bala'in da ba za ki iya da shi ba, tin da ke ki ke goyon bayansa ya ke yiwa ƴaƴan mutane abin da ya so." cikin mamaki Mommy ta ce "Baiwar Allah ban fahimta ba, ni da ko saninki ban yi ba?"
"Ai nasan ba ki sanni ba amma ni ta sanadin ɗanki na sanki, acan bayanku mu ke da zama, jiya yaron nan ya kama ɗana ya yi masa shegen duka a yanzu haka ya na can a kwance zazzaɓi ya ke yi, to wallahi ba zai yuwu ba dole ne ki ɗau mataki ko mu mu ɗauka da kanmu, yanzu yaran Unguwar nan gaba ɗaya sun maida shi kamar wani Sarki sai abin da ya ce su yi su ke yi, duk wanda ya yi masa ba daidai ba kuma ya doke shi ko ya sa yara su dake shi."
Cikin mamaki Mommy ta ke kallonsu, ta rasa ko wa ake nufi don kuwa ba ta tunanin akwai wanda zai iya zama shugaba a cikinsu. Kallonta ta mayar kan matar tare da cewa "Wanene daga cikinsu?" "Ƴaƴan naki masu kama ɗaya ni zan iya bambance miki ne??, idan ba yanzu ba ma waye ya san ƴan-huɗu ne?"
Mommy ta ƙare musu kallo kafin ta riƙo hannun Shahzaib cikin ɓacin rai ta ce "Kai ne me Zuciya nasan ba me yi sai kai."
miƙewa Shahbeer ya yi ya matsa kusa da matar a dake ya ce , "Ɗanki ya cewa ƴan-uwana Babanmu ya na dukan Mommy ni kuma ba zan iya ƙyaleshi ba shi ya sa na yi masa magana kuma ya yi mini rashin kunya shi ne na doke shi, ba na iya saurarawa duk wanda ya taɓa ƴan-uwana ko ni ko iyayena, ki gaya masa ya yi ladabi sai ya zauna lafiya." ya na kaiwa nan ya yi hanyar ƙofar gida.
Kallon kallo su ka shiga yi su duka Biyar ɗin, har su Shahmeer mamaki su ke yi bare Mommy da ta ke zaune a gida kullum. Mommy ta ce "Ki yi haƙuri baiwar Allah, ina ga ɗan nan nawa Aljanu gareshi, wallahi ban san ya na da irin wannan halin ba, ina ga ba shi kaɗai bane.
matar ta tashi tare da cewa "Allah i sauwaƙe." daga haka ta fice domin kuwa tsoron Shahbeer ya kamata, ba ta taɓa ganin ƙaramin yaro me tsaurin hali irinsa Ido-da-Ido ba.
A makaranta, Kamal shine shugaban tawagar fitinannun yara kuma marasa kunya duk wani iya shege da za su shuka shine Shugaba, kullum ya na harin shiga gonar su Shahbeer amma ya na shakka sai rana ɗaya tsautsayi ya sa shi ya sa yara su ka dinga yi musu ihu harda jifansu. Har su ka dawo gida bai ce komai ba haka aka kwana aka hantse, babu wanda ya san abin ya ɓata masa rai, Shahzaib kuwa sai mita ya ke yi.
Washe-gari, Kamal da ya ke ya ɓula ya ga jini bai haƙura ba haka ya ƙara shiga gabansa ya farfaɗa musu baƙaƙen magan-ganu masu ɗaci, har da kafa musu wasu ƴan dokokinsa kuma ya ce idan su ka tsallake sai ya sa yaransa sun yanka su.
