Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Allah i kyauta, ni dai ka ga tafiyata zan je in ce ba za ka ci ba. bai ce komai ba ya ƙara gyarawa Shahzad riƙo, a memakon ta bi Inna sai ta tsaya ta na kallonsa shima ya dakata da abin da ya ke yi ya zuba mata nashi idanun. ganin ba walwala a tare dashi ya sa jikinta ya yi sanyi ita dai a tunaninta ta na matuƙar Son Shahbeer amma fa ba ta ƙaunar ganin Shahzad musamman idan ta ga Shahbeer ɗin ya na ɗaukarsa gani ta ke kamar ya na takura mata duk ƴan kayan zaƙinta tare da shi ake shanye. "Halima Zo" ya faɗa gami da ɗan yi mata murmushin da bai wuci kan laɓɓa ba, ganin haka ya sa ta yi saurin ƙarasawa ya riƙo hannunta ya zaunar da ita kan kujera sannan ya zauna a wadda ta ke kallon ta-ta. "Baba wannan ne?" "A'a kece dai, kar ki ƙara dukar min Ɗa tin da ke ba ki san ciwonsa ba ni Ina son Kayana. tattaɓe baki ta yi ta na shirin ɓare baki "Ni ba na son shi. Ƙara girma idanunsa su ka yi da sauri ya ce "Da gaske wai?, Raina ɓaci ya ke idan ki na cewa bakya son shi ɗinnan, ba dan Allah ya jarrabeni da Sonki ba da na karɓe shi kema na haɗa ki da Babanki can ku yanka tin da kema bakya tausayin Ɗan wani." juya masa baya ta yi alamar ta yi fushi, bai ce komai ya ci gaba da ririta Shahzad. su na nan zaune har ta gama Fushin ta juyo, tsam ta yi ta na kallonsa yadda ya ke motsa bakinsa ya na yiwa Shahzad Magana ya fi komai tafiya da tunaninta, ba ita ya ke wa maganar ba amma ita ke murmushi sabi da farin ciki da jindaɗin Maganar tashi. ya na ankare da ita ya yi kamar bai ganta ba; ba zato ba tsammani ya ji bakinta akan nasa ta na rarumar Leɓensa. Rintse ido ya yi gami da furta "Subhanallah" ya na ƙoƙarin Ture ta Muryar Mommy ta ratsa kunnuwansa, "Shahbeer ya kamata ka san inda ke maka ciwo abin kunyar ya yi yawa Banda Ɗan Hannunka wani ka ke so ka ƙara samu?" itama jin muryar Mommyn ya sa ta yi zumbur ta ja baya ta yi firi-firi da ido. rungume Shahzad ya yi a cikin ƙirjinsa, Idanunsa su na neman zubda hawaye ya dakatar da su ta hanyar jan Dogon Numfashi ya sauke, lumshe su ya yi sannan ya ce "A'a Mommy." Zama ta yi kan kujerar da Halima ta tashi cikin muryar kuka ta ce "Kowa ya yarda da kai har ni kaina, me ya sa ka ke so ka gurɓata yardar da mu kai maka?, Ga Ɗan da babu Aure aka same shi amma hakan bai zamo maka izina ba, Idan ba ka yi shakkarmu ko ka ji kunyar mu ba ai sai ka ji Tsoron Allah, shi yasa ban yi ƙasa a guiwa ba wajen yarda da batun Aurenka da Malika. a firgice ya ce "Malika??" "E Malika DR ya na Falo ya na jiranka kuma Amincewarka ya ke buƙata ni kuma ina buƙatar ka Amince masa da Amincewata." "Mum Malika fa Shahbeer ya na Sonta, Adalci kenan sabi da son Rai sai a shiga tsakanin shi da Ita?" "Kai ne ka ke da son kai Shahbeer, ko menene indai ƴan-uwanka su na so sai ka yi musu ba ka duba da cewar idan ka yi musu kaza wa ka taɓa haƙƙin wa ka shiga ko kuma za ka cutar da kanka, ba sai na faɗa maka ba na san Ka san Malika ta na Sonka kenan indai za'a bawa Ɗan-uwanka abin da ya ke so ita ta mutu? ai ba zai yuwu ba ita ma fa ƴa ce, kuma ka sani Dr ya yi mana Adalci a rayuwa ya wuce