Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
lallai akƙwai baƙin bala'i walla.." a tsawace Shahzain ya ce "Kulll, kar na ƙara jin kalmar bala'i a bakinka" Shahzaib ya ce "Amma ai ka ji abin da ya ce ko?, wai har ma tutiya ya ke zai iya haɗuwa da Ita a wani gurin, Mahaifiyarmu ce fa!, wannan fa cin mutunci ne da zubar da kima" Shahbeer ya ce "Ƙarami, mu je ciki do Allah." raɓewa su ka yi gefe shi kuma ya shiga gaba. Mommy ta miƙe kenan da nufin komawa Sama ta ji sallamarsu hakan ya sa ta fasa tafiyar ta na murmushi ta ce, "Sai yanzu ake ganinku?." ko kallon inda take Shahbeer bai yi ba, da yake da umarninsa suke aiki su ma ba su saurareta ba suka wuce sashinsu. Komawa ta yi ta zauna "Yasalam" ta faɗa gami da dafe kai. Inna ta ce "Tirƙashi, Tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa ke duka, yau gashi kema kin jawo ruwan dafa kanki." Rintse ido ta yi da ƙarfi gami da girgiza kai ta ce "Na san dama hakan za ta faru dole, amma me yasa?" Inna ta ce "Allah dai ya kiyaye na gaba, yau dai kuwa wannan Mutumi ya gama lalata miki farin ciki, amma da bai zo a irin wannan lokacin da ya san za su iya dawowa ba." cike da damuwa Mommy ta ce "Inna ki yi shiru Don Allah surutun naki ƙaramin zafin yake." Inna ta ce "Na ma yi ai, ni madafa ma zan tafi." A sashin su. Shahzain ne ya ce "lallai ashe watan targaɗa duk wani abin da mutumin can yake taƙama da shi ya kama" Shahmeer ya ce "Wallahi ɗari bisa ɗari ina bayanka, wannan fa babba ƙalubale ne a garemu" Shahzain ya ce "Shi yasa lamarin yake ɗaure min kai, na rasa wane baƙin tsafin ya yi wa Mommy da har take zama ta saurareshi" Mitar abin da ya faru suke yi cikin ɓacin rai gami da damuwa, Shahbeer kuwa ko uffan bai ce ba. Shahzain ne ya ce "Inya, (Shahbeer) magana fa muke ta yi amma ka ƙi cewa komai ka biye wa wannan karen." Kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce "Ta yuwu shi Karen idan nace ya yi shiru ba zai ƙara magana ba." Shahmeer ne ya gyara zama kafin ya ce "Ni dama nasan surutan nan namu duk ba wanda ya hau ƙa'ida, faɗa mana me ya kamata mu yi? umarninka kawai mu ke jira." shiru ya yi na ɗan Lokaci sannan ya ce "Umma ta na buƙatar Zuwa Saudi Arabia don gudanar da ibada" murmushin farin ciki ne ya baiyana akan fuskar Shahzaib, ya lumshe idanunsa gami da cewa "Ka yi kyaun kai YaYa, kafin ta dawo mun gama yarfa masa rashin mutunci." murmushin gefen baki Shahbeer ya yi kafin ya ce "Cikin hanzari nake son ayi hakan." MOONASH. Daga Ƙungiyar, ELEGANT ONLINE WRITERS. BANI DA HUJJA Maimoon BRR SHAHEEDA Ayush SARƘAƘIYA Shaahd ZUMUNCIN ZAMANI Jikar Nashe WATA HANYA Indo ce.. *ALBISHIRINKU Masoyanmu, yanzu dukan littafan nan sun dawo kyauta za ku sha karatunsu ba tare da kun biya ko ficika ba, ina fatan hakan zai sa ku farin ciki, Much Lve😘* *INDO* [11/28, 10:30 PM] INDO CE: *WATA HANYA* 3 Ayeesha Abdulkareem *(Indo ce..)