ta karanta, dan haka zata fara aiki a wani gidan Jarida, ko saurarar Imran ba tai ba, tai breakfast tai ficewarta.
Imran ma kintsa wa yai ya fita, ba tare da wani da ga cikinsu yaiwa Amira sallama ba.
Rashin abunyi ya dami Amira, ta tashi ta sauke kayan wardrobe ɗinta gaba ɗaya ta sake shiryawa, ta sassauke kayan Kitchen ɗinta, suma tayi rearranging ɗinsu, ta fito nan babban falon ma, ta gyara ta kunna turaren wuta, tai girki iya cikinta wajen ƙarfe sha biyu ta kammala komai tai wanka ta fito falo ta zauna.
Ta kunna tv tana kallo, jin ƙarar buɗe gate tayi, ba ta motsa ba ta cigaba da kallonta, babu jimawa aka fara knocking ƙofar falon.
Tana ji tai Banza taƙi buɗewa, se kuma can ta miƙe ta tafi ta buɗe.
Imran ne a tsaye, ya kalleta yace "kina ji ina bugawa amma kika ƙi buɗewa?"
"Da can Ni nake buɗe maka? Naga ko ka saka key ka buɗe ko matarka ta buɗe maka" ta juya ta koma falon tana cigaba da mita.
Doguwar rigar material ce a jikinta pink me adon baƙi, kanta ba ɗankwali ta koma ta nemi guri ta zauna, Imran yabia bayanta da kallo harta je ra zauna, ba shi da lokacin Amira a yanzu, dan haka be bi takan abunda ta faɗa ba ya wuce.
Tana kallonsa ya kai ya kawo, ya shiga Kitchen ɗin falo ya haɗo cornflakes ya zo ya zauna ya na ci, da alama yunwa yake ji, ƙila Matar son ba ta bashi Abinci ba yau, Amira ta faɗa a zuciyarta.
Ya kammala ya ajiye kofin a gurin, ya tashi ze tafi.
"Gaskiya ku dena cin Abinci kuna barmin a falo, nifa ba baiwarku bace ehe, in ba haka ba wallahi aka kuma cin Abinci aka barmin a Falo sena jefe kwanon waje"
Waiwayowa Imran yai ya kalli inda Amira take, ya dawo da baya yazo ya zauna a kujerar da take, ya ƙura mata ido.
Seda ƙirjinta ya buga, dan wani Mugun kwarjini yai mata, da harya sa ta ɗan tsorata.
"Meyasa kika rainani ne?"
"Ni ba raina ka nai ba, naga baka buƙatar haƙurin da nake ne, shiyasa nake son inyi irin zaman da kake so"
"Ni kike gayawa haka?"
"Aini kullum ko nayi laifi ko ban ba a gurin ka laifi nayi, kuma nice mara Gaskiya, gara duk abun da yazo raina in faɗa maka, in yaso in ka ga dama ka kashe ni ka huta, tun da matarka bata laifi seni, kullum idan abu ya haɗamu se ka goyi bayan ta, gara in gaya maka duk abunda ya zo zuciyata, in yaso ka maidani in da kaje ka ɗakkoni"
Imran ya ƙara ƙureta da ido yace "Mata ta bata laifi ai, ko baki san kuna da banbanci ba, ba zan taɓa goyon bayanki ba, saboda ba kya ji sam, kinga illar rashin jin magana kenan, da tun a baya baki saba da fitina da rashin ji ba babu yadda za'ai a dinga baki rashin gaskiya, ina son matata sosai shiyasa na Aureta, ke kuma saboda ki dena rashin ji na Aureki, amma saboda tsabar rashin mutunci, har kike zagarmin Mata, kuma kike min rashin kunya ko? Saboda samun guri harda kuka dan na rungume matata, kin fiye rigimar gangan"
"An zageta ɗin, wallahi ta kuma ɓatamin rai sena mata rashin mutunci wallahi, in ba tai wasa ba sena mata illa, kuma ba runguma ba ka maida ita cikin ka ba abunda yaimin zafi"
Imran yana mamakin yadda Amira ke Kishi akansa, shi dai yasan ba'a kishin abu se ana sonsa, ya kasa gane inda Amira ta dosa.
