bawa Shahzain ke gaskiya ba'a yi mini Adalci ba kuma duk laifinki ne, me yasa bakya tausayina Shukriya?"
ya ƙarasa maganar kamar zai fashe da kuka.
"Ai kai ma ba ka tausaya mini ba, Kuma son Zuciyarku kai da Mamanka shi ne ya sa hakan, ni kuma ba zan Amince ku yi mini yadda ku ka yiwa Aunty Hadiza ba.
"Iya abin da tunaninki ya gaya miki shine wannan, amma ni nawa tunanin ba haka ya ke ba, Ba ki San So ba Shukriya, Kuma ki ce ni na gaya miki, shi ma ba son shi ki ke ba, ki je ki yi tunani za ki gane gaskiya na faɗa miki, Kuma ba zan dena Sonki ba ko da Hakan zai Zamto Ajalina na shirya mutuwa ko a yanzu ne indai ta sanadinki ne, Ba son Zuciya ba ƙarya ba Yaudara tabbas da ba Son gaskiya na ke miki ba da yanzu ba wannan labarin ake yi ba, Wallahi Tallahi Ina miki So Kyakkyawan So me tsafta, duk da na san ba za ki yarda ba amma nan gaba za ki Fahimta, ki koma gida Sannan ki samu Nutsuwa Ina fatan Ki yi kyakkyawan Bacci wanda ba ruɗani a cikinsa.
Ba ta ce komai ba sai tsaki ta Buɗe Motar ta fice cikin sauri ta koma gida.
01:03AM
Mommy, Akwatin ta da ta shaƙare da kayanta taf ta ke ja Babu alamar walwala a tare da ita, Kai tsaye hanyar fita ta nufa ta na shirin buɗe ƙofar ta fice.
Fitowar Inna kenan daga kicin Shahzad ya na ciwon ciki ta zo neman gishiri za ta bashi ta na fitowa ta hangi Mommy na shirin buɗe ƙofa, da sauri ta nufi gurin ta na tambayarta Lafiya, ganinta har da Akwati ya sa Hankalin Inna ya ƙara tashi, cikin ɗaga murya tace "Me ki ke shirin Aikatawa haka?? ina za ki je A'i????"
"Ba ruwanki da Inda zanje, Kar wanda ya ƙara yi mini magana kar wanda ya nemeni na dai gaya muku."
"Lahaula'walaƙuwata, A'i anya Lafiyarki Ƙalau?? fita za ki yi da daddaren nan to me mu ka yi miki da za ki fita kuma ki ce kar mu nemeki???"
"Ba na son ƙara ganinku, ku fita daga rayuwata.
ta faɗa lokacin da ta yi nasarar Buɗe Ƙofar.
Inna ta fara salati da Addu'o'i Ta haɗe dukan ƙarfinta ta riƙeta ta na cewa "Ki tuna fa ba ki da kowa sai Allah sai Ƴaƴanki, yanzu ya za su yi idan su ka wayi gari babu ke?? ki temaka mana.
watsar da ita ta yi can gefe ba tare da ta waiga ta ga halin da Innan ta ke ciki ba ta yi ficewarta.
_________
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
*INDO*
[12/28/2022, 1:00 PM] INDO CE: *WATA HANYA*
27
Ayeesha Abdulkareem
*(Indo ce..)*
ELEGANT ONLINE WRITERS.
Cikin sauri Inna ta miƙe jiki na rawa ta nufi sashin su Shahbeer, tin a bakin ƙofar Ta ke ƙwala musu kira da iya Ƙarfinta, Ya na zaune kan Sallaya ya na Lazumi bayan ya idar da Sallar Nafila, kamar a mafarki ya ji Inna ta na ƙwala masa kira ya yi saurin tashi ya fito su ka yi arangama. "Ga Aisha can ta fita da Akwati a daren nan na tambayeta inda za ta je ta ce ba ruwana, wallahi ba ƙalau ta ke ba ka bita kar mu shiga uku.
bai jira ta ƙarasa maganar ba ya fara gudu-gudu ta mara masa baya ta na ci gaba da bashi labarin yadda akai.
har ta je wajen Babban Get ɗin gidan kasancewar akwai tsaro a Ƙyauren sosai ba ta samu damar fita ba ya cimmata, hannunta ya riƙe gam ya na tambayarta inda za ta je, ta na huci ta ce "Gidan Mijina zan tafi, ba zan ƙara nemanku ba ku ma kar ku neme ni, ba na sonku Ni Mijina na ke so.
