yadda kasan ɗanka na cikinka amma idanunku ba iri Ɗaya bane don nashi wani kala ne sumar kansa ma ta bambanta da irin taka.
Zumbur ya tashi tsaye tare da cewa "Me???" zagaye gurin ya shiga yi cikin kaɗuwa da mamaki wasu tunane-tunane su ka fara yi masa yawo.
"Yanzu ina yaron?"
"Ban san inda su ka tafi ba, shi da wata mata na gansu a wajen askin mata, wai sunansa Shahzad ta ce.
wani lafiyayyen mari ya kwafsa masa kafin ya ce "A memakon ka kawo mini yaron sai ka kawo mini labarinsa? lallai-lallai a nemo mini shi, ina son ganinshi"
ya yi maganar cikin ɗaga murya, sauran yaransa na gurin suka tattashi su ka tambayeshi kamannin yaron cikin fitar haiyaci ya ce "Idan kun ga yaro ko babba me kama dani ku kawo mini shi!!" ya yi maganar cikin tsawa, dandanan su ka fashe su ka shiga gari neman me kama da Ogansu.
"Kenan Ƴar-Makafi ta na raye har yanzu?? kuma ta na ina?? ɗanta ne wannan ko na wata? meke shirin faruwa da ni haka?"
tambayoyin da su ke yi masa yawo kenan.
Gidan Hajiya Dada ya cika taf da ƴan Ɗaurin Aure sai warkajami ake yi.
a gidan su Shukriya ma Sai biki ake yi kowa ya na shagalinsa ba wanda ya damu da halin da ta ke ciki, irin wulaƙanci da cin kashin da Abida ta ke yi mata ya fi komai tsorata ta, sai faɗa mata maganganu ta ke yi ta na binta da kallon banza, cikin tsananin tashin hankali take musamman in ta na ganin lokacin da aka tsayar domin ɗaura Auren ya na ƙara gabatowa sai ta ji kamar ta haɗiyi Zuciya ta mutu.
10:00
Jama'a masu yawa suka shaida Ɗaurin Auren,
Aliyu Muhammad Jibril
DA
Zakiyyat Basiru Mukhtar Boza
Sai
Mukhtar Basiru Mukhtar Boza
DA
Hauwa'u Ibrahim Me Haƙuri.
_________
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
*INDO"*
[1/2, 12:23 PM] INDO CE: *WATA HANYA*
31
Ayeesha Abdulkareem
*(Indo ce..)*
ELEGANT ONLINE WRITERS.
Wata muguwar zabura Dada ta yi a masife ta ce "Uban waye ya sa a ɗaura Auren??"
Zayd ya ce "Wallahi Dada ba zato ba tsammani mu ka ji hakan ta faru, abin ya bawa kowa mamaki, amma da alamu Daddy ya san da hakan don kuwa naga suna gaggaisawa Da Alhaji Basiru har ma da Shahbeer Double Two Star da dai sauran magabatan Shahzain."
Kai-komo ta shiga yi ta na jinjina kai, ranta ya na wata irin tafasa Zuciyarta na tuƙuƙi, "Eh Lallai Alhaji Muhammadu ka cika har ka yi yawa, Har ni za'a rainawa hankali? ni?? ni?? za'a canjawa hukuncin da na yanke?, Ni da Ɗana amma a hana shi abin da ya ke so???? ba zai yuwu ba ya zama dole duk bala'in da za'ayi sai an yi shi, Ina Maalik ya ke??"
Zayd ya ce "Maalik tin da ya ji haka ya shiga bedroom ya kulle ba mu san a wane hali ya ke ba."
"Ni fa da Ɗana ya faɗi ba Nasara gwara a taka bakin faranti uban kowa ya ɓare, ba uban da ya isa ya Auri ƴar da Ɗana ya ke so idan ba shi ba, Lallai Muntari ya yi kuskuren ja da ni, Maza-maza ku je gidan Ibrahim ku ɗauke Shukriyar daga gidan, zan turo muku Address inda za ku kaita, sai dai Labarinta amma ba ita ba domin kuwa ba wanda zai ƙara ganinta anan za ta ƙare rayuwarta har ta mutu"
Ta kai maganar ta na huci a tsananin fusace.