Imran ya ƙara kallonta yace "Ƙarya kike, Kishi ke damunki, kuma bazan dena rungumeta ince ina sonta ba, kiyi mata illar kiga yadda zanyi dake, duk Matar da tai rashin ji a lokacin 'yan matanci ba ta taɓa daraja a gidan Aurenta, abun da a kaita nuna miki kenan kika kasa ganewa, darajar kamilar mace daban yake da wadda ta kasa tattalin kanta, dan haka karki sake haɗa kanki da Ihsan"
Amira ji tayi kamar Imran ya zuba mata garwashi a zuciyarta, nan da nan ta shiga sana'ar ta ta kuka, ta kalli cikin idon Imran, kawai ta fashe da kuka.
"Baka da adalci, wallahi se Allah ya sakamin abun da kake min, na barka da Allah"
"Ni kike cewa kin barni da Allah dan nace ina son mata ta?"
"Na faɗa na faɗa! Mara adalci bayan dukan da kamin ana gobe zaka Aureni, ka ɗau matarka kuka tafi lagos wata biyu, na tare a gidanka kana cigaba da muzgunamin kai da matarka, wallahi se Allah ya sakamin, Allah yana kallonka!"
Tai maganar tana kai masa duka ko ta ina a ƙirjinsa, ta haukace masa, riƙe hannunta yai gam, saboda yaji zafin maganganunta, da tace ta barshi da Allah, cikin haɗe rai ya murɗe hannayenta biyu.
Wani marayan Kuka Amira ta saki, tare da lumshe idanunta hawaye na Zuba ta gefen idonta.
"Wallahi kika kuskura kikamin Allah ya isa, se na nuna miki soja kike Aure ba civilian ba, Shashasha mara hankali"
Ya saki Amira ta zube a gurin nan, "Na barka da Allah, Allah ya sakamin, Mugu Azzalumi wanda baya tsoron Allah, Allah ne gatan maraya kuma insha Allah seya nuna maka ka taɓa marainiya"
Jin maganar Amira yai ta dira a zuciyarsa, dan gaba ɗaya mantawa yake Amira marainiya ce, be juya ya kalleta ba, ya wuce part ɗin Ihsan.
Ko da ya shiga ɗaki shiru yai yana lissafa abubuwa a ransa, yana tausayin Amira, amma ita bata tausayin kanta, bakinta da tsiwarta ke ƙular da shi, ko da zuciyarsa ta karaya a kanta, yana son ya ɗaga mata ƙafa, amma da ya tuna Karuwa ce se yaji a duniya babu wadda ya tsana sama da Ita.
A haka Ihsan ta dawo gida ta tarara da Imran, dama daren jiya ba Magana suke ba, ya shareta itama ta share shi, amma dai ta fuskanci kamar wani abu yana damunsa.
Ta shiga Kitchen ta fara ƙoƙarin ɗora girki, amma still Imran be kulata ba, sema tsunduma da yai a kogin tunani.
Se ƙarfe Uku ta gama girkin, ta sameshi a ɗaki tace "ga Abinci can na kai maka dining"
'na ƙoshi" shine abun da yace mata, ya tashi ya fice.
Da ya fito Falo ƙofar sashen Amira ya dinga kalla, juya wa yai ya fice daga gidan gaba ɗaya.
Abubuwan da Imran keyi sun fara bawa Ihsan mamaki, alamu sun fara nuna kamar Amira ta fara tasiri akan sa, idan ba haka ba ya za'ai ta masa abunda tai masa kuma ya ƙyaleta be ɗau mataki ba.
Wayarta ta ɗakko ta kira Mummynta.
Mummy na ɗagawa cike da damuwa Ihsan tace "Mummy akwai matsala fa"
"Matsalar me kenan?"
"Mummy, gani nake kamar Imran ze saɓa alƙawarin da yaimin, jiya yarinyar nan baki ga abunda tai masa ba amma ya ƙyaleta, kuma ya ɗau fushi dani, na bashi Abinci yaƙi ci, nima watsar da shi zanyi ba zan iya ba, mutum se baƙar zuciya tsiya"
"Ni ban gane ba, me tayi masa ne?"
