Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ba mutuniyar banza bace, wahala ce ta maida ita haka, kuma insha Allah in har ina numfashi, Amira ba zata tagayyara ba, zan zame mata uwa uba ɗan uwa sannan kuma miji, insha Allah wahalarta ta zo ƙarshe, ba zata sake kukan maraici ba" Yana gama maganar yasa hannu ya ɗago ta tana ta uban kuka, ya janyo hannunta za su fita daga ɗakin. Baffa Salahu ya riƙe ƙafar Imran yace "dan girman Allah Imran kuyi haƙuri,  kasa baki ta yafewa Yadikko" Imran yace "wannan ba hurumi na bane, ruwanta ne ta yafe mata, ruwanta ne ta ƙyaleta, amma da kasan iya wahalar da ta sha tsayin watanni uku zuwa huɗu akan larurar da tayi ta isa Allah ya kamata, banda azabtar da ita da ku kai tun ƙuruciyarta banda yarfe da ƙage da kuka dinga mata, dan kawai marainiya ce, mahaifiyar ta ta auri mahaifinku, ni ba zan tulasta mata ba, tana da damar yin abunda ta ga shine dai-dai" Ya ja hannun Amira suka fito, Sadiya ta taho da sauri gaban su Amira tana kuka tace "Amira dan Allah ki yafemin, kar inje abun da ya samu su Yadikko nima ya sameni, dan Allah ki yafemin Amira" A fusace Amira tasa hannu ta haɗa Sadiya da jikin bango tace "duk irin azabtarwar da kukamin a gidan nan, na yi iya ƙoƙarina akan in danne zuciyata, in maida komai ba komai ba, saboda mun fito tsatso ɗaya da ku, duk ƙyama da wariya da kuka dinga nunamin, amma ban taɓa zaton zaku iya aikatamin abunda ku kai min yanzu ba, bazan yafe muku ba na barku da Allah, Allah ya bi min hakkina" Imran ya janyo Amira, dan yaga a zuciye take matuƙa kar tai masa asarar Babynsa, dan yaga yadda jikinta yake rawa, da yadda ta janyo Sadiya kamar ita kaɗai ce ba cikin a jikinta. Waje yai da ita, ya sakata a mota ya rufe ya zaga ya shiga ya kunna yaja motar. Suna tafe tana kuka, Hannu ɗaya yana tuƙi ɗaya kuma ya rungumota yana rarrashin ta yace "Haƙiƙa rayuwarki darasi ce Amira, gaba ɗaya mutane na miki kallon baibai, a yayin da idan aka duba aka zago laifin na masu aibataki ne, kinyi rayuwa a wahale ba tare da mataimaki ba se Allah, ni kaina ina Nadama akan abubuwan da suka faru a baya, amma Please and please Amira, kiyi haƙuri ina ƙara naman afuwarki a karo na babu adadi, saboda nayi zaton WUTA A MAƘERA katsam sega WUTA A MASAƘA. Amira zuciyarki me kyau ce, kina da haƙuri da yafiya, nasan an cutar dake, amma insha Allah ba zan sake bari ki zubda hawaye akan rashin wani abu ba, insha Allah zan rayu da ke da zuciya ɗaya, zan faranta miki iya gwargwadon iyawata, kiyi haƙuri ki dena kuka" Cikin kuka tace "Imran" "Na'am Amira" "Imran me na yiwa Yadikko? Laifin me nayi mata? Meyasa zata min haka? Imran duk yadda zan kwatanta maka ba zaka gane azabar da sukamin ba, why? Laifin me nayi mata haka?" Tai maganar tana sake rushewa da kuka. Parking Imran yai ya shiga share nata hawayen yace "ba abunda ki kai musu, sedai ki gode Allah ke 'yar gatan Allah ce, ya dubi zuciyar ki ya sa abunda sukai miki be tasiri akanki sosai ba ya mayar musu abunsa kansu, kuma ya ganar da mijinki abunda suke faɗa akanki ƙarya ne, ina sonki Amira son da bazan iya musalta miki ba, kuma har gobe ina jin nauyin ki akan laifin da nai miki, ki kwantar da hankalinki kinji