A kwana na uku ne asalin ƙaddarar Kamal ta baiyana, Shahzaib ya na ƙetara dokokinsa ya tattaro yara ya sa su ka fara dukan Shahzaib, ganin Shahbeer ya na doso gurin ya sa shi dakatar da su sannan ya zaro Aska cikin Aljihunsa wadda ya ke yawo da ita ya na yiwa yara barazana, ya na shirin yankar Shahzaib, Shahbeer ya jefe shi da dutse kafin ya murmure ya ƙaraso wajen kawai ya hau shi da duka kuma ya ƙwace wuƙar su ka fara casuwa, Kamal ya na da cika baki da kuri shi yasa bakinsa ya ƙi mutuwa, hakan kuma ƙara tunzura Zuciyar Shahbeer ya ke kawai ya buɗe Askar ya kekketa masa mazaunai, dandanan jini ya fara zuba Kamal ya fara kuka yaran kusa da su kuwa duk su ka firgita su ka yi baya, wasu kuma jiki na rawa su ka je su ka sanar.
Anyi ɗauki ba daɗi da iyayen Kamal haka ma Malaman Makaranta duk sun ce ba za su yarda ba, Dr Idris ne ya ɗauki nauyin komai a hannunsa shine ya yi duk yadda zai yi aka daidaita.
Tin daga wannan lokacin Kamal da Shahbeer su ka zama Abokan Dabi.
haka rayuwa ta ke tafiya cikin wannan halin Alhaji Basiru ne kawai ya ke iya wa Shahbeer don kuwa ba fasa gana musu Azaba ya yi ba, daga baya kuma sai ya dena zuwa gidan sai tashi ta kawo shi zai zo wajen A'i. a lokacin kuɗi sun zauna masa ta ko'ina ya canja rayuwarsa ya watsar da kowa, iyayensa da kuma iyalinsa dama su ba ƙaunar su ya ke ba.
yau su na zaune da daddare ya shigo fakatan-fakatan, tin daga soro ya ke kiran "A'i!! A'i!!!!" cikin sanyi ta miƙe tare da cewa "Gani nan." "Ki na cikin mayun yaran nan ko?? shegu da fararen fuskoki kamar na Aljanu, ai dama nasan mayu za ki haifa wallahi, yanzu gashi ya je ya kama yaron jama'a ya yi masa duka hatsabibin shaiɗanin can, kin ganni daga ofishin ƴan-sanda nake, amma inda na godewa Allah dama daga yau ba zan ƙara zuwa inda ku ke ba, na gode da ki ka temaka mini na yi kuɗi dama don na yi kuɗi na Aure ki kuma na yi don haka zan barki sai ki ci gaba da rainon jarababbun mayun can, ni yanzu Aurena da wadda na ke so ya kusa saura sati ɗaya."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Yanzu Basiru ko kunyar faɗe ba ka ji ba ka ke cewa za ka tafi ka barni da yaran nan?? waye zai bamu ci da sha har ya tufatar da mu??" "Ai ki na da kwartonki wannan likitan, ni dama ai ban taɓa baki Abincin da za ki ci ke da ƴaƴan nan ba kuma ni ban taɓa yi musu tufafi ba don haka in na tafi ma ba abin da zai rage ku, sai ki ci gaba da karuwancin ana ba ki Abinci."
daga haka ya yi ficewarsa.
Durƙushewa ta yi ta fashe da kuka me tsuma.
duk su ukun kuka su ka fara yi Shahbeer kuwa sai dai na Zuci.
sai da ta gaji da kukan don kanta sannan ta rarrashi kanta ta koma kusa da yaranta lokacin Shahmeer da Shahzain har sun yi bacci.
Shahzaib ya ce "Mommy wai me yasa kowa ya tsanemu??" ta ce "A'a ba tsanarku aka yi ba, ku dai ku yi haƙuri da duk halin da ku ka tsinci kanku, Allah shi ke son ganinmu a haka lokacin da ya so kuma zai fitar da mu daga cikin ƙunci."
Shahbeer ya ce "Umma ni na tsani wan can mutumin." a ɗan razane ta kalleshi tare da cewa "Me?? waye???" ya ce "Wanda ya fita yanzu, Azzalumi ne kuma na tsane shi ba na son ganinshi gwara da ya tafi ku dena kuka ma, sai mun fi farin ciki idan ba ya nan." Shahzaib ya ce "Nima na tsane shi wallahi." kasa magana Mommy ta yi sai dai kallo kawai ta ke binsu da shi.
