ta zo kin fita."
da sauri ta ce "Amma in abin kirki ne ba."
bai ce komai ba Su ka ci gaba da Hira.
Har ta shirya ta fito kira ya shigo wayarta, ta amsa gami da cewa ''Fatima Ya ne? jiya kirana Uku amma ba ki ɗauka ba kuma ko ki kira."
"Ki yi haƙuri lamura ne sun gama rincaɓe mini wallahi, yanzu sam ba na samun nutsuwa."
ƙasa-ƙasa ta yi kafin ta ce ''Ayya meke damunki haka?, ko dai tunanin Aljanin da ki ka yi gamo da shi ki ke yi?? "
"Yanzu ai ba abin da na ke tunawa sai shi, gaba ɗaya ba na maida hankali akan komai sai shi.
"Ƙaddara ta riga fata, kai jama'a?, Meye naki na tunanin wanda kin san ko kun haɗu ba lallai ki ganshi ba?, ai wannan mutumin sai Aljani ba dai mutum ba, ace dan bala'i duk wani motsinki ya sani? gaskiya ki dinga Addu'a kar Aljanu su rikitar mini da ke.
"Ai ba wannan ne ma abin takaicin ba Shukriya, ni fa yanzu na matuƙar kamu da son shi.
da sauri ta ce "Laa!!!! A'uzubillahi, kin fara son shi? a matsayin wa kenan? mutum ko Aljan?"
"Ko ma waye ni dai ina son shi Shukriya, amma ina ta Addu'a ina roƙon Allah ya baiyana mini shi.
cikin sanyi Shukriya ta ce "Ayya Aminiyata, ban yi zaton kema za ki faɗa tarkon So haka ba, amma ba yadda mu ka iya in sha Allahu za ki ganshi, idan anjima za mu yi waya yanzu fita zan yi."
Fatima ta ce "Shi kenan, sai anjima, nima ai na kusa zuwa gidan naki."
"Yee!!" ta faɗa ta na dariya, daidai lokacin Shahzain ya ƙaraso wajen ya tsira mata ido, katse kiran ta yi kafin ta ce "Mr Gigi wai idan aka dameka da turo Message kuma ka kasa gane kowaye kuma in ka kira ba ta shiga ya za ka yi kenan??"
"To ke meye haɗinki da wannan tambayar?"
"Amsa ya kamata ka bani ba wai ka tambaye ni ba, Ƙawata Fatima itace ake turowa kuma na soyayya amma ta rasa kowaye, kasan ma wai abin takaicin? wai har ta fara son shi kuma fa ƙila Aljani ne don haka naga alama.
"Aljani dai?, to Allah ya yi mana tsari da su, ni kam ban san yadda ake gane kowaye ba.
Ta turo baki tare da cewa "Dama ai ba lallai ka sani ba."
murmusawa ya yi kafin ya ce "Mu je ko?" gaba ta yi ta na ci gaba da bashi labarin Fatima da Aljanin nata.
Da daddare Hajiya Dada da Mami da Daddyn Maalik suka halarci gidan.
Tin da Dada ta shigo ta ke ƙwala ido don ganin ta inda Mommy za ta ɓullo, Su Inna ne su ka tarbesu hannu bibbiyu. kasa jurewa ta ce "Ina Hajiya Aisha ne?"
Inna ta ce "Ta na ciki, ai za ta fito .''
Dada ta ce "To ko dai ba ta san mun zo bane?"
"Ta sani, tin da na ce za ta fito ai sai ku yarda"
Inna ta faɗa a ƙagauce don kuwa haushin Dadar ta ke ji tin ba ma yanzu ba, tin lokacin da ta so shiga Tsakanin Ɗan jikallenta da wadda ya ke So.
Mami ta ce "Haba Dada ƙagara ta mece kuma?"
shiru ta yi musu don kuwa ta san ba za su fahimci abin da ta ke ji ba, har yanzu mugun mamakin ganin Aisha a wannan halin ta ke yi abin da ba ta taɓa zata ba, lallai ta na da son Zuciya ba kaɗan ba.