"Faɗa mu kai da ita, ya shigarmin ta buga masa bokiti a ƙirjinsa amma ya ƙyaleta, dama jiya babansa ya zo, yana ta ƙara nanata masa wai yayi adalci, ni gaskiya bazan yadda in haɗa miji da wannan jakar ba"
"Idan ba zaki yadda ki haɗa miji da ita ba, ai ta ƙwace shi ta barki, ke da wannan zaune a gidanki zaki yi watsi da mijinki, dama abunda take so kenan, to maza kiyi watsi da shi karki janyo shi ki tattala shi, ni na rasa meyasa baki da wayo wasu lokutan, ki manta da lamarinta ki kama mijinki gam karki ba da wata dama daze kalleta"
"Mummy, kinga shigar da take tana yawo a gida kuwa?"
"Ke ma meya hana kiyi, a banza a waje tabi mazan wasu ina ga wanda aka ɗaura musu Aure? Muna nan muna ƙoƙarin ganik yadda zamuyi, kawai ki cigaba da haɗasu faɗa da ita, kuma ki kame shi sosai ki riƙe shi sosai"
"Shikenan Mummy nagode"
"Yawwa ki gaishe shi"
*To zeji"
Ta ajiye wayar tai shiru tana tunani akan maganganun Mummy, yanzu haka za ta cigaba da bin Imran, yana mata wulaƙanci wasu lokutan, dole tayi yadda za tai ta cigaba da haɗa gwaramar da za'a kori Amira, ko a raba musu gida gaba ɗaya,in yaso ta riƙe Imran ta hanashi zuwa inda Amira take, a haka har ta gaji ta kama gaban ta.
A
mira kuwa tana tsaka da kukan ta sega wayar Yadikko, abun ya bata mamaki ƙwarai, nan da nan ta goge hawayenta ta ɗaga wayar tai sallama.
Yadikko tace "wato Amira kin samu duniya kin manta damu"
"Haba Yadikko, ya zan manta daku, ni na isa ne, gani nai kamar kum manta dani, Babu wanda ya nemeni, seni na neme ku, shiyasa kawai nima na dena kiran ku a waya"
"Hmm ai shikenan, kina nan lafiya kuwa?"
"Sumul ma kuwa, baki ga yadda nai ƙiba ba, ƙalau nake"
"Ya kishiyarki kuma da mijin naki?"
"Lafiyar mu ƙalau Alhamdilillah"
"Kuma yanzu Imran ɗin yana sonki?"
"Dama ya taɓa ce miki baya sona ne? Yana son abarsa lumui muke zaune"
"Hmm ai shikenan, ai yaron nan ya banu mamaki, duk abun da ya dinga miki, kuma se gashibya Aureki kuna zaune"
"Eh, haka lamarin Allah yake"
Yadikko tace "dama zamu zo ganin ɗakinki ne, zamu zo garin Kaduna"
Cikin Amira ya bada ƙuuuu, tace "Aikuwa zamuyi tafiya ni da Captain, sedai in mun dawo"
"Yaushe zaku tafin?"
"Very soon, sedai in mun dawo"
"To shikenan, idan kun dawo ɗin seki sanar mana"
"To shikenan Yadikko, kice Usaman ya turon account lambarsa in turo masa kuɗi a sai miki kaza"
"Ahh har kuɗi yake dunƙulewa ya baki kenan?"
"Ƙwari kuwa, Kuɗaɗe ma ba kuɗi ba, a turomin zan tura kuɗi a sai miki kaza ki more tsufanki"
Yadikko tace "to madalla, ai na ɗauka an manta dani gaba ɗaya"
"Haba dai ni na isa, a gaida kowa da kowa"
Yadikko na katse wayar tace "tsinanniyar Yarinya, Allah ya kawo sanadin da za'a sakoki, makirar banza yana can tana hutawa, ku nemomin Usaman yazo a turo kuɗin, raba arne da makami ai ibada ne"
Umma tace "wai dagaske Yadikko zuwa gidan nata zakiyi?"
"Ƙwarai kuwa, se naje naga ƙwal iwar daka".
"Aikuwa ma biki, muma muje muga tsiyar da take ci take hura hanci tana fafa"
Yadikko tace "ai ko bangon duniya zauje su dawo, se naje gidan Amira na gano"
Amira kuwa ido ta zubawa wayar, tana tunanin idan su Yadikko suka zo suka ga irin zaman da take shikenan zasu zuba ruwa a ƙasa su sha ne dan murna.
