Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
riga ta ce ta na son ayi, tin tana ganin za ta iya dena tunaninsa har ta gaji ta fara ɓarza kuka a cikin kukan Bacci me cike da mafarkai kala-kala ya samu nasarar sunkuceta. washe-gari da tunaninsa ta farka, duk jikinta ya gama mutuwa zuwa yanzu ta yarda wani sabon babi na ƙaddararta ya kuma buɗewa, ya za ta yi ta samu Number Safyan har ta ji muryarsa??, shine abin da ta sa a ranta kuma ta ke neman hanyar ido rufe. Cikin sanyin da ta yi ta ke tafiya Zuwa sashin Maalik, ya na zaune ya na aikin waya da ƴan-mata kamar yadda ya saba, ganinta ne ya sa ya ajiye wayar duk ya maida hankalinsa gareta cikin damuwa da damuwarta ya ce "Shukriya duk da na san ba lallai ki faɗa min gaskiya ba amma alamunki sun nuna ki na cikin damuwa, kuma in na ankara kamar daga jiya zuwa yau ne, ko kin gaji da zama da mu??" girgiza kai ta yi alamar "A'a" gami da ƙwaƙulo murmushin ƙarfin hali, "Maalik na ga yau ba ka neme ni ba ko na yi wani laifin ne?" "A'ah, ina tare da ke a cikin Zuciyata kuma idanun Zuciyata suna haska min ke hakan ya sa na barki ki huta dan nasan ba son ganina ki ke ba. "Uhm, Yaushe za ka koma UK??" "Sai bayan na Aureki" yadda ya yi maganar kai tsaye ne ya sa ta ƙara zuba masa ido, sai ka ce shine me yau da gobe da har yake wani sai ya aureta kai tsaye haka, ɗan murmushi ta yi gami da cewa "Me ku ka tattauna ne kai da abokin ka ya sunansa ma?" "Safyan Basiru Boza, kinsan dai mu maza magadan iyaye maza ne kuma ni da shi duk Iyayenmu ƴan-kasuwa ne kin ga kuwa bai wuce akan hakan ba. "Lamarin ya shafi Double Two Star ko??" "E, duk ƴan-kasuwar da su ka zauna hira ba su yi zancensu ba ai ba su cika ƴan-kasuwa ba, amma fa yadda ki ke tunani ba haka bane, ni bani da ra'ayin cutar da wani sabi da na buɗe WATA HANYA tawa ina da duk abin da nake buƙata ba abin da nake nema na rasa to bayan haka kuma me zai sa na yi ƙoƙarin daƙile wani? ai samu ya fi zubarwa me nema. Sosai Shukriya ta ji daɗin jin hakan daga gareshi yau rana ta farko da ta ji wani hali na shi ya burgeta, fatan ya ci gaba da hakan shi kawai ta yi a cikin ranta sai dai ba ta samu zuwa gaɓar da take buƙata ba dan kuwa so take ta samu hanyar da za ta nemi Safyan. "Shukriya me ya sa ki yawan tunani ne jiya zuwa yanzu?" "Ohh Maalik tunanin aikina kawai nake yi ban san labarin da zan bayar gobe ba. "To ki ba da Labarina mana?" Murmushin takaici ta yi ba tare da ta ƙara magana ba. miƙewa ya yi gami da cewa "Ina zuwa." Gyaɗa kai kawai ta yi, ya na fita ta ɗauki wayarsa cikin sa'a kuwa ba Key, contact ta shiga ta fara dubawa cikin sauri jikinta har rawa ya ke yi kafin ya dawo ta samu ta copy number ta na ajiyewa ya shigo, "Me ki ka ajiye a wayar tawa da za ki ɗauka?" ya jefo mata tambayar gami da kasheta da idanu. 