duba agogo ƙarfe sha ɗaya, miƙewa tai ta fito tana tunanin Imran ya fita, dan haka da rigar baccinta a jikinta ta fito, sedai tana fitowa taga Imran yana nan yana falo be fita ba, kallo ma yakeyi shi da Ihsan.
Imran ya ɗaga ido ya kalleta daga sama har ƙasa, ya saki ajiyar zuciya ya ɗauke kansa.
"Ina kwananku?" Ta gaishesu.
Imran ya kalleta ya jinjina kai, yayin da Ihsan ko motsawa ba tayi ba, balle ta kalli inda Amira take ba, seda Amira ta nufi dining, sannan Ihsan taga shigar dake jikin Amiran, ai ba shiri Ihsan ta miƙe zaune, ta kalli Imran amma taga ba Amira yake kallo ba, hankalin sa yana kan TV.
Amira taje ta bubbuɗe kwanukan dake kan dining, ta samu sun rage Abincin ta kama ci.
"Ke kika ajiyemin da zakije ki taɓa min kaya ba izinina?".
Kunnen uwarshegu Amira tai da Ihsan, ta cigaba da cin Abincin ta.
Imran ya kalli Ihsan ya girgiza mata kai alamar tai shiru.
Imran satar kallon Amira yake ba tare da Ihsan ta sani ba, Amira ta kammala cin Abincin ta, maimakon da ta gama ta koma ɗakinta, se ta tashi ta koma kujerar da ke facing ɗin Imran, ta zauna tana kaɗa ƙafa tana danna wayarta.
Imran ya kasa dena kallonta, saboda kusan sashi mafiya yawa na rigar Net ce, gashi ta baje kitson attachment ɗinta, ta haɗe rai kamar ba ita ba.
Tana ɗaga ido sukai ido huɗu da Imran, hararasa Amira tai ta kashingiɗa a jikin kujearar ta lumshe idonta.
Takaici ne ya kama Imran, ganin ta kama shi yana kallonta har da hararsa, Cike da salon tura takaici, ya fara kissing ɗin Ihsan.
Duk yadda Amira ta so ta daure kasawa tai, se ga hawaye na bin fuskar Amira, Ihsan ta bawa Amira baya dan haka bata ganin Amira, Imran ke facing ɗinta Imran yaiwa Amira murmushin mugunta, ganin tana kuka.
Nan da nan tai sauri ta goge hawayen, dan kar ma Ihsan ta gani ta rainata, duk taɓarar da suke a gabanta ta maze, ta cigaba da dannan wayarta, sedai ƙirjinta har wani nauyi yake mata saboda azabar kishi, Imran ya riga ya fara gano Amira ma na da tsananin kishi.
Seda suka tashi suka bar falon sannan Amira ta bawa hawayenta damar zubowa sosai, tafi jin haushin Ihsan fiye da yadda take jin na Imran, jiki a sanyaye ta tashi ta tafi ɓangaren ta itama.
Amira ta tsiri se suna falo, za tai shigar matsatsun ƙananun kaya ta fito, ta fito musu a Karuwarta da suke faɗa.
Da safe Amira ta sanya wani ƙaramin wando da wata 'yar ƙaramar riga,ta fito tana ta gyara babban falo tana goge TV, se ga Ihsan ta fito, ita kanta da tai arba da Amira seda gabanta ya faɗi, ta kalli Amira tace "ke meye haka ne wai?"
"A ina kenan?"
"Wannan wac irin banzar shiga ce? Malama gidana ba bariki bane bafa, dan me zaki wannan shigar ki fitomin falo bayan kin san lokacin fitar mijina ne yanzu"
Amira ta kalleta tace "kema kije kiyi irin shigar mana dan ki hana shi kallona, ki kiyayeni fa na daɗe da fita sabgarku nima ku barni inyi rayuwata"
"Ni kike gayawa haka?"
"Na gayamiki ɗin, uwata ce ke? Kema in kin cika mace kije ki saka mana ki fito, in kuma ba ki da abun sawa ki nuna Ni da nake da shi seki bari in saka in fito ya kalla, da yaje waje ya kalla fa?"
