗa baki sukace "Innalillahi wa innalillahi raji'un" "Ya naji kuna salati haka?" Amina tace "dan Allah wai dagaske kike koda wasa?" "Y za ai in muku ƙarya, da ƙarya nake meya hana mu tafi tare da ita, ko baku ji ɗazu ana zancen mata biyu aka aura masa ba" Sojan da yake jansu a motar yace "gaskiya ta gaya muku, Oga mata biyu ya aura Amira da Ihsan haka aka sanar a gurin ɗaurin Aure" Umma tace "Amma ya za'ayi a aurar da ita ba tare da izinin dangin ubanta ba?" Fa'iza tace "in dai Aure ya cika sharuɗan da suka dace bisa koyarwar addini, babu wani batun amincewar wani" Gaba ɗaya jikinsu yayi sanyi, dan ba ƙaramin shanmatarsu akayi da wannan lamarin ba. Amira kuwa take jiki ya sake rikicewa, wani zazzafan zazzaɓi ya sake rufeta, aka maida ita ɗakin da take aka cigaba da samata ruwa da allurai. Haka aka ƙarasa wunin bikin nan duk ba daɗi, danshi kansa Angon bashi da cikakkiyar lafiya dan da ciwon kai ya wuni, Ihsan ma na can nata fama da nata darun, tace ba ita ba zaman Gidan Imran, yaje yai harkarsa tai tata, yaje ya zauna da waccan matar tasa, Yayin da Gimbiya Amira ma haka ta wuni cikin yanayin kuka da rashin lafiya. Da magariba 'yan ɗaukar Amarya sukaje, amma Ihsan fafur taƙi fitowa, rarrashin duniya amma tace ba ita ba Imran, ƙarewa taje ta ƙule a gado taƙi tashi. Aka kira Yayan Babanta aka sanar masa, babu jimawa se gashi yazo gidan, har ɗakin da take ya shiga cikin tsawa yace "ke bana son sakarci da iya shege, mu zaki kunyata, wallahi kin bani mamaki Ihsan, ina tarin ilimin naki, na Addini dana zamani, amma ki dinga wannan shashancin haka, tashi kije kiyi wanka kisa kayanki ina falo ina jiranki, da kaina zan kaiki ɗakin miji" Kasancewar Ihsan na tsoronsa sosai, haka ta tashi taje tai wanka tana kuka tana komai, ta sa kaya aka fesheta da turare, Mummy ta dinga cewa "kiyi haƙuri Ihsan, ki kwantar da hankalinki, zamu san abunyi Insha Allah, ki tafi kina Addu'a" Haka aka saka Ihsan a mota, Wan babanta ya tafi kaita ɗakin miji. Gidan Da Abba ta bawa Imran ya haɗu sosai, anyiwa Ihsan kaya na gani na faɗa masu kyau da ƙayatarwa, ɓangaren Amira ne a rufe ba'a sa komai ba a ciki tukuna. Seda Ya raka Ihsan har cikin bedroom ɗinta sannan ya shiga yi nata Nasiha "Ihsan nasan babu matar da takeson kishiya, amma ki tuna ƙarin Aure ga namiji umarnin Ubangiji ne idan har ze Adalci, karki ja da hukuncin Allah, ki zauna da mijinki da zuciya ɗaya, kiyi masa biyayya ki zauna lafiya da abokiyar zamanki, batun waiwani karuwace ko menene ba ruwanki da surutan mutane, seda aka bincika lafiyar ta kafin ya Aureta, kuma ita ba yanzu zaki tare bama, se nan gaba, dan haka kiyi haƙuri, ki zauna lafiya a gidanki Ubangiji Allah ya haɗa kanku ya baku zaman lafiya" Sam Ihsan harya gama surutansa ya gama bata san meyake cewa ba, hankalinta na can wani gurin tana tunane tunane, dan sam maganganun sa basu shigeta ba, bama sta saurareshi ba balle maganganun su shigeta. Imran kuwa kamar mara laka, haka yayi wanka ya sa kaya, ya shiga cikin gidansu, mata na ta rangaɗa masa guɗa ana Soja angon mata biyu. Part ɗin Abba ya tafi ya shiga ya tarar da Abba na kallon labarai, yana ganin Imran ya saki murmushi yace "Ina gwanin wani ga nawa, Angon Amira Angon Ihsan" Imran ya sunkunyar da kai cikin ladabi ya durƙusa a