matsayin neman Alfarma a gurinmu haka ya rufe ido ya nema amma sai mu ce ga wasu ƴan dalilai namu?, Da ya yi ta son raina ma da bai tsaya bi ta kaina kawai ya tsayar da lokacin Aurenku ai Babanka ne, ka je gurinsa kuma ka gaya masa ka Amince, ba na son ƙara jin komai daga gare. Ya yi ƙasa da kai gami da cewa "To Mommy." miƙewa ta yi ta bashi guri ya kalli Halima lokaci ɗaya ya ji Zuciyarsa ta ƙara karyewa, kallon Shahzad ya yi cikin tattausar Murya Ya ce "Yanayi ya sa zan dangata Mahaifiyarka da wata, Ina Addu'ar Allah ya kawo daliliin da za'a fasa Aurena da Malika." ya na gama faɗen haka ya miƙe, "Baba!" ta kira sunansa kamar za ta yi kuka don kuwa ba ta son ganinsa cikin damuwa. juyowa ya yi kafin ya ce "Ki yi Haƙuri Halima Don Allah ki barni in tafi. bai jira abin da za ta ce ba ya ci gaba da tafiya. Dukansu su na Falon Amma banda Ma'arufa, jiki a sanyaye ya zauna kusa da Dr gami da gaishe shi, ya amsa cikin sakin fuska ya na shirin yi masa bayani Mommy ta ce "Na riga na sanar masa." girgiza kai ya yi gami da cewa "A'a Baba Shahme..." a tsawace Mommy ta ce "Ya isa haka!!, ban ce kar ka ƙara kawo min irin soke-soke nan ba?. na riga na Amince kuma kai ma ka Amince. miƙewa ya yi tare da cewa "Na Amince Baba amma don Allah ku bani Lokaci. "Ba zai yuwu ba hakan, iya lokacin da za mu iya baka bai wuce wata biyar ko shida ba, idan kuma ka yi wani takun zai dawo wata biyu" Mommy ce ta yi maganar cike da baƙin ciki da takaicin baƙar Alƙar da ke tsakaninsa da Halima. cikin hanzari ya fara tafiya gami da cewa "Okay Mamma." kafin su yi wata maganar tini ya yi nisa, wani ɗaki daga cikin na Falon nasu ya shiga ya kulle ƙofar, kwantar da Shahzad ya yi a kan gado sannan ya koma gefe ya zauna gami da dafe goshi, Wasu zafafan hawaye su ka shiga wanke masa fuska... Shahmeer tashi ya yi ya bar wajen cikin sanyin jiki, mukullin Mota ya ɗauka sannan ya bar gidan don kuwa ba zai iya zama ba abin zai yi masa yawa. "Yayar Babana ce, kuma ta na so in Auri ɗanta" "Ba za ta iya shiga tsakaninmu ba indai Allah ya yi tare za mu rayu don haka ki dena damuwa da ita. "Ta na da faɗa fa, kuma duk ra'ayinta su Abban nawa su ke bi. "Hakan ba zai firgita ni ba, ni dai ki yi min Alƙawarin ba za ki juya mini baya ba" Murmusawa ta yi gami da yin ƙasa da kai "Har Abada ba zan juya maka baya ba ina tare da kai na yi Alƙawari. "Na gode Shukriya Allah ya baki ikon riƙe Alƙawarin, zan iya tafiya yanzu?" girgiza kai ta yi alamar a'a sannan ta ce "Sai ka ci Abinci." bai yi musu ba ya gyara zama ta shiga shirya masa abubuwan da su ka yi masa ita da Fatima. "Don Allah ka barni in koma wajen su Umma" Ma'arufa ta yi maganar cikin marai-raicewa kamar za ta fashe da kuka, "Su na lafiya ba sa buƙatar dole sai kin je, yanzu ma ba sa ɗaya gidan na canja musu wani, ban Amince ki fita ba kuma kar ki fita har sai da izinina. Tin da ta ji ya kattafe ta haƙura, cikin ɗakin da ya zama nata ta shige gami da turo ƙofa. Shahzaib ya ce "Za ki yi ki gama ne, ba zan Aureki ba kwana biyu ki ce mini ina hanyar gidanku." ba tare da ya damu da fushin nata ba ya bar wajen. Shahmeer bai dawo ba sai 10:44pm