08:06am Cike da kulawa Shahzain ya ce "Sannu Ƙarami ya jiki?" gyaɗa kai kawai Shahzaib ya yi ya na ƙara tsuke baki. Shahmeer ya ce "YaYa kar mu biyewa Ƙarami fa ka kira Maleeka ta duba shi tin da yaƙi zuwa Asibitin kuma ya ƙi a sanarwa Baba da Mommy." cikin zafin rai gami da zafin zazzaɓin jikinsa ya ce "Ku rasa wa za ku gaiyato min sai kwartuwar yarinyar nan? idan na ji motsinta a kusa da ni sai na zubar mata da haƙora." ya yi maganar cikin nuna tsantsar gaskiyarsa shaidar zai aikata abin da ya faɗa ɗin. cikin tausasawa Shahbeer ya ce "Kwantar da hankalinka ba me gaiyato maka ita amma Don Allah ka sha magan..." kafin Shahbeer ya gama faɗe ya rufe baki Shahzaib ya ce "Wallahi ba zan sha" cike da shagwaɓa irin ta mara lafiya ya yi maganar kamar zai fashe da kuka. Shahzain ya ce "Wanda in ba shi da lafiya ko ruwa ba ya sha sabi da ƙiyayyar magani ai kasan ba zai yarda ba." Shahbeer ya ce "Shi kenan to zan sanarwa Baba." bai jira abin da zai faɗa ba ya fice daga ɗakin. "Ni fa wallahi ba na son maganin nan a ƙyaleni zan warke" Ya faɗa tare da ƙara yin kicin- kicin Shahzain da Shahmeer ne su ka yi zaman lallaɓa shi har zuwa lokacin da Baba ya zo, ya fi yarda da Allura hakan ya sa Baba bainyi masa maganar magani ba. Cikin rawar baki irin mara gaskiya ta ce "Ba komai, am, kawai dai na ɗauka ne kuma dan na ma ɗauki wayarka laifi ne?" "Ba cewa na yi laifi ne ba tambaya kawai na yi amma dan mata ta ɗauki wayar mijinta ai ba laifi bane. tashi ta yi tare da cewa "Daga baya kenan, ni gurin Dada zan je kuma saura ka biyoni." "Cikin kwanakin nan ina yin ƙoƙarina don ganin na na gujewa Abin da ba kya so, ki je sai gani na gaba. ta yi murna da samun kuɓutar da ta yi cikin sauƙi ta na tafiya ta na murmushi, zama ta yi a gefen gado ta ƙarewar Lambar kallo murmushi me haɗi da ƙwalla ta yi, "Bai zamo lallai ka ɗauki magana ta a nutsuwa ba amma hakan ba zai sa na karaya ba zan jarraba sa'a ta" kamar ta tura kiran kamar kar ta tura Zuciyarta ke raya mata abubuwa iri-iri, daga baya ta yanke shawarar haƙura sai wani lokacin. Ma'arufa da Inna ne su ka shigo falon tararwa su ka yi Shahbeer ya na ta fama da Shahzaib akan ya sha ruwa amma ya tirje. Inna ta ce "Oo Allah buwayi gagara misali, wato lamarin iri sai addu'a shegiyar tirjiya ta yi muku yawa ƴa-ƴan nan." "Haba Baby ya za ki faɗi haka akan ɗan-uwana kuma ba shi da lafiya?" Shahmeer ya faɗa cikin haɗe rai, da sauri ta ce "Godewa Allah Baby ai ɗan-uwanka ya samu lafiya, yau kwana biyu kenan kuma jikinsa ya yi tangaras kawai ɗan sauran da ba a rasa bane, kuma da ya na shan ruwan ai da zai ji ƙwarin jikinsa." Shahbeer ne ya ce "Inna Do Allah ki ce ta ajiye tray ɗin nan ai sai ta gaji da yawa, ku bar zancen Ƙarami zai sha ma na sani" Inna ta ce "Mommyn ku ma fushi ta yi ta rabu da shi sabi da ya ƙi shan ruwan kai ma ka sa shi ya ƙi ka ga kuwa ai ba wanda zai iya, shi ga laulayi kamar mace da ciki inda Allah ya rufa mana asiri ma ba ya doguwar jinya da tuni rai ya yi halinsa." murmushi Shahzaib ya yi gami da cewa "YaYa Inna ta faɗi gaskiya, don Allah ka ƙyaleni." Malika ta ce "Duk wannan masifar ta shi da son girma ashe bai dena abin yara ba, in banda ƙuruciya ta ya za'a ce ba za'a sha ruwa ba bare magani to Allah ya sittira." "To mara kunya ban yi niyar Sha ba dan haka ba zan sha ba ba wanda ya isa ya sa ni na sha. miƙewa Shahbeer ya yi cikin ɓacin rai ya ce "Ranar da kasan ciwon kanka sai ka dinga sha, Inna bashi abinci idan kuma ba zai ci ba ki ƙyaleshi ni na gaji da magana, Malee, Jariri, Auta, ku biyo ni." ba