Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
zan kula su ba." Shahmeer ya yi murmushi gami da cewa "My Love ko me ki ka bani ai na ƙauna ne dan haka hannu bibbiyu zan karɓa" Shahzaib ya ce "Da gaske dai ka koyawa Tsohuwar nan soyayya, subhana gaskiya ni da soyayya sai da in ga anayi." dariya su ka yi, Inna ta ce "E dai mun ji dama ba za tai maka kyau ba gwara ka bar mana sarari, Shahbeer kai ka ƙyale wannan Tuzurun ka gaya min wane abinci ka ke so?" Shahbeer ya ce "Abin da ki ka bawa Masoyin naki nima shi nake so." ta ce "Aff!! ai fa da an canja muku suna." Shahmeer ya ce "Baby ina fatan dai ba tare da Beauty kalar kyau ku ka yi aikin ba dan wannan tsaf idan mutum ya ci abinci zai ƙi zama." da sauri Inna ta ce "A'a o'o rufani ka saya ni Baby dama kiranta na yi ta tawo muku da shi idan na haɗa." jinjina kai ya yi gami da cewa "To ko ke fa.'' ƙasa Ma'arufa ta yi da kai Zuciyarta sam ba daɗi wannan nuna mata ƙasƙancin da su ke yi ba ƙaramin ci mata Zuciya yake ba amma ko menena ma Mahaifinta shi ne ya jaza mata. tunanin nata ne ya tsinke lokacin da ta ji Shahbeer ya na cewa "Inna ki maida Beautyn ɓangaren kicin dan akwai buƙatar ta iya girkin kafin lokacin da za mu fara cin abincinta." kallo-kallon su ka yi su duka ukun, cike da son gane gaskiyar Abin da Shahbeer ya ke nufi, Ma'arufa da Inna kuwa ba'a bambance wadda ta fi shan mamaki dan dukansu kasa magana su ka yi. Sai da Shahmeer ya ce "Babyy!!" Sannan Inna ta iya rufe bakinta ta ce "Uwmm!! My Love." Dariya su ka sa iya su huɗu Inna ma ba ta gane Abin da su ke yiwa dariyar ba bare Ma'arufa sai ta ji duk ta targu. Inna ta taɓe baki ta ce "Allah ya kyauta dai, ke yarinya mu je kawai dan tin da suka fara shakiyancin nan sai ta Allah ba ta mutum ba." Shahmeer ya ce "Haba Baby ban gaji da ganinki ba fa." Harara ta daka masa gami da cewa "Oho maka ni na dena Auren." dariya kawai ya yi ba tare da ya yi magana ba. Inna kuwa jan Ma'arufa ta yi suka nufi kicin. Shahmeer ne ya ce "Gaskiya na yi mamaki da ka yi maganar nan Inya (Shahbeer)." Murmushi me sauti ya yi, bai ce komai ba ya ci gaba da abin da yake yi. Sintiri Alhaji Boza yake a Office ɗinsa wanda aka ƙayata shi da abubuwa na alatu da more rayuwa, duk ya kasa yin aikin komai wasu tunane-tunane na baya ne suke ta taso masa hakan ya sa hankalinsa ya ƙara tashi fiye da da. Safyan ne ya shigo ko sallama babu ya fara cewa "Daddy wallahi Kamfanin shinkafarmu zai zama tarihi idan mu ka zuba ido" "Hankalina ne yake ƙara dugunzuma idan ina tuna wasu abubuwa Safyan, yanzu yadda za'ayi mu rage farashi ya zama dai-dai da na Double Two Star inaga idan mutane su ka ga ta yi sauƙi za su dawo kanta. "Dad ka na ganin hakan ba matsala? yanzu idan mu ka rage kuɗinta ai .... katse shi ya yi da cewa "Safyan ka kasa zama ka fahimci su waye yaran nan, ko dan ba ka sansu ba shine dlili, ta wace hanya ka ke ganin za mu iya ja dasu in ba ta nan ɗin ba?, ka je ka aiwatar da abin da nace kawai shine." Safyan ya ce "Shi kenan amma ko me ya faru kai ne ka janyo