Da sallama Mommy ta ƙaraso wajen, Mami da Inna ne kawai su ka amsa Dada kuwa ta kasa cewa komai sai kallonta da take yi kamar za ta cinye ta, "Astagfirullah, Allah ka yafe mini ba dan kaina ba" shine abin da ta furta a ƙasan Zuciyarta, har Su ka gama gaisawa da Mami ba ta ce komai ba sai da Mommyn ta ce "YaYa Hanne! Abin ko magana babu?"
firgigit ta dawo daga Duniyar tunanin da ta leƙa, ta sauke nannauyar ajiyar Zuciya kafin ta ce "Me zai hana na yi miki magana Hajiya Aisha sai dai in ba ni da bakin, Ina wuninmu!"
"Lafiya ina fatan kowa da kowa lafiya lau.
"Wallahi ƙalau A'i ya haƙuri da halayena?, kin ga yanzu Allah ya nuna mini iyakata gashi mun ƙara Alaƙantuwa ta sanadin ƳaƳanmu, Ki yafe ni A..."
katse ta ta yi da ce wa "Haba YaYa Hanne ai wallahi ban riƙe ki da komai ba, na riga na yafe miki, Ina Maalik? na ɗauka da shi za ku zo ai, Ɗan Albarka me rikici."
Ƙasa ta yi da kai ta na murmushin dole don kuwa ji take kamar ta fashe da kuka, kunya da takaicin halinta ya sa ta ke jin gaba ɗaya ta tsani kanta, cikin sanyi ta ce "Maalik ya na gida ya ce zai zo Babansa ya ce a'a; Ni kam Hajiya Aisha na ce yaushe za ki je Dutse?"
Rausayar da kai ta yi gami da cewa "Toh, YaYa Hanne ai kinsan ni ba zan iya tsallake hukuncin iyayenmu ba, ba su neme ni ba don haka ko ƳaƳana ban bari sun je ba, kar in je abin ya zamo na ɓacin rai."
"Don Allah ki rufe ido ki je, ai yanzu kowa ya gane mu ke da laifi da ni da Babana duk mun yi ne don son Zuciyarmu, ki yi haƙuri don Allah na san ko kowa ba ya nemanki iyayenki su na buƙatarki.
"Zan je amma fa har sai an neme ni, Ina ganin mu bar maganar nan don ni na gama tawa, mu yi magana akan Alaƙar Ƴaƴanmu, lallai ya na da kyau Maalik ya san Halin da Duniya da Ababen cikinta su ke ciki kafin ya zama Shugaban wasu; ina nufin nan gaba kaɗan zai zama Uba in Allah ya yi, to ina ganin ya na da kyau mu fara Inganta rayuwarsa da musar da shi sauƙaƙƙar hanyar da za ta zamo haske wa rayuwarsu ta gaba."
Dada ta jinjina kai ta ce "Wannan haka yake Hajiya, in sha Allahu zan kula da hakan sosai, sannan ai kema ɗanki ne zan dinga turo miki shi kullum ki na yi masa Nasiha."
Mommy ta murmusa gami da cewa "Na gode da hakan."
Mami ta ce "Ai banga abin Godiya ba Hajiya Aisha, ai Ɗa na Kowa ne, Ni kuma Abida ce sai Addu'a wallahi."
Mommy ta ce "Na manta ma ban tambayeki su ba kawai na tambayi Ɗan-uwana, duk suna lafiya da Hadiza da Abida da Abid ko?"
Mami ta ce "E su ne fa, duk su na lafiya, idan Abban nasu ya samu lokaci ai zai kawo su duka."
Mommy ta ce "Ya yi kyau."
ci gaba su ka yi da tattaunawa akan abin da ya shafi Ƴaƴansu da danginsu.
Yau, Alhaji Boza da Ƙaninsa da Dr Idris da Shahbeer su ka je gidan su Ma'arufa don gaisawa da Mahaifinta kuma su nema wa Shahzaib Aurenta. Cikin Mutunci da Mutuntaka su ka haɗu kuma su ka rabu kowa ya ji daɗin haɗuwa da kowa.
Shahbeer, Gidan da su Halima ke zaune ya wuce don duba lafiyarsu kamar yadda ya saba.