Cwthrt, ki dena kukan nan komai ya wuce, mu koma gida mu buɗe sabon shafin rayuwa me cike da Soyayya da ƙaunar juna" "Thank you my Brother" Tai maganar tana murmushi, cikin son nunawa Imran ta gamsu da maganganun sa. Yace "Never mind Dear, me zamu tsaya mu siya kici ne nasan kin fara jin yunwa yanzu?" "Muje gidan Anty Fa'iza" ta bashi amsa. Imran ya ja mota zuwa hanyar gidan Fa'Iza, duk da haka suna tafe Amira na share hawaye, ya fuskanci zubar da hawayen shine samun sauƙinta, dan haka be cigaba da takura mata ba ya ƙyaleta. Suna zuwa gidan Fa'iza yai parking, ba ta ce masa komai ba ta buɗe motar ta fita, ta shiga gidan. Da sallama ta shiga ta tarar da Bashir yana wankin kayan su, Fa'iza kuma na Kitchen tana girki. Itama Fa'iza na ta cikin ya tsufa, dan yafi na Amira tsufa ma, da ƙyar take tafiya haihuwa ko yau ko gobe. Fa'iza na ganinta tai murmushi, tace "lallai yarinyar nan, zuwa ba sanarwa to koma bana murna da Zuwan" Bashir yace "ba ina da zata koma, duk da ni kunya ma naji, ban taɓa zuwa gidanta ba amma ina maraba da zuwan nata" Yaran Anty Fa'iza kuwa da gudu suk tafi suka rungume Amira, Amira ta rungume su, sedai ta kasa Magana. Fa'iza tace "Khairat ƙyale Amira baki ga halin da take ciki ba, kar ki buge mata kan ɗa" Duk yadda Amira ta so dakewa kasawa ta yi, ta fashe da kuka a gurin. Bashir yace "Subhanallah, Amira Lafiya kuwa? Meyafaru kuma?" Kasa magana Amira tayi, se cigaba da kukan tana daga tsaye. Fa'iza ta kama hannunta suka shiga ɗaki, tace "Amira lafiya kuwa? Ko Imran ɗin ne yai miki wani abun?" Ta girgiza kai tace "tare muke yana waje ma" Bashir yace "Amma kika barshi a waje? Amma ina fatan lafiya dai" "Anty Fa'iza, kin san rashin lafiyar da nayi aka ɓoye miki kusan taɓin hankali na samu, wata na uku ko in da nake ba na son Imran ya zo, wai ashe Yadikko ce tai min Asiri, aka kirani jiya ba ta da lafiya na tayar masa da hankali se da ya kawoni yau, shine take gayamin asiri tai min? Me nayi mata haka?" Amira tai maganar hawaye na zuba daga idonta, Fa'iza tace "Amira ki ɗauka wannan jarrabawar ki ce a haka, shekaranjiya naje gidan, da bakinta nima take gayamin ita tai miki Asiri, wanda ni ban san ma takamaiman rashin lafiyar da ki kai ba, Abba ya ɓoyemin kema da kika warkw baki gayamin ba, ance min kawai laulayi ne kike, na kaɗu matuƙa da jin abunda Yadikko ta gayamin, sedai ban miki zancen bane dan bana son tayar miki da hankali, Ba abunda za muce wa Allah se godiya da Allah yasa abun beyi tasiri akanki sosai ba" Amira tai shiruu tana cigaba da jin yadda zuciyarta ke cigba da bugawa, da zunzurutun mamakin abunda Yadikkon ta aiakata mata. Bashir ne yaiwa Imran iso, ya shigo Gidan, nan suka cigaba da tattaunawa gami da jajantawa juna akan abunda ya samu Amiran. Fa'iza tai musu girki, suka ci Abinci su kai salla, sannan suka kama hanyar komawa Kaduna, sedai suna fitowa daga unguwar su Fa'iza sega Sultan a babur ze wuce. Da sauri Amira tace "Amran tsayar min da Sultan mu gaisa dan Allah" Imran ya sha gaban hanyar da Sultan ze wuce da mota, aikuwa a fusace Sultan yace "malam meye haka? Ko dan kaga kana mota shine zaia min wannan gangancin?" Imran na sauke glass Sultan ya ganshi, gabansa ya