mana." Murmushin takaici Alhaji Boza ya yi, bai iya bawa Safyan amsa ba dan kuwa ya lura duk yadda zai yi dan fahimtar da shi ba lallai ya fahimta ba. kujera ya ja ya zauna gami da sauke gwauron numfashi "Ya zama dole na ziyarci Bokana dan kuwa komai nema ya ke ya taɓarɓare min" Alhaji Boza ne ke wannan tunanin bayan ya dafe kansa da yaji ya fara yi masa ciwo, lallai yaran nan sun cika cikakkun hatsabibai. haka ya yi ta tunani kala-kala kuma ya tsayar da ranar da zai ziyarci Bokan nasa. Dariyar Yaro baisan wuta ba sai ya dafa Auta (Shahzain) ya yi kafin ya ce "Boss Jini, wai mutuminka ya sauke shinkafarsa ta dawo dai-dai da tamu." tsaki Ƙarami (Shahzaib) ya yi, ya ce "Amma wallahi ya rasa ma abin yi, to ko mutum makaho ne ai yasan shinkafarmu da tashi akwai bambanci, ya ga yawanta kuɗin ba zai yi ba shine ya dawo dai-dai damu ai kuma kyaunta ba ɗaya bane." Shahmeer ya ce "YaYanmu nasan ba'a haɗa kafaɗa da kai, yaya kenan?" "Ku karya shinkafar ta zama itace mafi ƙarancin kuɗi a cikin kamfanu-nuwan shinkafa, shi karya Abokin kasuwanci da kuma kuɗi kawai ya ke so mu kuma muna da muradin samawa Talaka sauƙi." Dariya su ka yi dan kuwa sun san hakance za ta faru, Shahzaib ya ce "Ayya na tausayawa Boza, baisan faɗa da Aljani ba riba ba kuma ya riga ya kai kansa, Shahmeer do Allah ka bibiyi direban nan namu Motar da muka bawa Lamba Tara naga har yau bai isa inda ake son ya isa ba." Shahzain ya ce "Allah ya sa lafiya na ga wancan karon kamar ya yi abin da ya dace." "Ta yuwu rashin kyaun hanya ne kawai, Auta fito mana da kaya do Allah, ku kuma ku tashi ku yi wanka kafin na gama abin da nake yi. Da "To" suka amsa gami da miƙewa dan aiwatar da abin da ya ce. _________ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ (Ina gaisuwa ga Masoyana) *INDO* [11/30, 7:13 AM] INDO CE: *WATA HANYA* 5 Ayeesha Abdulkareem *(INDO)* MOONASH. Alƙaluma Shida daga Ƙungiyar ELEGANT ONLINE WRITERS. BANI DA HUJJA Maimoon SARƘAƘIYA Shaahd BARRISTER SHAHEEDA Ayush AUREN ƘAUYE Nazlarh ZUMUNCIN ZAMANI Jikar Nashe WATA HANYA Indo Alhaji Boza ne durƙushe a gaban Bokansa wanda babu alamun imani ko abin da ya danganci hakan a tare da shi. cikin murya me cike da mugunta ya ke cewa "Ai kaine ka jawowa kanka wannan bala'in da ya ke tinkararka, ka riga ka zubar da makamin nasararka yanzu komai baya zai yi maka, siyasarka ba za ta yi tasiri ba, kuɗinka ba za su tumbatsa su shahara ba, ba zaka zama shahararre a Duniya ba sabi da ka riga ka bi WATA HANYA wadda ba mu muka ɗoraka akanta ba, hhhhhhhhh." Firfita Alhaji Boza ya ke yi da Hularsa duk da iska na kaɗawa shi zafi ya ke ji har da gumi, ya na da bala'in burin zama cikakke shahararren me kuɗi a Duniya yanzu kuma ace ba wannan ai rayuwarsa ta shiga matsala dan haka ko menene zai yi. numfashi ya ja ya sauke gami da cewa "Amma Boka ina da wannan burin na taso dashi tin da ƙuruciyata, amma yanzu ace ba zai cika ba kenan duk wahalar da na sha a baya ta zama ta banza, ka nema min mafita Boka ban san yadda zan yi ba idan burika na