kazar, tana bawa Imran a baki yana karɓe kayarsa.
Aka fara kiran wanda za'a karrama, tace "wai kai baza'a baka ba?"
'ai ban dani, masu ƙwazo ake bawa"
"Kai, ana nufin kai baka da ƙwazon ne? Da na san baza'a baka ba da bzan zo ba wallahi"
Tana cikin mitar aka kira Imran, zumbur ta miƙe tana tafawa Imran, tace "You deserve it dear".
Imran yai murmushi ya kama hannunta, suna tafe ana musu hoto yaje ya karɓo ƙaton frame ɗin da aka bashi, da hotonsa da sunansa, da rank ɗinsa na major, kan a bashi seda aka dinga koɗashi, ana faɗar jajircewarsa.
Amira kamar ita aka bawa, ta karɓe frame ɗin ta riƙe.
Suka dawo in da suke zaune su ka zauna, tace "da ba'a baka ba da tafiyata zanyi"
"Kin san hanya ne in kin tafin"
"Ai da tare zamu tafi, amma tunda an baka tashi Mu tafi gida"
"Ki tsaya a ƙarasa, Yanzu za'a gama"
Basu baro gurin nan ba se bayan goma na dare, tun a hanya Amira ke gyangyaɗi.
Seda Imran ya tsaya a hanya ya sai gasassun kaji, da youghurt me sanyi, sannan suka tafi gida.
Suna zuwa ta bar Imran da kaji, tai ɗakinta da frame ɗin nan, ta na zuwa tai wanka haɗe da alwala ta fito tai salla.
Har ta kwanta Imran ya shigo yace "ga kazarki can na biya a dena min gori, kuma naga kin zo kin kwanta ba ki ci ba"
"Se da na roƙa za'a saimin, na ƙoshi se gobe in Allah ya kaimu zan ci"
Ya ƙaraso ya zauna a kusa da ita akan katifar, yace "to bani frame ɗina"
"Taɓ, ai ba zan bada wannan frame ɗin ba, idan mun koma gida a falo na zan kafe shi"
"Kin haƙura zamu koma taren ne?"
"A'a, Kano zan tafi, daga nan ba zan tsaya ko ina ba se Kano"
Imran yai ƙasa da murya yace "wai ke meyasa abu baya wucewa a gurinki ne? Ba in da zaki koma se ɗakinki"
"Nifa ka dena wannan kashemin Muryar, dan nayi Imani da Allah da ka sameni saɓanin budurwa haka zaka cigaba da min wulaƙanci, kuma na da baka so, ai matar so ta isheka, ni temakamin a kai"
Shiru Imran yai, be kuma cewa komai ba yana ajiyar zuciya, bi sa kasada ya jarraba Amira ko zata yadda da shi?
Bisa ga mamakinsa, ba taurin kai ba gaddama ta ƙyaleshi yai budurinsa, abun ya bashi mamaki sosai, tabbas yasan da Ihsan a matsayin Amira, ba zata taɓa yadda da shi ba.
Imran ne ya fara tashi ya shiga yai wanka, da kansa ya haɗa mata ruwa itama, bayan ta fito daga banɗakin ta tarar da shi kwance akan katifar.
"Ya naga haka?" Tai maganar tana ɗan haɗe rai.
Imran yace "me kika ganin?"
"Ka tafi ɗakinka mana kwanciya zanyi"
"Ai a nan zan kwana"
"Saboda me?"
"Saboda nan ɗin ɗakin matata ne"
Wani kallon banza Amira taiwa Imran, a ranta tace "lallai wasu mazan halinsu se Allah, ji yadda ya ke wani kwantar da murya wai ɗakin natarsa"
Amira tace "matarka dai Ihsan ba Amira ba"
"Amiran ma matata ce"
"A yanzu ba, amma a baya ai ni ban kai a kalleni a matsayin matar ba"
Amira ta dinga masa tsiwa son ranta, amma Imran ya gaza cewa Komai saboda yasan ba shi da gaskiya.
Taje ta kwanta tana mitar ita gaskiya ya tashi ya bar mata ɗaki, tunda ya gama abunda ya kawo shi.