_________
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
*INDO*
[1/14, 10:14 AM] INDO CE: *WATA HANYA*
40
Ayeesha Abdulkareem
*(Indo ce..)*
ELEGANT ONLINE WRITERS.
Baban Halima da Salim su na zaune su na hira ya yi sallama, Salim ya tashi cike da ladabi ya ce ''Barka da zuwa Shugaba."
fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce "Na sameku lafiya?"
"Lafiya lau" ya faɗa tare da yin hanyar fita.
Kusa da Baban Halima ya ƙarasa ya zauna kafin ya ce "Barka da yanzu Baba."
"Ɗana ku na lafiya?"
"Lafiya Baba, Halima fa?"
ya ce "Ta na ciki, ita dai har yanzu ta kasa komawa yadda ta ke Da, a yanzu ko da yaushe a takure ta ke."
murmushi ya yi gami da cewa "Za ta warware, Baba mun je Nemawa Shahzaib Aure daga can mu ke."
"Alhamdulillahi, na ji daɗi Allah ya sanya Alkairi."
"Ina ga ma lokaci laɗan za'a saka, za'a haɗa ne da Shahmeer sai kuma Ni ina fatan dai za ka bani Halima."
murmushin Manyance ya yi kafin ya ce "Ko shakka babu Ɗana, fatana Allah ya yiwa rayuwarku Albarka kawai."
"Na gode Baba, Amma to Ƙaninka ko YaYanka fa? ya na da kyau a sako su a ciki."
"Allah sarki Ɗannan; ai ni yanzu ba ni da kowa sai Allah sai Ƴata Ɗaya sai ku da Allah ya haɗamu; asalinmu Mafarauta ne Ina da Wa guda Ɗaya da Ƙani guda Ɗaya, tare mu ke rayuwa a Babban gandu da mu da Yayan Babanmu guda Ɗaya da kuma kakanmu da matarsa; duk sun riga ni Aure YaYana har ya ƙaru da Ƴa Ɗaya, A Ƙauyenmu ba wanda bai sanmu ba, Sabi da mun yi fice tin daga kan Me-Dawa Mahaifinmu kenan, Uban-dawa kuma Kakanmu sai mu ma mu ka gaje su, sai dai a cikin Yaran duk an fi Sanina kuma Mutane sun fi nuna mini ƙauna, a cikin haka aka wayi gari Kakarmu ta rasu, bayan rasuwarta ko wata huɗu ba'ayi ba Kakan namu shi ma ya rasu, ba'a rufe shekara ba wata Rana YaYana ya shiga Dawa aka dawo mana da gawarsa Maƙiya sun kashe shi, Bayan ya rasu Da shekara guda na yi Aure ba'a Daɗe da hakan ba sai Rasuwar Babanmu shi ma Maƙiya sun yi galaba akanshi, haka mu ka ci gaba da haƙuri mu ka karɓi Hukuncin da Allah ya yi mana, a kufi-kufi mu kai ta samun rashi, bayan rasuwar Mahaifinmu, Mahaifiyarmu da Ƴar YaYana da Matarsa da Ƙanina sun yi tafiya akan hanya su ka yi Haɗari dukansu ba wanda ya rayu, Na ci gaba da rayuwa tare da YaYan Babana da Matarsa, ana kwana ana tashi mu ka wayi gari da rashin Uwa Matar YaYan Babana; A taƙaice dai bayan wani lokaci duk na rasa dangina ya rage daga ni sai Matata a wannan lokacin ni kuma na wayi gari babu Ido; Zaman Ƙauyenmu ya zame mana ƙunci don haka me ɗakina ta takura akan sai mun barshi, shine silar dawowarmu nan cikin birni kuma mu ka zama ƴan-gari a cikin Lungun Makafi, anan mu ka haifi Halima bayan haihuwarta Itama me Ɗakina ta rasa idanunta daga bisani sai ta rasu, sai ya zamana ciki da waje saura Ni da Halima; Kaga yanzu ba ni da kowa Sai Allah, ya fi mu son Bayinsa shi ya sa ya karɓesu."