* *(BAYA BA ZANI, shine sunan da na sa da farko, ku yi haƙuri a bisa canjin da aka samu, ya faru ne sabi da wani dalili, ku cigaba da bina da wannan sunan WATA HANYA don jin yadda labarin yazo, Salo ne na Musamman, dan ma dai ba kyau yabonkai da kanku ma za ku yabeni In sha Allah🥰😘😘)* MOONASH Daga Ƙungiyar ELEGANT ONLINE WRITERS. Auta (Shahzain) ya ce, "Kamar an gama ne Boss, duk yadda ka ce hakan ta zauna." Mommy ta kasa zaune ta kasa tsaye, ba ta da mafitar da ta wuce janye bakarta dan shine kaɗai maslaha tsakaninta da fusatattun ƴan Huɗunta, ta daɗe ta na kai kawo kafin ta danne Shakkar Alhaji Boza da take yi ta tura wa Lambarsa kira. Zaune suke suna hira cike da farin ciki, Alhaji Boza ne ya ce "Ai tattaunawa ta yi nasara dan kuwa yanzu ina gab da kaiwa gacci, Ƴan Huɗun nan sune nakasu akan komai nawa, yanzu bani da mafita illa haɗewa da su indai suka dawo jikina to ko President nake son zama sai na zama ƙarewar kafuwa a Siyasa, To nasan ba za su saurareni ba dan haka na yi musu ta manya naje na samu Uwarsu, kuma kunsan Hajiya A,i Shakkata take ba za ta iya ƙin karɓar Umarnina ba, to tinda ba kangararru bane su na jin maganarta kin ga idan ta sa su za su yi shi kenan ni kuma masakina ya cika" "Yess Dad!!! Wallahi ka mugun yi min, ashe za ka iya yin hakan ka bari na zauna ina ƙarar da tunanina akan ta inda zan biyo musu, ohh Thank You Dad!!" Safyan ya yi maganar cike da nuna farin ciki da murna akan maganar Daddyn nasa. Alhaji Boza ya ce "Hajiya Uwar gida ran-gida ba ki ce komai ba." Wani yalwataccen Murmushi me cike da shu'umanci ta saki gami da cewa "Ka yi amfani da damarka kuma wadda ta dace, Na yi shiru ne sabi da Ɗana ya na magana, Dole ne ka samu lambar yabo a gurin kowa ma bare a gurina, ɗaukaka da ci gabanka ai duk nawa ne domin kuwa ni na haifi magadanka, Babu Sauƙi a cikin lamarin yaran-nan Dan Haka sai ka yi da gaske Alhaji." "Ai kar ki damu na karya lagonsu... Shiru ya yi sabi da wayarsa da ta fara tsuwwa kuma ya na ɗauka ya ga sunan A,I ya na yawo akan wayar, ɗan tsaki ya yi ya ce "Kin ga wai kira ta ke yi ko me za ta ce?, ni ba ma zan ɗauka ba." Safyan ya ce "A'a Dad, ba ka san me za ta ce ba gwara ka ɗauka." sai da ta katse wani kiran ya shigo sannan ya ɗauka gami da sallama. Addu'a ce ɗauke a bakin Momi lokacin da Alhaji Boza ya amsa kiran, Ajiyar Zuciya ta sauke cike da Ƙarfin hali ta ce "Na kiraka ne domin na sanar maka na janye Alƙawarin da na yi maka, na fi shakkar ƴa-ƴana akanka, kai ta yuwu wata ƴar alaƙa ce ta haɗamu amma su sune komai nawa, ƴa-ƴa iyaye ƴan uwa abokan arziki sune farin cikina kuma sune raunina dan haka bazan faɗa musu wata banzar magana taka ba." daga haka ta kashe kiran. Kamar saukar Aradu Haka Alhaji Boza ya ji saukar Maganar Mommy, "Shi kenan Yaran-nan sun ƙara tarwatsa min muradi" Ya faɗa gami da zame hular kansa cikin kiɗima da rashin sanin