Zaydu ya ce "To Dada."
ficewa ya yi ya je ya nemi Abokanansa yan gurugubji su ka nufi gidan su Shukriya don aiwatar da abin da Dada ta faɗa.
Dada kuwa ɗakin Maalik ta nufa don ganin halin da ya ke ciki.
a zauna ta same shi ya yi zugum, ba um ba um-um sai idanunsa da su ka yi jajir ya ke zazzarewa.
ta zauna kusa da shi kafin ta ce "Maalik, wannan Ɗan Fatarar ya sa na kasa cika maka Alƙawarin da na ɗauka, gashi yadda su ke da taurin kai ba za su taɓa yarda da saki ba, amna kar ka damu yadda ba su bari ka mallaketa ba haka su ma ba za su mallaketa ba, zan sa a kulleta har ƙarshen rayuwarta kowa ya rasa."
girgiza kai ya yi gami da cewa "A'a Ammi, kar ki cutar mini da Shukriya nasan ba ta da laifi, Ki barta ta je ta rayu da wanda ta ke so, ni kuma idan na mutu ma kwanana ne ya ƙare, amma fa indai da raina ba zan taɓa bari Ƙanwarsu ta Shaƙi iska me daɗi ba, numfashi ma sai na sa ya gagareta sai ta ce gwara mutuwa da rayuwa haka ƴan-uwanta za su yi dana-sanin Aura mini ita, wannan Alƙawarina ne kuma Wallahi tallahi Billahillazi sai na aikata, sai na yi abin da har su mutu ba za su taɓa mantawa ba, yadda su ka ƙuntata mini nima sai na ƙuntata musu.
Daɗi ya gama mamaye Dada, ta yi mugun farin ciki da jin kalamansa, amma cewar ta ƙyale Shukriya ba za ta ƙyaletan ba amma za ta yi kamar ta haƙura, ci gaba ta yi da famfashi ta na ƙara ɗora masa irin izayar da ya kamata ya yiwa Zakiyyat.
(Waiwayen baya)
Daga Mommy sai Shahzain a Falon, fitowar Shahbeer kenan ya tarar su na magana,
cikin tausayawa Mommy ta ce "Shahzain, na rasa meke damunka ba ka walwala gashi Ɗan-uwanku shi ma ya na cikin damuwa nasan da shi ne mutum na farko da zai fara tambayar damuwarka."
"Mommy ba wata damuwa bace, game da Shukriya ne kuma na riga da na haƙura.
"Me ya faru da Shukriyan? wani abin ta yi maka??"
"A'a Umma kawai ni na fauwalawa Allah, na haƙura da soyayyarta.
"Wai to ka faɗa mini dalili mana?"
"Ba wani abin bane ki manta kawai.
"Ba zai yuwu ba Shahzain, ba gaira ba dalili ban amince ka fasa Aurenta ba, ya zama wajibi ka gaya mini gaskiya.
kamar zai yi kuka ya ce "Umma ba na son faɗa miki ne, amma gaakiyar itace Auren Shukriya da Maalik ya rage saura kwana huɗu gashi ma har yamma ta yi saura ƙiris a dawo kwana uku."
"Danƙari, Wai ita Dadan nan me ta taka ne da ta ke nuna iko akan kowa haka? Shin Mahaifiyar Alhaji Ibrahim ɗin ce?"
"A'a YaYarsa ce amma bansan dalilin da ya sa ta ke musu hakan ba.
"To ai kuwa indai har ba Mahaifiyarsa bace ba ta isa ta Ida tarwatsa farin cikinku ba sabi da wani Son Zuciya nata, nima zan nuna mata ba wai a banza na haifeku ba, abin ya isheni haka dole ne na shigo cikin lamarin.
Shahzain ya ce "Umma ni na haƙura ki ƙyalesu tinda ƴarsu ce."