gaban Abba yace "Abba zan tafi, sannan ina amfani da wannan dama gurin godiya ga Ubangiji da ya nunamin wannan rana, da kuma godiya gareku iyayena bisa jajircewarku, da goyon bayanku a gareni har kawo wannan lokaci, Allah yasaka muku da mafificin Alkhairi, nasan bani da abun da zan biyaku da shi face Addu'a, sannan ina neman Afuwarku idan akwai laifi dana aikata ina sane ko cikin rashin sani, ina neman ku yafemin" Seda Abba yaji ƙwalla ta taru a idonsa, dan yana matukar son Imran. "Imran na yafe maka, kuma ka cancanci yabo da jinjinawa, haƙiƙa kamin biyayya kuma ina fatan biyayyar da kayimin yayi sanadiyyar shigarka aljanna, sannan ina me maka wasiyya da ka kula da iyalinka kaji tsoron Allah a gurin yi musu adalci, saboda gaba ɗaya suna da haƙƙi akanka, karka fifita wata akan wata, nasan Ihsan kake so ba Amira ba, amma ina fatan ka dinga ɓoye hakan a gaban Amira, gudun kar taji Babu daɗi, tashi kaje Allah yayi maka albarka" "Ameen Abba nagode" Imran ya miƙe jiki a sanyaye ya nufi cikin gida gurin Ammi, sedai yana tunakarar cikin gidan gabansa na cigaba da faɗuwa. Ya sameta a falo da mutane, tana ganinsa ta haɗe rai sosai, mutane nata masa Addu'a ta fatan Alkhairi wasu na masa nasiha akan Adalci. Ammi tace "shiga bedroom ka jirani" Imran ya tashi ya shiga bedroom ɗin Ammi ya zauna yana jiranta, cam se gata ta shigo ta maida ƙofa ta rufe ta kalleshi tace "Sannu ko" Ya sunkunyar da Kai ƙasa, "Nace Sannu, ka haɗa kai da ubanka kun munafurceni, ya maka Aure sannu ɗan gata" Imran yace "wallahi Ammi biyayya naiwa Abba na Auri Yarinyar nan, ba zan iya ce masa A'a bane, amma wallahi ba laifi na bane". "Dallacan rufemin baki, ni zakaiwa ƙarya? To ka buɗe kunnenka da kyau ka saurareni, Ihsan itace matarka da na aminta da ita, dan haka ba kai ba Amira! Karka kuskura ka yadda wani abu ya shiga tsakaninka da ita, ban da Abun Mahaifinka mezakayi da Yarinyar titi wadda ta gama raba jikinta ga maza daban daban ka auri sauran titi, Mazinaciya! Haka nan Imran yaji kalmar Mazinaciya ta daki ƙirjinsa da ƙarfin gaske, dan seda yai ajiyar zuciya saboda hakan. "Kasan abunda kake ciki tun wuri, a waje ba'a iya controlling ɗinta ba, dan ka Aureta ne zata dena gantalin mussaman kai da ba mazauni ba, da ka bar gari itama ta kama gabanta azo ana haifar yara ana gwamutsa maka wanda suke naka da ba naka ba, karka kuskura ka yadda wani abu ya faru tskaninka da ita, zuwa randa zata gaji ta tattar tayi gaba, bana son yin fito na fito da Mahaifinka akan magnar nan saboda naga yadda ya ɗaukaki Maganar, idan na matsa zamuyi Babu daɗi dashi, naji ana cewa tana gidan Alhaji Hashim, se bayan wani lokaci zata tare, kota tare ba ruwanka da ita kaji abunda na gayamaka?". Imran yace "Naji Ammi, kuma zan kiyaye insha Allah' "Tashi ka ban Guri maza" Imran ya tashi ya fita, maganganun Abba na masa yawo a ka, gana Ammi gefe kuma ga ra'ayin zuciyarsa dan yafi karkata ga maganganun Ammi, dan baya jin ze iyayin wata mu'amala da Amira saboda kallon ƙazanta yake mata. Haka ya fito jikins a sanyaye, suka shiga motoci zuwa gidan Imran, a hanya su Khalifa suka sai kaji da youghurt suka raka Imran da su gidansa. Koda sukaje duk an watse se Ihsan da wasu Cosuin sister's ɗinta guda biyu, nan abokan ango suka dinga zolayarsu, Ihsan