makama. dogon tsaki Mom ta buga kafin ta ce "Ashe duk a baki ne ba iyawa ka yi ba, to ka ji sakama-konka yo dama waƴannan Ƴa-ƴa kamar ƴa-ƴan Fata haihuwar ƴa-ƴa huɗu lokaci ɗaya ai daga ji ba Alkairi a cikinta bare aka samu yara masu taurin kai da tsauri akan ra'ayinsu uwa uba shu'umanci Sun tara daula sun tara kuɗi da dukiya sun haɗa Duniya, Da-can ALHAJI BOZA Kawai ake magana akan kasuwancin komai amma yanzu Kowa DOUBLE TWO STAR ba rin kasuwancin da ba su iya ba a kuɗi kuwa yanzu waye yake ta kai? ai ka zama ƙafaffiyar Rijiya su Kuwa Shakundum, na ji haushin ma murnar da na fara yi kafin na tabbatar da nasarar taka, yanzu ƴar siyasar ma da za ka yi ka zama wani nema suke su toshe hanyar, Alawadai da wannan abin." daga haka ta bar musu wajen a fusace. da ido suka rakata kafin Safyan ya ce "Ka ga dai Ran Mom ya ɓaci, yanzu dai-dai kenan ? in ba za ka iya da su ni ka barni da su Dad, wallahi cikin Sati zan sa a dena faɗensu a Duniya." Alhaji Boza ya ce "Faɗen bikin ba bikin bane Safyan, Sanin sunansu ko ganin fuskarsu ba zai sa ka gane ko suwaye su ba, mu bi su da sigar yaudara da kissar kasuwanci amma idan ka ce ƙarfa-ƙarfa za ka yi musu to tabbas za ka ga yadda reshe ya ke yin juye da mujiya, yanzu ka kwantar da hankalinka dole daular za ta bar hannunsu ta dawo naka duk yadda zan yi sai na yi hakan ta faru." Safyan ya ce "Ka yi Alƙawari Dad?" "Na yi Alƙawari da duk abin da na dogara da shi sai na cika maka burinka ɗana. "Sam bana ƙaunar ganin dariya ko farin cikinsu Dad. "Kar ka damu lokacinka zai zo Safyan. miƙewa Safyan ya yi ba tare da ya ce komai ba ya bar wajen. Da Sallama Mommy ta shigo Bedroom ɗin nasu, Shahzain ya na kwance ya yi matashin kai da cinyar Shahbeer yayin da shi kuma ya ke duba takardu, Shahmeer da Shahzaib kuwa danne dannen waya su ke yi. ciki-ciki Shahzaib ya amsa Sallamar, ta ƙaraso cikin sanyin jiki ta ce "Yau kun ƙi saurarar kowa Inya! (Shahbeer)." Ƙarami (Shahzaib) ya ce "Ai ya fi mu sauƙin kai Mama shi yasa kin fi riƙe sunanshi, wai akan me za ki bar wancan kayan dattin ya shigo mana gida? ki na ji har faɗe yake zai iya haɗuwa da ke a duk inda ya ga dama wannan ai ɓata suna ne." Jariri (Shahmeer) ya ce "Ai ni tambayar ma me ya zo ya gaya miki??" cike da damuwa ta ce "Haba ku tsaya ku fahimceni mana, ni fa ba ni nace ya zo ba da ya zo ɗin kuma ba wata magana ce ta shiga tsakaninmu ba, Alfarma ya zo nema a gurinku kuma da na san ba za ku yi ba na gaya masa ba zai yuwu ba, shi kenan fa, yanzu daga ni sai ku ba maganar kowa a tsakaninmu." Auta (Shahzain) ya ce "Don Tabbatarwa ya zama dole sai kin yi nesa da mu Ummi, ki yi haƙuri fa Inya ya bamu umarnin shirya miki tafiya Saudi Arabia kuma ba buƙatar ƙarin shawarwari." "Subhanallah, wai duk na meye hakan?" Inya (Shahbeer) ya bata amsa da cewa "Na ba ma son ganin Alhaji Boza a tare da mu ne, ke kuwa Ummi kin kasa gane cewa