"malama rufemin baki, wallahi ki kiyayeni baki isa ki zo gidana kimin karuwanci ba wallahi, mijina yafi ƙarfin ki"
"Waye mijin naki da yafi ƙarfin tarkon Karuwa, ki zuba ido kiyi kallo zaki ga Karuwa ganin idonki wallahi, zan nuna miki abunda karuwa zata iyayi"
"Me zaki iyayi, ƙarya kike mijina ya faɗa tarkonki, asararriya wadda ta gama raba jikinta ga maza a titi, a kai mata alfarma akaa Aureta"
Amira tace "Kinga bariki tayi riba, na gama gantali nazo na Auri mijin shashasha ba"
"Ni kike cewa shashasha?"
"Na faɗa, Shashasha me kama da bushshen kifi"
"Ke Amira wa kike cewa shashasha?"
Muryar Imran ne dake ƙoƙarin fitowa daga ɓangaren Ihsan.
Sedai yana ganin Amira yai sororo yana kallon Amira, saboda shigar da tayi, cikin jarumta irin ta Maza ya dake yace
"baki da kunya ko, ke ba'a gayamiki magana kiji ko? Kike ce mata Shashasha, ke akwai babbar shashasha ma sama da ke? Ke ba'a kalleki ance miki shashasha ba kece me dogon bakin ce nata Shashasha ko? Kika bari na kuma jin Magana makamanciyar wannan kin gayawa mata ta sena ɓata miki rai"
Amira tace "Wallahi ni ba shashasha bace"
"Ni kike cewa ke ba Shashasha bace?"
"Eh ni ba shashasha bace, kuma wallahi ta kuma cemin Karuwa sena nata rashin mutunci, sena maƙure mata wuya na kakkaryata"
Imran yace "An faɗa miki Karuwa, ba Karuwar bace? Ina nan har Abuja kika tafi gantali gurin rawa, ki kai hotuna da ƙaton Arne, yana nema ya sa a kulleki, ko duk ƙarya a kai miki? Ga ranar rashin ji nan, kika kuma ce mata Shashasha sena saɓa miki"
Tuni idon Amira ya ciko da ƙwalla, ta kalleshi tace "ni idan ka kirani da Karuwa ba yamin ciwo dan ba Kai ka fara ba, Amma idan matarka ta kuma cemin Karuwa wallahi sena mata rashin mutunci"
Tai maganar tana zirara da hawaye daga idonta.
"A gabana kike cewa zaki ci mata mutunci?"
Amira dai ba dan kar tayi ƙarya ba, se tace ciwon zuciya ya kamata, saboda baƙin cikin da take kwasa.
"Eh wallahi ta kuma cemin Karuwa sena mata dukan tsiya wallahi"
Aikuwa Imran yai kan Amira, ta ruga da gudu tai part ɗinta, aikuwa ya bita ya cinmata a bedroom ɗinta, kan gado ta haye ta tsaya tana masa magiyar "dan Allah kayi haƙuri ba zan sake ba"
"Ba dai baki da kunya ba, zanyi maganinki"
Ya maida ƙofa ya rufe "wayyo Allah na shiga uku, dan Allah kayi haƙuri"
Nan suka shiga wasan zilliya, Amira ta shammace shi ta baya, ta rungumeshi tana
"dan Allah kayi haƙuri karka dakeni"
Gaba ɗaya se Imran ya rasa nutsuwarsa, yasa hannu ze cire hannayenta daga jikinsa, amma ta sake maƙaleshi sosai, yai ajiyar zuciya yace "cikani"
"A'a ni dai dan Allah kayi haƙuri"
"Ai na haƙura, cikani kawai"
"A'a wallahi tsoro nakeji dan Allah karka dakeni"
"Ai nace ba zan dake ki ba, ki cikani kar raina ya ɓaci"
Shiru tai kuma taƙi cikashi, ya shammaceta ya rabata da jikinsa ya fizgota gabansa, tai fiƙi fiƙi da ido, kamar wadda ta aikata rashin gaskiya.
Imran yace "Allah ya shiryeki"
Maimakon ta amsa seta hau tura baki, tana masa wani kallon ƙasan ido.
Seda ya shafe wasu seconds yana kallonata, sannan ya bar part ɗin nata.
Ita Ihsan zatonta zuwa yai yayiwa Amira rashin mutunci.
Amira ta dena fitowa sosai balle ta shiga sabgarsu, saboda ba ƙaramin baƙin ciki suke ƙunsa mata ba.