Imran ya rungumeta sosai sannan yace "Dan Allah Amira abunda ya faru ya wuce Please"
"Baze taɓa wucewa ba"
"Meyasa, dan Allah kiyi haƙuri ya wuce, ban san yadda akai ma kika yadda da ni ba, har kika nuna farinciki ki akan nasarar da na samu, hakan ya nuna baki da riƙo, dan Allah ki yafemin Komai ya wuce, nasan kina da zuciya me kyau Amira"
Amira a ranta tace "Ai nia ba irin sokuwar matarka bace, da zan biyewa abunda yafaru nima in wulaƙantaka ba, in je ka hango wata, da Wannan damar zan mallaki abunda ta gaza riƙewa, in rama cin zarafin da tai min"
A fili kuma tace "Imran ban jina zan taɓa mantawa da mummunar kalmar Karuwa da mutane da yawa suka dinga jifana da Ita, kalma me nauyi da munin gaske, tabbas nasan nayi kuskure da na biyewa son zuciyata na dinga tafka taɓara son raina, ba tare da sauraron maganar kowa ba.
Mutane sun gaza yi min adalci ko yaya, babu wanda yasan dalilin da yasa na zama haka, babu wanda yai tunanin me za'ayi dan tallafar rayuwata, da dawo dani kan hanya se zagi cin mutumci da miyagun maganganu da mummunan fata.
Haƙiƙa maraici abu ne wuya da ɗaci, kuma Allah yana jarabtar bawansa ba dan baya sonsa ba, wanda duk ya tashi cikin maraici idan har ba mariƙi ka samu nagari ba, haka zaka tashi a rayuwa me wahala da ƙunci.
Bayan rasuwar mahaifiyata, na kasance a hannun dangin mahaifina, Yadikko bata ƙaunar kakata, mahaifiyar Abbana, Abbana a hannunta ya ƙarasa tashi, ta asabtar da shi azabtarwa me muni, ta yadda seda ta raba tsakaninsa da mahaifinsa, duk da tsakanin gidan mahaifina da gidan su babanmu ba nisa, amma mahaifiyata ta sha wahala a hannun Yadikko.
Duk da ba itace ta haifi Abbana ba, amma Mamana ta mata biyayya sosai, bayan rasuwar mahaifiyata aka kaiwa Yadikko ni, duk abunda za'amin na cutarwa, yana gani baze iya Magana va, saboda yana mata biyayya kamar mahaifiyarsa.
Ina da shekaru huɗu zuwa biyar mahaifina yai hatsarin mota ya rasu, bayan an share zaman makoki haka na zauna a gidan Yadikko da ya kasance family House, da yawa duk 'ya'yanta ne a gidan da matansu, da ma Abbana shikaɗai Mamansa ta haifa.
Ba wanda ya damu dani a gidan nan, duk da ƙanƙantar shekaruna, hakan baya hana Yadikko da iyalanta azabtar dani, ta hanyar sani aiki me wahala wanda yafi ƙarfina.
Banda duka akan ƙanƙanin laifi, duka wanda shekaruna sunyi ƙanƙanta ai min wannan dukan.
Watarana lokacin ina da shekaru takwas a duniya, Abba yazo daga Kaduna duba ni, ya zo ya tarar bani da lafiya, ga Yadikko ta iya siyasa, dan haka ba'a gane azabtar dani take, tai ta nunawa Abba ai tana sona, suna ƙoƙari a kaina.
Abba ya fito ze tafi, wani maƙocinmu ya samu Abba yace "idan da hali, tunda ɗan uwan mahaifiyata ne, ya tafi dani ya riƙeni, idan ba haka ba izayar da ake min ze iya sawa in rasa raina ko nakasta ni.
Abba yazo Kano, yace lallai tafiya zeyi dani, shi ze riƙeni.
Yadikko tace baze yuwu ba, seda suka kai ruwa rana sosai, sannan Yadikko ta bari ya ɗaukeni ya tafi dani.
Se dai muna zuwa, Ammi ta ganmu tare, ta haɗe rai tace ya ta ganmu mu biyu?.
Yai mata bayani, a take Ammi tace wallahi ba zata riƙeni ba, ɗan riƙo ba ɗan goyo bane, duk abunda zaka masa baza'a gani ba, gar tyn wuri yasan in da ze kaini amma ba gidanta ba, da fari ina ta murna zan baro baƙar wahala da aiken gidanmu, amma karɓar da Ammi tai min yasa na sha jinin jikina, ta dinga faɗa tana ɗaga murya tace a Lallai se na bar gidan.