Idanu ya wararo akanta lokaci guda Maganar ta-ta ta sa shi suman tsaye, ko ba'a faɗa ba ya san Mommynsa ba lafiya ta ke ba duk da ya san irin shirkar Alhaji Boza ta na bibiyarta amma bai yi tunanin dare tsaka za ta faɗi hakan ko ta aikata ba. Ji ya yi ta na ƙoƙarin ƙwacewa daga riƙon ya yi saurin dawowa hayyacinsa, "Meke Faruwa haka da daren Allah Mom?? wani laifin mu ka yi miki??"
"A'a ni dai zamana da ku ya ƙare na gaji da zama tare da ku gidan Mijina zan koma kar ku neme ni.
jinjina kai ya yi yanzu ya gane karatun, Haka kawai Zuciyarsa ta raya masa wata Baƙar Wutar Alhaji Boza ya kunno musu.
ɗan murmusawa ya yi kafin ya ce ''Haba Umma, Mu ma fa Mahaifinmu ne gidansa gidanmu ne to dan ki na can me ya sa ba za mu nemeki ba?"
"Ai ba kwa Son shi ni kaɗai na ke son shi, ni dai ka ƙyaleni"
" Sanyi Mana Mamma! kin sani dai Mu na buƙatarki a raye ko da bakya tare da mu, Dare ya yi yanzu ki bari gobe zan kai ki da kaina sannan zan bashi haƙuri kuma in sanar da shi yanzu mu na Son shi, ki yi haƙuri mu koma cikin gida In Allah ya Yarda zan kai ki.
"A'a ba zan koma ba na san ba za ka kaini ba.
"Kar ki yi wannan tunanin Mommy Ai na ce Allah kin ga na gama magana, in sha Allah zan kai ki, amma fa idan ba ki koma ba gaskiya akwai matsala raina zai yi ƙuna.
"To zan koma amma da sassafe za ka kai ni.
"Na yarda"
ya faɗa tare da jan hannunta.
a Falo ta maƙale a cewarta ba za ta ƙara shiga ɗaki ba.
Inna kuwa tini ta bi ta tattashi kowa dukansu sun Hallara akan Mommy amma juyin Duniya ta ce sai dai in gawarta za a kai ciki dole su ka barta a wajen.
Maƙurar Ɓacin rai ya gama kaiwa gaba ɗaya ya kasa zama sai shawagi ya ke a gurin, idanunsa sun canja kamanni sabi da Tsabar Ƙunar rai. Ganin bacci ya fara ɗibar Mommy ya sa shi ciro wayarsa ya tura kira bayan an ɗauka ya ce "Alhaji Basiru Boza ku killace mini shi, idan ya yi gardama ku Harbeshi a ƙafa Idan abin ya ci tira ku Ɓatar mini da shi ba na buƙatar ƙara ganinsa.
zumbur Ma'arufa ta miƙe gami da cewa "Mee??? Ya Shahbeer anya Lafiyarka ƙalau kuwa?? Mahaifinka ne fa amma ka ke cewa haka??"
Rikitattun Idanunsa ya zuba mata Gami da cewa "Dama ai ba ni da Lafiya, mahaukaci ne ni, haka dai ki ke so ki faɗa ko???"
A fusace Shahzaib ya ce "Ai ka yi da ƙauna ma ni da cewa ka yi su tarwatsa masa kai kawai, ke kuma ki rufe bakinki idan ba za ki iya ji ba ki bar wajen dama ai ba Sabgarki bace."
