yai kanta, amma ko gezau balle tai yunƙurin guduwa.
Yana zuwa ya murɗe kunnenta ɗaya, seda ta wani uban fitsari ya matsota, "ni kikewa rashin kunya ko? Kinga kwana biyu ina saurara miki ko? Shine kika samu damar yin wannan rashin mutuncin ko?"
Riƙe hannunsa da ya riƙe mata kunne tai tana kuka, ya dungurar da ita a gurin, ya nufi inda Ihsan take, ya riƙo hannunta yace
"Am sorry my, kiyi haƙuri wallahi ban san yadda a kai haka ta faru ba"
Ya ja hannun Ihsan zuwa ɗakinsu, yaje yaita lallaɓata yana tunanin yadda ze gaya mata ze tafi da Amira Lagos.
Seda ya tabattar ta haƙura, sannan ya tashi ya fita sallar magariba, ya wuce Amira a falo tana kuka, shi har mamakin yadda Amira ɓarin hawaye kamar ba daga jikinta yake zuba ba yake, ya wuce ta ya tafi masallaci.
Ihsan ta fito ta kalli Inda Amira take ta yatsuna fuska tace "Wallahi in dai zaki cigaba da takara da ni a gidan nan, baƙi ciki Yanzu kika fara kwasa"
Amira bata tanka mata ba, tai ta gama ta koma ɗakinta.
Imran ya dawo daga salla, ya kuma hango Amira a zaune, yana nan tsaye be shigo ɗakin ba, se aka ɗauke wuta, nan da nan ta miƙe da sauri, tan waige waige tana ƙoƙarin laluben hanya, dan ba laifi Amira akwai tsoro.
Jin ta tayi a jikin mutum, ware murya tai za tayi ihu, amma ya haɗe bakinsa da nata, ƙoƙarin ƙwacewa take daga jikin Imran, amma ya riƙeta gam.
Seda yai me isarsa sannan ya kai bakinsa kunnenta yace "to fitsararriya, ga rashin kunya ga tsoro, ki shirya kayanki jibi in Allah ya kaimu zamu tafi Lagos tare"
"Bazanje ba, ka tafi da Wannan ƙandararriyar"
"Ni kike cewa ba zaki ba, ai ƙandararriyar ta fiyemin ke, Abba zaki cewa ba zaki ba, saboda idan na tafi dake ba wani amfani da zakimin, kuma a ƙandaren nake sonta"
"Eh kaita son nata, ni cikani in tafi, ka murɗemin kunne ban maka Komai ba"
"Cigaba da ɗaga murya, ta zo ta ganki a haka zaki mata bayani ne, hadda saura raba kwana saboda baki da kunya"
"To tsoron ta nakeji? Ai ba tsoronta nake ji ba, kuma ina kai ina tunanin Kunya a tare da Karuwa, ni ka ƙyaleni dan Allah"
Ɗan saroro yai yana kallonta, duk da a duhu ne tana sauke numfashi a fuskarsa shima yana sauke mata, a hankali ya cikata ya juya ya nufi part ɗin Ihsan.
Yana shiga ya zauna, sega wayar Abba nan, ya ɗaga ya gaida Abba, Abba yace "Imran yaushe ne tafiyar ka Lagos ne?"
"Abba jibi in Allah ya kaimu ne"
"To kasan dai yadda mu kai da kai, wannan karon tafiyar ta Amira ce, dan haka kai mata Magana ta fara shiri, nayi waya da kakarta da zasu zo da weekends, amma na gaya musu zaku tafi lagos, se Allah ya dawo daku tukuna"
"To Abba, zan gayamata insha Allah"
Ihsan ta kafe Imran da ido ko ƙiftawa ba tayi
SHARE PLEASE
A ko yaushe ina alfahari da ku, ina jin daɗin sharhin da kuke akan littafin nan, ina matuƙar godiya sosai, masu gyara, sharhi da ƙorafi duk ina godiya, wanda ban samu amsa saƙonninsu ba a dinga min Afuwa, abubuwane da yawa, sannan dan Allah masu bina pc suna in basu daga farko, ko in basu oage kaza, dan Allah ku dinga min uzuri, abubuwa sun min yawa sosai, ku dinga tambaya a groups ko Ku duba a watpad, nasan sone yasa kuke neman littafin, amma dan Allah a dinga min uzuri, sannan ga wanda suka turan kuɗin ruɗin Ƙuriciya kuma, su sakemin magana Please in saka su a group, this week zan fara free pages insha Allah, Nagode"
Domin Sharhi, gyra ko shawara
07063065680
[2/8, 7:57 PM] Ayshercool: 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
WUTA A MASAƘA
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P. W. A
*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA)
*BAƘIN TABO (Labarin gasa)
*AƘIDATA (Paid Book)
* WUTA A MASAƘA
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in
❌❌❌
Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.