Abba yace tayi haƙuri washegari ze maida ni, haka akayi kwana na ɗaya a gidanku, ban manta ba akan tiles na kwana, ga sanyi gashi ban saba ba, washegari Abba ya maida ni hannun su Yadikko.
Rayuwa ta cigaba da tafiya a haka, kullum jiya i yau, maƙocinmu shine ya sani a makaranta, duk yaran gidan nan suna zuwa amma banda ni, maƙocinmu ya sani a makaranta.
Wataran sedai in saci jiki in gudu makaranta, ga rashin Abinci ga rashin kulawa, idan yuwa ta isheni se in daidaici lokacin cin Abinci a maƙota sannan in ci, ta ƙarfi da yaji na koyi kwaɗayi.
Idan aka je Guri naga Abinci jikina har tsuma yake a bani in ci saboda yunwa.
Kaya sedai in an samu kwance a bani in saka, wai salla tayi a saimin kayan salla ba ruwan kowa dani, kuma ga gidan da mahaifina ya mutu ya bari suka saka 'yan haya a ciki, suna karɓe kuɗin, suka ƙi bari a raba gado, ƙarshe baffa salahu ya tashi Auren 'ya aka saida gidan su kai hidimar biki.
Anty Fa'iza itama mamanta ta rasu, 'yar gurin Baffa Salahu ce, itama ta sha wahala sedai ta ta bata kai tawa ba, saboda ita jikar Yadikko ce, itace wataran ta kan kula ta bani kaya ko ta saimin takalmin sawa, saboda tana 'yan sana'oi.
Kasancewar gidan Yadikko akwai manyan samari a gidan, suka fara amfani da damar rashin galihuna, suna nema su lalatani, idan naƙi se asan yadda za'ai a ƙullamin sharrin da za'amin dukan tsiya a gidan, dama Abinci ba ban ake ba se an gadama, ya zaman har daga naƙota se a turo wai inje, a sani wanke wanke share share da aike, wataran in nayi a bani Abinci, wataran nayi a bati, ga rainon 'ya'ya, duk wadda ta haihu a sirikan Yadikko rainon yaron nan a kaina yake.
Sadiya da Amina sun ɗan girmeni, amma kusan kanmu ɗaya saboda ina da jiki, amma duk wani aiki suna zaune sedai a sani, idan kuwa rigima ta haɗani da su, nice bani da gaskiya se zagi da duka da cin mutunci.
Duk motsin da zan, ko inyi laifi ko ƙiriniya irin ta yaro sedai Yadikko tace "Allah ya watsa ni, insha Allah munyi hannun riga ni da abun arziki, yadda kakata ta mutu a tsiyace nima haka zan mutu, kuma se na barwa zuriyar Hafsatu wato kakata mummunan abun kunya"
Tun abun yana damuna har nazo ya dena damuna.
Akwai tazarar gaske daga Makarantar mu zuwa gidanmu, amma haka nake kwasa a ƙafa inje in dawo, har talla Yadikko ta kasamin, bayan ga jikokinta, amma duk da haka ina naniƙe da ita, nice wankinta, kitsonta lallenta, gyaran gurin kwancciyarta, aike idan zata aikeni bangon duniya ne ba zan taɓa musawa ba, zanje da ƙafafuwana.
Ba ni da ƙyuya ko ƙyashi, ga biyayya ga kowa, duk Alkhairi na ga Yadikko da iyalanta hakan be hanasu cigaba da yi min fatan lalacewa ba, an haka ai kayiwa Fa'iza Aure, bayan an kai ruwa rana taƙi aurar wani me kuɗi da suke so ta aura.
Na fara zama budurwa, amma babu kayan gyara, gashi bana son ƙazanta, ina son kayan kwalliya nima in gayara, amma babu me bani, brezia wannan se in Fa'iza ta bani kwancen ta ta, akwai lokacin da wandon da zan saka guda ɗaya ne tak dani, shima duk ya mutu, ba kayan turare ba me saimin audugar da zan amfani da ita lokacin al'ada, gashi na zama budurwa.
Allah yai min ƙirar jiki me ɗaukar hankali, hakan yasa maza suka dinga bina, suna son suyi amfani da rashin gata na su ɓatamin rayuwa.