Ma'arufa ta ce "Kai ma hakan ka ce?? ashe a cikinku babu wani cikakken Mutum me Nutsuwa ? akan me za ku dinga faɗen munanan kalamai akan Mahaifinku haka? ko da Mahaukaci ne me yawon Bola ko kuma shi ne mafi girman Kuskure a Duniya bai cancanci haka ba domin ya haifeku dole Mahaifinku ne.
fassss!!! Shahzaib ya wanketa da wani mugun mari, ya na huci ya ce "Mun sako ki a cikin zancenmu ne?? ko tambayarki mu ka yi? akan me za ki faɗa mana wasu banzayen maganganu akan abin da ya shafemu?, Wallahil Azim ƙaramin aikina ne in karairaya ki A gurin nan." Shahmeer ya ce
"Ƙetare ki bar wajen Beauty, ki dinga kulawa idan ki ka ji Anyi abu makamancin haka to da walakin ki dinga tambayar ba'asi kin ji?, Rayuwar Mahaifinmu ba Rayuwa bace domin wanzuwarsa a Duniya Barazana ce ga mutanen cikinta rashinsa zai fi Alkairi akan kasan-cewarsa a raye.
Shahzaib ya ce "Barta, ta ƙara yin magana anan sai na ɓare mata baki wallahi.
Sim-Sim ta bar wajen ta koma Ɗakinta cike da tunanika iri-iri, Menene Dalilinsu na ƙiyayya me tsanani a tsakaninsu da Mahaifinsu?? mene ya sa su ke cewa gwara rashinsa a Duniya? wane Zunubi ya aikata da har su ke tunanin hakan? waye shi? me ya yi musu? me yasa ba sa son shi?, da wannan tunanin ta kwanta ta yi lif har bacci ya kwasheta.
A Falo kuwa tin da ta ji hayaniyarsu ta farka daga baccin ta ƙara tuburewa sai da su ka yi da gaske su ka lallaɓata.
Washegari tin sassafe ta ce ta shirya ko a kaita yanzu ko ta tafi da kanta. Akwatin nata Shahbeer ya karɓa ya yi gaba ya na cewa "Inna ki rakata mana."
"To Yaro bari in zo.
da sauri ta ɗakko gyalenta ta fito su ka ɗau Hanyar gidan Alhaji Boza.
a haraba su ka tarar da Mommy da Safyan da mai gadin gidan sai jimami su ke yi, ganin su Mommy ya sa hankalinsu ya ƙara tashi, a fusace Mom ta ce "Menene ya kawo ku gidanmu??, kuna so ku ƙarasa tarwatsa mu ne?, kun cuce mu kun illata rayuwarmu ko meye ya faru da mu ta dalilinku ne kun talauta mu kun hanamu farin ciki da zaman lafiya."
a dake Shahbeer ya ce "Ah Malama ba wai surutanki mu ka zo saurara ba, Ina Alhaji Boza ya ke??"
Fashewa ta yi da kuka ta na cewa "Ban sani ba tin da ba ajiyarsa ka bani ba, mugun yaro me baƙar aniya Allah ya isa tsakanina da kai, ban san inda ya ke ba, banda rashin kunya ma har za ka iya kiransa da Mahaifinka? Munafukin banza."
Shahbeer ya ce "Wannan Matar ta kwarkwance, kai Safyan gaya mini inda Babanmu ya ke ko in karya ka, ba na son ɓoye-ɓoye."
Safyan ya na kumbura ya na batsewa ya ce "Ba mu san inda akai da shi ba, wasu ƴan ta'adda ne su ka zo har gidannan su ka tafi
dashi ƙila ma sun kashe shi don na ji ƙarar harbi, kuma da mu ka tambayesu inda za su kai shi sai su ka rufeni da duka wai zan yi musu fitsara."
Ya kai maganar ya na matsar ƙwallah.
shafa kai Shahbeer ya yi ya saki murmushi kafin ya maida fuskarsa kalar tausayi ya ce "Mama kin ji abin da ya faru da Alhaju Boza, Ko su waye kuwa sai na yi maganinsu, ki zo mu koma gida, kinga in kin zauna anan waɗannan ba za su kula da ke ba tin da ba sa sonki Azzalumai ne, Gashi an yi Kidnapp ɗin Alhaji Boza, wayyo Abin ba daɗi"
yadda ya ƙarasa maganar kamar zai yi kuka ya sa jikinta ya yi sanyi, Inna ta jinjina kai gami da girmama Shu'umanci irin na Shahbeer shi yasa dai kowa ya ƙi yarda Shahzad ba ɗansa bane domin kuwa Tamkar Wahainiya haka ya ke rikiɗa.