ba su cika ba, ka tuna fa na sha wahala ba kaɗan ba kafin mu zo wannan maganar da ake yi yanzu." "Hhhhhhhhhhh, Akwai mafita,,, akwai mafita,, amma muddin Yaran-nan ba sa tare da kai ba za ka iya yin komai ba, mafitar itace ka shiga jikinsu ku dinga mu'amala mu kuma za mu yi namu ƙoƙarin daga nan za ka tumbatsa ka shahara,hhhhhh. Boka da kamar wuya su dawo garen....." cikin tsawa ya katse shi da cewa "Shine kuskuren da ka aikata a baya, kar ka bari ka ƙara mai-maita shiiiii. da sauri Alhaji Boza ya ce "Na fahimta Boka zan yi duk yadda ka ce, zan yi bakin ƙoƙarina dan na dawo dasu gareni." dariya Boka ya kece da ita ya na cewa "An sallameka,,, an sallameka,,,, an sallameka,,,,," jin haka ya sa Alhaji Boza miƙewa ya fito daga surƙuƙin duhuwar dajin, tafiya ce me tsayi sosai tsakanin tsibirin Boka da iya inda mota za ta iya kurɗawa a dajin. Zaune ta ke kanta a ƙasa ta na sauraren irin sangarta da lalacin da Maalik ya ke yi wa Dada ita kuma ta na biye masa, mugun haushi abin ya ke bawa Shukriya kamar ta haɗiyi Zuciya ta mutu gashi tsaurin ra'ayin Dadan ya sa ta hanata tashi ta basu guri wai itama ai ƴarta ce. Tunaninta ne ya katse jin Dada ta na cewa "Maalik na gaji da ganinku daban-daban kai da Shukriya dan haka yanzu maganar aurenku za'a fara." wani malalacin Murmushi ya saki ya na kallon Shukriya wadda mamaki da tsoron maganar Dadan ya sa ta ɗagowa ta zuba musu idanu, suna haɗa ido ta yi saurin kawar da kai Zuciyarta na wani mugun tsalle, Addu'ar neman tsari da kariya ta shiga jerowa a cikin ranta. "Ta na da kunya sosai Mom kin ga ma ta kasa haɗa ido da ni, ni kuwa namiji ne dole in zage in nuna farin cikina, Mom wallahi ko yanzu ki ce a ɗaura a shirye na ke. "Idan kai ka shirya to ita ƴata ba ta shirya ba ko Shukriya?" gyaɗa kai kawai ta iya yi dan kuwa ba za ta iya magana ba. "To ka ji ta ce ba ta shirya ba dan haka ka bamu lokaci, ka kasance cikin shiri kawai ai Shukriya mallakinka ce koma daren-daɗewa. "Uhm, Na gode da kyautarki Mom... ƙarar wayar Shukriya ne ya sa Dada ta fasa maganar. da sauri Shukriya ta ɗauka gami da tashi tabar wajen sannan ta amsa kiran. Sallama Fatima ta yi, Shukriya ta amsa tare da sauke ajiyar Zuciya, Fatima ta ce "A'a? lafiya kuwa na ji kina wannan ajiyar Zuciya haka Shukriya Gigi?" "Lafiya ai ta fi komai daɗi Fatima ina kuwa lafiya?" "Me ya faru kar dai ki ce min Maalik ɗin ne?" "To waye zai hana ni farin ciki in ba shi ba?, yanzunnan kiran da ki ka yi wai zancen aurenmu su ke yi ni kuma Allah ya gani kuma ya shaida bana son shi kuma ba na ƙaunarshi ba zan taɓa son shi ba har abada. "To fa wallahi abin ya na ban tsoro Shukriya, amma komai ya yi zafi maganinsa Allah kar ki damu akan hakan dan Allah, nasan idan ba alkairi bane a gareki Allah zai hana faruwar auren, ki ci gaba da addu'a kawai ƙawata. "Zan ƙoƙarta na gode matuƙa Fatima. Fatima ta ce "Ai da Maalik ba sonki ya ke ba da ba mu san abin da zai faru ba, inda Allah ya rufa mana asiri ya na sonki." Shukriya ta ce "Wallahi kuwa." ci gaba su ka yi da hira