"Allah ka kawomin ɗauki dan alfarmar shugaba Sallallahu alaihi Wasallam"
Ta miƙe ta gabatar da sallar la'sar, ta zauna tai Addu'oin ta da azkar, sedai still zuciyarta babu daɗi, ta rasa yaushene ita ma zata samu farinciki a rayuwarta.
Gaba ɗaya ta gaji da zaman Gidan Imran, ji take kamar a kurku take, ba walwala ba abokin hira, ga wulaƙanci da cin fuska da take fuskanta, gaba ɗaya taji zaman Gidan ya isheta, babban falo ta dawo ta kwanta, ta kunna TV, sedai sam hankalinta ba' kan TV ɗin yake ba.
Imran restaurant yaje ya cika cikinsa, sannan ya nufo gida, yana tafe yana tunanin maganganun Amira da tace "ta barshi da Allah" tabbas ya gaza kamanta adalcin da ya dace
Ihsan ta fito tana wani yatsine yatsinen fuska, kallo ɗaya Amira tai mata ta ɗauke kai, dan a ciki take da Ihsan, jira take tace mata tak, ta yaga ta.
Aikuwa seda Ihsan tai Magana "malama nan fa ba filin gala bane da zaki ƙure mana sautin kiɗa a gida"
Gyra kwanciya Amira tayi, ta cigaba da kallon TV, banda neman tashin hankali irin na Ihsan da rashin son a zauna lafiya, Music ɗin ƙasa ƙasa yake tashi, shima a cikin film ne aka sako waƙar, amma ta tsaya tana neman faɗa.
Dama Amira ƙiris take jira, ga haushin Imran a ranta ga Ihsan na ƙoƙarin tunzurata.
Ihsan kawai ta ɗau remote ta kashe TV, Amira ta miƙe tsaye tace "meyasa zaki kashe min TV"
"Saboda nan ba gidan magajiya bane, kuma ba gidan Gala bane, gidan mijina ne"
"Ni kuma daga yau zan maida shi gidan galar, na gaya miki karki ƙara shiga sabgata"
Amira ta sa hannu ta fizge remote ɗin hannun Ihsan.
"Wallahi ba za'a mayar min da gida na gala ba"
"Tun da mijinki ya auri 'yar gala, dole ayi gala a gidan nan"
Amira ta kunna TV, ta na komawa ta zauna, Ihsan ta kuma kashe TV tace "in kina da zuciya, ki koma in da kika fito gidan karuwai, kiyi a can"
Ai Amira yadda ta kawo wuya, idonta har rufewa yake saboda ɓacin rai, tana tashi ta janyo wuyan rigar Ihsan, tai jifa da ita tsakanin kujeru.
Wani uban Ihu Ihsan ta saki, ganin bakinta na zub da jini, Imran da ke ƙoƙarin rufe mota a gigice, ya nufo falon hankali a tashe jiyo kururuwar Ihsan.
Yana shigowa ya tarar da Ihsan a durƙushe, baki na zubar da jini, Amira na tsaye ta na huci.
Imran ya ƙarasa in da Ihsan take da sauri, ya ɗagota bakinta yai jawur yana jini, ga goshin ta ya kumbura.
Amira tace "wannan kaɗan kenan kika gani, ki kuma buɗe baki gayamin baƙar Magana wallahi sena tattakaki a gidan, sena watso miki haƙora waje.
Imran ya dinga goge mata jinin dake bakinta, ya kalli in da Amira take, idanunta duk sun kumbura, da alama ta daɗe tana kuka ne.
Maganganun ta suka kuma dawo masa na tabar shi da Allah, jikinsa ya kuma yin sanyi musamman da ya tuna yadda ya mirɗa hannayenta ɗazu ta dinga zubar da hawaye, girgiza kai kawai yayi yaja hannun Ihsan zuwa sashin ta.
Suna zuwa bedroom ɗinta ya saki hannunta ya kalli Ihsan yace "meya haɗaki faɗa da ita har tai miki haka?"
"Ai mema ya haɗamu kake tambaya? Ba zaka ɗau mataki ba, kalli bakina da goshina amma ka tsaya kana kallonta, wai me kake nufi ne?"
