Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kai masa Abincinsa ɗakinsa, ya zauna yaci sannan ya ɗakko wayarsa, ya kira Ihsan. "Hello masoyi" "Na'am, abar ƙaunata kina lafiya?" "Alhamdilillah, ya hanya?" "Nayi fushi, bayan baki kirani ba" Ihsan ta marairaice murya tace "haba My Own, tunda kaje kano mukayi waya, daga baya idan na kira bata shiga, na kira meenal tace min baka dawo ba, ɗazu naji Mummy suna waya da Ammi tace ka dawo, kuma lokacin salla ne, shiyasa ban kiraka ba, saboda nasan wataƙila kana salla ne" Imran yai murmushi yace "to shikenan masoyiya ta, kin wuni lafiya?" "Lafiya ƙalau, sedai kewarka da ta dameni my own" "Nima nayi missing ɗinki tawan, naso in biyo in zo in ganki, Amma nagaji sosai, kuma ina cikin damuwa ne" Ihsan tai ajiyar zuciya tace"naji alamin damuwa a muryarka, sedai ban matsaka bane saboda wataƙila abin ba hurumina bane, kar in shiga hurumin da ba nawa ba" Imran yace "hakane Ihsan, amma abun ya dameni sosai yadda bazan iya ɓoye miki ba" "Mene ne wannan yake damun gwarzon mazaje, da har yake nema ya hanamun shi sukuni?" "Ihsan, gurin wannan'yar uwar tawa da Abba ya aikeni, Ihsan abun da na tarar ya ɗagamin hankali sosai" Ihsan tace "subhanallah wani abun ne ya sameta?" "A'a lafiyar ta ƙalau, sedai ta ɗauki layin daze ruguza rayuwar ta, koma ince ya ruguza rayuwar ta gaba ɗaya" Ihsan tace "haryanzu ban fahimceka ba My" "Yarinyar nan ta ɗauki hanyar banza, tana bin maza saboda kuɗi, kuma bata jin kunya ko shakkar ta faɗi abunda take, Abun takaicin yarinyace ƙarama da befi ace tana makaranta ba" "Innalillahi wa innalillahi raji'un, amma ya akayi ta lalace ina iyayenta" "Iyayenta sun rasu, a hannun dangin babanta take" Ihsan tace "so Sad, Amma addu'a yakama ayi mata, Ubangiji Allah ya shiryeta yasa ta dena, irin wannan tunda kaga tana haka, wataƙila tunda ta fara ba'a ɗau matakin daya dace bane" "Hakane nima nayi tunanin haka, amma abun ya dameni" Ihsan tace "ka dena damuwa, addu'ar ka tafi damuwar, bana son abunda ze dameka, ka rame kan lokacin bikinmu" Imran yai murmushi yace "kina ɗokin lokacin nan kuwa My Ihsan" "Eh mana" "Anya kuwa? Gaskiya ban yadda ba na fiki damuwa sosai, kamar in janyo lokacin nan haka nakeji" "Hmmm My Own kenan, ka kwanta ka huta kaji, nasan ka gaji sosai" "Idan na kwanta bazan iya baccin ba yanzu" "Meyasa?" "Tunaninki zan tayi, da mafarkin gashi munyi Aure" Tai murmushi tace "kwanta in maka addu'oin kwanciya bacci" Ba musu ya kwanta ya lumshe idonsa yace "na kwanta my wife" Cikin muryarta me daɗi ta shiga karantowa  Imran addu'oin kwanciya bacci, Imran yai shiru yana saurarenta wata irin nutsuwa tana saukar masa, a haka bacci ya kwashe shi. Amira kuwa kwana tayi da zazzaɓin nan, da ƙyar tayi sallar Asuba ta koma kwanta, tana jin yunwa sosai, rabonta da Abinci tun jiya da rana, ga ulcer ha duka da ɓacin rai, abun ya haɗu yai mata yawa, cikinta ya ƙulle yana mata ciwo, tai ta juyi a ɗakinsu, amma Babu wanda ya damu da ita, murna ma suke Gidan yayi tsit, saboda Anyi maganin Amira. Can ta fita tsakar gida da gudu, ta shiga sheƙa amai, ga ba komai a cikinta, ta dinga kakari ba abunda yake fita se yawu, idonta yai jawur ta riƙe cikinta saboda yadda yake yamutsawa. Tafa hannu Yadikko ta shiga yi tana 'la'ilaha illalahu, Muhammadu Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallama, jama'ar