Hannun Mommy ya kama cikin sigar rarrashi ya ce "Kar ki damu Allah zai baiyana shi."
Ta na hawaye ta ce "Za ka dawo mini da shi?"
"Ƙwarai kuwa me zai hana, indai da ransa zai dawo mana, yanzu dai mu tafi Mommy Don Allah.
cikin sanyin jiki ta bi shi su ka nufi gurin mota, ya na jin Mom Safyan ta na ta tsine-tsine da ɗiban Albarka ya yi mata banza don ba lokacinta ne da shi ba.
Mommy ta ci kuka sosai kafin su koma gida, cikin sa'a kuma ana komawa ta yi shiru ta manta da komai.
Bayan Dr Idris ya gama sauraren abin da Shahbeer ke cewa ya ɗora da cewa "Gaskiya Allah shi ne me tsare bayinsa, Ba shakka da ta fita a wannan Daren ba'a sani ba da an samu matsala babba, to Alhamdulillahi tinda an samu hankali ya kwanta sai mu farka daga baccin da mu ke yi, mu zage da Addu'a Sadaka dai nasan ƴar kullum ce ta zame muku jiki domin itama ta na da kyau, Sannan mu Rarraba Sauka ta Alƙur'ani Me Girma, ai ta taya mu da Addu'a har Allah ya sa ta dawo haiyacinta, ba abin da zai haifar da haka sai aikin Shirka, Allah ya yi mana tsari da Shirka da masu yinta kuma ya ƙara tsarkake Zukatanmu.
"Amin" Shahbeer ya amsa, da haka su ka yi sallama sannan ya ajiye wayar.
Daidai Lokacin Inna ta shigo ta na cewa "Masoyina ina Ɗan-uwanka wannan uban Zuciyar?"
Shahmeer ya ce ''Ya na jinki Baby."
"Au ka na ji na ka yi shiru?"
Ba tare da ya kalleta ba ya ce "Menene Inna?"
"Matarka dai Fushi ta ke da mu ta ƙi kula kowa ta yi ƙuƙi a ɗaki ita kaɗai ko fitowa ba ta yi ba tinda garin Allah i waye, in gaya maka ko Karin Kumallo ba ta yi ba.
Shahzaib ya ce "To me akai mata?"
Tsaki Shahbeer ya yi kafin ya ce "Kai ka ma manta Marin da ka yi mata jiya kenan, to Ni dai ba ruwana wannan abin da ya dameku ne kai da ita.
ya na kaiwa nan ya wuce Bedroom.
Shahzaib ya ce "Inna tsaya ni to.
"Ai sai ka yi sauri don ni komawa zanyi Gurin Shahhzad shi kaɗai na bari, kar Halimeme ta doke shi.
duk surutun da ta ke yi tini ya wuce ta ba tare da ta lura ba.
"Ma'arufa Ki yi haƙuri Don Allah.
girgiza kai ta yi ta ce "Ba komai, ina cikin damuwa ne sabi da furucin bakinku, na tsorata sosai kenan kowa ma haka ku ke yi masa?"
"Ohh, Wallahi ɓacin rai ne ya sa mu ka ce haka, amma ba abin da zai faru kuma bai taɓa faruwa ba, Ba mu fara akan wani ba wannan ne karon farko kuma shi ne na ƙarshe, Don Allah ki yi haƙuri Ba za mu kuma ba.
"Gaskiya Ku dinga rage Zafin rai, ba lallai idan laifinsa bane amma ku ke ƙoƙarin hukunta shi, ya riga ya yi Nadama ya gane kuskurensa me yasa ku ke tunanin zai sake cutar da ku? ni dai ban yarda ya na da laifi ba kuma ku yi tunani tukunna,, sannan ko me ya yi ai Mahaifinku ne.