*🌈NIMCY'S LIBRARY🌈*
_Readers gareku, masu tambayar old books na NIMCYLUV SARAUTA, tayi shiru ne domin tana bada bunus kafin azumi, to Finally the day is here, tana sai da littafan ta gaba ɗaya akan 3k gaba ɗaya littafan guda 14 ne, to bisa Bunus ɗin da tayi na tsayin sati guda dukkan mai so zai biya 1500 mai makon 3k😍, nasan baku karanta littafan ta na baya ba, da am sure za kuce sunma fi na yanzu daɗi❤️🤨_
So what are waiting for.....??? Go and subscribe your own...
Abu Maleek
Sirrin mu
Uncle ne
The new emir
Izzar so
Sai na aureta😍
Tsintacciya
E.t.c guda 13 via 0116886423 sulaiman Naima s union bank evidence of payment 08119237616 a biya asha karatu Tabbas za kuyi farin ciki littafan babu baya #Love #Romance #Destiny
Bonos ya fara 6/2/2022
Share fisabilillahi😍
41_42
Ya ajiye wayar, ya kalli Ihsan zeyi magana ta ɗaga masa hannu, "Yanzu Imran da ita za ka tafi, ina ji ina gani ka barni a nan? Ka ɗauketa ku tafi, Imran ina alƙawarin da kai min? Nasan ba zaka taɓa cikawa ba".
Tai maganar zuciyata na matuƙar tafasa.
Imran ya gyara zamansa Sannan yace "Ihsan, wallahi dan ta ni kin san ba zan ɗau yarinyar nan in ce zan tafi da ita ba, da kunnenki kin ji ai, Abba ne ya bada umarnin nan ba wai ra'ayina ne hakan ba, ki fahimceni mana".
"Ni ka ƙyaleni, ba abunda zan fahimta, wannan ai cin fuskane taya zaka je ka zauna daga ita se kai a gida, kuma hankalina ya kwanta ba abunda ze faru? Gaskiya ni ban yadda ba"
"To me ki ke so ayi? In cewa Abba bazan tafi da ita ba ko kuma yaya?, Da da bani da Aure mutuwa nayi? Ko kuma kwanakin da nayi a daji ba mace wani abu ta sameni, ke kanki da nake so in ki kamin laifi muna kwana shimfiɗa ɗaya kuma in ƙaurace miki, meyasa kike tunanin wani abu ze haɗani da ita, haryanzu kin kasa yadda dani"
Gaba ɗaya maganganun Imran jin su take a matsayin kalaman yaudara da rainin hankali, ta miƙe ta ɗau wayarta, ta tafi ɗayan ɗakin ta rufe ƙofarta.
Imran ya shafi sumar kansa, ya kwanta akan gadon, ya fuskanci idan ya biyewa matan nan zasu maida shi mara hankali, kowacce da kalar tata rigimar, ba ƙaramin kwarjini ne da shi ba ko a wajen aiki, amma idan ya dawo gida mata su dinga caza masa kai, ya ɗakko wayarsa ya hau chatting.
Yana dubawa ya ga Khalid online, yai masa sallama Khalid ya amsa yace "kai Angon biyu ya? Ka wartsake kenan?"
"Tun yaushe, zan dawo aiki ma"
Khalid yace "Haba? Yaushe zaka zo?"
"Jibi in Allah ya kaimu, zan taho insha Allah"
"Masha Allah, wannan karon kai ɗaya zaka taho ne?"