Shahbeer ya jinjina kai cike da tausayawa "Ya ce Allah i yi musu Rahma." "Amin, Ni dai ba abin da zan ce sai dai in yi maka godiya Abu na biyu kuma shine in damƙa Amanarta gareka, Ni bani da ƙarfin da zan iya tsaya mata amma na Mallaka maka ita ka zamo mata Danga, idan ka yi mini haka to fa ka biyani Allah ne kaɗai zai iya biyanka Lada"
"In sha Allahu Baba, Kar ka ɗaga hankalinka."
riƙo hannunsa ya yi tare da cewa "Yauwa Yarona Allah ya yi maka Albarka ya shiga tsakaninka da maƙiyanka."
"Amin.
Baban Halima ya ce "Ɗana a tafin hannunka na ji wani abu na rashin daɗi." dariya ya yi gami da cewa "Baba kai Ɗan-baiwa ne halan?? ba kai mini bayani akan haka ba."
"Yaro ai kuwa wannan Baiwa dai zan iya ce maka gadon gidanmu ce amma daga Kakanmu sai YaYan Babana sai kuma ni mu kaɗai ke da ita; Idan ka na so in faɗa maka to." ya ce "Ina so mana." "Ka yi mini Alƙawarin ba za ka damu ba, ka ɗauka cewa Alkairi ne hakan a gareka.
"To Baba ina ji.
"Za ka rasa wani daga cikin Ƴan-uwanka sannan Mahaifinka ma za ka rasa shi.
gabansa ne ya yanke ya faɗi, lokaci guda Jikinsa ya yi matuƙar sanyi salam, Addu'arsa ɗaya Allah ya sa ba a cikin Ƴan-uwansa guda Biyar zai rasa ba, Shahmeer Shahzaib Shahzain Sa'ad Zakiyya.
Baban Halima ya ce "Ka yi mini dai Alƙawarin ba za ka damu ba." ya murmusa tare da miƙewa ya ce "Gaskiya ne Baba, Ina Halimatu?"
Bai ce komai ba shi ma Shahbeer bai ƙara magana ba ya nufi Ciki, ta na Falo ta na Kallo ya yi sallama, ta na ganinsa ta yi saurin miƙewa tsaye ta na kallonsa, "Tsaya daga nan Ɗan Saurayi." ta faɗa gami da yin ƙasa da kai, murmusawa ya yi kafin ya ce "Ohh to, Kina lafiya?"
gyaɗa kai ta yi gami da cewa "Kai ma haka?" "Umm, amma ba duka ba, ba ki tambayeni Ɗana ba.
Shiru ta yi ganin ba ta da niyar magana ya sa shi cewa "Mun kusa Aure ni da ke, ki kasance cikin shiri a koda yaushe."
maganar tasa ta zo mata da girma ko ɗago kanta ta kasa yi, ya yi dariya gami da juyawa ya nufi Hanyar fita ya na cewa "Tin da na ganki dai ko ba ki ce komai ba shi kenan."
"Da sauri ta ce Ɗan Saurayi!!..." juyowa ya yi ya zuba mata idanu. Juyawa ta yi ta na murmushi ta kuma rasa abin da za ta ce masa, har cikin ranta ba ta gaji da ganinsa ba hakan ya sa ta yi masa kiran da ba ta shirya ba.
"In zo in zauna ne? idan ma aiki za ki sa ni a shirye nake.
ta dara gami da cewa "Ka tafi kai kam, Ka ce ina gaida YaYa Malika da Mommy."
"To ba komi, amma da zan yi magana to na fasa tin da ko gurin zama ba'a bani ba.
bai jira abin da za ta faɗa ba ya fice.
Bayan wani ɗan lokaci.
Cikin shirinta ta fito ta yiwa Umma sallama sannan ta ɗauki hanya.
ajiyar Zuciya ta sauke bayan sun gama waya ita da Shukriya.
Tin a bakin get ta yi karo da Shukriya ta na jiran isowarta, ta na zuwa su ka rankaya zuwa ciki.
ko ruwa ba ta sha ba ta ce "Shukriya ni fa ina ga kwanana ne ya ƙare."
