ku faɗa mini? me yasa ko ba ku da aikin yi ne da za ku tawo gurina? na ji sauƙi fa."
"To ai ko mu na da aiki mu masu ajiye shi ne don mu zo mu ganka, Don Allah ka fito mana kar ka sa mu karaya.
"Ai gani nan zuwa.
kafin ya yi magana ya ji ana ƙoƙarin buɗe ƙofar don haka ya fasa ya katse kiran.
Bayan sun gaisa da Maman Ramadan ta ƙara da cewa "Ya ɓangaren Mahaifinku kuma?"
"Shi kam ya na lafiya Safyan ne dai ba mu san halin da ya ke ciki ba don wuyar gani ya ke Mamarsa ta ɓoye shi.
Shahmeer ya faɗa cikin ko'inkula
"To Allah ya ƙara masa lafiya, yaushe ne Auren naku? an nemawa Shahzaib Abokiyar haɗi, Allah ya sanya Alkairi ya bada zaman lafiya.
Shahbeer ya amsa da 'Amin' sannan ya ci gaba da cewa "Ya kamata a haɗa da Yayanmu don ya girma da yawa, kin ga ni yanzu Ta biyu zan yi ma."
ta yi dariya gami sa cewa "Ai in lokacinsa bai yi ba dole sai haƙuri Inya!, amma idan ka na da Ƙanwa ko Abokiyar kirki mu na ciki don na yarda da zaɓinka duk wadda ka bashi sai mu yi godiya."
"To ai ni na siyar"
Ramadan ya faɗa ya na dariya.
Shahmeer ya ce "Ka sayar da me? ba fa labarin kasuwanci ake yi ba."
Shahzaib ya ce "Kai fa Ajawo ne wani zubin, tin da ba ka kwashe ba gyara mini gefensa in ji wacece ta saya?"
Shahzain ya ce "Gaskiya kuwa, Wacece Ɗan-uwa? amma fa komai son da ka ke mata in ba ta yi nana ba za ka canja."
ya ce "Abu ne me sauƙi ai, bare ma na san za ku so ta."
Mamar Ramadan ta ce "Allah ya yi mana me kyau dai kawai." su ka amsa kafin su ci gaba da hira.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya Kwanaki su na wucewa lokaci ya na shuɗewa.
Fakatan-fakatan Safyan ya shigo ko sallama babu ya tsaya mata aka, a masife ya ce "Mom wai meye ke faruwa haka ne?, duk wannan bala'in da mu ka faɗa amma ki ka zauna ki na cin Abinci?? anya kuwa ba turin jeka ka mutu ki kai mini ba?"
"To Safyanu idan ban ci Abinci ba da yunwa ka ke so in zauna?? ji mini Ɗa, ko meye ma ya faru ai laifinka ne tinda kai na bawa wuƙa da nama.
"Yadda fa ki ke tunani ba haka bane, Komai fa namu ƙasa ya ke yi a kowane Minti na Duniyar nan, kinsan cewa yanzu tamkar wutar karmami haka duk wannan Dukiyar da mu ka tara ta zama??, kullum ƙarewa ta ke yi na ma rasa ina take tafiya.
cikin sauri ta miƙe tare da cewa "Kan Ubancan!!!!!, Me??? ka na nufin duk zaman da na yi tare da Basiru don in tara Arzikin kaina ya zama na banza?, Ina Babanka Alhaj Salahu ?"
"Bazawarinki dai ta ina ya zama Babana? Ɗan wahala shege ya ɗebi rabonsa ya tsallake, nifa na gama shiga tashin hankali Mum kwanan nan wasu abubuwa na ke gani na tashin hankali, ni ba ma ta Dukiyar kawai ba ji na nake kamar wani zautacce.
"Eh, Lallai Salahu, na kashe Auren da ke tsakanina da Basiru don shi amma sai ya kwashi Dukiyata ya gudu? in ya isa Allah i ƙona ni, gashi komai ya yi ƙasa ko? ai kuwa gurin Bokan zan je sai dai ayi duk wadda za'ayi .