gidan ku fito ku fito me nake gani haka? Dama tunda na dawo Nake ganin wasu alamu a tare da yarinyar nan, shikenan ta faru ta ƙare, anyiwa me zani ɗaya sata, ta ƙunso abun" Aikuwa nan aka dinga fitowa, aka kewaye Amira dake ta fama amai ya fito, amma ba komai a cikinta, ta gama amanta ta zauna a guri ɗaya tana hutawa. Sadiya tace "shikenan dai abun Kunya ya tabbata a gidan nan, cikin shege dai gashi an yayimo shi saura kuma cuta" Umma tace "taɓ, mutuncin gidan nan kuma ya ɓare, yanzu za ai ta gantali damu a bakin duniya, wace irin masifa ce wannan" Amira ta tashi ta ɗebo ruwa ta kuskure bakinta, ta koma ɗaki tai kwanciyarta, kamar bada ita ake wannan surutan ba. Nan suka saka sabon faifai akan Amira, wasu suna a kira Imran a waya, wasu suna a bari a tabattar tukuna. Har magariba Amira bata sa komai a cikinta ba, dan haka ta kasa ko miƙewa tsaye, ta dinga juyi tana kuka tana wayyo Allah cikina, zan mutu. Baba yace "ina ga fa yarinyar nan ɓari zatayi, ta san tana da cikin ne ta sha wani abu dan ya zube" Yadikko tace "ko kuma dukan data sha jiya ne yasa cikin fita, ba yadda ba zata faru ba" Usman ne yai Sallama, suka amsa masa gaba ɗaya, ya gansu cirko cirko a tsaye yace "lafiya? Meke faruwa ne?" Yadikko tace "meke faruwa kuwa? Ai kasan baze wuce matsalar wannan yarinyar ba Amira, ciki take ta kwaso mana" Sakin ledar hannunsa yayi yace "ciki kamar yaya?" "Kamar yadda aka gaya maka mana, baka ji ne?" Cewar Umma. "Amma ya akayi kuka san ciki ne?" Yadikko tace "yo tell m safe take amai, meye inba ciki ba? Ciki ta ƙunso ta sha wani abun ta zubar dashi kuma yaƙi fita tana ta wahala" Usman ya nufi ɗakinsu Amira da sauri, ya ɗaga labule ya ganta a kwance tana juyi, tana wayyo Allah cikina. Ya shiga ɗakin ya durƙusa yace "Amira, menene meya sameki?" Cikinta ta nuna masa, amma ta kasa magana, se jujjuya kanta da takeyi. Usman yace "yakamata a kaita Asibiti, koma menene a can zamu ji" Sadiya tace "uban waye ze wani kaita Asibiti? Ta mutu ma waya damu, tunda bata ji kunyar kwaso abun kunya ba, ai se a barta ta sha wahalarta ita kaɗai" Usman yace "Baba, kasan halin mutanen gidan nan, duk da halin Amira idan ba a kaita Asibiti ba ta mutu a haka, se an ƙulla maka wani sharrin, gara ma a kaita Asibiti, kuma duka mugun halin Amira, da yadda take ɓatawa mutane rai, bazan manta yadda ta dinga min wahala ba, lokacin dana karye a hannu, yarinyar nan tana da tausayi, kuma koba komai tana da alaƙa da mu" Baba yai ajiyar zuciya yace "shikenan, a kaita ba dan halinta ba" Usman ya samo Napep, aka sakata a ciki aka kaita Asibiti. Suna zuwa aka karɓeta, aka gayawa likita abunda yake damunta, ya rubuta mata tasa tasai, akayi result ya nuna typhoid ce da malaria ke damunta, sekuma ulcer. Yadikko tace "likita yarinyar nan fa cikine da ita, taje ta sha wani abun dan ya zube take ta shan wahala haka" Likita yace "ba matar aure bace?" "Ba wani Aure budurwa ce' inji Yadikko. Likita yace "to ai har test ɗin ciki akayi mata, ba ta da komai kuma tace shekarnjiya ta gama al'ada, amma duk da haka mun mata test bata da juna biyu" Yadikko tace "a'a kun dai haɗa baki, amma ba yadda za'ai ace ba ciki bane" Usman yace "to ai Allah ne ya rufa mana Asiri Yadikko, koke so kike ace cikin ne Asirinmu ya tonu a gari?" Amira