faɗi dan be manta shaƙar da Imran ya taɓa masa ba. Imran yai murmushi ya miƙa masa hannu, a tsorace Sultan shima ya miƙa masa hannu, yana son tabbatar da ko dai ba Imran bane gizo yake masa. Imran yace "ƙanwar ka ce tace in tsaya ku gaisa" Yana gama maganar sega Amira ta fito daga motar, Sultan na ganinta ya kafe babur ɗin ya sakko yace "Gimbiya Amira kece?" "Nice Sultan, ka watasar dani gaba ɗaya" Sultan ya sosa kai yace "ke tsoron mijinki nake ji shiyasa, kuma kinga kinyi Aure be dace in dinga bibiyar ki ba" Imran ya fito daga motar yace "ka de na tuna baya, wannan ya wuce ai, kuma Amira ta gayamin dukkanin alaƙar dake tsakanin ku saɓanin ni wadda aka gayamin, kuma nagode Sosai da gudunmawar da ka bata a rayuwa, duk da ta wani fannin gudunmawar ba ta arziki bace, amma duk da haka ka temaketa, Nagode sosai, kuma ba zan yanke zumuncin da ke tsakanin ku ba, insha Allah duk ran da muka zo Kano, zan nemeka ku gaisa" Sultan yace "Alhamdilillah, Allah sarki rayuwa, inaiwa Amira burin Auren mutumin daze kula da ita, saboda wahalar rayuwa da ta sha, da fari banji daɗin Aurenka da ita va, amma yadda na ganta ya tabattar min tana cikin nutsuwa sosai, Allah ya ƙara haɗa kanku ya baku zaman lafiya" Imran yace "Ameen ya Allah, nagode Sosai Sultan" yaiwa Sultan alheri sannan suna tafi. Amira tace "meyasa ka yadda muka gaisa da Sultan, har ka masa alheri ka yadda da cigaban zumuncinmu?" Imran yace "Saboda na baki dukkanin yarda Amira, na san ko bana raye ba zaki zubar da mutuncinki ba, sannan Son da Sultan yake miki gamon jini ne kawai, ba sonki yake dan ya Aureki ba, yana sonki dan tausayin ki ne, kuma tare na ganku, dan haka be kamata in datse zumuncin ba, kuma insha Allah zan cigaba da bibiyarsa in ga ta inda zan temaki rayuwarsa, kamar yadda ya temaki taki da koya miki rashin ji" Murmushi Amira tayi da seda haƙoranta suka bayyana, a lokaci guda kuma hawaye na bin kuncinta. Imran yan cigaba rarrashin Amira, yana sake kwantar mata da hankali da bata tabbacin zeyi iyayin sa, dan ganin ta samu farincikin da bata samu a baya ba. Amira ta nisa tace "Amran, na yadda da duk abunda ka faɗamin, sedai haryanzu ina da sauran damuwa sosai" "Damuwar meye?" Ya tambaye ta. "Har yanzu Ammi ba ta ƙaunata, sannan bana son kaiwa Ihsan irin abunda kaimin nasani babu daɗi, ni idan na yafe maka ita ba lallai ta iya yafe maka ba" Haɗe rai Imran yayi yace "me nayi mata?" "Ka dena shiga sabgarta, ka dena zuwa inda take gaba ɗaya, ranar kwananta ba ka zuwa inda take sedai ka kwana a ɗaya bedroom ɗin nawa, baka cin Abincin ta, wannan abun babu daɗi sam, nasan ciwon hakan dan Allah kayi haƙuri ka koma mata, kar a shiga hakkinta, bana son Allah ya kama ka da laifin rashin adalci" Kallon Amira yai, yana jinjinawa haƙurinta, yai murmushi yace "'yar aljanna kenan, Allah ya barmin ke Amirana, kullum zuciyarki fes kamar Abba haka kike" "Naji kana neman ka maida abun jokes" "Au aljannar ce jokes Amira?" "A'a ba haka nake nufi ba, But atleast ya kamata ka ɗau maganar tawa da mahimmanci" Yace "serious na ɗau maganarki Amira, Ammi zata gane abunda takeyi kuskure ne nan ba da daɗewa ba, sedai kamar yadda kika fuskanci ƙaddara a taki rayuwar, nima