"To me kike so inyi, ya kike son in yi ne? In bita in ta duka Ihsan? Kokuma in ta faman ɗaga murya saboda na Auri mata biyu, kamar a kaina aka fara aure, na miki kashedi na miki jan kunne akan karki dinga shiga sabgar Yarinyar nan Amma kin ƙi ji, ki cigaba da biye mata watarana seta miki lahani"
Ya juya ze fice, hawaye shaɓe shaɓe a fuska Ihsan tace "yanzu kana nufin ta daki banza kenan? Banda zagi na da cin mutumci na iyayena da take, yau har da duka amma ba za ka ɗau mataki a kai ba"
"Ihsan na gaji da halinki na yawan ƙorafi, ke kullum cikin yi miki laifi ake, an tired na gaji da wannan yawan ƙorafin naki, she's also human being, ba zan ƙare kullum cikin shigar miki faɗa tana rainani ba, in kinga dama ki cigaba da shiga sabgarta ranar da ta karyaki kyayi bayani"
Imran ya juya ya fita yana huci, fashewa da kuka Ihsan tayi ta ɗakko wayarta, lambar Ammi ta nemo ta kira.
Ammi ta ɗaga wayar tare da yin sallama, kuka Ihsan ta saka hadda sheshsheƙa.
"Subhanallah, Ihsan lafiya kuwa?"
"Ammi na gaji, na kasa gane inda Imran ya dosa, matarsa ce ta dakeni, baki ga bakina ba kuma ba matakin daya ɗauka, Ammi na fara jin tsoron ko wani abun tayiwa Imran, da ma na ganta tana binne wani abu rannan, Ammi dan Allah kiyi wani abu"
"Amiran ce ta dakeki?"
"Wallahi Ammi duka na tayi, har da fasan baki"
"Kina me kika tsaya ta dakeki, baki samu abu kin rusa mata a ka ba, saboda wulaƙanci, gani nan zuwa gidan naku, shima Imran ɗin ze gauraya dani, gani nan zuwa"
Ihsan ta ajiye wayar tace "wallahi ba zaka maida ni 'yar iska ba, da mahaifiyarka zan dinga haɗaka, har seka rabu da wannan banzar"
Amira kuwa zamanta tai a falon, ta cigaba da kallon TV, labarai take kallo, taga yadda ake sanar da kisan sojoji a daji, da irin wahalar da suke sha a daji, gaba ɗaya ko motsi ba tayi, ta ƙurawa TV ido, ba zato ba tsammani taji Imran ya janyota daga kan kujerar .
Kunnenta ɗaya ya riƙe yace "ban gayamiki bna son rigima a gidana ba, ko nan yai miki kama da gurin dambe da zaki daketa, dan kinga kinfi ƙarfinta ko? Kin manta dukan da nai miki kenan kina son in sake Miki wani kenan?"
Shiru Amira tayi ta sunkuyar da kanta ƙasa, "idan kika kuma yunƙurin dukanta, ko makamancin haka sena rama mata, kin saba dambe da hauma haumarki a waje to ni ba zakimin a nan ba, na gaya miki"
Ya dungurar da ita a gurin, ya miƙe ya juya ze fita, kawai yaji sheshsheƙar kukanta, har yaje bakin ƙofa ya juyo ya ganta zaunia gurin, tana kuka girgiza kai kawai yai ya fice.
Seda akayi sallar magariba sannan Amira ta tashi ta koma ɓangarenta.
Tana nan kwance takaici yana nuƙurƙusar zuciyarta, Hasbunallahu wani'imal wakil kawai take maimaitawa don samun sassauci a ranta.
Ihsan ta gani a kanta ba zato ba tsammani, ɗaga kai tayi ta kalli Ihsan.
"Kin zata kin dake ni kim daki bulus ne, ai wallahi gidan nan ko da tsiya se kin barmin gida, kije uwar masu gidan tazo da kanta, dan in tabattar miki da na fiki power a gidan nan"
Seda ƙirjin Amira ya buga, jin Ammi ce ta zo gidan, Ihsan ta juya ta fice daga part ɗin.
Amira ta miƙe ta sanya hijjabi ta fita falo, ta tarar da Ammi a zaune, Imran na ƙasa a gefe, Ihsan ma haka.