Duk da haka akan samu na arziki suzo neman Aurena, amma da an zo tambaya se su Baba su ɓatani a gurin iyayen mutum, suce ni mutuniyar banza ce, a faɗar Yadikko ba zan Aure ga su Amina a zaune ba.
Islamiyya da ƙyar na samu nai sakukar Alƙur'ani, saboda kullum cikin korata ake ban biya kudin makaranta ba, ga shi zan kammala sakandire babu kuɗin jarrabawa, nan na shiga tunanin yadda zan na samu kuɗi.
Ina da wata 'yar ƙaramar waya, da na kan kaiwa me caji yaimin turi kyauta, a unguwar su Fa'iza, ya turan funa funai, da raye raye.
Tamu ta zi ɗaya da shi sosai, ya kan cemin ƙanwarsa, ya bani labarin yana da ƙanwa Amira, amma tana ƙarama sosai ta rasu, wasu lokutan har kyautar kuɗi yake bani, abunka da me buƙata ko a'a bana cewa nake karɓewa.
Wataran naje gurin Sultan me caji, akace yana bayan layi gurin wani biki, na bishi can ina zuwa na tarar da shi a can, yana cikin yaran D.J.
Ya koma gefe muna magana, nace masa "Yayana, naje ka turan cigaban series ɗin nan ba ka nan, ashe kana nan"
Sultan yace "eh ina nan, biki aka gayyacemu, ki bari in kin dawo zan turamiki"
Ana haka aka kira Sultan zeyi wata rawa kan zuwan amarya, sedai aka rasa macen da za suyi rawar tare, me DJ ya saka naira dubu goma ga duk yarinyar da tayi wannan rawar.
Take na shiga lissafi da tunani, idan na samu dubu goman nan, zan sai phants, brezia, pad da underwear, bani da takalmi me kyau, gashi ko turare bani da shi, sedai in nai wanka in jiƙa gishiri in shafa.
Ban gama yanke hukunci ba, na tsinci kaina a wannan Filin rawa, saboda burina in samu wannan kuɗin in biya tarin buƙatun da nake da su, wannan shine ma somin faɗawata harkar raye raye...........
Gyra, sharhi, ko shawara
Ayshercool
07063065680.
[2/13, 7:52 PM] Ayshercool: 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
WUTA A MASAƘA
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P. W. A
*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA)
*BAƘIN TABO (Labarin gasa)
*AƘIDATA (Paid Book)
* WUTA A MASAƘA
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in
❌❌❌
Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.
45_46
Amira ta cigaba da cewa "tun daga lokacin da na fara iya hawa kan stage, a gaban dubun dubatar jama'a inyi rawa, kunya ta ƙauracewa idona, mussaman da Ni nake ɗaukar ɗawainiyar kaina, ni nake wa kaina komai, dan haka na dinga ganin nafi ƙarfin kowa, ba wanda ze taka ni in saurara masa.
Sultan ya dinga goyon bayana, yana tafiya dani guraren raye raye, sedai ya kan cemin 'Amira ba'a son raina nake zuwa dake gurin rawa ba, ina fatan Ubangiji Allah ya baki miji me sonki, wanda ze riƙeki da amana"
Ya yadda yaje dani ko ina, in dai fannin rawa ne ba zan ba shi kunya ba, sedai be yadda wani yaci mutuncina ba, Mutane na zaton mutuniyar banza ce ni, sedai duk wanda ya raɓeni da maganar banza, sena masa ƙaramin hauka, dan tabbas har da ƙaramar wuƙa nake yawo saboda tsaro.
Idan aka ɓatamin rai a gidan, gidan Anty Fa'iza nake tafiya, saboda tun tasowa ta ban san wani abu wai shi rarrashi ko ja a jiki ba, amma ba dangin iya ba na Baba, mijinta Bashir yake mutuntani, yake girmamani kamar ƙanwarsa.
Shiyasa nake tafiya gidan inyi kwanaki, tunda aka gane ina zuwa raye raye, Yadikko ta laƙaba min kalmar Karuwanci, ni kuma na karɓa na hau kai na zauna, na nuna mata na amince itan ce, saboda ba abunda zanyi wanda zesa ta janye abunda take faɗa a kaina.