a yanayin sa ne kawai za ka gane ya na cikin matsananciyar Damuwa amma hakan bai hana shi fara'a ba don shi ma'abocin Murmushi ne. Mommy, Inna, Shahzain, Shahzaib, Shahzad, duk su na zaune sai dai ba wata hira su ke ba wajen ya yi shiru, Gaishe da su Mommy ya yi kafin ya zauna, Shahzain ya ce "Ina ka shiga haka ba ka sanarwa kowa ba?" Ɗan gyara zama ya yi gami da cewa "Oil Company na je, kuma Aiki na yi." Shahzaib ya ce "Ka kyauta, amma ko me za ka yi ai sai ka sanar mana." "To ku yi haƙuri, yanzu dai ina Boss?" Basar da zancen Shahzaib ya yi, Shahzain ya fara ƴan kame-kame, Inna ce ta ce "Maganar gaskiya tin Da aka yi zancen Aurensa da Maalika duk ya sa kansa a Damuwa ko Abinci ma bai ci ba, da a ɗaki ma ya kulle kansa sai da mu ka dage sannan muka shawo kansa ya fito, yanzu haka ya na ɗakinku. Murmushin ƙarfin hali Shahmeer ya yi gami da cewa "Ayya bari in je" Mommy ta ce "Son Zuciya ne ke naman illata mini Ɗa, sabi da ya na so ya ci gaba da rarumen ƴaƴan mutane kawai sai in ƙi Aurar dashi, ai dama ina da niyya ko da ba Malika ba da sai dai ku ji na Aura masa wata kowacece ita. Cikin takaicin maganarta Shahzaib ya ce "Haba Mom me yasa ki ke son faɗen irin haka ne, abin da ya wuce fa ya wuce don Allah ki dena kallonsa da haka." ta ce "To Babana na dena." tashi su ka yi duk suka bar gurin. ya na kwance akan gado ya ɗora Laptop akan ƙirjinsa ya na dube-dube, Kallo ɗaya ya isa a gane baya cikin yanayi me daɗi; a kowane motsi nashi ji ya ke Zuciyarsa ta na yi masa Zugi. a gefensa Shahmeer ya zauna gami da cewa "Inya!" Ganin Shahmeer ɗin ya sa shi tashi ya zauna gami da riƙo hannunsa cike da ƙauna ya ce "Ina ka tafi Shahmeer?, me yasa za ka bar gida don ka na jin ba daɗi, ba na son hakan kar ka kuma, indai ni ne zan Aura maka Malika ko da hakan zai ....." Shahmeer ne ya katse masa maganar ta hanyar rungumarsa, cikin kuka ya ce "Ɗan-uwana kai Adali ne a gurin masu Adalci, ka tausayawa Malika kar ka hana ta abin da ta ke so, indai a kaina ne ni na haƙura, ba zan iya yi mata son da zai sa na tauye mata haƙƙi ba, Don Allah kar ka yi tunani akaina, ka tuna cewa itama Malika ƙanwarka ce, ka sama mata farin ciki Don Allah. "Ko da na Aure ta ba zan iya yi mata Adalci ba Jariri, Zuciyata ba ta gareta na riga na mallakawa Halima. jin ɗumin hawayensa akan kafaɗarsa ya sa ya ƙara fashewa da kuka hakan kuwa ba ƙaramin dugunzuma Hankalin Shahbeer ya ke ba. Su Shahzain ma jikinsu duk ya gama yin laushi tini su ka fara zubarda hawaye, Ganin hawayen Shahbeer ne ya sa duk nasu hawayen ya kasa zama a mazauninsa dole sai da ya fito, ba ƙaramin abu bane ya ke sawa a ga raunin Shahbeer bare har a ga hawayensa, bai yarda da kuka ba sam yakan ce kuka alamar rauni ce, tin ya na ɗan ƙaraminsa ya ke da taurin Zuciya ba azabar da ta ke sa shi karaya har a gane lagonsa, sai gashi yau RINTSIN SO (Na Ayeesha Abdulkareem INDO) Rintsin So ya sa shi zubar da hawaye. soshe-soshe Alhaji Boza ke yi cikin kiɗima da fitar haiyaci ya na cewa "Gani nan Gani nan Bokana gani nan, yanzu zan zo" mukullin Mota ya ɗauka ya fice a hanzarce; ko da Safyan da Mom su ka tare shi da tambayar