Cikin ƴan tsirarun shekarunsa ya fara sana'a don burinsa a rayuwa bai wuce ya ga ya tsaya wa Mahaifiyarsa ba, Dr Idris ne ya gaya masa sai ya yi hankali kuma ya fara sana'a sannan zai iya yi musu komai don haka ya sa a ransa zai yi sana'a ko ƴar ƙarama ce.
Yau bayan an dawo daga Masallacin Jumu'at ya je kantin Layinsu da ya ke babban kanti ne akwai kaya da yawa.
Me kantin ya na murmushi ya ce "Shu... Shugaba ne da kansa yau a gurinmu??"
ya gyaɗa kai, Malam Ashiru ya ce "To Shugaba me za'a baka??" kai tsaye ya ce "Sana'a na ke so na fara yi sabi da na dinga saya mana Abinci ina temakawa Mamarmu." Malam Ashiru ya fito daga cikin kantin ya zauna kan kujerar da ke gurin don ya fi fahimtar inda ya dosa, cikin mamaki ya ce "Sana'a za ka yi fa ka ce??" "E, kuma ba ni da kuɗi ka temaka mini ka bani Alewa sai in dinga sayarwa in kawo maka kuɗin ribar kuma sai in riƙe. Malam Ashir ya yi dariya tare da cewa "Shugaba wayo za kai mini??" ya girgiza kai alamar a'a sannan ya ce "Da gaske na ke, na yi maka Alƙawarin ba zan yi maka wasa ba." Malam Ashir ya rausayar da kai kafin ya ce "To, Ba'a ƙwacewa yaro garma, amma gaskiya ta Hamsin zan baka sai in baka ta goma a matsayin riba."
_________
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
*INDO*
[1/9, 9:06 AM] INDO CE: *WATA HANYA*
37
Ayeesha Abdulkareem
*(Indo ce..)*
ELEGANT ONLINE WRITERS.
Gyaɗa kai ya yi ba tare da ya ce komai ba, Malam Ashir ya lissafa masa Alewar sannan ya bishi da fatan Alkairi.
Mommy na zaune ta zuba tagumi gidan shiru ba wata hayaniya, Sallama ya yi cikin nuna farin ciki ya ce "Mommy kin ga na saro Alewa." dariya ta yi kafin ta ce "Ka na da zumna Shahbeer Allah ya bada Nasara, amma ban san ta yadda sana'a za ta yuwu da hakan ba." wucewa ya yi ɗaki tare da cewa "Ni zan iya kayata." ta ce "To Allah i taya maka, ai ni ina son hakan don ya fi ka je ka ɗauki na wani." Shahzaib ya ce "Inya in zo ka bani Ɗaya?" ya ce "Kai bari sai na fara saya da kuɗina tukunna idan na tara, ai yanzu idan na baka kuɗin Malam Ashir zai ragu." Mommy ta ce "Gaskiya kuwa, ka adanata sosai ka ji? kuma kai ma kar ka sha, ka zama me Amana da cika Alƙawari, kamar yadda ya baka ka mayar masa da kuɗinsa haka." ya ce "To Mommy."
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya. da ya ke Shahbeer ya na da farin jini dandanan yara su ka fara sayen Alewar a gurinsa da ya karɓo da ta ƙare, ribar da Malam Ashir ya ke ɗora masa akai sai ya Adana har sai da ya tara kuɗin da zai iya sayan jakarta ɗaya, da haka ya ci gaba da yi kuma Allah ya yi wa sana'ar tashi albarka, tin ya na yi da kaɗan ya na juyawa har su ka fara yawa shima ya na ƙara tasawa ya na ƙara wayo da dubara.
Duniya me ya yi da haka aka zo zamanin da ba iya Alewa ba duk wasu tarkacen yara har ma da wanda manyan ke saya a gurinsa ake nema, kafin mutum ya je kanti ya nema a gurinsa, hakan ya na yiwa wasu daɗi wasu kuwa baƙin ciki su ke ji.
Sun fuskanci ƙalu-bale kala-kala a rayuwarsu tin daga kan baƙin cikin Mahaifinsu har na Mutane, sai su ka zama tsarar manya ba ma iya yara ne ke musu baƙin ciki da hassada ba, wasu sukan goranta musu akan halin Mahaifinsu wasu ma su ce shegu ne wasu kuma sukanyi wani abin daban don su ƙuntata musu.