Amira tai sallama ta nemi Guri ita ma ta zauna, Ammi ta kalleta a wulaƙance tace "ai na zata ba zaki fito bane hakima"
"Ammi sannu da zuwa"
"Rufen baki, ba sannu da zuwanki na zo ji ba, wato kin far fafutukar haɗa husuma a tsakaninsu, hadda duka kin fara gwada halin naki na 'yan tasha, ki Aure mata miji sannan ki dake ta banda binne binnen da kike dan ki rabasu ko? Wallahi ba da ina tunanin wani abu ba, wallahi da A daren nan zan sa ya sakeki ki koma in da kika fito, 'yar marasa mutunci mara tarbiyya kawai, wallahi da wasa kika kuma gangancin dukan Ihsan seya sakeki, kuma yanzunma ba haƙura nayi ba se na kashe Wannan Auren, da ɗana baze zauna da Karuwa ba lalatacciya irinki.
Kai kuma, wallahi ko da wasa na sake jin ta daki Ihsan ba ka ɗau mataki ba, ni zan zo in ɗauka kuma sena ci mutuncin ka"
"Ammi ya zanyi, kullum cikin tashin hankali suke, Ihsan ta kasa jan girmanta, ta fiye kishin tsiya...
"Rufemin baki, ya ba za tayi kishi ba? An Auro Karuwa an ƙaƙabo mata gida? Dole tai Kishi, haka kurum saboda son a sani na Mahaifinka ya ƙaƙabo maka wannan yarinyar, wadda ta gama gantalinta a waje, ta gama bin maza a bariki, ya sa ka Aureta, ai ko ba ta so seta bar Gidan nan, ba zan zuba ido ina kallo a kawomin mugun iri cikin zuriyata ba wallahi"
Amira ta ɗaga kai ta kalli Ammi, ta sunkuyar da kai, Imran ransa ya ɓaci da gayawa Ammi da Ihsan tayi, a jejjere A 'yan kwanakin nan baze iya lissafa adadin lokutan da ya ga Amira na kuka ba, shi tsoronsa ma kar wani ciwon ya kamata.
Ammi ta wanke Amira da baƙaƙen maganganu da cin mutuncin a gaban kishiya, Amira ta kawo iya wuya, dan zuciyarta raya mata take ta zagi Ammi, in yaso Auren ya mutu da hujja kowama ya huta, amma ta daure zuciyarta taita ambaton Allah.
Seda Ammi tayi ta gama, Sannan ta tashi ta tafi, Ihsan ta riga Imran dawowa falon, ta kalli Amira ta kwashe da dariya tace "a zatonki bariki sekayi Iskanci sannan zaka iyata, wallahi na fiki Rashin mutunci kuma gidane sekin barmin shi da mijina wallahi"
Amira ba ta ko ɗaga kai ta kalleta ba, Imran ya shigo ya kalli inda take zaune, ba ta tashi ba, sosai yajiata bashi tausayi, Ammi taci mutuncinta da yawa, amma haka shima ya shareta ya wuce ya barta a gurin.
Ihsan ta zaci Imran yana shigowa zasu shirya, sedai taga sam ko kulata beyi ba.
"My wai haryanzu fushin kake?"
A fusace yace "tambayata ma kike? Idan har Amira zata iya rufamin Asiri ta ɓoye laifina a gurin mahaifina, ke meyasa kikamin haka? Am disappointed on you"
"Amma meye dan na gayawa Ammi, na faɗa mata ne dan taiwa tufkar hanci, kar inje ka zagaye ka koma gurinta"
Ran Imran ya ɓaci matuƙa, be kuma tanka mata ba ya bar mata ɗakin, ya koma ɗaya ɗakin ya rufe ƙofa.
Da Asuba ya fito zashi sallar Asuba, sedai ga mamakinsa ya ga Amira kwance a falon nan inda suka barta, a gurin ta kwana.
Seda Imran ya firgita, ya ƙarasa inda take da sauri, sedai yana dubawa yaga Bacci take, se ajiyar zuciya take.
Ya ɗan ƙuramata ido, gaba ɗaya tausayinta ya mamaye zuciyarsa.
Tashi yai yaje salla ya dawo, sedai da ya dawo ya tarar ta tashi daga gurin.
Wani zazzafan zazzaɓi ne ya rufe Amira, ga ɓacin rai ga damuwa, se rawar sanyi take a ɗaki ita kaɗai.