"Ai gwara ayin ko ma me za'ayi don rayuwata ba za ta yuwu ba idan ba kuɗi.
Jaɓar ta koma ta zauna, wata muguwar zuffa ta wahala ta na karyo mata.
Shukriya da Ma'arufa da Malika su na Falo su na hira Su Dada su ka yi sallama, Da sauri Shukriya ta miƙe ta na cewa "Wa na ke ji haka kamar Innajo Matar Baba Aminu??"
Dada ta na dariya ta ce "Ai har da Baba Aminun har ma da Baba Habibu, sun yi tattaki zuwa ga ƴarsu."
ihu ta buga kafin ta yi ɓangarem Mommy da gudu ta na murna.
Ma'arufa ta yi ƙasa da kai ta na ɗan murmushi.
Malika ta miƙe cikin fara'a ta ce "Sannunku da zuwa Hajiya Dada, ku ƙaraso ciki mana."
Ƙarasawa su ka yi Ta basu gurin zama su uku ne Mata har Dadan.
Malika ta ce "Ina su Baba Aminun fa? ai su ma su shigo kar su zauna a waje."
Innajo ta ce "Wannan ita ce Kishiyar tawa?"
Dada ta ce "E Innajo ita ce, ita ma ɗayar Kishiyar taki ce amma ba'a kai ga ɗaura Auren ba tukunna."
Cike da ƙauna Innajo ta ce "Kai Madallah, a gaida ƴan Albarka, Ashe shi ya sa ta ke ƙoƙarin ƙwace mana mazajen ai kuwa dai da tsohuwar zuma ake magani ba zai ce ya na so ba."
Dariya Malika ta yi gami da cewa "Cikin sauƙi kuwa zan ƙwace su, sai ma na zaɓi kyakkyawan ciki tukunna."
Gwaggo ta ce "Ai kuwa ni na yarda ki ɗauki tsohon ki bar mini sabon jini."
Dada ta ce "O, an shanya su Baba a waje."
Malika ta ce "Ma'arufa shigo da Ƴan Samarin nan, ki zaɓi ɗaya tin kafin ku shigo."
ta ce "To" sannan ta fice.
Mommy ce ta ƙaraso tare da Shukriya da Inna cikin sauri.
Gurin Innajo ta nufa ta faɗa jikinta gami da fashewa da kuka ta na cewa "Innajo ashe zan ƙara ganinki?, ban yi tunanin zan yi tsawon ran da zan ƙara ganinku ba Innajo.''
Innajo ta share ƙwallah kafin ta ce "Meye na kuka Shatu, ai abin duk ya wuce nan, Ranar farin ciki ai ta fi gaban kuka, ki yi haƙuri ki dena ki bamu damar ganawa mu yi farin cikin da ba mu yi ba a baya.
Baba Aminu ne su ka yi Sallama, Ma'arufa ta shigo da su gami da basu gurin zama, Kasa zaman ya yi sabi da ganin Ƴarsa na kuka.
da sauri ta dawo gurinsa ta durƙusa a gabansa ta ƙara fashewa da wani sabon kukan.
"Ki yi haƙuri ki bar kuka, Aisha ai ba abin kuka bane farin ciki ya kamata mu yi tinda Allah ya haɗamu.
Baba Aminu ya faɗa cike da tausayin Ƴar tashi.
Baba Habibu ya ce "Haba Aisha, in ki na kuka me zai hanamu yi muma? ki yi haƙuri."
Gwaggo ta share ƙwalla kafin ta ce "Ai kuka ya zama dole sai dai kawai ayi haƙuri a danni Zuciya, Allah ya huci Zuciyarki Ƴar Nan."
Baba Aminu ya ce "Tashi-Tashi maza zauna nan sama mu gaisa."