"Ina fa, Abba yace sena taho da Amira"
Khalid ya tura masa emoji na dariya yace "gaskiya Abba ya kyauta, ka ga an biyata kwanakinta da Ihsan tayi"
"Wallahi Khalid mata na da matsala ta gaske wallahi, Ihsan ta ɗau fushi da kumbura baki Abba yace in tafi da Amira, ban taɓa sanin haka Ihsan take ba, ban san da yawa daga halayenta ba se da na Aureta, ta fiye ƙorafi da rashin haƙuri, ina tausaya mata da ɗaga mata ƙafa amma ba ta gani sam"
"Ai dama hakane, kai ma nasan ba ta san da yawa daga halayenka ba se yanzu da ku kai Aure, sedai ku cigaba da haƙuri da juna, ka dai rarrasheta kar ka tafi ka barta a damuwa"
"Ai na fara gajiya da rarrashin nan, anyway na san dai abunyi"
"Aikam ya kamata kasan abunyi tun da wuri"
"Shikenan sena shigo Lagos ɗin"
"Allah ya kawo ka Angon Amira"
Imran yace "za kaga Angon Amira, idan Ihsan ta jika"
"Ai ni Amira nakeyi dama"
Suka cigaba da hirarsu ta abokai.
Ihsan kuwa zuciyarta na tafasa ta kira mahaifiyarta a waya, kusan missed calls uku bata ɗaga ba, ta ajiye wayar tana safa da marwa a ɗakin, tana jin Kamar zuciyarta tai bindiga.
Mamanta ce ta biyo kiran da tai nata, da hanzari ta ƙarasa ta ɗauka, ta na ɗagawa tace "Mummy na shiga uku"
"Innalillahi wa innalillahi raji'un, kika shiga uku da me?"
"Mummy wai da Amira ze tafi lagos, na rasa me naiwa tsohon nan ya tsaneni, baban Imran sam baya ƙaunata, baya sona da ɗansa, akan mw za'a ɗau Amira a tafi da ita? Me nayi masa haka fisabilillahi, kin san Yarinyar nan karuwa ce, wallahi tsaf zata iya jan hankalinsa"
Mummy tace "tsaya, wai waye ya gayamiki da ita ze tafi ne?"
"Ammmi yanzu fa yai waya a gabana da Abban, ya sake maimaita masa ashe tun da ya dawo aka tsara in ze tafi Lagos ya tafi da ita, amma be gayamin ba, wallahi Ammi tsoro nakeji, karya tafi da ita kashina ya bushe yaje tai masa wnai abun"
"Ke kwantar da hankalinki, ba abunda zefaru nasan abunyi"
"Mummy meye abunyin to?"
"Ki ɗan sauraramin, zan waiwayeki Insha Allah"
"To amma fa Mummy jibi zasu tafi"
"Ba abunda zefaru tsakanin su, nina gayamiki"
"Amma Mummy, wane tabbaci ki ke da shi akan hakan?"
"Ke ina ruwanki ne? Ina da abunyi ni a kai"
"To Mummy, Allah yasa abun yayi".
Ta kashe wayar a sanyaye, ta gayawa Ijsan hakanne dan kawai hankalinta ya kwanta, amma ba ta da wani abu da zata iyayi a kai, tasan halin Ihsan da damuwa da saka abu a rai.
Lambar Ammi ta kira, seda ta kusa katsewa sannan ta ɗauka tace "Afwan bana kusa da wayar ne,barka da dare"
Mummy tace "Yawwa barka, ya iyali?"
"Alhamdilillah, ya zafin nan?"
"Gashi nan Alhamdilillah, nace kin san kuwa Imran jibi in Allah ya kaimu ze tafi Lagos da matarsa?"
"Bari kawai, naji wallahi ba yadda ban ba akan in shawo kan mahaifinsa a janye maganar nan, amma abu ya gagara duk ta in da na ɓullo masa seya kange, kwana biyu na kasa gane kansa, amma ku kwantar da hankalinku, Shi Imran ɗin na san yadda zan dashi, tunda nina haifeshi dan Allah karku damu akan Wannan Yarinyar"
"To shikenan, dama Ihsan ɗin ce ta kirani a waya hankalinta a tashe, shiyasa nace bari in kiraki, amma tunda kince haka shikenan"
"Bakomai, dan Allah ki kwantar mata da hankali, ba wani abu Insha Allah"
Mummy tace "shikenan, seda safe, ki gaisarmin da daughter na please"
"Za taji insha Allah".