har Fatima ta fara mantar da Shukriya damuwar da ta ke neman hanata sukuni, jinta a ƙirjin mutum ya rungumeta ya sa ta waro ido gami da sakin ƴar ƙarar da ba zato ba tsammani. Haka Alhaji Boza ya dawo gida cikin matuƙar damuwa da tunanuka iri-iri ya rasa ta inda zai fara shawo kan matsalar. Sa'ad ne ya ke ta shirya sallama a falon Alhaji Boza jin ba shi da niyar amsawa ya sa ya kutsa kai, zaune ya sameshi dafe da kai ya yi nisa ƙololuwa a cikin Duniyar tunani da damuwa. Sa'ad ya ce "Daddy ba ka da wata damuwar da za ta sa ka wannan damuwa idan ba kuɗi ba, wai dan Allah me yasa mu mutane ba ma nemawa kanmu salama a wajen Allah?, ka na da kuɗi ka na da dukiyoyi ka tara an tara maka to me ka ke so bayan haka?" "Sa'ad kai kamar ba jinina ba, kasan ma'anar kuɗi kuwa? ba ma wannan ba yanzu suna nake buƙata ba kuɗin kawai ba, ina so na yi suna a ko'ina na faɗin Duniya ya zamana Alhaji Boza ake faɗe kawai. "Da na kasance ba jinin naka ba inaga da na fi farin ciki, yanzun ma nan gaba nima idan ka yi niya za ka iya maida ni ba jininka ba cikin sauƙi, Allah ya kyauta, ba zan yi fatan ka samu abin da ka ke so ba Daddy dan Allah ne yasan abin da za ka shuka idan dama ta zo hannunka" Sa'ad ya faɗa cike da takaici. banza Alhaji Boza ya yi masa ganin haka ya sa shi tashi ya bashi guri. "Haba ni ne fa Sweetheart me yasa ki ke da saurin tsorata ne?'" tsaki ta ja ta ce "Sakeni Maalik, ba na son irin wannan banzar ɗabi'ar taka ni ba haka iyayena su ka koyar da ni ba ka gane?" "Sai kin ganar da ni zan gane, ki dena yawan yi min tsaki dan hakan fusata Zuciyata ya ke ina sauƙaƙa ne kawai idan na tuna ke tawa ce. "Ba na so na ji kana maganar banzar nan ko dan ka ji Dada ta na wani zancen aurenmu? ni fa a gaskiya Maalik ba zan taɓa sonka ba ka je ka nemi wadda za ta so ka a gurina wahala za ka sha. da hannunsa da ke kan ƙugunta ya juyota suna fuskantar juna cike da rashin damuwa akan abin da ta faɗa ya ce "Ban damu da sai kin so ni ba dan hakan ba zai hanani na so ki ba kuma ba zai hana ni samun abin da na ke so ba." ya ƙarasa maganar tare da kai fuskarsa daf da ta-ta ya na ƙara kasheta da miyagun idanunsa, bakinta ya kasa furta komai dan ƙiris ya ke jira ta yi magana ya rufe bakin ga shegen kallon nasa mugun kashe mata jiki ya ke. "Me ya sa ba za ki soni ba?" Ya jefo mata tambayar cikin murya me rikitarwa, rasa yadda za ta yi masa tai dan haka ta fashe da kuka ta tattaro iya ƙarfinta ta shiga tureshi, ba dan ya so ba ya saketa rai a ɓace yabar wajen kamar me shirin yin dambe da iska. da gudu Shukriya ta wuce ɗakin da aka sauketa, ta na shiga ta kulle ƙofa dan gudun kar ya biyota. haka rayuwa ta ci gaba da tafiya a kowane ɓangare. Bayan watanni biyu. Zaune suke a Falo tare da Inna hira su ke cikin nishaɗi ba tare da wata damuwa ba, Inna ce ta ce "Ai yanzu Alhamdulillah Ma'arufa ta iya wasu girke-girken." cikin haɗe rai Shahmeer ya ce "Inna Sabi da Allah mu na hirarmu me daɗi sai ki sako mana zancen Wannan yarinyar?" ta yi sauri gyara zama gami da cewa "Uff ɗan