"Kwananki ya ƙare?,wannan maganar sam ba ta dace da ni ba Juna Biyu fa gareni, haba Fatima ai sai ki sa in shiga wani hali."
"Ni abin ya gama bani tsoro Shukriya ba ki ga duk yadda na firgice ba?, Messages ba dare ba rana ba safiya ba yamma har Asbahi, na rasa ko waye gaskiya dole Aljani ne.
"Idan ma Aljanin ne sai ki kira mana Mutuwa?, gaskiya ki dena ki dogara ga Allah kawai, ni barin fito daga kicin, ki na neman tayar mini da hankali.
"To A fito lafiya.
ta faɗa gami da gyara zama.
Shukriya ta na barin gurin Saƙo ya shigo wayarta da sauri ta fara karantawa "Barka da Zuwa Baƙunta.
zaro ido ta yi ta dafe ƙirji, ku ji irin Jarabar fa, har an san na fita na je wata baƙunta.
wani saƙon ta ji ya shigo ta duba "Tsorona ki ke ji yanzu ko?" da sauri ta bashi amsa "Dole in ji tsoron abin da ban taɓa gani ba ban san kowaye shi ba amma shi ya san duk wani motsina.
"Idan ba tsoro ba ki fita zuwa bayan gidan da kike yau za ki ganni, idan kin fita ki kira lambar tawa yau za ta shiga.
"Ko jarrabawa ba zan yi ba don ina tsoro.
"Tsoro ba na Jarumai bane Sarauniyata, ki aje shi gefe ki buɗe ido don ki ga Mahaukacin Masoyinki.
"Waye ya ce maka Mahaukaci?"
"Ko ba'a faɗa ba nasan na Haukace akan sonki.
"Ba na so ka ƙara faɗen haka, wannan shine Asalin hankali, indai har da gaske za ka nuna mini kanka zan fito.
"Ban taɓa gaya miki haka ba sabi da haka tin da na faɗa da gaske nake.
"To yanzu zan zo.
"Ina jiranki.
miƙewa ta yi ta fara ƙwalawa Shukriya kira, ta fito da sauri ta na cewa "Lafiya kuwa."
"Zan ɗan fita baya ne, kar ki neme ni ki rasa.
"Ke tsaya, Abinci fa na ke haɗo miki.
"Ai yanzu zan dawo in sha Allah.
ta na jin Shukriya ta na magana ta yi mata banza ta fice, cikin sanɗa ta zagaya bayan gidan, babu kowa sai tsirrai na Fulawoyi, ta na jin tsoro amma ta na matuƙar son ta ganshi, Da Addu'a a bakinta ta tura kira, ta bayanta ta ji ƙarar wayar ta yi saurin juyowa a matuƙar firgice don kuwa a kusa da ita ta ji Ƙarar.
cikin sauri ya ce ''Kula fa."
ta ƙara zabura, ta yi baya da sauri ta na zaro ido akansa, shima kallonta ya ke yi fuskarsa ɗauke da murmushi, ganin ta kasa yin magana ya sa shi cewa "Shahmeer!! Aljanin Messages."
baki na rawa ta ce "Kai ne??"
"Ni ne, yau Allah ya yi na bayyana.
"Me yasa to ka ke tsorata ni?"
ta yi masa tambayar cikin narkakkiyar murya kamar za ta rushe da kuka.
Durƙusawa ya yi kan guiwoyinsa kafin ya ce "Ki hukunta ni ko kuma ki yafe mini, na rasa ta yadda zan baiyana Soyayyata gareki sai ta wannan hanyar, Ina sonki ina so na rayu tare da ke Fatima, kin Amince mini?"
Murmushi ne ya suɓuce mata, cikin ranta ta furta Alhamdulillah, Allah na gode maka da kai mini kyautar Ɗan-adam ɗin da na ke matuƙar So, kuma bai kasance Aljani ba.
"Ki ce wani abu Don Allah, shirunki ya na karya mini Zuciya gashi na shiga fargaba don ban san abin da ki ke tunani akaina ba."
murmushi me sauti ta yi kafin ta ce "Har da durƙusawa kai kam, Komai zan yi tunani akan ka me kyau ne, ka riga ka ɗauke Zuciyata tin kafin na sanka Ni ma Ina Sonka.