Amira kuwa cike da nishaɗi ta koma ɓangaren ta, tana ji a jikinta burinta na daf da cika tunda Imran ya fara sakin layi, ga kuma tafiya za suyi tare.
Anty ta fara kira a waya ta sheda mata cewar zasu tafi Lagos jibi tare da Imran, Anty taji daɗin hakan sosai tai murna, Antyn tai ta yiwa Amira Nasiha, sannan ta gargaɗeta da anyi mata wani abu na ba daidai ba wanda ba ta gansu da shi ba ta sanar da ita.
Amira tace Anty ta bawa direba Akwati ya kawo mata, ta haɗa da tata dan tata ƙarama ce, wadda zata haɗa kayanta a ciki.
Imran haka suka kwana ɗaki daban daban shi da Ihsan, da sassafe Ammi ta kirashi a waya, wai ta na son ganinsa, ko karyawa beba ya tafi gidansu.
A bedroom ya iske Ammi, tana karyawa, ya gaisheta ta amsa masa sama sama, yace "Ammi naji kince kina nemana, Allah yasa lafiya?".
"Lafiya ƙalau, da ma ba wani abu bane ba, batun tafiyar ka da Yarinyar nan da ubanka ya dagw a kaine na kiraka in maka kashedi, kamara yadda na sha gaya naka da farko, ni ba zan taɓa murna da haɗa zuriya da tsohuwar kilaki ba, dan kowa irin Arziki yake bibiya bana tsiya ba, ina me ja maka kunne da kiranka da babbar murya, ba kai ba Wannan Yarinyar kar inji ko inga abunda ze ɗagawa matarka Ihsan hankali ko ya ɓatamin rai, ina Ganin mutuncin mahaifiyar Ihsan dan haka ba zan taɓa bari ko in goyi bayan a wulaƙanta mata 'ya ba, idan kuka je Lagos ka nemi wani gidan a Barrack ko a waje ka ajiyeta, karka kuskura ku zauna a gida ɗaya tare"
Da mamaki ya kalli Ammi yace "Amma Ammai, idan na ajiyeta ita kaɗai wani abun ya sameta Abba ze ɓatamin rai".
"'yar yayace ita da swka kula da ita ko kuwa? Kabi umarnina ka zauna lafiya, idan ka kuskura wani abu ya shiga tsakinka da Yarinyar nan zan iya mummunan saɓa maka, bana ƙaunar yarinyar nan so nake yadda tazo gidanka ta fita ba tare da wani abu ya haɗaka da ita ba"
Imran ya jinjina kai yace "to naji zan kiyaye insha Allah"
Ammi tace "da yafi maka, ka tashi kaje falo ka karya"
Tai maganar tana miƙewa tsaye, falo suka fito jikin Imran duk a saluɓe, suna fitowa Abba yana shigowa falon, ya kalli Imran yace "kai lafiya kuwa, kake tafe a safiyar nan?"
Imran ya dake yace "lafiya ƙalau Abba, nazo yi muku sallama ne kasan gibe in Allah ya kaimu da la'sar zamu tafi"
Abba yace "Au ai na zaci wani abunne ya faru, maimakon ka taho dasu ko ka tabo da ɗaya se ka taho kai kaɗai? Ko da kwaɗayin girkin mamanka ne ya kawo ka?"
Imran ya ƙaƙalo murmushi yaiwa Abba yace "A'a Abba"
"To shikenan, ina Minal ta kawo mana kayan Abinci nan mu ci gabaɗaya"
Aka kawo musu Abincin nana, suka ci tare, suna ci Abba yana sakewa Imaran Nasiha daban daban akan Rayuwa, da kuma riƙe matansa da amana da gaskiya gami da adalci a tsakaninsu...
Anty kuwa da kanta ta kaiwa Amira akwatin, ta nunnuna mata abubuwan da sukafi mahimmanci ta tafi dasu.