Auren Ihsan ne tawa ƙaddarar" Ta kalleshi da mamaki tace "kamar yaya kenan?" Gaba ɗaya annurin fuskar Imran ya ɗauke, damuwa ta maye gurbin fuskar tasa, idanunsa su kai jawur yace "Amira a zamana da Ihsan, na mata dukkanin adalcin da zaka iya yiwa abunda kake so, kina kallo saboda ita na biye mata na kasa sauke  naki hakkin da ke kaina, sedai ina tunanin wuta a maƙera se ga WUTA A MASAƘA!" Amira tace "nifa ka sani a duhu, me kake nufi ne?" "Zaki gane very soon, but let's keep this aside, Bana son Maganar gaba ɗaya" Se bayan la'asar sosai sannan suka isa Kaduna, a part ɗin Amira suka sauka, yai ya jasu jam'i sukai sallar la'sar tare. Amira tace "My me zan ɗora maka ne, nasan kana jin yunwa yanzu" Imran ya kalleta yace "No, ba zaki wahalar min da kanki da Babyna ba, zanje in mana takeaway" Amira ta ɗan yatsina fuska tace "nifa kasan ban fiye san Abincin siyarwa ba". "Ni kuma baza'a wahalar min da mata da ɗana ba" Amira tace "masu mata da ɗa manya" Tai Maganar tana murmushi ta shafa cikin nata tace "Allah ne yayi cikin na da nisan kwana, da tuni babu shi" "Ai ba ƙaramin godiya nake wa Allah ba, ni kaina nasan ikon Allah ne ya riƙe cikin nan, ina fatan Allah ya ƙara inganta mana shi, ya rabaku lafiya" "Ameen my Amran" Haka suka cigaba da hira se daf da magariba sannan ya tashi ya fita salla, daga nan ya samo musu abunda zasu ci. Amira ta tashi gaba ɗaya jikinta a sanyaye yake, ta shiga banɗaki tai alwala ta fito tai sallar magariba. Tana kan daddumar da tai salla tana lazimi, taji ana kurma ihu a falo, da hanzari ta miƙe ta fito falon da sauri. Sedai me tana fitowa ta ci karo da Imran ya shaƙo Minal da hannu ɗaya yai jifa da ita, yana dukan Ihsan kamar jaka. Da saurin gaske Amira tai kansa, tana faɗin "lafiyarka kuwa? Meye haka kake matarka ce fa da ƙanwarka" Ba shi da niyyar saurarar Amira, dan tamaula kawai yake da Ihsan, Amira ta nufe shi ta riƙe shi, amma ya hankaɗeta Allah ya temake ta ta faɗa kan kujera akan hannunta, amma duk da haka seda taji ɗan cikinta ya juya. Seda ya dake su iya yinsa, tun suna ihu har suka kasa gashi Imran ya kulle ƙofar falon. Kawai ya koma gefe ya zauna akan kujera yana zub da hawaye. Amira ba tayi fushi ba ta sake jan jikinta, ta ƙarasa in da yake tace "haba dan Allah, meyasa zaka mus wannan dukan haka? Me sukayi maka? Kuma ka zauna kana kuka why? Ka sani a duhu" Imran kasa Magana yai, ya kuma kallon Ihsan baƙin ciki ya kuma mamaye masa zuciya. Ya sake tashi a fusace ya dinga takata da ƙafarsa. Amira ta firgice Sosai, ta koma part ɗinta, ta ɗau waya ta kira Abba yana ɗagawa tace "Abba dan girman Allah idan kana gari ka zo gudanmu, wallahi Imran ze kisan kai, ya sumar da Ihsan yana nema ya kashe Minal, dan Allah ka zo" Abba gaba ɗaya ya rikice yana ƙoƙarin sake tambayar ta, amma ta kashe wayar, ya miƙe a razane Ammi tace "lafiya kuwa?" "Ina fa lafiya wai Imran yana can ya sumar da Ihsan, ya shaƙe Minal" "To me sukai masa?" "Nima ban sani ba, bari inje gidan inji" Ammi tace "A'a muje dai tare inji ba'asi, in ka barni ai hankalina baze kwanta ba" Nan ta ɗakko hijjabinta suka nufi gidan Imran. Amira na katse kiran ta fito falon da sauri, amma babu alamar sassauci a