Asalin maƙiyinki ne mutumin nan." "Amma Shah.." da sauri ya katse ta da cewa "Kin fi kowa sanin na tsani na yanke hukunci a ƙi ɗauka Mommy." gyaɗa kai ta yi gami da cewa "Na sani kuma zan je amma duk ba wannan ba, ku dena fushi dani ku yi haƙuri ba zan kuma sauraron shi ba in Allah ya so." "Waye ya isa ya yi Fushi da Jarumar Uwa? ko waye to tuba yake Umminmu" Shahmeer ne ya yi maganar cikin fara'a. Shahzain ya ƙara da cewa "Kansa bisa wuyansa a yafeshi Mama." Murmushin farin ciki ta sako dan kuwa yanzu ta tabbatar komai ya wuce sun sakko daga dokin Zuciyar tasu. Shahbeer ne ya ce "Mommy zauna mana." "A'a Ba zan zauna ba na bar Inna ta na jirana na ce mata bazan daɗe ba. "Mu je in raka ki" Shahzain ya faɗa tare da dirowa daga kan gado. da sauri Mamin Shukriya ta fito daga kicin tana amsa sallamar da ake ƙwalawa a tsakar gida, "Sannu da Zuwa Hajiya shigo mana kun tsaya daga nan?, ina can ina girki ne hankalin ya yi nisa" Mami ta faɗa cikin nuna girmamawa ga Hajiya Dada. Cikin takun isa da ƙasaita ta ƙaraso ta zauna sannan ta ce "Da yake ba gurin kowa ma na zo ba gurin ƴata na zo ta na ina?, MAALIK zai dawo gida dan haka ina so da zarar ya dawo Abincin Matarsa zai fara ci sabi da haka da ita zan tafi maza-maza ki shirya min ita." cikin sanyin jiki Mami ta ce "Ta je gurin aiki kuwa Dada amma ki yi haƙuri ta na dawowa ba zan bari ta ɓata lolaci ba zan sa ta taho." murmushi Dada ta yi gami da cewa "Ki tabbar yau ta kwana a gidana" daga haka ta nufi hanyar fita ba tare da ta amsa gaisuwar da Mamin take mata ba. Zaune take a takure ta haɗe kai da guiwa kuka ta ke yi sosai wanda har ya jaza mata ciwon kai , ta na ji Umma ta yi sallama sai dai ba ta da bakin amsawa dan kuwa kukan ba zai bata dama ba. da Sauri Umma ta zo ta zauna kusa da ita ta na tambyarta abin da ya faru, cikin kuka ta ce "Umma ni ba zan kuma zuwa aikin nan ba." Umma ta ce "To me yasa Ma'arufa?, wani abin ne ya faru? " "To Umma ba su da aiki sai ci min mutunci da wulaƙanta ni kuma ni ina aikin da aka sa ni sosai, ki cewa dillaliya ta nemo min wani gurin ni bazan iya da nan ba" Kamar Umma za ta yi kuka ta ce "Ma'arufa ke fa ba kowa bace baiwar Allah ce kawai to me yasa za ki tashi hankalinki dan suna yi miki haka? ki yi haƙuri ki dena kuka wata ran fa sai labari a ganina indai ba za su tauye mana haƙƙi idan kin yi aikin ba ai ba komai dan sunyi duk wannan, Ma'arufa ni dai ban goyi bayan hakan ba, idan ki ka bar aikin kenan ya za mu yi?" Fiddausi ta ce "Umma ni in ba za ta iya ba sai a kaini in ci gaba dan hakan shine rufin asirinmu." Shiru Ma'arufa ta yi ta na nazari kafin ta ce "Allah Umma cin mutunci akwai ciwo, amma dai zan ci gaba sabi da ku ke kuma Fiddausi ki ci gaba da zuwa Islamiyyarki kawai ni tinda na yi karatun ke ma sai ki yi." murmushin Farin ciki Umma ta yi gami da cewa "Allah ya yi miki Albarka Ma'arufa." "Amin" su ka