Miƙewa ta yi ta zauna kan kujera shi ma ya zauna sannan ya ce "Mun sameku lafiya?" gyaɗa kai ta yi ta na ƙoƙarin dakatar da kukan, da kyar ta ce "Ina Wuni Baba"
"Lafiya lau, duk ya iyalin ya bayan rabuwa?"
"Su na lafiya, Baba Habibu Ina wuni."
da sauri ya ce "Uhm Lafiya lau A'i ya juriyar abin da mu ka yi? to dai yau gashi kanmu bisa wuyanmu mun yi tattaki mun zo sabi da neman maslaha."
Kakalo murmushi ta yi me haɗe da ƙwalla, cikin rawar murya ta ce "Wannan duk ya wuce Baba Habibu."
Daidai lokacin su Shahbeer su ka yi sallama, curko-curko su ka tsaya ganin baƙi a Falon.
Innajo ta ce "Sannunku Yaran kirki, ku ne ƴan huɗun ko?"
kallon-kallo su ka yi murya ƙasa-ƙasa Shahzaib ya ce "Su kuma waɗannan waye ya gaiyato su?"
Shahzain ya ce "Suwaye to?"
Shahbeer ya ce "Ku dallacan, Kakanninmu ne fa, iyayen Mommy na san ba me gaiyato su sai Dadar can, da faskeken kanta."
harararsa Shahmeer ya yi gami da cewa "Kai ne ka halittar mata kan da za ka tanka mata?"
ya ce "To dai gaskiya ce ga girman kai ga shegen faɗin ran tsiya .
Malika ta ce "Ku ƙaraso mana, ko ba ku ganesu bane??"
"Ke mun ji" Shahzaib ya faɗa ya na sauke rumfar Ido.
ƙarasawa su ka yi bayan sun yi ciɗin-ciɗin da rai.
Har su ka gama gaggaisawa Mommy ba ta ƙara cewa uffan ba kuma ba ta fasa kuka ba, sai da su ka yi da gaske sannan su ka rarrasheta, Daga nan kuma su ka fara hirar yaushe gamo.
Yau Su Alhaji Basiru su ka je gidan Su Fatima aka tsayar da maganar Auren su Shahmeer, daga nan kuma su ka wuce gidan su Baban Halima domin tattaunawa da shi a ji ta bakinsa.
Inna ce ta rausayar da kai cikin nuna alamar ba ta ji daɗin abin ba ta ce "Ban so ku tafi yau ba wallahi, na so ku bari sai bayan Bikin nan da za mu yi."
Innajo ta ce "Kwantar da hankalinki Uwargida ai za mu dawo in dai Allah ya yi, har da sauran iyalu ma duk za mu zo bi'izinillahi."
Inna ta ce "Allah i yarda, to Allah ya tsare kwa gaishe mana da waɗanda ba su zo ba."
Gwaggo ta ce "In sha Allahu, ke dai Allah i saka miki da Alkairi, kin ƙoƙarta sosai akan Ƴarmu da Iyalenta."
Inna ta murmusa kafin ta ce "Ba komai ai yiwa kai ne, ba gashi yanzu komai ya wuce ba? nima wanda bai sani ba ba zai taɓa cewa ba ni da alaƙa ta jini da A'i ba tamkar Uwa haka na ke a gurinta; kai ai Aisha sai dai mu ce Allah i yalwata mata ni'imominsa Duniya da Lahira amma samun ƴa kamarta akwai wuya gaskiya.
Gwaggo ta ce "Ni ma na shaida Allah i yiwa zuru'unta Albarka.
ci gaba su ka yi da hira daga waccan sai waccan.
Ƙarfe 02:00 su ka ɗauki hanyar komawa, haka aka rabu cike da kewar juna.
Cikin watanni Uku na biki da aka sa an yi rabi tini an fara shirye-shirye don kuwa lokacin ba wuya.
"Shahzad!!!" "Baba gashi nan" ya faɗa cikin ɗaga murya yadda Shahbeer zai jiyo shi.
