Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ce ku zo." "Okay beauty Kalar kyau" Shahzain ya faɗa fuskarsa ɗauke da murmushi, "Ƴan-Duniya hayaƙin taba" Inna da ta shigo yanzu ta faɗa gami da neman guri ta tsaya. dariya su ka yi kafin Shahzaib ya ce "Inna mu na zuwa ba sai an zo an sa mu gaba kamar za'a cinye ba." ƙasa Ma'arufa ta yi da kai don kuwa ta tabbatar da ita ya ke. Inna ta ce "To ɗannan ku tashi Baba ne ya zo kuma jiranku ya ke yi Hali Dubu ce ba lafiya. Zumbur Shahbeer ya miƙe ba tare da ya sani ba, "Halima??" "E mana ba ta da lafiya" Inna ta bashi amsa. bai jira sauran ba ya nufi ɓanfaren Mommy cikin sauri, kusa da Baban ya zauna gami da gaishe shi a fizge ya na son yin tambaya akanta amma sai ya haƙura. Baba ya ce ''Da sauri haka Ɗana na ɗauka sai kun gama ja min aji za ku zo?" ya yi maganar cikin sigar zolaya. murmushin ƙarfin Hali kawai Shahbeer ya yi, Baba ya ce "Halimatu ba lafiya Shine Hajiya A'i ta sanar min na iso, to na dubata babu komai In sha Allah yanayin lauyi ne sabi da cikin jikinta." Cikin kaɗuwa Shahbeer ya ce "Ciki Baba????" "Ƙwarai kuwa wata ɗaya da kwanaki ina tunanin lokacin da ka haɗu da ita ne ma don yanayin lissafi hakan ya nuna." Ido Ya tsirawa Halima da ke kusa da Mommy ta na ƴan wasanninta hankali kwance, wani mugun abu ne ya tokare masa maƙoshi ga wata irin karyewa da Zuciyarsa ta yi. Baba ya kalli Mommy gami da cewa "Yanzu kulawar da ake bata kamata ya yi ta ninka ta da don kuwa ita ba a hayyacinta ta ke ba dole ku ne masu kula da ita, don Allah kar ku barta ta yi abin da zai kawo mata matsala." cikin ƙarfin hali Mommy ta ce "In Allah ya yarda za mu kula da ita sosai da sosai, Allah ya raba su lafiya." "Amin summa Amin" Baba ya amsa kafin ya ci gaba da cewa "Shahzaib ba kwa cigiyar Ƙanwarku abokiyar rigima?'' Shahzaib ya ɗan murmusa gami da cewa "Ace dai ina gaida Mammi amma banda Malika gaskiya." Baba ya yi murmushi gami da miƙewa ya ce "Shi kenan za ta ji zan cewa Malika ba kwa cigiyarta ta zo ban haƙuri." da sauri Shahzain ya ce "Kai! ƙyaleta Baba rikicinta yawa gareshi ace dai ni da Jariri (Shahmeer) muna gaisheta." "Zan gaya mata, sai anjima." Miƙewa su ka yi Shahzain ya ce "Bari mu taka maka Baba." bin bayansa su ka yi domin raka shi mota. Cikin kuka Mommy ta ce "Duk da bansan ko cikin waye ba amma jikina ya na bani zai zamo silar rasuwar farin ciki a gidannan Shahbeer." sai lokacin ya sauke idonsa daga kan Halima, cikin ko-in-kula ya ce "Mamma ni tin ba yau ba na riga na rasa nawa farin cikin yanzu ba sauran komai." ya na kaiwa nan ya miƙe ya nufi sashinsu. Kuka Sosai Mommy ta ke yi Inna da Ma'arufa suna ta ƙoƙarin Rarrashinta. zagaye ƴar barandar dake sama ya ke yi hannayensa goye a bayansa, "Me ke shirin faruwa dani? waye ya aikata laifin da ya ke neman zama nawa?? ya akai Zuciyata ta alaƙantu da yarinyar cikin lokaci kaɗan? me yasa na damu da damuwarta? me yasa Mommy ta ƙi yarda dani?? me yasa nake jin zafi da ciwo