lafiya, irin wannan ai seki gayamin, ko Abinci in dinga aiko miki, dan nasan irin wannan situation ɗin bakomai zaki iya ci ba"
Amira tace "hmmm" a ranta tace dama Ammi ce ke wannan farinciki haka, duk da cikinta ba halak ne, amma tana jiyewa abunda zata haifa ƙiyayyar da ze fuskanta daga dangin ubansa.
Anty tace "Amira lafiya kuwa, naji kin ce hmmm kuma kinyi shiru?"
Kawai Amira ta fara kuka, cikin damuwa Anty tace "Ya salam, Amira menene? Ki gayamin meyafaru?"
"Anty bana son in dinga gayamiki abun damuwa, amma har ga Allah bana farinciki da cikin nan"
"Kai Amira baki da hankali ne? Wasu an nema ido rufe da kuɗinsu kice ba kya murna da cikin? Kina kallon abokiyar zamanki ban sani ba in ba yanzu ba, Amma Allah be bata ba, ke kuma kin samu zaki ce ba kya murna? Meye hujjarki bayan da Aure kika samu"
"Anty, Ammi tazo gidan nan da safe, a gabanta na dinga amai sedai ta nuna ba ta maraba da hakan, kuma tace ita tana doubting idan na Imran ne" ta ƙarasa maganar cikin kuka.
"Innalillahi wa innalillahi raji'un, ni wai meke damun Hajiya Jamila ne kamar ba taje makaranta ba? Wane irin abu ne haka take yi kamar ba musulma ba? Idan ita bata maraba da shi mu munayi, kuma ɗanta yasan ai ɗansa ne, dan haka kark kuma sa wanan a ranki, mu mun gode Allah da ya raba baiwar sa ya bamu, Allah ya rabaku lafiya in ba sa so kema kuma va kya so, in kin haifa ni ki bani, dan Allah ki kwantar da hankalinki, ki raini cikin ki ki haihu lafiya, idan kika kuskura jininki ya hau da ciki, zaki iya jijjiga idan kin haihu, dan haka kar inji ko in ga kince ba kya son ciki, ki lallaɓa abunki kiyi Addu'a Allah ya rabaku lafiya kin ji jo?"
Amira tace "To Anty Insha Allah"
"Yawwa Amira, me kike buƙata in sa Fadila ta girka miki a kawo miki?"
"Bana son komai Anty, naci Abinci"
"To shikenan, da kinji kina son wani abun ki kirani a waya kinji Amira"
"To Anty insha Allah, nagode Sosai"
"Yawwa, Allah yayi albarka"
Amira ta ajiye wayar.
Imran kam ɓangaren Ihsan ya nufa, yaje ya tarar da ita tasha kuka, duk tayi wani iri saboda azabar kishi, tausayinta ne ya kama shi, duk da wasu lokutan halinta ne yake ja mata komai, amma yaje ya zauna a kusa da ita, sedai yana zama ta matsa daga kusa da shi.
Hannu ɗaya ya saka ya janyita ta ƙarfin tsiya, tana fizge fizge amma ya riƙeta gam ya zuba mata ido, cikin kwantar da murya yace "haba Ihsan, wallahi kin bani mamaki, yanzu duk da tarin soyayyar da ki ke min amma zaki iya juyamin baya haka? Gaba ɗaya kin watsar dani, ta yaya Hankalina baze karkata wani gurin in nemawa kaina mafita ba?"
"Dan Allah ka ni ka ƙyaleni, kaje ka ƙarata ka rabu dani bana son ganinka ma, maci amana kawai, ka min alƙawarin da ka san ba zaka iya cikawa ba, kuma kana nema ka juyamin baya"
Imran yace "tabbas nayi dana sanin yi miki alƙawarin da na gaza cikawa, amma ni ko sau ɗaya bani da niyyar juya miki baya, kece ma ki kai watsi dani gaba ɗaya, kuma karki kalli tarayyata da Amira a matsayin cin amanarki, Ihsan na biye miki a baya nayi kuskure, saboda Amira itama matata ce tana da hakki a kaina, ama na take na dinga biye miki dan kar hankalinki ya tashi, amma ni haryanzu ina sonki a raina, matsayin Amira daban a gurina, kema matsayin ki daban a gurina dan Allah ki kwantar da hankalinki mu rayu cikin kwanciyar hankali"
"Ba dai dani ba, kaje can dai ka rayu da ita ba da Ihsan ba"
Riƙe ta yai ya fara kissing ɗinta a hankali, amma ta dage iya ƙarfinta tana tureshi, Imran ya kalleta yace "Ihsan meke damunki hakane?"