"Okay ya cewa Ummi Ta kawo wa Baba Coffee.
"To Baba.
juyawa ya yi ya koma bedroom ɗin Malika ta na zaune gaban Madubi ita ba kwalliyar ta ke ba sai afkin tunani, ba ta ɓata lokaci ba ta tashi ta haɗo masa.
Ta na miƙa masa Shahzad ya karɓe ya na cewa "Baba Shi zai sha."
Malika ta murmusa gami da cewa "Tsaya in kawo maka naka wannan na Baba ne."
karyar da kai ya yi ya ce "A'a"
Haɗe rai Shahbeer ya yi a tsawace ya ce "Bata ta ajiye mini mana!, ka san dai ba na son gardama ko?"
Da sauri ya saki ya na ficin-ficin da idanu gami da ɗan murmushi, murya ƙasa-ƙasa ya ce "Baba ya bashi ai."
Malika ta yi dariya tare da cewa "Wannan Ɗa akwai wayo Tubarkallah, wato idan faɗa ya fi ƙarfin shi sai ya maida shi wasa."
Shahbeer ya ce "Do Allah idan kin ba shi Coffee ɗin ki kai shi wajen Mommy ko Inna, saura kuma kar ki dawo da wuri ki barni anan ina shan Iska."
"To yanzu zan dawo bani ɗan lokaci, dama ina so mu tattauna akan biki.
ɗan ƙaramin tsaki ya yi kafin ya ce "Ke ta bikin ma ki ke ba ta ni ki ke ba? sai kin gama ɓata mini lokaci kafin ki tafin.
"A'a ai yanzu zan tafi; ko ta me zan yi ai a bayanka ya ke Noor."
Kurɓar Coffee ɗinsa ya yi ya lumshe ido sannan ya ce "Sai da Safe Shahzad."
_________
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
*INDO*
[1/16, 12:53 PM] INDO CE: *WATA HANYA*
42
Ayeesha Abdulkareem
*(Indo ce..)*
ELEGANT ONLINE WRITERS.
Alhaji Boza ne zaune ya yi shiru ya lula Duniyar tunani, Mommy ta iso gurin ta zauna kusa da shi kafin ta ce "Ka na yawaita tunane-tunane kuma ba ka sanar wa wani abin da ke damunka ba."
"Me ya sa zan sanar wa wani haka kawai in hana shi farin ciki?"
"Hmm, ai Abokin kuka shi ake gayawa Mutuwa, ni dai ina ƙara gaya maka tunani ya na illa musamman ga kai da kake da matsalar Zuciya.
ya jinjina kai kafin ya ce "Haka ne Hajjaju, Amma Kwana nawa ne zan dena? ki kwantar da hankalinki indai tunani ne kwata-kwata zan dena shi ya riga ya ƙare, ni dai Addu'arki kawai na ke buƙata." kauda wancan zancen ta yi da cewa
"Saura sati Ɗaya Auren yaran nan, hakan ba ya sanya ka farin ciki sosai?"
"Farin cikina ban san ta yadda zan iya bayyana shi ba, amma in ya na yawa har ya yi mini; Allah ya sa za mu ga lokacin.
"Amin; Shahbeer ya ce ba ya ra'yin irin shagulgulan nan sosai ina ganin ranaku biyu ne kawai na bikin Rana ɗaya Dinner sai kuma ranar ɗaura Aure, hakan ya yi kuwa?"
"Ya yi, mu kam anan hakan za mu yi, kuma ƴan-uwan nasa sun Amince?"
"Babu me ja da hukunci idan ya yanke, tin daga yarintarsu har zuwa yanzu shi tamkar wani ginshiƙi ne garesu, dama mutane sukan ce a kowane Ahali ana cire mutum ɗaya zakka to ni kam ina tunanin tawa zakkar kenan, kowane ɗan-adam da irin baiwar da Allah ya bashi, Shi Shahbeer Shugaba ne kuma Jajirtacce.