tare da Imran, dan yanzu Minal yake ta gwarawa a bango. Sake gigicewa Amira tai, ta kira Anty a waya tana kuka, tace "Anty dan girman Allah idan Daddy yana nan ko wani yazo yaiwa Imran Magana, ze kisan kai wallahi" "Amira wace irin kisan kai kuma?" "Wallahi Anty ze kashe su Ihsan na kira Abba haryanzu be zo ba" Gaba ɗaya hankalin Amira ba a kwance yake ba, dan haka ba tai mata wani Bayani sosai ba, hakan yasa itama Antyn ba shiri ta nufi ɗakin Daddy ta taso shi. Gaba ɗaya Imran a gigice yake, zuciyarsa wata irin tafasa take ji yake tamkar ya kashe Ihsan ya huta. Dan Ihsan ko motsin kirki ba ta iyawa, da ƙyar take sauke numfashi, dan tasha duka, Minal kuwa bakinta se fidda jini yake. Imran ya koma gefe ya zauna ya dafe kansa, jikinsa na wata irin tsuma. Amira kam komawa gefe tayi ta zuba masa ido, tare da bin su Minal da ido, tana mamakin laifin da sukai masa haka. Suna nan zaune aka fara buga ƙofar falon, Amira ta kalli ƙofar taga a rufe take, bata san in da ya ajiye mukullin ba. Yana ji ana bugun ƙofar, amma yai banza se da ya gaji da jin bugun, sannan ya tashi jiki a sanyaye yaje buɗe ƙofar falon, Anty ce da Alhaji Hashim, Anty ta shigo tana faɗin "Imran lafiya kuwa? Meke faruwa ne haka?" Imran be ce komai ba ya wuce cikin falon ya zauna. Alhaji Hashim ya kalli inda su Minal ke baje, suna numfarfashi yace "Imran meke faruwa haka a gidanka?" Imran yai shiru be Magana ba, ana cikin haka sega su Abba sun iso gidan. Mamaki ne ya kama Ammi ta nufi inda Minal take da sauri tace "Imran meye haka? Me kai musu me sukai maka haka?" Shiru Imran yai ya zubawa Ammi ido. "Ba Magana nake maka ba? Me kayi haka? Ina fatan ba akan wannan ballagazar Yarinyar kai musu wannan abun ba?" Abba yace "Imran, kai magana mana" Imran ya share Hawaye yace 'bazan Magana ba, se an kira mahaifiyar Ihsan da wan mahaifinta tukuna" Alhaji Hashim yace "meyasa se an kirasu mu bamu isa ba?" Anty tace "bamu san meyasa yace haka ba, a kira su kawai" Haka akayi aka kira Iyayen su Ihsan, sedai lokaci lokaci Imran yana share hawaye. Gaba ɗaya abun ya ɗaure musu kai. Ba jimawa se ga Mummyn Ihsan da wan mahaifinta. Suma abun ya basu mamaki ganin yadda aka hallara haka da yawa a falon. Mummy tace "lafiya kuwa?" Anty tace "muma abunda muke son ji kenan yace se kunzo" Abba ya kalli Imran yace "to muna sauraren ka" Imran ya ƙurawa Ihsan ido sannan yace "ki gaya musu abunda ki kai min" Girgiza kai ta shiga yi tace "Imran dan Allah kayi haƙuri ka rufamin Asiri, karka tona min Asiri" "Ihsan na baki duk wata dama da zan iya, kallonki kawai nake, amma hakan be sa kin fuskanci na san me kike ciki ba, yau an kai point ɗin da ba zan iya jurewa ba, kuma ina tabattar miki daga gurin nan, zaki ƙara gaba ki barmin gida na" A gigice Ihsan ta shiga girgiza kai tace "dan Allah Imran kayi haƙuri, kar kaimin haka" A fusace Imran ya kalli Minal yace "ke  se ki gaya musu abunda ku kai" Girgiza kai Minal tayi tana kuka, amma ta kasa Magana. Abba yace "to kai ka gaya mana, mana muna jinka kuna tai mana wasa da hankali" Imran yace "Abba, lesbian na kama Matata da ƙanwata su nayi red-handed, a gadona na Aure bayan ta ƙauracemin sama da watanni, Abba matata da