"Komai ya wuce, Lafiyar Ummanmu itace abar damuwarmu da zarar ta samu Lafiya za mu manta da shi, kuma ya na lafiya ba abin da ya same shi, Amma don Allah ki yi haƙuri jiya sabi da saurin hannuna har marinki na yi fa.
shiru ne ya biyo baya kafin Ma'arufa ta ce " Ni fa har na ma manta, amma Zan so jin Abin da ya yi muku me tsauri haka har ku ke tunani irin wannan akansa.
miƙewa ya yi tare da cewa "Bari in kawo miki Abin karin kumallo, ki ajiye wannan tambayar sai nan gaba za ki samu amsarta."
da ido ta raka shi har ya ɓacewa ganinta sannan ta numfasa.
Bayan wani lokaci.
Tin daga ranar Mommy ba ta ƙara Kwatanta irin haka ba, Ko zancen Alhaji Boza ba ta ƙara yi ba, abin da ta sa gaba shine Batun Auren Shahbeer da Malika.
shi kuwa abin da ya fi komai ƙuntata masa kenan, Tin da Mommyn ta yanke hukuncin Wata Biyu ya rage a Ɗaura Auren su ka dosa Damuwa daga shi har Shahmeer ko da yaushe babu farin ciki ba Annushuwa, har gwara Shahbeer idan ya na wasa da Shahzad yakan ji Damuwarsa ta ragu.
Alhaji Boza ya na cikin Mugun Mawuyacin hali sabi da barazanar da ya ke fuskanta a gurin Boka, da ya jarraba taso Bala'i daga kan Mommy ya ga bai yi Nasara ba sai ya koma kan Sa'ad, Tin daga US aka dawo dashi gida sabi da wani mugun zazzaɓi me zafi da ya ke yi kuma anyi maganin anyi maganin abin ya ci tira dole ya dawo gida anan ɗin ma Alhaji Boza ya yi duk yadda zai yi amma ba sauƙi sai na Allah, Mom Safyan da Safyan kuwa dama ba ƙaunar Sa'ad ɗin su ke yi ba shi yasa ba su damu ba ƙoƙarinsu ɗaya su tattala Dukiyar Alhaji Boza, DR Idris ne kawai ya ke temaka masa ta ɓangaren Samawa Sa'ad Sauƙin wani abin.
a ɓangaren Shahzain da Shukriya ba abin da ya canja sai ƙarin So da Ƙauna sai kuma matsalolin da su ke fuskanta a gurin Dangin Mahaifinta daga shi har ita ba wanda su ka ragawa kuma duk sun janye hannunsu sun ce babu su a ciki tin da aka bujirewa Dada. sai kuma ƴar tsama tsakanin Maalik da Shahzain kamar Ƴan-tsaki haka su ke faɗa duk ranar da Allah ya haɗa su, kuma kowa in ransa ya ɓaci akan Shukriya ya ke hucewa ba sa ganin laifin junansu sai nata, Ba ta da Makamin kare kanta sai dai ta yi kuka ta manta don kuwa ba ta da riƙo da abu ya wuce shi kenan.
_________
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
*INDO*
[12/29/2022, 11:01 AM] INDO CE: *WATA HANYA*
28
Ayeesha Abdulkareem
*(Indo ce..)*
ELEGANT ONLINE WRITERS.
Shirye-Shiryen Bikin Shahbeer da Malika ya gama kankama amma a iya ɓangare Ɗaya, Mommy Da Dangin Malika sai kuma ƙawayen Mommyn, su Shahbeer kuwa duk ba su damu da abin da ake yi ko za'ayi ba, Musamman shi ko sauraren abin da ya shafi Malikan ba ya yi ganin abin ya ke ma kamar ba me yuwuwa ba.
Mommy ta zage ta gyara wani sashi na cikin gidan inda anan ta yiwa Malika Masauki, ta shirya komai tare da temakon Aminanta da Su Shahzain amma ban da Shahbeer idan ya ji maganar ma ta yi yawa sai ya ɗauki Shahzad su bar gidan.
Da ya ke ba wani Taro ta haɗa ba don ba ta da kowa Sai Allah sai Aminai, salin-alin aka ɗaura Aure Amarya ta tare a ɗakinta. A gidansu dai sun yi Bikinsu Sosai sun yi Farin ciki, duk wani shagali da su ka yi Babu Ango haka nan aka yi shi aka miƙa Amarya ɗakinta.