A Kitchen ɗin falo Amira kan shiga ta samo abun dafawa, dan nata Kitchen ɗin ba Komai a ciki, sedai ya ajiye mata a Kitchen ɗin Falo.
Gajiya tai da zaman shiru, ta fito Falo da niyyar ɗaukar abun da zata dafa, sedai ta na fitowa gabanta ya faɗi, dan Ammi ce ta zo ita da Minal, suna falo suna hira da Ihsan Imran ma yana falon suna hira.
Jiki a sanyaye Amira ta ƙaraso falon tace "Ammi sannu da zuwa, ai ban san da zuwanku ba"
Ammi ta kalleta sama da ƙasa tace "dama nace miki na zo dan ke ne? Ko kuma ce miki a kai gurinki na zo? Gurin matar ɗana na zo, ba ke ba"
Amira ta sunkuyar da kai tai shiru.
"Ki tashi ki bani guri, ki dena wannan sumi sumi da kan, dan ba zaki yaudareni ba, ba zakimin Karuwanci ba, kuma ki tabattar kayanki suna ƙulle, daga yanzu zuwa ko wani lokaci zan iya murƙushe wannan Auren naki, dan ni gaba ɗaya zuriyarmu Babu Karuwai, gara tun wuri ki fara tattara komatsanki, bamu da buƙatarki ba dan Baban Imran ya matsa ba me zeyi dake? Sauran titi"
Amira ta sunkuyar da kai, hawaye na ta bin fuskarta.
Ihsan tace "Ammi ki gaya mata ke ko taji, se wani rawar kai take a Lallai seta ƙwace Imran"
Minal tace "a hakan? Wallahi Yaya Imran yafi ƙarfin haka"
Kawai se Imran yaji ba daɗi maganganun da ake mata, se tsiyayar da hawaye take, amma yai shiru bece komai ba, kar yai wani abu da ze tunzura Ammi.
Suka ƙarewa Amira cin mutumci, abun mamaki Amira duk wannan tsiwar ta Amira amma haka ta gaza cewa komai.
Ta koma ɓangaren ta jiki a sanyaye, ji take kamar ta kira Anty, ko Fa'iza ta gaya musu halin da take ciki a gidan Imran, amma ta danne tai shiru ba ta gayawa kowa ba.
Sedai Ranar tayi kwanan baƙin ciki sosai, zuciyarta a cunkushe bacci ya ƙauracewa idonta, saboda ɓacin rai, ga ƙiyayyar miji da kishiya, gata mahaifiyarsa ita dai gata nan ba wani gatan Kirki.
Suna kwance akan gado, Ihsan tana ta zuba taɓararta, Imran yace "My Wife, ina son zan roƙe ki wata alfarma ne"
"Ina jinka my own"
"Dan Allah ki dena Kiran Amira da Karuwa, kamar yadda ta buƙata duk da nasan ba'a canzawa tuwo suna, bana son yawan kukan da take"
Tashi zaune Ihsan tai tace "Imran me kake nufi? Son ta kake kenan?"
"Ko ɗaya, sedai ina tsoron Abba ya gano irin zaman da muke, nasan ba ƙaramin ɓatamin rai ze ba"
"Kar ka damu insha Allah ba ze gane ba, a haka harta gaji ta tattara kayanta ta tafi ta bamu guri"
Imran murmushi kawai yai be kuma cewa komai ba.
Abun mamaki duk san Amira da bacci, amma ya gagareta, tai sallar Asuba, tai addu'oi da karatun Alqur'ani, amma idonta babu bacci, ta koma kan gado ta kwanta ta rintse idonta amma bacci yaƙi zuwa.
Gajiya tai da kwanciyar ƙarfe tara da rabi ta fito, ta kama aikace aikace duk dan ta rage damuwa.
Ji tayi ana ƙwanƙwasa ƙofar babban falon, taje ta sako hijjabi ta buɗe, Abba ta gani a tsaye hannunsa riƙe da wayarsa.
Murmushi Amira tai tace "maraba da babban baƙo"
"Yawwa Amira, in shigo?"
"Shigo mana Abba"
Tai masa iso zuwa falon, tace "Abba jiya su Ammi suka zo, ya akai baku zo tare ba?"
"Ai ni jiya bayan sallar isha'i na sauka, kuma naji Lallai ina son in zo inganku, nace bari inyi sammako dan anjima ma ina da gurin zuwa"
"Masha Allah sannu da zuwa, ya su Ammi sukaje gida"
'lafiya ƙalau, ina Imran ɗin da abokiyar zamanki?"