"Nima ƴata ce, kuma ya zama dole in ƙwatar mata haƙƙinta, idan kuma ka san ba ta sonka Maalik ɗin ta ke so ka gaya mini gaskiya idan ma cikinku ba wanda ta ke so ka faɗa mini wanda ta ke so ni kuma zan yi mata Uwa in yi mata makarɓiya, wannan ai zalumci ne.
Sai a lokacin Shahbeer ya yi magana "Fushin Uwa ba daɗi, Momma na fa ji daɗi da kika ce haka, amma ina neman Alfarmarki, ki bar mini fagen idan na gama yaƙin sai ki share filin, Na tsinkayi labarin duk da cewar Autana bai gaya mini ba, don haka na shirya, Na sanarwa Babanmu zan Aurar da Ƙanwata ga Maalik sannan zan Aurar da Ƙanina wa Shukriya, kuma na gaya masa shine maɗaurin Auren duka, yanzu karo na farko kenan da zai shiga lamuranmu a matsayin Mahaifinmu, amma ba wani farin ciki na ke da hakan ba kawai dai don ya na bani tausayi ne."
Mommy ta yi murmushin farin ciki kafin ta ce "Ni kuma na ji daɗi kuma ina farin ciki da faruwar haka, mu ma Allah i yafe mana kusa-kurenmu kamar yadda mu ka yafe masa nashi, kuma na yi murna da hukuncin da ka yanke akan Auren."
"Amma hakan ya zama sirrin junanmu domin in wani bare ya ji shirina zai lalace kuma za'a samu matsala.
Shahzain ya ce "Na gode Inya.." da sauri ya ce "Ba na son godiya fa." "To Boss na dena" ya yi maganar tare da dariya.
Tin daga ranar su Shahbeer su ka ci gaba da shirye-shirye ba kama hannun yaro.
Mommy da Inna da Mommin Malika da Malika, Sallama su ka yi a gidansu Shukriya Matan da ke tsakar gida su ka amsa, ganin baƙin fuska kuma cikin shiga ta Alfarma ya sa su ka fara Ɗar-ɗar, mace ɗaya ce ta yi jarumtar cewa "Sannunku da Zuwa, ai uwar bikin ta na ciki bari a nemota."
Mommy ta murmusa gami da cewa "Kafin ki nemo Uwar bikin fara haɗa ni da Ƴata wato Amaryar Hauwa'u Ibrahim (Shukriya) gurinta na zo domin na fi buƙatarta fiye da kowa."
Matar ta ce "To ku shigo daga ciki. ta yi maganar tare da yin gaba, su ka mara mata baya ta kaisu ɗakin da Shukriya ke zaune ita da Fatima da wasu ƴan tsirarun mutane.
Da sauri ta miƙe tare da cewa "Mommy!!" cike da mamakin ganinta.
Mommy ta ce "Ƴata ki na daga ciki?, to sannunku."
Fatima ta ce "Sannu da zuwa Mommy." tabarma ta shimfiɗa musu tare da cewa "Da kanku Mommy, Allah ya sa lafiya ba laifi mu ka yi ba." "Lafiyar ce ta kawo haka, Mun zo ne mu tafi da Shukriya ɗakin Mijinta.
duka ba su fahimci abin da ta ke nufi ba ta so ta yi tambaya shigowar Mami ta katseta, bayan sun gaisa Mami ta ce "To ban ganeku ba dai amma ku yi haƙuri."
fuskar Mommy ɗauke da murmushi ta ce "Ai tambayar itace daidai rashinta ɗin shine kuskure, Sunana Hajiya Aisha Mahaifiyar su Shahbeer da Shahzain wanda aka ɗaura Aurensa da Shukriya a yau, ko da ba'a ɗaura ba mu na sa ran ana gab da ɗaurawar."
Mamaki ya cika mutanen wajen dan da nan kowa ya ɗauka ya na tofa Albarkacin bakinsa. Mami kuwa farin ciki ne ya lulluɓeta, ta faɗaɗa fara'arta tare da cewa "To Alhamdulillahi, Amma ya akai haka mu har yanzu ba dan kin faɗa ba mun yi tunanin da Maalik YaYanta za'a ɗaura."