dai ta takure ta duƙunƙune a gado, taƙi ko ɗago fuskarta ta kallesu, haka suka gaji suka miƙe zasu tafi. "To Amarya zamuce ko uwargida?" Cewar wani abokin Imran. Khalid yace "Amaryar dai, Uwargidan bata tare ba tukuna, kasan na waccan aka fara ɗaurawa" "What so ever dai, tunda wannan ce ta fara zuwa a gurinmu itace uwargidan, to Ango Allah ya sanya Alkhairi, semun zo rako Amarya kuma" Sukai musu sallama suka tafi, Ihsan a ranta tace "ta tabbata dai Amira aka fara ɗaurawa Aure sannan ita" Bayan Imran ya dawo daga rakasu, ya shigo bedroom ɗin Ihsan, ya daɗe a tsaye yana kallonta, sannan ya ƙarasa ya hau kan gadon ya zauna, ya ɗagota daga duƙunƙunewar da tayi a cikin mayafi. A fusace ta ture hannunsa, taja da baya idanunta sunyi jawur sun kumbura, alamr ta sha kuka bana wasa ba. Jiki a sanyaye Imran yace "Ihsan, nasan kina fushi dani ne, amma haryanzu ko sau ɗaya baki bani dama na miki bayani ba" Cikin dashashshiyar muryarta data sha kuka tace "wani bayani nake buƙata daga gareka, banda wanda na hani a zahiri? Kamin ƙarya ka ɓoyemin abubuwa wannan itace sakamakon Yadda da nai da kai? Kace min yarinya ce ƙarama, kace min babu komai a tsakanin ka da ita, ba yau ba gobe kana hanyar Kano, mekake a Kano sekace min Abba ne ya aikeka, ashe shirin Aurenku ake, har hotonta na nuna maka, na haɗu da ita a Abuja se cemin kai baka santa ba, katsam se Ranar ɗaurin Aure aka gayamin ai mu biyu zaka Aura, Imran duk da kasan yadda nake sonkabda kishinka, amma ka rasa dame zaka sakamin se wannan yimin kishiya da Karuwa, kuma gurin ɗaurin Aure aka fara ɗaura Aurenka da ita sannan nawa, kuma ka ɓoyemin baka gayamin ba, am disappointed on you, kaje kayi rayuwarka inyi tawa, dama 'yar uwaka ce na bar maka ita kaje ku ƙarata" Gaba ɗaya jikin Imran yai sanyi, ya miƙa hannunsa ze rungumota jikinsa ya rarrasheta, amma ta miƙe ta sauka daga kan gadon da sauri, tana kuka hawaye na bin idonta haka ta sakko ta na kallonsa. Imran ya dafe kansa, ya rasa mema Yakamata yayi, Gaba ɗaya kansa ya kulle. Ƙarshema ɗaya ɗakin tai tafiyarta ta kulle ƙofa ta kwanta, dan haushin Imran take ji. Su Fa'iza kuwa daf da magariba suka isa Kano, yana sauke su yai salla ya juya. Yadikko ta fara jin sauƙi, dan tana iya tashi ta lallaɓa ta fito tsakar gida da kanta, tana jin sallamarsu Amina ta hau washe baki "Sannunku da zuwa mutanen Kaduna, marabanku lale, ai nayi zaton se gobe zaku dawo, an gama biki yau, ku huta sannan ku taho" Ganin fuskokinsu tayi duk wani iri, ba karsashi, ba fara'a ba komai kamar wanda suka dawo daga jana'iza. "Wai meye haka naga kuna wani haɗe fuska kuna muzurai? Ko wani abun akayi muku? Ko dai akwai matsala ne" Sadiya tace "Yadikko labarin babu daɗin ji ne, shiyasa kika ganmu haka?" 'to ku gayamin abunda ya faru mana, ni da nake saka ran inga kun dawo min da daddaɗan labarin daze sa in taka rawa, Amma kuce min wai mummunan labari" Amina tace "Yadikko Amira" "Meya sami Amiran? Taje gurin bikin ne? Naga nan ta bar gidan nan ta tafi nata gantali" "Ai ranar data bar gidan nan dan munafurci, Alhaji Ali ya turo ɗansa ya ɗauketa zuwa can gidan sa" Cikin ƙosawa Yadikko tace "se akayi yaya kuma? Ba dai kuna nufin a can zata zauna ba?" Umma tace "bari dai in taƙaita miki Maganar nan, sun Aurar da Amira" Wani