"Yana ɓangaren ta, ina ga basu tashi bane"
Abba ya kalli idanun Amira da ke kumbure yace "ina fatan dai lafiya ba wata matsala?"
"Ba matsalar komai Abba, se kewar Anty Nafisa da su Anty Fa'iza na"
"Lallai kinji daɗin zaman Gidan Hashim, ita ma tana kewarki sosai"
"Gaskiya naji daɗin zaman Gidan sosai, ta na da kirki, ta kula dani kamar 'yar da ta haifa"
"Ai na samu labarin hakan, nima nyi farinciki sosai"
"Abba bari in musu magana, su zo ku gaisa"
Amira ta miƙe ta shiga part ɗin Ihsan, ta na ta addu'a, Allah karya sa taga abun da ze sata kuka.
Da sallama ta shiga falon, Imran ya amsa tace masa "Ina kwana"
"Lafiya ƙalau"
"Gaskiya My, kai nata magana ta dena shigomin, akan me se ina buƙatar keɓewa da kai zata dinga faɗomin ɗaki"
Ihsan tai maganar tana kwaɓe fuska.
Dama Amira a ƙule take da su tace "dalla rufemin baki, kina magana da baki kamar an yaga tsumma, uwar me zanzo gani ko yi a part ɗin naki, daƙiƙiya jahila, in kun ga dama ku zo falo Abba ne ya zo"
Ai Imran yana jin haka ya miƙe da sauri, cike da fargabar Allah yasa ba gayawa Abba tai irin zaman da suke ba, ya zari jallabiyarsa da sauri ya zira ya fito.
Amira kam komawa gurin Abba tayi suka cigaba da hira, Imran ya fito yana kallon fuskar Abba ko ze gano wani abu a fuskarsa.
Se dai Abban na ganinsa yai murmushi yace "Sannu ɗan hutu, ace har yanzu baka tashi ba?"
Ɗan sosa ƙeya Imaran yai yace "Abba sannu da zuwa"
"Yawwa, ya gidan ya Iyalan naka?"
"Duk suna lafiya ƙalau Abba"
"Ina ɗaya 'yar tawa ban ganta ba?"
Imran yace "yanzu zata fito"
Amira ta miƙe ta cigaba da shirin haɗa breakfast.
Da ƙyar Ihsan ta danne zuciyarta ta fito, dan haushin Abba take ji sosai yake ƙular da ita.
Ta ƙaƙalo murmushin dole, ta fito ta gaisheshi.
Abba yana shirin tafiya, Amira tace lallai seya tsaya ya karya, seda Abba ya tsata ya sa albarka, saboda ya riga ya karya a gida, ranar su Imran ma Abincin Amira suka ci saboda idon Abba.
Abba ya tashi ze tafi, Amira taje ɗakinta ta ɗakko turare me kyau, ta saka a wata 'yar jaka ta biyo Abba da shi.
Ta tarar da Abban da Imran a jikin motarsa, yana masa Nasiha.
"Abba ga wannan ka fesa"
Abba yai murmushi yace "duk wannan nawa ne?"
"Abba ba yawa"
"To Nagode, Ubangiji Allah yayi Albarka, ina fatan dai babu wata matsala ko?"
Amira ta kalli Imran sannan ta kalli Abba ta girgiza kai.
"Amira bana son ɓoye ɓoye, naga kina kallon Imran, idan yana miki wani abun da ba kyajin daɗinsa ko yana muzguna miki ki gayamin"
Ƙwalla ce ta taru a idon Amira, amma ta daure tace "ba abunda yakemin Abba"
Abba ya kalli Imran a ɗan hasale yace "Anya Imran ba wani abu kake wa Yarinyar nan ba? Nifa ban gamsu da amsar da ta bani ba, Imran kaji tsoron Allah, in kasan cutar min da ita kake gara a nemi mafita da wuri, kar mu sake wani laifin"
Inda inda Imran ke neman farayi, Amira tace "Abba ka dena yi masa faɗa, ba abunda yaimin fa, ni kawai haryanzu 'yan gidanmu sunƙi zuwa"
"Anya Amira, wannan ne kawai ze sa inga damuwa a fuskarki, ki gayamin gaskiya"
"Abba Gaskiya na gayamaka Abba, ba abunda yaimin na rashin daɗi, ina kewar 'yan gidanmu ne kawai"
"To shikenan, na yadda da abunda ki ka faɗa, zamuyi waya da su Insha Allah, za'a ga yadda za'ayi"
Amira tace "Nagode Abba, a gaida su Ammi da Minal"
"Za suji insha Allah"
Imran yai mamakin yadda Amira ta rufa masa Aisiri, Abba ya tsare shi ya cigaba da yi masa Nasiha.