Sannan tace "Amira, you got a very nice to win your husband heart, kin samu cikakkiyar dama daga ke seshi, ba wani shamaki ko damuwa da zata gifata muku, ki tabbatar da kinyi duk me yiwuwa ki janyo hankalin sa kanki, sannan ki duƙufa da addu'a kin san itace gaba akan Komai, ki jajirce ki ƙwatarwa kanki 'yanci a gidan miji, kishiyarki ba ta fiki Komai ba, duk abunda ake nema agurin mace kema Allah ya baki, dan haka ki dage kiyi ƙoƙarin yin duk wani abu da zw janyo hankalin sa kanki kinji ko?"
Amira ji tai tamkar Anty ta san halin da take ciki a gidan, duba da yanayin nasihar da take nata, Amira tace "to Anty insha Allah, zanyi abunda kika ce"
Anty ta bata wasu zafafan turarraykan, da kayan gyara jiki sannan tai mata fatan Alheri ta tafi"
Amira ta raka Anty har bakin motarta, suna tsaye suna magana Ihsan ta dawo, tana zuwa ta gansu a tare da Anty ta ja wani uban tsaki ta wuce, daga Amira har Ihsan ba wanda ya kulata, suka cigaba da maganarsu bayan sun gama, sannan Anty ta hau mota ta tafi.
Tafiyar Anty babu daɗewa sega wasu 'yan uwan Ihsan sunzo, cousins ɗinta biyu da ƙawayenta biyu.
Ihsan ta saukesu a Babban falo, suka baje suna hira, ta kawo musu Abinci suka zauna nan suna ci ɗaya daga cikin su tace "ke wai ni ina kishiyar taki ne, tun da nake zuwa ban taɓa ganinta ba fa, duk zuwan da mu kai bata nan"
Ɗaya tace "to ta ina zata zauna, matar da aka ce miki Karuwa ce, sufa irin wannan ba denawa suke ba, da Auren ma se subi maza"
Ihsan ta yatsina fuska tace "ba dai kishiyata ba, dan wannan ba ta kai kishiya a idona ba, Karuwace fa bin maza take, kwararo kwararo aka ɗakkota aka liƙa masa dan a temaka mata, kuma zaman gadi take dan ba ta kai mijina ya saurareta ba wallahi"
Wata uwar shewa suka saki gaba ɗaya "Lallai Ihsan ba ki da dama, wato liƙa masa ita a kai, to ai shikenan, ni dai ina son in ganta"
Suna cikin hirarsu 'yar halak sega Amira ta fito, hannunta da labulaye zata bada wanki, ta kalli Baƙin Ihsan da su kai tsit saboda fitowarta, tace "baƙi mu kayi ne? Sannun ku da zuwa"
Shiru su kai, se ɗaya daga cikin su ce tace "Yawwa sannunki"
A fusace Ihsan tace "Nabila ina ruwanki da ita? Meye na amsa mata, gurinta ki ka zo?"
"Au ko itace kishiyar taki ne?"
"Itace fa"
"Kan uba, lallai wannan ai 'yar galace, ba itace kwanaki akace za ta fito a wata rawa ba, video ɗinta ya dinga yawo ba"
Ihsan tace "to itace ta sa aka fasa Auren Uncle Hassan, ta rufeshi a banɗaki"
Wucw su Amira tai, taje ta kaiwa me wanki kayan, ta dawo ta kuma wuce su zata shiga parr ɗinta.
'gaskiya wannan annamimiyar Karuwa ce, taɓɗijan wallahi kibi a sannu kar kema tai waje dake, Allah ma ya tsare kar a samiki HIV, tunda tabi musulmi tabi Arna dan tsabara iya Akuyanci"
Amira ta juyo ta kallesu tai murmushi tace "Ai Karuwanci ya gama min Komai, nai suna nai kuɗi a dalilinsa ƙarshe kuma Allah ya bani mijin sokuwa na Aura, ai Karuwanci yai riba" ta ƙarasa Maganar tana shigewa ɓangaren ta, nan suka ɗau salati gaba ɗaya, suka dinga ziga Ihsan, suka dinga zigata akan yadda za tai da Amira, ita kuma ta dinga cika baki tana cewa ai mijinsu baya sonta, dan ko ɗakinta baya shiga, ta dinga gayamusu yadda Imran yake wulaƙanta Amira, suna shewa suna ƙara ɗorata a keken ɓera.