Mugun haɗe rai Yadikko tai tace "Kamar yaya? Wace irin maganar banza ce wannan, Ban gane sun Aurar da Amira ba, da izinin wa aka aurar da itan? Ke tsaya ma wa aka Aurawa?" Sadiya tace "ɗansa ya aurawa, kusan dai zan iya cemiki bikin Amira mukaje Garin nan, mu kanmu bamu sani ba, Fa'iza kawai aka gayawa" "Ku dalla bana son shirmen banza da hauka" Umma tace "wallahi dagaske ne, anjima ki kira Fa'iza ki tambayeta, wallahi ya aurawa ɗansa Amira, mata biyu ya aura lokaci ɗaya" "Innalillahi wa innalillahi raji'un, amma wannan mutumin nan anyi munafuki tsinannen, dama sintirin da yake gidan nan kenan, abunda suke ƙullawa kenan da baƙin hali da mugun abu, shine be aura masa nutsatstiya ba a cikinku se wannan watsatsiyar Yarinyar, ashe shima watsasten ne ban sani ba, Zailani ya shigo ya kiramin shi a waya, inji dalilin daya sa ze aurar da ita ba tare da izinin mu ba" Amina tace "Yadikko koma fa me zakiyi mutumin nan yafi ƙarfinki, kuma an riga an ɗaura ba yadda zamuyi" "In Allah ya yadda Auren nan ba inda zeje, saboda tsiya da baƙar mugunta, Yarinya ta gama gantalin ta da watsewa kuma ta Auri miji kamar Wannan Yaron, shima ɗan banza munafuki yazo yaita zazzare mata ido amma ya koma ya Aureta dan tsiya da baƙin hali, bayan gaku kamanmu nutsatstu" Sadiya tace "Yadikko, ki kwantar da hankalinki, bana tunanin ya Aureta ne dan yana sonta, ana gobe za'a ɗaura Aure, baki ga dukan da yai mata da wayar wuta ba, yanzu haka ma tana can bata da lafiya, in dai da wannan Mugun halin nata ne ba iya zaman Aure zatayi ba, sakota zeyi kwanan nan" Yadikko tace 'ke bari, wannan Yarinyar algunguma ce, se ta baki mamaki kiga ta zauna lumui, bari ayi sallar magariba, a saka kati a waya a kiramin Alhaji Alin inji ba'asin wannan maganar, amma wannan abu sam bame yuwuwa bane" Haka Yadikko ta cigaba da sababi da nuna adawa ƙarara da Auren Amira. Anty Fa'iza kuwa gaba ɗaya damuwa ta hanata sukuni, bayan sallar isha'i Bashir ya dawo, ya tarar da ita a gida ta dawo, yaji daɗin tarar da ita a gida, dan tunda sukai Aure bata taɓa zuwa wani gurin tayi kwana biyu ba, shiyasa duk ya damu gidan yai masa faɗi, ba ita ba yara da Khairat kawai ta tafi, namijin ta barshi a gidansu Bashir. Yana zuwa ya rungumeta yana "sannu da dawowa Ummu Khairat, maimakon kimin waya kice gaku nan in miki girki, kawai sedai in dawo in ganki" Tai murmushi tace "to yanzu ba Gashi nayi girkn ba ni" "To ya hanya ya kuka baro su?". "Lafiya ƙalau, anyi biki lafiya an gama" "Masha Allah, Allah ya sanya Alkhairi, bari in zuba mana Abinci, in munci ki bani labarin gidan bikin". Fa'iza kawai tayi yaƙe, dan bata son daga dawowarsa ta gaya masa matsala, suna cin Abinci yana mata hira yana tsokanarta, sedai ya lura Abincin kansa ba wani ci take ba, kuma bata responding ga maganganun da yake. "Ummu Khairat, meke faruwa ne na ganki kamar a damuwa fa" "Wallahi Abu Khairat damuwa fa akwai ta" "Subhanallah, wace irin damuwa kenan?" "Baka tambayeni ya muka ƙarke ina mutuniyarka ba?" "Wallahi tana raina, ina son in tambayeki ita, nayi zaton kun taho tare ta wuce can gidane" "Hmm Amira tayi Aure" "Kamar ya?" "Kamar yadda na gaya maka" "Bana son wasa fa, wane irin Aure ana zaune ƙalau" "Baka yadda ba kenan?" "Ej gaskiya ban yadda ba, wane irin Auren haka lokaci