Ya murmusa kafin ya ce "Ma sha Allah, na yi farin ciki da hakan, Ke ma da ki ka basu Wannan tabiyar Allah ya saka miki da Alkairi, Ƴar Baiwa Jarumar Uwa, wannan sunan shi ya fi dacewa da ke."
Murmushi ta yi kafin ta ci gaba da bashi labarin Shirye-shiryen biki.
"Ɗan Saurayi ba kai bacci ba?"
ta yi maganar cikin ƙasa da murya.
"Ta ya zan iya bacci tinda ban ji Muryarki ba, ki ce ke har kin rintsa, ohh kin iya baccin wuri gaskiya yanzu Goma ta yi fa amma naga kamar gani ki ke dare ya raba ko??"
Ƴar dariya ta yi gami da lumshe ido "Ban daɗe da yin sallar Isha'i ba na kwanta.
"Gobe za ki dawo nan don ina so Mommy ta dinga kulawa da ke da kanta yanzu lokacin ya kusa gwara ki dawo hannunta.
"To Ɗan Saurayi Allah ya kaimu goben, amma Maman Ramadan ma ta na kula da ni sosai.
"Duk daɗin Uwar wani dai ba ta kai ya taka ba, kawai ki ɗauka an gama, Daga nan kuma sai gidana.
Jin ta yi shiru ya sa shi cewa "Baccin ki ka ƙara yi ne?"
"A'a sauraronka na ke.
"Shine ki ka mini shiru?, kar ki sa in taso in zo yanzu fa.
da sauri ta ce "Yi haƙuri Ɗan Saurayi, dare fa ya yi ba na son wahalar da kai."
"To na haƙura, kwana bakwai dai i yanzu kin san dai kina Ɗakina wala-alla ma.... to dai bari nai shiru.
"Ai gwara dai ka yi shiru"
ta faɗa ta dariya.
Hira su ka ci gaba da yi cikin ƙauna da kwanciyar hankali.
Yau ta kasance Ranar Ɗaurin Aure gidan ya cika ta ko'ina, dangi na nesa da na kusa duk an haɗu, Ɓangaren Mommy da Ɓangaren Alhaji Basiru Boza duk sun haɗu ƙwansu da kwar-kwatarsu.
A ranar aka Ɗaura Aure da dare aka raka Amare Ɗakinsu, a washegari Baƙi su ka fara bajewa zuwa kwana biyu gidan ya rage daga su sai halinsu.
"Kin dena Magana ne?"
kallonsa kawai ta yi ta kauda ta na cinno baki gaba, ya yi dariya kafin ya ce "Allah ya huci Zuciyar Sarauniya, Na yi laifi ko?"
Tattaɓe baki ta yi za ta fashe da kuka ya yi saurin dawowa kusa da ita ya na cewa "Ayya, Fatimata Don Allah kar ki yi kukan nan, wallahi ba zan ji daɗi ba, Farin cikinki shine abin da na fi so."
cikin Shagwaɓa ta ce "Ba dariya ka ke mini ba? kuma yau ƙafata ciwo ta ke yi kuma sai na wuni ina kuka."
"Subhanallah, Wallahi Ba zan rabu da tashin hankali ba kuwa indai ki ka wuni kina mini kuka, Indai dariya ce na dena tashi ma zan in je gaida Su Mommy, tashi mu je tare."
Noƙe kafaɗa ta yi ta ce "A'a ni kunyarta na ke ji."
"Kunyar Mommy ki ke ji Habibty?, ai kuwa ki dena don ita a matsayin Ƴaƴanta ta ɗauke ku, ina ganin ma ta fi sonki Akaina duk da kasancewata Jariri."
dariya ta yi kafin ta ce "Jariri kuma ka na amsawa, idan muka Haihu fa sai a rasa wannene Ɗan Wannene Uban."
zaro Ido ya yi ya na dariya ya ce "Kai Fatima daga yin abin kuma sai Haihuwa? Allah i sa Ƴanhuɗu ne, kai amma fa na ji daɗi."
tafukan hannunta ta sa ta rufe fuskarta ta na dariya cike da kunya.