Yadda Ihsan tai watsi da Imran, shima haka ya shareta, dan ya gaji da aikin rarrashin ta, shima ya shiga haɗa nasa kayan, tun daren ds zasu tafi Ihsan take fargaba take faman koke koke, ta bi ta dami kanta ta ƙi cin Abinci saboda fargaba.
Amira ma ta kammala shirinta tsaf, ta haɗa duk wani abunda take buƙata, wajen ƙarfe sha ɗaya na safe, Imran ya shiga ɓangaren Amira, kai tsaye ya tafi bedroom ɗinta, ya tarar da ita daga ita se underwear tana shafa mai, da alama wanka tayi.
Ya ɗanyi turus saboda tozali da kyakykyawar surarta, fatarta se wani sheƙi take kamar bata shiga rana, Gashi ta shafa mai se ƙyalli take, gashi ta ciko da ga Wannan ramar da tayi, saurin ɗauke kansa yayi yace "ki zama cikin shiri tun ƙarfe biyu zamu tafi airport, idan kuma kika ɓatamin lokaci ba jiranki zan ba, zan tafiyata ne"
Ɗago idanunta tai tana kallonsa tai wani murmushi tace "to My zan shirya da wuri insha Allah"
"What? Waye my ɗin naki?" Yai Maganar yana kallonta
Ta ɗan kashe murya tace "Gashi nan a tsaye a gabana, namijin duniya sha gwagwarmaya, soja maganin wani sojan, ɗaya kake tamkar da goma, sadauki me abun bajinta, dogo Mijin Amira me hannun kyauta"
Imran be san lokacin da murmushi ya suɓuce masa ba, that girl is very Funny at times, duk da abun haushinta yafi yawa, yace "Kin fiye shirme, ni dai ki shirya da wuri"
"An gama ranka ya daɗe, na haɗa Akwatina ma"
Yace "good sannan ya juya ya fita"
Tabi bayansa da kallo tai murmushi haɗi da jinjina kai.
Ta shirya cikin riga da skirt na shadfa, ta fito falo, tana ta kaiwa tana komowa tana shiri, ta fita farfajiyar gidan ta tarar da Ihsan tana waya, Ihsan ta watsa mata wani Mugun kallo, Amira tai murmushi tace
"Wai ke dama da na gayamiki se zaki san kin tafi da mijina Lagos kinyi wata biyu, ba ki zaci zan rama ba kenan? Ai dama na gayamiki tuntuni gara tun da wuri ki dena wannan harare hararen, he is now my not yours, don't ever under estimate the power of a Woman like me, Karuwancina me license ne, kuma lokaci ne yazo da zan ɗanɗana miki abunda kika min, wallahi Ihsan se kin zubar da hawaye fiye da yadda kika sa na zubar, bana riƙo ina da manta abu, amma kin shiga sahun Mutanen da har in koma ga Allah ba zan manta abunda su kai min ba, ni ba zan cutar da ke kamar yadda kika min ba, Amma daga yanzu ki rubuta ki Ajiye cewar Imran namu ne mu biyu ba ke kaɗai ba, Ihsan iliminki na addini da larabcin da kike ba suyi miki amfani ba, idan har son tsakani da Allah ki kewa Imran, bekamata ki zuba masa ido ya kai kansa ga halaka ba, hakkina kawai ya isa ya nesanta shi rahamar Ubangiji, Amma son zuciya ya katange miki idanunki, kanki kawai kike kallo, Yanzu zan nuna miki match ɗin da kika tari ba ki da 'yan wasa sam, yanzu za'ai playing game ɗin yadda yakamata, zan nuna miki kishi da Karuwa se macen da ta shirya" ta ƙarasa Maganar tana huci, ta bar Ihsan a gurin baki a buɗe tana kallonta.
Amira ta koma ɗaki ta kwaso Akwatinta, ta fito dasu harabar gidan ta ajiye, da duk abubuwan da take buƙata.