akan abin da akai wa yarinyar??" tambayoyi masu tarin yawa ya ke jefawa kansa sai dai ya rasa me amsa masa su, kansa ya gama ɗaukar zafi Zuciyarsa ta na ƙonuwa iya ƙonuwa gashi bai san wanda ya yi masa ƙanƙancin ba bare ya yi maganin abin. Shukriya cikin sanyi ta ce "Abida bani da zaɓin da ya wuce haka, ai Allah bai ce Ayi Auren da ba soyayya ba fahimtar juna ba fisabilillahi Safyan na ke so, kuma yau ɗinnan in Allah ya yarda zan faɗa masa abin da ke cikin raina na riga na yanke wannan hukuncin." "Aunty ina tsoron halin maza wallahi, ke dai ki guji wulaƙancin namiji akan cewa ki na son shi." "Ba zan iya ci gaba da ɓoyewa a Zuciyata ba hakan zai iya yi mata illa, zan faɗa masa idan bai amince dani ba sai hankalina ya fi kwanciya har na haƙura dashi amma indai ban gaya masa ya ban amsa ba ba zan iya haƙura ba." "Ina miki fatan Nasara Aunty." Abida ta faɗa tare da jinjinawa girman lamarin Shukriya. kasa bacci Shukriya ta yi sabi da tsoro da zullumin amsar da za ta samu daga Safyan Bayan ya karanta saƙon da ta tura masa ta Whatsapp, ta na rungume da wayar sai juye-juye ta ke yi bini-bini ta duba sai ta ga bai dawo da amsa ba ko dubawa bai yi ba, haka ta dinga yi a tsawon daren nan duk ƴan mintuna sai ta duba, sai da Assubhi ta gabato sannan bacci ya kwasheta. Ba ta daɗe da yin baccin ba Abida ta tashe ta Sallah, kafin ta yo Alwala sai da ta duba taga dai ba abin da ya canja sannan ta tashi, Addu'a ta yi sosai bayan ta idar sannan ta miƙe ta koma bakin gado ta zauna ta ƙara ɗaukar waya. har 07:00 wayar ta na hannunta ta na danne-danne, ganin shigowar saƙonsa ne ya sa ta bar abin da ta ke yi ta tafi dubawa. "Idan ba damuwa ina so mu haɗu yau. da sauri ta mayar da amsa "Ba damuwa. "Okay Zan zo na ɗaukeki. Kallon Rubutun ta ke yi ta na Nazari, me ki ke shirin Aikatawa haka Shukriya? ta yiwa kanta tambayar, goge ƙwallah ta yi kafin ta rubuta "Shi kenan ina jiranka. Murmushi me cike taf da manufofi Safyan ya yi gami da shafar sumar kansa ya ajiye wayar a gefe, wani irin daɗi d farin ciki ne ya ke ratsa shi tin daga ƙasan Zuciyarsa, "Gaskiya ni ɗan-baiwa ne Damata sai zuwa ta ke ta ko'ina, Hauwa'u Ibrahim Ƴar-Jarida!!! dama kin daɗe da shiga gonata yanzu lokacin ya yi. Duk bugun numfashinta ta na yin sa ne cike da abubuwa da dama, Addu'ar Safyan ya amince da soyayyarta, Wata irin fargaba wadda ba ta san meye asalinta ba, Tsoron abin da ka iya zuwa ya zo, har da ma wasu abubuwan da ta kasa gane ko me su ke nufi haka kawai ta ke jinta duk a yamutse. _________ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ *INDO* [12/14, 8:49 AM] INDO CE: *WATA HANYA* 15 Free Buk Ayeesha Abdulkareem *(Indo ce..)