bakina, to ai My Love ka san bakin ne sai addu'a, kuma gani na yi tin da yayanku ne ya sa ni koya mata girkin ya kamata na faɗa masa halin da ake ciki." Shahmeer zai yi magana Shahbeer ya katse shi da cewa "Inna to yau ki sa ta ta yi mana girkin." cikin sauri Zaib ya ɗago brown eyes ɗinsa ya zubawa Beer cikin tsananin mamaki ya ce "Inya...." dakatar dashi Shahbeer ya yi ta hanyar ɗaga masa hannu ya ce "Ba na son jayayya ka sani." ƙasa Zaib ya yi da ido Zuciyarsa cike da tunane-tunane. Inna ta ce "Ai kuwa za ta baku mamaki Oga." ya ɗan ɗage kafaɗarsa alamar ko a jikinsa. miƙewa Inna ta yi ta nufi ɓangaren ƴan-aiki. Atika da Ma'arufa su na zaune Atika na ta ƙoƙarin janta da surutu sai dai ta ƙi sakin jikinta dan in ba jinta ta yi a ɗan kurkukun gidansu ba gaba ɗaya jinta ta ke a ƙasƙance hakan ya sa ba ta son ta saki jiki har ta wuce gona da iri, jin Sallamar Inna a wajen ya sa suka miƙe tare da amsawa suka ja suka tsaya dan jin abin da Inna ta zo musu da shi, "Ma'arufa Shahbeer ya ce ki je ki yi musu girki. dummm Zuciyarta ta buga hakan ya sa jikinta ya ɗau karkarwa, a matuƙar tsorace ta ce "Ba zan iya ba wallahi, Inna ni ban kai matsayin da zan yi wa mutane irinsu girki ba dan Allah..." da sauri Inna ta dakatar da ita da cewa "Ko Mahaifiyarsu sabi da ƙaunar da take musu ba ta jayayya da abin da Shahbeer ya faɗa." Atika ta ce "Innalillahi, ke yanzu Ma'arufa wannan damar da kowa ke nemanta ta zo miki amma sai ki banzatar?? wallahi ke ƴar'baiwa ce dan haka ki karɓa hannunki bibbiyu ba ma iya talakawa ba har ƴa-ƴan masu kuɗin ma neman wannan damar su ke ba su samu ba." Inna ta ce "Ko ma ba wannan ya zama dole ta yi dan ni cika umarni shine nawa, ina jiranki." daga haka Inna ta yi tafiyarta. "Subhanallahi" Ma'arufa ta faɗa tare da zubowar hawayenta. "Ke wallahi ban haushi gareki Ƙawata, na gaya miki Allah ne ya zaɓeki daga cikinmu dan ya share miki kukanki, ai ni tin da ki ka ce su na wulaƙanta ki na ji inama nice ke, wallahi mu ko kallo ba mu ishe su ba ke kuwa daga kawoki gidan har sun san da zamanki yanzu kuma har za ki fara yi musu girki wallahi ki godewa Allah kar ki butulce masa." ban da sharar ƙwalla ba abin da Ma'arufa ta ke yi, cikin sanyin jiki ta nufi kicin ɗin, Inna ta ce aikina kawai nuna miki wasu abubuwan dan kuwa yau ba zan sa miki hannu ba. Zain ne ya ce "Inya! (Shahbeer) Ya kamata wani ya je Lagos ya duba yanayin tafiyar kasuwan-cinmu." "Abeer zai je zuwa gobe in sha Allah, tin da Ummi ba ta nan ba zan so mu yi nesa da gida ba mu kasance tare, ina so aje Jigawa ma ko dai kai zan tura?" da sauri Zain ya ce "A'a Boss kasan fa ni ɗafa gareni har yanzu ban girma ba." Zaib ya ce "Ɗafar taka ta ci uwata shakiyin banza." dariya su ka yi banda Shahbeer da ya ke wasa da Ricky karensa sai dai yalwataccen murmushin da ke shimfiɗe akan fuskarsa zai tabbatar da ya na cikin yanayi mai daɗi. Kamar daga sama su ka ji sallamar Mommy, cikin sauri su ka tashi tsaye su na kallon hanyar shigowa cike da mamaki. fuskarta ɗauke da murmushi ta shigo