ƙanwata fa" Tsit kowa yayi, se tashin salati da Sallama da ke tashi a falon. Amira kuwa gani tai be dace ya musu wannan tonon Asirin haka ba, dan tun kan ya sani ta san Abunda Ihsan take, tun lokacin da suka haɗu a Abuja, ta ganta a Hotel ɗin da ta sauka, tare da wata hamshaƙiyar mace dai tai suna a dandalin sada zumunci, kuma wadda ake raɗeraɗin sana'arta kenan. Ammi tace "ƙarya kake Imran, wannan sharri ne ban yadda ba" "Ammi wace riba zan tsinta idan na musu ƙarya? Ga su nan ki tanbaye su mana, Ana zaton WUTA A MAƘERA sega WUTA A MASAƘA, wane irin cin mutuncin ne ba'ayi wa Amira ba ana ce mata Karuwa? Duk da ku Iyaye ne a gurina, amma ranar wanka ba'a ɓoyen cibi, ni na fara sanin Amira mace, ba karuwa bace, yau daga Kano muke gurin duba kakarta, duk rashin lafiyar da Amira tayi ita tai mata Asiri, kuma da bakinta take faɗar Amira ta yafe mata saboda ƙagen da ta dinga mata, Ammi ki tambayesu idan ƙarya nayi musu?" Ammi tace "Minal da gaske ne abunda yayanki yake faɗa?" Minal ta jinjina kai cikin kuka, Ammi ta ɗora hannu a ka ta fashe da kuka tana salati. Anty tace "Alhamdilillah ala kulli halin, tunda Allah ya wanke Amira, kuma ni tun zamanta a gurina na tabattar da ba karuwa bace, wannan shine abun da turawa ke cewa 'Never judge book according to it's cover' sannan Magana ta biyu Imran haƙuri za kayi, ka rufawa matarka da ƙanwarka Asiri, ka cigaba da zama da ita kayi haƙuri" Imran yace "over my dead body, i already write her divorce, bata ne kawai ban ba, ina tunanin in bata ko in yafe mata, Yarinyar nan ba kalar rashin mutunci da cin fuskar da ba tai min ba, a fari na biye mata ita da mahaifiyata na dinga muzgunawa Amira, daga baya komai ya daidaita, ita kuma ta juyan baya da wulaƙanci da cin mutunci, da fari Ihsan was not virgin, seda ga baya na gane, amma na rufa mata Asiri ban nuna mata ba, secondly na ganta da ɗinki a cikinta nace mata meya sameta, tace min an taɓa mata aikin appendicitis ne, ashe ba haka bane, mahaifa aka cire mata, amma ya Aureni a haka ban sani ba, badan mahaifina ya auramin Amira ba haka zan cigaba da zama da ita ban sani ba, likitan da yai mata aikin was a military doctor, mun haɗu a Lagos muna tare da ita, daga baya ya gayamin shine likitan da yai mata tiyatar nan, se kuma yau na kamata red handed da ƙanwata, Ihsan me nayi miki haka?" Nana aka shiga kallon kallo, aka rasa wanda ze fara Magana, da kyar Alhaji Hashim yai jarumta yace "Ihsan muna son ji daga gareki, meye gaskiyar abunda Imran ya faɗa?" Ihsan tana hawaye tace "Imran be ƙarya ba duk abunda ya faɗa hakane, bayan rasuwar mahaifina babu wanda ya damu dani da mahaifiyata, ba wanda yake kula damu, kowa ta kansa yake kawai, ana haka Mummy ta fara bin gidajen Manyan masu kuɗi tana wanke wanke, idan na tashi daga makaranta ina binta gidan aikinta, abunda ake biyanta na albashi be taka kara ya karya ba, baya isarmu buƙatunmu na rayuwa. Katsam megidan yaje mata da wani batu, yace akwai aikin da aka bashi zeyi, amma da ƙaramar Yarinya ake so kamar ni, lokacin ina da shekaru goma sha biyar, yace ze bata kuɗi naira dubu ɗari biyar, ba tunanin komai ta amince, mutumin nan ya tafi dani, ya dinga amfani da ni ta bayana, da