musu su ka rufa masa baya, falon ya rage daga shi sai Ma'arufa da Inna, Inna ta ce "Za ka ci abincin ko wahalar da ni za ka yi?" kallonta ya yi ya kauda kai ko niyar yin magana bai yi ba. cikin ƙarfin hali Ma'arufa ta ce "Amma Yallaɓai ya kamata ka daure ka sha ruwan nan, duk da ban sani ba amma na lura Ya-Yanku ya na lallaɓa ku ya na kulawa da ku kuma ya na son abin da ku ke so, yanzu ka sa ya yi fushi gashi Mommy ma ta yi fushi ta ƙyaleka ɓata musu ran da ka yi dai-dai kenan yallaɓai?, Ba Don mu ba Don Allah ka yi haƙuri ka sha ko kaɗan ne." Inna ta ce "Ga yadda leɓensa ya bushe don Allah, wannan ai rashin sanin ciwon kai ne." "Inna ina shan juice da Tea su ma ai ruwa ne. murmushi ne ya suɓucewa Ma'arufa, ta yarda har yanzu akwai tarin ƙuruciya a tare da shi kuma dama ance ko'wane ɗan adam da kalar tashi ƙuruciyar, Cikin sassanyar murya ta ce "Ba lallai ka yarda ba Yallaɓai amma duk yawan abin da za ka sha indai ba farin ruwa bane to duk ba zai kashe maka ƙishi ba kawai zai ɗan rage wani abin ne bayan nan kuma dole da buƙatar ka sha ruwa, amma ka yi haƙuri da karam-banina na shiga maganar da ba tawa ba." Ɗan tsaki ya yi kafin ya ce "Na ji zan sha miƙo min ruwan." miƙa masa ta yi ya karɓa, sai da ya rintse idanu sannan ya iya shan ɗan kaɗan ya miƙo mata sauran. Inna ta ce "Ma'arufa me taurarin Sa'a kin sa wannan kafaffen ya yi abin da Ba wanda ya iya sa shi." "Inna Za ki ɓata min rai fa, ki yi abin da ya kawo ki kawai. da sauri ta ce "To ɗannan kasan bakin nawa ne akwai faɗi ba'a tambayeka ba, Ma'arufa temaka min da wani abin..." katse ta ya yi da cewa "Ba na so ta je kawai in ba za ki iya ba zan yi da kaina." Ma'arufa ta na jin haka ta yi hanyar fita, Inna ta ce "Ai kin yi ƙoƙari kedai Allah yai miki albarka." a cikin ranta ta amsa da "amin" bayan kwana bakwai. Shahzaib ya samu lafiya garau har sun ci gaba da gudanar da lamuransu kamar yadda su ka saba. _________ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ Jaririyar ELEGANT😊 *INDO..* [12/5, 10:44 AM] INDO CE: *WATA HANYA* 9 Ayeesha Abdulkareem *(Indo ce..)* MOONASH Alƙaluma Shida. Daga Ƙungiyar ELEGANT ONLINE WRITERS. SARƘAƘIYA Shaahd BANI DA HUJJA Maimoon BARRISTER SHAHEEDA Ayush AUREN ƘAUYE Nazlarh ZUMUNCIN ZAMANI Jikar Nashe WATA HANYA Indo Zaune suke suna hira cike da farin ciki Ba tare da wata damuwa ba, Inna ce ta ce "Hajiya A'i kin san wani abu kuwa?" Mommy ta ce "A'a sai kin faɗa Inna." Shahmeer ya yi saurin cewa "Inna ban da labarin da zai tashi kanmu fa, ina ganin kawai ki haƙura da hirar nan dan nasan tatsuniyar gizo ba ta wuce ƙoƙi." "Sai na faɗa" ta yi maganar gami da murguɗa baki. Mommy ta ce "Ko dai laifi ku ka yi ba kwa son na sani??, Inna ƙyaleshi ki faɗa min." gyara zama ta yi sannan ta ce "Ai abin farin ciki ne ba na baƙin ciki ba ka ga faɗensa ya zama dole, in gaya miki gaskiya ki fara shirin aurar da Ƙarami dan ya samu wadda yake so." yadda ta yi maganar a haƙiƙance ya sa har Shahbeer sai da ya dakata ya tsaya kallonta. Cikin hanzari Shahzaib ya tashi daga kwanciyar da ya yi ya zauna gami da cewa "Me???? kin fara shan wani abu ne??" Mommy ta yi dariya gami da cewa "Maida wuƙarka mana, bari Inna