ta na cewa "Gani na dawo, waye yake nemana waye ba ya nemana?" Shahmeer ya ce "Mommy wai dan Allah ke ce??, kar fa mu je gamo muka yi." ta ce "ni ce mana Ba dai kun koreni ba? to na gaji da zama ni so nake na dawo kusa da ku." Zain ya ce "Amma Ummi ba ke kaɗai ki ka dawo ba kin samu matemaki." ƙarasowa ta yi gami da cewa "Ba ku kalli bayana ba ashe." ta haɗe cikin wasu shegun riga da skirt na atamfa, Simple make-up ta yi wanda ya karɓi fuskarta sosai sai baƙin glass da ta saka, ta harɗe ƙafa ta coge ta na taunar cingam cikin salo da ƙwarewa. kallo ɗaya Shahbeer ya yi mata ya ɗauke kai, cike da hargagi Zaib ya ce "Mommy wannan iblishiyar yarinyar ce ta dawo dake ko?, sai na targaɗa ta mara mutunci." Murguɗa baki ta yi ta shiga takawa cike da kwarkwasa, "Ai ba mara mutunci a duk Duniya sama da kai, kaine lamba ɗaya" ta yi maganar cikin salon tsiwa. _________ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ *INDO* [12/1, 12:06 PM] INDO CE: *WATA HANYA* 6 Ayeesha Abdulkareem *(Indo ce..)* MOONASH Alƙaluma Shida. Daga Ƙungiyar ELEGANT ONLINE WRITERS. BANI DA HUJJA Maimoon SARƘAƘIYA Shaahd BARRISTER SHAHEEDA Ayush AUREN ƘAUYE Nazlarh ZUMUNCIN ZAMANI Jikar Nashe WATA HANYA Indo A harzuƙe ya ce "Ni za ki gayawa haka dan kin raina mutane ko?" Mommy ce ta shiga zancen da cewa "Faɗa ya yi daɗi har kun manta da ni , ko ruwan sha ba wanda ya ce min gashi ko dai in koma ne?" ta yi maganar dai-dai da zamanta a kusa da Shahbeer wanda idanunsa suke a ƙasa kamar wanda aka ce ya na ɗagowa zai yi karo da wani mugun gani. Shahmeer ne ya dawo kusa da Mommyn ya zauna, "Mama mamakin ganinki ba zato ne ya sa duk muka manta da komai, na yi farin cikin ganinki matuƙa" ya ƙarasa maganar cikin sigar shagwaɓa. murmushi ta yi ta ce "Hayaniya Tsakaninsu Malika ta ƙi ƙarewa." Shahbeer ne ya ƙara haɗe rai a tsawace ya ce "Malika ba za ki iya yi masa banza bane? ko baku da aikin yi sai cacar baki??" girgiza kai ta yi alamar "a'a" ɗan tsaki ya yi sannan ya maida kallonsa ga Mommy Cikin fara'a ya ce "Mommy mun yi kewarki sosai, bari su kawo miki abin sha." "Ba na so na yi fushi" ta faɗa gami da haɗe fuska. dariya Shahzaib ya yi ya na cewa "Mommy!! Allah ya bar min ke ni kaɗai abina." sai a lokacin Shahzain ya ce "Mommy kin manta da Autanki ko?" "Sai yanzu na tuna da Autan nawa, taso ka zo nan kusa dani ka zauna kabar masu faɗa a tsaye. Shahmeer ya ce "Mommy komai ya wuce fa, dama yanzu na gama cewa yau girkinki nake son ci." dariya ta yi gami da cewa "Ai kuwa tin da na dawo duk wannan me sauƙi ce, ina Inna?" Shahzaib ya ce "Mommy can da yawarsa, don Allah kar ki ce za ki yi wani girki yanzu shi ma da wasa ya ke yi, Inya (Shahbeer) ya ce yau girkin ƴar-aikinki ɗinnan za mu ci." murmusawa ta yi gami da cewa "Hakan ya yi min daɗi sosai, to ku bani labarin abin da ya faru anan bayan tafiyata." da sauri Malika ta ce "Mommy gaskiyar ba za ki ganeta anan ba ai Allah ne kawai yasan wainar da suka toya ." Shahzaib ya ce "Ke ta shafa mara kunya kawai." Inna ce

Chapter 3 of 30