ɗaya ba manemi ba bincike bakomai, Kodayake nasan tana da manema, amma ba sune a gabant ba" "Wan mahaifiyarta ya bawa ɗansa Aurenta, yau aka ɗaura musu Aure ya Auri mata biyu, yanzu haka Mun baro Amira a can, ta zama matar Imran" Bashir yai shiru sannan yai murmushi yace "ta wani fannin inayiwa Amira murna, tabbas Aure tamkar mutuwane, lokacine dashi idan yazo dole ayishi, Ubangiji Allah ya sanya Alkhairi ya basu zaman lafiya" "Abu Khairat akwai matsala fa" "Matsalar me kuma Allah ya rufa mata Aisiri, kina kiran matsala" "Imran baya son Amira sam, jiya da daddare baka ga dukan daya mata da wayar wuta ba, kasan halin Amira da rashin son raini, ƙanwarsa ta tsokaneta suka hau dambe, aikuwa ya haɗasu yana duka, Amira ta masa Allah ya isa, ƙarshe a wani gidan ta kwana harda suma, aka dinga mata ƙarin ruwa, kuma wayewar garin yau aka ɗaura mata Aure dashi, ina tausayin Amira matuƙa ina jiye mata irin zaman da za tayi da Imran ga kuma kishiya, ga babar Imran kanta bata sonta, Amira ta sha wuyar rayuwa, naso ta samu miji nagari me sonta, sedai ta ɗaukarwa kanta wata rayuwa ta daban, wannan Auren an mata shine fa dan a samu ta nustu ba wai dan shi yana sonta ba" Bashir yace "Allah sarki Amira, bata da burin da ya wuce Allah ya bata miji me haƙuri da sonta komai talaucinsa, ki kwantar da hankalinki ita irin tata jarrabawar kenan, da kuma ƙaddarar insha Allah ina fatan da kuma sa ran Auren nan ze zame mata haske da kuma Alkhairi a rayuwart, amma ni kaina ina tausayinta sosai" Suka cigaba da tattaunawa da yiwa Amira fatan Alkhairi. Gidan Oga Imran kuwa, haka kowa ya kwana a ɗaki daban, kowa yana saƙawa da warwarewa a cikin zuciyarsa. Imran ko sallar Asuba be fita ba, a gida yayi sallarsa. Da gari yai haske Ammi ta bawa direba Abinci ya kawo musu, a gate yaje ya karɓo Abincin yace bame shigowa Ihsan bata jin daɗi. Ya karɓi Abincin ya shiga dashi cikin gidan, Ƙofar ɗakin da Ijsam ta kwana yaje ya tura ya shiga da Sallama, tana zaune a guri ɗaya tayi shiru tana zancen zuci, ya sake yin Sallama ta ɗago ta kalleshi amma bata amsa ba, ya ƙaraso ya zauna a gabanta yace "Ihsan ga Abinci Ammi ta aiko dashi, ki tashi muje mu karya" "Na ƙoshi" ta bashi amsa a taƙaice. "Dan Allah Ihsan karki horamin kanki da yunwa, ki tashi muje kiyi breakfast" "Dan Allah ka dena pretending ko nuna kamar ka damu da halin da nake ciki, ka ƙyaleni ka bari zuciya ta ta samu nutsuwa, karka yaudareni kasa in sake Amincewa da kai a karo na biyu" Imran yasan ba'a kyautawa Ihsan ba sam, shiyasa yake ta rarrashinta, amma fafur taƙi sauraronsa haka ya ƙyaleta ya tashi ya bar Mata ɗakin. Amira kam jiki ƙara rikicewa yayi, ga duka ga kuna damuwar an mata Aure ba tare da saninta ba, an Aura mata mutumin da takewa Kallon mugu mara imani, dan haka zazzaɓi ya ƙaru ba abunda take banda aikin Kuka, Anty tayi rarrashin duniya amma sam Amira bata dena kukan nan ba, saboda ita kaɗai tasan abinda take ji a zuciyarta. Ammi ta ɗau gaba da Abba, sam bata shiga sabgar Abba, shima yai watsi da ita, ya cigaba da rayuwarsa, yana zaune yana duba wasu takarfu sega kiran Baba, ya ɗaga wayar suka gaisa. Baba yace "Wani labari mukaji ne, shine muka bugo muji sahihancin labarin daa bakinka" Abba yace "eh nasan labarin baze wuce batun Auren Amira