Lokacin da su ka kai Shekaru shabiyar zuwa sama a lokacin rayuwarsu ta ƙara canjawa su ka ƙara shiga gwagwarmayar Rayuwa ba sa karaya bare su gaza, a koda yaushe ta fannin kasuwancinsu ba ya baya sai dai gaba kafin wani motsin cikin ikon Allah su ka zama asalin ƴan-kasuwa.
akan hakan su ka taso har girmansu, lokacin rayuwa ta yi musu sanyi domin kuwa Allah ya kai su gaɓar da sai dai su kwanta su huta, su ne masu temakon wasu su ne masu sanya sauƙi cikin Kasuwancinsu domin na ƙasa da su su ji daɗi, su ne wanda da temakonsu wasu masu kuɗin su ke kaiwa gacci, su ne waɗanda sunansu ya buwayi wasu saƙo da lokon na Duniya.
Sai a wannan lokacin Alhaji Basiru Boza ya fara tunaninsu, ba dan komai ba sai dan sun kere kafaɗarsa sai kuma ya koma wanda ya fi kowa son ya ga ya kassara su sai dai Allah ya riga ya Amince musu, duk wata suka ko mugunta ta mutane ba abin da ta ke rage musu tamkar ma ƙarin taki ne garesu.
Shiru Falon Mommyn ya yi har lokaci me tsaye sannan ta miƙe tare da cewa "Zan koma ciki, don Allah ki yi ƙoƙarin haɗa zumunci tsakanin ƴaƴanmu ba wai ki farraƙa su ba, dolen-dole dole ce tin da jininsu ɗaya." murmushi me tafi da hawaye ta yi gami da cewa "Allah sarkin Kyauta, Ni ce na sha wahalar ƴaƴana tin daga kan goyon cikinsu har bayan haihuwarsu har girmansu amma ba su yi kama da ni ba gaba ɗaya Mahaifinsu su ka kwaso, Ramadan da Sa'ad ma haka."
ta na kaiwa nan ta ci gaba da tafiya, Ramadan ya ce "Mommy don Allah ina zan ga Mahaifina?" "Ƴan-uwanka za ka tambaya." ta na bashi amsa ta yi ciki.
zazzafar iska ya furzar gami da buga tagumi. Ummansa kuwa in banda ido ba abin da ta ke zazzarewa, sun ɗan ɗebi lokaci a haka kafin Ramadan ya ciro waya ya kira Shahbeer,, cikin sanyi ya ce "Shahbeer, ina son haɗuwa da Babanmu." "Ka nemi su Shahmeer ni yanzu ba ni da lokacin hakan" ya faɗa a ƙagauce. da sauri Ramadan ya ce "Ni fa ba ni da Lambarsu taka kaɗai na ke da." ya ce "Ai ba su bar gidan ba sai ka nemesu, ni kar ka ɗaga mini Karagar Rayuwa ka san dai Matata ba ta da lafiya kuma yanzu ina tare da ita, ina ganin idan kun gama abin da ku ke yi ya kamata ku ɗaware ku bamu guri iska ta shigo gidan."
ya na gama faɗen haka ya katse kiran. Ramadan ya bi wayar da kallo, wata muguwar karaya Zuciyarsa ta yi lokaci ɗaya wahaye su ka shiga gudu akan fuskarsa, Sai a Lokacin Mamansa ta iya yin magana cikin sanyin jiki "Ramadan, kukan me ka ke yi?, ai mu sai mu godewa Allah domin kuwa tamu ƙaddarar me sauƙi ce.
ya ce "Mama ya akai duk ba ki yi tunanin nan ba da sai yanzu da ki ka riga ki ka raunata zumuncinmu?, wai ni kam ko da cutar da ke aka yi me yasa ba za ki yafe ba sai ki ce sai kin rama?, yanzu gashi ba'a yi miki komai ba kinsa na zalumci har waɗanda bai kamata ba." kuka ta fara yi ta na cewa "Sai haƙuri Ramadan nima ban yi tunanin hakan ba kwata-kwata, na yi dana-sanin aikata hakan; nima sai na ji dama na raineka ta irin hanyar da A'i ta raini ƴaƴanta, amma ni ban koya maka sana'a ba sai dai ɗaukar kayan wani, kaicona ni Furaira." ta ƙarasa maganar ta na kuka, shiru ya yi mata don kuwa ba shi da abin ce mata.