Wannan shine dalilin da yasa nake rashin ji, nima ba son raina bane rashin gata ne, mata da yawa suna lalacewa ne saboda rashin gata, wata da ta rasa breziar da zata saka gara ta bada jikinta ta sam kuɗi, amma ni bana aikata zina ni ba karuwa bace.
Tai maganar tana rushewa da wani irin kula me Ratsa zuciya.
Imran yai ajiyar zuciya, ya rungumeta tana dukan bayanta a hankali da sigar rarrashi yace "Am so sorry Amira, tabbas an miki ba daidai ba, an cutar dake sosai mussaman da munanan kalamai, daga gareni amma dan Allah ina neman afuwarki Amira, dan Allah kiyi haƙuri ki yafemin"
Ba ta iya cewa Komai ba , se cigaba da kukan ta da tayi, ya rungume ta yana shafa bayanta.
Tun daga ranar Imran ya shiga matsananciyar Nadama, yake nan nan da Amira, duk a ƙoƙarin sa na wanke laifinsa, dan tabbas yasan abunda mahaifiyarsa ma tayi ba ta kyauta ba, na nunawa Amira tsana tun tana ƙarama, ba zata taɓa mantawa da abunda tai mata ba, da wanda take mata a yanzu ba.
Amira ta nuna kamar ba abun ɓaci rai da Imran ya taɓa yi mata, hakan ba ƙaramin ƙara mata kima yai a idon sa ba, duk da wasu lokutan idan taso tsiya, rashin mutunci take masa, amma baya duba hakan dan shi be zaci ma za ta iya saurarsa ba haka da wuri, saboda yadda ya dinga mata a baya.
Tana kula dashi sosai, ba ƙorafi da yawan kawo matsala, sedai in kishin ya motsa ko Ihsan ta kira ta yayyaɓa masa Magana son ranta.
Basu ƙara raba gurin kwana ba, daren da yake idan ya fita ya dena, kullum yana manne da Amira (maza manya, ya manta da kashedin Ammi 😂😂😂)
Ranar Saturday yana baccin safe, Amira ta tashi duk tayi aikinta, tai wanka tai kwalliya, ta zo ta zauna kusa da shi, ya ɗora hannunsa a ƙirjinsa yana bacci, ta ɗora nata hannun akan nasa, hannunta ya sha jan rani, ta ɗau wayarsa ta ɗauki hotunan hannunsu a haka, ta ajiye masa wayarsa.
"Amran ka tashi ka karya mana" tai Maganar tana shafa gefen fuskarsa.
Ya buɗe ido a hankali ya kalle ta, yai murmushi yace "You look so cute"
Wani irin fari tai masa sannan ta kashe masa ido tace "dama dan ka yaba nai kwalliyar, tun da ka yaba kwalliya ta biya kuɗin sabulu"
Murmushi yai ya shafa gashinta yace "Amira Amma wannan gashin ki ne ko?"
Ta jinjija masa kai alamar eh.
"Ka tashi muje ka karya, bana son ulcer ta kama min kai fa"
"Duk yadda kike kula dani ɗin nan, ina ulcer zata ganni, kiss me se in tashi"
Tashi tai daga jikinsa tace "naƙi wayon"
Wayarsa ce ta fara ringing, Amira ta ɗakko za ta bashi, amma taga my wife a kai, ai kuwa ta haɗe rai tai rejecting ɗin kiran.
"Amira ya haka?"
"Nifa gaskiya na fara gajiya da halin matar nan, ta barni in sarara Nima, Lokacin da kuka tafi kuka barni ni kirana kake? Ya za tabi ta addabeni wallahi ba zaka ɗaga wayar nan ba"
Ta kashe wayar gaba ɗaya, Imran yai ajiyar zuciya yace "muje inci Abincin"
Yasan dai rigimace Amira ta janyo masa tashin hankali a gurin Ihsan.
Bayan Imran ya karya, har bayan azahar yana gida, se wajen la'asar sanan ya fita, bayan fitarsa ya duba wayarsa, yaga missed calls ɗin Ihsan rututu da na Ammi.
A kiɗime ya kira layin Ammi, dan yasan da ƙyar in ba ƙararsa Ihsan ta kaiwa Ammin ba.