"Na godewa Allah domin shi ya mallaka mini ke, ba ni da ƙarfin da zan iya mallakarki da kaina, Na gode da Amsata Fatima.
za ta yi magana Muryar Shahzain ta katseta "Sannun Tantabaru iyayen ƙauna."
"Subhanallah" ta faɗa a ɗan zabure don kuwa ba ta yi zaton wani a kusa ba.
"Ba na son sa idon tsiya"
Shahzaib ya faɗa ya na dariya.
"To in banda abin ku lokacin da ku ke soyewa waye ya ke takura muku, do Allah ku tarkata ku ware daga nan, Fatima Na gode da karɓar tayin Jaririna."
Shahbeer ne ya yi maganar ya na ƙasa-ƙasa da ido irin Babban nan.
kunya ta gama lulluɓeta ji take kamar ƙasa ta tsage ta shiga ciki, sai rarraba ido ta ke ta rasa abin cewa.
Shukriya ce ta ƙaraso wajen ta na dariya gami da cewa "Na tayaku murna fa, wallahi komai ya yi mini daɗi, gani ga Ƙawata Wannan lamari sai Godiyar Allah, tawo mu je ki ci Abinci ki share waɗannan in ba haka ba sai sun sa ki kuka."
Hannunta ta kama su ka koma ciki, binta kawai take zangai-zangai jikinta duk ya yi sanyi, ta ko'ina tunanin Shahmeer ta ke yi.
Shshzaib ya ce "Bari in je in yiwa Mommy Albishir."
Shahzain ya ce "Ni kuma a ban kuɗi in haɗowa Inna kayan faɗen Kishiya in ba haka ba mu sa Rikici."
_________
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
*INDO*
[1/15, 10:11 AM] INDO CE: *WATA HANYA*
41
Ayeesha Abdulkareem
*(Indo ce..)*
ELEGANT ONLINE WRITERS.
Taɓe baki Shahmeer ya yi kafin ya ce "Mace muku tai kai da ita."
Shahbeer ya ce "Kun yi magana da Ramadan kuwa?"
Shiru su ka yi kafin Shahzaib ya ce "E, Jiya da dare dai mun yi magana ya ce mini ba ya jin daɗin jikinsa yau kuma ni ban bi ta kansa ba."
tsaki ya yi kafin ya ce "Sakarcin banza, amma ka san ba ya da lafiya ba ka sanar mana ba kuma kai ma ba ka yi ta tashi ba har wani faɗe ka ke yi?"
Ƙasa ya yi da kai tare da cewa "A yi haƙuri."
"In an jima za mu je."
Amsawa su ka yi kafin suka rankaya zuwa ɓangaren Mommy.
Haka Fatima ta koma gida ta na jinta kamar ba'a gaske ba, sai ka ce mafarki haka ta ke ganin komai.
Umma ta na ganin yanayinta ta ce "Sauyin Yanayi, meke faruwa? kar dai ki ce mini ƙuruciya ta sa kun yi Rigima ke da Shikriya?"
girgiza kai ta yi gami da cewa "Ai in wannan ne da sauƙi, Wai Shahmeer na ke So ashe ban sani ba" ta yi maganar ba tare da ta maida hankali akan me za ta ce da kuma wanda ta ke maganar ba.
Cikin mamaki Umma ta ce "Shahmeer Fatima?? ki na nufin shi ne ke turo miki Saƙonni iri-iri?"
sai a lokacin kunyar Umman ta kamata ta miƙe ta na murmushi ta yi hanyar ɗaki ta re da cewa "Ni ma mamaki na ke a tunanina ma bai san ni ba."
Umma ta murmusa kafin ta ce "Allah ya yi mana zaɓin Alkairi.
Su na zaune shi da Mamansa wayarsa ta yi ƙara ya ɗauka tare da sallama, "Mu na ƙofa ka buɗe mana" Shahzain ya faɗa masa.
da sauri ya tashi ya na cewa "Kai Zuwa ku ka yi amma ko
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 27 Chapter of 30