inda zai je sai ya bangaje su ya wuce. kai tsaye ya nufi Sarƙaƙiyar Dajin da bokan nasa ya ke. sai da ya isa gabansa sannan ya ji hankalinsa ya kwanta akan Da da ya ke jin idan bai ga Bokan ba haukacewa zai yi. Boka ya yi dariyar mugunta sosai sannan ya ce "Kiranye!!!! Kiranyee!!!! Kiranye mu ka yi ma Basiru, Waye ya ce maka ana barin tsafinmu cikin sauƙi????? hhhhhhhhhhhh Tsafin mu zai daina tasiri akanka da wanda ka yiwa ne kawai bayan ka shayar damu Jinin Gudan jininka wanda ka fi so hhhhhhhhh cikin ƴaƴanka wanne ka fi sooooo?????" Fitsari ne ke neman tsiyayo masa sabi da asalin tsoratar da ya yi cikin rawar baki ya ce "Safyan na fi so" "Hhhhhhhh Ƙarya!!!! Ƙarya!!!!! ƙarya!!!!!!ƙarya ka ke Da ne ka ke son wannan amma yanzu MUKHTAAAAR¡¡¡¡¡¡¡¡ SHAHBEEER!!!¡¡¡¡¡¡ ka ke SO shi za ka bamuuuuu!!!!!!!!!!!" _________ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ *INDO* [12/26, 8:39 AM] INDO CE: *WATA HANYA* 25 Ayeesha Abdulkareem *(Indo ce..)* ELEGANT ONLINE WRITERS. Ambaton sunan Allah Alhaji Boza ya ke yi ya na neman temakonsa, a yanzu idan aka ce ya bada ɗaya daga cikin su huɗun ma ba zai iya ba bare kuma wanda ya fi ƙauna a cikinsu, tini ya fara kuka shaɓe-shaɓe gashi ya rasa abin da zai cewa Bokan. Ganin ya yi shiru ya sa Bokan cewa "Za mu kunna bala'i da Masifa a cikin Ahalinka har sai lokacin da ka shayar damu jinin Ɗanka, idan ka kasa bamu da kanka za mu nemo shi da kanmu, bama yafiya ba ma barin bashi, mun baka lokaci idan ba ka kawo mana shi ba za ka wayi gari ka ga gawarsa, ka tashi ka tashi!! mun sallameka." Hankali tashe ya bar wajen ba tare da ya san ina ya ke sa ƙafa ba, a jigace ya dawo inda motarsa ta ke sannan ya ɗauki hanyar gida. Shahzaib ne ya goge ƙwallarsa sannan ya ce "Don Allah ku dena kuka nan komai ya na ga Allah shi ya san me ke ɓoye a cikin hakan." Shahbeer ne ya yi ƙoƙarin tausar Zuciyarsa ya shiga rarrashin Shahmeer har ya samu hankalinsa ya kwanta. ............................................... ______________________________ Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya ba tare da komai ya canja ba, wani lokaci farin ciki wani lokaci baƙin ciki. A ɓangaren Alhaji Boza kullum cikin Damuwa ya ke tare da Nadamar Abubuwan da ya aikata a baya yanzu kuma sun dawo suna ta bibiyar rayuwarsa. Shigowarta gidan kenan ta fara jiyo Muryar Hajiya Dada gabanta ne ya yanke ya faɗi cikin sanyin jiki ta wuce ɗakinsu, ta ɗauki lokaci kafin ta daure ta fito don ta san ƙin zuwa gaida Dadan ma wani sabon faɗan ne. daga bakin ƙofa ta durƙusa ta gaisheta ta amsa ba tare da walwala ba, Mami da Abba ta gaisar kafin ta miƙe da nufin barin ɗakin Dada ce ta dakatar da ita da cewa "Zo nan." Gabanta na dukan tara-tara ta matsa kusa da ita sannan ta durƙusa ta sunkuyar da kai cike da shakkar abin da bakin Dadan zai furta. "Sannu Shukriya, na samu labarin kin samu ɗaya daga cikin Manyan Ƙasa kin yi fatali da batun Maalik, ki dena hangen matsayin da Allah bai kai ki ba indai kuɗi ne ko Dukiya to Maalik ya haɗa komai ba abin da za ki nema ki rasa to kuma me ki ke hari a nan gaba?? ko dan za ki so a dinga cewa ke ce Matar