amsa, Ma'arufa ta koma ta kwanta su kuma su ka ci gaba da hira. Cikin rawar kai irin nata ta yi sallama ba ta jira a amsa ba ta ci gaba da ƙwalawa Mami kira. kusa da Mamin ta zauna ba tare da ta yi duba da yanayin damuwar da take ciki ba dan kuwa sam ba ta ankare da hakan ba, ta na dariya ta ce "Mami yau kuwa kin saurareni??." Mami ta girgiza kai alamar "a'a" ta ci gaba da cewa "Na so saurararki amma Allah bai yi ba, a dai-dai Lokacin ne nake ga Hajiya Dada ta shigo." Rass gabanta ya yanke ya faɗi baki buɗe ta ke kallon Mami cike da fargabar abin da zai fito daga bakinta, "Maalik zai dawo shine ta ce yanzu-yanzu ki tafi gidansu da itace ma za ta biya ta ɗaukeki. "Maalik ɗinnan fa ɗan-iska ne wanda bai san dokokin Addini ba Mami, shi kenan farin cikina ya ƙare yanzu nasan abin da za'ayi min ko matarsa ta aure albarka, a bari mana a ɗaura auren sannan ko me za'ayi sai ayi, ni wallahi Mami ba zan iya jurar wannan rashin darajar ba ni rayuwa nake me cike da farin ciki da nishaɗi ina tare da ƙannena a gidanmu kawai sai a maidani wajen wani Maalik, Ba Dada ba Allah yasa... Da sauri Mami ta katseta da cewa "Ke i shiru mana bakya cikin nutsuwarki ne?, Ko Mahaifinki fa ladabi ya ke yi ga dukkan kalmar da ta fito daga bakin Dada akan me za ki dinga faɗen maganar son rai akanta?, to ba dani ba bazan watsa tarbiya da tsarin da iyayenki su ka taso akai ba, maza-maza ki shirya ki tafi cewa nai mata ko zama ba za ki yi ba zan ce ki tafi dan haka tashi kar lokaci ya ƙure." jiki a sanyaye Shukriya ta tashi ta fara harhaɗa kayanta dan kuwa tasan ita da dawowa gida sai Lokacin da Maalik ya bar ƙasar nan, ta na yi ta na sharar ƙwalla har ta kammala shirin ta fito ta yiwa Mami sallama sannan ta ɗau hanyar gidan Hajiya Dada. *INDO* [11/29, 8:55 AM] INDO CE: *WATA HANYA* 4 Ayeesha Abdulkareem *(Indo ce..)* MOONASH Alƙaluma Shida. Daga Ƙungiyar ELEGANT ONLINE WRITERS. BANI DA HUJJA Maimoon SARƘAƘIYA Shaahd BARRISTER SHAHEEDA Ayush AUREN ƘAUYE Nazlarh ZUMUNCIN ZAMANI Jikar Nashe WATA HANYA Indo Ɗaya-bayan-ɗaya suka gama shiryawa cikin ƙananun kaya Riga da wando baƙaƙe sai P-cap wadda take temakawa wajen ɓoye wani sashi na fuskarsu. Shahbeer ne ya yi hanyar da za ta sada shi da sashin Mommy ya na cewa "Shahzain, ɗakko Makulli guda ɗaya Shahzaib ne zai yi driving." ba musu ya nufi inda Makullen motar suke, a parking space ya same su har Inna da Mommy wadda ta kammala shirinta na tafiya, Hankicif fari Shahzain ya wurga wa Shahmeer tare da cewa "Karɓi wannan ka ɗaura nima da har na manta sai da na tuna sannan na ɗakko." karɓa ya yi ya ɗaura akan karan hancinsa sannan ya ɗora baƙin tabarau ɗin da ke riƙe a hannunsa, hakan ya sa kamarsa ta ɓace ɓatt, kamar yadda Shahmeer ya yi shima Shahzain haka ya yi sai su ka zama su biyu Shahbeer da Shahzaib kuma iya Tabarau su ka saka su ma sai su ka zama su biyu. Mommy ce ta kallesu