Aikuwa yana kira ta ɗaga, "Sannu mara mutunci sallamamme"
Imran yace "Subhanallah, Ammi meyafaru?"
"Dole ka tambayeni meyafaru mana, kira nawa nai maka baka ɗauka ba? Ihsan ta kiraka kai rejecting kaƙi ɗagawa, nima na kira kaƙi amsawa saboda tsabar wulaƙanci da rashin mutunci ko? Wato kana tare da Karuwa Imran ka tsallake maganata kenan ko?"
"Yasalam, Ammi ba haka bane ba, ina tare da oganane, meeting akayi ba damar in ɗaga waya shine dalilin, amma banda haka ba abunda ze sa in ƙi ɗaga wayarki, ko in bijirewa maganarki"
"Hmm ai na zata ka fara biyewa waccan watsatsiyar ne, gaba ɗaya Ihsan ta tashi hankalinta, duk yadda za kai kayi ka dawo gida ka kula da matarka"
"Ammi ba za'a bani pass Yanzu ba"
"Be dameni ba, ka dawo gida kawai ni ban yadda da zamanka da wannan Yarinya a guri ɗaya ba, kome kake ka baro kazo ka kula da matarka"
"Shikenan Ammi, zan va yadda za'ayi, amma ko ta biyo jirgi ta taho nan ɗin?"
'ban yadda ba, ka dawo shine Umarnin da na baka"
"Shikenan, zan dawo insha Allah"
Ba ta kuma magana ba, ta katse wayar, Imran ya dafe kansa yai shiruu ya rasa abunyi gaba ɗaya, Ihsan ta fara sire masa da abubuwan da take masa sun fara ƙular dashi.
Yadda Imran ya fita ba haka ya dawo ba, hakan yasa Amira ta fuskanci Imran ɗin yana cikin damuwa, dan haka tace "Amran"
Ya kalleta yace "Nifa na kasa gane ma'anar Amran ɗin nan"
Tai murmushi tace "Amira_Imran shine Amran"
"Wow, sunan yayi kyau sosai my dear"
Ta jinjina kai tace "meke faruwa ne?"
"Wai Ihsan ba lafiya, Ammi ta matsa in koma gids, zan karɓi pass mu koma"
"Allah ya bata lafiya, wataƙila mun kusa ɗaukar baby ne"
Kallonta Imran yai, koma har zuci ta faɗi maganar ba, tayi ƙoƙari ƙwarai gurin ɓoye damuwarta.
Watan su Ɗaya da sati biyu cif a Lagos, Amira ta sha kula da taraiya, kamar yadda Imran ya samu kyakkyawar kulawa daga Amiran, gaba ɗaya sunyi ƙiba kai kace yanzu yai Aure.
Amira ma tau wani fresh kamar ba ita ba, ta ƙara kyau da nutsuwa sosai.
Abun takaici da suka isa gidan Ihsan bata nan, Amira ta wuce sashenta ta shiga gyagygyarawa.
Imran yace "Amira bari inje guda gurin Ammi"
"Shikenan, kace ina gishesu"
Bayan fitar Imran, seda ta gyara ko ina ta ɗora girki, sannan ta kira Anty a waya.
Anty ta ɗaga tare da sallama.
Amira ta amsa tace "Uwata ta kaina"
"Na'am 'yar albarka, ya kike ya Lagos?"
"Ai mun dawo Anty".
"Ahh haba yaushe kuka dawo?"
"Ɗazun nan muka dawo"
"Meyasa baki gayamin ba, ai da nasa an muku girki"
'bakomai Anty, ina Yayata, koda yake ita jiya munyi chatting da ita"..
"Tana nan ta tafi school, ina fatan dai komai lafiya ko?"
"Lafiya ƙalau Anty"
"To shikenan, dan Allah ban da rigima, ku zauna lafiya ki kula da mijinki yadda ya kamata"
"Insha Allah Anty, Nagode"
"Yawwa se anjima"
Ta ajiye wayar ta fito, fitowarta ba daɗewa sega Ihsan ta dawo, kamar waa korarriya duk tayi rama tai wani iri.
Murmushi Amira tai mata tace 'Sannu da zuwa Ihsan"
Kallon banza Ihsan ɗin tai mata taj uban tsaki ta shige.