Ta tofar da yawun bakinta tace "ban sani ba, Allah ya kiyaye ka haɗa baki da Karuwa sannan ka samin bakinka a nawa Allah ya suttura"
Murmushin takaici yayi Yace "she's virgin, ba Karuwa bace, idan ma karuwar ce ta fiki sona duk da yadda ki ke da'awar kina so na, da Amira ce ba zata mik abunda kike min ba, duk da tarin laifukana a gareta ba ta taɓa watsar dani kamar yadda kike ba, satina biyu da dawowa amma kin ƙauracewa shimfiɗa ta gaba ɗaya, na biyoki amma still kin min wulaƙanci, dan me ba zanje in da za'ai maraba da ni ba? Amira na da wata daraja ta mussaman a idona, saboda halayenta, abunda tai a baya ma kuskure ne, ina fatan Ubangiji Allah ya yafe mata, kiyi wa kanki faɗa Ihsan kishi ba hauka bane, gidan Annabi Sallallahu alaihi Wasallam mata goma sha ɗaya ne, duk da son da yake wa Nana A'isha radiyallahu anha, abokan zamanta goma ne, balle ke Ihsan, ina ilimin ki da na sanki da shi? Ina tarin karatunki na addini, duk kishi yasa kin ajiye a gefe? Allah ya ganar dake akan lokaci, ki shirya jibi insha Allah zan tafi Lagos, tare zamu tafi"
"Ba zani ba, ka ɗau barbaɗaɗiyyar matarka ku tafi tare"
"Ai kuwa ko a ƙafa na jata bina za tayi, matar aljanna kenan"
Ihsan taji kamar tabi Imran ta shaƙeshi.
Yana fita ta kuma rushewa da kuka, ta sa hannu ta ɗauki wayarta tana kuka ta kira Mummy.
"Hello Mummy kina ina ne?"
"Ina gida lafiya?"
"Mummy Ina fa lafiya, Mummy Imran ya yaudareni mugu ne, bayan tafiyar su Lagos kinga ta dawo da ciki, gaba ɗaya wulaƙanci yake min, ya dena saurarata ya dena shiga harkarta na shiga uku Mummy ta ƙwacen mijina"
"Innalillahi wa innalillahi raji'un, dagaske ciki ne da ita?"
"Ciki ne da ita Mummy, kuma yau a gaban Ammi ta dinga amai"
"To me Jamilar tace?"
"Mekuwa tace? Ta yi musu hargowa ta tafi, na abunda yafi damuna shine da tace min wai inje Asibiti a dubani, ɗanta lafiyarsa ƙalau tunda matarsa ta samu ciki, ni shikenan na shiga uku"
"Ki kwantar da hankalinki Ihsan, ba ki shiga uku ba"
"Wallahi na shiga Mummy, shikenan Bani da wani amfani yanzu, zuwa nan gaba duk da tace ba zata krɓi jika da ga gurin karuwa ba, nan gaba idan ban haihu ba, ko dai ta karɓi 'ya'yan Amira, ko kuma ko ta sa ya ƙaro Aure"
"A'a ki kwantar da hankalinki, hakan ma ba zata faru ba insha Allah"
"Mummy k ka ce in kwantar da hankali na, how? Ta yaya Hankalina ze kwanta, bayan ni da ke mun san batun kwanciyar hankali babu shi? Shikenan ni na san abunyi, sedai a zauna kowa ma ya rasa"
Ta kashe wayarta ta zauna a gurin tana cigaba da kuka.
Da daddare Imran yana gurin Ihsan, sedai fafur taƙi sauraron sa, shikuma ya gwada mata ƙarfi, gaba ɗaya Abun duniya ya sake ƙule Ihsan, ya tashi yai tafiyar sa ya barta, nan ta ƙara tabattar da Imran yanzu ba ta gabansa.
Ya kints jikinsa ya shiga gurin Amira, ya tarar tana bacci amma jikinta raɗau da zazzaɓi, ya shafa gashin kanta ya sumbaci goshinta sannan ya bar ɗakin.