kamar ta fasa ihu, jin yadda Yadikko ta kafe akan lallai se an tabattar da cikine da ita, aka yiwa Amira ƙarin ruwa da Allurai, ta samu sauƙi aka sallameta. Tunda ta koma gida ba wanda yasake jin kanta, ta dena shiga sabgar kowa take rayuwarta ita kaɗai, a zatonsu duk ta kintsune saboda barazanar Imran. Sedai haryanzu bata yadda da a sata aiki tayi ba, ko wani ya nemi ya rainata ba. Bayan kwana uku ta warke, sedai rashin ƙarfin jiki, tana zaune a ɗakinsu su Amina suna karyawa, Yadikko ta shigo da waya a hannunta ta kalli Amira tace "karɓi nan Imrana ze miki magana" Wata uwar harara Amira taiwa Yadikko, ta ɗauke kanta daga kallon Yadikko. "Bazaki karɓa ba ina miki magana?" Amira ta zumɓura baki, sannan ta karɓi wayar. "Wayarce bazaki karɓa kenan? Ana miki magana kikayi banza" Shiru ta kumayi ba tace komai ba. "Ba kyaji na ne?" "Ina jinka" Amira ta faɗa a daƙile. "Amsawa ce baza kiyi ba kenan?" Amira tace "nifa bani da lafiya, kuma ni ka takuramin" "Eh rashin lafiyar taki aka gayamin, You Are pregnant, and you take abortion pills, are you really ok?" Ya ƙarasa Maganar a fusace Amira ta kalli Yadikko, tasan itace zata gaya masa, wani malolon baƙin ciki ya tokare mata ƙirji. Cikin tsawa Imran yace "ba kyaji na ne? Uban waye yai miki ciki har kika je kikayi ƙoƙarin zubarwa?" Amira tai shiru ba tace komai ba. "Ba magana nake miki ba? Definitely zan shigo kano a satin nan insha Allah, Enugu zan kaiki makarantar kangararru su horaki ta nda baki da mutunci, kuma ki gayamin waye ya miki ciki?" "Kaga dan Allah ka dena min tsawa, idan kaga dama ka kaini bangon duniya makarantar sheɗanu bata kangararru ba, ina ruwanka da lalacewa ta? Meye naka a ciki? Meye alaƙata da kai dan ina ɗaga maka ƙafa ba tsoronka nakeji ba, inka ga dama ka yo fiffike kazo yanzu" Ta ƙarasa maganar hawaye na zuba a idonta, tai wurgi da wayar Yadikko tsakar gida, aikuwa wayar ta tarwatse a gurin, ta miƙe tsaye ta kalli Yadikko tace  "abunda kikemin ya isheni, ya isa haka, na gaji, nayi ƙoƙarin yi miki biyayya iya yina, Amma ke kullum burinki, kiga kin tozartani, se zaƙewa kike akan lallai senayi abun kunya, Yadikko da kakata fa kikayi kishi ba da uwata ba, me nayi miki? Me nai miki Haka a rayuwa kike burin kiga masifa ta sameni, Insha Allah abinda kike min fata sedai ki ganshi a kan su Amina ba a kaina ba" "Ke Amira, Yadikko kike gayawa haka?" Cewar Zailani "Na faɗa ɗin, a gabanta likita ya faɗi abunda ke damuna, Amma ta dage cikine dani harta kira wan uwata a waya ta gaya musu, to cikin ne dani nayi cikin kuma kome na ke aikatawa a rayuwa da sa hannunki da zuriyarki, kuma wallahi rashin ji yanzu na fara mu zuba mu gani, koni ko ke!" Amira ta juya ta ɗau jakarta, da wayarta ta fito zata fita, Zailani ya biyota yana ƙoƙarin hana ta tafiya, amma tace wallahi ya taɓata seta masa illa, ta sa kai ta fice tana cigaba da zubar da hawaye. Da taji garin ya mata zafi bata da gurin zuwa, sama da gurin Yaya Fa'iza Dan haka yanzu ma gidanta ta wuce, tana zuwa ta tatar da Bashir na wanke babur ɗinsa, yana ganinta ya fara murmushi yana "Anty Amira Sannu da zuwa" Sedai ganin da yayi idonta na zubds hawaye ne ya ɗaga masa hankali, kai tsaye ta wuce falon Fa'iza, tana zuwa ta zauna ta cigaba da kuka. Fa'iza tace "Anty Amira, meyasameki haka? Meke faruwa?" Bashir yace "Amira lafiya kuwa?" Kasa magana tayi ta cigaba da kuka, can ta ɗago tace  "Fa'iza Yadikko, in Yadikko wallahi idan ba tayi wasa ba, sena karya matar nan wallahi" Bashir yace "Subhanallah, me tayi miki" "Yaya Bashir na gaji, am tired, ban san me matar nan take so dani ba, ta kira wan mahaifiyata tace musu ina yawon banza, ya turo ɗansa yai min rashin mutunci shekaranjiya, hadda duka, na kama rashin lafiya munje Asibiti, a gabanta likita yace malaria da ulcer le damuna, Amma ta kuma kiransu a waya tace wai ciki ne dani, nayi abortion nake ta sha wahala, meye haka takemin? Me nayi mata dan tayi kishi da kakata seta ɗoramin karan tsana? Bata fatan abun Alkhairi ya kusanceni se ita da zuriyarta, wallahi zan shiga duniya in bar mata gidan" Bashir yace "Subhanallah, ki dena faɗar haka, shiyasa nace ki dawo Gidan nan mu zauna, ki baro can ɗin kawai, su dena ɓata miki rai, Allah ba ze hana yadda za'ayi ba" Amira tace "ni ba zan dawo gidanku in zauna ba, saboda Allah be ɗora maka ɗawainiya ta ba, wanda Allah ya ɗorawan tunda sunƙi yi Shikenan" Fa'iza tace "Amira, ire iren wannan abubuwan nake jiye miki yasa nake miki faɗan ki dena abunda kike, dole ko kinyi abu ko baki ba ace kinyi, Saboda halinki da ɗabi'un da kikeyi" Amira tai shiru, zuciyarta na cigaba da tafasa, da zafi akan abunda ake mata, shikam Bashir haƙuri yaita bata yana rarrashinta. Message ne ya shigo wayar Amira, ta ɗakko wayar ta duba, Sultan ne ya turo mata saƙo "Ina ta kiran wayarki, Amma baki ɗaga ba, komai ya zama ready, jibi in Allah ya kaimu zamu tafi" Kashe wayar tayi ta mayar aljihun wandonta, ba tare da tace komai ba, Bashir yace "Ummu Khairat, sama mata abunda zata ci, naji tace bata da lafiya" Fa'iza ta zuba mata Abinci ta bata. Imran kuwa lamarin Amira ya dena bashi mamaki, yadda ta gaya masa baƙaƙen maganganu ma ya ɗaure masa kai sosai, hankalinsa ya tashi jin Wai har ciki tai yunƙurin zubarwa, yaita bin lambar Yadikko amma bata shiga, dan tunda Amira tai jifa da wayar komai na wayar seda yayi ɗai ɗai. Yaji kamar ya kira  Abba a waya ya sanar masa, amma yasan hankalin Abba ze tashi ne, kuma yana da hawan jini, kuma ma dai wannan ba labarin faɗa bane, dan haka ya yanke shawarar ze kuma komawa Kano, dan yaga me ze iyayi akan lamarin, ya bar maganar a ransa ko Ammi be gayawa ba. Wajen ƙarfe tara na dare Amira tace ita gida zata koma, Fa'iza tai tai da ita ta kwana a gidanta tace ba zata kwana ba, Bashir yace ze mayar da ita gida, nan ma tace bata yadda ba. Ta kama hanyar komawa gida ita kaɗai, data koma gidanma ba wanda ta kula kuma babu wanda ya kulata, ta shiga ɗakinsu, ta nemi guri ta zauna ta shiga haɗa abubuwan da zata buƙata a wata travelling bag. Ta gama haɗawa tsaf, sannan ta nemi gurin kwanciya, cikin dare Sultan ya kirata a waya yace mata yana ƙofar gidansu, ta tashi ta ɗau jakar nan data haɗa, taje ta zare sakata ta buɗe ƙofar, ta bawa Sultan jakar, ya karɓa ya tafi da ita, ita kuma ta koma ɗakinsu. Imran yana ta shirin yaga ta yadda za'ayi ya koma Kano, aka kira shi daga gurin aiki akace lallai yaje ana san ganinsa, Babu yadda zeyi ya kaucewa wannan kiran, haka ya haɗa kayansa, yaje yai Sallama da Ammi, ya biya ta gidansu Ihsan dan yayi mata Sallama. Tunda Ihsan taji komawa zeyi taji kamar ta ɗora hannu a ka tayi kuka, tace "Yanzu my Own