gami da cewa "Dan Allah ku kula da junanku idan ba na nan kar ku yi wauta ,ko me Alhaji Boza zai yi kawai ku ji shi ku kalleshi kar ku biye masa dan ni ina tsoron ya illata min ku dan ba Allah a ransa" Murmushi Shahbeer ya yi ba tare da ya yi magana ba. Shahzain ya ce "Haba Haba ai shi ma ya san iya gonarsa ko ya sha giyar wake ba zai hauro tamu ba dan mu ƴan yau ne ba na da ba, mu mun fi shi lalacewa." Mommy ta ɗan murmusa sannan ta ce "Shi kenan mu tafi ko?" gyaɗa kai Shahzaib ya yi kafin ya zagaya mazauninsa na direnba suna gama shiga ya ja motar. da kuka suka rabu da Mommy, ta na matuƙar sonsu da son kasancewa tare da su amma gashi ta sanadin Alhaji Boza su da kansu sun sa ta nesanta da su. dukansu Zuciyarsu ba daɗi su ma ba son kasancewarsu ba tare da ita suke ba sai dai ba yadda za su yi a cewarsu tinda ya fara da haka nan gaba har abin da ya fi wannan zai zo ya juye akanta. su na gaf da shiga Motar Wani matashin saurayi ya kira sunan Shahbeer, cak ya tsaya kafin ya waigo dan ganin wanda ya kira sunan nasa, cikin sauri ya ƙaraso wajen yana fara'a ya ce "Ya-Ya Ni ne Sa'ad, ina za ku je ne? ko wani ku ka rako?" dogon tsaki Shahbeer ya doka gami da watsawa Sa'ad wani shegen kallo me cike da ƙyama da ƙiyayya. a take Annurin kan fuskar Sa'ad ya gushe lokaci ɗaya ya ji ya raina kansa, bai fasa ba dan hakan ba shine zai kawo ƙarshen muguwar ƙiyayyar da ke tsakaninsu ba, cike da shishshigi ya kuma cewa "Ya-Ya Shahzai..." kasa ƙarasawa ya yi sabi da ɗaga masa hannu da Shahmeer ya yi cikin haɗe fuska da nuna ƙiyayya a zahiri. ya na kallo suka shige mota su ka bata wuta, baki ya saki ya na bin inda su ka ajiye motar da kallo, takaici da baƙin ciki ya cika masa Zuciya. ya na zuwa gida Ya fara yiwa Mom mita gami da tambayarta menene silar ƙiyayyar tsakaninsu da su Shahbeer, kauce-kauce kawai ta shiga yi masa da ya gane ba wata ƙwaƙƙwarar hujja sai ya bata guri cike da ƙudurin wata rana sai sun kira shi a matsayin wani nasu. Shukriya, ƙarewa jikinta kallo ta yi a cikin Madubi sai da ta saki murmushin da ba ta shirya ba ganin yadda ta yi mugun kyau, anyi mata lalle ja da baƙi ga gyaran gashi da aka kashewa kuɗi sannan aka zauna aka cakara mata kwalliya, turɓune fuska ta yi da ta tuna wanda aka yi kwalliyar dan shi gashi dai ta yi kyau ba damar ta turguɗe kwalliyar dan kuwa itama ta na da son ado sosai. Ta na nan ta na mita a cikin ranta ba zato ta ji an kira sunanta cikin wata irin muryar da ta kasa bambance ainahinta. Dariya ya yi ganin yadda ta zazzare ido, "Ba ki yi tunanin ganina a yanzu ba ko?, Ammi ma ban sanar mata ba ta na nan ta na shirin zuwa ɗakkoni dama na ce dirar bazata zan yi muku. Murmushin yaƙe Shukriya ta yi gami da cewa "E, ai ka kyauta, amma kasan dai ba'a shiga ɗakin mace kai tsaye." Shu'umin murmushin nasa ya yi gami da cewa "Sabi da ke na baro UK ba shiri na dawo gida idanuna