Ranar Shahbeer bai kwana a gidan ba sabi da tsabar takaici, Sam ba ya son ya dinga Haɗa Ido da Ɗan-uwansa Shahmeer sabi da zallar Damuwa da Ciwo da ya ke gani a tattare da shi gashi ba shi da yadda zai yi ya magance masa ita.
Malika kuwa Kwanan Fargaba ta yi domin ta na bala'in Tsoron Shu'umancin Shahbeer. ta san Damuwa da baƙin ciki su ta sayawa kanta sai dai ba'a Son ranta ba Don ba ta san Lokacin da Son shi ya mamayeta ba.
Shahmeer ne ya kalli Shahzaib da Shahzain cike da damuwa ya ce "Inya ya kasa Manta komai, Ina matuƙar jin ba daɗi idan na ganshi cikin damuwan nan."
Shahzain ya ce "Idan ba ka so ya damu kai ma ka dena damuwa, indai kuwa zai ga Damuwarka to fa ba zai Dena Damuwa ba.
Shahzaib ya ce "Kuma haka ne, sai dai saƙon Zuciya shi fuska ta ke isarwa, ka na jin ba daɗi ne shi yasa fuskarka ta ke nunawa, kuma ka san dai Gane Halin da ka ke ciki abu ne me sauƙi a gurinsa."
Murmushi ya yi cikin ƙarfin Hali ya ce "Ni kam In banda abin sa ai ba abin damuwa bane, na ɗan lokaci kaɗan ne nima zan manta da ita.
"Shayin Goriba Na ke So"
Muryarsa ce ta katse musu hirar. Shahmeer ya yi dariya gami da cewa "Yaushe ka dawo ne wai ina ma ka je??"
Shahzain ya ce "Yau kuma Shayin Goriba za ka sha?"
Sahzaib ya ce "Wai to me yasa ma ka tafi??"
"Jarabar Tambayar za ku yi mini ne ko kuwa za ku ban Shayin??"
Shahmeer ya tashi tare da cewa "Ba fa ni na kar Zomon ba Ratayar ma ba'a ban ba, bari in cewa Masoyiyata ta yi maka, kai da ba ka gajiya da Tsayayya, ko huce gajiya ba ka yi ba ka fara faɗa."
Shahbeer ya ce "Barta zan zo in yi da kaina, kai kuma Dattijo Uban ƴan Mita."
Shahzain ya yi dariya tare da cewa "To shi kenan tinda ka rama gaya mana ina ka je?"
"Dalla ji na yi ba zan iya zaman gidan ba na tafi, can na je gurin Baban Halima mu ka kwana tare.
Shahzaib ya ce "Ashsha, wasa-wasa fa Jahilin riƙo gareka Shahbeer ba ka mantuwa har abin da aka yi ka na Jariri duk ba ka manta ba.
Shiru ya yi, gaba ɗaya ya tafi Duniyar Tunani, ba abin da ya faɗo masa sai Lokaci Yarintarsa a lokacin ne ya fuskanci tashin hankali na yau daban na gobe daban wanda ko wani Babban ba lallai ya iya jura ba.
Shahmeer ya ce "Tunanin me ka ke kuma?, Ko dai Amaryar taka ka ke tunawa?"
girgiza kai ya yi ya ce "A'a, Ina tuna Rayuwarmu ta baya ne amma na san ku kun manta wani abin kuma ba ku san shi ba, Dole ne ma Wani ka tsaneshi tsana kuma me tsaurin gaske."
salam jikinsu ya yi Sanyi, Shahmeer ya ce "Ka dena tunanin irin wannan abin Don Allah, kasani dai ba ma son abin da zai ɓata maka rai ko ya ƙuntata maka.
Murmushi ya yi dai-dai lokacin da ya tashi tare da cewa "Abin ya zame min larura, ya haɗe ya zamo Cuta, Nima ina so na manta amma na kasa, har yau ban dena mafarkan da su ke tunatar da ni ba haka kullum na ke a firgice, Ba
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 18 Chapter of 30