"Ashe dai ana Sona har haka? Ra'ayinmu iri Ɗaya ne nima ina Matuƙar son inga gudan jininki Habibty.
da sauri ta tashi za ta bar masa wajen ya yi saurin riƙo hannunta ta faɗa jikinsa, "Nima kunyar tawa ki ke ji?, to ko a garin Fulani dai inaga ban taɓa ganin me Kunya irinki ba.
"Don Allah Shahmeer ka je ka dawo kawai.
"Za fa ki dena indai kunya ce"
ya yi maganar ya na kallon Fuskarta, sabuwar ƙaunarta ta na ƙara ratsa Zuciyarsa, haƙiƙa wani hanin ga Allah Baiwa ne, zai iya cewa sai yanzu ya san Asalin Ƙauna da ya faɗa Son Fatima. "Ina Sonki Fatima, So na Asali nake miki ba kame-kame ba"
Ya yi maganar ba tare da ya san ta fito ba.
Ido ta zuba masa kamar yadda shima ya zuba mata, cikin tattausar Murya ta ce "Ina Sonka, fiye da yadda na ke son kaina mamallakin Zuciyata, Mijina Abin Alfaharina a koda yaushe."
Idanunsa ƙasa-ƙasa ya fito ya na sanye da Ƙananun kaya farar riga da baƙin wando.
kai tsaye kicin ya nufa don ya san ba ta wuce can.
Bai yi motsin da za ta san ya shigo ba kawai sai ji tayi an rungumeta, ta ja wani firgitaccen Numfashi, ta matuƙar Tsorata, cikin sauri ta ce "Innalillahi!!!"
"Mijinki ne dai ba wani ba"
ya faɗa ya tare da kwantar da kansa saman kafaɗarta.
ta murmusa gami da sauke ajiyar Zuciya sannan ta ce "Zaib wallah ka tsorata ni matuƙa, gabaki Ɗaya na tafi tunani."
"Tunanina ki ke yi?"
"Uhm, a'a akan me zan yi tunaninka?, ni Tunanin Mijina na ke yi, dama ya san ina nan ne?"
Murmushi ya yi kafin ya ce "Dama na san ba abin da za ki tuna sai shi, nima tunanin Matata na ke yi don haka ma Zuciyata ta gaya mini ta na Kitchen don ita Sarauniyar girke-girke ce, ko me ta ke dafawa?"
"Ba zan faɗa maka ba.
"Idan an gama zan gani dai Ƴar Farar Matata, nikam ban tambayeki ya gajiya b...
da sauri ta katse shi da cewa "Turarenka ya na da daɗin ƙamshi."
"Wai da gaske??"
"E.
"Ina zuwa Farar Matata, bari in je gurin Mommy.
"Ka gaisheta kafin na zo.
"To" ya faɗa sannan ya fice.
A Falo ya tarar da Shahzad, Inna, Malika su na sha'aninsu, ya gaida Inna kafin ya ce "Mommy ba ta fito ba?"
"Ba ta fito ba Shahzaib, Kai kuwa gararin bikin nan da ta sha ma kaɗai ya isheta.
"To Inna.
Malika ta ce "Ina Ƴar-uwata?"
"Ta na kicin kinsan Ita da Kicin Hassan da Hussaini suke.
Murmushi ta yi kafin ta ce "Idan ba ta yi ka ce ba ta yi ko?, ai ta burgeni."
"Dole ta burge ki tinda macece Inda Namiji ne cewa za ku yi iyayi ne ya sa baya gajiya da aikin amma tinda Ciwon Ƴa Mace na Ƴa Mace ne dole ki ce daidai ta yi.
Dariya kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba.
Inna za ta yi magana Isowar Shahbeer da Halima ya dakatar da ita.