"Eh haka ne, an samu maslaha ne a tsakankanin iyayen yaran, Maalik an Aura masa Zakiyya ƙanwar ƳaƳana a bisa Amincewar Mahaifinsa, yanzu dai maganin tasowar wata fitina ta ƙuruciya ya sa mu ka yanke shawarar ana ɗaura Aure za mu ɗauketa sai mu wuce da ita, mun zo da Motoci wanda za'a Kai danginta su gano ɗakinta.
"Kai ma sha Allahu, to babu komai bari ta shirya kuma ta yi sallama da sauran ƴan-uwa, Aunty Nafisa don Allah ki ja ta ta fara shiryawa.
wadda aka kira Aunty Nafisa ta ƙarasa wajen Shukriya da ta zauna ta yi ƙasa da kai gaba ɗaya ta rasa wane irin Farin Ciki za ta yi sai ƴan hawaye ta ke yi.
Aunty Nafisa ta kama hannunta tare da cewa "Tashi ko sai mun ɗaga ki da kanmu, Farin ciki ya isheki kin Samu Shahzain ."
ta yi maganar ta na dariya cikin sigar zolaya.
Fatima ta ce "Ai ni kaina murna na ke yi Aunty Nafi"
Jan hannunta su ka yi zuwa Ɗakin Mami su na yi su na zolayarta ita dai dariya kawai ta ke musu yau ba bakin magana.
Su Mommy sun samu ƴan hira har lokacin da aka gama shirya Shukriya, Har Nasihohi da jan kunne duk iyayenta da ƴan uwa na kirki sun yi mata sannan aka sanar wa su Mommy Amarya za ta fito, sallama su ka yiwa Su Mami sannan su ka koma mota, bayan Amarya da danginta sun gama shiga Motocinsu aka ɗau hanya.
su na fita daga layin Su Zayd su ka shigo su na zuwa aka sanar musu dangin Mijinta sun karɓe abarsu, hakan bai yi musu daɗi ba sam dole su ka koma da gwanjon Kunya su ka Gayawa Dada yadda aka yi, abin ya yi mata ciwo sosai kuma ta ƙudiri niyar ɗaukar Fansa ko ba ta nan ɓangaren ba.
Wani sabon bikin aka buɗe a gidan Mommy domin an yiwa ƴan rakiyar Amarya kyakkyawar tarba.
Wasu wuni su ka yi sai yamma su ka tafi wasu kuma da Rana su ka koma.
acan gefen Gidan Gandu, wato Part ɗin Mommy anyi gidaje Huɗu ƴan madai-daita wanda cikin su huɗun kowa da nashi, Nan aka zubawa Amarya kayan ɗakinta kuma ta tare anan.
su na zaune su na hira kowa ya na tofa Albarkacin bakinsa, Ma'arufa ta ce "Ya Shahzain Ka je gurin Amarya mana kar ta yi fushi."
ya yi dariya gami da cewa "Zan je Beauty."
Shahzaib ya ce "ita nan fa murna ta ke yi anyi bikin wata, amma idan akai maganar nata sai ta yi shiru."
Shahmeer ya ce "Au ka raina kenan, me ka ke so ta ce maka? ta ce asa rana ka ke so ko kuwa? mu fa baƙin sauƙi ne idan kun shirya sai mu ƙara yin wani bikin."
Ma'arufa ta yi ƙasa da kai cikin jin kunya.
Shahbeer ya ce "Kai ware, waye zai wani ƙara Aurar da su yanzu to ba da ni ba, sai na dawo haiyacina tukunna, barsu su ci gaba da Fasa Love ɗinsu a Falon Mommy."
Malika ta ce "A'a gaskiya su ma ya kamata su ɗan motsa mu rage Tuzurai."
Shahzain da Shahbeer sun yunƙura da niyar yin magana Wayar Shahbeer ta dakatar da su.
da sauri ya ɗauka ganin Salim me kula da su Halima ne ya ke kira.
Cikin inda-inda ya ce "Me gida Wallahi Halima ta bar gida, mun yi iya yin mu ni da su Kacau amma ba mu ganta ba ta safemu wallahi."