* ELEGANT ONLINE WRITERS. Jiki a sanyaye ta gama shiryawa don kuwa Safyan ya sanar mata ya na hanya, kasa gayawa Mami ta yi sai Abida ta sa ta faɗa, Addu'a kawai Mami ta yi mata dan ta lura Shukriyan ta gama zurfafa zuba mata ido shi ne sauƙi a cewarta. Shiru Motar ta yi babu me cewa ƙala a cikinsu, Shukriya kanta a ƙasa ta kasa ɗagowa bare su haɗa ido dashi wata muguwar Kunyarsa ta ke ji gaba ɗaya ya cika mata ido, ta na cikin tunane-tunane Muryarsa ta ratsa dodon kunnenta. "Mun Iso Ƙanwata. Cikin sanyin jiki ta fito daga Motar ta na ƙara yin ƙasa da kai, kusa da ita ya zagayo ya tsaya ya na murmushi ya ce "Kunyata ki ke ji ne?" girgiza kai ta yi alamar "A'a" ya ce "Na yi mamaki matuƙa da ki ka ture Son da Maalik ya ke miki ki ka so ni ki me yasa??" gyara tsayuwa ta yi gami da sauke gwauron numfashi, jin shiru ya sa shi ƙara jefo mata tambaya "Ƙanwata tabbaci na ke son samu Don Allah gaya min me ya faru?" "Ba ni ce na tsara hakan ba, nima bansan ta ya akai na fara sonka ba, tin daga kallon farko da na yi maka na ji Zuciyata ta na buƙatar Shaƙuwa da kai" Ta na maganar ta na rintse ido. "Na yi farin cikin samun soyayya daga kyakkyawa Shukriya, amma fa ki yi haƙuri ni kam ba zan iya karɓar soyayyar ki a wannan lokacin ba. da kyar ta iya ɗago idanunta da su ka yi mata nauyi ta ɗora akansa wata irin sarawa kanta ya ke yi atake wani malalacin zazzaɓi ya fara sakko mata.. Baban Halima ne zaune kusa da Shahmeer cike da damuwa ya ce "Ɗannan ba ku ga ƴata ba har yanzu?" "Ka yi haƙuri Baba za'a ganta in sha Allah, ka dena namuwa mu ma fa ƴaƴanka ne. "Ai ban san halin da ta ke ciki bane shi ya sa. "Kar ka damu ta na lafiya ba abin da zai faru in Allah ya yarda. Baban Halima ya murmusa gami da cewa "Allah i yarda, Allah ya yi muku albarka ku ma yadda ku ka mutuntani Allah ya yi muku fin haka. da "Amin" Shahmeer ya amsa kafin ya miƙe gami da cewa "Baba Zan wuce su na jirana." "To Allah ya tsare ka ji ɗannan, ka ce ina gaida ƴan-uwan naka harma Mamanku. "To Baba. Halifa ne ya ce "Yallaɓai Allah ya tsare." Shahmeer ya ce "Amin Halifa don Allah ka ci gaba da kulawa da bawan Allahn nan ki ji." "In sha Allahu Alhaji zan ci gaba fiye da da. bai ce komai ba ya fice daga gidan cike da tausayin Baban Halima da ƴar tasa. Cikin sauri-sauri Ma'arufa ke tafiya alla-alla ta ke ta isa gida don kaiwa su Umma ƴar Taliya guda biyun da ta ɗakko, Kallon hanya kawai ta ke amma ba ta lura da inda ta ke tsoma ƙafarta sabi da tunani kala-kala da ta ke yi, mafi yawancin tunanin nata akan Shahbeer ne wanda ta kasa gane gaskiyar lamarinsa gashi Zuciyarta ta na gaya mata abubuwa da dama, ta wata fuskar sai ta ga kamar ba zai iya aikata hakan ba amma idan ta tuna yadda Mommy ta kasa yarda da shi kuma sai ta ji itama ta kasa yarda dashi don kuwa tin da Mahaifiyarsa ba ta yi masa shaidar kirki ba ba wanda zai yi masa, zuwa yanzu ta fara jin tsoronsa dan kuwa ta na gudun abin da ya faru da Halima ya faru da ita, sallama ta ji ana yi a kusa da ita hakan ya sa ta bar tunanin ta maida hankali gurin da ake mata sallamar, amsawa ta yi gami da bin Saurayin da ido Black beauty dashi ya sha kwalliya cikin yadi milk sai murmushi ya ke mata. "Sannu da dawowa. da ɗan mamaki ta ce "Yauwa sannu." "Ba ki sanni ba ni kuma