ta gama yi min bayani kar in je tsokanata ta ke yi murnar ta koma ciki." Inna ta ce "Da gaske nake Ma'arufar nan ya ke so wadda Zulai ta kawo ta gidannan aikatau, ko lokacin da bashi da lafiya ita ce ta sa shi ya sha ruwa kuma ya sha bayan famar da mu ka yi da shi." "Jan-bala-i Wallahi Mommy ko a wuya aka ɗaure min ita sai na kwance sai dai in a ƙafar gado za ku ɗaurata, haba Inna wai kuwa kin san wa ki ke nufi? Shahzaib ne fa ba Shahmeer ko Shahbeer ba dan nasan ko Auta ma ba zai yi wannan taɓarar ba, ki dinga gane mutane don Allah sai kin fi banbance abin da ke faruwa sannan ki zo ki ɗorar. Inna ta ce "A'a yo anya kuwa ba makuwa na yi ba? ko dai kaine Autan?? ku fa ba ku da kirki yanzu sai ku juye na kasa gane da wa nake magana." Mommy ta murmusa gami da cewa "Na ji daɗi matuƙa da faruwar hakan Inna, ba ki yi kuskure ba Shahzaib ɗin ne dai, ni fa shi yasa na ji ina son yarinyar." murmushi Shahbeer ya saki ya ce "Ƙarami ba abin mamaki ko abin gudu bane idan Allah ya rubuta sai Ka ga ta faru, ta na da nutsuwa sosai nima ta na burgeni ta fi Malee hankali." Shahzain ya ce "Ina haɗi tsakaninsu? ai Shegen faɗin rai shi ke sa Malika hauka, Amma dai gaskiya Arufa ta na da hankali amma YaYa ko dai ka faɗa ne??" ya yi maganar ya na kallon Shahbeer da murmushi ya gaza gushewa daga kan fuskarsa. Shahmeer ya ce "Zan faɗi gaskiya Mommy Shah....ne ya..k...ke..son..t.." Duka suka ware masa idanunsu cike da shakkar abin da zai faɗa, jin ya yi kwalo-kwalo ya ɓulle ya sa Shahbeer sauke ƴar ajiyar Zuciya sannan ya ce "Mommy ba lallai idan akwai tabbaci akan zancen nasu duka." Mommy ta ce "Na so a samu tabbacin nan amma duk da hakan ina fata na gari akanku." Shahzaib ya ce "Ku bar zancen nan haka kar ku sa na mutu dan takaici." Inna ta ce "ka mutun mana ina ruwan kallo da gajiya?, ni dai gaskiya na faɗa kuma ki ce ni na gaya miki." "Ai kuwa za mu gani" Shahzain ya faɗa tare da miƙewa don barin wajen. Zuciyarta ce take wani mugun tsalle bayan ta turawa Safyan kira, har ta kusa katsewa sannan ya ɗauka, sallama ta yi cikin rawar baki, a ɗaya ɓangaren ya amsa kafin ya ce "Da wa nake tare?" "Shukriya ƙanwar Maalik. cikin mamaki ya ce "Ƙanwar Maalik abokina? ki na lafiya? amma na yi mamakin ganin kiranki fa." murmushin yaƙe ta yi gami da cewa "A'ahh ai kira na yi domin mu gaisa kuma a gurin Maalik ɗin ma na samu lambarka. "Okay ya yi kyau ya Ammi ta na lafiya?." gyaɗa kai ta yi gami da cewa "E, ta na lafiya" ya ce "Ki gaishe min ita na san ba lallai Maalik ya na miƙa min gaisuwata ba." "Za ta ji, zan iya kiranka ko da yaushe mu dinga gaisawa??" shiru ya ɗan yi ya na nazari kafin ya ce "E mana haba ƙanwata sai ma kin tambayeni?? ai nima yayanki ne." murmushin farin ciki ta yi gami da cewa "Na gode Sosai, sai na ƙara kira." daga haka ta katse kiran cike da farin cikin ta samu dama ta farko. A ɓangaren Safyan ma mamaki sosai ya ke yi duk iya tunaninsa ya kasa gane dalilin kiran nata gareshi. "Fiddausi Tashi ki ci abincin nan kar ya huce, taliya ce Ma'arufa ta tawo mana da ita daga gidan aikinta shine na dafa" Umma ce ke maganar cikin tausasawa. Usman ya ce "Aunty Ma'arufa ta ce saura kwana biyu a