Da safe ma seda ya koma gurin Amira, ya tarar idonta biyu ya dafa tea ya bata, tai wanka yace "ko kina sha'awar wani abun in siyo miki"
Tace "A'a bana son komai, idan naci ma amai zanyi"
"Sannu Amira"
"Yawwa my dear"
"Bana jin daɗin rashin cin Abincin nan da kike yi"
"To ya za'ayi larura ce ai, kasan me nake sha'awar ci?"
"Se kin faɗa"
"Ina wannan tebar da aka kawo mana, ranar da muka je Lagos?"
"Eh na gane"
"To da zan samu ita nake so"
Imran yace "bari in fita zan duba gurin masu sai da Abinci, ko zan samu"
"No i don't mean you should buy it for me, kawai dai gaya maka nayi"
"Da na iya da da kaina zan miki Amira"
Amira tai murmushi tace "Never mind"
Imran ya gyara zama yace "Amira, zan koma Lagos , amma Ihsan ta ƙi yadda mu tafi tare, kinga dama ba ki da lafiya ko zamu tafi tare?"
Girgiza masa kai tayi tace "A'a, ai wannan zuwan da ita ya kamata ka tafi, idan ka tafi dani ba kayi adalci ba".
"Amma kin san haryanzu akwai sauran sati uku da ya kamata muyi tare, watanmu biyu da sati ɗaya da ita lokacin da muka tafi Lagos"
Amira ta harareshi tace "meya hana a biyani tun a wancan lokacin se Yanzu?"
Yai murmushi yace "Allah ya baki haƙuri"
"Yawwa Amran, dan Allah nace ina son zuwa Kano, ko sati biyu inyi kan ka dawo"
"Wa kika ajiye a Kanon da zaki je?"
" 'yan uwana mana"
"To ban yadda ba, ko zaki ba Yanzu ba"
"But Why?"
"To banda Fa'iza gurin wa zaki je? Kuma ko sati biyu ba'ayi da barin su nan ba"
"Haba Amran, ko ba komai Yakamata in je, tunda na baro Garin ban kuma zuwa ba fa"
"A yanzu dai ban yadda kije ba, sedai ko nan gaba"
"Shikenan"
"Yawwa tawan, shiyasa nake yinki, duk da tsiwar ki ana iya saki ko a hanaki, keep it up dirling"
Duk da taji haushin hanatan da yayi, amma tai masa murmushi.
Har satin ya shuɗe Imran be koma gurin aiki ba, saboda yanayin jikin Amira, tana shan wahalar cikin nan sosai, yana matuƙar tausayinta sosai, ga rashin cin Abincin komai taci se tai amai, kankana ko apple suka ɗai ke iya zama idan ta ci.
Gefe guda Ihsan abubuwan ta sam ba sauƙi, kullum gaba suke yi, tashin hankalin yau daban na gobe daban, kullum da kalar rikicin da zata ɓallo wanda ze ɗagawa Imran hankali.
Imran yana tausayinta ne, amma ya ga abun nata ba na ƙare bane.
Amira ta gaji da kwanciya, ta ɗan fito babban falo dan ta huta, taji ƙamshi ya cika gidan, Ihsan tana suyar dankali da ƙwai.
Nan da nan jikin Amira ya hau tsuma, yawunta ya tsinke, taji ranta ya biya.
Ta tashi ta koma ɗakin ta dan ta dena jin ƙamshin amma abun ya gagara, ta shiga Kitchen ɗinta da niyyar itama ta girka, amma tana haɗo kayan gyara dankalin taji bata so, wanda yake ƙamshin nan kawai take so.
Amira ta fito ta nufi part ɗin Ihsan, ta na zuwa ta tarar da Ihsan a Kitchen tana aiki.
Tace "Ihsan sannu da aiki"
Ihsan ta ɗago ta kalleta tace "uban me kika shigo yi min? Meya kawoki munafuka"
"Dan Allah kiyi haƙuri, dan girman Allah ki sanmin dankalin nan, ko kaɗan ne"
"Sannu mayya, nace sannu mayya, ai gara ki biyoni ki sake gayamin ki na da ciki, wallahi idan baki bar part ɗina ba, sena ƙona ki da mai, Allah ya sa cikin ya zube uban kowa ma ya huta"
"Naji, koma dai menene ni dai dan Allah ki sanmin Ihsan ko kaɗan ne, dan son da kike wa Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam"
"Wallahi ko ƙiyama zaki tafi, idan baki ci ba se dai ki tafi, dan wallahi ba zan bayar ba matsiyaciya algunguma tsohuwar karuwa"
Hawayen takaici ne suka fara zubo mata, ba abunda Ihsan ta gaya nata ne ya ɓata mata rai ba, rashin bata dankali ne ya baƙanta mata rai.