na sanki sabi da ina son alaƙa da ke, Sunana Bashir a Unguwar nan gidan iyaye na ya ke amma ba mu daɗe da tarewa sosai ba, ba mu fi shekara ɗaya ba, ina yawan ganinki amma na san ke ba ki taɓa ganina ba ko?" Gyaɗa masa kai ta yi, ya ci gaba da cewa "Abokaina sukance girman kai gareki ba za ki saurareni ba, ni kuma na kasa yarda da hakan yau dai na yanke hukuncin yi miki magana kuma idan kin bani dama in baiyana miki abin da ke ɓoye a cikin Zuciyata." Ɓoyayyar ajiyar Zuciya ta sauke ba ta yi magana ba kuma ba ta tafi ba. gyara tsayuwarsa ya yi cike da murnar sauraren shi da ta yi, "Na yi farin ciki da ki ka bani dama haka Ma'arufa, to maganar gaskiya ba zan iya ɓoye miki ba Ina sonki. Ido ta zazzaro akansa ta na masa kallon mamaki da kuma tsoro, a zamanin nan duk irin lamuran nan tsoro suke bata a son ranta ma ba za ta yi Soyayyar ba ma bare ta yi Aure ta bar Mahaifiyarta da ƙannenta . jin ta yi shiru ya sa shi ci gaba da cewa "Don Allah kar ki ƙi amsa min Ma'arufa ki temaka kar na zauce." In ce masa a'a?? ko dai in amince?? tsakan -kanin magana biyu ta ke ta juyayi, kasa tsayar da shawara ta yi don haka ta ce "Am.. ka yi haƙuri sai na yi tunani." ta na cewa haka ta yi gaba da sauri. da ido ya rakata ya na Addu'ar Allah ya sa ta amince. Sallama ta yi a tsakar gida, Umma da Fiddausi su ka amsa, gaida Umma kawai ta yi ta dire Taliyar ta koma gefe ta zauna ta lula Duniyar tunani; Umma ta na so ta yi Aure, itama kuma ta na so ta yi don kuwa itama ta girma sai dai ta na tsoron barin su Umma kuma ta na tsoron yaudara irin ta Mutane sai ka yarda da Mutum ka so shi da Zuciya ɗaya shi kuma ashe son bai je Zuci ba, ta na matuƙar tsoron hakan shi yasa duk ta faɗa yanayi kuma ta kasa bambance ɓangaren da za ta ɗauka. Ganin ta yi Zuru-zuru ya sa Fiddausi cewa "Meke damunki ne Anti?" "Abin da yawa Firdausi. kusa da ita ta dawo ta zauna, a hankali ta ce "Gaya min, rashin wanda za ka yi magana dashi shi ya ke sa abar abu a rai kuma ke ki na damu don haka gaya min abin da ya sa ki ka canja ɗinnan." kamar za ta yi kuka ta ce "Ba komai fa wani ne ya ce ya na sona kuma ni wallahi tsoron soyayya na ke ji kuma ba na son abin da zai rabani da ku. Umma ta yi saurin cewa "Allah sarki Ma'arufa baiwar Allah, sabi da mu ai ba kya ƙi Ibadar Allah ba, Aure ai ke ya kama a matsayinki na mace, mu iyaye ai mu baku tarbiya mu raineku ku girma sannan mu Aurar daku shine cikarmu iyaye, kuma shine mu ka riƙe amanar da Allah ya bamu, ki yi haƙuri ki yi tunani akan kanki idan kin ji bai miki ba shi kenan Allah zai kawo wanda ya yi mikin." ƙasa ta yi da kai ta na tunano Bashir ba ta ji wani abu me kama da ƙi a game dashi ba, ba za ta iya cewa ta na ƙin shi ba. Usman da ya shigo yanzu ne ya fara murna gami da cewa "Anti za ta yi Aure, Anti Za ta yi Aure." Fiddausi ta ce "To Shashasha ba Aure za ta yi ba wani ne ya ce ya na sonta." za ma ya yi gami da cewa "To dan Allah ba sai ta so shi ta yi Aurenta ba?" share ƙwalla