komawa zakayi?" Imaran yace "to Ihsan ya zanyi? Dole in koma kar in fuskanci hukunci" Tai ajiyar zuciya tace "to yanzu se yaushe kuma?" "Nan da sati biyu insha Allah" ya bata amsa cikin damuwa. "Ya salam, lokacin bikinmu yazo daf  fa kenan" "Eh Ihsan, ya zanyi idan ba hakan ba, But am sorry kiyi haƙuri kinji? Ba laifina bane, nima ba haka naso ba" "Shikenan My, da har nace da Mummy na fasa zuwa Abujan nan, amma gara in tafi dama saboda kai na fasa" "Ba haka naso ba my, Amma ba yadda na iya, kinga kan lokacin bikinmu yazo, ina dawowa se biki mu tare kawai" Ɗan murmushi tayi tana sunkunyar da Kai, sukayi Sallama ya tafi. "Ali 'yata! 'yata Ali! Aliyu 'yata Kar ka bari 'yata ɗaya dana bari ta lalace, dan Allah Ali kayi wani abu a kai, kar 'yata ta lalace kaima 'yarka ce, dan Allah Ali ba dan ni ba 'yata 'yata 'yata Aliyu!!! Share Please Follow me on watpad@Ayshercool7724 What's app@07063065680 [1/7, 7:03 PM] Ayshercool: .🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 WUTA A MASAƘA PERFECT WRITERS ASSOCIATION (WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS) https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P. W. A *Story and written by* AISHA ADAM (AYSHERCOOL) The experience writer of *ABDUL JALAL* * WATA KISSAR.... (SAI MATA) *BAƘIN TABO (Labarin gasa) *AƘIDATA (Paid Book) * WUTA A MASAƘA SADAUKARWA GA ƘUNGIYAR PERFECT WRITERS ASSOCIATION, DOMIN TAYA MURNAR CIKA SHEKARU BIYU DA KAFUWA https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in ❌❌❌ Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba. *Innalillahi wa innalillahi raji'un, ina me amfani da wannan dama, wajan miƙa ta'aziyya ga ɗaukacin al'umar musulmi akan rashin da mukayi na Shehin _malami, Dr. Ahmad banba B.U.K ina fatan Ubangiji Allah yayi masa rahama yasa ya huta, in tamu tazo yasa mu cika da imani*_ Afuwan banyi Editing ba                                                               6_7 A gigice Abba ya farka daga baccin da yake cikin tashin hankali, mafarki yake da mahaifiyar Amira, ta riƙe rigarsa tana kuka akan ya temaka kar 'yarta ta lalace. Ya dafe kansa yai shiru yana tunani, can ya miƙe yaje ya ɗakko wayarsa, ya nemo lambar Imran ya kirashi, sedai wayar taƙi shiga sam. Ya duba lambar Ammi ya kirata, a ɗan firgice ta farka daga baccin, jin wayarta tana vibrating, ta duba screen ɗin wayar ta kalli agogo, dare yayi sosai ta ɗaga wayar tace "Hello, Abba lafiya kake kira a wannan daren haka?" Abba yai ajiyar zuciya yace "ina Imran yake?" Cikin Rashin fahimta tace  "Imran kuma? Me Imran ze maka a wannan daren?" "Ya kike tambayata ne? Yana nan ko baya nan?" "Ai Imran tun safe ya koma Maiduguri, an masa kiran gaggawa" "Yasalam" "Amma Abba lafiya, nifa ka tayarmin da hankali" Abba yace "Bari kawai, mafarki nayi da Zahra'u" "Wace ce kuma Zahra'u?" Abba  yace "'yar uwata mana, nai mafarki da ita tana kuka, tana in kula mata da 'yarta karta lalace, na tsorata ƙwarai ina ga tunda Imran baya nan, ni zan dawo gari zanje inga meya kamata inyi akan yarinyar nan" Ji tayi kamar ta zagi Abba dan takaici, a hasale tace "yanzun Dan Allah akam wannan abun ka nemi ka tayarmin da hankali, a wannan uban daren ina bacci? Mafarki ne fa kayi ba gaske ba, kawai ka ɗagamin hankali ka hanani bacci" "Kinga ba kowane mafarki ne kawai ba, wannan