Ta fito daga part ɗin hannunta riƙe da plate tana kuka, har Imran ya shigo tana zaune da plate a gaba tana kuka.
Imran yace "Amira lafiya meya sameki haka?"
"Ihsan ce ta hanani dankali"
"Wane dankalin?"
"Dankali take soyawa nace ta sanmin ya hanani"
"To dena kukan ya isa haka"
Ya nufi part ɗin Ihsan, ya tarar ta gama grikinta, har tayi wanka yace "Ihsam meyasa kike hakane?"
Ta kalleshi tace "kamar yaya?"
"Ihsan meyasa baki da tausayi ne?, Amira kina kallo tana fama da rashin lafiya amma ko sannu ba ki taɓa ce mata ba, bata ko iya cin Abinci, amma duk da irin zaman da kuke tazo tace ki bata abu ki hanata, haba Ihsan"
'ni na mata cikin da zan girki in bata, bazan bayar ba ban niyya ba"
"Eh gaskiya ne, ni nai ciki, kuma ni nake nemowa in kawo gidan nan, dan haka baki isa ki hanani iko da abinda yake mallakina ba"
Yana gama maganar ya shiga Kitchen da kansa, ya zubawa Amira dankali yai waje.
"Imran kar ka bata Abinci na ba kai ka dafa min ba"
Ko saurararta be ba, yaje ya samu Amira ya bata, Amira kamar ta goya Imran dan murna, ta dinga cin dabkalin nan tana murmushi.
Allah ya temake ta harta gama ba tayi amai ba.
Ihsan ta koma ta shiga safa da marwa a ɗakinta, tana tunanin yadda za tai taga Amira ta rabu fa cikin nan, ko ta tsiya kota bala'i.
Ihsan fafur tace ba zata bi Imran ba, dan haka ya ƙyaleta, amma ana gobe ze tafi ya kai Amira gidan Anty, shi kuma ya tafi Lagos, lokacin cikintavya cika watanni uku cif.
Amira ta ɗanji dama dama komawarta komawar ta gidan Anty, duk da ba ta dena laulayin gaba ɗaya ba but, ta kan samu ta ci Abinci sosai.
Duk lokacin da Imran yake gida, yana kiran Amira ya ji ya jikin ta, sukan daɗe suna waya suna hira.
Ɓangaren Ihsan ma ya na kiranta, wataran ta ɗag suyi rigima, wataran kuma taƙi ɗagawa gaba ɗaya, duk ta maida hankalinta kan yadda za tai ta raba Amira da cikin nan, kuma ta koreta.
Wataran da daddare Anty tace "Amira, sako mayafinki muje gidanku"
Amira ta kalli Anty da mamaki tace "wane gidan namu?"
"Gidan su mijinki mana"
Take gaban Amira ya faɗi, saboda tasan karan batta ta da Ammi ba daɗi.
Bata son yiwa Anty musu, dan haka ta ɗau mayafinta suka fita.
Anty tace "Abban ku yana gari ne, ya dawo, kuma ya daɗe baya gari, shiyasa nai girki za mu tsaya a hanya mu sai fruit, muje ki gaishe shi"
Hankalin Amira ya ɗan kwanta ta, jin Abba yana gari ta san Ammi ba zata mata komai ba.
Tace "Amma naji daɗi, kwana biyu ban ganshi ba"
"Ai shiyasa nace muje tare".
Da suka je gidan, Anty ta riƙo fulasan kayan Abinci, Amira ta riƙe ledojin kayan marmari, tana gaba Anty na biye da ita.
Amira tai knocking ƙofar falon, Minal ce ta zo ta buɗe ƙofar, tana ganin Amira ta haɗe rai tana mata kallon banza.
Amira ma haɗe rai tayi, tace 'ban Guri in wuce"
Minal za tayi magana kenan, taga she tare suke da Anty, dan haka tai shiru.