Amira kam ciki ta koma, ta cire hijjabin jikinta, ta fito a skin tied jeans ɗinta, vest ta tsefe kanta, ta haɗa da attach ɗin tai parking gashinta, ta zo tana tattare kayan da aka ɓata na Abinci, ta zuba ruwa tana mopping falon.
Ihsan na fitowa ta kalleta ta ja tsaki, Amira ta rasa dalilin da ya sa Ihsan ba ta son zaman lafiya, ko bata kula ta ba se ta nemi abunda zata takale ta da faɗa, shiru Amira tai Mata ta cigaba da abunda take.
"Dama aikin wanke wanken kika je kika fara a gidajen masu kuɗi, dan kinfi da cewa da hakan, dan ƙarshen karuwa ba kyau ne da shi ba"
Amira girgiza jikinta tai tace "Ke aka ɗaukeni aiki a gidan masu kuɗi ai akwai gwarama, yadda mijinki ke sakin baki ya kalla suma haka zasu saki baki su kalli kaya, mussaman idan matansu irinki ne, aba a jingine kamar allo, ke ba fasali ba ba shape ba, ai duk namijin da ya auri irinki sedai haƙuri da maleji, dan baki da maraba da maza"
Aikuwa Ihsan ta ƙule tace "Eh na naji, amma na fiki kima a idon miji, duk da ni me kamar mazance Karuwa kawai"
"Da ubanki na fara, shiya koyamin"
Buɗe baki Ihsan tayi, ta fusata ainun, maganar da Amira ta daki ranta, ta rasa abunda za tayi, kawai taje tai ball da Ruwan mopping ɗin Amira, tace "karki ƙara zagarmin Uba, Uba na ya mutu ba sa'anki bane, kuma Ubana ba mazinaci bane"
Amira ta kalli yadda tai mopping amma Ihsan ta kwarar mata da ruwa a gurin, Amira tana damuwa da gyaran falon nan, saboda kana shigowa shine a farko kan ka shiga in da kowacce su take, tun da Amira tazo Ihsan ta dena gyara falon, Amira ce keyi, Amma ta zubar mata da ruwa agurin.
Amira tace "can ta matse miki, ina sake miki kashedi ne, duk randa haƙurina ya ƙare sena koya miki hankali, kina kuma cemin Karuwa da ubanki na fara yi, idan kin son sa ki dena gayamin, idan baki dena ba kuwa wallahi baki fini baki ba, banda ma nayi sanyi ke kin san wace Amira, ɗaga muku ƙafa kawai nake, Amma wallahi da rigimata seta hanaku sukuni a Gidan nan, shi Ya sani ai, kuma wallahi daga yau na dena shiru, dai dai nake da ku"
Imran ya shigo yace "to kaji sarakan faɗa, ke Amira kullum bakya iya zama sekin nemi Magana ko?"
Ta kalleshi up and down tace "eh dayake nice Sheɗan ba, dole kace min ina neman faɗa, to bani na fara ba, ga ƙaramar ibilishiyar da ta tsokaneni nan"
Ihsan ta fashe da kuka, tace "Imran zagin mahaifina tayi tace mai mazinaci, Ubana da yake binne ya mutu, me yayi mata zata zagarmin uba, tace masa mazinaci?"
Kalmar ta daki Imran yace "Mazinaci kuma?"
Ihsan ta jinjina kai alamar eh.
"Amira waike wace irin banza ce? Saboda rashin daraja, da rashin sanin kimar iyaye ki kira uban wata Mazinaci?"
Girgiza kai Amira tayi tace "Captain kayi bincike mana, ni me tacemin na gaya mata haka? Kuma ni ban....
"Shut up i know you can do more than that, wulaƙancin naki har kan iyaye, mara Kunya fitsararriya, ke kina da bakin kiran Mahaifin wata Mazinaci, bayan baya raye, kece Ma..