bata kuɗin aikinta kinga sai ta siyo miki maganin da Likitar ta ce ko Umma?" Umma ta ce "Da zarar mun karɓi kuɗin burinmu shine mu nemi abincin da za mu kwana biyu ba mu nema ba sannan mu sayi sabulun wanka da na wanki kaga ko anan kuɗin sun ƙare bansan yadda za mu yi ba kuma, Allah dai ya baki lafiya Fiddausi." Cikin kuka Fiddausi ta ce "Ni duk rashin lafiyar ba ta damuna akan Babanmu, wai ina ya shiga Umma???" rausayar da kai Umma ta yi ta ce "Ba mu san duniyar da ya ke ba Fiddausi, ki manta da shi kawai kamar yadda ya manta da mu ba na so ki dinga tuno shi dan kuwa hakan zai sa ki a damuwa." Usman ya ce "Shi kenan Umma ba zai dawo ba? me yasa ya tafi ya barmu?, yaran unguwar nan fa ce mana suke gidanmu ba Uba" Share ƙwallar da take ta famar sharara daga idanunta ta yi ganin dukansu sun shiga damuwa ya sa ta yi ƙoƙarin danne ta-ta, "Banda abinka Usman wa yake biyewa Surutun mutane?, kar ku damu in Allah ya yarda wata rana sai ku ga ya dawo garemu, Fiddausi tashi ki ci abincin nan za ki fi jin daɗin jikinki dama Likita ta ce akwai rashin cin abinci." Umma ta ce "Tohh, ba sai da shi ba za'a cin?" "Haka ne Umma, ni bari na ɗan shiga maƙota, ina zuwa" Ma'arufa ta faɗa tare da miƙewa ta zari hijab ɗinta. Alhaji Basiru Boza ne zaune kan wata hamshaƙiyar kujera ya kwantar da kansa a jikin makarin kujerar, Mom ce ta shigo tare da sallama, ƙasa-ƙasa ya amsa ta nemawa kanta mazauni sannan ta ce "Tunanin ne har yanzu ka kasa denawa?, na gaya maka indai akan kasuwan-cinka ne ka na da magaji dan Safyan ba abin da ba zai maka ba ka ga Ko Zakiyyat ma za ta iya riƙe maka wani abin don itama ba ta da maraba da irin halinka." girgiza kai ya yi kafin ya ce "Nasan ina da Safyan to amma akwai abin da na rasa, akwai tunanin da na ke yi wanda ba wannan ba na rasa ta inda zan fara shawo kan matsalata." "Kai ka jiyo dan wannan sa kai a uku ne, ni dai yanzu maganata ba ta wuce akan abin da ya shafi ƴa-ƴana dan haka Safyan zai yi maka bayanin abin da suka shirya. daga haka ta fice daga ɗan madai-daicin falon wanda aka tanadeshi a keɓance. ta na fita Sa'ad ya shigo ko zama bai yi ba ya ce "Zan je Germany Dad." ba tare da ya kalleshi ba ya ce "Duk abin da ka ke so ka nemi Safyan ni ka barni da abin da ya dameni gwara ma ka tafi dan ba amfani gareka anan ba." murmushin takaici Sa'ad ya yi sannan ya ce "Ko na tafi ba hakan ya na nufin haƙarka zai cimma ruwa ba Daddy, nima gajiya na yi da irin hali da ɗaɓi'ar Ahalinka na kasa jurar ganin wata banzar rayuwa da ake yi a tsakan-kaninmu, Dad ba za ka taɓa kaiwa gacci ba a rayuwarka domin kuwa ka riga ka ƙirƙiri makamin da zai tarwatsaka, ban san adadin mutanen da ka cutar ba amma ina jin hakan ya zo ƙarshe daga kan wasu ba za ka kuma ba." miƙewa Alhaji Boza ya yi cikin mamakin abin da ke futowa daga bakin ɗan nasa, takawa ya shiga yi a hankaki ya na jinjina kai, "Ina tantama akanka Sa'ad anya kuwa kai jinin Basiru da Habiba ne?? ba haka halayyar jinina ta ke ba, wai gashi ka buɗe ido ka na sharara min maganganu na son ranka magana mara daɗi Sa'ad Ni?? Ni??? Ni??" ya faɗa gami da nuna ƙirjinsa cikin tsananin mamaki yake maganar gami da shakku akan kalaman