Amira tai murmushi tace "Iska na wahalar da me kayan kara"
Imran kuwa yana zuwa gida a Falo ya tarar da Ammi, tana ganinsa annurin fuskarta ya ɗauke gaba ɗaya, ta haɗw rai ya durƙusa ya gaisheta ta amsa da ƙyar tace "ka g damar dawowa kenan?"
"A'a Ammi, pass ne ban samu da wuri ba"
"Rufemin baki da zancen wani pass, 'yar mutane ta na ta fama da rashin lafiya amma ko a jikinka, kaje kai zamankansabida kaka tare da Karuwa ko? Imran idan ka kuksakura na samu labarin wani abu a tsakanin ka da Yarinyar nan se nayi mummunan ɓata maka rai, wanda baka taɓa zata ba, bna son Yarinyar bana ƙaunarta, kuma ba zata cigaba da zama a cikin zuriyata ba balle a samu iri daga garera ba, sam bazan marba da ɗa daga Karuwa ba"
Gumi ne ya shiga tsatstafowa Imran, dan yasan aikin gama ya riga gama, inma cikinne wataƙila Amira ta samu, dan baya nacewa Ihsan ma kamar yadda yakewa Amira, kuma baya jin ze iya sake yadda ya nesanta kasan da ita, mussaman zamansu ɗin nan, da suka samu wata irin shaƙuwa da soyayya a tsakanin su.
"Ammi dan Allah kiyi haƙuri, kinga Amira idan lalacewar da tayi da halinta wani abun mun bada gudunmawa, ƙil da kin riƙeta ta samu kulawa ba lallai haka ta sameta ba"
"Karuwa tafi uwarka kenan da kake gayamin magana ko? To ban riƙe ɗinba kuma bazan riƙe ba, kaima kuma ba zaka riƙe ba, ina daf da datse wannan Auren dan ba sonshi nake ba"
Imran da ya sunkuyar da kai yai shiru, tai ta zazzaga masa masifa, seda tai ta gaji, sannan ya tashi ya tafi ransa a mummunan ɓace.
Da ya koma gida ya tarar da parr ɗin Ihsan a buɗe alamar ta dawo, bega Amira a falo ba, dan haka ya shiga paer ɗin Ihsan, ya sameta tana sallar la'asar, ya zauna ya jira ta idar, ta tashi ta naɗe sallayarta, ta ajiye.
"Ihsan baki ga na dawo bane?"
"Na gani mana me kake so in maka?"
Ya jinjina kai yace "ya jikin naki?"
"Ai da ka damu da jikina da baka kai wannan lokacin ba ka dawo ba, da ka dawo lokacin da nake jin zuciyata na daf da tarwatsewa, takaici da baƙinciki suka kwantar dani, amma har in kiraka a waya ka dinga rejecting, hakan ya tabattarmin da kaci amanata saboda waccan Karuwar, ka gaza cika alƙawarin da kaimin, in ba haka ba, ya za'ai in kiraka kai rejecting call ɗina, in maka magiya kaƙi dawowa?"
"Yanzu Ihsan irin wannan karɓar yakamata ki min? Wata guda da sati guda bama tare, ai idan ma laifin nayi miki kya bari ki min sannu da zuwa hakalina ya kwanta, seki min duk abunda zakimin ko, irin abunda yake haɗani dake kenan, ke ba kya uzuri, ba kya tunanin komai abunda zuciyarki ta raya miki shi kikeyi"
"Eh abunda zuciyata ta rayamin shi nakeyin, meyasa kamin alƙawarin da ba zaka iya cikawa ba? Ka dena sona kake na barwa karuwa kai"
"Karki kuma ce mata karuwa, bana son tahsin hankali daga dawowata"
"Na faɗa, ba karuwar bace, karuwa na faɗa na ƙara"
Idan Imran ya cigaba da tsaiwa, zuciya zata iya ingiza shi, yaiwa Ihsan lahani, dan haka ya fito daga part ɗinta, zuciyarsa na tafasa.
A falo yai karo da Amira, tana masa Magana amma idonsa ya rufe yai waje da sauri.
Hakan ya tabattar mata da Faɗa sukayi da Ihsan, Amira tace 'cigaba da wulaƙantashi, ke da gatanki da mahaifiyarki amma ni da nake marainiya ai dole in
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 25 Chapter of 31