"Shut up Imran, wallahi karka soma kirana Mazinaciya, na yadda dan ancemin Karuwa matsalarku ce, amma wallahi ka kirani Mazinaciya sekayi mamakin abunda zan aikata, kun fara ƙureni haƙurina ya ƙare, za'ayi irin zaman da kuke so, kuma wallahi idan matarka bata kiyayeni ba sena mata illa wallahi"
Ta ƙarasa Maganar tana hawaye, harta juya zata tafi, ta kalli Imran ta kalli bokitin da Ihsan ta zubar mata da ruwan mopping, ta ɗau bokitin ta jefawa Imran shi a ƙirjinsa tana huci, a ƙoƙarin ta na samun sanyi daga raɗaɗin da zuciyarta ke mata.
Tofa!
Share Please
A gaskiya ba zan iya gayamuku farincikin da nake ji da Comments ɗin da kuke ba, ina godiya sosai da sosai, Allah ya bar zumunci, Comment ɗinku na sani nishaɗi.
Ga masu san shiga group na RUƊIN ƘURUCIYA, You can subscribe it for
₦300 only.
Shima nasa salon daban ne, don't miss it.
Ayshercool
07063065680
[2/2, 4:25 PM] Ayshercool: 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
WUTA A MASAƘA
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P. W. A
*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA)
*BAƘIN TABO (Labarin gasa)
*AƘIDATA (Paid Book)
* WUTA A MASAƘA
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in
❌❌❌
Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.
35_36
Saroro Imran yai yana kallon Amira, da tuni idanunta su kai ja, ta juya ta koma part ɗinta zuciyarta na wani Mugun tafasa.
Duk da jifan sa da Amira tayi da bokiti, ko gezau be ba haka bokitin ya daki ƙirjinsa da ƙarfi ya faɗi.
Ihsan zuba ido tai ta ga Iya abun da Imran ze, ta ga matakin da ze ɗauka akan Amira, amma taga kawai yai waje ba tare da yace komai ba ko ya ɗau wani mataki ba.
Mamaki ne ya cika Ihsan, wai kenan Amira taci bulus? Me Imran yake nufi da ƙyale Amira ba tare da wani hukunci ba? Ta masa wannan fitsarar har da duka amma ya gaza ɗaukar mataki?
Amira kam seda tai ƙaramin hauka a ɗaki ita kaɗai, gaba ɗaya ta fita hayyacinta saboda kuka, ta zama kamar wata wadda ta daɗe ta na cuta, idanunta suka kumbura su kai jawur saboda kuka.
Haka tai me isar ta ta haƙura, ko Abincin rana kasa ci tayi saboda yadda take jin zuciyarta.
Imran kuwa bayan fitarsa Khalid ya kira shi a waya, kamar ya share kiran kar ya ɗaga, seda ta kusa katsewa sannan ya ɗaga.
"Malam wai baka kusa da wayar ne da se da ta kusa katsewa sannan zaka ɗauka, ko duk matan ne suka ɗauke maka hankali?".
"Ƙyaleni kawai Khalid, suna neman su maida ni mahaukaci ne kawai".
"Mahaukaci kamar Yaya?"
"Wai dama haka Auren mata da yawa yake? Kullum cikin faɗa da tashin hankali, yau ni Amira ta jefawa bokiti a ƙirji, ni nama rasa me zanyi, dan idan nace zan dake ta rainani zata yi kawai, kuma zan iyayi mata illa, dan duka zan mata na gaske"
Khalid yace "Subhanallah, wai haryanzu Amira ba tai hankali ba kake nufi?"
"Ina Wannan yarinyar za tai hankali, kullum cikin faɗa kamar dage, ba afuwa a lamarinta kullum cikin neman rigima".
"A'a Imran, haka kurum ba zata nemi rigima ba, me a kai mata ta nemi rigima, ka dinga mata adalci fa"
"Kaga dan Allah ƙyaleni, karka ƙara tunzurani, dan tunanin hukuncin da zan mata nake"
"Wane hukunci, ai tunda ba ka hukunta ta a lokacin ba kawai ka manta, kayi haƙuri ya wuce kawai".
"Saboda rashin mutunci, ta min laifi kuma in ƙyaleta?".
"Kai me kai mata tai maka hakan?"