ta yi kafin ta ce "Usman Tsoron Duniya na ke, ina tsoron yaudara da zalumci ba ka ganin mu ba wasu bane anya kuwa za mu samu me son mu da Aure tsakani ga Allah ba don wata manufa ba?" Shiru su ka yi suna tunani Umma ce ta ce "Allah ba ya barin mutum cikin tsananin damuwa, idan bai baka tanan ɓangaren ba sai ya baka ta nan, don mu talakawa ne kar ki yi tunanin Allah ba zai kawo miki mijin Aure ba." Fiddausi ta ce "A ina ku ka haɗu kuma Anti?" "A layin can ne kafin na ƙaraso namu layin wai sunanshi Bashir ɗan Unguwar nan ne. Usman ya ce 'O!! ai na ma san shi, kuma wallahi Mutumin kirki ne Anti ya na sana'ar shi ba ruwanshi da shiga sabgar ƴan-iskan Unguwa abokansa ma duk mutanen kirki ne, ina ga fa da gaske ya ke Anti." Umma ta ce "Ka tabbatar ba mutumin banza bane? kuma ka san gidansu?" "Ƙwarai kuwa Umma Na san gidansu sarai, wani lokacin ma har aikena ya ke gidan, mata biyu ne ma. Umma ta ce "Ma'arufa ki daure ki saurari bawan Allahn nan ki amince masa daga baya za ki fahimci wasu halayen nashi idan kin ga ɗabi'unsa ba su yi miki ba sai ki sanar min." gyaɗa kai kawai ta yi sannan ta miƙe ta shige ɗaki, a gado ta kwanta ta fara sharɓar kuka mara sauti don kar su Fiddausi su ji. Suna shiga Falon Halima ta fara murna, har ya ƙaraso ya zauna ku sa da Inna idanunta na kanshi sai dariya ta ke wadda da an gani ansan lafiyar sai a hankali, bayan sun gama gaisawa da su Mommy ya ce "Halimatu" Dama jiran kaɗan ta ke ya na faɗen sunanta ta tashi da sauri ta dawo in da ya ke cike da murna ta ce "Baba Alewata." Shahzaib ne ya ciro Chocolate a Aljihunsa ya miƙo mata gami da cewa "Yau ya manta Baban naki." Shahbeer ya ce "Wai ban rabaka da shan zaƙin nan ba?" ƴar dariya ya yi gami da cewa "Ai ta-ta ce ba tawa bace nasan za ta nema shi yasa na aje mata." "Ohh ka shanye takan ken..." Halima ce ta katse masa maganar ta hanyar ƙanƙameshi sabi da murna. rintse ido ya yi gami da cije gefen leɓensa "A'uzubillah, Astagfirullah" ya furta a cikin Zuciyarsa. ganin idon Mommy akansu ne ya sa Shahmeer miƙewa ya ja hannunsa gami da cewa "Tashi mu je Mu yi lissafi Inya." saɓuleta ya yi daga jikinsa cikin ƴan dabaru sannan ya miƙe, kamar wanda aka sassara ƙafafun nasa haka ya ke tafiya a hankali a hankali har su ka isa sashin nasu. Murmushi Safyan ya yi kafin ya ce "Wasa nake miki Shukriya, duk wanda ya samu soyayyarki kuma ya banzatar ai bai more ba, na faɗi haka ne don naga zan iya auna adadin son da ki ke min?" ya ƙarasa maganar gami da kashe ta da wani shu'umin kallo; ba ta san lokacin da Murmushin farin ciki ya baiyana akan fuskarta ba ta sauke ajiyar Zuciya ta kasa dena murmushi dan kuwa ba ƙaramin farin ciki ta yi da jin hakan ba. "Na kasa Auna adadin sona a Zuciyarki Shukriya gashi kuma ina son ganewa ba dan komai ba sabi da in san babban matsayina a gurinki ta yadda zan fifita ki fiye da yadda ki fifita ni, Don Allah za ki temake ni Shukriya??" yadda ya ƙarashe maganar a marai-raice ya sa ta yi