suna buƙatar ganinki akan me kuma zan yi wa kaina shamaki bayan nasan ke ɗin tawa ce?" ''Shukriya ta me rabo ce ba ta Maalik ba, kar dai zaman ƙasar waje ya sauya maka yare ka dena gane Hausa?" cikin rashin gane bayanin nata ya sake tsira mata ido gami da cewa "Yaa? kenan ba Hausa na yi ba?" "Hausa ka yi sai dai ba ka yi ta akan ƙa'ida ba, ban fa riga na aureka ba Maalik ka dinga saita kalamanka mana, ka fiye wuce gona da iri wai ma me na yi wanda ya sa ka dawo sabi da ni?" shiru ce ta biyo baya dan kuwa ba shi da shirin ba ta amsa sai wani mayen kallo da rikitaccen murmushi yake binta da su. ganin abin ya yi yawa ya sa ta zame daga gurin ta nufi hanyar fita, da sauri ya riƙo hannunta ya na cewa "Kar ki barni a tsaye ta dalilinki Shukriya, bakinki ba ya iya mutuwa ya kamata ki koyi sarrafa shi tin kafin na fara sarrafa shi da kaina, ba ki ji amsar tambayarki ba ki ke shirin tafiya, amsar a bayyane take sabi da ba na son wani ya ja ra'ayinki har ki kamu, na ji kin fara labari akan wani ɗan kasuwa fatana ba wata alaƙa a tsakanin ke da shi." "Ba wata alaƙa a tsakanina da kowane namiji ma ba iya shi ba, kawai dai ka tsargu ne mutumin ma da ban san shi ba ban san waye shi ba ba ni da tabbacin ma mutum ɗaya ne ko su na da yawa, anya kuwa ba wani dalilin? dan na yi magana akansu sai ya ɗaga hankalinka ka dawo gida?" "Matata Shukriya ba na son jin kalmar DOUBLE TWO STAR a bakin nan naki, da so samu ne indai ba Maalik bakin zai furta ba to ya yi shiru kawai. "Za ka ɓatawa kanka lokaci ne a banza, ko dai kaima ka na ɗaya daga cikin maƙiyansu?" "Uhm, ba lallai ki fahimta ba Shukriya ba ni kaɗai ba duk wani babban ɗan kasuwa dole zai tsani Double Two Star. "Kashhh! an samu matsala Maalik, ni kuwa Allah ya yi ni da mugun son yin hira akan wannan cibiyar kasuwancin, ka na Sona ni kuma ina son sanin labarai akan Double Two Star, indai sona ka ke da gaske wannan ma hanya ce wadda za ta bani damar fahimtar gaskiya da kuma matsayina a gurinka. fincikota ya yi ta faɗa kan ƙirjinsa ya matseta gami da cewa "Idan kuwa haka ne to ba za ki iya fahimtar komai anan ba face soyayyarki, kin ɗauka da wasa nake? Ƴan-mata gareni kamar yashi amma da yake ke Matata ce kin bambanta da sauran, na san ba'a son ranki ki kai wannan kwalliyar sabi da ni ba kuma kin yi fitaccen kyau sai na ji ba na son na yi nesa da ke ko da tazarar ƙafa ɗaya" tsaki ta doka ta na ƙoƙarin zame jikinta ta ce "Gaskiya ba ka da lafiya Maalik, sakeni in fita kafin Mahaifiyarka ta ce zan iskanta ka bayan kaine ɗan-iskan." murmushi ya yi gami da cewa "Ba inda za ki shiga ki tsere min a gidan nan har gaban Ammin zan biyoki." banza ta yi masa ta ci gaba da tafiya. Zaune suke a Falo suna taɓa hira kaɗan-kaɗan, Inna ce ta yi sallama Ma'arufa na biye da ita, zama ta yi gami da cewa "Baby me za ka ci?, ka tambayar min ƴan-uwanka dan ni ba

Chapter 2 of 30