Tsaki Imran yai yace "ka ga, kiran me kayi min ne?"
"Dama kira nayi inji lafiyar ka, sannan ka kalli News ɗazu da safe kuwa?"
"A'a ban kalla ba, ni ban ma gaya maka ba, ɗazu Abba ne fa yazo yana tafiya suka fara rigima, abun da ya bani mamaki ne wuce yadda Yarinyar nana ta rufamin Asiri a gurin Abba ba"
"Asirin me ta rufa maka?"
"Nifa tun da ta tare, ba abunda ya haɗani da ita, ko ɗakinta ba na zuwa"
Khalid yace "tirƙashi amma ba ka da Imani Imran, wallahi ba ka kyautawa kanka ba"
"Khalid look, Yarinyar nan da a nutse na Aureta, zan iya haƙuri in zauna da ita har wani abu na auratayya ya haɗani da ita, amma to be sincere, ina jin takaici idan na kalli Yarinyar nan na tuna abubuwan da tayi, kuma ace mata ta ce, raina ɓaci yake"
"Imran waye ya gaya maka ana Jihadi cikin sauƙi ne, yanzu an samu ta nustu ta zauna a gidanka ba yawo, ba komai kana ganin rashin kula da ita ɗin nan baze sa ta koma kan laifin da take a baya ba?"
"Wai da Aurena tayi gantali?"
"Ƙwarai kuwa" Khalid ya bashi amsa.
"Wallahi da sena kasheta"
"Sannau uban marasa hankali, ai seka kashe ta ɗin, kai baka sauke nauyin da Allah ya ɗora maka ba, saboda wani usless excuse ɗinka ba, za ka wani cika baki, back to business, kace ba ka kalli News yau ba ko?"
"Eh ban gani ba, mene yafaru?"
"Our heroes are killed in the yesterday operation, more than 30 of them were killed, and some of them were injured"
"Innalillahi wa innalillahi raji'un, may their Souls rest in Jannatul firdausi"
"Ameen, abun ba daɗi sosai, so You have to get set, Komai ze iya faruwa"
Imran yace 'ai kullum a cikin shiri muke, ko mu kashe ko a kashemu, Allah ya bamu zaman lafiya a ƙasar nan"
"Ameen ya Allah, se anjima zanyi wani aiki ka gaida matanka"
"Hmm se anjima".
Imran ya kashe wayar yana jinamin labarin da Khalid ya ba shi na kisan da akaiwa sojojin, a fafatwarsu da 'yan ta da ƙayar baya.
Imran be koma musu gidan nan ba se da yai sallar isha'i.
Daya dawo ƙofar part ɗin Amira a rufe, ya tafi ɓangaren Ihsan, ya tarar da ita a bedroom fuskarta babu walwala sam, dan da ƙyar ta amsa masa sallamar da yai..
Be kulata ba ya shirya ya shiga wankansa, ya fito ya sanya kayan baccinsa, yana ƙoƙarin kwanciya.
"Wai yau a ina ka wuni ne?"
"Kin aike nine?"
"A'a amma gani nai ba haka kake ba"
"To ya zanyi, idan ba haka nake ba yanzu na fara, ku kenan kullum cikin faɗa da ɗagmin hankali naras wace me gaskiya wace mara gaskiya, kuma idan Amira na da fitina wasu lokutan kece kike tsokanarta, kuma seda na miki kashedi akan shiga harkarta"
"Wane irin shiga harkarta nai, ita wanan se an shiga harkarta take abunda take? Taci mutuncin mahaifina ta buga maka abu amma ka ƙyaleta ba abunda kai mata"
"Me kike so in mata, in bita in ta duka, ba kiga ni abunda tamin na rufin Asiri ba yau? Ke da ta gayawa Abba abunda ke faruwa Allah kaɗai yasan abun da zemin, shiyasa na ƙyaleta"
"Yanzu dai kana nufin taci bulus kenan ko?"
Tsaki Imran yai yaja bargo ya rufe jikinsa ya lumshe idonsa, bin Imran tai da kallo, wani mugun haushinsa ya mamayeta, itama kwanciya tai ta juya masa baya, dan tayi alƙawarin wannan karon ba zata lallaɓashi ba.
Washegari ya kama ranar da Ihsan zata fara zuwa gurin da za tai service, mass communication
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 19 Chapter of 31