saurin gyaɗa masa kai. Murmushin gefen baki ya yi cike da farin cikin haƙarsa ta kusa cimma ruwa, "Abin akwai wahala amma kasancewarki Ƴar-jarida kece za ki iya temakon Al'umma ƴan-uwanki Musulmi, na tsani azzalumi na tsani zalumci ki temaka min mu kawo ƙarshen abin, nasan ki na ɗaya daga cikin ƴan-jarida masu aiki tuƙuru domin Al'umma amma idan ba za ki iya ba ba damuwa kar ki sa kanki a ciki. shiru ta yi ta na tunanin menene kuwa abin da Safyan ya ke so ta yi??, sauke numfashi ta yi sannan ta ce "Zan yi iya bakin ƙoƙarina don ganin na temaki ƴan-uwana, gaya mini me ya faru??" "Na san kinsan DOUBLE TWO STAR, kuma ki na son jin labari akansu. haka kawai ba ta san dalili ba ta ji gabanta ya yanke ya faɗi, jimm ta yi kafin ta ce "Na sansu, amma me su ka yi me zafi haka har ya zama na cutar da Al'umma? ." ya yi murmushi me kama da na takaici kafin ya ce "Wane irin labari ki ka sani akansu?" "Ƴan-kasuwa ne masu sana'a goma maganin me gasa, su na yin abubuwa iri-iri kuma komai nasu ya na da sauƙi fiye da na kowane kamfani, Shinkafa, Gishiri, Maggi, Mai, Taliya , Fulawa, Robobi. da dai sauransu, amma sun dai fi ga kayan Masarufi sai kuma wasu ɓangarorin kasuwancin irin su Gidan mai, Super Market da Shaguna a kasuwa da suke ɗora mutane akai, Suna Kasuwanci Daban-daban wanda ba lallai ma in iya faɗa maka adadinsu kai tsaye ba, Da ina tantama akan su Ƴan-huɗu ne amma na yi bincike sosai na gane hakan kuma na yi bincike akan kasuwan-cinsu na Ƙasashen-mu Nigeria, Niger, Chadi, Ghana, da dai sauran ƙasashen ƙetare, Ƴan-kasuwa ne masu damawa a ko'ina, inaga wannan kawai shi na sani akansu. "Gaskiya kinsan abubuwa da yawa akansu, amma ya kamata ki binciki suwaye su kafin ki san duk wannan, ba ki taɓa tambayar kanki Ƴa-ƴan waye a ƙasar nan ba??" Shiru ta yi ta na Nazari, kuma fa haka ne ban san Asalinsu ba, da sauri ta ce "Za ka iya gaya min??" "Ba su da wani Tarihi me kyau domin kuwa ba'a san Mahaifinsu ba, iya bincike na ya nuna min Ba ta kyakkyawar Hanya aka samesu ba, sannan..... _________ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ *INDO* [12/15, 10:13 AM] INDO CE: *WATA HANYA* 16 Free Buk Ayeesha Abdulkareem *(Indo ce..)* ELEGANT ONLINE WRITERS. *(Masoyan INDO CE, Ban yi mamaki ba da na ga kun fi son WATA HANYA Fiye da DOGON YARO, amma na kaɗu sosai da naga FANS na WATA HANYA suna neman fin na TAJMAHAAL Yawa, To wai meye Sirrin ne?😜😊. INA GAISUWA GAREKU MASOYANA MASU BIBIYATA A KODA YAUSHE, Da wanda na sani da wanda ban sani ba, Har kullum kuna raina❤️)* ..Sannan sun yi amfani da Yardar da Al'umma suka basu su ke cutar da mutane, ba su da aiki sai sayar da ƴan-mata da lalata yaran mutane sabi da rashin imani, kuma a yanzu haka maganar da na ke miki sun haɗe kai da Maƙiyan ƙasarmu masu son ganin bayanmu za su zuba mana guba a cikin Kayan Abinci ta yadda za'a dinga cutuwa a sirrince ba tare da an yi zarginsu ba, ina tsoron wannan ta'asar tasu ta cika Duniya shi

Chapter 9 of 30