mafarkin da nayi ba kawai bane, an nusar dani kuskure na ne ta mafarki, wanda yakamata in gyara tabbas" "To yanzu me kake nufi?" "Duk yadda ake ciki gobe in Allah ya kaimu zan dawo, zuwa jibi insha Allah zanje inga yarinyar nan da kaina, something is not wrong, seda Safe kawai" Ya kashe wayarsa ya ajiye, ƙirjinsa na cigaba da bugawa da sauri da sauri, Ammi kuwa tsaki tayi, ta jefa wayar bayanta, tace  "Aikin banza, kawai ze ɗagamin hankali akan wata banzar yarinya, sekace nina saka ta yawon banzan" Tai tsaki ta juya ta cigaba da baccinta, tana takaicin Yadda Abba ya tashe ta ya ɗaga mata hankali a wannan Uban daren. Ana idar da salar Asuba, Amira ta ƙarasa tattare duk abunda take buƙata tai waje, su Sadiya na kallonta amma ba wanda ya iya ce mata wsni abu, dan yadda tske cika tans batsewar nan, duk wanda ya tanka mata zata iya sauke masa rashin mutunci. Haka ta fita zuwa Office ɗinsu na rawa, ta tarar dasu Sultan sun shirya tsaf, ana jiran mutum biyu, seda suka karya wajen ƙarfe goma sannan suka tafi airport. Sultan yana kula da yadda Amiran bata walwala sam, yaso yai mata magana amma ya fasa, saboda wani lokacin halin Amira se a hankali, tana da sauƙin kai, amma bata fiye son a shiga lamuranta ba. Se ƙarfe biyu Sannan suka ɗaga, Amira na Jin yadda jirgin ya tashi, maimakon hakan ya sanya Amira cikin farinciki kasancewar karonta na farko kenan da ta hau jirgi, sema wani baƙinciki da ya addabi zuciyarta data rasa na menene, kawai ta jingina ta lumshe idonta, hawaye na zuba daga idonta. "Gimbiya Amira yau an hau jirgi, ba saban ba, za'a ƙaro wulaƙancine" Sultan yai maganar yana murmushi, sedai ganin Amiran na hawaye yasa jikinsa yin sanyi. Cikin damuwa yace "Amira lafiya kuwa? Kukan me kike haka?" Girgiza masa kai tayi alamar bakomai. "Amma Bakomai kike kuka haka? Karki sa hankalin mutane ya dawo kanki fa" Ta goge hawayen ta tace "karka damu, bakomai" Haka Sultan ya ƙyaleta, amma Amira ta kasa tsaida hawayen dake bin fuskarta. ***************************** "Amma Alhaji Ali baka ganin tafiyatka a yau zata iya kawo matsala, kana cikin kwamitin da shugaban ƙasa ya kafa, kuma kusan kaike jagorantar kwamitin nan, be kamata ka bar garin nan yau ba" "Dole in bar garin nan yau ɗin nan, ina da damuwa ne, kano nake son zuwa gobe in Allah ya kaimu" "Amma wace irin damuwa ce da bazaka iya haƙuri a gama ganawar ba sannan ka tafi?" "Hashim, bazaka gane ba sam, nasan abunda zan gayawa Excellency, Amma ƙarfe uku zanbi jirgi in koma" Hashim yace "shikenan, Allah ya kyauta koma menene" Alhaji Ali ya amsa da "Ameen" Yadikko ta fito tsakar gida tana cewa "ina wannan yarinyar take ne, ta kassaramin waya wayata taƙi tashi, ta fito ta bada kuɗi a kaimin ita gurin gyara" Amina tace  "wai wace yarinyar kike nufi?" "Amira Mana" Amina tace "to bayan idar da sallar Asuba ta fita" "Ta fita taje ina?" Sadiya tace "wa take gayawa inda zata? Gantalinta ta fita, yau hadda jaka ta haɗa ta tafi" Yadikko tace "jaka gidan ubanwa taje? To ko ina taje ina nan zatazo ta sameni, wallahi seta biyani wayata" Yadikko ta cigaba da sababinta, tana se Amira ta biyata wayarta data fasa mata. Alhaji Ali daga airport be tsaya ko ina ba, se gidansa sedai sam Ammi bata wani nuna murna da dawowarsa ba kamar yadda take a baya ba idan yaje wani guri ya dawo ba, dan