Sa'ad, "Daddy da ka so Kyakkyawar rayuwa me cike da nasarori da ba ka bi WATA HANYA mara kyau don cika burinka ba, ba shakka a kalamaina ba na zubarwa dole akwai ranar nadama. Cikin hargagi Safyan da ya tsaya ya na saurarensu ya ƙaraso ya na cewa "Kai wane irin dabba ne za ka dinga gayawa mahaifinka maganar banza sabi da wasu ƴan iska a gari !!." "Ni fa Dolena ne na gaya muku gaskiya kuma na nuna muku kyakkyawar hanya har zuwa lokacin da za ku gane abin da nake nufi, kar ka ƙara kirana dabba dan hakan zai fusatani. "In ba dabban ba to menene?? Ka ƙara yi min magana anan sai na yi ƙasa-ƙasa da kai shashasha kawai." "Da bakina ba za ka hanani magana ba ba uban da ya isa, Kuma na faɗa sai wannan rayuwar taku ta tarwatse dan ƙarya ba ta yin nasara akan gaskiya.." fassssa Safyan ya bashi wani kyakkyawan mari me zafin gaske, sai da ya ga wasu ƴan taurari su na yi masa maraba na ɗan wani lokaci kafin nutsuwarsa ta dawo, cikin rawar murya me cike da baƙin ciki ya ce "Ba zan rama ba amma ka sani Akwai ranar ƙin dillanci, kuma na ji zafi sosai amma kai zafin da za ka ji sai ya ninninka wanda ka sa na ji, ka bani kuɗi zan tafi Germany." "Kai mahaukaci ne ina magana ka na mayar min martani??? sai yaushe za ka san inda ke maka ciwo ne?? Germany gidan ubanka ne??" "Kai ma ba na ubank bane ai ka ga ina da damar da zan je na yi abin da nake so." Hanƙoro Safyan ya ƙara yi zai hau kan Sa'ad da duka Alhaji Boza ya yi saurin shiga tsakaninsu, cikin fitar haiyacin da ya fara yi ya ce "Kar ku yi haka duk da akwai banbancin hali a tsakaninku amma ina so naga kun haɗa kanku, ku dena sa-in-sa ku dena hargowa wa junanku, Safyan Ka barshi ya tafi kaima kanka za ka fi jin daɗi." "Alawadaran naka ya lalace" Sa'ad ya faɗa gami da yin hanyar fita. da harara Safyan ya raka shi jiki na rawa sabi d ɓacin rai, tsaki ya doka ya ce "Da ka barni na tubirbiɗa shi dan ubanshi." "A'a Safyan hakan ba riba, yaron nan ya fi mu gaskiya ka da mu yawaita matsanta masa hakan zai iya jawo mana wata matsalar dan kuwa kyakkyawar Zuciya gareshi kuma Allah ba ya son a dinga cutar da irinsu. Safyan ya ce "Ni ina ruwana? kawai abin da na sa gaba shi na ke yi ba wanda ya is ya hanani ya na ɗan ƙarami da shi sai Zuciya irin ta jaraba anya kuwa ba ɗan Ahalin Su Shahbeer bane??" "Dena wannan maganar Safyan, zauna ka gaya min abin da Mom ɗinki ta ce za ka gaya min. zama ya yi ya ci gaba da mita Alhaji Boza sai haƙur-ƙurtar da shi yake har ya samu ya dena ya bashi labarin tsarin nasu. Shahzaib ne a kusa da ƙafafun Mommy Shahzain kuwa kwanciya ya yi ya tada kai da cinyarta Shahmeer ya na gefenta na dama Shahbeer kuma ya na kusa da Shahmeer hira suke yi sosai amma ban da Shahbeer da ya ke ta wasu tunane-tunane har da marasa kan gado da waɗanda bai taɓa karo da su a rayuwarsa ta zahiri ba amma yau ya ji Zuciyarsa ta na raya masa labarin kamar a mafarki kamar abin da ya faru a baya. wayar Shahzain ce ta yi ƙara ya ɗaga gami da sa handsfree, Sallama aka yi a ɗaya ɓangaren Shahzain ya amsa "Yallaɓai Shahbeer ni ne Salman Audu me kula da shige da ficen motocin Tirela ɗinku, Yallaɓai ina kan layin bibiyar direba wanda aka bashi

Chapter 5 of 30