Message ne ya shiga wayar Imran, ana nemansa da gaggawa turasu Zamfara aiki.
Nan da nan ya fara shiri, duk da a ƙule yake da Ihsan, yaje ya sameta yace "Ihsan, Anjima zan tafi Zamfara, an turamu aiki"
Cikin ko in kula tace "Seka dawo"
Abun ba ƙaramin mamaki ya bashi ba, duk da sun samu saɓani amma ta kasa nuna a sign of care to him.
Amira ji tai sanyi ya dameta saboda zazzaɓin dake jikinta, fitowa tai Kitchen na Falo, dan ta dafa tea ta sha ko zata dena jin sanyi.
Imran ta gani sanye a Uniform ɗinsa na Sojoji, hannunsa riƙe da wayarsa ya sata a kunnensa yana Magana.
"Wallahi Abba nima cikin dare naga message ɗin, an turamu Zamfara ne kasan last week an kashe sojoji sosai, to ina cikin wanda aka tura, naso in biyo gida in muku sallama, amma an zo ɗaukata zamu tafi ne yanzu"
Saroro Amira tai tana kallonsa, dagaske Zamfara ze tafi.
Har ze fita Amira ta ƙarasa da sauri in da yake, ta riƙe hannunsa.
Waigowa yayi ya kalleta, ya kalli inda ta riƙe hannunsa, ya kalli fuskarta duk cizon sauro fuskar a kumbure.
"Wai Zamfara zaka tafi?"
"Eh, can zan tafi" ya bata amsa.
"Dan Allah kar ka tafi, kashe sojoji ake"
Kallon Amira yai, dagaske take maganar, mamaki ne ya cika shi, duk da tarin abun da aka mata, amma tana kiran kar ya tafi, ana kashe mutane.
"I was Born to serve my country, ko in dawo a raye ko a kashe ni, just pray for me"
Ya kai hannu ya goge hawayen da ke zubowa daga idonta, hakan yasa yaji jikinta da zafi yace "idan na mutu a can forgive me please!"
Domin gyara, Sharhi ko Shawara
Ayshercool
07063075680
[2/4, 7:37 PM] Ayshercool: 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
WUTA A MASAƘA
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P. W. A
*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA)
*BAƘIN TABO (Labarin gasa)
*AƘIDATA (Paid Book)
* WUTA A MASAƘA
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in
❌❌❌
Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.
37_38
Sake fashewa da kuka Amira tayi tace "ni dai ba na son ka tafi"
Ɗan shiru yai yana kallonta "meyasa ba kya so na tafi?"
"Ana kashe mutane, kuma bana so a kashe ka"
Jikin Imran yai sanyi sosai, ya kalli yadda ta riƙe hannunsa, ga idanunta na zubda hawaye.
Gyara tsayuwarsa yai, ya ɗago fuskarta, ta na kallonsa, fuskarta duk cizon sauro ga idanunta sunyi jawur"
A hankali yace "kin kwana a falo sauro ya cije ki, kinga zazzaɓi ya rufeki, kije ki kwanta zuwa anjima ki kira Anty a waya, a kawo miki magani, zan tafi abokan tafiya ta suna jirana, dan Allah ban da faɗa ko tashin hankali, ni na tafi"
Ya zame hannunsa a hankali, ya juya ya fara tafiya, bayansa ta bi da kallo, har ya fita daga falon.
Jiki a sanyaye ta koma ta Kitchen, ta leƙa window, ta ga sojoji a harabar gidan jikinsu da Uniform, suka hau mota suka fita.
Amira ta zauna a Kitchen ɗin ta haɗa kai da gwiwa tana maimaita 'Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"
Sun yi nisa a tafiyar, Imran ya kira Anty, tana tsaka da aiki ta ga kiran nasa, amma tai ƙoƙari ta ɗaga wayar "Anty barka da safiya"
"Yawwa barka Imran, ya kake ya gida?"
"Lafiya ƙalau, ya aiki?"
"Aiki Alhamdilillah, mun fito tun ɗazu"
"Masha Allah, dama Anty nace dan Allah idan ban takura ki ba, kinga an turani aiki Zamfara ne, kuma na bar Amira ba lafiya, ban san lokacin
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 20 Chapter of 31