Suka shiga falon, cikin sa'a kuwa Abba yana falon a zaune yana kallo.
Yana ganinsu yai murmushin yace "manyan baƙi ke tafe a daren nan?"
"Gamu nan dai, nace bari muzo mu kwashi gaisuwa"
"Ahh Lallai kun kyauta, ina mutumin nawa ko baya gari?"
Anty tace "Ai Daddy kusan watansa uku be zo ba, Hajiya Jamila ina yuni?"
Ammi ta ɗan yatsina fuska sanan ta amsa.
Amira ta gaida Abba sannan ta gaida Ammi.
Sun daɗe suna hira a gurin, Abba yace "tunda 'ya ta ta kawon Abinci, Minal zoki ɗau naku Abincin nata zanci"
Amira tace "Abba ni zanci nakan"
Yace "shikenan kinga anyi musaya"
Suka yi dariya, Minal ɗakinta ta tafi dan takaici, dan ta tsani Amira akanta Yayanta a mareta kuma ake wulaƙnta Ihsan.
Se kusan goma da rabi sannan suka tafi, Abba yaita sawa Amira Albarka yana wa Anty godiya.
Bayan tafiyarsu Ammi tace "daka sa ba zaka ci Abincin nan ba be kamata ka sa in girka ba"
Abba yace "Jamila, ke kina da kunyar yi min Magana ma? Ace ina nan da raina, amma matar abokina ita ke ɗawainiya da 'yar 'yar uwata wadda take 'ya a gurina, kinji kunya Jamila, kallonki kawai nake, ba irin wahalar da ban miki ba ke da 'yan uwanki, amma ni kin gaza min kara akan'ya guda ɗaya Nagode"
Yana gama maganar ya tafi ya barta a gurin.
Se da Imran yai wata biyu be dawo ba, cikin Amira harya fara fitowa, tunda ya tafi basu kuma haɗuwa da Ihsan ba.
Ranar da yai mata waya ze dawo kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha dan murna, nan taje gyaran kai da lalle, tace za ta koma gida saboda dawowar Imran.
Ana gobe ze dawo Anty tace "ba zan bari ki tafi ke kaɗai ba, ban san me zasu miki ba, ku tafi da Fadila, idan ya dawo ta taho.
Haka Fadila tabi Amira gidan, su kaita shirye shiryen karɓar Imran, sedai tun da tasa ƙafarta a gidan, Ihsan ta fita ba ta sake dawowa ba se Ranar da Imran ɗin ze dawo.
Ranar da ze dawo da safe Fadila ta bar gidan, ta koma gidansu.
Se wajen huɗu na yamma sannan ya dawo, Amira ta sha kwalliya se zuba ƙamshi take, ta kame a falo.
Yana shigowa da ita ya fara tozali, ta ƙara haske ga cikinta ya fara tasawa.
Da gudu taje ta rungume shi, shima rungumeta yai yana cewa "I miss You Baby"
"Miss you too my dear, ya baby na?"
"Shima yayi missing ɗin ka" ta faɗa tana dariya.
Dan kar Ihsan tai surutu, ya je part ɗinta, sedai ba wata tarbar kirki ya samu daga gurinta ba, dan bata sauya zani ba.
Shi kuwa ya koma ɓangaren Amira, yaci ya sha yai wanka, Amira na ta nan nan da shi.
Ko da dare yayi be ko kalli in da Ihsan take ba, yai zamansa a part ɗin Amira.
Sun kwanta kenan, ya janyo ta jikinsa yana "I Miss You Lovely dear"
"Miss you More"
Tai maganar tana rungumeshi, sedai tana rungumeshi ta saki wani razanannen ihu, ta zabura ta tashi daga jikinsa tana ihu.
KUYI HAƘURI BANYI EDITING BA NAYI BUSY OVER
Ayshercool
07063065680.
[2/18, 9:32 PM] Ayshercool:
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
WUTA A MASAƘA
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P. W. A
*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA)
*BAƘIN TABO (Labarin gasa)
*AƘIDATA (Paid Book)
* WUTA A MASAƘA
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in
❌❌❌
Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.
49_50
Imran ya kalli Amira a gigice yace "Amira meye haka? Lafiya kuwa, meyafaru?"