Su na cikin haka Alhaji Boza tare da Sa'ad su ka yi sallama, cikin sauri su Ramadan su ka miƙe tare da zuba musu ido.
Alhaji Basiru ya ƙaraso ya na kallon Ɗansa, Sa'ad ya gaida Maman Ramadan ta amsa da kyar sabi da kukan da ta ke yi. cikin rawar murya Alhaji Boza ya ce "Ramadan!!" Fashewa ya yi da kuka ya na cewa "Baba!!! Baba me yasa ka banzatar da rayuwarmu, abin da ka yiwa ƙannena har ya girmi wanda ka yi mini, kaine silar komai, kun ja mini sanadin da na cutar da ƴan-uwana, Baba me ya sa ka ke da son Zuciya?" cikin kuka ya ce "Tabbas na yi aikin nadama Ramadan, na gane kuskurena kuma ba zan ƙara aikata shi ba, don Allah ku yafe mini." rungume shi ya yi ya na murmushi ya ce "Baba mun yafe maka mu ma Allah i yafe mana." Alhaji Boza ya yi murmushi cike da ƙaunar ɗan nasa.
Malam Sa'ad ka tsaya kallonsu ka yo ciki mana."
Shahbeer ya faɗa lokacin da ya ke sakkowa daga sama.
Sa'ad ya ɗan murmusa gami da cewa "Na tsaya kallon me kama da ku ne?" ya yi dariya ya ce "Ai iri ba ya ƙarya kaima ai ka yi kama da shi." Ramadan ya ce "Baba wai dama ka san mun zo??" ya ce "Shahbeer ne ya kirani tin ɗazu." murmushi ya yi kafin ya ce "Baba don Allah ka taya ni neman yafiyar su Shahbeer.'' Shahbeer ya ce "Laa mene hakan? ai mu mun yafe maka tin ba yau ba ma, mene amfanin ƙin yafiyar? ai babu don haka ka kwantar da hankalinka, nemi guri ka zauna bari in sa Ma'arufa da Inna su kawo muku Abinci." zaman ya yi tare da cewa "Na gode Ɗan-uwana."
su na cin Abincin su na hira su duka har Mommy. sai dare sannan su Ramadan su ka bar gidan.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya daidai. Kullum sai Ramadan ya zo gidan sun sha hira.
Shahbeer ya na zaune Shahzad ya na taya shi surutu wayarsa ta yi ƙara, ɗauka ya yi ba tare da ya duba kowaye ba, cikin kuka ta ce "Ya Shahbeer ni ce ƙanwarka Zakiyya." da sauri ya ce "Ki na lafiya Zakiyya? ki yi haƙuri fa ba na cikin yanayi me daɗi ne shi yasa ki ka ji ni shiru, kinsan Malika ba ta da lafiya gashi lokacin mu ka rasa Halima, amma meke faruwa na ji kina kuka?" "Yaa Shahbeer don Allah ka temaka mini wallahi Maalik wahalar da ni ya ke yi, don Allah ka yi masa faɗa ya dena." ''Kai jama'a Maalik anyi mara mutunci amma; barni da shi zan zo kar ki damu. ''To YaYa" ta faɗa kafin ta katse kiran.
tashi ya yi ya na cewa "Shahzad ya na ina??" leƙowa ya yi ta bayan kujera ya na dariya ya ce "Baba gashi nan." ya ce "Ya je gurin Ummi Ma'arufa ko Inna, Baba kam fita zai yi." ya noƙe kafaɗa ya ce "A'a Mama Shukriya zai je." dariya Shahbeer ya yi tare da cewa "Ku ji ɗa kamar ya san tare da ita zan fita, Shahzad ya je gurin matarsa to, ya je gurin Mommy gaskiya."