Ɗaya a cikin DOUBLE TWO STAR kamar yadda kafin yanzu ba ki da zance sai nasu, to maganar gaskiya ba zan lamunta ba kai Ibrahim. ta kai maganar gami da kallon Abba cike da son jin abin da zai ce. gyaran murya ya ɗan yi kafin ya ce "Haka ne YaYa, Shukriya Maalik ya kusan dawowa sannan kinsan dai Aurenku da shi kawai ya rage mana to don haka duk wata shiririta ki barta." Dada ta ce "Ba iya wannan ba, da a fusace na zo gidan nan don in yi miki dukan tsiya sai akai rashin sa'a bakya nan, to ki shiga taitayinki, indai ina a raye ba wanda za ki Aura sai Maalik don haka kar ki sa wani abin Duniya a ranki har ya zamo miki abin baƙin ciki." Cikin kuka ta ce "Wallahi ni ba abin Duniya nake so ba kawai ni ina..." tsawa Abba ya daka mata hakan yasa ta yi saurin rufe bakinta. "Hmm ai dama ya riga ya hure mata kunnuwa, ba dai ɗan gidan Alhaji Basiru Boza bane?? akwai shaiɗani sama da wannan mutumin a Duniya? ai idan ba ku yi a hankali ba wallahi sai an rabata da mutuncinta itama, wawuyar yarinya da ba ta san ina ke mata ciwo ba, Dukansu ba mutumin kirki a cikinsu gashi dai yanzu idanunku sun gani, yarinyar da idan anai mata faɗa ko ɗago kai ba ta yi amma yau itace mu ke faɗe ta na faɗe sabi da gangin shaiɗanin ya gama ratsa mata Zuciya, To Maalik gobe zai dawo sai ki shirya kuma da ya dawo kinsan zai zo ya ɗauke ki don haka ki kwana cikin shiri, tashi ki bani guri na dena ganin ƙyalli-ƙyallinki a nan. miƙewa ta yi a daddafe ta koma ɗakinsu, lokaci guda wani zazzafan ciwon kai ya sakko mata har duhu-duhu ta ke gani, zubewa ta yi a ƙasa gami da fashewa da kuka me cike da abubuwa kala-kala. ba shakka ta ji raɗaɗin magan-ganun Dada akan Shahzain gefe guda kuwa fargabar ranar da za'a yi mata katanga da shi ta ke yi ga tsoron Auren Maalik da baisan Dokokin Muslinci ba, tunane-tunane ta ke yi sosai cikin kukan, ba wanda ya rarrasheta har sai da ta yi me isarta ta dena, waya ta ɗakko ta shiga kiran Shahzain sai dai ba'a amsawa. "Ɗan nan ni dai har yau ban fitar da tsammanin ganin Halima a Duniya ba, jikina ya na bani ba ta mutu ba wata rana zan ƙara ganinta ta dawo gareni" Baban Halima ne ya yi maganar cikin tsananin tausayin kansa da ƴar tashi. numfashi Shahbeer ya ja ya sauke shi tare da wata zazzafar ajiyar Zuciya, Ba zan iya dawo da Halima gareka ba a yanzu don ji za ka yi inama ta mutu ba ka ga baƙin ciki ba, ni kaina da nake Namiji Mahaifiyata ta na nuna ƙyama gareni bare ita Mace, gashi ba ta haiyacinta ko za ayi mata me ba za ta yarda Baban nata shine Mahaifinta ba. tunanin da ya ke yi kenan a cikin Zuciyarsa, Baban Halima ne ya katse masa tunanin da cewa "Yarona ko dai kana tunanin ta Mutu ne??" yadda ya yi masa tambayar ya sa Zuciyarsa ta ƙara karaya. cikin ƙarfin hali ya ce "A'a Baba Halima ta na raye, in sha Allahu bayan wani lokaci za ta dawo gareka, Don Allah ka ɗauka tamkar ni ne ita kar ka damu Akwai lokacin da za ka ƙara ganinta." Baban Halima ya ce "To ɗana, ai yanzu ba ni da tamkarku kai da ƴan-uwanka domin kuwa kun yi mini komai a rayuwa, amma kaima sai na ga kamar ka na cikin Damuwa ko ɗan nan? ka ga ka ce ni Tamkar Mahaifi nake a