ba, dama ko baku bugo ba ni nai niyyar zan bugo muku waya, sannan in tako ƙafa da ƙafa inzo, da farko dai zan fara da neman Afuwarku da baku haƙuri akan yanke hukunci da nayi ba tare da izinin ku ba a matsayin ku na dangin mahaifinta, nayi hakane badan in muzanta ku ba, sedai nayi hakan ne saboda sanin halin ita Amiran, muddin tasan da Maganar Auren zata iya bijirewa hakan, na duba naga Aurar da Amira ga Imran ita kaɗaice masalaha, wadda zata hanata rashin jin da takeyi, shiyasa na sama mana sauƙi ni da ku, kuma bana buƙatar komai daga gareku, yanzu haka komai da iyaye sukewa 'yarsu nayi mata, na sai komai ina jiran seta kusa tarewa sannan aje a shirya mata ɗakinta, ku kwantar da hankalinku dan Allah" Yadikko tai maza ta fizge wayar tace "Amma fisabilillahi ranka ya daɗe baka kyau mana ba, dan akwai wanda mukayi wa alƙawarin bawa Auren Amira, amma kawai semuji ka aurar da ita, ka maida mu ƙanan nan mutane" Abba yace "Subhanallah, ai ban sani ba, baku taɓa gayamin cewar Amira tana da manemi ba, da kun gayamin tunda fari ai da se a san abunyi tun a lokacin amma yanzu bakin alƙalami ya bushe, kuyi haƙuri ku bawa wancan ɗin haƙuri" "Koma dai meye mutuncinmu ya zube mun zama masu Magana biyu, ƙirƙiri mun yiwa wani alƙawari amma mun gaza cikawa" "Ai nace kuyi haƙuri, ni idan nazo ku haɗani da shi in masa bayani nasan ze Fahimta" "Banji daɗi ba gaskiya, ace yaro kamanme kamar wannan yaron ka aira masa wannan yarinyar, bayan ga mata nutsatstu kamanmu har tayin jikokina nai maka, amma kace zeyi Aure, kawai se naji haɗashi da Amira Yarinyar da kwararo kwararo ba inda bata zuwa bin Maza" Abba yace "Subhanallah, abar maganar nana dan Allah, ya riga ya wuce insha Allah ya zama tarihi, Insha Allah shiriyarta ce tazo a sanadin Auren nan" be jira me zasu kuma cewa ba ya kashe wayarsa. Kwanan Ihsan uku a gidan Imran, amma sam taƙi amincewa Imran yaje inda take balle wani abu yafaru, dan fafur take nuna masa bata ta tasa yanzu. Da daddare bayan sallar isha'i Imran yana falo yana kwance yai shiruu, ya rasa abunda yake masa daɗi, message ɗin Abba ya shigo wayarsa. "Ku buɗen ƙofa, ina ƙofar gidanka" Imran ya tashi da sauri ya tafi gate, yana buɗewa yaga Abba, murmushi Imran yai yace "Abba sannu da zuwa" Abba yace "Yawwa Ango" Imran yai masa jagora har cikin gidansa, a falo Abba ya zauna suka gaisa da Imran. Abba yace "Ina 'yar tawa take?" Imran yace 'bari in kirawo ta" Jiki a sanyaye ya tafi ɗakin Ihsan, tana zaune a gefen gado yai Sallama, daƙyar ta amsa masa a ciki, Imran yace "kizo ga Abba yazo, yana son ganinki a Falo" Ba tace masa komai ba, ta miƙe ta saka hijjabi ta bishi falon, fuskarta ba yabo ba fallasa haka ta gaida Abba. Abba ya amsa cikin kulawa, nan yai tayiwa Ihsan nasiha tare da bata haƙuri akan abunda akayi mata, nayi mata kishiya ranar Aurenta ba tare da saninta ba, yaita mata Nasiha yana rarrashin ta. Daga ƙarshe yace Imran ze rakashi unguwa, ba daɗewa zasuyi ba. Imran ya tashi yabi Abba, ya rufe Ihsan ta waje, ya shiga motar Abba, Suka tafi. Suna tafe a hanya Abba yace "Imran ka sake duba ya jikin Matarka kuwa? Bana jin kota waya ka kira kace ya jikinta? Imran ina sake jan kunneka da kaji tsoron Allah akan riƙon da zakayiwa marainiyar nan, kayi adalci a

Chapter 13 of 31