"Tantabaru iyayen Soyayya" Inna ta faɗa ta na Murmushi.
''Inna Ina kwana Ya gajiya ya tsufa ya Kishi?"
"Ba zan amsa gaisuwar nan ba" ta faɗa gami da juyar da kai gefe. ya ce "Kin yiwa kanki, in ta wuce dai sai ta wani lokaci gwara ki amsa ko kya rage Zafi."
ta ce "Oho dai."
Kusa da Malika Halima ta wuce sai da ta zauna sannan ta gaida Inna, maida kallonta ta yi kan Malika kafin ta ce "Na ɗauka ki na Ɓangarenmu na je nemanki."
ta murmusa gami da cewa "Na tawo Nan gurin Inna daga ni sai Shahzad mun kaɗaice da yawa, gashi a sabon guri ne kinsan idan ka saba da guri kuma ka canja sheƙa kafin ka ji daidai za ka ɗau lokaci."
"Gaskiya kam, Ina kwana"
"Kin tashi lafiya?"
"Lafiya lau; Ya Shahzaib Ina kwana.
"Ahh Lafiya ya Amarci?"
ƙasa ta yi da kai ba tare da ta yi magana ba.
Shahbeer ya riƙo hannunsa kafin ya ce "Ina ka baro Beautyn ne?"
"Tana kicin" ya faɗa ya na dariya.
Murmusawa ya yi kafin ya ce "Ya Ramadan fa Kullum Laulayi ya ke, na tsorata Sosai Ƙarami."
danne nashi tsoron ya yi ya ce "Ban sanka da tsoro ba fa, kar ka damu ba wanda ya isa ya yi mana abin da Allah bai so ba, mu yi haƙuri mu karɓi duk yanayin Ƙaddara da rayuwa ta zo mana da shi, wata rana dole farin ciki za mu wata ranar mu yi baƙin ciki, Idan mun rasa Ɗaya daga cikinmu ba hakan ya na nufin za mu yankewa kanmu farin ciki ba ko da kuwa Nine na mutu."
Dogon nimfashi ya ja sannan ya ce "Kaico, Allah sarki Babanmu, ya riga ya jawo ruwan da zai cinyemu gashi yanzu abin dame shi. Rayuwar da Ba tsoron Allah kuma ba dogara da shi ba ta da wani amfani Mutuwa ta fi ta sauƙi, Ya Allah kar ka bamu ikon aikata Zunubi ko yaya yake."
"Amin" Shahzaib ya faɗa cike da damuwa.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya ana kwana ana tashi.
Mom Safyan ce tsugunne a gaban Boka ta gama yi masa ƙorafi akan Dukiyar da su ka tara, Bayan ya gama saurararta ya ce "In faɗa miki gaskiya?"
gyaɗa kai ta yi a tunaninta mafita zai bata sai ta ji ya ce "Duk abin da aka gina shi ta WATA HANYA ba me kyau ba, to ƙarshensa rusashshe, ke kanki ma za ki ga yadda Allah zai yi da ke bare Dukiyar da aka sameta ta hanyar zubda jinin dabbo da kuma wata mace, ki sa a ranki taki ta ƙare, ni ma nan da ki ke ganina na riga na san ba zan yi ƙarshe me kyau ba; kuma ku ne ku ke kawo mana mu na yi da ba kwa zuwa da ba mu yi wani abin ba don haka ni da ke ba bambanci duk sai Allah ya kwankwaɗa mana Azabarsa."
"Kutmar Ubanka, Tsinanne la'ananne, haka ma za ka ce mini? me ka maida ni ne? to wallahi sai na yi maganinka, har ni za ka faɗawa haka dan na zo neman mafita, dan Uwarka ka san ba za ka iya yin komai ba ka fara aikin?"
"Hhhhhhhh ni ba me imani bane, Zuciyata tamkar kauɗa haka take sabi da Bushewa, kin zagowa kanki Bala'in da ya fi karfinki, za
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 28 Chapter of 30