gurinka to ka gaya mini kai ma abin da ke damunka." "Baba, Aure Mommy ta ke son yi mini kuma gaskiya ina da wadda na ke so. Baban Halima ya yi murmushi irin nasu na manya sannan ya riƙo hannun Shahbeer da nufin tausar shi, gabansa ne ya faɗi sabi da wani tashin hankali da ya tsinkayi Zuciyarsa a lokacin da ya riƙe hannun Shahbeer ya hangi abubuwa iri-iri a tattare dashi sai dai ba zai iya sanar da shi kai tsaye ba. Shahbeer ya ce "Baba meke faruwa? na ga kamar fuskar ka ta canja lokaci guda." "Ɗana ba komai, dama ina so ne in ce maka ba abin da ya kai yin biyayya ga iyaye indai har ba a kan turba mara kyau za su ɗoraka ba, idan ka yarda da zaɓinsu to Da yardar Allah ba za ka taɓe ba, ka yi haƙuri ka kawar da duk wani tunani da ka ke yi ka rungumi ƙaddararka a duk yadda ta zo maka; ko wace rayuwa ta na ƙunshe da irin nata ƙalu-balen Juriya da Haƙuri kuma su ne kawai maganin hakan ka Jure akan tafarkin gaskiya komai tsananin da ka iski kanka a ciki, ni dai ba zan so ka ƙi yin biyayya ga Mahaifiyarka ba, ka yi haƙuri ka Amince. Shiru ya yi ya na tunani har wani ɗan lokaci sannan ya ce "To Baba in sha Allahu komai ya wuce." "To Alhamdulillahi, bayan wannan ka kasance me Adalci da fita haƙƙin iyalinka ka ji?" "Zan kula in Allah ya yarda. Baban Halima ya ce "To Allah ya yi maka Albarka ya kare ka daga sharrin kowane irin shaɗanu. ya amsa da "Amin" Shahzain Ya na shigowa sashinsu ya yi karo da wayarsa akan tebur ta ci kuka ta ƙoshi ba'a kawo mata ɗauki ba, da sauri ya ɗauka ya na cewa "Subhanallah, Shukriya anya lafiya wannan jerin karan?" cikin sauri ya bi kiran nata har ta gaji ta haƙura, ta na fara ringing ta ɗauka don kuwa a hannunta wayar ta ke. Kuka ta saki gami da cewa "Sai kiranka na ke yi ba ka ɗauka ba." "Ya Allah, wallahi na barta a sashin mu ne ina gurin su Mommy don Allah ki yi haƙuri, meke faruwa na ji kina kuka??" "Maalik ne, Don Allah kar ka bari Hajiya Dada ta Aura mini shi ba na son shi kuma ta ce ya kusan Dawowa. "Amma akan hakan ki ke kuka haka?? haba Farin ciki, kar ki bari abin da bai taka kara ya karya ba ya soke miki sunanki, ban sanki da irin haka ba Don Allah ki dena kar ki sa Zuciyata ta karye nima. jerarriyar Ajiyar Zuciya ta sauke kafin ta ce "Na san idan ta ce za ta yi ba fashi shi yasa na ji tsoro sosai, ina matuƙar tsoron ranar da za'a shiga tsakanina da kai Zain, da kai na ke so na rayu kuma ina so in ƙare rayuwata har ƙarshenta a tare da kai. "Indai da rai da lafiyata Na yi miki wannan Alƙawarin har sai in ba raina sannan za ki rayu da wani wanda ba ni ba. Sosai maganar tashi ta sanyaya mata Zuciya kuma ta ji ƙwarin guiwar samuwar ƴancinta. sai da ya tabbatar ya kwantar mata da hankula sannan su ka yi sallama. Ya na juyowa su ka yi ido huɗu da Shahbeer hannayensa harɗe a ƙirjinsa ya zuba masa idanu. ƙasa ya yi da kai gami da cewa "Sannu YaYa." "Shahzain meke faruwa haka, kar ka ce za ka yi mini ɓoye-ɓoye alamunka sun nuna damuwa a tare da kai sosai. "Shahbeer Ni da ita mu na son junanmu sosai, amma YaYar Abbanta ta na so ta Aura mata Ɗanta, da ni da ita duk ba mu san a wane hali za mu ƙare ba

Chapter 16 of 30