sunan yana neman wata biyan buƙatar da bokaye sukace se yayi hakan. Nayi kuka nayi kuka akan hakan, amma dana gayawa mahaifiyata sam bata damu ba, hankalinta yana kan abunda mutumin nan yake bata ne kawai, ya canza min makaranta zuwa ta kuɗi, ya sani a Islamiyya me tsada wadda a nan na sauke Alqur'ani na haddace wani sashi, duk lokacin da ya bushi iska ze nemeni ya danƙara mana kuɗi masu yawan gaske, wasu lokutan har Abuja yake tafiya dani. A haka ana wannan haramtacciyar alaƙar matrsa bata sani ba, ita kuma ta janyo mahaifiyata tana sama mata 'yan aiki ta kaisu gidan ƙawayenta, amma a baɗini less ake dasu, itama matar gidan ta fara bibiyata tana nemana, tana kashemin maƙudan kuɗaɗe, nasan manya manyan matan da take hulɗa da su, ba abunda ban sani ba na sirrinta, gefe guda ga alaƙar dake tsakanina da mijinta, wadda bata sani ba, babu wanda ya isa yace yasan ina wannan harkar saboda a zahiri ina iya yi na inga na tsare mutuncina. Na tarawa mahaifiyata maƙudan kuɗaɗe, ta wannan ƙazamar hanyar, sedai a wannan harkar da nake, na gamu da larura wani ƙari ya fitomin a mahaifa, a yadda ba yadda za'ai da shi sedai a haɗa da mahaifata a cire, haka a kaimin aikin nan cikin sirri ba wanda ya sani. Ranar da na fara ɗora idona akan Imran naji duk duniya ba namijin da nake so sama da shi, nai aniyar tuba daga waccan mummunar rayuwa da nake yi, da taimakon Allah da mahaifiyarsa na samu soyayarsa harya Aureni. Amma a hakan sheɗan ya cigaba da ƙawatamin ƙanwarsa Minal, sedai lokacin da mukaje gidan uwaɗakina da Minal tare, ita ta rigani bayyana nata buƙatar akan Minal, kuma bamu wani sha wahala gurin shawo kan Minal ba. Tun da Imran yai watsi dani ya fara tatara hankalinsa akan Amira, ni kuma kishi yasa na koma ruwa, na cigaba da saƙa a mugun zare na, ba tare da sanin Asiri na ya daɗe da tonuwa ba, amma dan Allah Imran ka yafemin, ku rufamin Asiri. Tsit sukai suka kasa Magana, se Ammi da ta fashe da kuka hadda sheshsheƙa. Imran ya miƙe tsaye ya nufi part ɗin Ihsan, ya dawo da takadda a hannunsa ya jefawa mahaifiyar Ihsan, yace "ki tattar 'yarki ku barmin gida" Ihsan tace "dan Allah Imran kaimin afuwa, ka rufamin Asiri" Ammi tace "wallahi baze miki afuwa ba, muguwa Azzaluma kawai, kun cuceni kun ɓatamin 'ya, kun sa na tsaya ya auri Ihsan, ashe abun naku zalunci ne" Abba yace "Ai shi Allah ba Azzalumin sarki bane, yadda kika takurawa Amira, da tsana da Mugun fata, sega WUTA A MASAƘA, Yarinyar da kika ƙallafa ranki a kai, sega sakamakon ki nan, kisa a ranki wannan alhakin Amira ne, Ubangiji ya nuna miki shi shiriyar 'ya'ya ba a hannun mutum take ba, a hannun Ubangiji take" Ammi tana kuka tace "tabbas maganar ka haka take, Amira dan Allah ki yafemin, nasan na cutar dake, rashin sani ne dan Allah ki yafemin" Amira ta share hawaye tace "ni Ammi ba abunda ki kaimin, komai ya wuce" Alhaji Hashim yace "shiyasa Annabi Sallallahu alaihi Wasallam yace mu faɗi alkairi ko muyi shiru, shiyasa aibata mutum dan yana aikata wani laifi be kamata ka aibata shi ba, seka nemawa al'ummar musulmi shiriya gaba ɗaya, sannan kai ɗan uwan mahaifin Wannan Yarinyar ko kana da ta cewa?" Yace "A'a me kuwa zance, sedai ince

Chapter 30 of 31