Da sauri ya miƙe tare da cewa "Ta bar gida?, to garin ya?"
"Me Gida ban sani ba wallahi kawai ina ɗakin da nake kwana sai zuwa na yi na tarar ba ta nan.
"Aje waya"
Shahbeer ya faɗa cikin sanyin jiki.
zama ya yi gami da cewa "Wai Halima ya ta ke so na yi da rayuwata ne?"
"Me ya faru kuma?"
Su ka jefo masa tambaya.
abin da Salim ya faɗa masa ya maimaita musu sannan ya ci gaba da cewa "Allah ya sa ta faɗa hannu na gari to"
Malika ta ce "Ya Shahbeer nima ina son gaya maka abin da idanuna su ka gane mini sai dai bansani ba ko zaka yarda ko ba za ka yarda ba.
Zuba mata idanu ya yi alamar ya na saurarenta.
"Ranar da na fita zuwa Asibiti kafin bikin su Ya Shahzain, naga wani me kama da ku amma kamar ba irin yadda ku ke ku huɗun nan ba ya na dai yanayi da ku gaskiya.
Ba iya Shahbeer ba dukansu sai da su ka kasa motsi sabi da mamaki da Al'ajabi, Shahzaib ya ce "Kinga Hasiya ki ke ko Malika? Ba na son ƙarya da faɗen gaibu, a ina mu ka samu wani da zaiyi kama da mu ban da kin ci kwayal?"
"Ya Shahzaib Duka Sunana ne, Hasiya sunana ne Malikan ma haka, amma ya kamata ku yarda da ni don ban taɓa zuwa muku da irin zancen nan ba."
Shahbeer ya ce "Duk da abin da mamaki amma ni na yarda.
daga haka ya tashi ya bar gurin.
Halimatu ,,,,,,,,,,,,,, Har yanzu
ta kasa yarda ba Hannun Shahbeer a cikin wanda su ka zalumceta hakan ya sa ta tsani ko da sunansa, kullum ba ta da magana wa Baban Halima sai ya tashi su bar gidan kasan-cewar shi da Hankali bai bata goyon baya ba don haka ta yanke hukuncin yau ko mutuwa za ta yi idan ta bar gidan sai ta barshi, a cewarta idan Baban nata ya ga ta tafi zai bi bayanta.
sai da ta faki idon Salim sannan ta fito saɗaf-saɗaf ba ta yi motsin da Baban Halima zai san za ta fita ba. cikin sa'a ko rashinta ta samu ta fice, tin 12:00PM ta ke watangaririya har yamma ta yi liƙis, Guri ta nema ta zauna domin hutawa gashi ba ta san kowa ba ga yunwa ga ƙishirwa.
ta na nan zaune kan wani dutse wasu samari biyu su ka iso gurin su na kallonta , su a nasu ɓangaren kallonta su ke ko za su samu waya a hannunta su ƙwata, kamar da wasa su ka ci karo da Fuskar ƳARMAKAFI. kallon kallo su ka yi kafin ɗaya ya ce "Dafe mana nan ni bari in je in sanarwa Oga."
ɗayan ya ce "ka yi sauri to."
Ɗaya ya ƙarasa wajen Halima Ɗaya kuma ya yi baya ya fara kiran Ogan nasu a waya, cikin sa'a kuwa Matemakin Ogan ya ɗauki wayar ya sanar masa abin da ke faruwa shima ya sanarwa Oga.
Halima kuwa da ya ke ba saninsu ta yi ba nan su ka daddafeta da tambayar ina za ta je ina ta fito meke damunta.
_________
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
*INDO*
[1/3, 9:56 AM] INDO CE: *WATA HANYA*
32
Ayeesha Abdulkareem
*(Indo ce..)*
ELEGANT ONLINE WRITERS.
Suna nan suna yaudararta har Ogan ya ƙaraso, bai fito daga Motarsa ba ya yi musu umarnin su kira masa ita da sunan za su kaita gidansu ta kwana.
ba ta yarda da hakan ba don haka ta miƙe ta ci gaba da tafiya bayan ta sanar musu ba za ta iya hakan ba.