Cikin kuka tace "wani abu naji a jikinka kamar ƙadangare"
"Ƙadangare kuma Amira? Bakomai a jikina fa"
"Wallahi ƙadangare ne a jikin ka"
Ya tashi ya kunna fitla, ya cire vest ɗin jikinsa, ya juyo mata bayan yace "kin gani bakomai a jikina"
Ƙirjin Amira se dukan uku uku yake ta na sake ƙare masa kallo, tabbas bakomai a jikinsa, amma ita kam taji tamkar ƙadangare ne a jikinsa.
Da ƙyar ya lallaɓata ta yadda ba komai a jikinsa, ta dawo ta kwanta, a cikin matsananciyar fargaba ta yadda da Imran, dan gani take kamar da ya taɓa ta zata ga ƙadangaren.
Imran ya manta da batun ƙadangare, ya sha soyayyar sa, sedai har sukai wanka bacci ya ɗauke shi Amira ba tai bacci ba.
Ta dinga juyi tana karanto duk Addu'ar da ta zo bakinta.
Can bacci ya ɗauketa, sedai tai mafarki ƙadangaru sun babibaye jikinta, haka ta kuma tashi a razane tana gumi, ƙarshe haka ta kasa bacci, har Asuba tayi.
Gaba ɗaya fargabar komawa baccin ma take, dan haka ta zauna akan dadduma ta cigaba da lazimi, gari na yin haske ta fita Kitchen ta ɗora breakfast.
Har ta kammala Imran yana baccin sa, seda tai wanka ta shirya tsaf tai kwalliya cikin ƙananan kaya, sannan ta tafi bedroom ɗin da Imran ke kwance, ta kunna turaren wuta.
Ta hau gadon da yake kwance, ta ɗan yaye bargon jikinsa, ta hau kansa tace "My cwt Amran, wake up na, babyn ka na jin yunwa fa"
Murmushi yai ya sake gyara kwanciyarsa, itama murmushin tayi, ta zira hannunta cikin bargon da niyyar ta rungumoshi, sedai taji ta danƙi ƙadangare.
Take ta zunduma ihu, ta dire daga kan gadon da gudu tana kurma uban ihu.
A zabure ya miƙe yace "Amira lafiya wai? Meye hakane?"
"Wallahi ƙadangare ne a jikin ka"
"Wai wane irin ƙadangare ne haka? Bakomai a jikina, ki kwantar da hankalinki"
Yai maganar yana ƙoƙarin tunkaro ta, amma ta sake fasa ihu a gigice tace "ba ga ƙadangaren nam yana bin ka ba, kar ka zo in da nake, gashi nan ina kallo yana binka"
Wan ƙaton ƙadangare Amira ke gani a jikin Imran, girmansa ya shallake girman ƙadangaren da take gani a zahiri, gashi a duniya Amira ray tsani ƙadangare.
Ganin Imran ze tinkaro ta yasa ta jiya ta zura da gudu Falo tana ihu, ihun Amira da Ihsan ta jiyo ysa ta fito da sauri.
Garin gudu Amira tai gware bango, ta faɗi a gurin, amma ta miƙe ta kuma sheƙawa a guje.
Imran ya biyo ta yana "dan Allah Amira ki tsaya, kar ki jiwa kanki ciwo ko abunda ke cikinki"
Ina idonta ya rufe tai waje da gudun gaske, kan ta je gate Imran ya cin mata, ya riƙota gam.
Wata gigitacciyar ƙara ta saki, tamkar wadda ake yayyanka wa da wuƙa, ganin Imran yana nema ya ɗorata a kan ƙadangaren da ke jikinsa.
Silalewa tayi sumammiya a jikinsa, cikin damuwa ya ɗauke ta zuwa falo, ya shimfiɗe ta.
Ya ɗaga kai ya kalli Ihsan da ke binsu da ido yace "Ihsan dan Allah bani ruwa in shafa mata ko zata tashi"
Wata uwar harara ta banka masa ace "Allah ya kiyaye, Allah yasa daga haka ma ta mutu, alhakina ne ya kamata koma menene"
Ta ja tsaki tai tafiyarta, seda Imran ya buɗe baki dan mamaki, ya tashi ya shimfiɗe Amira, ya tafi fridge ya ɗakko ruwa me sanyi, yazo ya fara shafa mata.
Ajiyar zuciya ta ding saukewa, a hankali yace "Amira kina gani na"?