Ihsan kuwa ɓangaren ta ta koma, ta fashe da kuka hadda sheshsheƙa, ji take kamar ta kunnawa gidan wuta duk su mutu a ciki saboda baƙin ciki, Imran se biyu saura ta shigo gidan, a gurguje ya leƙa ɓangaren Amira, ya tarara ta shirya tsaf, yace "yawwa gara da kika shirya ai, an sa miki kayanki a mota, kaya kawai zan canza mu tafi"
"Ya ma za'ai in tsallake maganar Husband ɗina, na shirya tuni"
Bece komai ba ya wuce part ɗin Ihsan, aikuwa ya tarar tana ta uban kuka, idonta kamar an zuba mata barkono, sunyi jawur kamar ba ita ba, ya zauna ya dinga bata haƙuri yana kwantar mata da hankali, Wani Mugun haushin Imran take ji, ji take tamkar ta shaƙeshi, dan ita gani tai Kamar yana ɗokin tafiyar, ya miƙe a gurguje ya watsa ruwa, ya canza kaya yace "Ihsan ko bakin mota ba zaki rakani ba?"
Girgiza kai tayi tace "A'a kuje kawai"
"No taso ki rakani"
Haka ya janyo Ihsan suka fito, yana ta cigaba da rarrashin ta yana rungumeta, Amira kuwa ta sha ɗaurin ture kaga tsiya, tayi parking ɗin gashinta.
Fuskarra babu kwalliya amma shar da ita tai kyau se ƙamshi take.
Amira gani tai Imran ya lalace a gurin Ihsan, se hawaye take yana goge mata yana Magana ƙasa ƙasa.
Amira tace "My love kace kar in ɓata maka lokaci, na shirya da wuri amma kai ka tsaya Sallamar ta isa haka"
Gaba ɗaya suka tsaya suna kallon Amira, kalmar my love ɗin da Amira faɗa ce ta daki ƙirjin Ihsan, ba shiri ta zame hannunta daga na Imran ta koma cikin gida, Idan Imran yace ze bita yasan faɗa zasuyi babu lallai ma ta saurareshi, ga lokaci yana ƙurewa dan haka kawai ya nufi inda motar take.
Ya buɗe gaban motar ta shiga, sojan da ya kai Amira gurin Kwalliya shine Yake jan motar, Imran be cewa Amira uffan ba, itama ba ta tanka masa ba, har sukaje airport.
Ƙarfe biyar da mintuna goma suka isa Lagos, se wajen shida saura sannan suka isa gidan Imran da ke barikin soja na Ikoyi.
Amira ta san tazo Lagos saboda bambancin al'ada, tunda syka shigo cikin Barack ɗin take ganin mutane kala kala, har suka isa gidan Imran.
Da alama akwai kyakkyawar alaƙa tsakaninsa da abokan aikinsa, dan tun daga gate da suka taho, yake gaisawa da mutane.
Gidan ɗan madaidaici ne me kyau, kan Imran yazo yasa aka gyara gidan, amma duk da haka gidan yayi ƙura sosai, ba wani gayara a kai masa na musamman.
Imran ya kalleta yace "ki shiga wancan ɗakin akwai toilet kiyi alwala kiyi salla.
Ta amsa masa da to.
Ya shiga ɗaya ɗakin, yai alwala yayi salla, saboda lokacin salla ya ƙure ba ze samu wanda za suyi jam'i a masallaci ba, ya idar da salla ya fito ya tarar da Amira a zaune a inda ya barta ya kalleta yace
'Ke sallar ma ba zakiyi bane? Nace ki shiga kiyi alwala kiyi salla amma kin zauna"
A gajiye take ta ɗan zumɓura baki, kai tsaye tace "period nake"
Ɗan taɓe baki Imran yayi yace 'ai seki tashi ki shiga da kayan, ko a nan zaki ta zama?"
"Nifa gani nai gidan duk ƙura, a haka zan saka kayana?"
"Zauna in zo in gyara miki" yai maganar cikin gatse.
Knocking ƙofar falon a kayi, Imran yaje ya buɗe wata mata ce me ɗan shekaru ta shigo hannunta ɗauke da flask na Abinci, suka gaisa da Imran cikin broken English Matar tace "Oga wannan kuma sister ɗin ka ce?"
Imran yace "A'a matata ce itaama"
Matar tace "Ka rabu da waccan ne?"
"A'a matana biyu ne ai"
Matar tace "yayi gata kyakykyawa, ga Abinci na kawo muku, dama megidana ne yace ai muku girki zaka zo"
Imran ya karɓa yana murmushi yace "mungode
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 23 Chapter of 31