Fitowa ya yi daga Motar ya mara mata bata, hannunta ta ji an finciko har sai da ta kusa faɗuwa, ido warwaje ta ɗago don ganin wanda ya yi mata wannan Aikin, da sauri ta yi baya jikinta ya fara kakkarwa cikin rawar baki ta ce "Ramadan???"
"E, Ramadan, wuce mu tafi gidanmu ko kuma in gwada ƙarshen asalin rashin imanina akanki.
girgiza kai ta yi tare da fara kuka ta na cewa "Ko me za ka yi mini ba zan taɓa binka ba azzalumi."
ba ta gama rufe baki ba ta ji saukar wani lafiyayyen mari wanda ya sa ta ganin taurarin azabu su na yi mata lilo. cike da mugunta ya ce "Ko a da ba ƙaunarki na ke ba bare a yanzu da nasan Shahbeer ya riga da ya mutu akanki, idan bakinki ya ƙara kirana Azzalumi ki tabbata sai na faffasa shi, wuce mu je ko kuma inyi abin da zan iya."
Ido ta zuba masa ta na tunanin Shahbeer da ta ji ya furta, wai shin da gaske ba Mutum ɗaya bane?? sai yau ta lura muryarsu ma akwai bambanci duk da ba wani mugun sani ta yiwa Shahbeer ɗin ba. hannunta ya kama ya fara janta, ta maƙale cike da ƙarfin hali ta ce "Ba zan bika ba ka yi duk abin da za ka yi."
Kyawawan maruka guda biyu a jere ya bata sannan ya ƙara kama hannunta ya ja ta zuwa Mota, in banda kuka ba abin da ta iya yi don kuwa ta maru.
kai tsaye gida ya nufa da ita ya na shiga ya fara ƙwalawa Mama kira ta fito da sauri ta na tambayara, turus ta yi ganinsa tare da Halima lokaci ɗaya Annurin kan fuskarta ya gushe "Ina ka tsinto wannan kuma?? kar dai ka ce mini ka bar baya ba zani??"
cikin ɓacin rai da tsananin tsanarta ya hankaɗata wajen Maman gami da cewa "Ashe ta sama na yi tufkar ta ƙasa ta warware, Yadda na so ba haka na samu ba, wai Mama wannan yarinyar ta haifawa Shahbeer GUDAN JININA abin takaicin ma Shahbeer ne ya raineshi kuma ya raɗa masa sunansa Mukhtar Sannan ya yi masa laƙabi da Shahzad, na yi niyar muzguna masa ta hanyar Ɗana masa tarko da Halima ashe wai ta manta komai sai yanzu ta tuna, amma ba komai tinda ya na sonta ni na samu gamsashshiyar Hanyar da zan Ƙuntatawa rayuwarsa."
Mama ta jinjina kai kafin ta ce ''To yanzu meye shirinka?"
"Zan ɗaureta a wancan ɗakin, sai na ce ki bata abinci ko ruwa sannan za ki bata, wannan shine shirina, sauran kuma za ki gani daga baya.
ya na kaiwa nan ya fice daga gidan kamar zai tashi sama.
"Ɗagwas-Ɗagwas takun Amarya" Mom Safyan ta faɗa ta na dariya, Zakiyyat ta murmusa gami da cewa "Mom wace magana ma ki ka ce za mu yi?"
"Ke na manta, gashi yanzu lokacin miƙa ki ɗakinki ya yi, abin da na ke so da ke Zakiyyat ki yi amfani da damarki, Allah ya kawo mana WATA HANYA da zamu ƙara gyara Hanyarmu, ki riƙi Maalik hannu bibbiyu kar ki sake ki bari ya kuɓuce miki, kinga shi kaɗai ne Namiji a cikin ƴaƴan gidan guda uku, kinga kece Babba Za ki taka wanda ranki ya ke so, ga kuɗi ga jinkai, sannan ki dage ki ƙara ɗorashi akan turbar tsanar Su Shahbeer ta yadda
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 21 Chapter of 30