ya fara bata haushi akan yawan zancen Amira da yake kwanan nan. Tunda ta masa sannu da zuwa, ta bashi Abinci bata bashi chance, ko fuskar da zasu tattauna maganar Amira ba. Minal ce ta shigo falonsa tana faɗin "Abba, ya kuma ka dawo gida yau, base jibi in Allah ya kaimu zaka dawo ba?" Abba yace "na dawone saboda batun 'yar uwarku" Minal tace "wace 'yar uwa tamu? Anty Khadija?" "A'a, 'yar uwaku dake Kano, Amira" Ammi tace  "Dan Allah ka dena haɗamin yara da wannan yarinyar, ni yarana nutsatstsune" "Koma dai menene, ni 'yata ce kuma dole in damu akanta" Ammi tace  "eh kai ta zamewa dole ba yarana ba, ka dena haɗata dasu" Abba yai shiru yana tunani, sam Ammi bata masa kara a kan 'ysn uwansa, Magana in dai bana 'yan uwanta ba, sam bata son taga yana morawa wani nasa komai, be kuma  cewa komai ba ya tashi ya shiga bedroom ɗinsa, ji yake kamar ya tafi Kano a lokacin, sedai Yamma ta riga tayi, ba damar yin hakan lokaci ya ƙure sosai. Amira kuwa tuni suka sauka a babban birnin tarayya, Sultan yai musu jagora zuwa Hotel ɗin da aka kama musu, Amira ɗakinta ita kaɗaice, Babban ɗakine sosai dan yafi nasu Sultan girma da kyau, hatta Abincin da zasu ci ayi bikin a gsma, seda aka biya musu, Sedai gaba ɗaya Amira a damuwa take, kawai dai gata nan ne dai, ji take kamar ko rawar ma bazata iya ba ranar bikin Washegari da wuri Alhaji Ali ya shirya ya tafi Kano, be tsaya ko ina a ba se ƙofar gidan kakanin Amira, da shida jami'an tsaron dake masa Rakiya, a wasu rantsatsun motoci na Alfarma, wanda seda aka mutane suka fara tunanin waye wannan ya kawo musu ziyara haka layinsu. Yai Sallama ya shiga gidan, a ƙofar ɓangarensu Yadikko ya tsaya yana Sallama, Baba ne da kansa ya fito dayake daf yake daya fita, yayi mamakin ganin Abba, dan rabonsa da gidan nan a ƙalla ya shekara shida, tun kafin a masa muƙami a gwamnatin tarayya. Baba ya washe baki yace "Alhaji Ali kaine ke tafe da kanka haka? Masha Allah yau mun karɓi babban baƙo Bismillah shigo" Alhaji Ali ya shiga yana faɗin "Ayi haƙuri munyo sammako haka ba sanarwa" Baba yace "haba dai bakomai, sha ɗaya na Safe ai ba sammako bane, sannu da zuwa Yallaɓai" Kana kallon Alhaji Ali zaka san shine mahaifin Imran, saboda suna kama sosai. Aka masa iso har ɗakin Baba, nan Yadikko ta shiga rawar kai tana washe baki tana  "Sannu da zuwa, Sannu da zuwa Alhaji Ali, ya hanya sannunka da zuwa Sannu Sannu, kai Zailani zokaje ka siyo masa ruwan roba, manya basa shan irin ruwan da muke sha" Abba yace  "A'a bakomai, na taho da ruwana a mota, nagode sosai" Suka shiga gaisawa da yaushe gamo, can Abba yace "nifa banga 'yata ba, nazo ne in gani inda yuwuwar in tafi da ita, saboda labarai marasa daɗi da naji a game da ita, sam abun be min daɗi ba, na turo Imran yazo shima, sedai feedback ɗin dana samu daga gareshi sam banji daɗinsa ba, abun ya tsayemin shiyasa na ajiye ayyukana na taho kawai" Baba yace "to Amira dai iya ƙoƙari munyi a kanta, ɓangaren kulawa da ita, cinta shanta suturarata da kuma makaranta, munyi iya ƙoƙarin mu bata tarbiyya nagartacciya kamar wadda muke bawa duk wani ɗa dake gidan nan, Amma Amira taƙi, hankalinta na kan wani abu daban" Yadikko ta ɗora da cewa  'Sam Amira bata jin magana, ga fitsara da rashin Kunya, taurin kai ga neman magana, ga rashin ta ido da gantali na tsiya

Chapter 5 of 31