gaba ya yi ya na cewa "To ya tafi." bin bayansa ya yi ya ɗaukeshi sannan su ka nufi sashin Mommy, ya na fitowa ya nufi sashin su Shukriya ya yi sallama ta amsa ta fito ta na fara'a ta ce "Ya Shahbeer shigo mana." ya ce "Gafarceni Shukriya ina son mu fita ne yanzun nan." gwalalo masa idanu ta yi gami da cewa "Mu je ina??" ya ce "Ko na san inda ake sayar da mutane dai ke kinsan ba siyuwa za ki yi ba sabi da surutunki." "To Ya Shahbeer ai na ga tafiyar ne kamar ta gaggawa, kar Autanka ya yi mini faɗa. "Na riga na sanar da shi, ai ba zan ce ki fita ba tare da Amincewarsa ba.
murna ta fara yi ta na dariya gami da cewa "Dama tin da na shigo gidan nan ban fita ba, gaskiya na ji daɗi."
ciki ta koma ta shirya ba ɓata lokaci ta fito su ka ɗau hanya.
bubbuga gidan ya yi aka yi sa'a ya buɗe cikin sauƙi don kuwa ya zo fita ne su ka fara bugawa, ganin Shahbeer ya sa shi haɗe fuska a fusace ya ce "Menene ya kawo ka gidana? faɗa mini mana!!!!" "Kar ka manta gidan ƙanwata ne kuma ita na zo gani, kai tsaye ma zan iya cewa na kawo maka taka ƙanwar nima ka bani tawa. sololo ya yi ya na kallonsa kafin ya ce ''Ban gane ba fa." Mari Shahbeer ya kifa masa kafin ya ce "Yanzu ka gane ko sai na ƙara maka??, sakaran banza da wofi, kai ba ka san yarda da ƙaddara ba? ko an gaya maka dole sai abin da ka so ka ke samu?? to ita rayuwa ba haka ta ke ba, Wani abin in ka so shi haka nan za ka haƙura ka barwa wani, kai jin kanka ka ce ƴar-uwarka ce Shukriyan to ai nima ƙanwata ce ta jini." "Taya??, wannan ai rainin hankali ne ka shigo gidana ka mareni sannan ka na gaya mini wasu zantuka na banza ku da ko asali ba ku da shi??" "Asalin Mahaifiyarka shine asalin Mahaifiyata hasalima Hannetu Mahaifiyarka ita ce silar rabuwar Mahaifiyata da danginta akan son Babanmu, idan kuma ka na shakka ka je ka tambayeta. cikin zaro ido Maalik ya ce "Me kenan?? ka na nufin Mahaifiyarka dangin Mahaifiyata ce??" "Ko shakka babu; ita Mommy ta ganeta amma ita ba ta gane Mommyn ba, kuma na yi bincike na gane hakan, ɗan wa da ɗan ƙani su ke ita da Dada, kuma Mahaifin Dadan ne ya hana Mommy komawa cikin danginta, ka ga kuwa Shukriya ƙanwata ce, amma ni yanzu ba wannan ba fito mini da ƙanwata ka karɓi taka ai Aure ba ya na nufin cin zarafi da mutunci ba, ga Shukriya nan sai ka kwaɗanta ka cinye, idan ma sakinta ku ke so ya yi cikin sauƙi zai saketa.
da sauri Shukriya ta zagayo gabansa ta ce "Kam bala'i wallahi ban yarda ba, ku kaishi kotu ku ce ya na zalumtar ƙanwarku amma ni ban yarda a raba mini Aure ba ." Shahbeer ya ce "Dama ai sai kin Amince yanzu kuma dolenki ki zauna a gurin danginki har sai sun san ina ke musu ciwo tukunna."
ya na kaiwa nan ya yi cikin gidan Maalik ya raka shi da ido, mamaki ya ƙamar da shi a gurin sai ido kawai ya kalli Shukriya ya Kalli Shahbeer.
_________
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 25 Chapter of 30