Da sauri ta buɗe ido, tana ganin Imran ta miƙe zumbur daga jikinsa, ta fara ja da baya tace "dan girman Allah ka dena zuwa in da nake, kaje ka cire ƙadangaren da ke jikin ka, dan Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ka tashi ka bar falon nan, kaje ka cire abun da ke jikin ka"
A ɗimauce Imran yace "Amira, jikina ba komai ni bana ganin komai fa"
Kuka ta sake fashewa da shi tana ja da baya, tana ƙoƙarin miƙewa ta sake artawa a na kare.
Ya nufo ta da sauri ze sake riƙeta amma ta faɗi a gurin.
Yasa hannu ya ɗauke ta, ya maida ita falonta, yaje ya kwantar da Ita.
Ya ɗakko wayarsa ya kira Abba, bugu biyu Abba ya ɗaga yace "Soja marmari daga nesa"
"Abba akwai matsala"
Abba yace "subhanallah, matsalar me?"
"Abba Amira, na easay meke damunta, tun jiya take koke koke tana ihu, sam na kasa gane kanta"
"Innalillahi wa innalillahi raji'un, Amiran meya sameta?"
"Ban sani ba Abba, da naje kusa da ita take fara ihu, na rasa meke damunta"
Abba yace "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Allah ya kawo mana ɗauki, gashi ina Kebbi yanzu haka, amma kira antynta a waya ka mata bayani, duk yadda ake ciki ka gayamin"
"To Abba Nagode"
ya katse wayar ya kira wayar Anty, Anty ta ɗaga da sallama, ko gaisjeta be tsaya yi ba yace "Anty Amira ba lafiya fa"
"Subhanallah jikin ne?"
"Anty tun jiya take ihu, na kasa gane kanta yanzu haka tana sume ne, sam ba ta son ko in da take inje fa"
"Yasalam, gani nam zuwa, kwantar da hankalinka gani nan"
Imran ya ajiye wayar yana cigaba da kallon Amira, dake numfashi kaɗan kaɗan.
Befi mintuna arba'in ba, sega Anty ta iso a kiɗime, kai tsaye ta nufi ɓangaren Amira, taje ta tarar da ita a kwance kamar gawa, Imran ya zuba mata ido yayi tagumi.
Anty tace "Imran, meya sami 'yata?"
"Anty nima ban sani ba, gaba ɗaya taƙi tsaywa ma in fuskanci meke damunta, se ihu kawai take'
Anty taje ta kama hannun Amira, ta ɗaure ta nemo jijiya tai mata wata allura, Sannan ta sa Imran ya dinga shafa mata ruwa me sanyin gaske.
Wata irin ajiyar zuciya tayi, kamar za ta shiɗe Sannan ta koma numfashi normal.
A hankali Amira ta buɗe ido,ta kalli Anty tace "Anty yaushe ki ka zo?"
"Yanzun nan Amira, mijinki yai min waya ba ki da lafiya, kinga bani da kwanciyar hankali kenan"
Amira za tai Magana idinta ya sauka a na Imran, aikuwa ta zabura ta ƙanƙame Anty tana salati.
Anty tace "Amira lafiya kuwaa?"
"Anty dan Allah ke ki gaya masa ko zeji, ki ce masa yaje ya cire ƙadangarem da ke jikin sa wai shi baya ganinsa"
Anty tace "wani irin ƙadamgare kuma? Ai bakomai a jikinsa"
"Wallahi akwai, wai Anty kema ba kya ganinsa ne, dan Allah karku ce nika ɗai nake ganinsa, gashi nan a kwance a ƙirjinsa fa"
Anty tace "shikenan yi shiru, Kai Imran nima naga ƙadangarwn nan, kaje ka cire shi daga jikinka"
Anty tai maganar tana ƙiftawa Imran ido.
Imran jiki a sanyaye ya bar falon yana waiwayen Amira.
Anty tace "ya tafi cirewa, ki kwantar da hankalinki ki yi ta Addu'a kinji?"
"To Anty ina yi, nace masa yaje cire ƙadangare a jikinsa, amma yaaƙi kuma binsa yake"
Anty tace "ai yanzu yaje cirewa, tashi ki karya, naji yace baki ci komai ba"
Amty ta zubawa Amira Abinci, ta sata a gaba taci.
Imran kam
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 27 Chapter of 31